Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi ta zauna tana bada dan tazara a tsakaninsu sannan ta gaidashi ahankali.

Ansawa yayi yana kallonta kamar zai hadiyeta don sosai tayimashi kyau kuma daya tuna cewa jibi warhaka tana gidanshi sai yaji ranshi yaqarayin fess.

Habeeb yazo tafiya don ba laifi yana hankali sosai ashraf ya riqo hannunshi yana cewa ina zashi?

Murmushi yayi yace ciki ashraf yace A'a su tsaya ai basu gama firarba don yasan kosun tafi bawani hira zasuyiba da saudart saidai suyita zaman kuramen dasuka saba don koyayi niyyar janta da fira bata bashi hadin kai sai taita amsamashi a taqaice ko tamayi shiru.

Haka sukaita firarsu tana jinsu ko dagowa batayiba shikau ashraf suna fira yana kallonta qasa qasa don sosai take qara chanza mashi gawani kyau datake qarawa kullum.

Haka akayi firar ranar tsakaninshi dasu habeeb while saudart tun maganarsu tafarko ko tari bata qaraba burinta kawai yatafi don atakure take sosai.

Saida akafara kiraye kirayen isha'i sannan yatashi da nufin tafiya.

Sallama sukayi sama sama tajuya tashige ciki kamar dama akan qaya take, binta yayi da kallo har saida ta shige sannan ya girgiza kai yana dan murmushi ya tafi dasu habeeb wajen motarshi yaciro kayan daya siyomusu suka amsa suna godiya sannan yashiga motarshi ya tadda yafita suna dagamashi hannu.


Tuqi yake amma sai sakin murmushi yake from time to time.

Jiyake babu wanda yakaishi farinciki yau aduniya, he can't wait jibi tayi yaxo yatafi da abinshi.


Da daddare bayan kowa ya kwanta Abba ke sanar daita yadda sukayi da Ashraf.

Sosai taji dadi don har saida hakan ya bayyana sosai a fuskarta.

Dariya abba yayi yace
"Dole ai kiyi murna tunda wanda ta tsaremiki wuri zata tafi, ai ina lura daku kwanan nan bakida abun hantara kamar ita"

Murmushi mamy tayi tace
"Wlh ba haka bane, saudart din ce sai ahankali gashi banajin dadin ganunta tana zaune haka da aure kanta"

"Ai hakan shine daidai don yanzu shi kanshi ashraf din bazai wahala ba kamar yadda zaiyi da tun farkon faruwar abun takoma, yanzu nasan zuciyarta tayi sanyi sosai kuma bazai sha wahala wajen shawo kanta ba don naga alamun ke tabiyo wajen taurin kai, kinga da ana gaba abin takoma ba qaramin wahala zaishaba wajenta amma kinga yanzu lokacin yadanja kuma yana yawan zuwa suna ganawa so sai inga yanzu it will be more easier for him"

"To allah yasa alhaji, kuma wlh kunyi dubara don saudart halinta sai ita idan ta nacewa abu ta nacemashi kenan, allah ya basu zaman lfy yakuma hada kansu"

Amsawa abba yayi da amin cikin jindadi da qaunar matar tashi dayakejinta daya tamkar dubu...✍

Sorry for jina shiru kwana 2.

Kusamu a addu'a anyi kidnapping din wani brother namu😭

Allah ya ku6uto dasu cikin qoshin lfy🤲


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[9/12, 5:42 PM] Aeesha umar aliyu: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)



088



Yana komawa gida yafadawa ummy yadda sukayi da abba cikin farinciki.

Itama ummy tayi farinciki sosai nan ta shiga yimashi fada da nasihohi masu matuqar amfani, bashi yakoma dakinshiba har sai wajajen shadayan dare.

Shima barcin qin daukarshi yayi dawuri haka yaita juyi yana ta saqe saqe har barcin ya sadado ya daukeshi.

Washegari tunda yatashi yashiga busy, be nan be can kamar jigida.

Shirye shirye yake sosai na tarar saudart wanda bemayi wannan doqin ba lokacin daurin aurensu, shi sai yanzu yake jin irin doqin nan na angwaye, jiyake kamar yajawo ranar taxo don beda burin daya wuce ace gashi ga saudart a muhalli daya amatsayin tashi halak malak.

Itakau saudart batasan wainar da ake toyawaba don babu wanda yace mata komai.

Ranar mamy da kanta tacemata ta shirya ta rakata unguwa.

Dadi taji sosai don tunda taxo gidan sau daya ta ta6a fita wanda tayi da A.A, sosai take cikin kewa da kadaici musanmman idansu habeeb basanan gashi batason tambayar fita wajen mamy don tasan tana iya sawa kuma ta gayawa ashraf.

Da harta ma fara shawarar komawa gidan daddy ganin batajin dadin zaman nan sosai amma kwata kwata mamy taqima bata fuska bare tayi yunqurin tunkararta da zancen.

Cikeda doqi ta shirya cikin wata milk colour roll silk gown mai adon flowers brown ta sanya brown madaidaiciyar hijabi dayai mugun mata kyau ta dan yi simple makeup sannan tafesa cool turarenta.

Koda tafito itama mamy tafito ashirye itama don haka batareda 6ata lokaci ba suka garzaya parking space saudart tashiga mazaunin driver kasancewar ita zata tuqasu itakuma mamy tazauna dayan gefen suka fice daga gidan.

Sosai saudart taji dadin fitarsu ta yau don yawo sukayi sosai gashi mamy is so free today babu fadan nan nata haka sukaita labari gwanin sha'awa.

Saloon suka fara biyawa aka wankemasu kai aka kitsesu, sosai shukku din saudart yayi kyau yazubo har wuyanta gasu qananu ne sosai.

Bayan haka aka mata qunshi mai shegen kyau na baqi da jaa kamar ba hannu ya zanaba.

Bayan haka suka biya supermarket sukayi shopping kala kala don ranar saida saudart ta jidi duk abinda take buqata bata samu damar fita siye ba.

Itadai mamy batace mata komaiba itama tashiga daukar mata english wears na nightie masu kyan gaske.

Haka suka gama shopping din suka fito sannan direct suka yi gidan wata qawar mamy.

Sundan dade gidan sannan suka taho bayan ta amshi turarrukan wuta dana jiki da su humra data bada sautun akawomata sannan suka baro gidan sukayo gida.

Koda suka dawo mamy bata zaunaba tayi kitchen ta hada mata wani shegen farfesun kayan ciki dasuka ji kayan hade hade kala kala da kunun aya dayaji madara da kwakwa sosai ta kawomata ta tisata gaba ta shanyesu tass.

Sannan ta hada mata kujerar garwashi yazuba turare aciki tasata tsugunno akai.

Itadai saudart yin abinda mamy tasata kawai take tana wondering meke faruwa, dukda tunda tazo gidan takemata wannan abin amma na yanzu yafi nada. Sharewa tayi kawai ta shashantar da zancen don gani tayi it doesn't worth 6ata lokaci wajen tunani akanshi.

Washegari tinda su abdul suka tafi makaranta takoma daki ta kwanta tana hutawa kafin lokacin girkin rana yayi.

Tana tsaka da waya da P.A dinta na bakery mamy tashigo dakin da sallama.

Murmushi tayima mamyn sannan tayima maryam din sallama akan zata kirata later.

Dagowa tayi ta kalli mamy da itama ita tazuba ma idanu tana kallo.

Murmushi tayi tace "mamy na?"

Ajiyar zuciya mamy tayi sannan ta qaraso ta zauna gefenta tana kallon yadda cikin yan kwanakin nan taqara wani kyau da cika.

"Angel?" Inji mamy cikin tattausar murya

Kallonta saudart keyi cikin jin dadin sunan data kirata wanda rabon da takirata dashi hartama manta.

"na'am sweet mamy na" tafada tana kwantowa kafadar mamyn a shagwa6e.

Hannu mamy tasa tana shafamata kanta dayaji qananun kitso sai daukar ido suke tafara cewa
"Saudart a rayuwa idan ba'a yafewa akuma mance komai baza'a ta6a samun cigaba ba.
Shikanshi ubangiji muna mashi laifi da saninmu, da gangan mudawo mu nemi yafiyarshi kuma ya yafemana mu su waye da baxamu yafema wanda sukayimana laifi ba?

Saudart nobody is above mistake, idan mutum yayi maka abu bisa kuskure kuma daga baya yagane kuskurenshi yadawo yatuba, bashi wata damar ake domin gyara kuskuren dayayi afarko bawai a qullaceshi aqi sauraronshi wanda hakan na iya sawa yakoma yasake tafka wani kuskuren makamancin wannan ko wanda ma yafi wannan.

Saudart Ashraf mijinki ne no matter what, aljannarki na qarqashin kafarshi, karki bari wani dalili naki na banza yarufemaki ido kikasa neman aljannarki.

Ina lura da yadda yake binki kina shareshi saudart, why? Koni dakika yiwa laifi na dauki lokaci mai tsawo ina fushi dake? Keda kikayi dagangan bare shi dayayi bisa mistake? Wlh kizo kiyi karatun ta nutsu, aji idan aka jashi dayawa tsinkewa yake, idan yacigaba da binki kina mashi wulaqanci gajiya zaiyi, dole wata rana ya gaji ya kyaleki, ya fita harkarki.
Bare shi namiji ne mijin mace hudu yana iya kyaleki ya auro wata wanda tasan qimarshi da darajarshi, shikenan idan mai wayauce saita janyeshi kwata kwata kizama borar gidan kuma koda kin dawo daga baya kina mashi biyyaya bazaki wani burgeshi ba don lokacin dayakeso bakiyi mishiba.

Ina fadamiki hakane amatsayina na uwarki, bari ganin ina matsamaki ne ko wani abu, A'a iyakar gaskiya kenan da duk mai qaunarki zai gayamiki.

Kiyi haquri komai yawuce aranki ki ajiye wannan shegen riqon naki ki fuskanci me kike ciki, duniyarnan inbakayi kau ban wuri ake, ga yan mata can bila adadin suna neman slight opportunity dazasu qwacema sakarai miji, da kinyi sanya saidai ki shafa kiji babushi, bare ke mai irin wannan mijin daya hada komai da yanmata ke buri, to wlh ki nutsu kisan abinda kike.

Bakuma cewa nayi baxai miki kishiya ba, A'a namiji nada damar zama da mace fiyeda daya muddin zai iyayin adalci atsakaninsu, saidai inason ya kasance koma auren zai qaromiki ya kasance kema danaki power ku goga atsakaninku.

Dan haka ki ajiye komai ki fuskanci rayuwa, idan kina ganin ashraf da laifi to babanki yafishi kuma tunda kika iya yafewa baban naki shima yakamata kiyafemashi komai yawuce hakanan, Allah yamiki albarka kinji 'yata mai biyayya? Yabaku zaman lafiya ya albarkaceku da zuri'a dayyiba"

Amin saudart da duk jikinta yayi laushi tace tana qara narkewa a kafadar mamy don sosai magangganun mamy suka shigeta.

"Yanzu tashi kifara packing din abubuwan dazaki buqata anjima dadaddare insha allah mijinki zaizo yatafi dake" inji mamy

Dumm gabanta yafadi sosai bashiri ta daga kanta daga kafadarta tana kallonta in a shock state.

"M...mene?" Tafada cikin shock

Hade rai mamy tayi tace
"I said anjima zaki koma gidanki so start preparing"

"M..mamy but it's too...too" saikuma tayi shiru takasa qarasa maganar

"It's too me?" Inji mamy tana harararta

Shiru tayi kawai gabanta na faduwa sosai don bata ta6a kawowa nan kusa zata komaba don ita har mantawa ma take cewa wai zata koma gidanshi.

Mamy ma kallonta take ganin yadda hawaye ke taruwa a idanunta tayi wani rau rau dasu.

Girgiza kanta tayi cikin takaici tace
"What are those tears for?" Inji mamy tana kallonta

Sauke idanunta tayi ahankali wanda hakan yaba hawayenta damar saukowa.

"Mtcheew, i don't have your time, yanxu kiyi yadda nace don kizama cikin shiri dayazo kutafi, ke da atunaninki nan zakiyita zama? Bakida aikin yi" tana kaiwa nan tafice daga dakin tabarta nan zaune tana matsar kwalla.

Hada kanta da gwiwa tayi tana hawayen sosai, ita yanzu wane irin zama zasu sakeyi da wannan mutumin? Tayaya zata iya zaman aure da wanda bataso, wane irin rayuwa zasuyi wannan karon?.

Wunin ranan haka tayishi sukuku zuciyarta cikeda damuwa da fargaba tama kasa tashi ta hada kayyayakinta da mamy tace.


Da ranama kasa cin abincin kirki tayi sai tsakura da tadanyi don jitayi batada appetite kwata kwata.

Mamy na ankare daita amma taqi tanka mata, daga qarshe ma ita taje ta harhadamata kayyayakin nata tareda sayyayar datayimata jiya na turarruka tayi packaging din komai da kyau.

Su abdul dasukaga saudart ta chanza sosai suka shiga tambayar mamy meyasameta don ko kulasu saudart batayiba.

Nan mamy tafadamasu komawa zatayi yau, sosai suma jikinsu yayi sanyi don sun saba daita sosai basu qaunar abinda zai rabasu.


Tana zaune bisa sallaya bayan tagama sallar magrib mamy tashigo dakin.

Riqe kugu daya mamy tayi tana kallonta cikeda takaici.

Dagowa tayi asanyaye ta kalli mamy dake binta da mugun kallo.

Sunkuyar da kanta tayi tana matsar kwalla ganin kallon da mamyn ke binta dashi.

Tsaki mamy taja kafin tace
"Wai saudart ke yarinyace koko? Ko ga aurenki bakiyi wannan sakarcinba sai yanxu? Cemiki fa nayi kiyi wanka kishirya this is to 8 ko ahaka zaki?" Ta tambayeta cikeda takaici

Shiru saudart tayi batace komaiba

"Wai bada ke nakeba?"

Fashewa tayi da kukan dake cinta tundazu ta kifa kai da gwiwa tana raira kukan ahankali.

Sakin baki mamy tayi tana kallonta na wani lokaci kafin tace
"Wai saudart lafiyarki lau kuwa?"

Cikin kuka mai cikeda shagwa6a tace
"Ni shikenan mamy baki sona, bakison ganina, sai korata kike don baki sona, you're eager intafi inbarmiki gidan don bakisona" taqarashe maganar tana sake rushewa da wani kukan

Riqe ha6a mamy tayi tana kallon yadda take kukan bilhaqqi, murmushi tayi sannan ta qaraso ciki ta zauna gefen gado ta jawo kan saudart ta dora a cinyarta sannan cikin lallami tace
"Haba anmata na? Ni na iya ince bansonki? Kefa kadaice baby girl dina, abin alfaharina. Ni ba koranki nakeba, kema kinsan darajar ya mace shine dakinta na aure, amma ba koranki nake ba, kema kinsan it's not proper kiyita zama nan da aure akanki ko?" Ta fada tana shafa kanta.

Turo baki saudart tayi tace
"Amma mamy meyasa baki fadamin tunfarko ba, it's too sudden"

"Ok mamy tayi laifi, kuma tana neman afuwa, forgiven?" Tafada tana leqa fuskarta.

Kauda kai tayi tana tura baki.

Murmushi mamy tayi mai sauti tana cewa
"Allah ya shiryaminke, yanzu tashi kishiga wanka saiki fito da alwala kiyi isha'i sannan ki shirya, kinji yar maminta?"

Kada kai tayi ahankali bakinta a so6are sannan ta tashi tacire hijab din jikinta ta fiddo towel tawuce bathroom.

Girgiza kai mamy tayi tana murmushi sannan ta tashi tafita daga dakin itama don zuwa gabatarda isha'i.

Bayan tagama takoma dakin ta isketa itama gamawarta kenan.

Wucewa tayi sip dinta ta ciromata wata dakkakiyar pupple shadda dinkin doguwar riga mai wrapper 'o' shape taji paint work tareda farin gyale mai stones ajiki.

Ita dakanta ta shiryata tana yi tana fadamata kalamai masu kwantar da hankali cikin tattausan murya wanda hakan ya kwantar da hankalinta sosai.

Tana cikin dauramata dankwalin kayan phone dinta yayi ringing.

Dagawa tayi ganin abba ne, nan yake gayamata ta taho da saudart falonshi ga ashraf dinma nan yazo, da to ta amsa sannan ta katse kiran.

Bata cewa saudart komaiba ta ida dauramata dan kwalin tayimata simple cool makeup sannan ta fesheta da turare mai shegen qamshi mai dadi sannan ta doramata gyalenta saman kai ta ajiyemata fararren takalminta saitin kaffafunta.

Tashi saudart tayi asanyaye ta zira takalmin ta dauki purse dinta dake kan mirrorn sannan tabi bayan mamy data kama hannunta.


Zaune ashraf yake kan centre carpet ya tankwashe kaffafunshi kanshi dayasha baqar hular dara akasa.

Sanye yake da dakakkiyar farar shadda dataji aikin boda kalar baqi, wrist dinshi sanyeda agogon rolex kaffafunshi sanyeda baqaqqen safa sai tashin qamshi yake.

Sallamarsu ce ta katsesu suka dan dago suna amsa sallama.

Tare suka shigo saudart kanta aqasa tayi wani mugun kyau cikin shigarta sai zuba qamshi take.

Tuna suka shigo qamshinta ya dabaibaye mashi hanci, alokacin babu abinda yakeso alokacin kamar ya dago ya kalleta amma kunya ta hanashi saima qara duqe kan dayayi don sosai yake kunyar mamy.

Jin motsi yayi kusadashi yadan saci kallon gefenshi ta qasa yaga itace ta zauna dan nesa dashi, kallo yabi hannunta dayasha henna baqi da ja data dora kan cinyarta kamar yakamo hannun don sosai qunshin yatafi dashi.

Jin mamy namashi magana yasashi saurin janye idanun daga hannun nata yashiga gaisheta cikin girmamawa.

Amsawa tayi tana tambayarshi ya mutan gida ya amsa da duk suna lafy.

Gyaran murya abba yayi yafara masu nasiha mai ratsa jiki gameda zaman aure da haquri dajuna.

Sosai nasihar tashigesu don har saida saudart ta zubda kwalla.

Yana gamawa mamy ma tadora da nata sannan sukasamusu albarka da addu'o'i sosai.

Bayan haka abba ya umarci ashraf yatashi yatafi da matarshi.

Kuka sosai saudart keyi kamar yaune ranar aurenta, haka su mamy suka rakota har bakin dalleliyar farar motar dayazo daita tashiga gaba gefen driver tana kuka sosai shikuma yashiga mazaunin driver.

Nan ya tada motar yana satan kallon saudart data rufe fuskarta da mayafi tana kuka sosai sannan ya ja motar su abdul nata dagamusu hannu a sanyaye suka bar
gidan...✍


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️[9/14, 5:23 PM] Makera: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)



Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)



089


Tuqi yake cikin normal speed gwanin burgewa, motar ta gauraye da both qamshin turarenshi da nata wanda suka hadu suka bada wani scent mai mugun dadi ga sanyin a.c din motar daya qarasa cikin motar extra cool.

Ahankali yaqara juyowa ya kalleta, kanta kifeda da cinyoyinta tana sheshekar kuka ahankali wanda yakejinshi har cikin ranshi.

Dauke kai yayi ya maida ga tuqin dayake yana jin badadi, duk zumudinshi da dokinshi duk sun kau dalilin kukan datakeyi.

Jiyayi shima yadamu sosai, meyasa take kuka? Kenan haryanzu she hate him? Yasan bata sonshi amma ai yaci ace ixuwa yanzu ta yafemashi koda bazata bashi zuciyarta ba.

Qara kallonta yayi asanyaye yasake maida idanunshi a kan titi yanajin badadi don sosai kukan nata ke ta6amashi zuciya, jiyake kamar ya rungumota ajikinshi yaita patting dinta hartayi shiru.


Horn yayi a bakin tangamemen gate din gidansu, ko minti biyu ba'a qaraba gate din ya wangale,

Jan hand brake din yayi baya sannan yaja motar yashiga cikin gidan dayake tarr da haske kamar ba dareba.

Parking yayi abaki bakin parking space don yasan yanzu zasu fito.

Dan satan kallonta yayi yaga haryanzu bata dagoba kuma bata bar kukan ba.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasa hannu ya bude murfin kofar yafita ya zagayo side dinta yabude mata kofar.

Qin dagowa tayi dukda taji tsayuwar motar dakuma bude murfin 6angarenta.

Sosai take cikin fargaba, fargaban irin zaman dazasu sakeyi dashi, tama kasa misalta zaman nasu a zuciyarta.

Kallonta kawai shima yake, da ba a wannan gidan bane da babu abinda zai hana ya dauketa kamar baby doll yakaita har dakinta amma that must wait, bazai iyayin haka ananba.

Hannunshi yakai yakamo tsintsiyar hannunta dayasha qunshi ya riqo softly.

Hakan yasa kukan nata ya tsaya cak kamar anyi ruwa an dauke, gabanta yashiga faduwa kadan kadan.

Qoqarin amsar hannunta yake amma takasa don ya riqe sosai.

"Ki sauko don allah, yi haquri" yafada cikin sigar rarrashi

Shiru tayi still bata dagoba, tanajin wani iri sakamakon riqemata hannu dayayi.

Ahankali yadan jawo hannun kamar zai dagota.

Haka yasa ta dago saidai kanta aqasa, ta ziro kafa daya ahankali sannan ta ida fitowa asanyaye feeling so awkward and weak.

Besaki hannunba dukda tafito din saima sake damqe hannun dayayi yafara tafiya.

Dole tabi bayanshi badon tasoba fargabarta na qara qaruwa.

Tafiya suke hannunsu acikin na juna, jinshi yake so on top, jerawa da ita haka hannu cikin hannu ba qaramin shauqi abin yasashi ba.

Wani abu ma saima sunyi settling, yayi alqawarin saiya kasheta da salo salo na love, saiya tsundumata a kogin soyayyarshi tasha tayi tatul.

Murmushi yadan saki daidai sun qaraso bakin kofa.

Dayan hannun dake free yasa ya danna doorbell din yana satan kallonta.

Shiru saudart tayi wondering meyasa yake danna doorbell, dama basu kadaine agidanba?

Budewar kofar ya katse mata tunani.

"Oyoyo my daughter! Maraba lale, marhaba biki" taji muryar ummy ana rungumota.

Saurin dagowa tayi takalleta taga ita dince tana qoqarin shiga daita ciki.

Saurin sunkuyar da kai tayi cikin tsananin kunya suka shiga ciki tana jikinta.

Murmushi ashraf yayi ganin ummy batama bi takanshi ba shima yashiga cikin ranshi yana cewa
"Saukin abin matata ce ba taki ba"

Saida suka shiga falo sannan saudart ta ida tantance inda suke, gidansu ashraf.

Haka ummy taqarasa daita ciki tana mata marhaban cikin fara'a harta kaita kan wani kujera ta zaunar daita kamar tana zaunar da kwai, itakau saudart tsabar kunya ko dago kai takasa.

Shima qarasowa yayi ciki yana kallon yadda umminshi ke wani binta ahankali cikin so da qauna, murmushi yayi yana jindadin yadda ake tarairayar gimbiyar tashi.

Da dane da yanzu yana nan yanata kumburi anfi nunamata qauna, amma yanzu he's happy don masoyanta masoyinshine.

Ahankali tazamo daga kujerar ta zauna qasa tana gaida ummy da itama zamanta kenan cikin girmamawa kai aqasa.

Amsawa ummy tayi cikin fara'a tana cewa takoma kan kujera ta zauna amma taqi tashi saima sadda kai datayi tana wasa da fingers dinta.

Qarasowa ashraf shima yayi ya zauna yana facing dinsu, kallo daya zakamashi kasan zuciyarshi fess take, don sosai yakejin wani sabon farinciki a zuciyarshi kamar yaune aka dauramusu auren.

"Wai ummy hayaniyar me nakeji n.." baby dake saukowa qasa tafara fadi, ganin kamar saudart azaune kan carfet yasa kingin maganar maqalewa a iska.

"Aunty!!" Tafada da karfi sannan tayo qasa dagudu tana skipping din stairs bama ta lura da akwai A.A a falon ba.

Wani irin fadawa kan saudart tayi ta qanqameta cikin farinciki don ita batamasan da zancen tarewarta ba.

"Hey are you mad!" Inji ashraf cikin qaraji ganin tawani fadawa matarshi

Saurin zabura tayi tasaki saudart dahar yanzu kanta ke qasa ta kalli gefen dataji tsawan don ita harga allah batama lura dashiba.

"Karyata zakiyi koko? Zaki tashi daganan ko saina sassa6a miki!" Yafada cikin daga murya.

Saurin miqewa tayi kafinma ya qarasa maganar tadawo gefen ummy ta zauna tana shigewa jikinta tana turo baki.

"To sannu, hanata zakayi su gaisa da auntyn tata?" Inji ummy tana gallamashi harara.

Dan sosa qeya yayi yace "ummy kingafa fadamata tayi, karta karyata"

"Eh tunda ga pencil ba dole ta karye ba?" Tafada tana harararshi

Sunkuyar dakai yayi kawai bece komaiba yana kwafa acikin zuciyarshi, shidai suyi sugama yatafi da matarshi basai sun qara ganinshi ba? Dama ciki yake dasu yadda suka sashi wahala musanmman ummy data kusan samashi heart attack lokacin data buqaci takardarta, dama yadau alwashin duk sadda ya dauki saudart yatafi sai baba ta gani, sai sunyi missing dinshi sosai don yaga alamar dan zaman nan dayayi sun wani rainashi, musanmman waccan tsinken sakacen (baby😂)

"Aunty ina wuni?" Inji baby dake maqale da ummy haryanzu cikin zumudi.

Dan dago kai tayi ta kalleta ta sakarmata murmushi sannan ta maida kan qasa don sosai takejin kunyansu gabadaya.

"Baby kaita sama dakina, bari na hadomata abinci" inji ummy

Saurin tashi baby tayi kamar dama kan qaya take tadan saci kallon ashraf daketa antayamata harara ta qasan ido, tai saurin dauke kai taqaraso wajen saudart ta kamota tana mata rada a kunne
"Welcome back"

Batace komaiba sai tashi datayi suka wuce stairs tare, ummy da ashraf na binsu da kallo.

Saida suka shige sannan ummy ta maido kallonta kan ashraf da har yanzu be bar kallon inda sukabi ba tayi gyaran murya.

Saurin dauke kai yayi daga kallon dayake ya sunkuyar dakai cikin dan jin kunya.

"Saika tashi kaje kaima ga abincin can dining in zakaci" tafada cikin daurw fuska.

Dan ta6e baki yayi yace
"No ummy am ok"

Azuciyarshi kau cewa yayi
"Abincin yasha zamansa, Idan naci ina zan saka kazar dazan siyamana?"

"Kai kasani" tafada tana tashi tabi bayansu baby.

Binta da kallo yayi harta haye sannan ya ta6e baki yana wondering meyasa kwananan ummy ke dauremashi fuska, gashi yanzu tagama washema saudart baki amma shi tawani hade mashi fuska.

Ta6e baki yayi yakoma ya kishingida a kujerar yayi balancing yaciro wayarshi yana daddanawa yana jiran tagamaci ta sauko su tafi😒

Sosai yakejin zuciyarshi fess, sai practicing din abinda zai faramata yake a zuciya, soyake ya koyamata darussan sonshi dalla dalla, zai maidata queen dinshi, sarauniya, yalla6iya, ko tsinke bazai bari ta dagaba, shizai mata breakfast, yazo ya tadata daga barci romanticly ya rakata har bathroom dama yariga ya hadamata ruwan wanka mai dumi da qamshin gaske, yajirata kofar bayin harta gama tana fitowa ya sunkuceta yakaita kan gado, ya zaunar daita, ya shafamata mai ya ciromata kaya tasa sannan yakaita dining, A'a sama zaikawo abincin, zaifi bada kala, ya bude yayi serving dinta ya saka cokali ko fock yafara feeding dinta, da ana iya taunamata ma dashi zai taunamata, tagama yabata ruwa tasha sannan yayo clearing din wajen yadawo ya sungumeta yakaita falo ya kunnamasu kallo ya kwantar da kanta bisa cinyarshi suna kallo yana massaging din kanta.. wooh soyayya dadi! Saiyafi sharukh khan ma iya zuba love, saiya rudata da salon soyayya ya tsundumata tsundum cikin kogin soyayyarshi yadda duk numfashinta saita shaqane da sonshi.


Haka yaita lisafe lissafenshi shikadai sai sakin murmushi yake, jin yafara gajiya dazama babu su babu alamar su yasashi daga kai yaduba agogo.

Waro idanunshi yayi ganin har goma ta gota.

Wannan cin abincin na lafiya ne kuwa? Almost two hours?

Shiga contact yayi ya dannawa number baby kira ya kara a kunne yana tamke fuska kamar tana gabanshi.

Saida takusan tsinkewa sannan aka daga
"Hello?" Yaji tafada cikin muryar barci

"Ke! Ya akayine? Haryanzu bata gamacin abincin bane?" Yafada cikin husky voice

Zaune tamiqe tana murza idanu don ita tama dan dade da kwanciya

"Wacece?" Ta tambaya tana hamma

"bansaniba! Nace ina saudart" yafada a fusace

Turo baki tayi sannan cikin marairaicewa tace
"Nifa tunda ummy tahau sama ta korani daki wai karna takuramata"

Tsaki yaja ya katse wayar kawai. Bin wayar tayi da kallo cikeda takaici sannan ta kasheta gabadaya tayi tilli daita kan gadon ta kwanta taja bargo.

Yana gunguni yashiga neman number ummy.
"Yanzu this is 10 sai dayan dare nufinta zamu tafi?" Yafada yana danna mata kira.

Itama saida takusan katsewa sannan ta daga

"Uhum?" Tafada daga dayan 6angaren

Turo baki yayi cikeda jin haushi yace
"Ummy this is past ten fa"

"Sai akayi yaya?" Inji ummy tana daure fuska daga dayan 6angaren.

Haushi ne yasake qumeshi
"Ummy sai midnight zamu tafi? Bata gama cin abincin bane haryanzu?"

"Wa kenan?" Taqara tambaya

Shiru yayi gabanshi nadan faduwa.

Wani tunani ne yazo mashi, saurin kauda tunanin yayi yana cewa no..no..no ummy bazakiyimin hakaba.

"Look idan bakada abin cewa zan kashe wayata, dama barci nike ka tadani" ta katsemashi zancen zuci da hakan.

Cikin dan rawar murya yace
"To kiyi haquri ummy, wai gani nayi dare nayine ga securities, idan nahau hanya yanzu suna iya tareni""yafada cikin zuciyarshi yana addu'ar allah yasa ba abinda yake tunani bane zai faru

"Ehen? Katafi mana, dama wani ya tsaidaka?"

Shiru yayi yanajin

Please Login or Register in order to submit comment