Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gwiwa sannan ta yane kanta da farin gyale.

Kamar kullum yauma simple makeup tayi, sai kuma purple janbakin datasa abaki ta feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta dauki wayarta ta fito.


Direct gidan Dr zahra tanufa.

Nan ta tarda su Loveth da sauransu ansha gayu sai hada hadan fita da abinci suke.

Suna ganinta suka ja suka tsaya baki bude suna kallonta.

Qarasawa tayi tana rufemasu baki tana cewa

"Kurufe kar quda yashiga" tafada tana hararsu

Sai a sannan sukadan sun bude baki

"Wow saudart, you look soo takeaway!" Inji Reyna

"Ni banma ganetaba dafarko na rantse" inji Loveth

Wata yar Korea mai suna chuchu tace

"Anya are you sure you're a Nigerian? Ni idan aka fadi Nigeria the first thing dake zuwa min arai shine baqaqe, munana, gajeru..." Hararar da saudart ke antayamata ya hanata qarasawa tafara dariya


"Nikuma idan akace Korea Abu na farko dake zuwa min arai shine mitsi mitsin idanu, qurmemen goshi, tsawo kamar pole sai nannanan hanci" saudart itama ta rama.

Nan duk aka kwashe da dariya, nan fa aka Dora kan inda aka tsaya dazu, suna kai abinci suna cafta har suka gama, nan suka fito suka zauna.


Wajen filine kamar filin kwallo qasan shimfide da Grass carpet, koina fayau kamar ba dareba.

Mata na daga bangaren haggu sun hada group dinsu hakama maza a bangaren dama sai cafta suke Wanda be wuce ta kwallo ko wrestling.

Sai gashi estate din dake tsit kodayaushe yau tacika da hayaniya yadda kukasan sallah ake ko wani gaggarumin Abu.

Saudart na can tsakiyar yanmatan tana maida yadda akayi, yadda kukasan ta Dade da saninsu, kusan itace centre of concentration don duk Wanda yabude baki saudart yake kira.

Cafta suke kan qasashe kowa na kare nashi yana kushwle na dan uwanshi, kusan duk tararmata sukayi don duk tafisu baki kuma tasan amsarda zataba mutum daidai da maganar shi kuma da wuya ta bada amsa bata Baku dariya ba, hakan yasa duk suka tararmata suna sukan Nigeria Itakuma tana karemu.

Acan bangaren maza kau zaune suke kashi kashi, wasu na games irinsu ludo ko whot wasu na caftar kwallo ko wrestling.

Ashraf na cikin masu buga whot, game suke mai zafi Wanda ko daga kai beson yi.


A cikin mazan akwai wani dan Spain dake zaune can gefe tundazu ya zubama bangaren mata idanu kuma ba kowa yake kallo ba sai wata cute, unique babe dabe ta6a ganin mai tafiya da zuciya farat dayaba irinta.

Tunda ya qyalla idanu akanta yakasa dauke ido akanta.

Maganarta, murmushinta, harararta duk sun tafi da imaninshi

Yana lura da yadda idan suka hada idanu take saurin kauda Kai cikin basarwa tana cigaba da surutunta.

Hannu bibbiyu yasa yabuga tagumi yana kallonta babu ko kyaftawa.

Jitayi an ta6oshi hakan yasashi dagowa ya kalli mutumin

"Yadai amir? Bakayin komai, kawani dawo nan ka buga tagumi, lfy?"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasake kallon saitinta kafin yace

"Ta tafi dani" yafada cikin shauqi

"Wa?" Inji mutumin

"Cutie... Na fada soyyayar cutie" yafada yana lumshe idanu

"Wacece cutie" inji mutumin

"Kalli can, duba dakyau, wacece kamar zahra acikin taurari? Haskenta na dabanne, kyawunta na dabanne, murmushinta? Wayyo! Idan tayi murmushi jiyake kamarvzan narke, ji idanun, soo perfect! Ya rabb kabani ita badon halina ba" yafada yana qara kallonta

"Wai wancan mai purple and white din?" Inji mutumin

"Hell yes! Itace, mii ruhi" yafada yana dafa saitin zuciyarshi


"Sistern wannan baqonne, I asked him yace tareda qanwarshi yake, qanwarshi ce"

Waro idanu amir yayi
"Dagaske? Ina yake?"

Nuna mashi Ashraf yayi dake buga whot dinshi hankali kwance.

Zumbur amir ya miqe yanufi wajensu ya zauna kusada Ashraf.

"Aslm alaika" yafada yana miqa mashi hannu

"Wslm" Ashraf ya amsa yana shaking dinshi


"Kaine baqonmu ko?" Inji amir yana murmushi

"Eh nine" inji shi yana murmushi

"Wow, nice to meet you, ni sunana Amir Khalid, iyayena mutanen morroco ne, amma anan suke zaune, nan suka haifeni, nan nayi karatuna har zuwa matakin PhD, yanzu ni constructional engineer ne ina aiki a company AL-DABB COMPANY LTD.."

nan yaita rattafo tarihinshi, Shidai Ashraf sauraron shi yake yana tunanin shi wannan kanshi daya kuwa? Daga ganin mutum saika bugs da bashi tarihinka?

Be qaseshi ba har saida yagama yadora da

"Tun ina qarami nake son Africans, kuma ina mararin hada alaqa dasu.. ERM..naga qanwarka...tunda nake ban ta6ajin abinda nakeji gameda itaba..please.. Please ka bani dama in tunkareta...ina... Sonta" ya qarashe maganar cikin dar dar don ganin yadda harya daga kati zai buga amma kalamanshi sunsa hannun maqalewa a iska.

Shima shiru yayi yana kallonshi a daddarce don ganin abinda zai biyo baya.

Sai gani yayi ya kara waya a kunnenshi yana amsa waya ya tashi ya matsa can gefe yana cigaba da amsar kiran.

Ajiyar zuciya amir ya sauke ganin Ashe waya zaiyi don shi a tunaninshi shi yasashi wannan qamewar.

Saitin matan yasake kallo yaganta tsaye itada wata zasu tafi hakan yasashi saurin miqewa yabi bayan su

Suna cikin tafiya da Reyna zasu qaro juice sukaji anaqwalamasu kira daga bayansu

Juyawa sukai, gabanta ne yafadi ganin wannan mayen mutumin ne daya addabeta da kallo.

Saurin Kamo hannun Reyna tayi don su tafi don ita tsoron shi ma take amma sai Reyna ta cije.

Dagudu ya qaraso wajensu yana shesheka duqewa.

"Kai matan nan saurin tsiya gareku" yafada yana shesheka

"Wai ma, muda muke tfy ahankali" inji Reyna tana bin saudart datayi gaba

Shima saurin bindu yayi yana cewa

"Eh mana, ba kamar wannan ba qauyar" yafada cikin tsokana

Harara saudart ta gallamashi Wanda saida zuciyarshi takusan barin aiki

"Wacece baqauyar?" Inji Reyna tana dry

Dakyar ya lalubo muryarshi yace " wannan mana, halan kurma ce?"

Dariya sosai Reyna tayi tace "A'a ba kurma bace amma baqauya ce, qauyen Nigeria" tafada tana dariya ganin yadda saudart ke hararta


"Nigeria Nigeria? Inanema Nigeria? Sai sunan yayi min shige da sunan zoo" inji amir cikin tsokana

Harara saudart ta gallamashi for the first time tace
"A'a cave ne ba zoo ba"

Dariya sukayi gabadaya

Amir yace
"Allah na ta6a zuwa Nigeria sau daya cikin wani watan Ramadan, munje wani project, the country is damn hot, kamar da oven akayi gidajen, ataqaice muna tsakiyar yin project din nafara ganin wani hazo hazo, inajin dum dum cikin kaina kamar ana daka, ataqaice saidai farkwa nayi naganni hospital, anamin qarin ruwa" dariya su saudart suke tunda yafara lbrin don yadda yake lbrin sai kayi dry


Cikin jin dadin sasu dry dayayi ya cigaba dacewa

"Ataqaice ranar aka samamin visar dawowa, azumi na kau tuni yazama sheqaqqe"

Nanma dariya suka fashe dashi amir na tayasu, basu ankaraba sukaga ansha Gabansu Wanda hakan yasa su saurin dagowa.

Ware idanu saudart tayi cikin matsanancin faduwar gaba ganin Wanda yasha Gabansu, fuskarnan tashi babu rahma...✍



Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲


Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲


Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)






050


Kallonta yake da rinnanun idanunshi dasuka chanza kala bako kyaftawa, hakan yasata jin cikinta na Neman juyewa don bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin ba.

Bata ankaraba taji ya chafko hannunta yafara janta.

Amir da Reyna dasukayi mutuwar tsaye tundazu sukayi saurin binsu

"Bro please don't hurt her, wlh I mean no harm, don Allah kayi hqr" inji amir dake binshi da sauri don shi duk a tunaninshi hukuntata zaiyi a matsayinshi na yayanta sbd ya ganta tsaye da wani.

"Please bro listen to me" yafada Yanajin kamar ya kwaceta da qarfi don be qaunar abinda zai ta6a lu'u lu'u dinshi

Ko kallon gefenshi Ashraf beyi sai Jan saudart dayake da sauri yanufi gida itakau saudart kasa magantuwa tayi sai binshi take kamar raqumi da akala


Saurin shan Gabansu amir din yayi yana cewa

"Please bro listen to me"

"Get lost you fool!" Inji Ashraf cikin qaraji

"Please kayi hqr, ni nazo na sameta, please don't hurt her" yafada pleadingly

"Bazaka kauceba?!" Inji Ashraf dakeson controlling din kanshi don jiyake kamar ya shimfidar dashi yaita naushinshi a fuska

"Please.."

Wani wawan bangaza Ashraf yayi mashi Wanda har saida yakai qasa sannan yasake damkar hannun saudart, fuuu sai hanyar gidansu.



Halbi daya yayi ma kofar ta bude yashiga yana tura saudart ciki Wanda batayi masauki a koina ba sai kan kujera.

Dagowa tayi tana kallonshi da idanunta dasuka fara chanza kala taga shima kallonta yake da rinnannun idanunshi.

"Waye shi?" Ya tambaya yana huci

Bata amsaba kuma bata bar kallonshi ba.

"Nace who the hell is he?!" Yafada cikin qaraji har jijjiyoyin wuyanshi na bayyana.

Gyara zamanta tayi batareda tace komai ba zuciyarta na suya, tashi tayi tana gyara squeezing din rigarta sannan tanufi hanyar dakinta

Shan gabanta yayi cikin quluwa

"Magana nake maki!" Ya daka mata tsawa

Watsamashi jajjayen idanunta tayi Wanda ke qoqarin Tara ruwa tace

"Give way"

"nace meye hadinki dashi?! Eh! Kin wani taho kina yaqe mashi baki kan hanya, abinda yakawoki nan kenan? No modesty no class, yazo yana maki magana..boom sai washe baki, wayasan what will come next? Are you that desperate?" Yafada cikin hayyayakowa

"And don't forget it's me! My life! Ina ruwanka! The last time I checked babu wata alaqa a tsakaninmu, I owe you no explanation, it's none of your damn business ko me kaga munayi! Ko hugging dinshi kaga nayi banga abinda yashafeka ba" tafada cikin tsawa itama

Damkar hannunta yasakeyi da qarfi don jitayi kamar zai qille dan hannun.

"Ni kike fadawa haka?"

Kiciniyar kwace hannunta take hawayen datake qoqarin 6oyewa na gangarowa

"Ka cikani you dirty pig!" Tafada cikin cracked voice

"Nace ni kike cewa you can hug him!" Yafada still damke da hannunshi, shi kanshi yasan what he's doing was wrong, amma yarasa dalilin dayasa yakasa controlling din kanshi, wani Abu mai zafi ke tasomashi daga qasan zuciya har zuwa maqoshi.

"Leave me alone!" Tafada tana daga dayan free hannun da niyyar marinshi amma ya damqeshi shima ya hada ta wancan ya riqe.

Fashewa tayi da kuka tana kiciniyar kwacewa don jitake kamar qarwashin wuta ke riqe hannun.

Jingina ta da bango yayi still riqeda hannayenta da hannunshi guda dayan kuma ya dago fuskarta data jiqe sharkaf da hawaye yace

"Don't.. Ever..let me see.. You with that.. Guy..again" yafada yana nishi sama sama kaman Wanda yayi wasan tsere.

Qalato yawu tayi a bakinta ta tofamashi yayi saurin kauda fuska

"I hate you! Damn you!" Tafada cikin kuka sosai

Tsayawa yayi yana kallon yadda take kukan jikinta har rawa yake in the process.

Sai yanzu yake wondering why yake behaving like this? Meye nashi don yaganta da wani? Ina ruwanshi?

Tsayawa yayi yana kallon yadda hawayen ta ke gangarowa, duk ga gangara daya jinshi yake kamar gangarar darma acikin zuciyarshi.

"I..hate..you...with passion" tafada cikin rawar muryar kuka.

Sosai Kalmar ta dakeshi, wannan shine karo na biyu data ta6a furta mashi Kalmar qi. Amma wannan Karon Kalmar tafi dukanshi bisa na farko.

Sakin hannayenta yayi yana kallonta.

Sulalewa tayi ta zauna qasa sannan ta cusa kanta tsakiyar kaffafunta tana cigaba da kuka.

Ahankali ya dinga ja baya still idanunshi akanta harya isa bakin kofarshi sannan yajuya ya budeta yashiga yarufo.

Jingina yayi da kofar yana sauraron siririyar sautin kukanta.

Hannu yasa cikin gashinshi yana dan harmutsawa, yarasa abinda yazo kanshi, he's too harsh on her, yarasa dalilin daukar zafin dayayi nan take.

Abinda yaguda kenan shiyasa tunda amir yafara gayamashi yana Sonta dazu yayi saurin bar mashi wajen don jiyayi yana Neman kasa controlling din kanshi.

Amma sai me? Sai ganinta yayi tareda shi suna fira harda dariya, be iya misalta abinda yaji a lokacin don baya misaltuwa, jiyayi kamar yayi diving wuqa acikin mutumin.

Shiru yayi yana sauraron sautin kukanta daya fara raguwa Wanda yakejin kamar ana digamashi darma ne a zuciya.

Jin be iya cigaba da sauraronta yasashi shigewa toilet yaje bakin sink ya bude tap din yana dauraye hannunshi

"I hate you!" Maganar ta ta dawo mashi.

Yasani tun ba yau ba cewa ta tsaneshi amma furtawan datayi dakuma yanayin data furta yau yasashi sanin ba qaramin tsana tayimashi ba Wanda kuma hakan ba qaramin karta mashi zuciya yakeba.

"Ya rabb, take control" yafada yana kallon kanshi ta madubin toilet din.




Itakau saida tasha kukanta ta qoshi sannan ta lalla6a tashige dakinta a daddafe ta kwanta sannan ta Dora daga inda ta tsaya, tunda take bata ta6a tsanar hallita kamar yadda ta tsani A.A ba kuma batajin zata iya tsanar wani kamar yadda ta tsaneshi.


Ataqaice dai dukansu biyun kai harma da amir yadda sukaga rana haka sukaga dare don babu Wanda tunani yabari yayi barci.








Washegari bayan sallar asuba Ashraf nakan hanyar shi ta dawowa gida yaji ana mashi sallama ta baya.

Ko be juyaba yasan amir ne, da farko kamar yayi banza dashi saikuma ya tsaya ya juya yana amsa sallamarshi fuska tamke.


Ganin yadda ya tamke fuska yasa amir miqamashi hannu suka gaisa cikin dar dar


"Bro please kayi hqr, nayima Sistern ka magana batareda izininka ba"


"It ok" inji Ashraf yana shirin wucewa

Saurin binshi yayi yana cewa
"Am so sorry bro, wlh tsakani da Allah nakeson sis dinka, please kabani dama please" yafada yana marairaicewa.

Wani zafi yaji zuciyarshi nayi mashi kamar dai jiya, dakyar yayi controlling din kanshi yace

"Ba sister ta bace... She's my *wife*"

Cak amir yayi suman tsaye idanunshi a ware

Shikau Ashraf be qara kallonshi ba yayi gaba zuciyarshi na suya.

Binshi amir yayi da kallo baki bude cikin tsananin mammaki da kunya

"Oh no! Matarshi? What have I done? Innalilahi"

Ya Dade nan tsaye cikin jimami sannan can da tsayuwar ta isheshi ya nufi gida jiki a sa6ule.





***********************************


Ahaka Saturday da Sunday tawuce babu Wanda yaqara saka dan uwanshi a idanu.


Wasan 6uya sukeyi tsakaninsu don basu yarda su hadu.


Ranar Monday ma saboda meeting din dazasu yasasu haduwa.

Meeting din marece ne don haka sai large hudu da Rabi suka bar gidan.

Kamar koda yaushe yauma motar tsit take babu mai ko motsin kirki.

Sanye take da Riga da skirt na material ta Dora baqar after dress akai tayi rolling din gyalen after dress din.

Kafafuwanta sanye da flat shoes masu igiyoyi, hannunta riqeda baqar purse.

Shikau sanye yake da baqar suit mai light blue din shirr daga ciki, necktie dinshi ma blue sai takalmi cover shoes baqaqe.


A harabar company din suka yi parking sannan suka fito.


Ashraf yayi gaba hannunshi riqeda briefcase Itakuma ta Mara mashi baya.


********************************


Alhamdullilah komai yatafi daidai sun biya Rabin kudin kuma sunyi signing dukansu harda shaidu sannan kowa Nada copy din takardar saboda tsaro.

Saida suka danyi fira sannan suka tashi suka tafi.

A wani corridor da beda nisa da office din dasukayi meeting din igiyar takalmin saudart ya warware.

Tsayawa tayi ta ajiye purse dinta kan wani tudunka ta duqa tafara maida daurin.

Jin kamar ba'a biyoshi yasashi tsayawa ya waigo.

Saurin daure takalmin tayi ganin ya zubamata wannan mayattatun idanun nashi sannan ta tashi ta taho suka wuce. Rabonda magana ta hadasu tun ranar juma'a daddare dinnan.

Haka suka jera har suka isa motar, harta kama handle din motar zata bude saita tuna da purse dinta.

Dan laluba jikinta tayi taji batanan sannan tajuya tana waige waige.

Ya lura da ita hakan yasashi tsayawa kallonta,

Dagowa itama tayi ta kalleshi taga ita yake kallo saita dauke kai.

"What?" Ya tambaya ahankali abinda be ta6a yiba kenan


"My purse" ta amsa qasa qasa

"Ok go get it" yafada yana shiga motar.

Babu musu ta juya don komawa daukowa tana mammakin yadda yake magana cikin sanyi kamar bashi ba.

Ta6e baki tayi tana tsaki don hakan bazai chanza tsanar datake mashi ba.

Shima binta yayi da kallo harta shige sannan ya sauke wata nannauyan ajiyar zuciya.

Hannu yasa yana shafa kanshi daga gaba zuwa baya yana tunanin abinda ke damunshi kwana biyu, haryanzu beson gasgata abinda yakeji game daita amma it look real.

Yakusan mintuna goma yana jiranta harya fara qosawa saigata.

Da ada ne da yanzu ya dau zafi amma sai tsintar kanshi yayi da kasa yimata magana.

Shiga tayi ta rufo kofar ta jingina da kujerar batareda tace komaiba.

Shima bece komai ba ya tada motar suka fice.

Saida suka fara tafiya sannan yajuyo ya kalleta yaga jingine da kujera take ta lumshe idanu kamar meyin barci

"Jibi zamu koma 9ja" yafada kamar Wanda akayi wa dole

"Ok" itama ta fada qasa qasa.

Daga haka babu Wanda yasake cewa komai har suka Kai gida...✍



Ummin fasihu ce

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





051





Washegari da hantsi tafito daga gidan sanye cikin doguwar hijabi har qasa don ba'a ma hango kayan datasa aciki.

Qarfe sha biyun rana ne amma sai kayi tunanin bakwai din safe ne saboda lullumi dakuma buji.

Direct block *37* tanufa ta kwankwasa kofar gidan.


Shiru taji hakan yasata sake bubbugawa.

"Yes!" Taji anfada daga ciki saikuma taji taku na tunkaro kofar.

Budewa akayi Reyna ta bayyana.

Waro idanu tayi kamar Wanda tayi gamo tana rufe bakinta da tafin hannu.

Harara saudart ta gallamata tana cewa
"To nashigo ne ko naqara gaba?"

Saurin Kamo hannunta Reyna tayi tana cewa
"Oh saudart! Ki shigo, am soo sorry, wlh tun washegari naso nazo amma tsoron shi nake, ina tsoron naje na taddashi ko ya taddani gidan, we're soo sorry!" Tafada tana jawota cikin dakin cikin kulawa.

"Mtcheew, wannan sorry din duk na menene to?" Inji saudart tana kwace hannunta ta nemi kujera ta zauna


Dawowa Reyna tayi kusada ita ta zauna tana cewa
"Wlh tun ranar muka shiga tashin hankali musanmman Amir, gani muke dukanki zaiyi, babu yadda beyi daniba nazo gidanku kona gayamashi block dinku amma tsoro ya hanani don gani nake a yanayinshi dinnan yana iya hadawa damu ya make, am so sorry, hope beyimiki komai ba?" Tafada tana dafa kafadarta.

Tsaki tasake ja tace "ni babu abinda yayimin dalla, ni Abu daban yakawoni kinzo kin isheni da surutu" inji saudart don kwata kwata batason ayi maganar

"Ayyah ai dole na damu ai, haryanzu amir bebar damuna ba, wai inbaki hqr besan ke Matar aure bace"

Dagowa tayi da sauri ta kalleta
"Waya fada miki ni Matar aurece?" Ta tambaya a mammakince

"Amir mana, sun hade da mijin naki yana bashi hqr anan ya fadamashi, ai wlh yanada gaskiya dole ne yayi kishi, imagine wata tazo tace maki tana sonshi kuma the next minute ki gansu tare dole kiji haushi" inji Reyna

Banza saudart tayi ta kyaleta don ita har mancewa take dawani aure dake kanta, jinta take soo free kamar ba Matar aureba.

Ganin zata sake magana tayi saurin katse ta da

"Look Reyna komai yawuce, ninan Abu daban yakawoni, idan kuma bazaki saurareni ba fine"

Saurin riqo hannunta Reyna tayi ganin zata tashi tana cewa
"Ok ok ina jinki, am sorry"

Saida ta murguda mata baki cikin wasa sannan tace
"Gobe zamu koma Nigeria"

Dafe qirji Reyna tayi da sauri kamar Wanda akayima mugun Abu.

"What? Please wasa kike? Nasan wasa kike ko?" Inji Reyna unbelieving

"Hmm wlh dagaske nake, meye abun wasa aciki?"

"Oh My good Lord saudart, akan wannan Abun zaku tafi? Please karku tafi zan kira amir yazo har gida yabaku hqr"

Tsaki saudart taja cikin takaici
"Look nifa nagayamiki nama manta da wannan babin, dama Abu yakawomu kuma mungama shiyasa zamu tafi" tafada tana kallon yadda duk Reyna tabi ta susuce

"No, nasan duk saboda abinda yafaru ne, please don't leave, wlh besan ke Matar aure bace" tafada cikin marairaicewa.

Tsaki saudart taja ta miqe tana cewa
"Bari kiga intafi tunda bakida ganewa"

Saurin shan gabanta Reyna tayi tana cewa
"Ok ki rantse please, ki rantse ba saboda hakan zaku bar nan ba"

Tsaki saudart taja tace
"Wai nata6a yimiki qarya ne?"

"Nidai please ki rantse"

"To na rantse, mungama abinda yakawomu shiyasa zamu tafi, ke ke tunawa da abinda yafaru ni harna manta, yanzu haka zuwa nayi naji babu inda zaki anjima Ku rakani shopping ke da Loveth?"

Sai a sannan hankalin Reyna ya kwanta har wani sauke ajiyar zuciya tayi

"Better, nazaci sbd haka zaku tafi and maganar shopping? It's capital YES! ko da inda zani bazan bari wannan damar kasancewa dake na qarshe ta su6ucemin ba, waya sani ko bazamu sake ganin junaba?" Tafada tana langwa6a kai gefe

"Insha Allah zamu sake hadewa ok? Koba yanzu ba" tafada itama tana langa6e kai

"I'll miss you" tafada tana rungumeta

"I'll miss you much" inji saudart tana murmushi

Ganin batada niyyar sakinta yasata yimata chakulkuli Wanda hakan yasata saurin sakinta suna dariya tare

"Ok now tafiyar nanan? Loveth zata samu zuwa?"

"Yes, yaushe zamu?"

"4:00pm dot zanzo nan, idan Baku shiryaba zan tafiya ta" tafada cikin kashedi

"Yes ma'am" inji Reyna tana sarawa sukayi dariya gabadaya sannan suka fito tare tayi mata rakiya harta kusan kaiwa gida sannan ta koma





*****************************************


*4:33pm*

"Mtcheew zanyi tafiya ta fa!" Inji saudart dake kofar gidansu Loveth fuskarnan a hade.

Reyna dake gefenta sanye da wando da shirt sai purple jacket ita gwiwa akai gashinta awaje ta kama hannun saudart tana cewa

"Kinga zomu tafi, she's not serious"

Saudart sanye take cikin lace jaa Riga da zani ta yafa gyale baqi stylishly, kallo daya zakamata kasan cikkakiyar bahausa ce.

"Mtcheew mutafi" inji saudart din tana bin Reyna.

Dagudu Loveth tafito daga cikin gidan takalmi a hannu tana cewa

"Kujirani please!"

Saida ta iso motar sannan ta ajiye takalmin tasaka tana numfarfashi wai don tayi Gudu.

Sanye take cikin baqar English gown mai tsaga a baya kanta kuma daukeda hula fara sai qatuwar handbag hannunta.

Haka suka shiga motar Reyna din sunama juna tsiya.

Reyna ce ta zauna mazaunin driver sai saudart gefenta sai Loveth abaya, haka suka tada motar suka bar wajen suka kama hanyar fita daga estate din.







Babu laifi sunyi spending din good time at are, shopping sukayi kamar babu gobe, duk abinda tagani ya burgeta saita dauka.

Haka suka jero suna shopping suna fira da dariya gwanin sha'awa, saida suka gama kaff sannan fa aka bude babin selfie, wai hotunan tarihi.

Sunyi hotuna harna hauka, daga qarshe rasa style din dazasuyi sukayi sai sukaita style din hauka suna dariya, it's a happy moment for them don jisuke kamar karsu dawo gida.


Ataqaice dai sai gab magrib suka baro supermarket din.

Nan suka sako duk kayan dasuka siya a mota suka shiga.

Wannan karon saudart ce ta tuqosu, suna tafe suna tsokanar juna suna dariya.

Koda suka iso gida har angama sallar magrib.

Kofar gidansu saudart suka yada zango don duk tafisu kaya, saida tagama sauke kayanta kaff sannan sukayi sallama akan saisun zo bankwana gobe idan ransu yakai.

Haka ta cicci6i kayan Niki Niki tashiga gidan.




A falo ta ganshi zaune yana danne danne a laptop, kallo daya tamashi ta kauda Kai tawuce shi kayan na rinjayarta.

Binta da kallo yayi harta kai bakin kofarta ta ajiyesu ta bude kofar sannan ta kuma kwasa tayi ciki tarufo kofar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi ahankali sannan ya cigaba da abinda yake.






*********************************

Washegari tunda ta tashi da asuba takasa komawa, dama jiya ba wani barcin kirki tayiba, jitake kamar tajawo lokacin don lokacin be wani yimata Gudu.

Flight din 10:00am garesu amma tun 7:00am take falo zauna sai gyara zama take agogo kau ta dubashi yafi a qilga.


9:00am sai jitayi ana knocking a kofar falon.

Saurin tashi tayi taje ta bude, ihu tasaki ganin Loveth da Reyna ta qanqame su cikin murna

"Hmm muda ba'a ganmu ba saimu juya" inji wata dake baya.

Sai a sannan saudart ta ankare dasu taga sunada yawa ma harda Dr zahra.

Saurin sakinsu tayi tana yi musu iso ciki fuska washe.

Nan suka shigo suka zauna taje ta kawo musu ruwan sha sai washe baki take.

"Hmm sai murna ake za'a gida kamar irin can yafi nan dinnan" inji wata cikinsu

Kamar jira ake nan falo ya kaure da cafta kowa na fadin albarkacin bakinshi itakau Dr sai dariya take musu.


Jin hayaniya a falo yasashi cikin mammaki sosai, to gidan dai babu kayan kallo bare yace kallo aka kunna kuma ma wannan beyi kamada kallo ba yafi jin hayaniyar a zahiri.

Saurin kammala shirin yayi yana duba agogonshi don har Tara da Rabi.


Turus yayi daya fito yaga gugun mutane zaune a falo saudart tsakiyar su suna dariya.

Ganinshi yasasu natsuwa suna gaidashi.

Qarasowa yayi yana amsawa yana kuma gaida Dr.

"Sai Nigeria ko?" Inji Dr zahra cikin tsokana.

Dariya kawai yayi yana shafa kanshi

"To Allah ya tsare, wish you safe journey, Ku gaishe da mutanen Nigeria, insha Allah zanzo watarana har gidanku, tunda duk munyi exchanging din number" tafada cikin fara'a

"To Allah yasa" inji Ashraf yana satar kallon saudart daketa murmushi.

Farincikin datake aciki afili yake baya 6oyuwa.
At last zasu koma qasarsu.


Fitowa sukayi tareda gungun mutanen sai tsokanarta suke tana biyemasu, har mota suka rakata harda budemata kofa tashiga.

Sai kuma a sannan suka fara marairaicewa wai zasuyi missing juna.

Haka dai suka rabu zuciya babu dadi sai dagawa juna hannu suke har suka bar hangen juna.

Komawa tayi ta jingina da kujerar tana sauke ajiyar zuciya tana murmushi.

Shima dayake satar kallonta tundazu murmushin yasaki ya kauda Kai yana mammakin saurin sabo irin nata, ji yadda mutane sukazo rakiyarsu kamar sunyi shekaru a qasar.


Haka motar tayi tsit har suka qarasa airport din.

Suna fitowa daga motar tafara bin airport din da kallo, kamar jiya ne suka shigo airport dinnan da niyyar shigowa qasar amma wai yau sune aciki da niyyar barin qasar zuwa qasarsu.

"Can't wait" tafada cikin zuciyarta tana murmushi

Saida aka gama komai sannan suka shiga jirgin.

Kamar wancan karon kusada juna suka zauna.

10:00am dot aka fara sannarwa na kowa ya daura belt dinshi.

Wannan karon ba'ayi qauyanci ba nan da nan ta daura.

Jin ana sanarwa na jirgi zai tashi yasa ta koma ta lafe a kujera murmushi a fuskarta.

Jin yafara tafiya yasa bugun zuciyarta qaruwa, jin

Please Login or Register in order to submit comment