Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "you must be very very silly Aliyu dahar zakai tunani zan iya sakin Aneesa sabida kace, I know the kind of pain you went through Aliyu, nine nasan wahalan dakasha, ikon Allah ne yasa kawai baka mutuba, Gadanga bazan yafema Aneesa ba wlh tunda taso cutar dakai saita biya bashin dataci sanan karka karamin maganan nasa asaketa dan hakan bazai iya faruwa ba" cikin wani irin murya Aliyu yace "Dady you are so cruel, so mean, so heartless and Dad you are so wicked!" dawani irin fushi Dady yadaga hannu zai zubama Aliyu mari. "Aliyu!" saikuma ya tsaya batare daya saukemai marinba, cikin mugun fushi Aliyu yace "slap me Dad, hit me kaman yanda kama Aneesa dayafimini dan u are not that man I use to look at as my hero, mutumin danake ma kallo as the best father in the world, u are not Dad, you are nothing but a heartless wicked Man with no any compassion" da yatsa Dady yanuna Aliyu yace "watch your tongue Aliyu sabida nasoka da yawa na lalataka doesn't mean u are the father am the son dazaka dinga gayamin magana ba, I did what I did to fight for you, sabida kai nai hakan, abinda nayi was for love and justice, bana zalunci she tries to kill you and polisawa sukai arresting nata for attempt murder" wani irin ihu Aliyu yayi kaman zai fasa gidan yace "how can you believe what you saw on CCTV footage Dad? I tot u are way smarter than this? Visuals can be deceptive Dad, sau nawa mukasha gani a movies anyi video dashi wanda yake video yasan baitaba yin abu makamancin abu hakaba, menene computer bayayi? The only thing da computer bayayi shine ya busama dan Adam numfashi, how can you believe this eh?" ahankali ya sassauta murya yace "okay Dad am sorry for yelling at you, kasa asaki Aneesa yau and I promise you cikin just 2 days two days kadai zaka bani I will prove to you cewa this is not a real video is just a set up I promise Dad amma kafara sa asaki Aneesan, Dad Aneesa bazata taba iya kasheni ba, bazata taba iya samin poison a abinci ba I promise you Dad, kasa asaketa kaji Dady" wani kallo Dady yamai cikeda taurin zuciya dakuma tsatsauran ra'ayi yace "No one breaks my policy easily Aliyu inhar akanka ne, batun yau nasha fadaba any body dat dares comes for you will definitely sees my other side, bazan taba sakin Aneesa ba Gadanga harsai tai paying for her crimes and that's final" wani irin kallo Aliyu yakema Dady kaman yanda Dady ke kallonshi kafin yawani irin juya yafita daga dakin azuciye da sauri Dady ya bishi yace "kai Gadanga ina zaka eh? Wai mesa kacika bakin zuciya ne, Gadanga" generator house dinsu Aliyu yayi Dady na binshi da gudu yana kwalamai kira har hakan yasa aka fara fitowa ana kallonsu, jarkan petrol Aliyu ya dauko da sauri Dady yamika hannu zai karba yace "lafiyan ka Gadanga ka haukace ne?" cikin ihu sosai Aliyu kaman wanda zai hadiye zuciya yamutu ya fizge jarkan yace "leave me alone" ya bude jarkan ya shiga antayama kanshi petrol din yana kallon Dady dake kallonshi a mugun rude saida yagama juye fuel din ajikinshi sanan yawani irin jefar da gallon din yatura hannunshi a aljihu yaciro wata sabuwar lighter, ihu Dady yayi yace "kai Aliyu ka haukace ne" yay kanshi cikin wani irin yanayi na kaman zarewa Aliyu yace "don't come here Dad ka tsaya a inda kake, yace badai nine matsalan kaba takaina kake azabtar da yarinya yau zan kona kaina, na kashe kaina, in mutu right in front of your two eyes Dad then you will understand the pain Mum is going through na rabata da yarta dakayi ka kaita chan wata duniyan da babu wanda yasani, Dad Aneesa ita kadaice macen da zuciyan danka ke bugun mawa, I love her, I love Aneesa Dad, how dare you ka kulle min wacce nakeso for a month plus eh Dad" Dad dayadawo kaman zararre yamikama Aliyu hannu cikeda lallashi yace "kaga Gadanga na kayakuri, calm down, kar wanan zuciyan naka yakaika ga halaka Hydar, ka kashe kanka wuta zaka, calm down okay, bani lighter kayakuri" girgiza mai kai Aliyu yayi cikin tsananin fushi yace "kasa ayi realising Aneesa right now Dad, right now Dad kona kashe kaina" da sauri Dad yana girgiza kai yace "to, to to naji, zansa" ya shiga laluben wayanshi dake aljihu yaciro yashiga dannawa dukya rude kaman zararre yace "don't do anything stupid Aliyu kanajina ko, zan kira yanzu" "Hello officer, I.....i...." yana maganan yana kallon Aliyu alamun kyasta lighter Aliyu yayi yace "now Dad" da sauri Dady yace "I withdraw the case against Fateema Aneesa Maikwato, ku saketa re...release her" katse wayan yayi yana maidawa aljihu ya kalli Aliyu yana mikamai hannu yace "done nafada zasu saketa, oya oya bani lighter, bani Gadanga kaji" wani irin kallon Dady yake kafin ahankali yace "ka azabtar da Aneesa right in front of her Mother's eye, Your pregnant wife the woman that was bearing your child in her womb suffered, got sick, always crying pleading kasaki Aneesa kaki, yan uwan baban Aneesa they all came sun rokeka kaki, Dad duk sabida ni wanan Aliyun daba komin komiba kake wulakanta mutane haka, akaina bakasan menene yafiya da hakuri da tausayi ba all this 3 u lost them, Dad now watch kasan Yaya mahaifiya keji idan taga abinda ta haifa nashan azaba" yana maganan ya kyasta lighter.................






Wani irin ihu Dady yayi kaman zai haukace. "Aliiiiyuuuuu......" chak ya tsaya yay shiru ganin hannun daya chape lighter tun kafin wutan yafito daga ciki, hannu Ammi tasa ta mareshi hawaye na zubowa daga idanunta tace "are you mad Aliyu kashe kanka kakeso kayi kamutu kafiri?" fashewa da kuka sosai Aliyu yayi yafada jikin Ammi for the first time yarugumeta. "am sorry Mum, am sorry mum, Mummy forgive me" da goshi tayi daga jikinshi tasa hannu ta sharemai hawaye tareda girgizamai kai tace "never in your life try such things again, Aliyu don't ever go this extreme sabida kanaso amaka abu, wuce kaje kai wanka ka chanza kayan nan" gyadamata kai Aliyu yayi yajuya yanadan dingishi yay hanyar flat dinshi batare daya kalli Dad ba, itama Ammi ta juya da sauri dan yanda ya shafamata petrol warinshi nasata jin amai sosai da sauri ta shiga bathroom dinta tana kaiwa flat dinta.







*_ZILANIOUS PRISON HOME AND CONFINEMENT_*

_Theatre_
Wutan theatre da aka chanza daga Red zuwa fari ne yanuna alamun angama operation din, bude kofa akayi wasu likitoci ne guda uku mata biyu saikuma namijin Dr dasuka saka a tsakiyan su dake rike da folder, folder yamika ma Dr dake gefenshi yace "hold this Dr Farida, write on the surgical procedure, I gat to go now, My Mum has been calling batajin dadi sosai" karban folder tayi tace "ayyah Allah kara sauki Dr Zaid" handglove din hannunshi yacire yazuba a abin sharan dake gaban theater sanan ya wanke hannunshi a wash hand basin din dake wurin ya cire lab coat dinshi yarike hakan ya bayyanar da cooperate dress din dake jikinshi na riga da wando blue da black yay zanzaro, ga neck tie, hannu yadaga musu alamun bye yajuya yafita, masu gadi dake bubbude mai kofa namai sallama harya fita wajen prison din inda ake parking motoci yashiga cikin wata fine jeep yarufo, yana kokarin tada motar ne wayarshi yashiga kara hakan yasa yadauka yakara akunne........






Da sauri Officer police din ke shiga prison din matan wasu mata masu ma'aikatan prison din matan biye dashi harzuwa gaban wani daki da aka rubuta _dark room_ ajiki, yawanci dakine da ake saka wayanda sukai laifi suyi kwana da Kwanaki aciki, makulli officer ya karba daga hannun daya daga cikin guards din dasuka biyoshi yabude kofan kafin yatura kofan da karfi dan tsakurkurin dakin ya bayyana da sauri wacce ke ciki tasa duka hannayenta tarufe fuskanta dan jitayi hasken kaman anzuba mata yaji a idanu takasa bude ido, da sauri officer yace "kufito da ita ku kaita waje an sallameta" daya daga cikin guard dinne tace "wai munhuta da jaraban _Barkono_ kenan" suka shiga kafin suwani irin fizgota gashinta ya barbaje ya rufemata fuskanta sukajata suka fito da ita kaman sun dauko mattacen rago har zuwa gaban kanta prison inda kake karban abubuwan da mutum yazo dashi prison yasaka yabasu kayansu, officer dake bayansu ne yace "kai yarinyar nan case din senate president ne yace ai release nata with immediate effect banda lokacin dazan jiraku nemo mata kayanta ku fitar da ita ahaka ta tafi da kayan gidan yarin mun bata, ku fitar da ita ta nemi hanyan gidan ubanta" da sauri sukace "yes sir" janta suka sakeyi kaman wata kayan wanki suka fito daga prison din......
Kika fitarmin da book waje? To banyafe miki ba
Yanacikin waya kaman ance yadaga kai yaga ya hango some security guard harsu hudu sunajan wata da baya iya hango fuskanta sabida gashi daya rufe kanta gabaki daya har wuyanta kaman wata animal, shi in his life he hates inhumane treatment daidai sunzo zasu wuce ta gaban motarshi yabude yafito da sauri duk suka tsaya sukace "sannu Dr" bai tsaya amsa gaisuwan suba yace "why are you people treating a prisoner like an animal jibi yanda kuka janta, by the way ina zaku kaita?" daya daga cikinsu ne tace "Sir an sallameta dama tuntuni ta addabemu a prison mun daketa mun daketa kaman jaka she's so violence shine daga baya muka kulleta a dark room dan ita tafasama yarinyar dakama surgery dazu ciki da karfe which anyi hani da sharp object a prison shine take receiving serious punishment, yanzu kuma kawai oga yazo yace ansallameta mufitar da ita waje ta nemi hanyar gidan ubanta" ahankali ya girgiza kai yace "kuji tsoron Allah no matter what, no matter how she is she's entitled to her constitutional right, wanan abin kuma is maltreatment, look at her condition how do u people expect her taje gida dakanta tamasan inda kanta yakene?" tabe baki daya daga cikin matan tayi tace "pls sir we are only doing our job, kai u are just a per-term doctor bakasan how things run in this school ba, kuma yarda ita mukoma ciki pls" sukabi ta gefenshi sukadanyi nesa kadan da inda yake suka wani irin jefar da ita kaman wata mushe sanan suka koma ciki batare dasun kalli ko inda yakeba.

Tsayawa yayi yana kallon yanda yarinyar ke akulle he took an oath a proffesion dinshi yay protecting life and to help anyone that is in need of medical attention bari yadauke ta yakaita asibiti inta warke properly saita koma gidansu kokuma yatayata kiran iyayenta suzo su dauke ta, tunanin hakan yasa ya shiga mota yatada yaja harzuwa inda suka jefar da ita sanan ya kashe motan yafito yazo inda take ahankali ya tsugunna yay bismillah yadauketa ko kadan batada nauyi sanan yabude bayan motan shi ya sakata yamaida kofan yarufe sanan yakoma gaba ya shiga yaja motar yana kallonta ta glass din gaban motar har lokacin fuskanta arufe da gashi.
In kika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa.





Kaman wacce aka tsungulla tadaga hannu ahankali tadaura kan gashin dasuka rufe mata idanu tajasu ta matsar dasu gefe fuskar Aneesa ya bayyana, idanunta sunyi bakinkirin ta labka wani irin uban kwalli kaman wata yar daba, fuskarta yay baki, pink lips dinta ne yakenan jajir kaman fresh meat, ahankali take bude ido dayake glass din motar tinted ne motan babu wani haske sosai yasa ta iya bude idanun kadan kafin ahankali tabude idanun duka fuskarta babu alamun ko digin dariya, idanunta sunyi wani iri kaman bana Aneesa ba ahankali take kallon saman motan zuwa ko ina na motan ahankali har idanunta suka sauka akan mutumin dake tuki abinshi hankalinshi akan tukin da yakeyi wani soft music natashi, wani irin daga kafanta tayi ahankali tajawoshi ta daidai inda hannunta zaikai ahankali tasa hannu taja wando ta sama, saiga wata yar wuka ta bayyana acikin bakar safar dake kafanta dake cikin kumbos din kafarta na prison, ciro wukantayi tawani irin tashi zaune tamike tsaye tadane bayan kujeran driver kaman wata yar biri takama kan Dr tadaura wukan akan wuyanshi cikin wani irin murya kaman ta rikakkiyar yar daba tace "waye kai? Me nakeyi a motar ka? Ina zaka kaini? Kasan waka dauko kuwa?" tai maganan tana kara rike kanshi gam ko motsi baya iyayi takara danna wukar akan makogoronshi kaman wacce ke shirin yanka rago motarsu a kwana kwana kaman zasuyi hatsari amma ko dar.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣3️⃣





Cikin wani irin yanayi na wanda ke kokarin kwatan kanshi yadan bugi hannunta dake wuyanshi trying to free kanshi da kyar yace "a....am..a..." baikai ga karasa maganan ba motar nasu tawani irin yin gefen hanya ta doshi wani babban bishiyar mango zai daki bishiyan dakenan gefen titi cikeda karfin hali irin na kwararren namijin daya iya tukin mota ya take burki da duka karfinshi hakan yasa tayoyin motar suka wani irin yin kara motar ta tsaya bayan sunyi kaman zasu fadi, hannun Aneesan yarike da kyar yanaja daga wuyanshi da kyar yace "pls....am....a....Doctor, likit....." ganin yana shirin mutuwa yasa ta janye hannun nata daga wuyanshi ya shiga tari kafin ta zagayo tadan hanyan dake in between kujerun gaban, tawani irin tsugunna kan wajen tai pointing mishi wukan hanun nata tana kallon yanda yake tari, ganin tarin yaki tsayawa yasa tadau goran ruwan datagani a motar ta bude tamikamai ahankali yasa hannu yakarba batare daya kalleta ba yakafa abaki saida ya shanye ruwan tass sanan ya cillar da goran kasa, saida yaji dama dama, tarin yadan natsu kafin ahankali yadago kanshi tareda juyowa ya kalleta hada ido yayi da Aneesan data tsugunna tana mai pointing yar wukan hannunta ko kyafta ido batayi kaman yay gamo da yar aljanna, saida gabanshi yafadi, gabaki daya sorrounding din idanunta sunji bakin lalle kwayar idanunta ne kawai fari, gashinan nata yay daka daka ya barbaje akan fuskanta ya sauka har kafadarta ya rurufe mata kunnuwa, cikin wani irin yanayi na mugun jin haushin ta yace "are you mad?" gyadamai kai tayi tace "yes" cikeda masifa yace "are you mad kasheni kikeso kiyi ne?" ko gezau batayiba da tambayanshi cikin dakewan murya tace "ba kashe ka zanyi ba, but zan kasheka yanzu in baka bani amsar tambayata ba, nace waye kai? Me nakeyi acikin motarnan" cikida fushi yace "naga some guards sun fitoda ke wai a sakeki suka yardake, they dumb u like a piece of gabbage, you don't look good bamakisan inda kanki yakeba shine I took you to drop you at any nearby clinic abaki taimakon dakike bukata, inhar kika tashi saiki tafi gida kokuma kisa akira iyayen ki suzo su dauke ki, but ni ba mugu bane and banda anybad intention akanki" tunda yake maganan take kallonshi saikuma takoma kan kujeran gefenshi ta zauna da kyau tana linke wukanta tace "yau wata daya da sati biyu kenan rabon da wani ko wata yamin mutunci kokuma yamin taimako, hahahaha" ta kyalkyace da dariya saikuma ta tsayar da dariyan tadan tashi tazo wajenshi da sauri yay baya yana kallonta adan tsorace yace "wai me haka? Kinga fita daga motana tunda dai kin farka kinemi gidanku, jibeki as small as ur are but u are so violence g......" hannunta data daura ahankali kan aljihun riganshi ko alamun tsoro batadashi tana kallon fuskanshi yasa yay shiru shima yana kallonta jidayayi hannunta zafi sosai alamun she's running temperature, wayarshi tazaro daga aljihun gaban rigan ahankali kirar iPhone ce wayar tarike a hannu takoma kan kujeran gefenshi ta zauna.





Yanda yabita da kallo yasa tace "relax, am not going to spoil your expensive phone" tana maganan tana saka number Ammi kafin tai dialing number takara wayan kan kunenta, saida wayar ta gama kuka ta katse Ammi bata dagaba, akaro na uku ne Ammi tai picking takai wayar kunne tareda sallama. "Assalamu Alaykum" wani irin lumshe ido Aneesa tayi heart dinta na girgixa after couple of days da aka kawota prison dinan tadinga kuka tanajin bakin ciki daga baya tazo ta hakura, this is the second time dataji wanan kukan bakin cikin na zuwan mata, she promised her self bazata kara kuka ba, she's a fighter, a strong girl, her mother's daughter da with or without Ammi she can live anywhere and survive.
"Hello waye banaji, helloooo waye?" wani irin ajiyan zuciya Aneesa ta sauke tana danne kukan datakeji yana tasomata da duka karfinta rabon dataji muryan Ammin ta harta manta, karan ajiyan zuciyanta da Ammi taji har cikin zuciyanta yasa kirjinta yawani irin buga, da sauri ta nemi gefen gado ta lallaba ta zauna kirjinta nabugawa sama da da, bakinta har rawa yake tace "A....Anee....s....sah.....na!" lumshe ido Aneesah tayi da sauri jin yanda Ammi ta takirata, cikin wani irin murya kaman na wacce ke shirin kuka Ammi tace "Aneesa talk to me, kece? Fateema na?" bude idanu Aneesa tayi ahankali kafin cikin dakewa da taurin zuciya da wanan muryan nata daya dawo kaman na wata rikakkiyar yar daba tace "Ammi!" wani irin fashewa da kuka sosai Ammi tayi ta wayan jin muryan Aneesan tace "Aneesah meya sami muryan ki? Me suka miki mutanen nan eh, mesa kike magana haka? Innalillahi wa innailaihi raji'un, Ya Allah gani gareka ka karemin yarinyar nan, Aneesah na what happens to you are you okay my baby?" lema leman dataji akan idanunta yasa ta sauri ta taba fuskanta hawaye taji da batasan tayaya ta fitar dasuba, da sauri ta goge fuskan cikin dakewa da wanan muryan nata tace "lafiyata kalau Ammi, kefa? Bakida lafiya ne? Kinyi wani iri menene Am....." bata karasa maganan ba Ammi tasake fashewa da kuka, bata ganin Aneesa amma hakanan tasan tanada babban aiki a gabanta, hankalinta yatashi wanan ba Aneesan ta data bama tarbiya mai kyau bace, this is anew Aneesa, yanda taji tana magana yasa taji zuciyarta ta tsinke kawai kiran sunayen Allah takeyi a zuci, da kyar ta daure ta share hawaye ta tareda tashi da sauri ta kulle kofar bedroom dinta da key sanan tadawo ta zauna ta share fuskanta tass, anatse tace "Aneesah na?" "uhm" ta amsata ahankali, sake daurewa Ammi tayi ta hana kanta kuka tace "kina ina yanzu haka a ina kika samo wanan wayar dakike kirana da ita? Tuntuni kina inane eh? Ina polisawan nan suka kaiki?" dan shiru tayi kaman bazata ce komiba saikuma ta dake zuciyarta nawani irin tafarfasa tace "prison! Ina gidan yari Ammi!" wani irin kuka dayazo ma Ammi yasa da sauri tadau pillow gefen gadon ta taushe bakinta tana kuka sosai, yarta ne Alhaji zaikai gidan yari? 20yrs old mace Alhaji zai aika prison? Me Aneesa tamai? Mai Aneesa tamai? Jibi yanda gidan yari yadawo mata da y'a? Dudda bata ganinta amma jibi muryan yarta, Alhaji ya cuceta bazata taba yafemai ba, Aneesan ta ce yanzu tai rayuwa a gidan yari? Tai wahala taga ukubobi na rayuwa haka? Ko hanyar gidan yari batasani ba amma tanajin labarin gidan yari tunko tana Amarya. Takai almost one minute ba tace komiba kafin ahankali ta janye pillow ta ijiye cikin wani irin muryan ban tausayi Ammi tana girgiza kai tace "how are you Aneesah na? Are you fine? Are you okay? Me suka miki achan? Sun wahalar dake?" gyadama Ammi kai tayi kaman tana gabanta cikeda dakewa tace "lafiyata kalau karki damu Ammi" gyadamata kai Ammi kawai tayi kaman tana ganinta tana mugun mamakin Aneesan, tasan she's just forming tasan karya take mata, tanaji a jikinta yarta ta wahala, tasha azaba, murya chan kasa tace "kina ina yanzu?" kallon hanya tayi tace "ina hanya ansakeni daga gidan yarin suka jefar dani wani mutumi yadaukeni zai kaini asibiti saikuma na farka yanzun nan" da sauri Ammi tace "kika farka? Suma kikayi?" girgixa kai tayi tace "Ammi karki damu, lafiyata kalau" "innalillahi wa innailaihi raji'un Aneesah, Aneesah, Aneesah wayyo Allah na zuciyata zan mutu" Ammi tama rasa natsuwarta sai sambatu kawai take tana kuka sosai da sauri Aneesa ta katse wayar dan inta cigaba da sauraron yanda Ammi ke kuka Ammi will just break her heart ne, kifa kanta tayi ahankali kan cinyoyinta mutumin nan nabinta da kallo, dudda wayan ba'a speaker takeba yana tsintar some maganganun Ammi cikima harda yanda Ammi ke kuka tana tambayanta meya sameta sosai yaji sun mugun bashi tausayi dudda baisan wacece itaba but hakanan yaji ajikinshi something da kuma situation ne yadawo da ita wanan yar daban.







Ringing da wayar ya shiga yi Aneesan taki dagokai balle ta dauka yasa ahankali yace "answer the call, ur Mum is calling again" katsewa wayar tasake yi wani wayan yakara shigowa ganin batada niyyan dauka yasa ya matzo ahankali ya karbe wayan daga hannunta ya kalli screen din kafin yay picking yakara a kunne. Cikin kuka sosai Ammi tace "Anee....sah na" ahankali guy din yace "Assalamu Alaykum" da sauri Ammi tace "bawan Allah waye kai? Ina y'ata?" ganin yanda duk Ammi ta daburce yasa yace "calm down Mum relax, sunana Dr Zaid, a per-term Dr prison din da yarki take, I only come idan akwai any surgical issues daza'ama prisoners, yau na shigo nai surgery bayan nagama naga anyi releasing yarki a sume, I could not leave her that way is against my professional code of ethics shine na dauketa with the hope nakaita asibiti aka dubata tana farfadowa saita nemi iyayen ta but kafin nakai saita farka, relax am not a bad person bazan taba cutar yarki ba dan nima inada kanwa mace sanan inada y'a mace shekarunta biyar aduniya bazan so wani ya cutanmini su ba, yanzu tell me kina ina nakaiwo miki ita nasan Abuja sosai dan wurin zuwana ne" ajiyan zuciya Ammi tasauke ta goge fuskarta tace "bawan Allah nagode maka, yanzu taimako daya nakeso kamin so nake ka tayani kaita Park, kasata a motar kaduna gidan kanin babanta zata" da sauri yace "kaduna Mum, ai am going back to kaduna yanzu haka, kin yarda dani natafi da ita kokuma na kaimiki ita Park din?" dan shiru Ammi tayi kafin ahankali ta nisa tace "na yarda dakai kodan diyarka dakacemin kanada, ka kaimini ita kaduna zan sanar da Baffan ta zai sameku ya karbeta ahanya" ahankali yace "to shikenan" zai katse wayar Aneesa tadago kai ta fizge wayar daga hannunshi ta kara akunne cikin wani irin murya tace "nace miki inaso naje kaduna ne Ammi?" shiru Ammi tayi kafin tace "keda gidan nan har abada Aneesa, ki tafi wurin Baffan ki nima zanzo nasame ki a wajen, duk wanda ya cutar mini dake nabarsu da Allah, Allah baya bacci no need for you to come back here and cause issues nasanki, ki barsu da halinsu, watarana sai labari kinji, kiyakuri, kije wurin Baffan ki kijirani anan, am coming for you okay" gyadamata kai tayi ta katse wayar ahankali tana huci. Kunna motar yayi yaja ta gefen ido yake kallonta ta mugun bashi tausayi ganin yanda take goge kwalla tana fighter tahana kanta kukan amma takasa, ganin yanajin tausayinta over yasa ya maida hankalinshi kan tukin dayake yi baisake kallonta ba.




Number Baffa Ammi ta nemo ta kira, ringing daya ya dauka, ahankali Ammi tace "barka da warhaka Baffa" "barkan mu dai Maman Aneesa" dan shiru Ammi tayi kafin ahankali tace "Baffa ansaki Aneesa yau tana hanyar zuwa kaduna, zan turama number mutumin daya dauketa, Baffa ka kulamin da Aneesah, Baffa Aneesa need strick care gidan yari Alhaji yaturata, zadaika ganta dakanka, Baffa rayuwata nacikin kunc....." takasa magana sabida yanda kuka yaci karfinta, haushin ta sosai Baffa yakeji amma ayanda Ammi ke kuka sai jikinshi yamai sanyi yasan koshi baikai Ammi jin bakinciki faruwan komiba, murya chan kasa cikeda lallashi yace "kinga, kinga Maman Aneesa, calm down komi yay tsanani maganin shi Allah, wanan jarabawa

Please Login or Register in order to submit comment