Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaida Aneesa suke Dady yarufe motan ya shiga gaba yaja motar soja yabude Gate suka fita.


Haddan nada dan nisa da gidansu babban makaranta ne wanda yaran manyan mutanen abujan nan keyi, ga security agaban gate din dake tsare su dan yaran senators da sauran sune kafin azo ayi kidnapping a premises din wajen parking Dady yayi parking yafito yabude musu suka fiffito kowa yay hanyar ajinshi itakuma Aneesa Dady yace ta tsaya, saida duk suka tafi Dady ya kulle motar ya kalli Aneesan yanda yaga tai zuru tana kallon makarantan dan tamafi wani makarantan boko kyau yace "muje karkiji tsoro ba'a duka saidai in baka bada hadda ba, so you have to be serious kinji ko kidage inkika haddace Al qur'ani duk abinda kikeso inhar inadashi saina miki aduniyan nan" murmushi tayi cikeda jin Dady tace "to Abbana zan dage" daidai nan suka karasa principal office din ganin Dady yasa daga malamai ustazai guda biyu da principal din wanda yake tsoho gashi fari balarabe dan balarabe ne mai karantan duk suka tashi suna gaggaisawa. "Alhaji kaine da kanka" cikeda fara'a dan yasaba dasu yace "eh y'ata nakawo" "bismillah ku" zama Dady yayi yanunama Aneesa kujeran kusada shi zama itama tayi Dady yace "akaramakallahu ga y'ata nan, daga islamiyya har hadda nakeso asata" gyadakai malami yayi yana kallon Aneesa kafin ya kalli Dady yace "shikenan ba matsala, zamu gwada ta sai musan ajin daza'a sata" faduwa gabanta ya shiga yi, ya dauko form da sauran abubuwa yace "acike wanan agida gobe kokuma Ince sati mai zuwa sai abata takawo" "to, to shikenan" Al qur'ani yadauko yabude chan suratun Ma'ida shafi nabiyu yace "bismillah, karanta mini nan naji" karba Aneesa tayi ahankali hannunta har rawa yake, kafadanta Dady yakama yana murmushi yasan she's nervous which is normal ahankali yace "relax karkiji tsoro gani anan, karanta musu muji" gyadama Dady kai tayi tanajin natsuwa, ahankali tai gyaran murya tafara karantawa bata sauke ba amma t iya hada baki hakan yasa zata iya karanta ko ina a Qur'ani, shiru Dady yayi yana sauraran muryanta dake da wani irin dadi saida tagama karanta shafin sanan malamin yace "barakallahu fiki, masha Allah ina ganin zamu sata aji hudu dan tanada matsala da tajweed, mataki na biyar kokuma nace aji na biyar su sun kware a tajweed" gyadamai kai Dady yayi cikin gamsuwa yace "to to shikenan ba matsala" daya daga cikin malamin ya kalla yace "akaita aji" gyadamai kai yayi Dady yace "tashi kibishi ajinki za'a kaiki" gyadama Dady kai tayi tabi malamin suka fita shikuma Dady yabiya kudin komi both hadda da islamiyya almost 150,000 sanan yabiya kudin littatafan ta both na hadda da islamiyya dazasu bata kusan dubu talatin sanan yamusu sallama yawuce yatafi dama sabida Aneesa ne yasa yau yakawo su da kanshi direban dake kaisu makaranta yaje yadauko su daban me a gidan.


_duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa_

A parking lot yay parking yafito part din Aliyu yayi baya falo hakan yasa yay hanyar bedroom dinshi yana kwlamai kira. "Son, Gadanga gusar yaki" hannu yasa zai bude bedroom din Aliyu yariga shi ta hanyar budewa yafito yana sanye da white singlet sai white wandon shadda ajikinshi yana kamshi sosai da alamu yagama wanka ne, dan yatsine fuska yayi yace "kadawo Dad" gyadamai kai yayi yace "dauko rigan muje to" dan turo baki yayi batare dayace komiba yakoma ciki shifa yagaji da wanan daukan shin da Dady yake duk in yayi sabon aure yace sai yaje ya gaida matar, rigan yasako yafito ko saka boturi baiyiba tsabagen rigima da yakeji, fess Dady yasan rigima yakeji saisa yaki biyemishi yace duk wacce tafitar min da littafi waje Ban yafemata ba wlh "mugani ka manta baka saka boturin rigan ba" yay maganan yana makala boturin yace "kayan sun maka kyau Gadanga, telan yay kokarin wlh, yana cikin kayan da Abdul yakaima dinkin ko" gyadama Dady kai kawai yayi yace "eh" suka fita daga dakin sukai hanyar part din Ammi bude kofa Dady yayi da sallama ya shiga Aliyu biyeda shi, ahankali yasa kafanshi ya shiga dakin wani hadadden kamshi ya daki hancin shi wani irin sanyi ne yaji ya ratsa shi ahankali ya maida kofan dakin yarufe yana kallon koina aranshi yace no bad dan ko ina a gyare zama yayi akan kujera Dady ya zauna kusada shi tareda kwalama Ammi kira. "Rukayya" daga sama Ammi ta sauko ahankali tana gyara lullubin mayafin ta tana kallon yaron datagani kusada Dady data kyautata zaton shine Aliyu kaman su daya da Dady saidai yafi Dady kyau sosai da haske, babba ne yanada dan jiki kadan yana sanye da faran shadda idanunshi kan TV yana kallon abinda akeyi a news, karasa saukowa Ammi tayi tace "barka da dawowa" yanda muryan Ammi yadaki kunnuwan Aliyu kaman yataba jin muryan yasa ya juyo da sauri hada ido sukayi da Ammi gani yayi kaman yataba ganinta awani wuri amma yamanta, cikamai ido sosai Ammi tayi murmushi ya kakalo tareda saukar da kanshi kasa ahankali yace "ina kwana Mum" cikeda so kodn yanda mahaifinshi keson yarta Ammi tace "Aliyu, Masha Allah yau gani ga d'ana Aliyu, sannu kaji Son, katashi lpy?" gyadama Ammi kai yayi yace "Alhamdulillah Mum" yay dan shiru yarasa me a kecewa murya chan kasa yace "welcome Mum, Allah sanya alheri" murmushi sosai Ammi tayi ganin yanda yaron keda natsuwa tace "tashi muje nahada maka breakfast kaji" tai hanyar dining tareda jan kujera daya baya ta kalli Aliyun dahar lokacin yakasa tashi tace "taho Aliyu" tashi Aliyu yayi ahankali cikeda kunya Dady sai washe baki yake kaman zaiyi ihu sabida murna, kujeran da Ammi ta nunamai yazo yazauna sanan tace "yauwa, akwai shayi, chips da liver source, sanan akwai pancake, me zanyi serving naka ko nadafa maka wani abu?" zaiyi magana Dady yakara so yaja kujeran dake kusada Ammi yace "tunda anga yara an manta da uba ai saimuzo ko ba'a gayyace muba" dan murmushi Ammi tayi ta shafa gemun fuskar Dady tace "tuba nake Yallabai na, bari naji da danmu saina dawo kanka kaji ranka shi dade" shi kanshi Aliyu baisan lokacin dayadan saki murmushi ba sabida yanda Ammi tai maganan so lovely, ahankali yace she's nice. Kallonta Dady yayi cikeda so yace "shikenan nahakura afara bama danmu to, yanason pancake sosai" gyadamai kai Ammi tayi tace "tom shikenan" plate ta jawo ta dibanmai pancake dat were looking so inviting tadau honey tace "kanaso da Honey ne Aliyu!?" gyadama Ammi kai yayi hakan yasa ta zubamai honey akai, sanan tadau cup tazubamai ruwan shayin dake kamshin kayan kamshi tasa spoon ta ijiye mai agaban shi ta matsar da madara da milo girgiza mata kai yayi yace "just sugar Mum" "OK okay, bakasha da madara" gyadamata kai yayi murmushi tayi tadau sugar tamika mai tace "very soon I will know my son likes and dislike ko" murmushi yasake yi hakanan yaji yanason matan she's so nice to him dudda baisan kodan taga Dady awurin bane but he felt gud yadade yana craving for this kind of affection and care amma bai samuba, karban sugar yayi ahankali yace "thank you Mum" murmushi daga Dady har Ammi sukayi atare, Ammi taja kujeran kusada Dady ta zauna tana kallon abincin tace "oya kafara ci to ko kunya na kakeji" girgiza ma Ammi kai yayi, Ammi ta kalli Dady dake binta da kallo kaman zai cinyeta yanaji kaman yabata duka duniya sabida abin nan datama Aliyu tace "Me zan baka yallabai na?" ahankali Dady yace "kome Yallabiyata tabani zanci" murmushi Ammi tayi tace "angama" chips tazuba musu a plate daya ta hada musu tea. Ahankali Aliyu yadau pancake din baida wani interest kan abincin sosai yakai bakinshi ahankali ya gutsura wani irin dadi yaji da baitaba ji ba the pancake is the fluffiest pancake daya tabaci in his life, Oh my God, like Oh-my God, shafa kunenshi yayi ya cigaba daci yadade rabon shi da pancake shidai arayuwan shi yansosn pancake dudda Dady na yawan cewa wai da pancake Mumy shi ta yayeshi saisa tundaga lokacin yakeso dan da aka yayeshi har cikin dare yana farkawa yayta kuka yana cewa pankyyyy, Mummy Pankyy saisa wani zubin idan Dady zai rsokane shi sai yace mai pankyyyy boy kawai shi kadai yake tunanin shi yanacin pancake din saida yaji yayi dam sanan yature, Dad da Ammi da tuntuni suke kallonshi yace "akaro ne Son" girgiza kai yayi yana shafa cikinshi yace "am okay" murmushi Ammi tayi tace "ashe haka kake son pancake, zan dinga sa Fatyma namaka in sha Allah" tashi yayi tareda daukan bottle water yakoma falo kwanciya zaiyi Ammi tace "banda kwanciya Son, ka zauna in abincin ya kwanta saika kwanta ko" gyadama Ammi kai yayi ya zauna yana chanza channel, ahankali Dady yakama hannun Ammi yarike gam kallonshi Ammi tayi lumshe ido yayi kafin yabude murya chan kasa yace "thank you for being a mother to my son, nagode Rukayya Allah yamiki albarka" girgixa mai kai Ammi tayi tace "karka kara godemin I can do anything for you Alhajina, yaro mara magana haka ba um ba umum" murmushi Dady yasake yi yay kissing hannunta yajuya ya kalli Aliyu yanda ya zauna hankali kwance yana kallon kwallo a binshi yace "bai taba shiga dakin matana yasake hakaba dan dolema nake sashi ya shiga, ko shashina he hardly come sabida su, jibi yanda yasake anan sabida yanda kikamai, Allah yamiki albarka nagode" murmushi sosai Ammi tayi ta tashi tana tattare flat din dasukaci abinci dashi Dady ya shiga tayata suka kwasa sukai kitchen atare suka wanke sanan suka fito suka dawo falo suna hira inka gansu zaka dauka Ammi ita tahaifi Aliyu kawai fatane dan Ammi bakace shine zaisa kagane ba itace maman Shiba, shima Aliyun yasake da Ammi sosai ahaka Momma da Abdul da Ihsan sukazo aka cika part din Ammi, Ammi ta shiga kitchen tana girki Momma taitai Ta tsaya Ammi Ammi ta hana Ihsan Momma ta tura itama da kyar Ammi ta yarda ta tayata, wuraren 1 Dady dasu Aliyun suka tafi masallaci Ammi kuma da Ihsan dahar tasaba da Ammi suka shiga jera abincin a dining Ihsan tace "Mum yaushe Aneesa zatadawo? Momma tace ta hadamu kawance" dan dariya Ammi tayi ta kalli agogo ganin daya yasa tace "baban ku yace karfe biyu suke dawowa daga haddan so nan da awa daya" murmushi Ihsan tayi zata kara magana Momma tace "ke dalla kin dami mutane da surutu" da sauri Ammi tace "kyalesu yaran yanzu ai haka suke, Aneesa tafi aku surutu" duk dariya suka shiga yi Ammi tace "ai bari inashan fama, Aneesa da surutu hmmm ba'a magana saidai in bata saba dakaiba" bude kofan da akayi yasa suka dago kai Dady ne da Abdul sai Aliyu, Dady ya zauna kusada Momma ya kalli Ammi yace "
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



3⃣5⃣



Dady yace "Ummu Aliyu akwai enough food yar abokina na hanya, wacce zata zo muga yazata kasance ai nafada miki ko" fashewa da dariya Abdul yayi ganin yanda Aliyu yay kini kini da fuska, kallon fuskar Aliyun Ammi tayi tadanyi murmushi tace "shikenan Alhaji, kutaso kuzo kuci" tashi dukansu sukayi sukai dining banda Aliyu da ranshi yake abace, Momma tace "Beta are you not eating?" daure fuska yayi yace "am not" Momma zata kara magana ahankali Ammi tace "kuna damun min d'a fa" dan dariya daga Momma har Dady sukayi Momma tace "Aliyu kayan haushi, munkusa ganinku arana indai wanan rubabben yaron ne" girgiza kai Ammi tayi tadau tray ta daura plate of fried rice da chicken akai sai coconut juice a jug da glass cup tafito daga dining duk Dady dayay kaman yanacin abinci yana kallonta, dan karamin stool taja takawo gaban Aliyun da kunya yakamashi ganin itada kanta tazo, stool din taja ta daura tray akai sanan ta zauna gefenshi abincin ta dauka ta mikamai tace "don't mind them ga abincin ka kaci bazasu ganmu arana bako" ahankali as usual yanda yakema Dady, a shagwabe yace "banda apatite nacin abincin Mum" dan shiru Ammi tayi tana nazarin fuskanshi kafin tace "okay let's do this" tai maganan ta yanda daga ita sai Aliyun zasu ji, hakanan takeson yaron sanan yana bata tausayi ganin yanda yakeyi, komi babanshi, komi babanshi, ahankali tace "anama iyaye biyayya ne dan asami albarka right" gyadamata kai yayi tai murmushi tace "gud, give it a chance, idan tazo kaganta bakasan wazaka gani ba kuyi gaisuwa na mutunci koba komi kanwar kace itama ai ko, so karkaji komi inhar ina gidan nan you get to marry wacce kakeso, am your Mummy I will always stand by you against all odd, are we gud now" tunda Ammi take maganan yake kallonta ta bala'in burgeshi kawai ya girma ne da baiga mezai hanashi rungume ta ba maganganun ta sunmai dadi sosai, wani irin cute gamshashen smile yasakin mata tareda gyada mata kai yace "Alright Mum" murmushi itama Ammi tamai tace "ga abincin ka, bari naje naji da baban ka" da sauri yamika hannu ya karbi abincin yafara ci murmushi kowa na dining din sukayi dan hankalin su na kansu kuma tsaf sukaji abinda Ammi tafadin mai dudda bada karfi take maganganun ba, Dady karkada kafa kawai yake yana tunanin mezema Ammi, shi inhar mutum zaiso Aliyun nan nashi to wlh zaima iya bama mutumin kanshi ta hanyar zama bawa agreshi, Aliyu is his life so duk wanda zaizo Aliyu yagamamai komi aduniya, kujeran kusada shi da Ammi taja ta zauna yasa ya yadaga kai ya kalleta itama kallonshi tayi cikeda so da kauna, abincinshi yadeba da spoon yakai bakinta akunyace ta bude baki ta karba batason tai turning nashi down but she's shy ga yara awurin kuma saisa kawai ta karba, sosa keya Abdul yayi ganin soyayyan tsofaffi kafin yaja plate dinshi ya sauka daga kan dining table din yakoma kan kujera wurin Aliyu, daga Momma har Ihsan sukai murmushi duk aka cigaba dacin abincin.





Dady ne yafara gama cin abincin dayamai shegen dadi yajuyo ya kalli Aliyu dahar yanzu baiyi rabin plate ba shi dama bai iyacin abinci da sauri sauri ba, baikuma iyacin abinci mai zafi sosai ba, bai kuma iyacin mai yaji ba yawuce yabude kofa yafita waje daidai lokacin yaga anbude gate wata mota ne ta danno kai cikin gidan hakan yasa yarage saurin dayake yanabin motan da kallo awajen parking space motar tai parking sanan aka bude kofa wata fine farar kafa ce dake sanye da prada hill mai ruwan gold, dayan kafar aka fitoda kafin wata yarinya tafito gabaki daya daga cikin motar, kyakkyawan yarinya ce fara tana sanye dawani riga da sket na Black lace yanada flawa mai ruwan gold tana sanye da takalmi Hill sosai mai ruwan gold tayafa wani siririn mayafi mai ruwan gold gold sai yar jakanta na Monalisa itama gold tasa wani sunshade a idanunta, zare glases din tayi fuskarta dauke dawani fine makeup an mata carving eye brows masu kyau sosai, da sauri Dady yace "oh Nafisa ce!" yay wurin motan maida kofan motar tayi tarufe da sauri tajuyo ganin Dady tana murmushi itama ta nufoshi, adan kunyace kanta akasa tace "Dady ina yini" cikeda fara'a Dady yace "sannu da zuwa Nafisa ke kadai kikazo, dakanki kikai driving?" gyadama Dady kai tayi, Dady yace "oh is risky, nafadama babanki fa ya dinga hadaki da bodyguard amma bayaji" murmushi tayi a shagwabe tana make kafada tace "Dady ni banaso fa" tabe baki Dady yayi yace "ahhh lallai taku kam tazo daya da Aliyun, ai yaron nan baya bari su bishi yanzu banma sanin lokacin dayake sabewa yafice daga gidan sabida karnace su rakashi, yara bakujin magana ba kusan kome mukeyi sabida kare lafiyanku bane" dariya tayi zatai magana Dady yace "common bance ki cikani da surutu ba, muje ki gaida matata, maman Aliyu, sai Momma shi my sister duk sunzo suna ciki" suna tafe suna hira da Dady har part din Ammi ahankali Dady yabude kofan tareda yin sallama hakan yasa dukansu suka dagokai, shigowa Dady yayi yana kallon waje yace "shigo Nafisa ki gaida iyayen ki" matsawa gefe Dady yayi ahankali ta shigo dakin batare data cire hills dinta ba, kallo daya tamusu ta sunnar dakai kasa ganin mutane cike adakin, tundaga kafa Aliyu yake kallonta har zuwa kai daidai da abu daya baigani tattare da itaba daya burgeshi, dauke kai yayi yacigaba dacin abincin shi Abdul na mintsilin shi tabaya amma yay kaman bayaji, tahowa Ammi da Momma sukayi ganin ta tsaya gefen Dady bata gaishe su ba bakuma takaraso ba yasa
Ammi tace "barka da zuwa Nafisa" dagokai tayi ta kalli Ammi da Momma murmushi tayi tace "ina yinin ku" duk murmushi suka mata sukace lafiya lau, dining Momma tanuna mata tace "kinzo adaidai muje dining kici abinci" da sauri Dady yace "No, fita zasuyi da Aliyu" ya kalli Aliyu dayay kaman baimasan da zuwan waniba yace "Gadanga na tashi kuje bukka ku zauna Ihsan zata taho muku da abin tabawa abaki" dago kai Aliyu yayi ya kalli Dady zaiyi magana Ammi ta girgiza mai kai wani irin nauyin Ammi yaji yamaida kanshi kasa, ahankali Ammi tace "taso kutafi kabarta atsaye Son" dan murmushi Nafisa tayi tadan dagokai ta saci kallon Aliyun dat she's seeing for the first time da Hajar tasha bata labarin shi cewa Dady su yafison shi agidan, oh wow dama haka yake da kyau, kawar da tunanin tayi ganin yataso tai kaman bata kallonshi nanko tsaf take kallon komi nashi bamashi kadaiba "my God he's so f*cking handsome, look at how tall he is, ohhh God, very very tall, My Gaint!" tafada aranta tana wani irin murna tanadan gyara tsayuwa tana addu'a Allah yasa yasota dan gayen yahadu to the extreme, yanda yake dan wawware kafa cikeda isa da izza yana tafiya ta kalla taji numfashinta na barazanan daukewa "my fevorite part, I think he has big machine gun, Ohh, wayyo Allah na kalli yanda yake tafiya fa, my Spartacus, My Gladiator, he's so f**king sexy and super hot, uuhuhu" duk ita kadai take zancen zucin nan tana kallonshi ta gefen ido harya karaso wajen, lumshe ido tayi while taking a deep breath, he smells damn gooood! Mai sifili hudu baimai biyu ba, "awesome perfume" tana jiran yamata magana yabi ta gefenta yay hanyar kofan fita, murmushi Dady yayi yace "bishi kuje Nafisa" gyadama Dady kai tayi tajuya ta kalli bayan Aliyun daidai yabude kofa yafita tabishi itama tasakai tafice tareda rufo musu kofa, hanyar bukkan Aliyu yayi, hadadden bukka ne dake compound din nasu akwai table sai kujeru masu kyau dasuka zagaye table din saikuma wani white flower verse da flowers jajaye ke tsakiya akan table din wurin so neat, irin wurin shakatawan nan na gidan yan gayu, zama yayi akan daya daga cikin kujerun, ahankali ta zauna kan kujeran dake facing dinshi wearing a smile tana kallonshi, ko 3sec basuyi da zama ba saiga Ihsan dauke da babban tray da kayan sha ke ciki sallama tayi sanan halin Ya Aliyu karya disgata, da hannu yamata alamu data shigo, shigowa tayi ahankali ta sauke tray kan table ta ciro drinks din ta ijiye musu sanan ta ijiye plate din dake dauke dasu samosa and spring rolls da Momma takawoma Ammi, ta ijiye dambun nama sanan ta dau tray ta kalli Ya Aliyu dake dan daddanna waya abinshi tace "intafi Ya Aliyu" gyadamata kai yayi tajuya tafice, kusan 15min suka bata sai kallonshi take shikuma Aliyu na taba waya abinshi dagokai yayi ahankali hada ido sukayi, da yatsa yanuna mata abubuwan dake gabansu yace "have something" murmushi tayi tace "sure" juice ta tsiyaya a glass cup din tana kallon Aliyu kaman yanda shima yake kallonta kallon dabazaka taba gane na miyeba cika glass cup din tayi da drink bama tasaniba tsabagen yanda take kallon Aliyun tacigaba da zubawa har juice din yafara zuba akasa yana gangarawa kasa wasu na zuba ajikinta, dan yatsine fuska yayi yay smirking yamata pointing glass cup din da yatsan shi} da sauri ta janye idanunta daga kanshi ta kalli gabanta da sauri ta daga juice din datake tsiyayawa a cup saura dan kadan aciki ta ijiye kan table din tamike da sauri kunya ya lullubeta looking at the mess datayi sabida kallon Aliyu yanzu yaganota, dan tsaki tayi tana kallon yanda lace dinta yajike da juice ta kasan riganta da skirt dinta tace "sh**t" tana yarfe hannu murmushi yayi daidai lokacin an bude gate din gidansu babban motan kai yara makaranta ne ya shigo juyar dakai yayi ya kalleta yanda take yarfe hannu dukya bata mata jiki ahankali yazaro white handkerchief daga aljihun shi yamika mata, bama ta lura dashiba sabida yanda take kallon skirt din, cikin husky voice dinshi yace "use this" da sauri ta kallai, ganin yana miko mata handkerchief dinshi yasa wani dadi yakasheta, ahankali tamika hanunta takama handkerchief din zata karba taji yarike baisakin mataba yana kallon fuskanta kaman yanda take kallon nashi, ahankali yace "ki rage kallon mutane okay" subhanallah wani irin kunya taji kaman zata nitse kasa, hayaniyan yara dayaji yasa ya sakin mata handkerchief din yajuya yana kallon yaran gidansu dasuke gudu kowa nayin hanyan shashin su itakuma Nafisa ta tsugunna tana goge kayanta.






Wani irin Uban harara Hajar tama Aneesa dake gefenta tace "aisai afita ko Malama tunda ba motan ubanki bane" ko kallonta Aneesa batayiba dama tun dazu take mata surutai bata tanka taba dan bataso tabatama Ammi rai da wlh dudda tafita girma saita lallasata karfi ba ajiki bane fess zata fasamata baki, ahankali tasa hannu tadau lunch box dinta da bottle din ruwanta ta tattara uban littatafan da aka bata kusan guda goma sha shida a hannu dan bataje da jakaba ta sauko daga motan da kyar kaman zata fadi abubuwan hannunta duk sun mata yawa, wani irin faduwa gabanta yayi dabata San mesa ba, kodai ciwon kirji ke neman damunta ne tana yawan having faduwa gaba this days, dan gajeren tsaki taja batason zagin da Hajar tamata yabata mata rai tafara tafiya ahankali zuwa shashin su, tunda motar tai parking Aliyu yake bin masu fitowa daga motan dai dai da kallo ganin Aneesa ta sauko ahankali daga motar yasa yawani irin mike tsaye yana kallonta ganin still ita yake gani tana tafiya ahankali as usual yasa yarufe ido da sauri yasake budewa yadaurasu akanta, still Aneesa yagani as usual da wanan dogon hijabin nata da safa akafafunta yasa yaji zuciyar shi na bugawa is he dreaming or what? Is he okay kodai yasoma samin matsalan kwakwalwa kaman yanda Abdul yake cewa? Is this his Aneesa ko idanunshi gizo sukemai?.....

Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa, duk wacce tafitar min da book Allah ya isa.

Kwasan lunch box Hajar keyi agaban motar tana kallon Aneesa yanda take tafiya ahankali, jitake kaman ta kasheta tsaki taja tace "tana mana tafiya cikin gidanmu agadarance kaman gidan ubanta ne, agola kawai" daukan bottle water dinta tayi da sauri tafara tafiya tace "zakici ubanki ne yanda kikazo gidan nan saikin gudu da kafafun ki kinbarshi munafuka" dawani irin sauri tahau tafiya harta cimma Aneesa, wani irin bangaje Aneesan tayi tasa hannu tawani irin turata, wani irin juyi juyi sau biyu Aneesa tayi tsabagen yanda tajuyata kafin tayi wani irin mugun faduwa tai wani irin ihun azaba lunch box da littatafan hannunta suka wawwatse a compound din hijabinta yadaga yarufe mata fuska tabuge gefen bakinta sosai da mandibular bone dinta, dawani irin sauri Aliyu yafito daga bukkan ganin abinda Hajar tayi, ganin Ya Aliyu yasa Hajar ta kwasa da gudu tai flat dinsu dan bamata luradashi ba tabude kofa ta shige tareda garkamewa da key, karasowa inda take Aliyu yayi tana kokarin tashi takasa, ahankali ya tsugunna batare daya tadata ba danso yake yakara tantancema idanunshi cewa Aneesa ce yagani ba daya daga cikin kanninshi ba dan zuciyar shi nacemai gizo idanunshi kemai, hannu

Please Login or Register in order to submit comment