Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya......" kasa karasa maganan yayi sabida yanda yaga Aliyu na kakarin mutuwa kumfa nafita daga bakinshi kaman yana wasa da shower gel, wani irin bugu kirjinshi yabada "dududu-dum!!!" bakinshi ma rawa ya shigayi, baimasan takamaimen inda hankalinshi yake and not knowing mema zaiyi, ahankali yadaga kafanshi yana pointing Aliyun da yatsa yace "Gadanga na mehaka kakeyi you know this is a hard joke ko" yay maganan yana tsugunnawa agabanshi ahankali yakai yatsanshi kaman wanda yazare yadaura kan tongue dinshi yace "me haka kakeyi? Why are you playing with your tongue kamaida shi ciki wai liquid sabulu ka kurba ne da bakinka ke kumfa haka Gadangana? Why are you struggling and stretching like this? Me kake jujjuya idanunka kana kafar da idanu iyye, kai Aliyu, Son" Dady yakirashi yana jijjigashi......



Ganin Rauda tadawo daidai yasa Ammi ta shafa kanta tana mata murmushi tace "menene why are you like this? Laifi kikama yayan naki?" da sauri Rauda ta girgixa mata kai tace "Mum Aliyu mutuwa Ya Aliyu zaiyi wlh he's doing somehow?" adan rude cikeda wani irin yanayi Ammi tace "kaman ya mutuwa zaiyi, what sort of joke is that?" da sauri Rauda na kuka sosai tace "wlh wlh da gaske naje dakin naga....." Ammi bamata tsaya taji mezata ceba ko takalmi ba tasaka ba tai flat din Aliyun tabude kofan, babu kowa falo saidai taji maganan Dady sama sama hakan yasa tai hanyar inda takejin maganganun Dady, abude Dady yabar kofan hakan yasa ta tsaya tsak numfashinta yadan tsaya kafin ahankali yadawo ta shigo dakin sosai tana kallon yanda Dady ya rungume Aliyun dake mukurkuso yana surutai da bamata gane meyake cewa da sauri ta tabashi tace "Alhaji, Alhaji tashi mukaishi asibiti" kallonta Dady yayi for some seconds saikuma yamata murmushin nan nashi mai kyau yace "wasa yakeyi min, soyake yaga nadamu, my Boy is playing pranks, April fool ne don't worry ummu Aliyu, wasa yake mana ba dazunan muka dawo daga gidan rasuwa tareba so he's just joking" ahankali Ammi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un" kafin da sauri tamike tsaye tafito da saurinta da Rauda dake kuka sosai sukaci karo, da sauri Ammi tace "jeki kiramin bodyguards din baban ku da driver ku imaza Rauda" da gudu Rauda tajuya Ammi kuma takoma daki ko one minute ba'ayiba bodyguards din Dady suka shigo dakin ganin Aliyu ba karamin hankalin su tashi yayi ba da sauri sukai wajen suka karbeshi daga hannun Dady, Dady yamike tsaye yace "kai ina zaku kaimin d'ana wasa fa yakemin" da sauri Ammi ta girgixa mai kai tareda cupping face dinshi ahankali tace "Alhaji look at me, kadawo hayyacin ka okay, Aliyu is sick you need to be back a hayyacin ka your son needs you, call ur doctor Alhaji" da sauri ya lumshe idanunshi kafin ahankali yabude maganganun Ammi sun shiga brain dinshi sunyi resetting na brain din ahankali Ammi tace "kace innalillahi wa innailaihi raji'un" ahankali batare daya bude idanun ba yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Ummu Aliyu da gaske Aliyu na nagani lying here kumfa na fita daga bakinshi?" hannunshi Ammi tarike tace "let's go to the hospital first bodyguards dinka sun fita dashi" da sauri suka fita Ammi ta zura wani takalmin Aliyun datagani abakin kofa tabi Abba Rauda ma tabisu tana kuka sosai, sauran Matan Dady duk suka fiffito suna kallon ikon Allah jin hayaniya da kukan Rauda daya cika gidan sosai.


Ahankali Aneesa da tun lokacin dataji muryan Rauda na kwalama Dady kira ta tashi ta tsaya a window tana kallon tsakar gidan tana kuka sosai ta sulale akasa gani datayi anfito da Aliyu kaman wanda yamutu kumfa nabin bakinshi yana did diga a compound dinsu, sai karanto duka addu'an datasani take so dama da gaske yake baida lafiya dama da gaske ne, she regret abinda tamai she regretted it, wani irin kuka tafashe dashi da tadade batai irinshi ba.







Wani babban private asibiti number asibiti da manyan Abuja keji dashi suka tafi, tun kafin sukai Dady ya danna ma babban likitan asibitin kira akan gashinan zuwa da danshi baida lafiya atanadi komi, Ammi tasan cewa Dady na tsananin son Aliyu amma bata taba sanin haka yake mai wanan mahaukacin son ba, Alhaji yadawo kaman wani zararre har fakan idanunshi take tana tofamai addu'a akai sanan tana kiramai sunayen Allah yana karba, cikin ikon Allah suka kai asibitin already anzuba nurses da hadadden gado agaban reception ana jiran senate president da danshi karban Aliyu da kaman babu rai ajikinshi sukayi ciki dashi Dady yabisu akai theater dashi aka rufo kofa batare da anbari Dady yabisu cikiba,.


Ahankali Ammi tazo har inda take, dan murmushi yakakalo mata ganin yanda dukta damu fuskarta ya shafa murya chan kasa yace "kidena damuwa am fine okay" gyadamai kai tayi tareda kakalo mai murmushi dan tasan he's just saying that to make her feel better, to calm her down, ahankali yace "muje su kaiki gida kiyi wanka akwai najasa a jikin mu" cikeda damuwa Ammi tace "kaifa?" "anjima zanzo nai wankan in sha Allah" gyadamai kai tayi tarike hannunta cikeda so sukai inda bodyguards dinshi suke tsaye yace "ku kaita gida" cikeda girmama wa sukace to sukai gaba Dady yace "bisu, I love you" gyadamai kai tayi ahankali tace "I love you too, be safe for me okay" gyadamata kai yayi tajuya tafita tana waigenshi kaman yanda shima yakasa dena kallonta yana bala'in son Ammi sosai harta shiga mota saida aka tada motan sukabar asibitin sanan yakoma gaban dakin yaciro wayanshi daga aljihu ya kira Momma.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4⃣6⃣ & 4⃣7⃣



_not edited_

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting a tsakanin soyyayya_


_zaki iya turo katin MTN idan baki da banki_

_*masu fitarmin da book waje you guys pay for subscription to read littafin nan bawai kunsai littafi bane bakuda ikon abina, dan haka duk wacce tafitarmin da book waje banyafe mataba*_

_*duk wacce ta karanta littafin nan batare data biyaba ban yafema ta ba, Allah ya isa*_
_*masu tsoron Allah dake cin karo da littafin nan su biyoni su biya kudi Allah ya saka Muku da alhairi yabiya muku bukatun ku na alhairi*_


_you can chat me up here 07012181461 for any business proposal, etc_

_VIP group is always open, group din hajiyoyi da manyan mata wayanda basuson jira, *sangartattu* na, gasunan duk *Boyayyun Mutane* da *In Bani* bazasuzo VIP ba, masu so can chat me up 07012181461 danku shiga wanan sahun_








Wuraren 5 suka shigo gidan parking bodyguard din sukayi daya daga cikinsu ya zagayo da sauri suka bude mata ahankali tafito hada ido sukayi da Maman su Rauda dake gaban flat dinta kan plastic chair tanacin stick meat, wani banzan kallo datama Ammi yasa tadauke kai batare datasake kallonta ba tazo zata zuwa saida Maman su Rauda tabari tazo daidai kusada ita sanan tadanyi shewa tace "wayyo yar gaban goshi murmushin bazai wuce daga yanzu zuwa safiya ba, hahahah" ta kyalkyace da dariya tareda zaro nama daya daga stick din ta jefi Ammi dashi chak Ammi ta tsaya ta juyo ta kalleta gira daya Mama ta dagamata tace "au sannu nazaci karyan gidanan nefa ashe kece, yamai jikin?" bakaramin zafi maganan Mama yama Ammi ba amma tadanne tawuce tai gaba Mama takara kecewa da dariyan tsokanan yau duniyan dadi take mata she just use just a stone like dutse dayafa kacal dazata hargitse rayuwa hudu dashi.



Kofar flat dinsu tabude da sauri Aneesa data kifa kanta akan kujera tana kuka tadago kai idanunta sun kumbura harsun godema Allah da gudu ta taso tafada jikin Ammi tace "Ammi ya jikin Ya Aliyu ya warke?" ajiyan zuciya Ammi tasauke tareda maida kofar tarufe ahankali tace "Alhamdulillah da sauki dena kuka" dagota tayi daga jikinta tasa hannu ta share mata hawaye tana murmushi tace "da sauki karki damu yayanku zaiji sauki, jeki hadamin tea bari na naje na watsa ruwa.



_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa_



Gyadama Ammi kai tayi tawuce kitchen tana share hawayen dasun kasa dena zuba Ammi kuma tai sama cikeda damuwa wanka tayi da ruwan zafi sosai dan jikinta ko ina ciwo yake mata kafin tasaka wata bakar doguwan riga mai duwatsu masu kyau, tundaga kan bene takejin sautin kukan Aneesa harta sauko kasa tana zaune kan kujera tana kuka karasowa falon Ammi tayi tace "waike kukan me kikeyi eh?" girgixa ma Ammi kai tayi wasu sababbin hawayen na fitowa binta da kallo Ammi tayi she really finds yanda take kuka weird and strange duka duka sau nawa suke magana da Aliyun dazata zauna taita kuka haka, zama Ammi tayi akan kujera tamata alamu da hannu datazo, tashi tayi ahankali ta taho da gudu fadawa jikin Ammi tayi sai kuka cikin kuka tace "Ammi ya jikinshi" , shafa bayanta Ammi tayi tace "da sauki kidena kuka he will be fine, uhmm share hawayen ki" hannu tasa ta share hawayen Ammi tanuna mata cup din tea data ijiyemata kan dinning tace "jeki kawomin nasha anan" sha Ammi tayi tass sanan ta tashi ta shirya tareda yafa gyalenta tama Aneesa sallama tafita har Gate taje batasami ko driver daya agidan ba daga bodyguards har driver duk sun fiffita cewan soja mai gadi, komawa ciki tayi ta zauna akan kujera tadau wayarta tai dailing number Alhaji harya katse bai dauka ba sake dialing number tayi akira na uku yay picking murya chan kasa tace "Alhaji ya jikin Aliyun?" cikeda damuwa Dady yace "Alhamdulillah har yanzu Dr bai fitoba balle naji wasu bayani ga Momma nan ma da Abdul sunzo" ahankali tace "Allah sarki angode, na shiryo nataho babu wanda zai kawoni nahau motan haya ne?" da sauri Dady yace "No no, karki hau, zasu dawo nina aika su sunje tahomin dawasu abokaina turawan likitan daga lagos sukazo suna Airport nan idan sun dawo zansa zuso, ki zauna yanzu kimin girki karki damu okay take care of yourself, ina Aneesa?" kallon Aneesan dake kuka har lokacin tayi tace "gatanan tun dazu kuka take dukta damu" "tell her not to worry, my son is a fighter zaiji sauki da izinin Allah, sai anjima" katse wayan yayi Ammi tasauke ajiyan zuciya takai kusan 20min zaune awurin kafin ta tashi tawuce kitchen bata kira Aneesa ba dan taga the girl is not fine haka tai girkin.

Shiru shiru har magrib driver basu dawoba balle su dauke ta har bayan sallan isha'i takira Alhaji yafi akirga baya dauka, ahaka har bacci ya kwashe su daga ita har Aneesan anan falo.

Kiran sallan asuba yatada Ammin tashi tayi ta tada Aneesa sukaje sukai sallan safiya sanan suka shiga gyaran gida ta kwashe abincin da Dady yasata dafawa jiya ta dumama snan tai tea.


Misalin 8 tana zaune a falo Aneesa zaune agefenta sukaji karan motan yan sanda a tsakar gidan da sauri Ammi ta tashi ta daga labule tana lekawa Dady ne yafito daga mota tareda wasu yan sanda ranshi abace cikin tsananin bacin rai yace "dukan ku kufito tsakar gidan nan, Kareema, Amina, Aliya da Rukayya gabaki dayanku kufito" yanda Dady yakira sunanta kai tsaye yasa tagane ba lafiya Aneesa dake gefenta ta kalla tace "ke bani hijabi na" hijabinta Aneesa tadauko daga kan kujera tabata tasaka sanan tabude kofa tafita Aneesa itama tsa hijabinta tafita amma ta tsaya agaban flat dinsu dan ba'a kira da yaraba itakuma Ammi tai inda suke sauran matan ma sun fiffito, ma'aikatan gidan Dady ya kwalama kira gabaki dayansu kusan ma'aikata takwas duk suka taho wajen aka tsaitsaya anan kallon Dady dagabaki daya ya chanza kana ganinshi kasan baida kwanciyan hankali.


Cikin tsananin fushi da mamaki Dady yace "as long as dasanina dudda abinda kukema Aliyu daidai magana ta banza na rana daya baitaba fadamuku ba, bari kuji da dukanku nan nake, na rantse da girman Allah, na rantse muku da girman Allah duk wanda yace shi da marayan d'ana zaiyi, yaron da baida mahaifiya, baida kani ko kanwa dasuka fito tajini daya, yaro shikadai, abin tausayin yarona, wlh duk wanda yace Aliyu zai taba zan iya ganin bayan mutum aduniyan nan, nida mutum zamu iya zuwa karshen duniya" Dady yay shiru sabida yanda zuciyar shi ke tafarfasa cikin wani irin tone kaman na wanda is about to cry yace "Aliyu was poison!" "innalillahi wa innailaihi raji'un! Poison kuma Alhaji" cewan matayen nashi da duk sunbi sun rude, cikin wani irin yanayin Dady yace "yes Aliyu was poison, idan kunga ruwan poison din da aka tsotso daga cikinshi saikun tsorata, Aliyu gadaishi nanne rai a hannun Allah baimasan inda kanshi yakeba, baima gane kowa, bakinshi gabaki daya yay jajir poison din yabata mai baki yarona na wahala rai a hannun Allah abinda kukeso kuji kenan ko?" Dady ya tambaye su yana kallon fuskokin su yace "dama kun tsaneshi so kuke ku kashe shi ko?" wani irin murmushi Dady yayi yace "to bari kuji kunga wayan nan yan sandan kusan su goma sha bakwai? Kowani dayansu na dauke da poison detector zasu bincika min kowani daki da lungu da sako na gidan nan, kusani, Allah kana shaida wlh kowaye kowaye yay niyyan kashemin d'a I mean kowaye billahillazi bazan barshi ba sai inda karfina yakare aduniyan nan, bazan taba yafema wanda yay niyyan kashemin Aliyu ba, hmmm" ya saukar da wata irin ajiyan zuciya sanan ya kalli yan sandan yace "kufara aikinku officer" cikeda girmanawa babban su yace "yes sir" sanan ya rarraba yaran nashi kowani yana turasu flat daban daban dan bincika ko ina nagidana, sosai gaban Mama ke faduwa tana kara tunani a inama tasaka katin maganin poison din badai tabarshi dakinta ba kaman kuma ta yarda abolan gaban kitchen din su Aneesa bolansu kai she's contemplating dan tsabagen rudewa tarasa inda tasa daurewa dai tayi ta cije kar wani yagane matsalolinta duk suna tsaye kowanne da abinda ke running azukatan su har wajen minti talatin sanan saiga polisawan from various flat wanda suka fito daga part din Aliyu suka fito dauke da tray da pancake ke kai, sai mug din coffee.



Officer ne yanunama Dady mug da tray dasuka saka a forensic Bag yace "Sir he was poison ta wayanan abincin biyu, coffee akwai high level a poison a coffee nan sanan akwai a pancake dinan bari kaga" kallon daya daga cikin ma'aikatan yayi yace "get me water" da sauri mai aikin yatafi dauko ruwa officer kuma ya tsugunna ahankali yay unzipping bag din already da safan hannu a hannunshi yaciro mug din sanan yaciro pancake din daidai Gardner yakawo ruwa a babban buta karba officer yayi, ahankali Officer ya tsiyaya ruwa kan empty coffee mug din chaaaa ruwan yahau kumfa amma ba sosai ba sabida babu coffee saiya tsiyaya ruwa kan pancake din saiga kumfa shima nan wurin yadauki hayaniya, mikewa tsaye officer yayi ya kalli Abba daya tsaya yana kallon ikon Allah yace "waye yabashi abincin nan?" cikeda mamaki Dady yace "Aneesah nace tamai pancake da coffee but ai Aneesa can't do this" da sauri officer yace "waye Aneesa" juyawa Ammi da gabanta kewani irin faduwa tayi takira Anessa dake gaban flat dinsu alamun tazo fara zuwa tayi gabanta na dukn uku uku daidai nan wasu polisawa guda biyu suka fito daga part din Ammi, wani katin nagani suka mikama ogan nasu daidai Aneesa ta iso wajen ahankali tace "gani" da hannu officer yadaga mata yace "tsaya tukunna" ya kalli Dady yamai pointing flat din su Ammi yace "wacece mai flat dinchan" da sauri Dady yace "amarya tace gatanan" yamai pointing Ammi dake kallonsu, dan ajiyan zuciya officer ya sauke yamikama Dady katin maganin yace "ga poison din da aka sama Aliyu a abinci nan, a bolan gaban kitchen din flat din amaryan ka aka gani" da sauri Ammi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wakhlifni khairan minha" taron jama'an yadauki kara kaman jira ake akira sunan ta Maman su Rauda tace "Allahu akbar ana zaton aga wuta tamakera sai akaga akasin hakan" cha cha cha sukahau yada kananun zancen duk Dady najinsu amma idanunshi nakan Ammi ne dayaga hankalinta yatashi and zuciyar shi bataso ta yadda itace no she can't betray him like that, kallon officer yayi yace "officer are you sure wanan poison ne sanan are you sure a bolansu aka gani?" ahankali officer yace "gasunan daga shashinta suka fito ai bari kaga" tsugunnawa yasake yi duk aka bishi da kallo akai shiru ballo kwaya daya yayi yajefa a ruwan mug din kofin wani iri chichi hi ruwan yayi yafara komawa bakin kirin salati aka dauka ana tafi da sauri Ammi tace "Alhaji me zamuyi da irin wanan maganin, tunda nazo gidan nan ko ciwon kai bamu yiba bamamu da nagani balle har munsami wanan za....." hannu officer yadaga mata yace "excuse me Madam ban katse kiba saura abu na karshe" wani karamin leda yamikama Dady da dan kunne kwaya daya keciki yace "wanan earing din kwaya daya munganshi akasan uwar dakan Aliyu ne" da sauri Dady yaciro dankunnen daga leda yadaga sama yace "dan kunen waye wanan?" faduwa gaban Aneesa yayi da sauri tasa hannunta ta taba dayan kunnenta aiko babu dayan da kunnenta, kafe dan kunen Ammi tayi da ido kirjinta na bugawa ganin dan kunen Aneesa ne tama kasa magana, ahankali Aneesa tadaga hannunta bakinta na rawa tace "n....n...nawane Abba" shewa Mama tadauka tace "ahayye nanaye idan baka mutuba zakaga abu aduniya" cikin fushi Dady yanuna Mama da yatsa yace "wlh kika sake cewa wani abu anan saina katseki da mari wawiya kawai" yajuya ya kalli Aneesa anatse yace "meyakai dan kunenki dakin Aliyu?" rawa jikinta yahauyi datama rasa dalili dawowa tayi kaman wacce bata iya magana ba kodan sabida yanda kowa na wurin kallonta ne oho bakinta narawa tace "y....ya... Aliyu yace nakawomai abincin bangaren shi cikinshi na ciwo bazai iya zuwa ba" da sauri officer yace "ta ina ya ganki yafada miki hakan?" bakinta narawa sosai tace "w....wa...ya" gyadakai officer yayi yace "ke kika dafa abinci ko kawai baki akayi ki kaimai?" ahankali tace "nina d...afa" "okay keda waye a shashin dakika dafa abincin" "n...ni kadai ne Ammi na wurin Abba?" "tun yaushe Ammi naki ta tafi wurin Abba? Kin fara abinci ko baki faraba?" muryanta narawa sosai tace "ban faraba....l...okacin" dan murmushi officer yayi yanuna mata katin maganin poison din yace "Aneesah sunan ki ko?" da sauri ta gyadamai kai, ahankali yace "kigayamin gaskiya, ni inhar mutum yafadamin gaskiya to komi na zuwan mai ta sauki inyamin karyane yakecin bakar wuya, a ina kika sami katin maganin nan? Kowani yabaki kisa karkimin karya bazan miki komiba, fadamin a ina kika sami katin nan? Wayabaki kisakama Aliyu a abinci?" girgixa kai Aneesa tayi hawaye ya gangaro tace "wlh, wlh nibansan katin maganin nanba, ni wlh banma taba ganinshi arayuwata ba wlh kuwan" hawaye suka zubo sharrr ta share da bayan hannu, murmushi Officer yasake yi yace "kin tsani Aliyu kin tsani Aliyu, luckily sai jiya babanshi yace kidafa mai abinci, sai abin yazama babu kowa adakin shine kika ciro magani kika samai danyaci yamutu hakane Aneesa?" fashewa da kuka tayi sosai tazo kusada Ammi tarike Ammi gam cikeda tsoro tace "Ammi kicemusu ni wlh bansan maganin nanba, ni bazan taba kashe Ya Aliyu ba wlh wlh kuwan" tafashe dawani irin kuka ajikin Ammi ahankali Ammi ke kallon Dady dayay shiru yana kallon Aneesan dake kuka girgiza kai yayi yace "No officer kubar yarinyar nan trust me something happen, Aneesa bazata iya kisa ba, dan ita tadafa abinci doesn't mean ita tasaka poison, banda haka ba itakadai ne agidan nanba sanan kowa anan can enter bangaren Aliyu" cikeda rashin kunya da rashin mutunci Maman su Rauda tace "me kake nufi Alhaji Aneesa bazata iya kisa ba to mune kenan zamu iya? Sonkai kiri kiri sabida yar gaban goshin kace, mukake zargi kenan mune zamu iya ko, nagadai akwai CCTV agidan aje aduba mana hakanan nifa na tsani zargi koba hakaba Amina" da sauri sukace hakane wlh, officer ne ya kalli Dady yace "Sir akwai CCTV agidan nanne?" gyadamai kai Dady yayi yace "akwai a compound dinan, banda haka akwai CCTV a bangaren Aliyu dashi kanshi baisani dashi ba, CCTV tareda kwan lantarkin dakinshi yake, nasaka ne sabida nasan matayena sun tsaneshi zasu iya komi akanshi saisa nasaka?" da sauri officer yace "ina zamuga footage din" "muje yana secret room dina" ya kalli matan yace "kar wacce ta tafi daki kujiramu anan" hanyar flat din Mama Dady yayi da Officer, wani irin murmushi Mama tayi zuciyata tai sanyi dama takira CCTV ne sabida tasa aduba, Dady yazaci shi kadai ysan password din shiga dakin baisani batun yauba tasan.



Dakin Mama sukayi sukai sama, agaban wani daki ya tsaya da handle din kenan kaman waya ga boturan dannawa, password din yasaka saiga dakin yabudu computers ne wurin shiga adakin, straight computer bangaren Aliyu Dady yanuna musu, officer ya zauna gaban computer yay rewinding back har zuwa footage din jiya, rewinding sosai yayi har zuwa daidai inda Aneesa tazo part dinshi ahankali yace "got it" tsayawa Dady yay akanshi ya shiga kallo kirjinshi na bugawa shigowa part din tayi rike da tray ta kalli ko ina kaman tana neman wani abu kafin suga tai tafiya da sauri ta shiga falon ta sauke tray din kan center table tana kalle kalle, sai sukaga ta chusa hannunta agefen zaninta basuga metayi ba sundaiga tafito da kwaya daya ta jefa a mug saikuma tadauko daya ta dagargaza kaman yanda ake dagargaza magi da hannu ta barbaza kan saman pancake ta kakkabe hannunta tadauka da sauri tai hanyar bedroom dinshi tabude kofa ta shiga dayake babu CCTV a bedroom dinshi basusan meya faru ba sundaiga chan tafito daga dakin aguje, baya Dady yayi zai fadi tsabagen yanda heartbeat dinshi yay weak polisawan suka tareshi suna salati wani irin fincike kanshi Dady yayi yafita daga dakin da mugun zuciya.







Tundaga yanda Ammi taga fuskarshi gabanta ya shiga faduwa ta shiga ambaton Allah, dawani irin zuciya Dady ke dumfaro su harya karaso inda suke tsaye hannu yasa yawani irin fizgo Aneesa dake tsaye kusada Ammi jikinta na rawa Dady baiyi wata wataba ya daga hannu ya watsa mata lafiyayyen mari "tass!" runste ido Ammi tayi dan har kashinta taji marin da Dady ya dauke Aneesa dashi, fashewa da kuka sosai Aneesa tayi tsabagen tsoro tamika hannunta tana kokarin kamo Ammi tace "wayyo Allah na Ammi, Ammi, Ammi, Ammi n...." zuba mata wani marin Dady yayi akaro na biyu da saita yasa tai shiru tai gum tama kasa magana sai dubu datake gani a idanunta cikin ihu da daga murya Dady ya jijjigata yace "me Aliyu yamiki? Meya miki kikeso kiashi lahira? Ubanwa yasaki kikashe min d'a??" yakara daga hannu zaikai mata mari na uku Ammi ta kirashi. "Alhaji" dago kai yayi ya kalli Ammi idanunta sunyi jajir suna shirin tsiyayar da hawaye, cikin raunin zuciya Ammi tace "kayakuri Alhaji ka kwantar da zuciyan ka abi komi ahankali, Aneesa bazata iya kisa ba, nasan abinda na haifa" cikin wani irin fushi Dady yace "nine makaryaci ko, kina zaton shiri nama yarki? Okay naji shairi namata a CCTV baya shairi ko to muje kigani" ya finciki Aneesa dahar lokacin bata gani sosai yay flat din Mama Ammi tabisu da sauri su Rauda dake kuka sosai da sauran matan Dady ma suka bisu har dakin cameran, shiga dakin Dady yayi rikeda Aneesa kaman wacce tai sata sauran matan ma da Ammi ma ta shigo cikin tsananin fushi Dady yace "play d footage back officer" dan bude idanu Aneesa tayi ta kafe computer da ido, wani irin faduwa gaban Ammi keyi lokacin da sukaga Aneesa ta jefa kwayar a mug da lokacin data dagargaza daya ta zuba akan pancake dakin yadau salati Mama tace "ga irinta nan ai, aure aure yau munga ranan aure aure, ka aurosu karufa mata asiri ka kawota gidanan da ita da agolan

Please Login or Register in order to submit comment