Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kikazo nuna jindadinki nazama mai sa'ar dazata aureni" ya katseta dafadin haka cikin raini.

'What!' Tafada azuciyarta.

Dagowa tayi ta kalleshi shima ita yake kallo

"No..no ba haka bane..."

"To yayane?" Ya sake katseta

"Kinzone don ki ganni kiji sanyine koko kinzo don kiyi selfie dani asamu abin dorawa a status? Ko kinzo ne don kina buqatar kudi?"

"What!" Wannan karon tayi exclaiming Afili.

"Ok nawa kikeso, Dama nasani Basai kinzoba, nasan Duk macenda wannan opportunity din yasameta saitaji kamar ta kashe kanta don dadi, Saidai dafatan tsohon naki yaga yamiki this is a contract marriage, babu abinda zai shiga tsakaninmu, zan baki kudi, da suna don Daga inda kika aureni kinyi suna Amma bazan baki kaina ba, am not that cheap, babban goro.... Ni mai tsadane, wutsiyar raqumi ke kanki kinsan tayi nesa da qasa, don haka karkiyi crossing limit dinki, yes..as I was saying nawa kike buqata diyar Shamsu?"


Saudart was shocked, dumbfounded, angry and overall embarrassed.

Kallonshi take idanunta na canza launi from pure with to red.

Tunda take ba'a ta6a cimata mutunciba irin na yau.

Bata ankaraba taji saukar Abu a fuskarta, razana tayi tabi abin da kallo inda yafadi taga wrapper yan dubu dubune guda biyu.

"Dauka ki 6acemin" yafada yana maida hankalinshi kan system din gabanshi.

"What!" Taqara exclaiming tana miqewa tsaye...✍

No editing🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





011





"What!" Taqara exclaiming tana miqewa tsaye ilahirin jikinta duk cira yake.

"Me?..." Tafada tana nuna kanta da yatsa hawaye na taruwa a idanunta.

"How dare you? How dare you?!" Tafada muryarta na cracking.

Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa
"Dalla mallama fitarmin a office ko kudin ne basu ishekiba?"


Jiki na rawa ta tsugguna ta kwaso kudaden tana mai yage paper da akayi bundling dinsu.

Be ankaraba yaji watsin kudaden a fuskarshi.

Saurin dagowa yayi yana kallonta a mammakince.

Watsi tafarayi da files din kan table dinshi wanda hakan yasashi saurin miqewa yana kallonta.

"Hey! Kinyi haukane?!"

"How dare you!" Itama ta daka mishi tsawa.

"Ni zaka ciwa mutunci? Who the hell did you think you are?! Uhm? Gayamin!"

Nunashi da yatsa tayi dake rawa don Duk ilahirin jikinta rawa yake abinka da mai zuciya.
Ga hawayen dasukaqi Tsayawa.

"Kayi kadan, kayi kadan ka wulaqantani! Kayi kadan nabika, me kake dashi dazan bika? You have nothing! Ni ba kallon namiji nake makaba don bakakai akiraka da namijiba haka zalika bakakai darajar maceba.
Yes nazo nan don maganar contract whatever, Amma ba don komai ba don infadama bakakai standard din zaka mallakeniba koda daidai da second dayane.
Bakada wannan quality din, and also kudinka basu isa susani kallonkaba saboda I don't fucking care about your goddamn money! Kai suka Dama ni ko ajikina, lastly kasan wanda zaka dinga ma wulaqanci domin yayinda wasu ke binka kamar yadda kake ikirari wasu ko sanin ka wanzu a duniyarnan basuyiba"

Ashraf dayayi mutuwar tsaye beko motsi yakasa cewa komai don he never expect this.
Dakyar yabude baki yana nuna kanshi da yatsa

"Ni? Kinsan koni waye?.."

"Go to hell! To hell with you and your personality, bansan ko kai wayeba kuma I don't fucking care!" Ta ida atsawace hawaye na gudu afuskarta sosai kamar Wanda aka laqadama shegen duka.

Daukar handbag dinta tayi sannan ta watsa mishi wani kallon tsana da rinnanun idanunshi tabuga tsaki tareda fadin "Bloody idiot"

Fuu tafice tana banging kofar da karfi.

Har tsakar kanshi yaji tsakinta da zagin dakuma bugawar kofar.

Bin inda tabi tafita yake da kallo kamar haryanzu tana wajen, zuciyarshi inbanda bugawa babu abinda take ga wani suya na musanmman da take.


Daidai yafito Daga office dinshi dauke da files yaga wucewarta dagudu.
Saurin binta yayi Amma ina harta shige elevator.

Tsaki yaja cikin takaici, saida fa yayi warning Ashraf karya cimata mutunci, a fusace ya nufi kofar office din Ashraf da niyyar rufeshi da masifa.


Turus yayi ganin yadda office din yakoma kamar na mahaukata, ga Ashraf gefe be ida dawowa hayyacinshiba.

"Ashraf?" Yakira sunanshi yana dafa kafadunshi Bayan ya qarasa wajenshi.

Dagowa yayi ya kalleshi, gaban sadeeq yafadi ganin yadda launin idanunshi suka canza.

"Ashraf menene? Meya faru?" Ya tambayeshi a rude yana kamo hannunshi.

Fizgewa yayi cikin zafin nama yana watsa mashi jajjayen idanunshi dasuka koma kamar gauta.

Hanyar toilet yanufa cikin sassarfa yabude yashige sannan shima ya turo kofar da karfi.

Sadeeq tsaye yayi yana kallon ikon Allah, 'to me yafaru?' Abinda yaita tambayar kanshi kenan.






Dagudu taqarasa wajen motarta tashige, kifa kanta tayi kan steering tana cigaba da kukanta.

'Dama wannan ne daddynta keson ta aura? Lallai'

"Shine kikazo yimin godiya Dana za6i inyi hakan da mahaifinki?" Maganar Ashraf yashiga amsa kuwa a kunnenta

"Koko kinzone don muyi selfie kisamu abin dorawa a status?"

Cizan yatsanta manuniya tayi da qarfi hawaye nazuba.

Bata ta6a danasanin yin Abu a rayuwar taba kamar yau.

Lallai aikau Duk abinda daddy Saidai yayi don wlh bazata ta6a yarda da buqatarshi ba.

Afusace ta tada motar tadau hanyar bakery dinta.



**********************************

Yau 'yan bakery sunci ubansu don rikitasu Saudart tayi, Abu kadan saita rufe mutum da fada kamar zata cinyeshi, sunsha mammaki, matarda ba ruwanta tashige cikin ma'aikatanta Ayi raha Ayi fira? Ko maryam P.A dinta tsoron tunkararta take da magana don sau biyu kenan tana masifeta.

Haka yau bakery yazama ba dadi don kowa yasan yau ran boss a6ace yake hakan yasa kowa ke taka tsantsan daita.



Koda aka tashi ficewarta tayi batareda sunyi sallama kamar yadda ta sababa.

Kawai haryanzu haushi takeji, ga maganganunshi sai eoching a kunanta yake.


A dining ta iske daddy yana cin abinci, gaisheshi kawai tayi ta haura sama unlike da dazataita binshi a marairaice.

Hakan yasa daddy sanin Duk yadda akayi anta6otane don idan Saudart tayi zuciya bakyau, abinka damai hqr.





"Ashraf Wai Meya faruwane, kavarni ina 6a66atu kamar wani dan iska" inji sadeeq afusace.

Ko motsawa Ashraf beyiba Daga balancing dayayi a kujera idanunshi lumshe.

"Ashraf!"

"What?!" Ya fada a tsawace kamar wanda aka tsakura.

"Wai meke damunka Ashraf?" Inji sadeeq cikin mammaki.

"You know what? Nakusan maqureka a office dinnan wlh, ina ruwanka dani? Spare me mana, aah aah?" Yafada afusace.

"Kaifa dan iska ne wlh, mekayiwa diyar mutane tafita tana kuka"

Harara ya dalla mashi yace "sainaji shaquri sannan, mtcheew, abeg kira wannan tsohon banzan kace wlh nanda kwanaki uku idan bezoba zanyi cancelling din deal dinmu ne"

A mammakince yace "meyasa?"

"Shine nace sainaji qarfin maqara, get out abeg!"

Ba yadda ya iya ya tashi ya fice don yasan halin mutumin nashi.

Jingina yayi da kujerarshi yana d'an jujjuyawa "hmm you're in hot soup, I swear" yafada yana tauna le6en qasa...✍




Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annoba (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




013



Kwanaki biyu kenan rabonda tasa daddynta ido, sanda zata fito bayanan bata kuma sanin dawowarshi.

Yau ranar Alhamis, as usual tadawo Daga aikine agajiye.
Dakyar ta iya kai motar wajen parking tayi parking.
A kasalance ta fito ta rufe motar.

Wata mota tagani a parking space din Wanda ba tasu bace.

Tsayawa tayi tana kallon motar taba tunanin to ta wanene?

Wucewa tayi ta murda kofan falon tashiga da sallama.

Tarin dataji Anayi ba qauqautawa ne, yasata jin ta wartsake nan take.

"Dad?.." Tafada idanunta waje.

Da sauri tanufi part dinshi tana kwala mishi kira.

Murda kofar tayi tashiga, Turus tayi tareda saurin rufe bakinta da tafin hannu.

Dad ne kwance yana tari kamar na fitar rai ga doctor ya duqufa kanshi yana qoqarin shawo kan tarin.

"Daddy!" Tafada da qarfi tayi wurgi da handbag dinta taruga wajenshi.

Kamoshi tayi tana kuka ganin yadda yake tarin Duk ilahirin jikinshi rawa na rawa.

"Nashiga uku daddy, doctor what's happening to my daddy?" Tafada cikin kuka sosai.

"Please miss Saudart kiyi hqr kifita"

"No!" Tafada tana qara rugumoshi tana kuka sosai.

"Please kinaso muyi loosing dinshi? Kibari nayi aikina"

Jin hakan yasata janyewa Amma still tana kuka.

"Kifita please, kijira waje, komai zaiyi daidai insha Allah"

Badon tasoba tafita tasamu wata kujera ta zauna tana kuka.

Meke damun daddynta? Dama bayada lfy? Tun yaushema yafara rashin lfy? Anya kau ta kyautama kanta? Ace mahaifinta suna gida daya Amma harya kwanta ciwo bata saniba?

Haka taita jerama kanta tambayoyi tana kuka.

Bayan kusan mintuna ashirin sai gashi doctorn yafito yana yarfe gumi.

Da sauri tamiqe tana kallonshi

"Doctor ya yake? Is he fine? Please tell me he is, please"

"Miss Saudart, ki kwantar da hankalinki please, zauna zamuyi magana"

Zama tayi hawaye nabin kuncinta

"Saudart garin yaya kuka barshi har yakai wannan stage din batareda kun kaishi asibitiba?"

Kan Saudart yasake kullewa

"Doctor meke damunshi ne? Wlh bansan baya lfy ba"

"Really? Kuma kuna kwana under roof daya ace bakida masaniya akan lfyanshi?"

Kasa amsawa tayi sai kuka.

"Well am sorry, Amma daddynki yakamu da ciwon zuciya"

Waro dara daran idanunta tayi tana toshe bakinta da hannu tana girgiza kai unbelievably

"No, it can't be"

"Yes miss Saudart, daddynki yakamu da ciwon zuciya sanadin damuwa, damuwa tamishi yawa har yayi sanadin stressing din zuciyarshi yanzu haka gab take da bugawa"

"No!!" Saikuma tafashe da kuka abin tausayi.

"Nashiga uku ni Saudatu, daddy idan katafi kabarni ya zanyi?"

"Bazai tafiba insha Allah idan kuna kiyayewa, Ku kiyayi 6atamishi rai, Ku dinga yimashi abinda zai faranta mishi, sbd next time yasamu wani attack din sai Allah"

Kuka take afujanjan, badai akan wannan auren contract dinba yakamu da ciwon zuciya ba? Badai tasoshi gaba yan banki sukayi ba? Ita Saudart ina hankalinta yatafi ta za6i tayi nisa da daddynta a lokacin dayafi buqatarta? Kaico.

"Ga magunguna can na ajiye a bedside locker akwai prescription dinsu ajiki, a dinga kulawa da maganinshi and I repeat aguji 6ata ranshi"

Daga haka yayi mata sallama yafice.

Ta dade zaune awajen tana kuka sannan ta lalla6a ta tashi tashiga dakin daddyn.

Ahankali taqaraso wajenshi tana kallonshi, kukane yakusan kufce mata tayi saurin dade baki don karta tadashi.

Zama tayi gabanshi ta riqo hannunshi tana murzawa ahankali.

"Dad ka yafemin, nakasa share maka hawaye ka yafemin" tafada cikin muryar kuka.

Saida tayi mai isanta sannan ta share hawayenta.

"Daddy insha Allah bazan ta6a bijirema ba, badai akan bashin bankiba? Insha Allah nizan sharema hawayenka.
Gobe insha Allah zanje in saka bakery na kasuwa, banga amfaninshi ba idan inada damar siyar wa in taimakekaba. Insha Allah damuwar ka tazo qarshe"

Don tsabar takaici jiyayi kamar yabuga uban tsaki Daga inda yake kwance.

Wai wacce iriyar yarinya ce wannan mai kunnen qashi? Wato har lanbon ciwonma bazai sata Amincewa da qudurinshiba? Tsaki yaja azuciyarshi, jiyake kamar yatashi yaita kifeta da Mari.
Wai bakery? Ana batun arziqi waketa tsinannen bakery can.

Haka taita sabbatunta shikau sai qumuwa yake da takaici Saidai ba halin yako motsa.

Aka ta kwana tana kulada Alhaji

Washegari kau tayi waya dawani wanda tasani akan maganar siyarda bakery dinta.

Saidai me? Duk inda akaje Saidai ayimasu tayin wulaqanci.

Tun tana daukar abin wasa har abun yafara bata tsoro, kwata kwata highest din tayin 5million.

Sosai tashiga damuwa, Duk inda akaje Saidai suce ai yanzu abubuwa sun rage daraja, corona virus.


Abinda batasaniba, daddynta ne keda sa hannu awannan abin, shi yasa akebin kwakwafinta Duk inda taje siyar wa saisu saye mutanen akan suyimata tayin wulaqanci.


Saidai naci da taurin kan Saudart yaqi bari ta hqr.

Ganin wankin hula na naiman kaishi dare yasashi watarana burkuce mata, aman jini yadinga yi ba kakkautawa.

Hankalin Saudart yatashi ainun idan banda kuka babu abinda take.

Koda takira doctor fada yayita mata kan idan Alhaji yamutu itace.

Haka taita kuka ganin dai babu sarki sai Allah tafara sabbatu.


"Wlh nayarda, nayarda zanyi auren, please kace yatashi"

Saura kadan Alhajin yabuga tsalle don dadi.

"At last, at long last" yaita nannatawa aranshi.


Tofa? Burin Alhaji shamsu fah yacika, zaizamo sirukin Sir A.A 😅

Cikin kwana biyu ya warke sumul sai nan nan yakeda Saudart, itako kwata kwata tarasa abinda kemata dadi.

She can't believe ta yarda da AUREN KWANGILA da wannan monster dinba.

Jitake Dama mutuwa tayi tahuta.

Ada batasan qiyayyaba, ko wuqa aka samata awuya akace tafadi maqiyinta daya bata iyawa.

Amma yanzu qiyayar datakema Ashraf bata misaltuwa, shine sanadin rugujewar farincikinta, shine silan rushewar burinta na aure mutu-ka-raba, uwa uba shine silan sa6awa ubangijinta.
She soo much hate him. With passion.



MONDAY


Su Alhaji shamsu yau ko barci ba'a komaba Bayan asuba, sai shirin ganawa da A.A ake.

Yau za'ayi signing din contract din auren...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, Karka barmu da kanmu🤲



Wannan page din nakune Mamman mama, sis hajara, Maman Ameerah, maman areefullah and lastly sisto ta ummie amaryar baba sama'ilanta😜

Ina yinku irin wujiga wujiga dinnan, nagode da addu'oinku gareni🙏

Ga page nan nakune kuyi yadda kukaga Dama dashi🤷‍♀




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)



014





Kwankwasa kofarta da'akayi ne ya tsaidata Daga shafa man datake.

Hijabi tazura tanufi kofar tabude.

Fuskar daddynta yayi mata maraba washe da fara'a.

Itama washe fuskarta tayi tana matsawa gefe don yashigo.

"A'a? Inyee? Dad wannan hadewa haka kamar wanda zaya gana da president?"

Dariya yayi sannan yace
"Ai wanda zamu gana dashi dinma yakai President dinma koma yafi sbd shi gumin kanshi yakeci bawai na al'umma ba, besides yanaga baki shiryaba?"

"Wlh Dad yanzu zan shirya, ai duka yanzu eight fa, inada sauran time"

"Bamuda time shalele, we ought to be there by 9"

"Wai Dad sai cewa 'mu' kake, dawa dawa?"

"Ni da ke mana"

"Tofa? Fita zamuyi Dama?"

"Mtcheew, kin cika shirme shalele, nufinki bakisan yau zamuje signing din contract dinba?"

Sororo tayi tana kallonshi

"Contract?"

"Mtcheew, Wai meke damunki ne, nufinki bakisan yau ake signing din AUREN KWANGILARKU BA"

Gabanta ne yafadi, dagaske kenan aurennan will push through?

"Kinyi shiru?"

"Dad yanzu fisabillilah kai zakaje shi bazai zoba, Dad indirectly zuwa tallana fa kake"

"Ya ilahi Saudart, don girman Allah kibar maido hannun agogo baya, Nike nema wajenshi so nizan je" yafada cikin Fushi.

"To Allah ya tsare, nikam bani zuwa, kuma please daddy karkace zaka tilastani don Dama auren bawani kwanta min yayiba" tafada tana zama gefen gado ta cigaba da shafa kafanta mai.

"Shalele ni kikema haka don kinga ina Neman Abu awajenki?"

Kamar wanda yacema tafara.

Aikau saita fashe da kuka, harda shesheka kamar wanda akayima tsinannan duka.

Sakin baki Alhaji yayi yana kallonta.

Ganin abin nata bana qarewa bane, saiya zauna kusada ita yajata jikinshi ya hau rarrashi.

"Shikenan Shikenan, Basai kinje ba, kibar kukan haka, kiyi shiru please"

Dakyar yasamu tayi shiru sannan yafice yatafi shi kadai.

Tashi tayi Bayan fitarshi.
"Ca6di! Wlh bana fatan wani Abu yasake hadani da wannan jerk din, tsinemin akayi?"

A gurguje ta shirya itama tafice bakery dinta.







***********************************************




"No way! Wannan Abu mu uku yashafa, don haka mu uku zamuyi sign kamar yadda kagani a paper"

"Nasani Mr A.A Amma kamar yadda na fadama bata jindadi ne, da daita zanzo"

"To sai abari saita warke sai Ayi, yanzu kai kayi sign din naka, idan ta warware saitazo tayi nata sannan zakaji alert" inji Ashraf da yake ganinma Alhaji shamsu yayi mugun raina mishi wayau.

Shiru Alhaji shamsu yayi yana tunani

"Look is not as if ina tilastama neba, idan wannan abin bazai yiwuba abarshi please"

"No..no bahaka vane Mr A.A, kawo inyi signing, insha Allah zuwa gobe idan ta warware zatazo tayi nata"

Yafada yana amsar paper, ya karanta sharuddan kamar dai yadda Dama yasani sannan yasa hannu wajen da yakamata yasa.

"Gashi insha Allah gobe zataso" injishi yana miqama Sadeeq da tundazun ko A bece ba.

"To Allah yakaimu" inji sadeeq while Ashraf yawani lumshe idanu kamar maijin barci.


Bayan tafiyarshi sadeeq ya kalli Ashraf da idanunshi ke lumshe haryanzu.

"Wai! Gaskiya yarinyar nan yar jin kai ce,komai saitaja aji?"

"Get out!"

"Toni menayi kuma?" Yafada cikin dariya.

"Kasan Allah ubanka zanci, nace out!!"

Harara ya galla mashi sannan yafita yana gunguni.






*************************************
WASHEGARI



A kasalance take shirinta nayau, haryanzu abinda yafaru tsakaninta da Dad jiya yaqi sakinta.

Sosai jiya daddy ya burkuce mata jiya don tace baza taje tayi sign ba.

A jiya tasan dayan 6aren daddynta, don be raga mataba tatass yamata abin ba dadinji.

Bata ta6a tunanin akan dan Abu irin wannan dad zai mata tijara irin najiya ba.


Don dole ta amince zataje don bazata iya da masifar Dad ba.



Shirya wa tayi cikin wani sky blue Arabian gown ta nade kanta da gyallen rigar sannan ta rataye side bag dinta sky blue.

Masha Allah tayi kyau musanmman data kwama baqin shade a idanu mai taken NO RESPECT.

saukowa tayi ahankali, a dining ta ga dad zaune yana kari, kallo daya yayi mata ya dauke kai.

Murmushi tayi taqaraso wajenshi tana cire glass din idonta.

"Good morning dad"

"Morning" ya amsa kamar mai ciwon baki.

Jawo plate din gabanshi tayi tasaka fork itama tanaci.

Ci kanki bece daitaba.

Ganin haka yasa ta dago ta kalleshi a marairaice.

"Dad!"

Shiru

"Dad don Allah kayi hqr, fushin ka agareni masifa ce"

Nanma shiru.

"Please Dad Kaga Daga nanma can na nufa, kayi hqr"

Dukda yaji dadi Amma ko nunawa beyiba saima banza dayayi daita.

Kuka tafara ahankali, saurin dagowa yayi tareda jawoya ajiki yana rarrashi don ga yadda tayi kyau dinnan beson tayi kuka kwalliyar ta6aci🤔

"It ok sweetheart, ya isa please, na haqura"

Shima saida yasha fama sannan ta hqr.

Har mota ya rakata yanata samata albarka.

Shiga tayi ta dagamashi hannu sannan ta tada motar ta fice cikin tuqi mai burgewa.

Naunnauyan ajiyar zuciya Alhaji yasaki yana girgiza kai, Saudart? Hmn halinta sai ita.







Tuqi take tana saqe saqe, she can't believe Wai zuwa zatayi tayi signing din aurenta da wanda kwata kwata besan darajar mutane ba.

Lallai, aikau yau she won't take shit, idan yayimata ramawa zatayi don ba tsoronshi ba takeji.

Tsaki taja, yanzu me zeta cemishi idan taje? Nazo signing din contract din auren mu? Mezai dauketa? Mai binshi din dagaske? Gashi tagama ikirarin bekai standard din mallakarta dadai da second dayaba, nezai dauketa yanzu?

"Kai wlh daddy kagama dani!" Tafada tana dukan steering

Saudart Nada sanyin hali Saidai bata jurar wulaqanci, Duk yadda kuke daita ka nemi raina mata wayau yanzu kunyi sama Ku tiqo qasa.

Tanada hqr haka kuma tanada zafi sosai, shiyasa ko a qawaye shakkar 6atamata rai ake.


Danna hancin motarta tayi cikin harabar company din Bayan an wangale mata gate din.

Yau company din bewani yimata kyau ba.

Tafi minti biyar amotar takasa fitowa kawai fargabar shiga take, dayake ruwa ruwace har hawaye sunfara kwanciya a kwarin idanunta.

"Dad ka gama dani, ka gama dani" haka taita nanatawa.

Saida ta tattaro sauran jarumtarta sannan ta bude murfin kofar tafito ahankali....✍


Sorry nasan yayi kadan ba chaji🙏


Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





015






Maida murfin kofar tayi tarufe sannan ta kulle motar.

Zaro baqin shade dinta tayi ta qwama a fuska wannan yakusan rufe Rabin fuskar sannan ta gyara zaman side bag dinta.
Ahankali cikin wani taku tanufi main entrance din.

Sanitizing din hannunta tayi sannan ta shiga ciki.

Direct elevator tanufa don ta riqe number floor din.

Cikin yan daqiqu abin yatsaya alamun anzo.

Ahankali tasanyo kafa tafito elevator din gabanta na bugun uku uku.

Allah yasani dauriya kawai take don zuciyarta fall take da fargaba.

Kamar kwanaki, Helen nanan mazauninta anci gayu cikin Riga da 6ingil din skirt, ga tulin gashin doki data tilama kai anmata style din baby face dashi.

Fuska a tamke ta qaraso wajen wanda qamshin turarenta ne ya fargar da Helen zuwanta.

Gaban Helen ne yafadi datayi tozali da wata unique super duper cutie, dukda shigarta simple ce ba qaramin kyau tayiba, gashi bawani kwalliya tayiba Amma kyan datayi baya misaltuwa.

"Is your boss around?" Inji Saudart cikin tsantseni.

"Yy..yes"

"Ok? Tell him yayi baquwa"

Tafada tana zama kan daya Daga kujerun wajen ta Dora kafa daya bisa daya.

Shiru kamar bazata tafiba, saikuma tatuna da haduwarsu na ranan, dan haka ta tashi tanufi office din.

"Yes? Come in" inji sadeeq dake tareda Ashraf yana nunamishi wani project dazakuyi presenting a wani meeting.

Helen ce tashigo jiki a sanyaye.

Gaishesu tafarayi sannan tace "sir kayi baquwa?"

"Who?"

"I don't know her name Amma seems Sir sadeeq yasanta"

Kallon juna sadeeq da Ashraf sukayi

"Ni?"

"Yes sir, wannan lady din ta ranan?"

Waro idanu yayi

"OMG!she's here, Alhaji shamsu's daughter, she made it at last" inji sadeeq cikin murna.

Kunya da takaici Yakama Ashraf, ji yadda yake Neman zubda mashi aji gaban wannan arniyar?

"Je kice tashigo" inji sadeeq da bemasan Ashraf nayi ba.

Juyawa tayi a ladabce

'Alhaji shamsu's daughter? Dama diyarshi ce?' Abinda yaita yawo azuciyarta kenan.


Yadda ta barta haka ta taddata sai wani kada kafaffu take ahankali.

"Kina iya shiga" inji Helen tana mata wani kallo marar fassara.

Ko a jikinta, ta tashi cikin nutsuwa ta gyara zaman kayanta sannan tanufi office din.

Ahankali ta bubbuga sau uku, sadeeq ne zaije ya bude mata Ashraf ya riqo hannunshi.

"Dan ubanka idan wannan rawar kan zakayiman zan koraka, idiot"

Sake bubbugowa akayi, ganin Ashraf Beda niyyar amsawa yasa sadeeq kware baki yana cewa
"Come in"

Ajiyar zuciya tasaki sannan ta runtse idanunta ta murda kofar ahankali, tashige.


"Ya subhanalillah!" Inji sadeeq cikin zuciya dayayi tozali da Saudart.

"Wow! Ta hadu ta hadu ta hadu!!!" Duk a zuciya yake zancenshi azahiri kuwa murmushi yake mata.

Shikau gogan kamar yadda kuka zata kanshi nakan system din gabanshi.

Sallama tayi ciki ciki, amsawa sadeeq yayi cikin fara'a yana mata iso.

Ashraf kamar ya shaqeshi don takaicin yadda yake wani rawar kafa.

A yangace tanufo kujerar da sadeeq yaja mata idanunta akan Ashraf Amma kasancewar baqin glass na idanunta ba'a ganewa.

Zama tayi ahankali sannan ta Dora kafa daya bisa daya.

"Ok boss, zan tafi in ida arrangement din" inji sadeeq yana tattara files din.

'What?' Yafada azuciyarshi, Amma mugun dan air ne sadeeq, nufinshi barinsu zaiyi su kadai.

Be ankaraba yaji qarar rufewar kofa alamun harya fita.


Wani irin shiru office din yadauka, itama kanta Saudart bataso tafiyar sadeeq ba don da niyyarta ta tambayi ina file din wajenshi tayi sign tafice don vataso ko kalma daya ya hadata da Ashraf.

Kusan mintuna biyar Amma shiru babu wanda ya motsa cikinsu, shi yana danne danne a system, ita tana shafe shafe a waya.

Minti biyar...Goma...Sha biyar Amma still ba wanda ya motsa.

Kowanne jira yake dan uwanshi yafara motsi.

Saudart takaici kamar tayi kuka, saitayi kamar tayimashi magana saikuma tafasa.

Shima hakan take a wajenshi, jiyake kamar yayi me?

(Ni Duk nafisu jin takaici, Wai wannan wane irin wulaqanci ne zasu barni sagale da Biro a hannu😠)


Ganin wankin hula na naiman kaita dare yasata motsawa, ahankali cikin yanga mai tattare da jin haushi tace
"Bani paper din inyi sign, Inada abinyi"

Murmushi Ashraf yayi cikin zuciyarshi, at last ta karaya.

Dago sharp cat eyes dinshi yayi ya doramata su a karo na farko tunda tashigo.

Ko seconds biyu beyiba yakuma dauke kai yacigaba da danne dannenshi.

Kutt! Lallai ma

Tashi tayi da niyyar ficewa don bazata iya jure wulaqancin shiba.

"Kina fita deal cancelled" yafada still hankalinshi kan computer

Dakatawa tayi zuciyarta na suya, gaskiya Dad yagama daita, wannan wulaqancin har ina.

Juyowa tayi tana kallonshi Jitake kamar ta rufeshi da duka.

"Look mallam inada abubuwan yi, let me sign the damn paper and leave"

Dagowa yayi Daga system din tareda komawa yayi balancing sosai a kujerar kamar irin dan sarkinnan.


Zubamata cat eyes dinshi yayi ya qureta da kallo.
Dukda glass din idanunta sun kareta Amma hakan be hanata jin tsinin idanunshi ba akanta.

"The paper?!" Tafada tsakankanin haqora cikin jin haushi don ko motsawa beyi yawani zubamata na mujiya.

"Paper? Which paper?" Ya tambaya cikin isa.

"Wanda kayi blackmailing din Dad na dashi mana, kabani inyi signing inyi tafiyata"

"Ba haka dad dinki yayi sadda yazo jiyaba, he begged for it, so kema ki roqa idan kinaso idan kuma bakiso?.." Saiya Daga kafadu sama alamun fine🤷‍♂



Shiru tayi tana kallonshi unbelievable, ta roqa? Yadda daddynta ya roqa? Kenan daddy strooping low yayi ya roqeshi? Innalillahi Dad yagama da ita.

Hawaye taji yana naiman saukomata, ga wani nauyi da zuciyarta tayi.

Qoqarin maida hawayen take don bataso yaga saukarsu yayinda tsanarshi sai qara farashi yake azuciyarshi.

"Miss shamsu, kina 6atamin time, beg me to marry you" yafada yana jindadin moment din don yasan ba qaramin wulaqanci yake shufka mataba.

Yasan babu yadda za'ayi tayi rejecting dinshi ko don daddynta, don Duk yadda akayi harta yarda yanada masaniya akai kuma yasan yanzuma forcing dinta Alhaji shamsu yayi hartazo.

Lumshe idanu Saudart tayi tana qoqarin saita muryarta

"Look, you don't have the idea of how I hate you, stop pushing it, give the paper let me sign and leave, am suffocating here" tafada muryarta nadan cracking.

Tashi tsaye yayi ya tako ya zagayo gabanta cikin takun qasaita.

"Really? Kin tsaneni Amma kikazo Neman aurena? Wannan wacce iriyar tsana ce"

Hadiye wani Abu daya toshemata maqoshi tayi kafin tace
"Ba aurenka nazo nemaba, albarka mahaifi nazo nema don nasan darajarshi da matsayinshi if not ko sanin da wanzuwarka bazan yiba bare ko kallo ka isheni" tafada idanunta na qara durar ruwa.

"Then ki nemi albarkar dakyau, kiyi biyyaya gareni kamar yadda uban naki yayi, beg!" Ya ida zancen cikin rad'a


Kasa riqe hawayen tayi, saurin kauda kai gefe tayi don karyagansu.
Jitake kamar tamutu don takaici.

Murmushin gefen baki yayi na mugunta ganin tana hawaye, Dama ya dauki alwashin saita raina kanta haduwarsu nagaba.

"Kinada minti daya kacal kiyi abinda yakawo ki ki fitarmin office don numfashinama sarqewa yake saboda odour"

Lumshe idanu tayi tana qara bama hawayenta damar gangara.

Shiru tayi atsaye still idanunta lumshe.

"10 seconds to go" yafada yana kallon agogo Bayan yakoma yayi balancing a kujera yana kallon yadda take hawaye.

Jan hanci tayi sannan ta goge fuskarta da hanki.

"Mr A.A kabani paper inyi signing.... Please" tafada tana sake lumshe idanunta tacikin glass.

Wani dadi Ashraf yaji jin tace please.
Amma saiya wani dago yana kallonta.

"Ban

Please Login or Register in order to submit comment