Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce da yardan ubangiji kuma zamuci, dan haka kiyihakuri, kuma karkiji komi akan Aneesa Allah yakawo ta lafiya koma me tadawo yarmuce ahaka zamu rungume ta da hannu bibbiyu sanan we will shape her to our like, addu'a kawai zakiyi tamata kinajina, kul karna karaji kinyi kuka kan zancen nan tunda ansakota Alhamdulillah, duk wata matsala da sauki ce da yardan Lillahi, share hawayenki" ahankali Ammi tasa hannu ta share hawayen tass ta sauke ajiyan zuciya, murya chan kasa tace "Baffa sai magana ta biyu" da sauri Baffa yace "oho ina jinki" ajiyan zuciya tasake saukewa tace "Baffa alfarma nakeso, inaso ka saidamin da shanayen Aneesa guda biyu so nake kabani dubu dari sauran kudin inaso kayi amfani dasu ka shigarmin da kara kotun musulunci anan kaduna, inaso araba aurena da Alhaji, dubu darin zan biyashi kudin sadakinshi dasu" shiru Baffa yayi tunda tafara maganan harta gama saida tace "kanajina Baffa" da sauri yace "inajinki" anatse yakira sunanta. "Rukayya" yanda yakira sunanta kai tsaye yasa Ammi tagane he's so serious dan he hardly call her name direct. Anatse Baffa yafara magana. "Rukayya na isa dake, sanan inada iko dake, kinada wani irin matsayi na yar uwata najini dabazan iya tsayawa ina ganin zakiyi shireba na barki, nasan kin tsani Alhaji sabida abinda yama Aneesa, bari kiji wata magana aduk lamarin nan laifin Alhaji guda nake gani, shine dabai tsaya yasaurare muba, kisaka kanki atakalmin shi, daga ke har Alhaji kunyi boko, yan boko kuma mutanene dasun yarda da technology, babu yanda za'ayi mutum kaman Alhaji yaga camera yakama abu haka bayan ya kalla kuma yace bahaka bane, tunda har yagani da idanunshi ga Aneesa nasaka poison bazai taba yarda ba itabace dole kuma ya hukunta ta, kar abin nan yasa kice zaki nemi saki, babu kyau saki, kin riga kinsa Aneesa tadawo wajena hakan dakikayi kin kyauta tabarmai gidanshi, Ke kiyi zamanki kicigaba da rayuwan aurenki, ki rubuta ki ijiye nina fadamiki wata rana Alhaji saiyazo yasa guiwanshi akasa yabaki hakuri, gaskiya bata boyuwa fa da dadewa, komujima komu dada gaskiya zata bayyana, Allah zai warwaremuku komi, zai wanke Aneesa dake, bama ke kadaiba, Alhaji harnan kaduna saiyazo ya roki Aneesa gafara, nidake bamusan gaskiyaba Allah zai bayyana mana gaskiya, kiyi hakuri bazan taba baki goyan bayan ki kashe auren nan kifito ba, amma kiyakuri dan ke wacce aka cutace, Allah zai bimiki hakkin ki kowaye awanan lamarin sai Allah yatona musu asiri dai dai, daya bayan daya namiki alkawari, Aneesa kiyita mata addu'a, kimata fatan samin miji nagari na aurar da ita muhuta kinji Rukayya kiyahakuri" hawaye Ammi ta share bataso tama Baffa gardama hakan yasa tace "shikenan Baffa nagode" "yauwa, Allah yamiki albarka, kituramin number kinji" to.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣4️⃣

_07012181461 chat me up in kinason wanan book din_



.........
Dady yakai almost 20min awurin a tsaye yana mamakin what just happen yanzunan tsakanin shida Aliyu, inda yabari Aliyu ya kona kanshi da yaya zaiyi? Da ina zaisa ranshi, dagokai yayi ahankali ya kalli ma'aikatan wajen cikeda sanyi jiki yace "agyara wajen nan dan petir nada hatsari sosai" sanan yawuce yana tafiya ahankali ahankali duk jikinshi yay sanyi sosai yana kallon yanda matayenshi ke tashi daga window dasuke leke suna komawa ciki yadauke kai yawuce shashin shi yafada kan kujera.


Agurguje Aliyu yay wanka kusan sabi uku sabida yadena warin petir din sanan yafito, agurguje yake shirya wa dan baiso yabata lokaci, 3quater na gucci yasaka da wata dark brown paco robbani logo print shirt daya haska fatar shi yafito da kyanshi, fesa turare yayi yasa takalmin shi na prada sanan yadau car key dinshi yana dingishi yafito yay flat din Dady babu alamun wasa akan fuskanshi, ahankali yatura kofan dakin da sauri Dady dake kishingide kan kujera yatashi yazauna da kyau yana kallon Aliyun kaman yau yafara ganinshi, har gabanshi Aliyu yakaraso ba yabo ba fallasa yace "Wani prison ka kaita Dad?" yadanyi shiru yana kallon Dady kafin ahankali yace "zanje nadauko tane" sosai Dady ke mamakin shi dansai yanzu yakara ganin son Aneesan akwance kan fuskar Aliyun, ahankali Dady yanisa yana kallon fuskanshi dasaiyau ya yarda da maganan manya cewa abinda kafiso shiyafi baka matsala banda haka ace duk wanan abin dayake ma Aliyu bayagani, yazaci in Aliyu ya warke yaji meyayi he will be proud of him yarungumeshi yace I love you Dad, you are the best saidai yaga akasin hakan, sabida shine fa ya kulle Aneesa amma duk bayagani, yarinyar dataso aikashi lahira saima haushin shi dayake ji, ahankali yace "Zilanious prison take" dago idanu Aliyu yayi ya kallai irin kallon nan na Dady zaka iya aikata haka kafin ahankali yajuya kawai yafita daga flat din Dady na binshi da kallo yawuce yafita abinshi batare daya waigoba koya juyoba.







Yayi tafiyan almost 30min sanan yakai prison din shima da taimakon Google map, parking yayi yafito yana zare bakin glases din idanunshi kafin ya shiga ciki hargaban kanta inda wata guard take ga katon book din rubuta name of visitors a gabanta, tun kafin Aliyu yakaraso inda take take wani irin jarababben kallonshi wani irin dan gayune yau haka yazo prison dinsu, turaren shi daya fara mata sallama yasa tadawo daga yar gajeran tunanin datake, tace "Well done Sir, barka da zuwa yallabai, wakazo gani?" girgiza mata hannu yayi alamun he's not here to visit anyone, cikin kwantacciyar muryanshi yace "am here to pick up someone da akai releasing" da sauri tace "what's her name sir?" "Aneesah is her name" zaro ido tayi ta kallai tace "Aneesah barkono? Ai indai itane ansallame ta tun dazu about 30-38min ago ma kam" dukan wajen yayi cikeda cinrai zaijuya yawuce tace "Sir excuse?" dan juyowa yayi ya kalleta, murmushi tayi tace "don't be offended zan dan yimaka personal tambaya ne" gira daya yadaga mata batare dayay magana ba alamun go on am all ear, murmushi tayi tace "Sir you are so cute wlh, please wats your relationship da Aneesah" dan tabe baki yayi ganin tambayan gulma ce yace "am her husband to be, and Aneesah is Cutie than I" da sauri tace "no way wlh, kai kaga kyan ka kuwa gaka fari kaman jinin bature, kafita kyau" ahankali yace "I will take that as a compliment, as 4 me tunda nake I've never set an eye on a lady that is as beauty as Aneesah ba in my life, she is the definition of Queen of heart, excuse me" yajuya yafice daga wurin da saurinshi ya shige mota yana duba agogon wayanshi maybe hala to takai gidama, dawani irin sauri yaja motar baida burin daya wuce yadaura idanunshi akanta and apologise to her on his father's behalf.


Ahankali sallan la'asar takama shi ya tsaya yayi sanan yakoma mota gabanshi na faduwa yakosa yaga Aneesan, parking yayi a compound dinsu ysauko daga motan yana dingisawa yay flat din Ammi, sallama yayi tareda bude kofan falon, Ammi ce kadai zaune kan kujera sai bowl dake dauke da sliced fruit masu sanyi da fork ta tasa agaba tana kallo takasa ci tadago kai tana kallon Aliyun, da sauri Aliyu yamaida kofan yarufe yakaraso gabanta tareda tsugunnawa yadafa hannun kujeran yace "Mum am just coming back from the prison ance tuntuni aka sallamota inkika fitarmin da novel waje Allah ya isa ban yafemikiba





Ina take Mum ta iso ne? Yay maganan yana waige waige ko ina kozai ganta kafin ahankali yajuyo da kanshi ya kalli Ammin kaman yanda take kallonshi yace "Mum tadawo? Kodai Dad baisa asaketa bane? Bari naje nasame shi" yay maganan yana mikewa tsaye zaitafi yaji ankama hannunshi, ahankali yajuyo ya kalli Ammin, ganin yanda take kallonshi yasa ahankali ya tsugunna yace "Mum, menene Mum? Baisakota bako kibari naje nasame shi" girgiza mai kai Ammi tayi ahankali tace "yasaketa Aliyu, amman Aneesa da gidan nan har abada tagama zaman shi" wani irin faduwa gaban Aliyu yayi yace "wat! Mum! Ina kikasa taje? Mum bazan iya rayuwa babu Aneesa ba, am sorry Mum bangaya miki ba, I love Aneesa sosai, I want to marry her, please Mum kisata dawo gida I promise you zan wanke Aneesa agaban kowa I will prove her innocent" tunda ya ambaci kalman so Ammi ke kallonshi jitayi kaman ya sosa mata inda ke mata kaikayi ko kadan bataso ta tsaneshi but idan tacigaba da zama tana tuna abubuwan da mahaifinshi yamata zata gaggasamai maganganune hakan yasa tamike tsaye ahankali tareda daukan bowl din fruits dinta zata wuce da sauri Aliyu dayakeji kaman zai zare yace "Mum dan Allah ki tsaya, please just tell me ina kikasa Aneesan taje? Mum dan girman Allah kifadamin wlh Mum kaman zuciyata zata fashe dan Allah karki rabamu, I love Aneesa and she loves me too, Mum aure zamuyi, Mum inason Aneesa sosa......." "Aliyu!!!" Ammi tawani irin juyowa tareda kiran sunanshi ta hanyar dakamai tsawa, da yatsa ta nunashi tace "karna karajin, karna karajin ka furta kanason y'ata, karna sakejin kace y'ata na sonka, Aneesah bazata taba aurenka ba har abada, bazan taba bada y'ata ga yaron wanda ya kulle min itaba, Aneesah tama barmuku garin gabaki daya bazaku kara ganinta ba that I promise, sanan ka tashi kafita daga flat dinan kafin raina ya mugun baci, get out! " Ammi ta dakamai tsawa tareda mai pointing kofa, ja idanun Aliyu sukayi kallo daya zakamai saiya baka tausayi kaman kamishi kuka, baki yabude zaiyi magana Ammi tace "I said out Aliyu" juyawa ahankali Aliyu yayi saida yakai bakin kofa ya tsaya yajuyo ya kalleta yace "nasan kina fushi Mum, and you have the to be, no body wish yaga an kulle mai da agaidan yari bama police station ba, Mum kisani ko banyi danke ba nothing is going to stop me daga wanke abin sona Aneesa, I will prove to everyone that Aneesah na is very very innocent someone putted everything, saina wanke Aneesah, and flat dinki kike korana ko saina dinga zuwa Mum, saidai in kiyita korana kullum" yay maza ya share hawayen daya zubomai yajuya yafita.
Da sauri Ammi tajuya tai sama maganganun Aliyu sun tabata ba kadan ba, takusa kuka daurewa tayi ta zauna akan gadonta tana goge kwalla.
Duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, duk wacce ta fitar da book dinan waje Allah ya isa ban yafeba.


Tunda yay nisa a tafiya take bacci, har Baffa yakira sukai magana yacemai a express road zai tsaya ya jirasu dan gidansu na danaba ne duk batasani ba bacci take kaman wacce tai shekaru batai bacci ba, taji dadin AC sosai, sosai yake gudu ana kiran sallan magrib ya shigo kaduna-Abuja express road, wayarshi yaciro yay dialing number Baffa, ringing daya Baffa ya dauka yace "sannu Malam, sannu da kokari kun shigo express road dinne?" "eh Abba mun shigo" da sauri Baffa yace "to shikenan ka karaso ina tsaye bakin titin zaka ganni nasaka jallabiya mai ruwan goro da bakar hula, akwai carbi a hannuna dan daga masallaci nake" "to" ya katse wayan yacigaba da tukin yana kallon gefen titi, yay tafiyan kusan minti uku sanan yahango Baffa dattijon kirki yana tsaye bakin titi yanajan charbi yanabin kowacce mota daya wuce da kallo, horn ya danna mai hakan yasa Baffa yadaga hannu da sauri, yadan karyo kwana ya parking daidai baki bakin anguwan da Baffa ke tsaye ya kashe motan tareda fitowa, Baffa da sauri yamikamai hannu yace "sannu danan, Allah yasaka da alhairi" kasa karban hannun Baffa yayi saidai ya tsugunna yace "barka da warhaka Abba daftan mun sameku lpy" murmushi Baffa yayi yace "Alhamdulillah, tashi, tashi, Allah shi albarka" tashi tsaye yayi yace "bacci take tunda muka shiga hanya gatanan" yay maganan yana bude dayan door din Baffa biyeda shi abaya, Aneesa yagani babu ko dankwali akai gashin nan yarufe fuskanta yabar kadan, tana sanye dawata koriyar riga tagidan yari da koriyan dogon wando, sai kambas fari daya dawo brown shima duk na gidan yarin ta takure jikin kujera tana bacci wani irin tausayi data bama Baffa ko baisan lokacin daya tsugunna gaban motar ba, ahankali yakai hannunshi ya yaye gashin fuskar nata yadaura hannunshi kan fuskanta zafi rau yaji kaman wacce ke zazzabi, murya chan kasa yakira sunanta "Aneesah, Fateema, Fateema" ahankali take motsi da ido jin ana kiranta kafin tabude idanunta duka ta saukesu kan Dr zaid dake bayan Baffa tsaye ya rungume hannu a kirji yana kallonta. "Aneesah" kiranta dataji an sakeyi yasa tasauko da kanta kasa ta kalli gabanta, Baffan ta tagani a tsugunne yadaura hannu kan fuskarta kaman yau yafara ganinta yama kasa cewa komi, ahankali tace "Baffa" kallonta Baffa ya tsaya yi yakai almost 2min abubuwa da dama nakai komo a zuciyan shi kafin yamike tsaye yamika mata hannu yace "sauko mutafi gida wanda yakawo ki karmu tsareshi dare nayi" yunkurin tashi tafito tayi taji kanta kaman zai cire sabida ciwo, tashi tayi ahankali tana dafa kujera idanunta na jujuyawa cikeda karfin hali tafito daga motar, kafafunta ne suka fara rawa kafin tasa hannunta ana Baffa tai baya luuu zata zube da sauri Baffa yatareta yana salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un Aneesa" da sauri Dr yazo wurin yatsun shi biyu yadaura kan wuyanta yace "ta sume batada lafiya, Inane gidanku Abba" da sauri Baffa yace "kasan layin nanne kadan" "shigo mota da ita na sauke ku inada kayan aiki mukaje saina dubata" adan rude Baffa yace "kai likita ne?" gyadamai kai yayi Baffa ya shiga motar ahankali rike da ita yarufo musu kofan ya zagaya ya shiga yatada motan Baffa na nunamai harsuka karasa wani gida dakeda dogon dakali agaban gidan, sai wata yar Honda da tayoyin gabaki daya sukai less pake a kofar gidan, parking yayi yafito Baffa yafito rikeda ita yace "mushiga ciki likita" boot Dr Zaid yabude yaciro wani akwatin aiki sanan yabiyo bayan Baffa shiga gidan sukayi babban gidane sosai mai fili daga ta wuraren zauren kiwo ake awurin shanaye da awakai ne da aka garkame su dayawa, sai kuma tsakar gidan sai dakunan dakenan ajera guda shiga, sallama Baffa yadoka yana kwalama matarshi kira yabude wani daki dababu komi ciki saiyar katifa akan gado maidan kyau ahankali ya kwantar da Aneesah ya kalli Dr Zaid dake tsaye yace "zoka dubata likita" karasowa Dr yayi yana sanya stethoscope a kunne yazo yadubata sanan ya dago kai yace "abani ruwa Abba" da sauri Baffa yafita, ganin Baffa yafita yasa da sauri Dr Zaid yaje wurin kafarta wando nta yaja sama nan yahango wukake har guda biyu a jikin safanta kwashesu yayi duka yajefa cikin aljihun wando shi hakanan yaji bayaso susan tana yawo da wukake ko ahaka ma jibi yanda tsohom nan da mahaifiyar ta suka dawo ai zasu shiga damuwa sukaga abinda tazama, drip yadauko da allurai yay aciki sanan yamakala mata yana cikin makala mata Baffa ya shigo tareda matarshi datadan mayyanta rikeda ruwan tace "subhallahi Aneesa ce haka, Allah yabaki lpy" takaraso tace "ga ruwan likita salla nakeyi ne dazu dakika shigo" karban ruwan yayi bayan yagama samata drip din sanan yay dipping hand dinshi inside the water yaciro yakai kan fuskarta yana shafawa wani irin ajiyan zuciya ta sauke kafin ahankali tabude idanun dasuka kankance ta daura akanshi, wani irin faduwa gabanshi yayi da sauri yatashi tareda rufe akwatin shi yadauka tareda juyowa ya kalli Baffa yace "zan tafi Baffa jikin zai sauka dan nai allurai a ruwan danake karamata, inhar jikin bai saukaba ka kirani gobe da safe saika kawota asibitin danake aiki, amma yanzu abata abinci taci sanan tai wanka ta tsaftace ko ina harda wanan gashin nata zataji dadin jikinta" "baza'a yiba din m we ruwan ka dani eh?" cewan Aneesa data farka cikeda karfin hali, dukansu juyowa sukayi suna kallonta barinma Baffa daida gabanshi yay mummunan faduwa dayaji yanda tai magana, tashi tayi ta zauna cikeda karfin hali tana kallon drip din cikin fushi tace "kazo kacire abunan ko wlh na tashi saina fedeka" ahankali Zaid yajuyo yazuba mata idanu kallo daya yamata yagane dudda uban karfin halinta inta tashi tafiya biyuma sunmata yawa saita sake zubewa ta sume dan babu abinci acikinta, Baffa daya kasa magana yana kallonta Zaid ya kalla yace "abata abinci Abba da madara tasha, saida safen ku" wani irin yunkurin tashi Aneesa tayi da sauri inna tace "a'a mutuniyata ihakuri zauna bakiga bakida lafiya ba" ta kalli Baffa cikeda saiyasa tace "Mai gida aje asayomata madaran, likitan mu gode" "niban godeba wlh" Aneesa tafada tana ballamai harara juyowa yayi ya kalleta kafin yadauke kai tafice daga dakin yana mamakin masifan yarinyar.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣8️⃣





Wani irin zaro idanu Maman Rauda tayi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un Rauda!" takasa gasgata abinda idanuwanta ke gane mata.

Aliyu ko motsi kirki yakasa saima wani irin rike Raudan tsam dayayi ajikinshi yakara barinta yanajin yanda take wani irin nishi akunne shi, arude Dady ya shiga kiciniyar karbanta yace "Rauda, Rauda Gadanga bani ita kaga" fitowa sauran polisawan da sojojin sukayi aka tsaitsaya ana kallo ahankali Dady ya karbeta jini na fitowa ta gefen bakinta tana wani irin nishi, taushe baki da hannu Hajar tayi tana kuka sosai, arude Dady da hankalin shi ke gab da fita daga jikinshi yace "call the Dr Aliyu, call him" ya kalli Raudan datake wani irin nishi hawaye na fitowa daga idanunshi yace "stay with me kinji y'a, u will be fine okay, likita yanzun nan zaizo, yayanki zai kira Dr" yay maganan yana dagakai ya kalli Aliyun daya fitoda waya amman yama kasa tabawa tsabagen rudewa yakasa dena kallon Raudan yanda jini ke fita tawajen scissors din yanabin interlock din tsakar gidan, Dady zaiyi magana yaga Rauda tadaga hannunta ahankali tana rurrufe idanu ta mikama Aliyu wani irin zubewa Aliyu yayi kasa ya kama hannunta gam saiga hawaye sharr da sauri ta girgixa mai kai tana wani irin nishi da kyar tabude bakinta dake fitar jini sosai tace "no crying uh'uhn, be strong for me, be a very strong man Ya Aliyu, k.....kada...wo namiji, inaso kahada kan kowa na gidan nan let's our family be united, no more sluggishness ka...ji" da sauri Aliyu yadaga kai wasu hawayen nazubomai sosai, murmushi tadanyi cikin tsananin azaba ta lumshe ido ahankali tace "D....a..d" da sauri Dady daya daurata kan cinyarshi yace "na'am Rauda na" hannun Aliyu tasake rikewa da kyau tace "Ya Aliyu na son Aneesah ka auramai ita, Dady!" tasake kiranshi da sauri Dady da muryanshi ke rawa sosai yace "na'am Rauda" dan shiru tayi takasa magana saikuma tabude idanunta ta kalli Hajar dake tsaye tana kuka sosai tana kallonta, murmushi tamata ta kalli Aliyu dake rikeda hannun ta hawaye nabin idanunshi, murmushi tamai tace "in Aneesa ta haifi Baby girl zakasa sunana Ya Aliyu?" dawani irin sauri Aliyu ya gyadamata kai hawaye na gangarowa daga idanunshi ya matse hannunta yace "yes Rauda, I will name her princess Rauda, the best, the most sweetest and the most caring little sister in the world" murmushi tayi sosai da saida duka hakoranta dasuka hade suka bayyana, hannunta daya rike ta shiga kiciniyar kwacewa hakan yasa yasaki hannun yana kallonta ahankali takai hannun kan idanunshi ta lakato hawayen dayake yi tareda girgiza mai kai tace "daga yau no more shading tears, no more crying over any abu dake damunka, kome kakeso kome kedamunka ka tashi tsakar dare ka gayama Allah, show the world ba old Ya Aliyu bane, u are strong, u are a fighter, u are capable, I hate seeing you cry, karka kara kaji" hannunta dake kan fuskarshi ya damke wasu hawayen na shirin fitowa ya hannasu ya fuzar da iska heart dinshi nawani irin strengthen and getting tough, wani irin ajiyan zuciya ta sauke sanan tajuyo da kanta ahankali tazubama Maman ta da officer yarike gam ido, yanda take kallon Mama yasa jikin Mama ya shiga rawa saita saki wani irin mugun kuka tace "kiyafeni Rauda, dan girman Allah kiyafen, kiyakuri, nayi nadama, inda nasan kezan sama da banyi ba wlh" wani irin numfashi Rauda ta shigayi tarike hannun Ya Aliyu gam da sauri ya kalleta, numfashin ta shiga yi da sauri da sauri ta juyo ta kalli Aliyu tana wani irin nishi lips dinta na rawa da sauri Dady yace "call Dr Aliyu" arude Aliyu ya shiga neman number Dr, ahankali Ammi ta tsugunna Dady yabita da kallo, hannunta ta daura kan goshin Raudan dake wani irin nishi jinin na bulbulowa sosai tana kallonta tace "la'ilaha illallah, Muhammadu Rasulullah, la'ilaha illallah Muhammadu Rasulullah" duka wajen daukan kalman akayi ana bata ahankali bakinta yadauka tayi kafin ta lumshe idanunta rup, hannu Ammi tasa tacire dankwalin kanta dayake babbane ta warware tarufa matashi ta kalli daga Dady harsu Aliyu dake jiran tacemusu wani abu ta girgixa musu kai alamun takoma ga mahallicinta.
Wani irin uban ihu Maman su Rauda tayi. "wayyoooooo Allah na na shiga uku na lalace, Rauda, na shiga ukuuuuuuu, mena aikata ni Kareema? Na kashe y'ata? Wayyo Allah na, wayyo Allah na, wayo wayo" juyowa Dady yayi da jajayen idanunshi ya kalli officer yace "dan Allah kufitar min da matanan daga gidan nan" turata cikin mota akayi tanaji tana gani aka fita da ita.

Kafin kace me mutane sun cika gidan da anguwan ma makil, bayan sallan la'asar akai jana'izan ta aka kaita makwancin ta.


_Ya Allah ka jikin dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah ka gafarta musu, Ya Allah kakai haske kabarinsu, Ya Allah kasa sunhuta, Ya Allah muda bamu riga munkoma gareka ba Ya Allah kasa mu mutu muna musulmai, Ya Allah kayafemana kurakuran damuka aikata, Ya Allah ka karemu zuwa hanya madaidaiciya. Ya Allah ka dubemu badan muba badan halinmu ba ka warkan da alumman ka daga wanan cuta ta corona virus, Ya Allah ka kawomana karshen ta, Ya Allah ka tsaremu ka tsare alumman musulmi gabaki daya, Ameen Ya Rabbil Alameen_


_*Good Morning GGM*__*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣9️⃣

_How to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya. For those dabasu da account zaku iya tura katin MTN ta WhatsApp number na 07012181461_


_*see in bakida kudi karma kisake ki karanta littafin nan dan wlh banyafe miki ba zaki biyani hakkina alahira*_

_*keda kika biya access fee kikai joining group dina danki karanta littafi ba littafina kika siyaba so bakida anything kimin sharing book waje, saisa nai free pages, masu neman free pages kuje Wattpad dina "mamanshakur" and read, inhar kika fitarmin da littafi waje wlh keda Allah, Allah baya yafe hakkin wani sai in shi ya yafe miki*_






_kaduna_
Sanin batajin dadi yasa Baffa yahana Inna karta tadata da asuban ya shiga dayan dakin yatado yaranshi maza guda uku dasuke gida, Khaleelu, Ibrahim da Mubarak sukai alwala suka dunguma suka wuce masallaci.


Wuraren tawas nasafiya Baffa ya shigo gidan yabar yaranshi a makarantan asuba da akeyi a masallacin, inda matasa maza da mata suke haduwa amusu karatu sai karfe taran safe ake tashi. Da sallama ya shigo gidan yatsaya wajen akuyoyinshi da shanaye yana dubasu ya kwalama Inna kira. "Maman Hamma" daga kitchen Inna ta amsa. "na'am mai gida kadawo?" "kinbama awaki dusan kuwa?" tana juye tafashashen

Please Login or Register in order to submit comment