Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "dan Allah ina Aneesah Ammi ta aikoni wajenta" murmushi tayi tace tana dakin su salamatu kaya ake chanza mata" da sauri yace "inane dakin?" Corridor ta nunamai hakan yasa yay corridor da sauri gabanshi nafaduwa har wani lumshe ido yake his eyes are eager to see her, kofar dakin dayagani abude surutu natasowa daga ciki yayi ahankali yakarasa bakin kofan tsayawa yayi chak yana kallon Aneesah dataci gayu sosai an mata hadadden makeup tasaka hadaddiyar doguwan riga na maroon and golds an mata daurin gwaggwaro daya mugun yimata kyau gashin gaban goshinta sun wani irin kwanta, tayi kyau kaman wata Celebrity, kayan jikinta sun mata kyau sunbi jikinta sosai, wata yarinya da ita kadai ke dakin tana daura mata agogo ahannunta dayasha wani hadadden lallen amare, chak numfashin shi ya tsaya kafin ahankali yadawo yawani irin sauke ajiyan zuciya, wani irin sanyi Aneesah taji ajikinta dayasa tadago kanta da sauri danji tayi kaman anbude fridge idanunta ne suka sauka akan wata katuwar doguwan matan dake tsaye abakin kofar dakin dasuke tana sanye da hijabi dakuma nikabi tasaka wani farin glass tana kallonsu, dan taba Salamatu dake samata agogo tayi hakan yasa salamatu ta dago kanta da sauri tace "menene Aneesah?" ganin inda Aneesah ke kallo yasa tawaiga ganin mata danikabi ta tsaya chak tana kallonsu itaba tai magana ba yasa tace "Anty lafiya wakike nema? Mama na gidan biki mune kawayen Amarya kawai ke fati a gidan nan" dago kafa ahankali Aliyu yayi yana wani irin kallon Aneesah data cigaba da gyara sarkan wuyanta tana kallon madubi tana murmushi da kanta dan ita kanta tama kanta kyau, lankwashe murya yayi da kyau gudun kar Aneesah ta dago ta yace "Ammi ta aikoni wajen Aneesah" da sauri Aneesa tadagokai ta kalleshi jin ya kira Ammi tace "Ammi na" gyadamata kai yayi yace "eh tace na kawo mata Ke yanzun nan komin hayaniyan dakuke na tabbatar nazo dake, Baffan ki dawani bakonshi da Ammi ki keson ganinki su uku, dauko hijabi kisa muje, ni muna girki ne ankusan daurawa" da sauri Aneesah ta kalli salamatu tace "ina hijabina salamatu?" hijabinta salamatu tabude wani jaka taciro tabata karba Aneesah tayi tasa hannu ta zare gwargwaron kanta dogon gashinta da aka daure dawani hadadden ribbon dayasha gyara ya sauko saida numfashin Aliyu yakusan daukewa ta zura hijabin tareda mikewa ta kalli salamatu tace "muje ki rakani" hararanta salamatu tayi tace "Inna biki wazaiji da bakin? Nidai kiyi sauri" juyawa Aliyu yayi yana tafiya ahankali Aneesah na biyeda shi suna fitowa falo akadau guda ana Amarya ina zaki, dariya Salamatu tayi tace "to iyayen gulma Ammi ke kiranta" suka fice lokacin ruwa yaragu saidai yayyafin da ake, sanin waje da maza yasa taja hijabinta gaba sosai suka fito tana biye dashi, ganin sunyi hanyar wajen layi yasa da sauri Aneesah ta cinmata tace "Ammi bata gidane?" gyadamata kai yayi yana make murya yace "gida da mutane suna gidanmu, chan layin dake kallon layin mu, motama sukasaka na dauko danna kawoki dawuri tace tundazu take kiranki dan salamatu tarakoki kizo baki dauka" da sauri tace "ayyah wayata na purse din salamatun ne saisa" ahankali suke tafiya haryakai wajen motarshi sai kallon hadaddiyar motan take yabude motar yace "yi sauri kinga wayana ma na vibration nasan ita ke kira" ko tunani Aneesah batayiba ta shige ya maida kofan ya rufe yazagaya da sauri ya shiga wajen direba ya zauna yay locking motar gabaki daya, sanan yatada motar batare daya ciro hannunshi daga hijabi ba yaja motar da mahaukacin gudu dahar saida Aneesah ta firgita gabanta nafaduwa sosai sai kallonshi take._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



6️⃣9️⃣ & 7️⃣0️⃣




Dudda batasan ko'ina ba dan ita bata taba zuwa kaduna da wayonta ba, sanan tsawon zamanta a gidan Baffa saida zasu kasuwa dawurin kapinta ne ta taba fitowa daga anguwan nan, but ganin yanda yake zabga gudu yasa gabanta yafara faduwa sosai ahankali tace "har yanzu bamu kaiba?" cikin muryan matan yace "yanzun nan zamukai, munkusa" sunyi tafiyan kaman na minti goma sha biyar saida yabari suka fita daga kawo sukadau hanyar zaria sanan ahankali ya gangara gefen titi yay parking tareda kashe motar, da sauri Aneesa datai wani irin danji tayi duk hankalinta yatashi ta kalli hanya ganin inda suke bakin dajinema kan hanya babu mutane ko daya awurin sai motoci dake gittawa daidai yasa da sauri tajuyo ta kallai gabanta nafaduwa sosai tace "anan ne Ammi na take?" ahankali Aliyu ya ciro fararen hannayenshi daga hijabin yakai hannun yazare glasses din kan idanunshi ya ijiye, wani irin bin hannunshi da kallo Aneesah take ga hannu wan farare tass kaman na ta mace kaman na namiji, ahankali yakai hannunshi bayan nikabin ya warware kullin tareda jan nikabin awanin irin hankali harya zareshi daga kan fuskarshi, wani irin mummunan faduwa da gaban Aneesah yayi saida tazabura tadafe kirjinta, dago jajayen idanunshi yayi yadaura akanta yana mata wani irin kallon So, shauki, kewa, kauna da bege dakuma fushi kafin ahankali yasa hannu yazare hijabin daga jikinshi gabaki daya ya yaye ya dunkule ya jefa a kujeran baya yajuyo ya kalleta yana gyara zaman riganshi, wani irin zabura Aneesah tayi kafin arude tasa hannunta ta shiga kokarin bude kofan motan danta fita daga motar, ahankali cikin sassanyar muryan shi yana kallon yanda take kicinyar bude motar yace "kozaki kwana kina kokarin bude kofar motar nan bazai taba abuduwan mikiba Fateema!" juyowa Aneesah tayi da sauri ta kallai hawaye yasoma taruwa a idanunta, gabanta nawani irin faduwa, bakinta narawa sosai tace "y.....y....ya akayi kasan inda nake?" kallonta yayi ido cikin ido wani irin azaban sonta na dakan zuciyan shi yace "inba dai aturbaya zaki boyeba ko ina abinda nakeso yaboye aduniyan nan zan iya nemoshi Fateemah!" yanda yake mata magana asanyaye kaman mara lafiya yasa taji jikinta yadau rawa, da sauri bakinta narawa har lokacin tace "k.....abude mini kofa nakoma gida yaune bikina kabude min kofa kafin afara nemana, kabude min nakoma gida" murya chan kasa yace "keda gida har abada Aneesah" wani irin kallonshi tayi hawayen daya taru a idanunta suka zubo sharrr, da sauri ta share hawayen tai dan murmushi tace "you are joking right? Please I take this as a joke, kindly take me back home Aliyu, kar kasa afara nemana agida, yanzun nan za'a dauramin aure" wani irin dukan gaban motan Aliyu yayi cikin fushi yay ihu dasaida ya firgitata yace "stop telling me yanzunan za'a dauramiki aure, bakida wani miji sama dani aduniyan nan cus I Love you, I love you Fateema, I love you" har zuciyanta taji kalaman I love you daya fadi mata, lumshe ido tayi da sauri tana hana kanta kukan dayake shirin zuwan mata tace "banason ka ni Aliyu, babu abinda zanyi dakai, babu abinda zanyi da wanda aka min shirin kisa akanshi, babu abinda zanyi da yaron da mahaifinshi yaturani gidan yari akai, Aliyu yanzu bada bane I don't want anything dat has to do with your family, so am telling you one last time bana sonka, bana bukatar ka arayuwata, kabudemin kofa nafita nakoma gida" wani irin girgiza mata kai Aliyu yayi yana dafe kirjinshi dakemai zafi kaman an yaba dalma akai yace "Anebaby! Society da invaders, my parents or yours, family issues ko abu makamancin haka are too small to break the bond of our love, Aneesah am sorry for abinda mahaifina yamiki, My Dad wronged you and I am sorry, I never wish for any of that to happen, kin manta soyayyar mu Aneesah? Have you forgotten the type of love we shared? Kin manta da salon soyayyar mu, kin manta da soyayyan mu Aneesah, are you willing to give it up? Are you willing ki saki soyayyan mu tabi iska sabida wasu? What about me love? Wat about my precious heart that knows no one banda ke? What about my soul, my body that yarns you only? Aneesah soyayyar mu, our love" shiru Aneesah tayi kuka kecin ta amma ina bazata yishiba, wani irin murmushi ciwo tayi tace "Aliyu kenan, mahaifinka yariga yaraba soyayyar nan dakasani, banda hakama ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu wata kyakyawar tsaftatatcciyar soyayya ta shigo, ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu akwai wata soyayya, IN BETWEEN OUR LOVE lies another love which I cherish, I have my man now da zuciyata ta aminta dashi, wanda mahaifiyata ta aminta dashi, yan uwana suka aminta dashi sanan suka soshi, mutumin daya rufamin asiri yasoni despite my flaws, he helped me rebuild my self and gain my confidence back Dr Hafiz Zaid, My husband to be wanda nake bala'in s........." "shut up!" Aliyu yamata wani irin mahaukacin ihu yana buga jikin motarshi kaman zai fasa da kafa, yasake ihu kaman wani zakin daji yace "shut up, stop telling me kinason another Man, Fateema u are my wife, u are mine, only mine, and am gonna show u that today, bakida wani miji inhar am alive a duniyan nan sama dani, ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu babu wata soyayya, babu wata soyayyar data isa ta shigo TSAKANKANIN SOYAYYAN mu, IN BETWEEN OUR LOVE lies no any love, you are mine Mrs Aliyu Hydar Gadanga, you belong to me, and inhar abu nawane baya taba zama nakowa, zuciyar ki na tareda sona we love each other, family issues ko anything is too small to break d bond of our love, we are connected, gap din da iyayenmu sukai creating ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu zamu ciketa, me and you are inseparable, and I love you very much" yana gama maganan yawani irin kunna motar kaman mahaukaci yajata, arude Aneesah ta kallai saikuma tasaki kuka tamugun tsorata da yanda taganshi yanajan motan ko idanunshi ma baya budewa da kyau tsabagen fushi da masifan zuciya, ganin sun cigaba da tafiya ne baimada niyyan komawa baya yasa tafashe da kuka tace "na shiga uku, ina zaka kaini Ya Aliyu, ka maidani gida, Ammi na zata nemeni, ka maidani gida" ko kallonta baiyiba sai gudun daya cigaba dayi, bakaramin bakanta mata rai abin yayiba, cikin fushi tanuna shi da yatsa hawaye nabin idanunta sosai tace "zakaja namaka illa wlh, Aliyu take me back home nagaya maka, wlh zanji maka ciwo" batare daya kalleta ba yace "do me a favour and kill me, ki aikani lahira shi yafimin da in bude idona naga kina auren wani wlh I will never allow that to happen saidai in bana numfashi" cikeda fada tai ihu tace "to me ruwanka dani haaa? I don't love you bana sonkai nace, dole ne, where are you taking me to, karabu dani, kaga Aliyu ka komar dani gida kona jimaka ciwo wlh" murya chan kasa yana numfashi ahankali ahankali kaman mai shirin suma yace "ki kasheni kinji Barkono" duk zuciyanta kasamai komi tayi dan gani tayima baida lafiya karfin hali kawai yake yana mata bala'in nan kaman ma baya gani da kyau sabida yanda yake kyapkyapta ido yana tuki da masifan gudu, fashewa dawani irin kuka tayi ta kife kanta akan cinyarta hankalinta ya matukar tashi tace "Aliyu me haka, me amfanin satoni dakayi? Baka da lafiya, ina zaka kaini eh? U are risking our lives, Aliyu dan Allah ka komar dani gida kar hankalin Ammi yatashi" dudda yanajin kukanta har zuciyan shi amma ko kala baice mataba harsukakai garin zaria yadauki hanyar gidan sarkin zazzau.








Harsuka kai gidan sarkin zazzau Aneesah kuka take, dogarawa ne suka tare motarsu agaban Gate din shiga cikin gida hakan yasa yay wining glass down, dogarin dake sanye da jan malummalum ne yazo yana leka motar yace "kai samari wakake nema kanada appointment ne koko bakasan gidan sarki mai daraja kake ba?" lumshe ido yayi ahankali sanan yabude, ahankali yace "acema mai Martaba Aliyu Ibrahim Muhammad ne, dan gidan senate president of Nigeria" yafada authoritatively, tsayawa chak dogarin yayi yana kallonshi kafin da sauri yace "gyara parking bari ashiga asanar dashi" yay maza yajuya daya daga cikin dogaran dasunkai goma awajen yaje yasama yamai magana a kunne da sauri dogarin yay cikin gida, parking Aliyu yayi agefe yanajin yanda take kuka har lokacin batare data dago kanshi ba dudda kukan natabamai zuciya amma baice komiba, lumshe ido yayi ya jingina da kujera ko kadan baida lafiya, almost 15min suna ahaka yaji anyi knocking tinted glass din motar nashi yaja glass din kasa, cikeda girmama wa dogarin haryana dan dukawa yace "angaishe ka yaron manya jikan manya, dan gidan hutu marika nijeriya kasarmu, Mai Martaba yace amaka iso zuwa fada, shigo da motar" kunna motar Aliyu yayi ahankali yaja motar cikin gidan sarkin, gidan kaman wata kasa tsabagen kyau da girma, parking yayi a inda ake parking yabude mota yafito dogarin na jiransu daga gefe, zagayowa ta inda Aneesah take yayi yabude kofar har lokacin kanta akasa, ahankali ya tsugunna ta wurin murya chan kasa ta yanda dagashi zai ita zasuji yace "tashi mu shiga ciki if not I will carry you a kafada na wlh" yitayi kaman batajishi ba hakan yasa yace "okay" tashi yayi ahankali tsaye yana tattare hannun riganshi yadaura hannunshi daya kan bayanta daya tawajen kafafunta zai dauketa da sauri ta tashi tana goge hawaye tana hararanshi da idanunta dasukai jajir duk hawaye yabata kwaliyan da akamata tace "wlh katabani saina wanka maka mari" murmushi yayi ahankali murya chan kasa yace "okay let's go in bakiso" fitowa daga motan tayi azuciye kaman zata bugeshi kamshin datake yi yawani bugi fuskarshi ahankali yamaida kofar yarufe yana binta da kallo, yakaraso inda take tsaye hannunshi yamika ahankali yakama hannunta ya rike ya kalli dogarin dake jiransu yace "muje" bugemai hannu tayi cikin kuka sosai amma yaki sakinta, ganin tafaramai gardama zatamai rashin kunya yasa yace "wlh zan dagaki, let's go" binshi tayi tana goge kwalla har aka kaisu durmemen fadan sarki dayaji kayan adon sarauta, wasu fadawa ne aciki, da kuyangu saikuma Sarkin Zazzau daya manyanta sosai danya tsufa tukup dake zaune kan kujeran sarauta yana kallonsu ga wasu bayi guda biyu dakemai fifita, faduwa kasa dogarin yayi yace "taakawanka lafiya sarkina sarkin zazzagawa, sarkin sarakuna, gashinan anshigo dashi" da kai sarki yamai alamu daya tafi hakan yasa yatashi yatafi, duk kukan da Aneesah take suna hada ido da sarkin tahadiye kukan tsaf dan gabanta ya mugun fadi, ahankali Aliyu yadan dukar dakai ya daga hannunshi. "barka da warhaka mai Martaba" gyadamai kai sarki yayi kafin ahankali cikin muryanshi na wayanda suka manyanta sosai yace "Aliyu, ina mahaifinka? Meke tafe dakai haka kwatsam kaman anjehoka? Wacece wanan atare dakai dake kuka haka?" yay maganan yana kallon Aneesah datama kasa magana sai goge kwalla take kanta akasa, cikin dakewan zuciya Aliyu yace "satota nayi Mai Martaba, yaune bikinta" shiru Mai Martaba yayi yana kallon Aliyun yanda idanunshi sukai jajir kallo dayama yamai yagane baida lafiya, sanan yasake kallon Aneesah, cikeda fikra irin na wayanda keda ilimin rayuwa yace "meke faruwa tsakanin mu biyun nan" ajiyan zuciya ahankali Aliyu ya sauke yace "sonta nake mai Martaba, itama kuma tana sona, iyayen mu sun sami matsala dake neman kawo nakasu a soyayyan mu dan aurar da itama yau zasuyi, bazan iya jurewa ba na shirya nai shigan mata naje na sato ta, nakawo ta nan dan kama soyayyar mu adalci da abinda yakamata" Aliyu yakarashe maganan ahankali yanadan taba kirjinshi dayakeji kaman zai tsage, ganin yana fama da ciwo yasa Mai Martaba bai cemai komiba yana kallon yanayin shi har na kusan minti hudu saida yaga yajanye hannun daga kan kirjinshi sanan yakira sunanshi cikeda natsuwa. "Aliyu, yimin magana da kyau, kafadi iyakar gaskiyan dakasani domin kuwa Allah nasama yana kallon mu gabaki daya, meke faruwa fadimani daga farko zuwa karshe kafahimtar dani" ajiyan zuciya Aliyu yasauke yace "mahaifina nada mata uku, wata hudu zuwa biyar dasuka wuce yakaro tahudu..........." anatse yake bama Mai Martaba labarin komi tundaga farko har karshe har zuwa Prison Aneesah da kuma yanda akayi yasato ta yau sanan yay shiru.






Kallon Aneesah mai Martaba yayi anatse yace "haka maganganun shi yake Fateemah?" gyadama mai Martaba kai tayi ahankali tace "eh hakane" shiru Mai Martaba yayi yana kallonsu, a ido kadai zaka gane irin son da Aliyu yakema yarinyar, shiru yadanyi sanan yafara jawabi. "Aliyu karkai tunani dan akwai kyakkyawan alaka tsakanina da mahaifinka zaka iya kawomin komi na dauka a'a sainai bincike, amatsayina na sarki inada ikon na aurar da yara irinku wayanda suke son juna tsakani ga Allah amma sabida wata matsala ko gaba dake tsakanin iyayensu da rashin jituwa yasa suka hana auren to a irin wanan case din, yaran kan iya kawo kansu gareni na wakilce su nakira shaidu na dauramusu aure abisa sunna, Fateema tambayoyin dazan miki yanzu shine zasusa na aurar daku dan haka kibani amsa tsakanin ki ga Allah, abinda kikeso shizan miki bazan taba miki doleba kinajina" gyadamai kai tayi ahankali tana goge hawaye, shiru Mai Martaba yayi yana jiran tasami natsuwa, wajen minti biyar yabata sanan yace "Fateema Bintu" ahankali tace "Na'am Mai Martaba" anatse yace "inaso ki gayamin tsakanin ki ga Allah, wanda zaki aura yau kina sonshi koko mahaifiyarki da Baffan kine sukace saikin aureshi? Kifadi mani gaskiya" hawayen daya zubo mata ta share, ahankali tace "nima bansani ba ko ina sonshi ko bana sonshi, amma Ammi na na sonshi tace na aureshi" shiru mai Martaba yayi yana kallonta, yay kusan minti biyu ahaka sanan yace "wanan karan ma baniso kimini karya kaman yanda kika amsamini tambayata ta farko haka nakeso ki amsamini ta biyun nan, tambayoyi uku kacal zan miki, me mahaifiyarki tace miki game da Aliyu?" shiru tayi tasa hannu ta share hawayen ta kafin cikin muryan kuka tace "ta...tace" tadanyi shiru kafin ahankali tace "tace inhar ita ta haifeni na manta da Aliyu arayuwata, zata nuna musu nima y'a ce kaman kowa kuma abin so, dan haka inhar ni yar halak ce babu abinda zanyi da dandan wanda yakaini gidan yari" takarashe maganan tana goge hawaye muryanta na rawa sosai, ahankali Aliyu ya lumshe ido he's so hurt kaman zai mutu yakeji, shiru Mai Martaba yayi yana kallonta duk tambayoyin daya mata na tattare da hikima, saida yabari ta natsu sanan yace "sai tambayata na karshe Fateema, inaso kigayamin tsakanin ki da Allah, Fateema kinason Aliyu?" da sauri tadago kanta ta kalli Mai Martaba ido da ido, anatse batare daya bari ta janye idanunta daga kanshi ba yace "karkimin karya, kinason Aliyu ko bakison shi" wani irin rawa kirjinta yafara kaman yanda na Aliyu ke dukan biyar biyar yana bala'in tsoron amsar dazata bayar, lumshe ido Aneesah tayi maganan ganun Ammi nadawo mata _"kicire Aliyu daga ranki, ki manta dashi, inhar nina haifeki keyar halak ce ki manta da Aliyu, baki ba Aliyu Aneesah, me zakiyi da yaron wanda yakaiki gidan yari"_ bude idanunta tayi ta kalli Mai Martaba tace "ba.....banason shi!" ji Aliyu yayi kaman an katsamai zuciya daga asalin jijiyan dake rike da ita tana lilo bayama jin kanshi, kallonta Mai Martaba yayi yanda tarufe fuska da hijabi jikinta na rawa sosai kana ganinta zakasan kuka takeyi, dauke kai Mai Martaba yayi ya kalli Aliyu dake gefenta yace "kaji amsanta ko Aliyu dan haka bazan taba iya auran da daya bayason dayaba sai in duka biyun keson junansu dan haka katashi katafi ita zansa amaidata gida iyayen ta suganta a daura mata aure, tashi katafi Aliyu" ahankali Aliyu yasa hannu yadafa center carpet din dayake zaune idanunshi nawani irin juyawa da kyar ya iya mikewa tsaye kara karfin kukanta Aneesah tayi sosai jikinta na bari, ahankali Aliyu yajuya yadaga kafa da kyar yay taku daya Aneesah nawani irin kuka da karfi, daga kafa yayi ahankali yay taku na biyu idanunshi na neman rufewa yana hanasu, taku na uku yadaga kafa zaiyi idanun suka rufe ruf yawani yanke jiki yazube asume arude Aneesah ta janye hijabin daga fuskarta ta waigo jin karan dataji, da sauri fadawan dake wajen suka zabura zasukai doki da hannu mai Martaba yamusu alamu karwanda yaje, wani irin kyafkyafta ido Aneesah tayi tana kallonshi ganin dai shine zube akasa asume yasa dawani irin gudu tamike. "Ya Aliyuuuuu" tsugunnawa tayi akanshi da sauri tasa hannu tajuyo dashi tana kuka sosai, ta bubbuga kirjinshi. "Ya Aliyu me haka? Katashi, Ya Aliyu dan Allah karka mutu kabarni?" arude tace "suma" wawwigawa tashiga yi ahaukace bottle water data hango agaban mai Martaba yasa ta tashi da gudu bamatasan inda kanta yakeba taje gaban mai Martaba tazuri ruwan tadawo da gudu tana kuka tabude bottle din ruwan ta yayyafa mai a fuska tana kuka sosai, ganin bai ko motsi ba yasa tasa hannuta kan fuskarshi tana wani irin sharemai ruwan fuskan tana kuka sosai tace "Ya Aliyun dan Allah katashi wlh ina sonka, ina sonka Ya Aliyuna, I love you so much wlh" ganin ko motsi baiyiba yasa tadaura fuskarta kan fuskarshi tana wani irin kuka mai tsumma rai hawayen ta na gangarawa suna sauka kan fuskarshi tace "Ya Aliyu dan Allah katashi, I love you so much, babu soyayyar data isa ta shigo TSAKANKANIN SOYAYYAN mu, I believe you, am yours Ya Aliyu na, wake up" tafashe da kuka sosai, dan motsin dataji yayi yasa tadago kanta ta kallai arude tareda kamo hannunshi tarike gam tace "Aliyu, am here wake up, inasonka kaji be stay with me" bude jajayen idanunshi dasuka kankance yayi yadaura akanta, fuskarshi tai cupping da hannayenta dasuka sha lalle sosai tana wani irin kuka ta gyadamai kai tace "yes I love you so much" hannunshi da baida karfi sosai yadaga yakai yatsar shi ahankali yashare kwallan datakeyi yana girgixa mata kai alamun tadena kuka, murmushi kuka tayi hawaye na zubowa ta gyadamai kai da sauri tace "okay bazan kara kukan ba" wani irin murmushi mai Martaba yayi ya kalli kunyangin wajen yace "adau Fateema akai cikin gida" ya kalli sarkin gida yace "akira likitan Mai Martaba sarkin gida, sannan akira jama'a yanzun nan suzo su shaida daurin aure tsakanin Aliyu da Fateema" da sauri kunyangin da mai Martaba ya tura suka karasa inda Aliyu da Aneesa suke suka daga ta sukace muje cikin gida a shiryaki za'a daura muku aure, ahankali ta share hawaye tana waigen Aliyu dake kallonta da idanunshi dasuka kasa buduwa duka, daga Aliyu fadawan sukayi aka kaishi kusada mai Martaba, fadawa da duka ma'aikatan gidan Mai Martaba suka cika falon danya bada izini akira kowa nan mai Martaba yadauka aure tsakanin Aliyu da Aneesah akan sadaki dubu dari dashi mai Martaba yabiya mai, wani irin ajiyan zuciya kawai Aliyu ke saukewa kafin hawaye su shiga saukowa daga idanunshi he just can't believe he's now Aneesah husband, wani irin nishi daya fara yasa Mai Martaba yace adaukeshi ayi chan wani kebantaccen flat da bakin Mai Martaba masu mahimmanci ne yakesawa akai wajen yasa aka kaishi daidai likita ya iso aka shiga dubashi, dubashi likita yayi tsaf sanan yamai allura bayan yama mai Martaba bayanin ciwon zuciyane da kuma tsantsan damuwa, saikuma zazzabi dan ruwa ya dakeshi amma wanan alluran zai saukar dashi, zai dawo da daddare yazo dubashi, godiya mai Martaba yamai sanan yatura kuyangi yace "ace in angama shirya amarya akawota bangaren mijinta".



_duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba, in kinason book dinan, chat me up 07012181461_
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



7️⃣1️⃣
_how to pay_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to my watsap number sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa bank zaku iya turo katin MTN_






_Gidan Biki_
Paracetamol Inna taballo tabama Ammi da kanta kewani irin ciwo zazzabi yarufeta

Please Login or Register in order to submit comment