Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ashe ranshi a6ace yake"

Mardeeya saboda dariya har saukowa qasa take tana dafe ciki, Nafeesa ancika faam tashi tayi tanufo Saudart data gama saka Riga ta bita da gudu.

Zagaye dakin suka shigayi suna dariya.

Mardeeya tahau yin kida da tsinken tsifarta tana kuchasu mata kuchasu, kuchasu ba mai hanaku.


Suna cikin haka aka banko kofar dakin aka shigo, Duk Juyowa sukayi don ganin mai shigowa.

"Yeee! Antyna!!!"

Ta ruga dagudu ta rungume Saudart tana tsalle kamar wata yar yarinya, Saudart namata dariya.

Sukau Nafeesa sagale sukayi suna kallonsu, musanmman baby dabasu saniba, shigartama kadai zai saka sanin yar Masu kudine ga fatarta dake sumul sumul alamun Hutu.

"Wow! Antyna kinganki? Wlh kin hadu! Bari muyi selfie yau akwai status"

Tsaki Saudart taja tana tureta

"Kekam Allah ya shiryaki baby, ke kenan daukan pics da dorawa status. Nikam banso"

"Haba aunty please"

"A'a nikam"

"Wayyo Ummy, wlh anty kuka zanyi" tafada tana zaman yan bori kan gadon dakin tana kwa6e fuska.

Kallon juna Nafeesa da mardeeya sukai sannan suka maida kallon kanta.

"Please anty*

"Ok Amma kwara daya".
Ihun murna tayi ta taso taciro qatuwar wayarta ta kashe Masu selfie.

" wow! Wlh yaya ya iya za6e wlh kinma fishi kyau"
.tafada tana Dora hoton a status da caption din *me and my cute in-law*

Sai a sannan ta lura dasu mardeeya daketa kallonta, suna hada idanu suka janye idanu cikin basarwa.

"Laa, anty suwaye wadannan naga kunadan yanayi"

Murmushi Saudart tayi tana shafa mai tace
"Cousins dinane"

"Wow! Hyy" tafada tana Daga musu hannu fuska fall murmushi.

"Hyy" suma suka amsa suna mata murmushi.

"Kuna kama wlh Saidai Antyna tafiku kyau"

Yatsina fuska Nafeesa tayi tana cewa
"To kina buqatar spec sbd da alama biki kike gani, wannan ai itace hajiya munin cikinmu"

Baby nasamu abinda akeso, aka wani gyara zama sannan akace

"Wa? Ca6 in-law ai ta dabance, kyawunta kamar watane a Daren sha hudu, kuka jerama baza'ama lura dakuba saboda Tun Daga nesa zata dukkan daukan idanu"

Mardeeya tace
"Allah yasa ranace a qarfe sha biyun rana, wannan ai fari ya ceceta, da baqace da kau ba'a magana, cuss kenan"

"Atleast dai farin ya ceceta, wasu kau koda farinma ba kyau sukeba kullum ana cikin yima fuska kwaskwarima" inji Saudart tana Masu gwalo.

"Gayamasu dai anty, farar mace alkyabbar mata, wasu da makudan kudinsuma suke naiman farin, karshe atoye fuska a banza, Daga baya akoma multi colour"

"To kinga kenan kalar mu ce mai tsada, chocolate colour wanda baya saiduwa bare asiya, shi fari ana sayanshi baqifa?"

Haka sukaita cafta tsakaninsu, dayake baby batada baqunta tuni suka dinke yadda kasan dama sunsan juna.

Basu suka kwantaba sai sha biyun dare saboda fira.




Washegari da azahar suka fita dukkansu wankin kai, basuyi wani wahalar rabon iv ba saboda online invitation sukayi Basai anwani sha wahalar zirga zirga ba, anko ma Duk ta online aka turasu da dressing code din walima wanda Arabian gown ne baqa kowa zaisa, a dinner kuma kaya pink and blue za'asa.

A saloon din aka wankema dukansu kai, akayi musu stretching dinshi.

Zo Kaga santi wajen su baby da aka gamama Saudart, don hauka Wai shima gashin daukar shi hoto zatayi ta Dora status.

Dariya su Nafeesa sukaita yima diramarsu don dakyar baby ta hqr bata daukanba.

Nan aka musu manicure da pedicure, qunshi kuma sai saura kwana uku za'ayi.

Basu dawo gidaba sai gab da magrib don Saida suka biya shopping suka jidi Kayan amfani na biki wanda Duk baby ta biya.

Koda suka dawo Sallah kawai sukayi sukaci abinci suka kwanta don Duk a gajiye suke.

Washegari saura kwana biyar biki, ranar kuma za'a kawo lefe, tunda safe su Saudart suka fita kitso banda baby wanda tayi zuciya saboda tace tafison Saudart tabar gashin hakanan ita kuma taqiya shine tace bata rakiyar.

Da qarfe hudu na marece dangin A.A suka kawo lefe na gani na fada.

Set biyu shaqare da tsadaddun kaya da wata mota da aka sako Kayan ciki fara qall qirar Prado.

Sosai akayimusu tarbar mutunci da karamci kuma suka basu tukuici mai tsoka.

Baby kau sana'ar aka hau yi.

Hoto taita daukar Kayan da motar sai iyayi take.

Sai tsokanarta danginsu suke Wai tagudo gidansu Amarya ai datayi hqr har gida zatazo tasameta, ita taita biyemusu suna raha.


Yauma sai can magrib suka dawo sukaga gida haryanzu dinke da yan ganin lefe.

Jikin Saudart ne yayi Sanyi ganin akwatina baje tsakar falon, batace komai ba ta haye sama batareda tayima akwatinan kallo biyu ba.

Su kau mardeeya wuri suka samu suka zauna sunata duba lefen suna santi.

Koda Saudart tashiga daki kuka ya kufce mata ta toshe baki da tafin hannun damanta tana kuka.

Dagudu tafada kan gado tana kukan, Shikenan dagaske auren dai za'ayi mata.

Wayarta taciro takira daddy taita mashi kuka.

Sosai yaita rarrashinta, saida yasha wahala kafin yasamu tayi shiru.

Tananan kwance su baby suka shigo dakin, kamar hadin baki suka fada Mata ajiki.

Nanfa suka shiga tsokanarta baby na kareta, itadai Saudart banza tayi dasu don ba Sune gabanta ba.

Sai Daga baya baby tazame dankwalin Saudart taga kitson.

Nanma rudewa tayi don yau tamafi jiya rudewa.

Shikku akayi mata qananu an tamkesu da qaton ribbon ya sauko har wuya.

Nanma Wai hoton kitson zata dauka, dakyar ta hqr da daukar hoton don Saudart qin yarda tayi, su Nafeesa mezasuyi musu inba dariya ba suna musu ihun sunji Kansu.


Yauma sai kusan dayan dare suka kwanta, yayinda Saudart bata samu barci ba sai wajajen uku sbd yadda Taita juyi tana tunane tunane...✍


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Ramadaan Ramadaan!! Ramadaan!!!

Watar alfarma Ramadaan

Wata mai cike da haske da ni'imomi Ramadaan

Watan da babu kamarsa Duk cikin wattani, Ramadaan.

To ya? Ko kun fara yima babban baqonmu tanaji?

Idan Baku faraba to Ku fara, mu dage mu kwashi gara6asar wannan wata mai albarka.

Mu nemi kusanci ga ubangijinmu mu kasance Masu yawaita istigfari, mu kasance Masu yawaita tilawar Al Qur'an mai girma.
Mu kwashi gara6asar wannan watan sosai don idan damar yin haka ya kufce mana ba lallai bane musake samun wata damarba domin babu mai tabbacin wani shekarar zai zagayo yanada rai.

Allah kabamu ikon yin tsarkakkaken ibada agareka a wannan wata mai alfarma🤲

Allah ka amshi ibadunmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





028







Yau saura kwana hudu biki, yau Saudart na gida bataje koina ba while su Nafeesa da la'asar sunje wajen tailornsu dasukaba dinki.

Zaman nata cikin kadaici yasata samun tunani da hasaso rikittaciya da 6audaddiyar rayuwar auren dazasuyi da wanda zata aura wanda a tarihin rayuwarta bata ta6a jin irin wannan auren yafaru awani wajeba.

Haka ta wuni zurr kwance dama ba tsarki garetaba so bata wani damu kanta wajen tashi ba, Saidai ta mirgina nan ta mirgina can, sam tarasa meke mata dadi.

Yauma da marece liss suka dawo kowa da shopping bag dinshi don shopping suka wuce Daga wajen dinki, itama Saudart sunmata nata sayayyar.

Nanfa aka dasa fira, uwar kaudi kau har gwada Masu irin rawar dazatayi take, kuma ba laifi ta iya rawa don sosai rawar tayimata kyau.

Nan ta zauna tana basu labarin qawayenta musanmman bestie dinta teema har tana cemasu karsu damu ai gobe zasu hadu a walima.

Haka sukaita hirarsu itadai Saudart na kwance tana jinsu idanu a lumshe, don abinda ya dameta ya daketa bata tasu takeba.



Washegari Tun goma nasafe mai qunshi wata yar Indonesia tazo gidan da ita da yaran aikinta biyu.

Nanfa suka kama aiki.

Ogan ita kema Amarya, yaran aikin kuma nama su yanmatan amaren.

Sai wajajen azahar aka gama.

Zokuga qunshi, ba irin jagwalgwalonmu ba🤣

Combination akayima Saudart jaa da baqi akayi mata wasu irin design kamar ba hannu yazanasuba.

Sosai qunshi ya hau da farar fatarta, suma su baby ba laifi nasu ma yayi kyau Saidai fa kunsan komai na Amarya yafi kyau.


Nanfa gida yafara dinkewa da jama'a yan walima dukda qarfe hudu za'a fara.

Su teema sai wajajen uku suka qaraso su biyar yan gayu yan kwalisa.

Nan suka hade aka fara 6arin iyayi, sai a sannan su Nafeesa suka gano dalilin kaud'in ta saboda Duk kusan haka qawayenta suke.

Nanfa daki ya hargitse da hayaniya kowa qoqari yake yafadi cikinshi, babu abinda ke tashi dakin sai shewa da surutu.

Da dai Saudart taga abin nasu azimun ne saita sulale tabar musu dakin takoma bedroom din mamy.

Wajajen qarfe 3:30pm saigasu maryam da Duk ma'aikatan bakery dinta mata.

Tafe suke da manya manyan robobi shake da snacks kama Daga cup cake, meat pie, doughnut, sausage roll, samosa, pizza, da dai sauransu.

Sosai Saudart tayi mammaki ganinsu da wadannan Kayan don kwata kwata batama Masu magana kwatankwacin hakaba.

Nan akayimusu maraba suma Duk sanye suke da baqar after dress wasu kuma Nada kwalliyar wasu kalolin.

Sosai Saudart tanuna jindadinta akan karamcin dasukayi mata wanda hakan ba qaramin dadi yayimusu ba.

4:00pm dai dai shaharrariyar malamar nan wato mallama wasila ta iso, izuwa lokacin harabar gidan dinke yake da mutane kowa cikin Arabian gown black.

Dayake harabar Nada girma sosai anan aka jera kujeru kowa ya zazzauna suna facing din inda mallamar ke zaune, itakau Saudart an tanadar mata mazaunin ta Daga gefen dama.

Saida komai ya lafa sannan aka fito da Amarya.

Wohoho nanfa kallo yakoma sama😳

Sanye take da atamfa Riga da skirt pieces Masu kalar jaa da fari saita Dora qatuwar alkyabba irinta ya'yan sarakuna fara qall mai aikin golden da zaiba , ta sanya hular alkyabbar wanda tarufe Rabin fuskarta.

Sosai akaita santinta saboda ta hadu iya hadewa, su baby Sune Masu tattare mata wutsiyar asoya dake Jan qasa harta samu ta qarasa wajenta ta zauna.

Nanfa akafara abinda ya tarasu, zikiri aka farayi mai ratsa zukata sannan aka dasa kirari mai sa jazaba don daidaikune wadanda basuyi hawaye ba Daga qarshe ta rufe musu da wa'azi mai ratsa jiki musanmman ga Amarya, tana gwada Mata nauye nauyen daya rataya akanta amatsayinta ba matar aure tana mata misali da Nana fadima da matan annabinmu Muhammad (s.a.w)

Sosai jikin Saudart yayi liqis, Kanta a duqe babu abinda take sai hawaye, don sosai wa'azin matar ya ratsa ga6o66in jikinta.

Sai wajajen shidda aka gama, nan aka shiga raba ledoji Masu dauke da sallaya ko doguwar hijabi da cazbaha hadeda snacks da akayi wrapping cikin irin wannan abun mai kyalkyali.

Anan na hango su tawagar yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP sun Kasa zaune sun Kasa tsaye kowacce burinta tasamu rabonta.

Can na hango ummu bilal ana ta miqa hannu za'a amshi Leda Bayan ga wata nan cikin qatuwar hijabinta sai kunbiya kunbiya take daita.

Dayan gefen kau sis hajara Nagani sai bin baby take kamar bindi Wai adole sotake su zama qawaye don tasamu hallatar dinner Bayan daurin aure.

Can gefe naga maman fateema da ummu arifullah suna leqa ledar juna don ganin me suka samu.

Itakau umman abdullra'uff ana gefe kan kujera sai gutsirar pizza ake ana tauna ana wani lumshe idanu (ba sabban ba🤣)

A can gefe kuma Mamman twins ce kamar tayi bindiga don bata samu komaiba, su twins sun hana🤣 basu tashi rikice mataba saida aka fara rabo, Maman twins fa ta kumbura, wazai kawo gudunmawar allura a saceta?🤣



Taro yayi taro inda aka hada malama wasila da shatara na arziqi, sai godiya take tana kwararowa auren albarka ana amsawa da amin.

Itakau Saudart dama ana gamawa tasamu ta silale daki ta kulle kanta tafada kan gado ko alkyabbar bata cireba sai kuka.

Sosai jikinta yayi Sanyi Jitake inama zata iya maida hannun agogo baya da kome daddy zaiyi da bata yarda da aurennan ba Amma inaa? Kin makara Saudart bakin alqalami ya buhe😏



Washegari kuma wato ranar Daren biki yayi daidai da ranar mother's Eve nasu Ummy.

Su baby amara qahon zuciyar biki don kau wannan Tawuce qirjin biki, shirya wa sukayi dukkansu suka wuce gidansu.

Babu yadda basuyi ba akan Saudart ma ta shirya sutafi tare Amma hausawa ma sunce shiru ma amsace don kwandon shara tasamu tasakasu ciki ta rufe.

Tafiyar su sukai suka barta ita kadai dama haka tafiso don taji dadin yin tunanin ta.

A gidansu A.A akayi mother's Eve din a garden dinsu dake can cikin gidan.

Sosai partyn ya qayattar, bawani chasu akayiba kawai zazzauna ake kowane table da kujeru hudu round dinshi ana zaune ana ci anasha ana fira ga wani sanyayan kida dake tashi a background.

A ataqaice sai 10:oopm su baby suka dawo gidan mamy kowacce agajiye liqis kuma kowa ce da burin data tanaddarwa gobe, wato ranar daurin auren.




*******************************************
Bankado kofar akayi da wani uban force kamar za'a qilleta.

"Gobene! Daga gobene fah! Gobene!! Gobene! Daga gobene haba! Gobene!"

Wani uban tsaki Ashraf yaja kamar bakin zai cire yana antayamashi wata uwa uban Harara.

"Waikai wane irin marar saiti ne zaka wani shigo na mutane daki bako sallama"
Yafada cikin Fushi

Daga hannuwa Sadeeq yayi alamun surrender yana dariya sannan yakoma bakin kofar ya kwala wata uwar sallama sannan yashigo.

Tsaki Ashraf yasake ja yana maida kanshi kwance yana cigaba da shafe shafen wayar shi.

"Ango! Ango!! Kaga ango wajen amaryar sa Saudatu tauraruwar mata, ango bada kanka asare kaje gida kacewa Ummy ya6ace, ango kasha qamshi, kana kuma cikin shan qamshi kuma zaka sha qamshi" ya qarashe zancen yana kashe mashi ido daya😜


Ashraf da tunda yafara 6a66atu yakeji kamar ya shaqeshi kowama ya huta ya juyamishi baya yana Jan tsaki.

"Ko tsakama datayi bataci ribaba, tsaki kamar wata tsohuwar karuwa, Nidai tashi su bash na falo don iskanci kawani zo ka qunqume uwar daka kamar wata sabuwar amarya"

"Bazan fitoba din! Kasan Allah Sadeeq? Wlh Allah zan mugu mugun sa6amaka, Wai ina ruwanka danine uhm? Dakai mayene dana kade har ganyena, wlh ka fita sabgata Tun kafin na shufkama rashin M"

"Tun yaushe kuma allaramma ango? Rashin m dinka ai harna saba dashi Kaga babu abinda zai tadamin hankali, oya miqe"

"Don ubanka miqar dani din" yafada cikin qulewa

"Wlh tsab kai kanka kasan ina iyawa Amma sbd kai angone Shiyasa nake ragamaka.."

"Dan ubanka karka ragamani, mtcheew dalla fita!"

"Yo ai hikenan, tunda hakan kakeso"

Yafada yana fita

Tsaki Ashraf yasake ja sannan yakoma ya kwanta, ba laifinshi bane don yaga nazo gidansu ne.

Be gama tunaninshi ba yaji ansake banko kofar, dagowar dayayi yaga su bash sunata shigowa sukai biyar da Sadeeq daya cika na shiddan.

Dafe kai Ashraf yayi yana komawa yana kwanciya, yasan yau tashi ta qare.

Nan kau suka hau tsokanarshi Tun yana Masu kumfar baki harya saduda don tsagerane suka hadu don wasu cikin su sunmafi Sadeeq qulluwa.

Haka ya zuba Masu idanu har suka gaji suka kyaleshi, shima saida yayi barcin qarya sannan suka shafamashi lfy, nan suka juya akalar firar zuwa na dinner gobe kowa na fadin albarkacin bakinshi.

Sai can wajajen dayan dare suka samu suka kwanta shikau Ashraf tuni dama barci yayi awon gaba dashi.



RANA BATA QARYA....✍


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu. Karka barmu da kanmu🤲


Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





029




RANA BATA QARYA......

Yau ranar jumu'a ce mai cike da tarihi a rayuwar wasu, jumu'ar da bazasu ta6a mantawaba.

Yau ne ranar daurin aurensu, AUREN KWANGILA.

Tunda ta farka ko matsawa Daga inda take batayiba, dama ba Sallah takeba bare ta tashi tayi.

Tana kwance ido lumshe kamar mai barci Saidai idanunta biyu tana sauraron Duk wani zirga zirga da hayaniyar mutane.

*yau ne* tafada cikin zuciyarta

*yau ba gobeba*
*yau zan zama matar aure*
*matar auren kwangila*
*matar mutumin da banajin ko digon sonshi daidai da qwayar zarra acikin zuciyata*
*matar aurenda nan da wani d'an lokaci zata zama baza wara*
*me kika yima kanki Saudart?*
*anya baki cuci kanki ba*
*anya daddy beso kanshi dayawa ba*
*inama ace mafarki ne*
*Allah yasa mafarki ne*
*Allah yasa ba gaske bane*

Hawaye suka silalo mata dukda idanun a rufe yake.

Wani nauyi taji zuciyarta nayi mata kamar an doramata qaton nutse a qirji.

Sosai hawayen keta silalowa batareda tayi wani yunqurin taresu ko sharesu ba.

Daidai nan mardeeya tashigo dama sunje amso dinkin anko dinsu ne dawowarsu kenan tabaro su baby qasa.

"Subhanalillah" tafada tana Qarasowa wajenta.

"Saudart" tafada tana dan jijjigata ganin idanunta haryanzu a rufe yake.

Banza tayi da ita Saidai hakan besa hawayen sun tsayaba.

"Sister menene? Dan Allah ki tashi, Meya faru?"

Nanma shiru saima juyamata baya datayi.

"Saudart kiyi hqr, nasan kukanki baya rasa nasaba da auren daza'a daura miki yau, Duk macen datasan ciwon kanta dole ta koka ranar aurenta ba don zata bar iyayenta kadaiba, don itama zata taka wani matsayi wanda bata ta6a takawaba a rayuwarta, nauye nauye zasu hau kanta wanda idan ba me dakkakiyar zuciya bace bazata iya dauke nauyin ba"

Kamo hannayenta tayi tariqe sannan cikin sigar rarrashi tace
"Sis kiyi hqr, Allah baya dorawa bawa abinda baya iyawa, ki kasance mai Neman tallafi a wajen Allah kuma ki kasance mai hqr, idan kinadashi ada ki Dora akai, darajar 'ya mace ke har namiji ma shine aure, ki kasance jajirttaciyar mace abun kwatance a fannin aure, ki zama abun alfahari ga mamy da daddy ke harma garemu gabaki daya, dukda aure rai gareshi idan ba'a mutu dashiba yakan mutu yabar ma'auratan don Allah aurenki yazama abin kwatance a family dinmu, babu yaji bare saki please, nafi kowa sanin yadda mamy ta kwallafa rai akan aurenki don sau ba adadi ina jinsu idan suna fira da ummina akan tanason kar aurenki yazama irin nata, tafison kiyi auren mutu-ka-raba, ya kasance yayanki duka nawajenki yadda zaki basu tarbiyya kuma su taso tare, please sister kicikama mamy wannan buri nata, ki jajirce sis, aure yanada dadi haka wani shafin idan aka bude yafi mad'aci daci, ki riqe Allah da manzonsa kuma ki riqe hqr.."

Shiru tayi ganin yadda kukan nata ya tsananta, shiru tayi tana kallon yadda take kukan, abinka ga ruwa ruwa sai itama taji digg digg hawaye sunfara digomata.

Nan aka rasa mai rarrashin wani cikinsu don hade kai wuri guda sukayi hannunsu cikin na juna sunata rizgar kuka.

Ita kukan Saudart ya Kasu kashi kashi, ga na fargabar aure da na barin iyaye gana fargabar yadda mamy zataji idan auren ya mutu.
Itakau mardeeya kukan tsantsar tausayinta take dama na mata gabadaya, wanda Daga inda kayi aure nauyi yahau kanka, gana miji, idan kuma aka hayyayafa gana 'ya'ya.

Ahaka su baby suka taddasu.

Turus sukayi abakin kofa suna kallonsu kowacce takasa motsi.

Baby ce ta fara takawa ta qarasa wajensu itama ta zauna ta rungumosu gabadaya itama ta bude nata muryar da Allah yabata tafara raira nata kukan.

Ganin hakan yasa itama Nafeesa tayi wajensu dagudu itama ta rungumosu sukaita kukan tare da wannan ya dauka sai wannan ya aje, da wannan ya aje sai wannan ya dauka.

(Nima ganin haka yasa nadan kauda kaina na matso guntun hawaye na😢 sannan na share da hanki)

Suna haka matar kawu bala tashigo, tana ganin yadda suka cure waje daya tafara sallalami tana tafa hannaye.

"Ni asiya mezan gani?"

Hakan yasasu dagowa Kowanne fuska jaga jaga da hawaye.

"Wannan wane irin sabon sakarcine zakuzo Ku cure waje daya kuna kuka? Meya faru?"

Nafeesa ta nunasu cikin muryar kuka tace "haka nisa baby mukazo muka tardasu suna kuka"

"Mtcheew Maimakon Ku rarrashesu shine kukayi joining? Ke mardeeya Meya sakaku kuka?"

"Haka nazo na isketa nima tanayi"

"Mtcheew, andaiji haushi Maimakon ki rarrasheta shine kika biyemata"

"Na rarrasheta taqi shiru"

"Mtcheew ni matsamin dalla"

Ta wuce ta kamo hannun Saudart da kanta ke duqe haryanzu tana hawaye.

"Ya isa haka baby, kiyi hqr kinji? Kowa haka yaji a lokacinshi, kiyi hqr, taho muje"

Tafada tana miqar daita tsaye suka nufi hanyar waje.

"Saura kuma Ku zauna karku tashi Ku shirya" tafada tana ficewa da Saudart.

Sun kusan mintuna goma zaune jigum jigum babu mai magana.

Can kamar an tsikari baby ta wani miqe tsaye tana kallon agogon hannunta.

"Guys har 11:30am yayi fa, Nidai bari kuga infada toilet, ato banmaga meye nawani kukaba Bayan ba aurena bane kuma ma aini farinciki yakamata nayi za'a rabani da dunqum"
Ta qarashe zancen tana Fadawa toilet.

Kallon Kansu sukayi Bayan sun rakata da kallo harta shige sai sukayi murmushi.



Bedroom din mamy anty asiya ta kaita don nan kadaine babu mutane.

Nan ta zaunar daita tanata yimata nasiha sannan Daga bisani ta hadamata ruwa mai dan gumi a jacuzzi tabata umarnin tashiga tayi wanka.

Ba musu ta shiga Bayan ta cire kayanta ta daura towel.

Ta dade sosai a toilet din sannan tafito tana tafiya kamar wanda Kwai yafashe mawa aciki.

Kayan data tadda kan gado wanda anty asiya ta fiddomata ta dauka tasa.

Doguwar rigace ta materials marar nauyi mai style din fish.

Sannan tadan shafa powder tasa kwalli a idanun ta kwanta don sosai kanta ke sarawa.

Can saiga anty asiya tasake shigowa da bowl hannunsu sai wata Leda.

Tada Saudart tayi wanda dama ba barci takeba ta tilastata shan farfesun da bread.

Saida tacinye Tass sannan tabarta Wai acewarta vazatabar diyarta da yunwa ba.

Paracetamol ta 6alla mata tasha sannan ta kwantar daita tafita ya rufomata qofa.




Dakinsu baby kau tuni yafara tashin hayaniya don su teema an iso.

Kowacce tasha anko dinta kowacce da irin daurin data kashe.

Baby ce tsaye gaban mirror ansha dinkin doguwar Riga mai budewa Daga qasa, dogon hannun rigarko Duk anyi raga raga ajikinshi wanda yaba farar hannunta damar fitowa cikin hudojin.

Fuska kau tasha simple makeup Wai sai ga dinner zatayi heavy makeup.

Ta wani kashe daurin ture Kaga tsiya.

Nanfa suka fara kashe selfie, Duk inda ka wulga flasher ce kawai ke wall wall akota ina kowa burinshi ya dauki hoton dayafi kyau, style din hotuna kam harda na hauka, haka sukaita yi ana dorawa a status, dp, pp e.t.c






*********************************************

"Wai Ashraf wannan wane sabon salon iskanci ne Wai, zaka wani shanya mutane waje kawani shige daki harda murza key? Ko bakasan qarfe nawa bane?" Inji Sadeeq afusace, yasha fararen dakkakiyar shadda da babban rigarta yar three quarter irindai ta gayun zamani yawani kashe hula gefen goshi.
Su bash suma cikin irin shigar zazzaune suna jiran tsammani Duk sun zubama kofar idanu.

"Baaam! Baaam!! Baaam!!!" Yasake bugun kofar cikin quluwa.

"Dan ubanka kafito kona kira Ummy yanzu yanzunnan!"


Tsaki Ashraf yaja yana daura agogon fata qirar apple a hannunshi sannan ya feffeshe turarrukanshi ya kaha hularshi akai, Duk cikin kwanciyar hankali yake hakan don yaqara qular dasu.

Saida yagama shan qamshinshi sannan yabude kofar yafito fuska a tamke.

Su Sadeeq dake jira ya fito sukusa cinshi danye suka Kasa motsi.


Hade yake cikin dakkakiyar shaddarshi milk colour mai aikin deep brown wanda yarufe kusan duka gaban babbar rigar sai hula kalar aikin Kayan takalmi da agogo ma hakan.

Ga fuskarshi datasha Gyaran fuska, dan siririn sajenshi sai walqiya yake.

"Tuff tuff, kuci kanku" yafada yana tuha Masu yawu.


Sai a sannan suka dawo Daga duniyar kallonshi.

"Wow! Wow!! Wow!!"

Haka sukaita fadi kamar wasu motocin yan sanda.

Tsaki Ashraf yaja yana cewa "idan kun gama jiniyar kusameni waje"

Kallon juna sukayi suka fashe da dariya

"Wooo! Tofah kunji, kuna 6atamishi time shi yayi gaba, he can't wait" inji wani mai suna Abbas's.

Nan suka fito sai tsokanarshi suke shikau ci kanku bece dasuba yashige wata farar motar ya danna lock yaba drivern umarni yaja.

Dariya suka sake kwashe wa dashi sannan suma suka hau motocin suka Mara mashi baya.




Unguwar ta cika maqil da mutane da manya manyan motoci, kallo daya zakayima taron kasan ana gudanarda gaggarumin abune.

2:30pm daidai aka daura auren ASHRAF AUWAL da SAUDATU SHAMSU KANKIYA.

Daurin auren daya samu hallatar manya manyan qusoshin gomnati da yan kasuwa.

Fuskar alhaji Shamsu kamar gonar auduga, yaudai burinshi yacika yazama surukin A.A

Nan akaita zomashi Allah yasa alhairi, a gefema Abba ne da tawagarshi shima sai barka ake mishi.

Can 6angaren angwaye ma abun ba sauqi sai Allah ya sanya alhairi ake zuwa yimashi, Shidai iyakarshi yaqe su Sadeeq ne Masu amsawa suna godiya.

Maroqa kau kasuwarsu ce tabude, nan suka baje kolinsu suna wasa ango da Amarya Dama abokan angon gabadaya, sunkau sha 6arin naira don su bash kamar basusan zafin nemaba haka sukaita watsa naira.

Masu daukar hotuna kau kowa burinshi ya dauka, Duk inda suka wulga Saidai sunji walai anata daukar su.

Ganin abun bana qarewa bane yasa Ashraf sulalewa ya fece.







Tunda taji sautin buda na tashi Duk ilahirin gidan gabanta ya tsananta bugu.

Sake cusa kanta tayi cikin bargo tana sakin wani marayan kuka wanda izuwa yanzu har idanunta sun gaji da tsiya yar hawaye, tausayin kanta yakamata nankau taita kuka kamar babu gobe.

Su baby anajin an daura tawani dale gado tana tsallen murna, Duk sai akaita mata dariya.

Wayarta ta kwace hannun wata safeena ta Danna ma Ummy kira tana rugawa toilet.

Ana dagawa tawani Danna ihu

"Ummy!!!"

"Ohh zaki kashe min kunne"

"Ummy finally, anty tazama family dinmu, finally yaya is married!"

"Yes sweetheart, mu gode wa Allah"

"Alhamdulilah Ummy zan sake kiranki"

Ta katse wayar ta fito waje ta tarda harsu teema sun fiddo mp dinsu sun Kunna anqure volume.

Aikau tayi joining suna rawar so na amana.




Sai wajajen 5na marece akazo daukar Amarya, zokaga kuka, ba Saudart ba ba mamy ba, dakyar aka samu aka 6an6aresu aka fito daita, Dama su yanmatan amare ana cikin mota an qame tundazu.

Fitowa akayi daita fuska lullu6e da lifaya aka sakata mota, tanaji tana gani aka shilla daita...✍


Toya? Wakeson acigaba yau? Koko abari sai gobe?

Adadin comments dinku zai bada amsa


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





030



Saida aka fara biyawa daita gidan daddy wato alhaji Shamsu,

Please Login or Register in order to submit comment