Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu hadu muba 'ya'yanmu tarbiyya, Wanda mutuwace kawai zata rabamu"

Wani sa'in ya kan tsokaneta da marar kunya tana fadamashi irin wannan mgnan a matsayinshi na mahaifinta.
Takan yi dariya lokuta da Dama tana rufe fuska sannan tace "Dad, ai gaskiyane, Aure wajibine ga dukkan musulmi Duk cikarka bazaka ta6a zama cikkake mai darajaba saikayi aure, name zanji kunya Bayan nasan koba dade koba jima saina yi auren?

Hakan daya tuno ba qaramin tada mashi hankali yayiba.

Me zaice mata? Zan hadaki AUREN KWANGILA da A.A sbd farfadowar company na? Impossible!
Bazai iya kiyasta tashin hankalin fasata shigaba idan taji hakan, aure? Na Wanda bata saniba kuma bata ta6a ganiba? Kuma qarin gishiri a ciwo Aure na taqaittacen lokaci? Kai da kamar wuya.


Haka yaita tunane tunanenshi harya iso gida jikinshi yayi matuqar la'asar.
Shidai abinda yasani no matter what, bazai bar wannan damar ta wuceshiba.




WAIWAYE (Adon tafiya🕴)



Manage please🙏


Ummin fasihu ce

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲

Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




007







WAIWAYE (Adon tafiya🕴)



Alhaji shamsu d'ane tilo ga Mallam yahya.

Su yan asalin garin kanjiyane dake jahar katsina.

Tun yana Dan shekara shida mahaifinshi yakaishi cikin birnin katsina almajiranci.
A makaranta wani babban malami wato mallam Ballo.

Haka suke rayuwa a wannan makarantar Wanda yawanci abincin dazasuci sai sunje bara suke samu, wani sa'in idan basu samuba haka suke haqura su kwanta kasancewar iyayensu basu wani had'osu da abincin kirkiba, gashi shima malamin ta kanshi yake don bazai iya daukar nauyinsuba kasancewar shima bamai wani hali bane ga d'aliban dayawa.

Haka rayuwa ta kasance basa komawa qauyensu saiga damina don taimakawa iyayen da noma, da kaka tayi sai asake turosu da guzurin dabe taka kara ya karyaba.

Rayuwa suke irin na sakakku wadanda babu mai tsawata Masu sai malaminsu shima a lokacin karatu, wani sa'in karatun ma ba dauka sukeyiba saboda ai sai ciki ya dauka sannan za'a maganar karatu, wani sa'in saisun yi aikatau sannan zasu sami abinci.

Haka rayuwarsu ta kasance wani sa'in tufafin dazasu sa sai sunyi bara suke samu shima dakyar, wasu kau Kayan jikinsu sbd tsabar datti ko zanen Kayan ba'a gani, wasu kuma kaya sun 6e66ere Masu ajiki Amma babu halin dinkawa.

Acikin wannan rayuwar wasu suke kauce hanya su fada munanan hali batareda an ankaraba tunda babu Masu sanyamusu ido, sai aga ba'a samo karatunba kuma 'ya'ya sun kangare sun gaggari al'umma.

Shamsu shi Allah ya tsareshi da fadawa irin wadanan halin Saidai yataso da kwadayin abin duniya, kudi ko ta hanyar haram ne yanabi yasamesu, gashi da tarin karatu Saidai be amfaneshiba.

Duk buga bugan dazaiyi yasamu kudi saiyayi don a tunaninshi kudi shine komai, idan kanada kudi to kowama kana iya takawa.

Tun yana komawa kauyensu Duk damina don taya babbanshi noma har ya daina.

Alokacin dakowa ke komawa kauye sai shi yashige cikin gari yana buga buganshi na Neman kudi, wani sa'in ya kwana a tasha wani sa'in a massalaci.

Babu yadda babanshi beyi dashiba don ya dinga leqosu koda sau dayane a shekara Amma firr yaqi, don aganinshi baya iya zaman kauye kuma, yasaba da riqe kudi da cin Abu mai maski mezeje yi kauye?

Abun ba qaramin damun mallam Yahya yayiba gashi shine d'a talin qwal nashi.

Haka ya haqura yazuba mashi idanu don yariga ya kangare bawai maganar kowa yakejiba.

Shamsu likafa taji gaba, Tun yana buga buganshi a katsina harya koma kano jin can anfi kasuwanci kuma anfi samun kudi.

Wani babban shago yasamu aiki na yaron shago inda ake siyarda Cosmetics Kala kala.

Sosai yake samun kudi don shagon shahararene kuma mai shagon na sallama mai tsoka.

Dayake Shamsu Allah yayimashi farin jinin mutane, cikin d'an qanqanin lokaci yasan kwastamomi dayawa, kusan kowa yasanshi saboda barkwancishi da iya mu'amala.

Ahankali ahankali yafara yiwa ubangidan nashi cuwa, yana mashi rinto, wani sa'in idan aka aikashi saro kaya saiya Dora nashi Asama kokuma wurin Saidawa ya qara akai.

Dayake uban gidan nashi ya yarda dashi kuma becika sa ido sosaiba, beyi saurin ganewaba, saida yayi mashi mummunar 6anna, sbd Duk kusan customers dinshi sunbar zuwa sbd yadda kayanshi suke tsada.

Ataqaice dai shago yarushe babu riba kullum sai faduwa, Daga qarshe Saidai ya sallami yaran shagon gabadaya yarufe shagon sbd rashin jari.

Shamsu daketa Tara kudaden dayake samu wajen rintonshi, yasamu wani qaramin shago cikin kasuwar yabude shima yazuba irin Kayan da oganshi ke Saidawa ada.

Ahankali ahankali, kasuwancinshi yadinga ha66aka, Allah yasa mashi albarka a kasuwancinshi.

Abu qarami yakoma babba Tun yana sari garuruwa harya fara fita qasashen waje.

Cikin shekara biyar ya bude wani qaton company mai suna A.S GALLERY

Duk abinda akeso na Kayan alatu yana Saidawa. Company nashi yazama shaharare Wanda ake tutiya dashi garin kano.

Wata shekara yadai runtse ido yayi aikin hajji shima sbd matsa mishi da abokan kasuwancinshi kemashi na yaqi aikin hajji.

Haka dukiyar Alhaji shamsu yacigaba da bunqasa Wanda Duk yawanci na ha'incine don sosai ya kware wajen ha'intar mutane.

Saidai abinka ga Dan kauye, Duk tarin dukiyarshi beta6a marmarin sayan kadaroriba sbd gaba kokuma yabude reshe awani wajen, Shidai Duk abinda yasamu ya narkawa company dinshi.


Ana haka rasuwar mallam yahya ta riskeshi, sosai ya girgiza don rabonshi da kankiya harya manta, yana dai yimusu aike bakin gwargwado.

Ba shiri yanufi qauyen, yayi kuka sosai jin baban nashi yadade kwance ba lfy, haka yaita Neman gafarar inno (mahaifiyarshi) harta yafe mashi.

Bayan Arba'in ya tarkata inno sai kanon dabo don acewarshi bazai iya cigaba da zama a kauyeba.

Shekara daya da rasuwar mallam inno ma tabishi, babu laifi mutuwar ta girgizashi na Dan lokaci sannan yacigaba da rayuwarshi.

Yana Dan shekara 32 yayi aure ya auri wata shuwa Arab Wanda suka hadu da ita awata tafiya dayayi Maiduguri.

Mace mai kyau, hankali da tarbiyya.

Bayan shekara ta sulu6o Masu da kyakyawar baby mai kammaninta sak masha Allah.

Saidai Tun Daga sannan suka fara samun sa6ani dashi a dalilin sata dayayi Wai tacire mahaifarta beson haihuwa diya daya ta isheshi.
Wai 'ya'ya babu abinda suke jawowa sai talauci.
Itakau firr taqiya Wanda hakan yaja mummunan sa6ani tsakaninsu Wanda Daga qarshe suka rabu da Abu yaqi dadi.


SAUDART Nada shekara biyar Alhaji shamsu ya amsota sbd yaji mahaifiyarta zatayi aure acewarshi 'yarshi baza taje wani gida agolanciba.

Saida aka kai ruwa rana sannan suka bashi ita da sharadin sai ta dinga zuwa Duk sati suna ganinta kuma yasata both islamiya da boko.

Soyayya sosai Alhaji shamsu ke nunama Saudart, wata irin shaquwa ke tsakaninsu na qin qarawa don sunfi shaquwa dashi bisaga mamanta.

Ya sakata both islamiyar da boko, Duk wani gata da diya zata samu wajen iyayenta tana samu don Saudart tadauko dukan halin iyayenta.
Kyaun fuska da hali na mamanta sai farinjini da siye zuciya irinna bbanta.

Tun tana yar shekara sha biyar tasauke Al qur'ani mai girma, a fannin boko kau tanada kwalin degree a fannin economics.

Saudart Tun tana yarinya ta tsani mutuwar aure, don shine silan rabuwanta da daya Daga iyayenta.

Tsanar yaqara karfine dataji a islamiya malaminsu ya gayamusu babu abinda Allah ya tsana kamar mutuwar aure don har sama girgiza take.

Tin alokacin take addu'ar Allah yabata miji nagari Wanda mutuwa kadai zata rabasu.

Tana gama degree dinta ta matsama daddynta ya bude mata bakery, sbd tsananin son datakema girki, da farko yaqi yarda don yafison tayi aikin office Amma data matsamashi dole yabude mata Wanda nan da nan Allah yasamata albarka a harkar har tayi fice a garin, babu Wanda beson ALHAIRI BAKERY ba.


Ana haka wannan cuta (covid19) tashigo duniya harta 6illa Nigeria Wanda hakan baqaramin rushe tattalin arziqin qasa yayi, cikin wadanda abun yashafa harda Alhaji shamsu don komai ya karye sakamakon rufe border da akayi.

Ga tarin basussukan da ake binshi na banki haka yasa dole yanemi taimakon shahararen kamfanin nan na A.A ENTERPRISES.

Saiga kuma yadda abun ya kasance...✍


Sorry babu dai editing🙏


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan cutar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)







008




Cigaban labari📖





Yau Saudart tafi zama busy saboda ita dakanta ke tsara cake din bikin Sir Wilson, abubuwa take cikin qwarewa while wasu tsirarun ma'aikata na gefe suna qara daukar kwas.

Aiki take Amma hankalinta na wajen daddynta.

Tun dazu take jiran kiranshi Amma shiru, Allah Allah take ta ida ta dawo gida, abindama yaja delay rashin samun kalar colouring dasukeso dawuri da tuni angama an hada da kingin snacks da akayi delivering dazu.


6:30pm ta kammala cake din, sai tashin wow! Wow!! Kakeji a dakin kamar jiniyar motar ambulance sbd haduwar cake din.

"Wow ma'am! This is the best cake I've ever set eyes on" inji wani mai suna Farouq yana tafawa.

Nan kowa yabi sahu sunata tafa mata.

Yar dariya tayi sannan tad'an dramatically tana cewa "thank you, thank you".

Ba ita tabar bakeryn ba sai 7:00pm Duk hankalinta yayi gida.

'Meyasa dad be kiraniba? I hope all is well' tafada acikin zuciya.




Da sallama tashiga parlourn, can ta hango daddy a dining yana sipping din coffee.

Dadi taji ganinshi cikin nishadi babu damuwar komai.

Amsamata sallamar yayi cikin fara'a saikuma yasha mur yana kai dubanshi ga wall clock.

Dan Waro idanu tayi tana Dan dariya ciki ciki yayinda ta qarasa wajenshi tana rungumo kafadunshi.

"Sorry dad, am late, wlh wani aiki ya tsayar dani"

Hararar wasa yayimata.

"Silly girl, harna fara damuwa danaji shiru" yafada yana dungure mata kai.

Shafa kan take tana turo baki
"Ai Dad Baka damu daniba, ko ka kira kaji lfy?"

Murmushi yayi yace "ai ina cikin shawarar kiranki sai gaki"

Jan kujera tayi ta zauna kusa dashi.

"So daddy how far? Guess ansamu nasara. Yadda kake washe bakinnan nasan ba banzaba"

Bugu yakai mata ta kauce tana dariya.

"Lallai kin maisheni kakanki ko?"

"Am sorry, Nidai ya kuka kaya?"

"Lau.. Tashi kiyi Sallah mufita, akwai outing yau"

Wani ihu tabuga tana tsalle
"Yeee! Kace anci nasara? Kai alhamdulilah! Dad am soo happy!" Tafada tana rungumarshi.

Dariya yayi yana janyeta.

"Tukunna dai, kidai je kiyi sallar ki shirya"

"Yanzu kuwa" tafada tareda yin hanyar dakinta da sauri harda hadawa da Dan gudu.

Binta yayi da kallo harta kule,
Ajiyar zuciya yayi yana sake qarfafama kanshi gwiwa.








Sosai Saudart taji dadin outing din don wurare daban daban suka je na shaqatawa, sannan sukaje wani had'ad'en restaurant sukaci abinci Daga qarshe suka biya shopping mall sukayi shopping Wanda Duk yawanci Kayan data kwasa dad dinta na siyarwa kawai shiya matsa saita saya.


Agajiye liqis suka dawo gida. Saida kowa ya watsa yayi sallar isha'i sannan suka dawo parlour suna kallo suna hira.

Soyake ya dauko mata maganar daketa cin ranshi Tun dazu Amma yakasa.

Can ya nisa ya kalleta da yanayi na seriousness yace "SAUDATU"

Dumm gabanta yafadi dajin yakira ainahin sunanta.

Kasa kai cokalin ice cream din tayi a baki ta ajiye sannan ta maida hankalinta kanshi.

Shiru ya ratsa falon yana tunanin yadda zaiyi mata presenting din maganar, can ya nisa yace

"Saudatu, baki tambayi yadda muka qare dasu mutanenki ba"

Ajiyar zuciya tasauke da qarfi

"Kai dad, harka bani tsoro, to ya kuka qare ba cewa kayi sun bakaba?"

"Eh sun bani Amma basu baniba"

Kallon rashin fahimta tayimashi
"Ya hausan sun Baka, basu bakaba?"

"Abinda yafaru shine....."

Cikin qwarewa da baiwarshi ta dadin baki ya labarta mata Duk yadda sukayi dasu Sadeeq.


Tunda yafara magana ta zubamashi idanu tana kallo ko blinking batayi don ita harga Allah batasan inda yadosaba.

Koda yakai aya batabar kallon shiba.
Shima kallonta yake don ganin reaction dinta Amma she's expressionless.

Kamo hannunta guda yayi yana Dan murzawa.

"Are you there shalele?"

Sai alokacin tayi blinking, ahankali ta motsa baki tace
"I don't get you dad, kaina ya kulle"

Murmushi yayi sannan yafito mata 6aro2 yace

"I mean so suke inbashi ke akan yarjejeniya Dana biya zai maidomin ke, ma'ana you guys are having contract marriage"

Zaro idanu tad'an yi sannan ga mammakinshi tafashe da dariya harda tafawa.

"Lol.. Amma dad mahaukatane ko? I guess company mahaukatane idan ba hakaba ina aka ta6a wannan irin auren? Ko a film ma banta6a ganiba, gaskiya a binciki brain dinsu"


Shiru Dad yayi yana kallon yadda tama maida abun wasa.

"Jewel this is not funny, please let be serious" yafada yana qoqarin danne 6acin ranshi.

"Ok..ok, naji sai kace musu me daddy?"

"Subani lokaci inyi tunani akai"

"Tunani? Tunani fa kace Dad? Meye abin Tsayawa tunani anan, amsar a Afili take, idan su jahilai ne mu ba jahilai bane, the amsa is capital NO!" Tafada itama cikin son danne 6acin ranta Amma deep down she's boiling.

Kamo dayan hannun nata yayi yahada biyu sannan a tausashe yace "shalele, please listen, ahalin yanzu banida za6in da yawuce..."

"Wait Dad.., come again, bamuda me? Bakada za6i fa kace? Don't tell me kana shirin yadda da jahilcinsune" ta katseshi tana kallonshi unbelievable.

"Saudart... Wannan ba jahilci bane, banida choice, sokike inzauna in nade hannu ina kallon company na yayi collapsing a gaban idanuna?"

Shiru tayi don she's speechless ma, kallon shi kawai take cikeda rashin yarda.

Matsa hannunta yafarayi a tausashe.

"Kinyi shiru shalele, please say something, yanzu kece last hope dina. Please speak up"

"Dad me zance? Ka kasheni da raini, nakasa yarda da abinda nakeji Daga gareka"

"Saudart auren nan ba dadewa zaiyiba, zanyi iyakar qoqarina wajen ganin na hada kudin dawuri, bazaki wuce 6months ba"

Fizge hannunta tayi ba shiri
"Dad! Are you kidding me? AUREN KWANGILA? Ni? Dad kasan abinda Allah yafi tsana shine mutuwar aure?
Wannan ma agefe, Dad atunanina kafi kowa sanina, kafi kowa sanin ra'ayina, kasan ra'ayina na aure.."

Katseta yayi dacewa "sanin hakan yasa na yarda da sharadin babu abinda zai shiga tsakaninku, believe me I.."

"Noo!" Ta katseshi da karfi tana toshe kunnuwanta.

"Shalele.."

Miqewa tayi bashiri still hannunta dade da kunnuwa, idanunta nakawo ruwa.

"I said No! Bazai yiwuba! Impossible!"

Saita juya dagudu tanufi stairs kuka ba kufce mata.


Binta yayi yana kwalamata kira Amma inaa shigewa tayi dakin tarufe harda sa sakata, sannan taruga tafada kan gado tana gunjin kuka.


Naushin iska yayi yana fadin "shit! Shit!! Shit!!!"...✍


No editing🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)




Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)

Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲





Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)









009







Aranar babu wanda yayi barcin kirki cikinsu, musanmman Saudart data kusan kwana tana kuka.



Da asuba a kasalance ta tashi tayi Sallah ko lazimi Kasa yi tayi barci ya dauketa akan sallayar saboda rashin isashen barci datayi jiya.

Sai 8:00am ta farka, wanka tashiga Bayan yan mintuna tafito sannan tayi shirin aiki a kasalance, har yanzu takasa yarda da abinda yafaru jiya.



Ahankali take saukowa a stairs din hannunta daya da waya danyen kuma rataye da side bag.

Dago kai yayi yakai dubanshi saitinda yajiyo takunta.

Kallo daya yayi mata yagane kukan datayi jiya ba kadan bane saboda yada idanun suka dan kumbura gashi basu ida washewaba.

Tunda suka hada idanu ta kauda kai sannan tanufoshi a kasalance.

"Ina kwana Dad" ta gaisheshi in a formal way.

Kamo hannunta yayi zai zaunar daita kusadashi ta janye cikin wayancewa.

"Dad, am late, zan wuce aiki"

Kara kamo hannunta yayi yace "break fa, baki karya ba"

"Am ok" ta amsa ataqaice.

"No, dole kici wani Abu, please sit down"

Zata bude baki tayi musu yayi saurin katseta da

"Please.."

Babu musu ta ja kujerar ta zauna, da kanshi yayi serving dinta sannan ya turamata gabanta.

Ba musu tajawo abincin tashiga ci Saidai Duk yadda yaso su hada ido taqi yarda.

Tutturawa taitayi har saida taci rabi sannan ta ture plate din tana goge bakinta da tissue.

Kamo hannunta guda yayi ganin tana niyyar tashi hakan yasa ta fasa tashin Saidai ko dagowa batayiba.


"Shalele?.... Fushi kike da Daddynki?"

Shiru tayi kanta Kasa

"Am so sorry shalele, banyi hakan don 6atamiki raiba. Kawai banida za6ine, shalele ko jiya saida akayiman barazana ta waya, ga banki kema kifini sanin halinda nake ciki Basai nasake miki bayaniba" yafada a tausashe yana murza hannunta.

Har yanzu shiru tayi batace komai ba kuma bata dagoba.

"Shalele idan da inada yadda zanyi nima Tun farko zanyi rejecting dinsu Amma a halin yanzu they are my last hope"

"Dan ba'aso mutum na fidda rai akan rahmar ubangiji, arziqi da rashinshi Duk na Allah ne, saboda bamason talauci saimu sa6ama Allah? Shin wayau zamu yima Allah? Kasani Allah yasan damu Kuma yasan halinda muke ciki, akwai wadanda suka fimu shiga matsala kuma sun dauki qaddara, why not Muma muyi koyi dasu? Dad wannan kwata kwata is not an option, haram ne"

"Shalele, Allah na yafewa Duk Wanda ya nemi yafiyarshi, zamu nemi yafiyar Allah Bayan mungama komai, Allah gafurun raheem ne"

Shiru Saudart tayi don takaici yama hanata magana

"Say something please jewel"

Janye hannunta tayi Daga riqonshi tace "Dad bazan iyaba, tunda bazaka iya rungumar qaddara nizan siyarda bakery dina saikayi settling din komai, inyaso saina nemi aiki"

Da ada ne zai yarda Amma yanzu babu abinda yakeso kamar yazama surukin A.A so maganar siyarda bakery ma be tasoba.


"Shalele siyarda bakery dinki won't help, kawai amincewarki ne kadai zai taimakeni"

"Then am sorry, bazan iyaba" tafada ta tashi afusace zata wuce.

Kamo hannunta yayi da sauri tareda juyota da d'an karfi

"Don't you dare walk out on me ok?! Ina miki magana zaki wani tashi min ki wuce, ni tsaranki ne?!" Yafada 6acin ran dayake dannewa yaqi dannuwa.

Kallonshi take idanunta suka kawo ruwa don tunda take beta6a yimata maganaba cikin wannan yanayin.

"Dad?.."

"It ok, kina iya tafiya, atunanina ke mai sharemin hawayena ce, a tunanina ke mai rufamin asiri ce but am made a mistake!"

"Dad..." Saikuma ta fashe da kuka.


"Go! Kawai ki tafi nagode" yafada yana barin parlourn Dama gidan gabadaya.


Kuka Saudart keyi kamar ranta zai fita, tarasa gane meyasa idanun daddynta yarufe har haka. Bakeryn dabata fitaba kenan, ranar taci kuka har ta godewa Allah.

Saidai tayima 'yan bakery dinta qaryar batajin dadi sannan ta wakilta P.A dinta tayi taking charge.


Yini tayi cikin qunci ranar tayita jiran dawowar daddy Amma hartayi barci be dawoba.


Washegari ma Tun kafin tafito yafita.

Duniya tayima Saudart zafi don kwata kwata Dad yafita harkarta.
Abinda be ta6a yi mataba, kullum cikin kuka take don bema barin su hadu, koda sun hadu baya amsa gaisuwarta barema azarce sa magana, Dama yaganta zai fice ko yashige dakinshi beqara fitowa.

Dukda damuwar datake ciki na shariyar daddy hakan be sata jin zata amince da buqatarshi ba, she's stubborn, tagado taurin kan maminta ne.


Yau Monday dawuri tashirya cikin wata gown din atamfa mai A, sannan ta yane kanta da kyale mai dan girma.

Sosai tayi kyau dukda kallo daya zaka yimata kasan tana cikin damuwa.

Fitowa tayi falo, kamar yadda tayi zato Dad yariga yafita.

Itama Sakai tayi tafita batareda ta kula breakfast da'aka jeramataba.

Motarta tashiga sannan ta karya motar hanyar company din A.A ENTERPRISES.

Dole ayita yau taqare, tagaji da attitude da daddynta kebata.

Bazata iya juraba kuma, dolene yau taga A.A......✍


Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan annoba (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲






Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)






010




Cikin kwarewa tashigo da motar cikin qatuwar haraban shahararen company nan datake tajin labarinshi.

Parking tayi a parking space sannan tafito ahankali.

Cikin wayencewa take qarema makeken qayattacen company din kallo tana tasbihi ga Allah.

Kallo daya zakayima kamfanin kasan mallakin tattacen mai kudi ne don Duk inda ka wulga glass ne, kamar dashi akayi ginin. Hatta entrance door ma na glass ne.

A wajen sanitizing hannu taje ta wanke hannunta kamar yadda yake doka akowani wajen da za'ayi cud'anya da mutane Tun shigowar wannan cutar (covid19), sannan taje wajen kofar ta latsa botton yabude sannan tashiga yarufe sannan tasake budewa taciki.

'Masha Allah' ta furta tunda tasa kafarta tashiga ciki.

Watakan wani Sanyi mai dadi ya bugeta mai cakud'e da sanyayan qamshi.

Zuqar iska tayi ahankali tana lumshe idanu sannan ta furzar.

Cikin natsuwa take takawa zuwa wajen receptionist dake gefe tanayi tana qarema wajen kallo a wayance, kujeru dake jefi jefi awajen ma abun kallone.

Wajen receptionist din tanufa, mace mai fara'a ta gaisheta.

"Welcome to A.A ENTERPRISES ma'am how may I help you" tafada fuskarta washe.

Dan Gyaran murya Saudart tayi sannan tace "thanks you, please I want to be directed to the C.E.O office"

"Ok ma'am, here you are" inji receptionist din tana miqamata wani card.

Amsa tayi tayimata godiya sannan tabar wajen tana kallon card din.

Wajen lift tanufa tayi typing din floor number din a sannan tashiga.

Cikin yan sakanni harya kaita, kofar tabude tafito.

Qauyancinta kusan fitowa fili yayi saboda haduwar wajen yawuce misali.
Sai yanzu taga can Kasa Ashe nafilane a kyau.

Cikin natsuwa ta taka zuwa desk din secretary din wanda hankalinta ke kan system din gabanta.

Ganin kamar ba musulma bace sakamakon 6ingillalun kayanta da uban gashin doki data tilama kai yasata cewa
"Hi" Maimakon sallama.

Dagowa Helen tayi tana kallonta, wata kyakyawar budurwa tagani mai mugun shiga rai, gatadai bawani ado tayiba ko kwalliyar hauka Amma ita kanta ta burgeta.
She looks so simple and unique.

"Hello, how may I help you?" Ta amsa tanamata wani kallon raini don atunaninta irin yanmatan nanne Masu kawo Kansu wa boss nata dukda taga wannan kamar nitsatsace koga decent shigartama.

Dukda ta lura da kallon rainin da matar ke binta dashi hakan besata nuna komai ba tace
"Yes, please inason ganin C.E.O ne"

Wani kallon up and down tasake binta dashi zuciyarta fall Kishi don itama a haukanta son boss take.

"Kunada appointment ne?" Ta tambaya a d'age.

"No Amma what I want to discuss with him is very important" inji Saudart da jikinta yafara Sanyi da yanayin kallon dataga matar ke binta dashi.

"Boss baya ganin mutum saida appointment so am sorry kya iya tafiya idan kika samu appointment dashi saiki dawo"

Ta maida hankalinta ga system din gabanta.

Shiru Saudart tadanyi tana nazarin me zatace mata tabari taganshi don sosai takeson ganawa dashi.

"Please I really.."

Katseta Helen tayi da "what? Waiku mata meyasa bakuda ajine, ayita koranku Amma kuyita naci, ke yanzu bakiji kunyaba? Kin wani wanko kafa kinzo gun namiji har office? Da anyi magana kuce Muslim, Masu tsoron Allah, ina tsoron Allahn yake? Kitafi kafin yafito don mutuncinki zaici don ba irin yan iskan mazannan bane"

Sosai kan Saudart ya kulle, Wai tsaya me take shirin kirantane?

Kafin tasamu zarafin magana kofar office din C.E.O din ya bude saigashi yafito cikin shigar suit baqi da shirt din ciki fari.

Turus yayi ganinsu tsaitsaye kasancewar tashi Helen tayi tana zazzaga mata bala'in.

Kallon Saudart yatsaya yi na yan daqiqu sannan ya kalli Helen

"Helen, what's going on here?"

Cikin ladabi tafara cewa "Sir, Wai Mr A.A take son gani kuma basuda appointment Sir"

Kallon Saudart yayi dake kallonsu itama yace "hello miss"

Dakyar ta iya cewa Hi saboda yadda takeji, she felt totally embarrassed jin yadda Helen ta fassarata.

"Mr A.A zaki gani?" Ya tambaya a tausashe

Kamar tace A'a tafasa saikuma ta daure tace

"Yes Amma ba prob tunda sai an samu appointment dashi, am sorry" tafada tana niyyar juyawa.

Saurin tsaidata sadeeq yayi dacewa "wait please, am so sorry. Ba haka bane bari inyimiki iso"

Juyo tayi asanyaye tace "A'a ba matsala fa, zan naimi appointment"

"No please ki tsaya bari nayimiki iso" yafada yana juyawa da sauri ya bude kofar daya fito ya shige.

Da kallon mammaki Helen tabishi dashi.

Itakau Saudart dadi taji koba komai zata samu damar rama wulaqancin da Helen tayimata.

"Hey.. Atunanina kallo daya za'ayima ni dake a tantace wa ya cancanci sunan karuwa, Saudart tafi karfin tabi namiji Saidai subita, maza dayawa sun mutu mata Masu kyau kudi da aji mezatayi da tsoho akwala (atunaninta tsohone mai kamfanin)
So it's better ki dinga tauna kalamanki kafin ki furtasu don mata suna suka tara".

Daidai nan sadeeq yafito yana fadin " bismillah madam"

Wani kallo tasake watsama Helen sannan tabishi abaya tabar Helen hangame da mouth😨



Ahankali tasanya kafarta cikin office din wani daddadan qamshi namata marhabin.

Saida tashiga sannan sadeeq yafita yana rufomusu kofar.

Tsayuwa tayi takasa gaba takasa baya don jitayi Duk qarfin gwiwarta data shigo dashi ya zirare.

Batama son dago idanu ta kalleshi don bata buqatar haka.

Haka taita Tsayuwa kanta Kasa tana jiran ayimata iso Amma shiru.

Shima 6angaren Ashraf hakan take don tunda sadeeq yazo ya kyankyasa masa ya tsinci kanshi cikin 6acin rai.
Wato like father like daughter, yadda uban keda kwadayi hakama Diyar tunda gashi takawo kanta, hakan yasa yaqi dagowa ya kalleta tunda tashigo.

Jin shirun yayi yawa yasamu dagowa lokaci daya, caraf suka hada idanu👀

Gaban Saudart yafadi tayi saurin janyewa don bashi tayi zaton ganiba.

'Wannan ne A.A din ko d'anshi ne?' Tambayar datayima kanta kenan.

Shikau ko a kwalar shirt dinshi don bawani Tsayawa qaremata kallo yayi ba.

"Good morning..sir" tafada cikin rawar murya.

Shiru yayi kamar bazai amsaba sai can kuma yace
"Morning"

Ganin Beda niyyar yimata iso yasata summoning courage ta qaraso gabanshi taja kujera tana fadin "may I?"

Banza yayi da ita itama bata jira amsarshiba tazauna don Allah Allah take tayi abinda yakawota takoma.

Shiru ya ratsa office din, tanata kokwanton tayi maganane kota bari yafara.

Ganin wankin hula nason kaita dare yasata yin karfin halin cewa
"Ehm.. Am Saudart shamsu by name"
Shiru tayi ganin ya dago yazubamata cat eyes dinshi daya kusan rikitata.

Janye idanu tayi saurin yi sannan dakyar tasake bude baki tace
"Ni diyar Alhaji shamsu kankiya ce"

"Uhum?" Ya buqaceta cikin tsareta da idanu.

"How may I help you Miss Shamsu?"

Jitayi ta takura da kallon qurrillar dayake binta dashi, cikin inda inda tafara cewa

"Akan.. Akan previous maganarku da Daddy ne, na...na.. Auren...auren contract... Shine..."

"Shine kikazo yimin godiya Dana za6i nayi hakan da babanki? Koko shine yasa

Please Login or Register in order to submit comment