Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawun bakinshi na qafewa, besan sadda ta zame hular kanshi ba yana fiffita kanshi

"ummy dan allah kiyi haquri, kibani saudart mutafi dare yayi" yafada cikin mugun surewa yana ganin yadda budget dinshu ke rushewa agaban idanunshi

"Wace saudart?"

"Ummy don allah, don allah kiyi haquri, please ummy, don allah" yafada duk ya rude yayinda danasanin biyowa tanan ya dirarmashi nan take.

"Mtcheew meye nawani tisani gaba kana begging? Me kayimin?"

"Wlh nima bansaniba ummy amma don allah kome nayi karki hukuntani da wannan, please sweet ummyna kinji?" Yafada cikin sigar rarrashi still yana yima kanshi fifita.

"Mtcheew saida safe, ka kashe duk kayan wuta dake falon sannan ka kullemin kofa idan zaka tafi" tana kaiwa nan ta katse kiran tama kashe wayar gabadaya.


Sakin baki yayi jin abinda tace, me kenan? Oh no! Wlh bazata sa6uba.

Saurin ciro wayar yayi daga kunne yasake re-dialing din wayar amma wayar akashe.

Ca6! Yau ake yinta, idan ya yarda yatafi tsaye๐Ÿ˜ก

Tilli yayi da hular hannunshi ya nufi sama kamar zaiyi fiffike yatashi sama yanajin kanshi na daukan zafi.

Beci burkiba akoina sai a kofar dakin ummy.

Bubbugawa yake yana huci, jin shiru yasashi qara bubbugawa wannan karon da qarfi don sosai zuciyarshi ke tafarfasa.

Jin kamar za'a 6alla kofar yasa ummy tasowa don ita guduma take kar ya tada saudart datayi barci tundazu wanda azahirin gaskiya ba barci saudart keyiba duk abinda ake harta wayar da ummy tagama yanzu duk a kunnenta ne.

Ganin ummy ta bude kofar tafita yasata dan dagowa ta yaye bargon kanta ta kalli sannan tasaki murmushin jindadi tajuya tagyara kwanciyarta tana dariya qasa qasa.


Shiru ashraf yayi yana kallon ummy kamar zai fashe da kuka, jiyake kamar yaita ihu ko zaiji sauqi.

"Nace menene! 6allemin kofar zakayi?!" Inji ummy tana binshi da harara

Qoqari yayi wajen sassauta muryarshi sannan ahankali cikin kwantar da murya yace
"Haba ummy, haba ummy? Dan allah ki tausayamin mana, dan allah kiyi haquri ki fiddota mutafi dare yayi"

Wani kallon uku saura kwabo take binshi dashi harya kai aya sannan tace
"Ka gama? To wlh ka fita idona in rufe ashraf, katafi kabani wuri tun muna mu biyu wlh, tun kafin in sassa6amaka"

Kallonta yake kamar zaiyi kuka, ahankali yace
"Ummi yanzu ina zani ni kadai?"

"Ohon maka amma wlh nakarajinka kusada kofarnan saika yabawa aya zaqinta" tana kaiwanan tajuya takoma dakin tareda bugo kofar.

Tsayawa yayi yana kallon kofar cikin rashin sanin abinyi, wai wane tsautsayima yasashi zuwa gidan ma tun farko, wannan shi ake kira rabon ayi, (nikuma nace ga qoshi ga kwanan yunwa๐Ÿ˜)

Ya dade sosai tsaye a bakin kofar kamar mai jiran tasake fitowa har saida yaji kaffafunshi sunfara sanyi sannan yajuya afusace ya sauka qasa feeling so mad in anger, jiyake kamar yadora hannu aka yaita ihu.

Motarshi yashiga afusace ya kunna yayi reverse, wani uban horn ya danna kamar ana yaqi sannan ya fice a tsiyace bayan an bude gate din.

Tuqi yake yana huci ga idanunshi dasukayi jajir, jiyake kamar yaita kuka don takaici, kai amma ummy tagama dashi wlh, duk wannan tsare tsaren nashi duk ta rusheshi kenan abanza?

Kwafa yayi yana danna kan motar cikin gidanshi bayan anyi scanning dinshi.

Ko parking din kirki beyiba ya sauko daga motar ya maidata ya rufe da qarfi sannan yayi cikin gida fuuu.

Jiyake kamar ya hadiyi zuciya kawai, he can't believe duk zumudin da zakwadin shi kadai zai kwana gidan at the end of the day, kai ummy tagama dashi.

Direct dakinshi yashige yawani bugo kofar da qarfi, baiwar allah yadda kasan ita tamashi laifin๐Ÿ˜•

Kokowa yashigayi da rigar jikinshi don cireta yadda kasan yasamu qaton gardi.

Dakyar yasamu ya cireta yana huci dukta cikwikwiye itama yayi cilli daita tana huci.

"Wlh ummy kin gama dani!" Yafada yana dafe kai cikeda takaici.

Tsaki yaja yafara safa da marwa dakin cikin tsananin 6acin rai, jiyake kamar yaita hauka.

Wayarshi yazaro daga aljihun rigarshi dayayi cilli daita ya lalubi number sadeeq ya dannamashi kira yana huci.

Kira har hudu amma ba'a dagaba da alamu dai ya dade dayin barci

Tsaki yaja yana cilli da wayar kan gado yana cewa
"Shege sleeping head kawai"

Ataqaice ranar ashraf kasa runtsawa yayi don baqinciki, tsaki kau yakashi yafi cikin kwando dama tusa hali bare anci wake๐Ÿ˜†

Yadda yaga rana haka yaga dare don azaune ya kwana don bakinciki...โœ

Please kucigaba dasa brother na a addu'a๐Ÿ™

Ummin fasihu๐Ÿงš๐Ÿปโ€โ™€๏ธ
[9/14, 5:23 PM] Makera: ๐Ÿคต๐Ÿป๐Ÿ‘ฐ๐ŸปAUREN KWANGILA๐Ÿคต๐Ÿป๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love๐Ÿ’–



090


Yauma da 6acin ran jiya ya tashi, dakyar ya iya tashi yayi alwala yafita masjid bashi yadawo ba saida gari yadan fara haske.

Tunda yadawo yashige daki ya kwanta shiru zuciyarshi fall takaici.

Ringing din wayarshi yasashi bude idanunshi daya lumshe sannan yadauki wayar ahankali yana duba mai kira, tsaki yaja kamar bakin zai tsinke ya maida wayar ya ajiye batareda ya dagaba.

Saida aka mashi 4 missed calls be dagaba sai a ba biyar sannan ya daga yawani tamke fuska kamar mai kiran na gabanshi.

"Amma A.A kaci uwar rainani, inta kiranka kaqi dagawa don iskanci?" Inji sadeeq a dayan 6angaren.

"Qodarka aka ban ajiya halan dazaka addabeni da kira kamar wanda yayi maka sata, ni nace ka kirani ne?" Yafada cikin 6acin rai

"Sai kace in kiraka dama? Mtcheew dama don naga missed calls dinkane har hudu yasa na kira inji lafiya ashe iskancinka ne ya motsa"

"Eh shi ya motsa, and batun missed calls ai tun jiya namaka don iskanci sai yanzu zaka wani kirani kaji lafiya? Don ka maidani maloho?"

"To allah yabaka haquri, ba laifinka bane, laifi nane dana kira at the first place, bye"

Qiit.. ya katse kiran.

Wani haushi yakuma qume ashraf, ciro wayar yayi daga kunnenshi afusace yasake dannamashi kira yana huci.

Saida takusan katsewa sannan ya daga yana cewa
"Menene kuma?"

"How dear you hang up on me? Kai wanene dazaka katsemin kira?" Yafada afusace, dama neman wanda zai juyewa kwandon bala'i yake

"Tofa? Meyasa nayi hanging? Mezai hana inyi hanging? Na tashi naga missed calls dinka wajajen 12 ba dole hankalina ya tashiba? Nakira kuma inyi comfirming ka balbaleni mezai hana inyi hanging up?" Yafada shima da alama yafara qulewa

"Eh din, an balbaleka din! Mezakayi? Nace anje an balbaleka din, ko dukana zakayi?" Yafada cikin tada jijjiyoyin wuya abinda ummy tayimashi nasake dawomashi a qwanya, da yanzu suna tareda abar qaunarshi, nurul qalbi dinshi.

Shiru sadeeq yayi kawai baki sake, lallai ma ashraf da alama rigima yakeji, tsawon kasancewarsu tare yasa yasan komai nashi, yasan halinshi ciki da bai, babu tantama 6atamashi rai akayi wataqila shiyasa ma yakira jiya din and da alama haryanzu yana cikin 6acin ran.

"Alright...alright am sorry to, allah ya huci zuciyar the boss himself" yafada yana murmushi

Tsaki ashraf yaja yakoma ya jingina da kan gado yana kalkada kafa ahankali sai muzurai yake.

"Yanzu gayamun waye yata6amana boss dinmu, the whole A.A himself"

Tsaki yasake ja batareda yace komaiba, shi komaima haushi yake bashi wlh.

Ta6e baki sadeeq yadanyi cikin zuciyarshi yace
"Kaji dashi, mutum abu kadan tsaki kamar tsaka"

Azahiri kuma yace
"Ko inzo ne?"

Tsaki yasake ja kafin ahankali kamar mai koyon magana yace
"Idan kaga dama"

Dan murmushi sadeeq yasaki sannan yace
"To ai hikenan, amma ka tanadarmin wani abu please ban karya ba"

Wani tsakin yaja cikeda haushi yace
"Ubanwa zai tanadarma? To kama cika cikinka don ba gidanmu ba nike, inanan gidana"

"Gidanka? Me kakeyi gidan?"

"Sainaji matsa sannan zan fadi, mtcheew"

Yana kaiwa nan ya katse wayar yayi tilli daita kan gado ya maida hannayenshi ya harde a qirji yana cigaba da kalkada kaffafu.

Sosai yaji dadin kiranshi da sadeeq yayi don dama ko be kiraba yanada niyyar kiranshi don a duniya babu wanda yake sharing din damuwarshi dashi kamar sadeeq, dukda wani sa'in he's so annoying amma he's the best kind of friend ever, haka yaita kalkada kaffafun yana tsumayin jiranshi, yazo yafadamashi ko zaiji sauqin abinda yakeji aranshi.


Sauke wayar sadeeq yayi daga kunnenshi yana girgiza kai, Allah ya shiyaka A.A da wannan shegiyar zuciyar, zuciya kamar kuturu.

Yamiqe ya ajiye wayar sannan yawuce bathroom don freshen up.




Dago kai tayi daga littafin addu'o'in datake karantawa na ummy ta kalli kofar tana amsa sallamar da akayi.

Baby ce tashigo, haqoran nan awaje don murna ta qaraso dakin tana kallon saudart.

Itama saudart kallonta take murmushi a fuskarta harta qaraso inda take zaune akan sallaya itama ta zauna kusada ita baki awashe tace
"Good morning sweet aunty!"

Murmushi mai sauti tayi tace
"How was your night?"

"Cool... wai aunty nan dama kika kwana?"

Harara ta gallamata ta maida kanta bisa littafin hannunta tana cewa
"Shafa kiji"

Wani irin dariya baby ta qyalqyale dashi harda dafe ciki, dagowa saudart tayi tana kallonta da alamar tambaya itama dariya nason kufcemata amma tana mazewa.

"Like seriously, you mean... nan kika kwana? Whoo no wonder jiya yaya ya addabeni dakira yana balbaleni, ashe kwalele akayimashi, kai amma ummy bomb ce" tafada tana qara kecewa da dariya.

Waro idanu saudart tayi jin abinda tace a qarshe sannan ta tallabe mata qeya tana cewa
"Ummin ce bomb, qaddara taji tagama"

Wata dariyar baby tasa kafin tace
"Ai gaskiya ne aunty, a kwacema matarka a very first night dinka? Ai angama dakai wlh"

"To ya isheki, tashi kifita kingama kinja na manta inda na tsaya" tafada tana maida dubanta ga littafin.

"Ni aunty naga ma kamar abin be wani damekiba, naga bashi kadai akaima buqulu ba harda ke"

Rolling din idanunta saudart tayi cikin qosawa da magangannunta sannan cewa
"Kinsan Allah? Zan hadaki da ummy wlh, tom"

Dariya baby tayi tana tashi tsaye
"A'a bani na kar zomon ba, ratayar ma ba'a banba, kai amma ummy ma ta iya, naso inga idon yaya jiyan nan" tafada tana fita daga dakin.

Binta da kallo saudart tayi sannan ta girgiza kai tana dan murmushi.

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

Tsayawa yayi yana binshi da kallon takaici yanajin kamar ya rufeshi da duka ko yaji sauqin abinda yakeji.

Don iskanci an 6atamai rai yakirashi don yasamu sassaucin abinda yakeji shine zai bige da yimashi dariya?

Ahankali sadeeq yafara tsagaita dariyar dayakeyi tundazu yana wani irin shesheqa don har cikinshi yafara ciwo saboda dariya.

"Are you kidding me?" Yafada dakyar cikin sheshekar dariya yana kallon ashraf da fuskarshi ke dinke tsab kamar wanda aka aikowa saqon mutuwa.

Hankerchief yasa ya tsane hawayen dasuka tararmashi a idanu saboda dariya yace
"You mean ummy ta riqe matarka? Hhhhhhhh to wai dama tarewa zatayi shine banji labari ba? Hhhhh amma ummy ta iya, ita haka ake? Saiki riqema mutum matarshi a ranar farko? Gaskiya ummy bata kyauta manaba" yakuma kece dawata dariyar.

Ashraf rasa inda zaisa kanshi yayi don baqinciki, wai yama akayi yakira wannan chali chalin dasunan ya gayamashi damuwarshi, gashi he is adding salt into his injury don dariyarshi ba qaramin tunzurashiba take.

"Gaskiya ummy bata kyautaba... muje musameta muji dalilin ta na yimana wannan ta-leqo-ta-koman?" Yafada cikin rawar murya irin ta masu dariyarnan sannan yakuma kwashewa da wata dariyar harda buga kafa qasa.

Tashi ashraf yayi a mugun fusace yana nunamashi kofa
"Don ubanka zoka fita" yafada cikin quluwa

Dakyar sadeeq ya danne dariyarshi sannan yace
"Ni? Menayi kuma?"

"Wlh koka fita ko in 6a66alaka acikin gidan nan kuma na 6alla banza na 6alla wofi, nace out!" Yafada cikin hargowa, jiyake kamar yaita kuka don takaici.

"Haba ashraf... nifa bani nayimaka ba, saika huce kaina?" Yafada yana faman danne dariyarshi saidai kallo daya zakamashi kasan dariya na cinshi sosai

"Wai bazaka fita ba!!" Inji ashraf cikin daga murya idanunshi sunyi jajur.

"To..to..to yanzu am sorry kaji? Am so sorry ok? I don't mean to hurt you, kawai abin ne daban dariya" yafada yana yin serious face ganin yadda ashraf ya kunnu

"Yanzu laifi ne don na kiraka na gayamaka damuwata? Saika tusani gaba kanamin dariya?" Yafada cikin jin ciwon abun.

Sosai sadeeq yayi qoqari wajen danne dariyar dake cinshi yace
"Haba bestie? Meyai zafi? Wlh i don't mean to hurt you, am sorry if i did"

Komawa ashraf yayi jagwab a kujera yana dafe kai, sosai zuciyarshi ke tafasa, jiyake kamar yaita kurma ihu ko zaiji sassauci.

"Sorry kaji insha allah matarka zata dawo gareka, i assure you" sadeeq yafada cikin sigar lallashi dukda yadda yakeson bursting to laughter amma beson yasake tunzurashi shiyasa yake dannewa.

Janye hannu yayi daga dafe kan dayayi ya kalleshi da idanunshi dasuka kada yace
"Yanzu idan kaine aka qwacewa mata at the very first day dazaku tare ya xakaji? Tell me" ya tambaya cikin yanayinda dole yabaka dariya.

Kasa amsawa sadeeq yayi don yasan muddin ya bude baki da niyyar amsawa to tabbass dariyace zata fito, non-stop laughter.

"Tambayarka nike, idan kaine zakaji dadi?" Yasake fada yana tsareshi da ido

Girgiza kai kawai ya iyayi don saura kadan yayi exploding.

Kuramashi idanu ashraf yayi sannan ya girgiza kai yace
"Kayi dariyarka mallam ban hanaka ba"

Dariyarce ta kufce mashi batareda ya shirya ba yayi saurin sa tafin hannu ya toshe baki yana yi sosai.

Sosai ashraf yaqara hawa hakan yasashi fara jifanshi da pillows din kijeru yana cewa
"Get out! Get out! Get out idiot!"

Tashi sadeeq yayi yana dariya sosai yana kakkare jifan.

Ganin abin nashi bana qarewa bane yasashi nufar waje dagudu yana dariya shima ashraf yabishi still yana jifanshi.

Haka suka fito har harabar gidan yana jifanshi da pillows din yana sake tsintarsu yaba jifanshi

"A.A please listen to me" yafada yana chafe wani pillow da ashraf ya jefomashi.

"Listen your head! Get out!" Yafada yana turashi.

Taga taga yayi kamar zai fadi yayi saurin maintaining din balance dinshi yana dariya sosai yace
"Wlh shawara zan baka listen to me"

Turashi yacigaba dayi harsuka qaraso wajen motarshi yana cewa
"Shawara my ass! Banso! Ka dau akwalar motarka kabarmin gida"

Haka ya tasa qeyarshi harya shiga mota yarufe sannan yaja baya yana huci kamar zaki.

Wining din glass din sadeeq yayi qasa yace
"Wlh ba zama zakayiba, kaje ka tisata gaba ta baka matarka idan ka zauna kuma zakaga zama"

Wani kallon 'au bazaka tafiba?' A.A yayi mashi sannan yanufi wurin wani dutsi zai dauko, hakan yasa sadeeq saurin bama motarshi wuta yafice aguje yana qyalqyalar dariya.

Kwafa ashraf yayi yana yadda dutsen hannunshi yana cewa
"Daka tsaya ai"

Sannan yajuya yayi cikin gida yana tsince pilluluwan daya watsar tsakar gidan.

Dawowa yayi ya zauna falon ya harde kaffafunshi yana dan girgizawa irin yanajin bala'in nan.

Shi wlh bazai jeba, badai saudart ba? To yabar mata ta jiqa ta shanye.

Haka yaita zama ranshi a 6ace daga baya kuma yafita yawuce wani restaurant don sama cikinshi wani abu jin yadda cikin ke kiran ciroma.

Koda yagama gidanshi yadawo yawuce sama ya rufe kanshi adaki, jiyake komai ma bemishi dadi, jiyake kamar yaita rotsa anything rotsable a dakin.

Haka yaita daurewa har zuwa bayan azahar, ganin dai yana neman kashe kanshi cikin gida batareda wanda yakeyi dansuba sun sani yasashi shiryawa ya dauki makullan mota yafita.

Hanyar gidansu ya dauka don bazai iya jurewa ba, yakasa yin zuciyar, gwara yaje duk yadda za'ayi ayi shidai abashi matarshi...โœ

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi kasiran!

Ina farincikin sanardaku an sako brother na yau, nagode qwarai da addu'o'inku, nasan hardasu suka bada gudunmawa har komai yazo cikin sauki.

Allah ya saka da alhairi๐Ÿ’–


Ummin fasihu๐Ÿงš๐Ÿปโ€โ™€๏ธ
[9/16, 3:22 PM] Makera: ๐Ÿคต๐Ÿป๐Ÿ‘ฐ๐ŸปAUREN KWANGILA๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป๐Ÿคต๐Ÿป
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love๐Ÿ’–
(Ummin fasihu)




091



Shiru yayi hannunshi kan sterring yana tunanin hanyar dazaibi yayi convincing din ummy tabashi matarshi.

Shi bemaga dalilin yin hakaba, wannan ai daukan alhaki ne, shi bema ganin laifin kowa sama da nashi, da beyi kicihin biyawa ta gidanba tun farko da yanzu wani labarin ake.

Shi wai irin ya kawota dinnan ayimasu nasiha ganin haka akayi wancan lokacin ashe ruwan dafa kanshi ya debo da kanshi.

Ajiyar zuciya ya sauke nannauya sannan ya cire seat belt dinshi ya bude murfin kofar yafito ahankali yana shakar fresh breeze din dake kadawa.

Ahankali cikin tafiyarshi ta qasaita yanufi cikin gidan yana ayyana yadda zaiyi yasamu yashawo kan ummy.

Danna doorbell yayi yamaida hannayenshi cikin aljihu ya zubama kofar idanu.

Jim kadan aka murda kofar aka bude.

Saurin sunkuyar da kai maid din tayi tana gaisheshi cikin girmamawa.

Amsawa yayi yana shiga cikin falon dauke da sallama a bakinshi.

Juyowa duk sukayi daga inda suke zaune a dining suna kallon cikin falon.

Dumm.. gabanta ya fadi sanadiyyar gaurayar da idanunta sukayi da nashi, sosai taji effect din idanun nashi anata wanda hakn yasata saurin sadda kai zuciyarta na chanza bugu.

Shima tsayawa yayi yana kallonta, jiyayi wata iriyar kasala ta sauko mashi nan take, sosai yaji yayi missing dinta daga jiya zuwa yau.

Ahankali yanufo wajensu idanunta akanta yana kallon yadda take jujjuya cokali a plate din gabanta.

Satan kallon saudart baby tayi ganin irin kallon dayake mata taga kanta na qasa sannan ta saci kallon ummy taga itama hankalinta nakan abincinta saima qara tamke fuskar datayi hakan yasata sunkuyar dakai tana danne dariyar karfin halin ummy, mutum da matarshi?

Jin ya qaraso wajensu yasata dagowa ta kalleshi taga tsaye yake yana kallonsu gabadaya.

"Oyoyo yaya! Please have a seat" inji baby cikin iyayi.

Wani tsarabar harara daya bata yasata yin tsit ta maida kanta kan abincinta tana turo baki.

Jan kujerar dake kusada ummy yayi ya zauna yana kallon saudart dake tsakurar abincinta atakure ta qasan ido sannan ya maida kallonshi ga ummy datayi kini kini da rai yace
"Good afternoon ummy"

Batareda ta dago kai daga abincin datake ciba tace
"Afternoon"

Shiru yayi yana kallonta ganin yadda tawani hada gabass sa yamma daga ganinshi, shi yarasa meyasa ummy kemashi haka.

"Yaya ina wuni" inji baby tana dan hura hanci adole an6ata mata rai.

Ko kallon gefenta beyiba bare tasa ran amsa saima maida kallonshi dayayi kan saudart dakejin kamar ta narke saboda yadda takeji.

Jin idanunshi akanta yasata qarajinta uncomfortable, allah yasani batason kallon nan ko kadan, yanasata jin wani iri sosai.

Ahankali ta cije ta dago, hada idanu sukayi tayi saurin janyesu sannan cikin calm voice tace
"Ina wuni?"

Wani irin farinciki yaji ya ziyarci zuciyarshi nan take, farincikin da rabonshi dashi tun jiya kafin yaje daukota.

Sakarmata cool smile dinshi yayi yace
"How are you?"

Batareda ta kalleshi ba tace
"Alhamdulillah" a takaice.

"Baby serve your brother" inji ummy dahar yanzu taki dagowa daga abincinta.

Tashi baby tayi ta zari plate tashiga zubama ashraf abincin tana satan kallon yadda yake kallon saudart ta qasan ido.

Sosai tayimashi kyau cikin doguwar rigar atamfa mai manyan flawowi yellow and dark green dake jikinta dinkin pieces taji stone works agaba, ta kamata cif cif kamar ajikinta aka dinka sai dankwalin data daura zahra buhari style, fuskarta has usual dauke da simple makeup don yau ko kwalli batasa a idanu ba sai lining din datayiwa saman idanun mai kyau.

Beta6a ganinta acikin shigar atamfa ba sai yau, yafi ganinta cikin arabian gowns ko shadda hakan yasa yaga ta chanzamashi sosai kamar ba itaba.

Dan ture plate din gabanta tayi ba don ta koshi ba sai don takasa kai komai abakinta saboda yadda takejin piercing eyes dinshi akanta ta zari tissue tana dan goge baki.

Dagowa ummy tayi tana kallonta ciki kulawa tace
"Ya dai?"

Murmushi tasakar mata tadan yamutse fuska tace
"Am full ummy"

Wani irin binta yayi da kallo ganin yadda ta shagwa6e fuska kamar wata baby doll yanajin kamar ya cinyeta don so.

"Hmm keda baby bansan gwani ba wurin rashin cin abinci, ku kuka sani ai" tafada tana sipping din ruwa.

Murmushi kawai tayi sannan tadanja kujerarta baya ta tashi tana cewa
"Ina zuwa"

Ta juya batareda jiran amsar kowaba tashiga takawa cikin takunta mai cikeda da nutsuwa tabar wajen.

Binta yayi da kallo qasa qasa yanajin badadi don beso ta tashi ba, begaji da kallonta ba da shaqar qamshinta.

Maida hankalinshi yayi kan abincin yanaci yana tunanin ta ina zai 6illowa ummy ta taimaka tabashi matarshi.

Ba'a jimaba baby ma ta ture plate dinta tana goge bakinta da tissue itama tayimusu sallama tabar dining din.

Shiru wurin ya dauka sai qarar cokala dazakaji suna haduwa da plate.

Shidai ashraf tsakurar abincin kawai yake, soyake ya dauko maganan amma yarasa ta inda zai fara.

Can dai ya nisa ya dago ya kalli ummy da kanta ke bisa abincinta tanaci fuska daure.

Ajiye spoon dinshi yayi sannan yayi interlocking din yatsun hannayenshi ya dora kan table yana kallonta.

"Ummy.." yafada ahankali yana zubamata hazal eyes dinshi daya gado wajenta.

Dagowa tayi itama ta zubamashi nata batareda tace mashi komaiba.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yaqara yin qasa da murya yace
"Ummy don Allah laifin me nayimiki ne kiketa fushi dani? Dan allah kiyi haquri ki gayamin ummy, wlh bansan me nayiba" yafada yana langwa6a kai kamar wani maraya.

Dauke kai tayi daga kanshi ta maida a abincinta tana cewa
"Cema nayi kayimin wani abu?"

"Ko bakice ba ummy ai fuskarki ta nuna, don allah ki taimaka ki gayamin ummyna" yafada cikin sigar rarrashi.

Ta6e baki tayi tace
"To ni bakamin komaiba, idan ma kayimin kasan ba tsoronka ba nake dazan tsaya 6oye 6oye, fitowa zanyi infadama inkuma dauki matakin daya dace akai, so stop bothering me" tafada tana kai abincin data debo abaki.

Shiru yayi yana kallonta nawani lokaci sannan ya sauke ajiyar zuciya ahankali
"To amma ummy meyasa kika hanani tafiya da saudart jiya?" Ya tambaya ahankali

"Saboda na isa daku duka, daga kai har saudart din, idan kuma nunamin zakayi ban isa dinba to" tafada tana binshi da harara.

Shiru yayi yana kallonta zuciyarshi namai zafi.
Wai meyasa ummy kemashi haka? Meyayi mata take son ganinshi cikin 6acin rai da kunci.

"Ummy kin isa damu mana amma gani nayi wannan..."

Dakatar dashi tayi ta hanyar dagamashi hannu.

Shiru yayi yana kallonta da idanunshi dasuka fara kadawa, yanajin zafi sosai azuciyarshi

"Idan maganar dazaka cigaba dayimin kenan kindly leave, kokuma ni inbarma wurin":tafada tana kallonshi strictly.

Sadda kanshi kawai yayi bece komaiba zuciyarshi na suya sosai, jiyake kamar yaita kuka ko zaiji sassauci.

Ko gefenshi bata qara kallo ba harta gama cin abincinta ta tashi takoma falo tabarshi awajen.

Haka ya zauna shiru a dining din, shikadai yasan yadda yakeji azuciyarshi, jiyake kamar yaita watsa kayan kan dining table din ko zaiji sauqi.

Jin ana kiraye kirayen sallar asr yasashi tattaro kingin kuzarinshi yatashi yana qoqarin wajen ganin yayi controlling din kanshi.

Falon shima yadawo inda ya tadda ummy zaune remote a hannunta.

Zama yayi kan wata kujera dan nesa da ita batareda ya dagoba yace
"Ummy zan tafi masjid"

Itama batareda ta kalleshi ba tace
"To allah ya tsare"

Tashi yayi yana cewa amin sannan ya nufi kofar fita yana ayyana shida gidan nan kuma sai baba tagani tunda babu mai sonshi agidan.

Direct motarshi yanufa yashige ya tada yabar gidan.

Tanajin fitar motar ta ta6e baki tana cewa
"Kafi ruwa gudu" itama ta tashi ta haura sama don haramar sallah.


Masjid yafara biyawa yayi sallah sannan yawuce gida.

Ranar dai haka yawuni rai adagule gashi fushi yake da sadeeq bare yakirashi yadanji sanyi, kodayake yanama iya kiranshi yafara 6a66akamashi wannan dariyar tashi ta mahaukata gwara ya rarrashi kanshi da kanshi amma yadauki alwashin bazai qara zuwa gidanba da sunan abashi saudart, yabarmasu su cinyeta.

Washegari ma haka ya tashi rai adagule, sadeeq tunjiya yake kiranshi amma yaqi dagawa don haryanzu fushi yake dashi, ummy kau saidai yakirata suka gaisa kawai don yariga ya qudura aranshi yayima gidan yaji bazasu qara ganinshiba saisun nemeshi dakansu.

Ranarma haka yawuni cikin kunci, ganin abin yayimashi yawa yasashi fita bayan asr yaita zagaye gari bashi yadawo ba sai wajajen 9 din dare.

Ranar ma kamar kingin ranakun haka ya kwana cikin kewar abar kaunar tashi.

Washegari monday tunda wuri ya tashi yafara shirin fita company don jiyayi duk zaman gidan ya fice mashi akai, gwara yafita aikin ko ya deba mashi kewa.


Wajajen 8:30am sadeeq ya iso company din.

Sosai mammaki ya cikashi dayaga wani staff yafito daga office din ashraf don beyi tunanin zaizo ba.

Gaidashi staff din yayi a girmame, amsawa yayi cikin fara'a yana tambayarshi ya iyali.

Fasa shiga office din nashi yayi yanufi na ashraf din ya kwankwasa ya murda handle din yashiga da sallama.

Ko dago kai daga typing din dayake beyiba bare yasaka ran zai amsa mashi sallamar, be damu da hakan ba saima qarasowa dayayi cikin office din yaja kujera ya zauna yana kallon yadda yawani hade rai yana sarrafa system din gabanshi.

Ganin beda niyyar kulashi yasashi jan tsaki yace
"Kaifa dan air ne, ji yadda kawani yi banza dani kamar ba wajenkaba nazo"

Dago kai ashraf yayi ya yimashi kallon up & down sannan ya maida kanshi kan abinda yake.

Ta6e baki sadeeq yayi yace
"Shine naketa kiranka kaqi picking ko?"

Shima ta6e bakin yayi batareda ya tankashi ba.

"Allah dai ya yayemaka wannan baqar zuciyar taka kona huta wlh, kaikam matarka tabani... wai yama naganka a office yau, kaida yakamata ace kanacan kuna honeymoon da sweetien taka?"

Wani mugun kallon yadago ya watsa mashi sannan ya kauda kai

Dariya sadeeq yafashe dashi yana cewa
"Au na manta ashe an kwace matar, hhhhh wannan shi ake kira ga qoshi ga kwanan yunwa, wai ya kuka qare da ummyn? Kashawo kanta din?"

Banza yayi dashi don koyace yayi magana yasan bamai dadi zaiyi ba.

"Kaji? Dakaifa nake"

Nan ma ko kallonshi beyiba bare ya tanka

"Karfa ace kayi surrender ne, lallai ma, to wlh ka zauna kaga zama na rantse, ni i thought ma tun ranar zaka dawo da matarka, ca6! Wlh idan nine idan na yarda intafi tsaye, matar tawa wanda dakyar nasamu bata kufcemin ba azo kuma sake nisantamu salon komai yaqara dagulewa? Ta6!"

Kallonshi ashraf dahar mood dinshi ya chanza yayi yanajin zafin abun aranshi sosai yace
"Na barmata ita, i've promised bazan qara samunta akan wannan case dinba, nabarmata

Please Login or Register in order to submit comment