Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana rikeda hannayenta gudun karta tafi, wani irin dauke kai Ammi tayi danko kadan baya freaking nata, cikin wani irin murya na bala'in ban tausayi Dady yace "ki yafeni, ki yafemin Rukayya, nai kuskure, naci amanan ki dana Aneesah, shirin shaidan ne da kuma kaddara wanda Allah ya kaddara sanan yarubuta cewa zai samemu, inason Aliyu bazan miki karyaba sanan ina sonki son dabanjin zan iya rabuwa dake aduniyan nanba, kidena maganan saki wlh inhar ina cikin hayyacina bazan taba sakinki ba" dan shiru yayi yana kallon fuskan Ammi yanda take kallon gefe kaman bada ita yakeba, ahankali yace "Aneesah na ina? Inaso naje naganta nabata hakuri na roketa gafara" dan murmushi Ammi tayi mai kara tace "Aneesah na bata bukatan roko koma menene naka, yarinya na have moved on, bazaka sake ganinta ba har abada" da sauri Dady ya girgiza mata kai zuciyarshi tamai wani irin nauyi kaman hawan jininshi nagab da tashi yace "karkice haka, Aliyu na bala'in son Aneesah da aure, banda burin daya wuce nakara karfafa zumuncin dake tsakanin mu, kiyakuri komi yawuce for the sake of yaranmu dakeson juna" da yatsa Ammi ta nuna kanta tana kallon Dady tace "inhar nine nan na tsugunna na haifi Aneesa da kaina y'ata bazata taba auran dan gwal dinka ba, Aneesah bazata taba auran danka ba namaka wanan alkawain walla...." da sauri Dady yatashi yadaura hannunshi kan bakin Ammi yana girgixa mata kai hawaye yacika idanunshi sosai, ahankali yace "karkice haka Rukayya, nina miki laifi, yanzu haka haryau Aliyu fushi yake dani wlh bayamin magana, don't punish Aliyu akan laifin da mahaifinshi ne ya aikata, Inaso yau around karfe biyu na dare ki leko ta window kiga, zakiga Aliyu a tsakar gida yana exercise kaman zai kashe kanshi, my son is suffering, Aliyu nacikin damuwa fiyeda tunanin ki kina ganin fuskanshi zaki gane hakan, Rukayya namiki laifi, namiki laifi kimini duk hukuncin daya dace dani anan gidan, amma karki hana marayan d'ana abinda yakeso dan girman Allah, ki barshi ya nemi auren Aneesah" hannunta daya rike Ammi ta fizge tace "lokacin daka kulle mini Aneesah karabani da ita baka taba tunanin ita marainiya bace dake kallonka amatsayin uba, ko maza sun kare aduniyan nan saida ta mutu ba aure data auri danka daka kulle ta agidan yari akai, gaka ga danka nan kajika kas......." kasa karasa maganan tayi sabida turo kofan da akayi atare daga Ammi har Dady suka dagokai suka kalli kofan Aliyune ya shigo babu ko riga ajikinshi saidan boxer idanunshi sunyi jajir yana kallon Ammi kaman yanda take kallonshi da shanyayyun idanunshi, daga Ammi har Dady kasa cemai komi sukayi, kama kofan Aliyu yayi yarike gam cikin wani irin murya kaman na wanda y yake abuge yace "Mummmmm, An...e.s" kasama fadin sunan yayi da kyau yawani irin zube awajen da sauri Dady yay kanshi. "Gadanga na, Aliyu, Gadanga na" ya shiga tapping kumatunshi yana kiranshi, kafe fuskar Aliyun Ammi tayi da ido kafin tawani irin juya tai sama ko kallo na biyu bata basuba.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



6️⃣3️⃣ & 6️⃣4️⃣

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa bank can also send MTN card to WhatsApp number na_


_GGM you guys have my heart abeg, thanks for loving ATSAKANIN SOYAYYA_


_inma bakida kudi karki karanta banyi forcing kowa ta karanta littafi na ba, dan wlh kika karanta baki biyaba ban yafeba_


_masu fitarmin da littafi waje kunma kanku kuma bazan gaji da fadi muku ban yafeba sai Allah ya sakamin_






Ko kadan Dady baya feeling heart dinshi na beating hakan yasa da sauri yadauko ruwa ya yayyafamai, bude idanunshi dasukai jajir yayi yadaura hannunshi akan kirjinshi yana nishi sama sama da sauri Dady da yagama rudewa yace "sorry Aliyuna, kirjinka kema ciwo? Sannu kaji karka damu Mummy ka zata hakura zata baka Aneesah, tashi muje nakira Dr yadubamini kai" da taimakon shi Aliyu ya iya mikewa tsaye yakaishi flat dinshi sanan yafito da sauri yaje mota yadauko phone dinshi danya kira Dr....




***
Sosai Aneesah tasaba da Dr Zaid, shima Dr Zaid din yasaba sosai da gidan dan Baffa ma yacemai inya zo ya dinga shigowa kai tsaye, tuni Aneesah tabama Inna da Ibrahim da Mubarak hakuri duk sun hakura yanzu suna zama peacefully thanks to therapy da Dr ke bata, banda haka Baffa yakarbo mata wani ruwan rubutu datake sha duk narage yawan fushi da zuciyan datake yi and Alhamdulillah yaragu sosai, tadawo kaman da, Baffa yanasamin kudi yabata dubu biyar yace Inna tarakata tadinko hijabai, aiko sukaje kasuwa ta dinga hijabai kala hudu har kasa Black, pink, maroon, da milk tadinka.
In kika karanta min littafi batare dakin biyaba ban yafeba.
Zaune suke a tsakar gida kan tabarma tana sanye da dogon hijabinta milk dayasha guga tana gyaran shinkafan hausa, Mubarak zaune kusada ita yana grating kayan miya da grater shikuma Zaid dake sanye da fararen kaya na wani soft yadi yana karanta musu wani english novel mai suna the killer tree sai murmushi suke labarin da dadi gaban tsoro, fece shinkafan Aneesa ta juya ta shiga yi tana sauraron labarin da Hafiz ke karanta musu, wani irin faduwa gabanta yayi dayasa tasaki farantin akasa hannunta ya shiga rawa, karan farantin yasa Hafiz yadago kanshi da sauri dagashi har Mubarak, Mubarak ne yace "laaaa kin barar da shinkafan Aneesah menene?" da sauri ta girgixa kai tasa hannunta ta shiga kwashe shinkafan tana cizan lips sabida kirjinta dataji yana mata ciwo sosai, kafe hannunta dake rawa sosai suna kwaso shinkafan tana zubawa a farantin Hafiz yayi yana nazarinta ganin all of a sudden kaman an tsikareta, wani irin lumshe ido tayi tareda daura fuskanta kan cinyarta tana sauke wani irin ajiyan zuciya, kwannan tamanta da batun Aliyu danta dade batai tunaninshi ba menene yanzun nan yake shigomata rai haka, dan juyowa tayi ahankali ta kalli Mubarak dake kallonta, hannu ta mikamai tana murmushi kokarin boye damuwarta ahankali tace "dan aramin wayarka nakira Ammi na Ya Mubarak" turo baki Mubarak yayi saikuma ya dauko yar wayan toculan nashi yamika mata yace "wlh karki cinyemin kudina" fizge wayan tayi. Inma baki da dari ukun biya karma ki karanta, in kika karanta ban yafeba.






Kika karanta min littafi batare dakin biyababan yafemiki ba, hakkina kuma saiya biki wlh.
Tamike tsaye dan satan kallon Hafiz tayi ganin idanunshi akanta yake yasa tadanyi murmushi tawuce labulen dakinta tabude ta shiga zama tayi abakin gado ta saka number Ammi data haddace sama da number kowa aduniyan nan tai dialing, ringing daya Ammi ta dauka murya chan kasa tace "Aneesah Ammin ta" murmushi sosai Aneesa tayi tace "Ammi na bacci kikeyi muryan ki chan kasa" yatsine fuska Ammi tayi tana kokarin danne baccin ranta ta gyara zama tace "no baby girl nagaji ne, ya kike yasu mamanki na wurin kowa lafiya ko?" gyadama Ammi kai tayi tace "eh lafiya" saikuma tai shiru, jin yanda tai shiru dan normally inta kira surutu kawai zataita yima Ammi amma yausatai shiru hakan yasa Ammi tagane akwai wani abu, murya chan kasa tace "menene Aneesah, akwai abinda kikeso ne? What is the matter?" sosai bakinta kemata nauyin fadin abinda takeso tafadi tace "a...a...ummmm" gyara zama sosai Ammi tayi tabata duka attention dinta tace "uhum ina jinki kiyi magana mana, menene eh babyn Ammin ta" ahankali cikin wani irin muryan rashin gaskiya dinan irin idan yaro yay laifin nan tace "Ya.......A...li...yy....u" saida zuciyan Ammi yawani irin girgiza da Aneesah ta tambaye ta Aliyu, Aliyu yasha cemata suna soyayya bata taba yarda ba saiyau da Aneesa da kanta takira mata Aliyu, shiru Ammi tayi dan batason tarufe ta da fada ko kadan ance idan kanason kasamu information din dakake nema awajen danka inya kawoma magana don't attack him immediately kasakin mai harya gama fadi maka komi kafin ka daki bakin gatarin da zafi, kaman babu komi Ammi tace "Yayanku Aliyu lafiyanshi kalau, menene dawani abune?" girgixa ma Ammi kai tayi hawaye na taruwa akan fuskarta kaman zata sakinma Ammi kuka ahankali tace "inaso nai magana dashi ki kaimai wayan Ammi" sake danne zuciyanta Ammi tayi kai tsaye tace "kicemai me?" kaman jiran tambayan Ammin take tasakinma Ammi kuka ahankali mara sauti sosai, cikin kuka Aneesah tace "Ammi kaman baida lafiya inajin haka ajikina sosai, gabana sai faduwa yake kirjina namin zafi duk in yafadomin arai saisa nakeso nayi magana dashi" karkada kafa Ammi ta shiga yi daga inda take zaune anatse tace "son Aliyu kike Aneesah?" tambayar da Ammi tamata saida yasa gabanta yafadi hakan yasa tasake sakinma Ammi wani kukan batare datai magana ba, sosai zuciyan Ammi ke suya tace "karki sake kimin karya Fateema, stop that crying and tell me the truth, son Aliyu kike?" yanda Ammi tamata tambayan cikin kakkausar murya yasa ta tsagaita kukan kirjinta na dukan uku uku cikin wani irin yanayi na kuka tace "Ammi nima ban saniba" karkada kafa Ammi tayi tai wani irin sound da iyayen nan keyi da baki idan yara sukai karya. "huhuhum" cikin wani irin muryan fada fada tace "batun yau nasan kina soyayya da Aliyu ba shida kanshi yafadamini, Fateema!" Ammi ta kirata dawani irin harsh tone dasaida yasa gabanta yasake faduwa murya chan kasa tace "na'am Ammi" tace "Aneesah ina sonki sama da yanda kike ganin baban Aliyu nason Aliyu banbancin shine soyayyar danake miki bata makatar daniba, I know the difference between right and wrong, ban sangarta kiba, I train you Aneesah, na koyar dake abubuwa da dama wanda koda yau nafadi na mutu zaki iya amfani da abubuwan dakika iya ki kula da kanki dasu, I train you nabaki ilimi, sanan nakoma miiki yan hikimomin rayuwa, yanda baban Aliyu ke takama danshi maraya ne baida mahaifiya haka kema kike marainiya bakida mahaifi, da ace da muka shiga gidan nan Aliyu ne yabaki poison koda sama da kasa zasu hade mutumin nan bazai taba iya hukunta yaron nanba talk more of yakaishi har gidan yari, Aneesa ninedai na haifeki ko, sanan jinina ne ke gudana ajikinki ko, inhar ni mahaifiyan nan naki na isa dake, sanan ke yar halak ce zakimin hallacci inaso kicire Aliyu daga ranki, kifadama zuciyanki mahaifiyarki tacemata ta nisanci Aliyu, bazaki taba auren Aliyu ba, bazan taba bari ki auri dandan wanda ya wulakanta mini ke aduniyan nan ba, bamu da kudi amma munada Daraja, zan nunamai ciwa inhar sone shi baima Aliyu komi ba danni babu wanda zai wulakanta mini abin sona na yafemai har abada! Bazaki taba auren Aliyu ba, kicire sonshi daga zuciyanki can you do that for me Aneesah?" hawayen dasuka kasa zubowa ta share da bayan hannu ahankali tace "eh Ammi n....aji" shiru Ammi tayi tana sauraron yanda muryanta ke rawa tasan kuka take, murmushi Ammi tayi tace "ke yarinya ce bazaki gane me nake miki ba, just stay put ki kulanmini da kanki kinji, nakusan zuwa wurinki kinji" gyadama Ammi kai tayi ahankali tana goge kwalla, dan shiru Ammi tayi for a while kafin ahankali tace "Dr Zaid fa meye tsakanin ku? Baffan ku yacemin kullum saiyazo wajenki meye tsakanin ku?" hawayen dasuka zubomata ta goge tace "babu komi yace shi Yayanane, kome ke damuna nadinga fadamai" murmushi Ammi tayi tace "to shikenan, jeki taya Inna aiki, sai anjima" katse wayan Aneesah tayi tafashe da kuka sosai tama rasa meke sakata kukan nan, tayi kuka na almost 10min sanan ta lallashi kanta tasa bayan hannunta ta share fuskarta tass, kafin tasa hannu ta dauki wayar Mubarak din tamike tsaye tareda juyowa Dr Hafiz tagani tsaye ya zuba hannayenshi a aljihun wandonshi yana wani irin kallonta idanunshi sunyi jajir jijiyan kanshi sun fito sosai yana kallonta, wani irin dan tsoro taji dan tunda take ganinshi batama taba ganin fushin shiba, talk more of ganinshi yana kallonta haka kaman zai rufeta da duka to meya faru? Metamai?" ahankali tabude baki zatai magana yanuna mata hannunshi azuciye alamun tamai shiru, sanan yanuna kanshi yace "kin tsaya kina zubar da hawayen ki kan wani banza da baima damu dako kina raye ko bake rayeba, mutumin da mahaifinshi yasa a kulleki agidan yari mafi muni d worse of all prison yards na Abuja, kina hawaye akan wanda yaraba mahaifiyarki yarta guda daya tilo aduniya takasance cikin bakinciki, gamai sonki, someone that has always being by your side tun ranan da aka sakoki trying to keep you happy, trying to keep you company, mutumin da abandoned his work na ceto rayukan mutane and come here just to keep you company and make you happy you think am doing all of that for fun Aneesah?" yafaka mata tsawa, saikuma yay dan murmushi irin wanda za'a kira da murmushin nan mai ciwo yace "okay you asked for it and here we go" yay dan shiru kafin yace "ina sonki Aneesan! Ina sonki so banawasa ba, I love everything about you, your strength da aggressiveness sune abu na farko daya fara pulling heart dina zuwa gareki, I fell deeply for you, I love you so much but you broke my heart yau danazo naji kina kuka kan saurayin da kika wulakanta aduniya sabida shi, kikaso kizama wata irin hallita da inda yan uwanki weren't patient enough ba'a taru an taimaka miki ba da yanzu kin zama wata abun daban, shine kikema kuka haka, u hurt me girl thank you" yajuya cikeda zuciya yafita daga dakin yawuce waje ya shiga motarshi zuciyan shi na tafarfasa.




In kika karanta baki biyaba Allah ya isa.
Tafi minti goma sha uku a tsaye tana tunanin kalaman da Hafiz yafadi mata, ita Hafiz keso? Dama abinda yasa kullum yake zuwa gidansu kenan? Tadade tana tunane tunane kafin tafice kitchen, ahankali ta shiga kitchen din ta tsugunna kusa da Inna dake gindin murhu tana tukin tuwo tace "kawo in tuka tuwon Inna" dan waigowa Inna tayi ta kalleta ganin yanda muryanta yay sanyi tace "nariga nagama kya kwashe, naga Likita yafita cikeda bacin rai meya hadaku? Kindai san samari na wuyako kwanan nan, kin sami yaro mai hankali ga aikin hannu mai abinyi, gashi yanason yan uwanki ya daukemu kaman iyayenshi kinamai wulakanci karki baridai ya subuce miki kinajina ko" tunda Inna ke maganan take kallonta towai waya fadamusu soyayya suke daman, dan juyowa Inna tayi ta kalleta jin tai shiru tana ciro muciyan daga tukunya tace "kinmin shiru bakiji minace bane?" girgixa kai Aneesah tayi ahankali tace "ba soyayya mukeba Inna, kawai yayana ne" dawata irin dariya inna ta kwashe tace "hohoho su Aneesah an girma nikikema karya, mutumin daya shigo dakin Baffan ki yace yanason Baffa yamai izinin yafara neman nakine saisama kike ganinshi yana shigowa gidan nan kai tsaye danmu mukamai izini mun yarda da tarbiyanshi shine kikemini karyan kunya sannu kinji zulliya" Inna tafashe da dariya tamike tsaye tasa hannu ta dungure kan Aneesan datai shiru tace "tashi nidai ki kwashe min tuwon bari naje na kwaso daddawan da Mubarak yadakamini a turmi nazo na hada miya" fita Inna tayi tabar Aneesah cikeda mamaki da yakasa boyuwa daga fuskanshi.

Kika fitarmin da littafi ban yafemiki ba.
Washe gari misalin karfe shabiyu Baffa da Kawu Nasani da tuntuni suna gida basu fita ko inaba sukai baki wasu manyan mutane ne maza sunci kayan alfarma, falon Baffa aka shiga dasu sanan taji anata zancen dudda batajin me suke cewa but tanajin hayaniyan su sama sama, saida ana kiran sallan azahar ne suka fiffito tareda su Baffa aka tafi, itadai tana daki jinta take wani iri kawai takasa mance maganganun Hafiz.



Kika karanta min littafi batare dakin biyaba ban yafemiki ba, littafin nan nakudi ne pay 300 access fee.
Sallame sallan isha'i da akayi yasa Baffa yamike da sauri yafito wajen masallaci tun araka'an shi na farko ake kiranshi yarasa wake kiranshi haka, ciro wayan yayi daga aljihu ganin Alhaji Ibrahim Muhammad ne yasa wani irin mamaki ya kamashi harsaida yace "Alhaji!" wayar ya tsaya yake kallo ganin kiran na neman katsewa yasa yace bari yadauka yaji kuma dawacce yazo kara wayan yayi a kunne. "Assalamu Alaykum" Dady yamai sallama anatse, Baffa baikawo komiba ya amsa kaman wani abu baitaba hadasu ba. "waallaikumu sallam Alhaji yau agarin, ya aiki? Ya yara yakuma Iyali da fatan kowa lafiya?" shiru Dady yayi yana wani irin jin nauyin Baffa sabida rashin mutuncin daya musu tayaya ma zai fara ga yamai abinda yake tafe dashi? Baitaba abinda yakejin danasani dakuma kunyan kanshi ba kaman wanan kuskuren dayayi akan Aneesa, he is so ashamed of himself, jin shiru Baffa yace "naji shiru Ince dai lafiya ko?" ajiyan zuciya ya sauke dahar Baffa saida yaji sanan yace "Alhaji nasan hausawa nacewa rama mugunta ga mugu ibada ne, amma nasan muminai masu zukata mai kyau bakwa amfani da wanan karin maganan al'adan mu na hausawa, Alhaji ni mai laifi ne ninasan da hakan, amma ban isa na chanza abinda Allah ya tsara cewa zai faru ba, Alhaji ayau nazoma da gingima gingiman zancen guda Biyu dan Rukayya taki kallona kokuma saurarena, Alhaji kiyafemin laifin dana aikata akan Aneesa, na tafka shirme da shirin mata yasa nai hakan, ka yafemin, ka yafemin dan girman Allah, wlh nai nadama, nai nadama matuka ban kyauta ma amanan Aneesah daka damkamini a hannu ba na kuma karbeta a matsayin mahaifi ba, Alhaji kiyahakuri dan girman ubangiji" da sauri Baffa yace "haba Alhaji kadena rokona bakamin komiba tuntuni na yafema, Allah kuma ya yafemana gabaki daya, amma komi yawuce babu wanda ya isa ya ketare jarabawan Allah, so komi yawuce wlh" ajiyan zuciya Dady ya sauke yace "sai magana ta tabiyu, Alhaji Aliyu baida lafiya sosai wlh yau kwanan shi hudu a asibiti kenan yana fama da mugun ciwon kirji, Alhaji Dr yace zuciyanshi yadan kumbura wlh" Dady yakarasa maganan kaman zai saki kuka dayasa Baffa yaji yamugun tausayamai yace "ubangiji Allah yabashi lpy, karkadamu kaitamai addu'a, ammadai wanan batu baimin dadi ba, ciwon yaro babu dadi ko kadan" cikin wani irin yanayi Dady yace "Alhaji alfarma nazo nema wajenka, Aliyu na matukar kaunar Aneesah batun yauba, nasan nai kuskure shima bada sanin shi nai hakanba da bazai barni ba lokacin baya cikin hayyacinshi, Alhaji ku taimaka mini badanni ba bakuma dan halina ba sai dan Allah kubama d'ana auran yarku, karna rasa Aliyu dan girman Allah, Alhaji nina muku laifi please karkuyi punishing d'ana for the mistake of his Dady dan kaunar ubangiji ku dubeni da fuskan tausayi badanni ba dan girman Allah" yanda muryan Dady yasauya kaman wanda ke shirin kuka yasa Baffa yagane lallai lallai kam Dady na cikin masifaffen tashi hankali amma kuma a yanzu ahaka babu abinda zai iya mishi. Dan ajiyan zuciya yasauke yace "Alhaji mu manya ne, ba'asan manya da magana biyu ba ko kwana kwana kokuma yin karya ba, karkuma kazaci abinda zan fadamaka kodan ban hakura bane kokuma wani abun uhm uhm wlh ko daya, ciwo yawuce komi, Alhaji bazanma karyaba a yanzu haka kudin auren Aneesa ma akanwo shi, yau dinan akai komi nasaka mata rana wata daya da sati daya sabida mijin likita ne zaije PhD a Cuba 🇨🇺 anaso dazaran anyi aure saisu tafi Cuban tare, kayakuri amma a gaskiya babu abinda zan iyamaka da kaman kazo dawuri ne, ina maka fatan alkhairi sanan Allah yatashi kafadan Aliyu yasa kaffara ne, Allah kuma yabashi lafiya yabashi wata matar tagari, nabarka lafiya agaida mai jiki saida safe" Baffa ya katse kiran.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



6️⃣5️⃣





Janye wayan Dady yayi daga kunenshi ya kalli Abdul dake tsaye gefenshi da baturen Dr Aliyun dayake tsaye shima duk suna jiran suji me Dady zaice amma yakasa magana sai Aliyun dake kwance kan gado an makalamai wasu irin abubuwa akan kirjinshi na asibiti yana numfashi sama da Kasa yake kallo, lumshe ido Daddy yayi alhakin Aneesah ke kamashi saisa abubuwan nan ke faruwa dashi, Rauda tarasu, Aliyu gashinan shima rai a hannun Allah, matayenshi dukya rabu dasu dan sune silan matsalolin shi, Rukayya tama tsani ganinshi, ga yaran shi duka agida Nannies daya dauko musu ke kula dasu, shi kanshi daurewa kawai yakeyi amma ko kadan baida kwanciyan hankali, dafa kadarshi da akayi yasa yadago kai Dr Aliyu ne, murmushi yamai yace "calm down Sir, I promise I will do everything in my power naga danka ya warke I promise you, just be strong for your Son" gyadamai kai Dady yayi yama kasa magana Dr yajuya yatafi, ahankali Abdul ya matso kusada Dady yace "Dady rana aka samata wai?" gyadamai kai Dady yayi ahankali Abdul zai saka wani maganan Dady yamike tsaye kaman wanda baida lpy yace "Abdul kazauna dashi ina zuwa" yafita Abdul ya bishi da kallon tausayi, a mota yasami bodyguard dinshi suka jashi sai gida, wuraren karfe goma da rabi suka shigo gidan, parking sukayi baima jira sun budemai ba yafito, flat din Ammi yawuce kofar yasa hannu zai bude yajita a kulle da sauri yay flat dinshi ba'a jimaba yadawo dauke da makulli yabude kofar, ahankali ya shiga babu kowa sai wanan mayen kamshin dakin nan nata dake tashi yay upstairs, ahankali ya tura kofar bedroom din Ammi da sauri Ammi dake kan dadduma tana addu'o'i ta dago kai ganin Dady ne idanunshi sunyi jajir yasa tadauke kai, ahankali ya shigo dakin tareda maida kofar yarufe yakaraso wajen dadduman yana kallonta, shafe addu'a Ammi tayi tamike tsaye tareda zare hijabin jikinta ko damuwa da yanda Dady ke kallonta batayiba gaban gadonta taje ta zauna tana kokarin cire dan kunnin kunnenta danso take tai bacci, ahankali Dady yazo wajen, zama yayi akasa tareda daura kanshi kan cinyarta yasaki wani irin kuka, to yama rasa mezaiyi abun duniya sunmai yawa, cikin kuka sosai yace "haba Rukayya, baki yafiya bazaki yafemini ba, nina miki laifi, ninama Aneesah laifi, please ki raba wanan zancen sa ranan Aneesah, don't punish my son over the mistake of his Dady, am sorry, bansan tayaya zan baki hakuri, kiyakuri badanniba badan halina ba kiyakuri dan Allah, ki tausayama Aliyu Rukayya, wlh natuba, nai nadaman abinda nayi" dago kanshi yayi da sauri suka hada ido da Ammi dake kallonshi kyam, ahankali yakama hannunta yana goge hawayen dake zubomai yace "naji ki rama dukan danama Aneesan, ki rama dan Allah kinji" ko alamun daga hannu batayiba hakan yasa yasaki wani irin kuka yana kallon yanda Ammi ke kallonshi yace "Rukayya wlh ina sonki kema kinsan hakan, kiyakuri for the sake of wanan cikin namu dakike dauke dashi kiyafe mini kibama Aliyu Aneesah" wani irin murmushi Ammi tayi tace "Alhaji kenan katuna sanda nake kuka haka ina rokonka ka sauraren? Ina ciwo ina fama da laulayi ina rokonka ka sauraren kamaji tausayina? Karabani da y'ata na kimanin sati hudu da kwana tara bansa abin sona araina ba kaji tausayina? Saidai kullum ka kama uwarta kana haiketa ba dare ba rana ba safiya ka maidani abinci amma y'ata nachan ka kulle ta agidan yari kaji tausayina?" lumshe ido Dady yayi wasu irin hawaye na zubomai masu bala'in dumi, tabe baki Ammi tayi tace "wlh d'a baifi d'a ba kaji yanda akeji, ciwo kuma Allah ne yadaura ma Aliyu shine kuma zai yayemai inyaga dama amma ko Aliyu na kakarin mutuwa ne bazan taba bashi y'ata ba kaje kajika dan gwal dinka kasha duniya daman fadi gareta dan hakin daka raina shike tsolemaka ido, danka baimin komiba yatace dai bazan bayarka kai amfani da kudaden ka da power ka kaje akero maka wata Aneesa ka kaima dan gwal dinka, sanan katashi please ka fitarmin daga daki cikin nan baison sautin

Please Login or Register in order to submit comment