Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ta juya tana kashe gas din tana hamdala a zuciyarta


Jin takun ummy na tunkaro falon yasashi saurin gyara zama ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana dannawa.

Sosai ummy tayi mammakin ganinshi amma sai ta basar tanufo cikin falon tana tsuke fuska

Dagowa ashraf yayi daga wayarshi ya kalli saitin ummy dake tahowa ya Dan sakarmata murmushi yana maida wayar a aljihu.

Zama ummy tayi tana kallonshi tana qara nazarinshi ganin yadda fuskarshi ke fayau bawani alamun damuwa unlike jiya ranan dayabar gidan rai 6ace.

Zamewa yayi qasa ya gaidata cikin girmamawa kamar yadda yasaba.

Amsawa tayi ba yabo ba fallasa tana dauke kai don tayi tunanin maganar ranan zai sake dauko Mata


Ganin yakoma ya zauna batareda yace komaiba saima maida hankalinshi dayayi a t.v yasata cewa
"Yaushe kashigo?"

"Ban dadeba" ya amsa a gajarce

"Wannan fa? Na wanene?" Tafada tana nuna trolley din dake tsakar falon

"Oh.. Nawane, yanzu zan wuce dashi ciki" yafada batareda yanuna yaga kallon datake Mashi ba.

"Naka? Tafiya zakayi?"

Dan murmushi yasaki ya girgiza kai yace
"A'a kayana anjima zan kaisu apartment dina"

Sai yanzu tagane inda ya dosa.

Lallai kenen shima yadawo nan da zama yake nufi ko me?

Aikau in yasan wata besan wata ba.

Bata qara cemashi komaiba itama ta maida kallonta kan t.v don Tama fasa zuwa tado baby din tinda saudart na kitchen


Haka suka cigaba da zaman kurame har saida sukaji motsin saudart ta fito daga kitchen din hannunta dauke da warmers.

Caraff suka hada ido tayi saurin dauke kai tanufi dining tana doddorawa akai

Binta da kallo yake harta gama doddorawa takoma kitchen din

Janye idanunshi yayi daga binta da kallon dayayi ya maida kan ummy, cikin taushin murya yace
"Ummy ina maid dinmu ne?"

Batareda ta kalleshi ba tace
"Ta tafi kasuwa"

"Baby fa?"

"Tana sama" ta amsa a taqaice

"Doing what ummy?"

Dagowa tayi ta gallamashi harara tace
"Bansàniba"

Dauke kai yayi yana dan turo baki sannan qasa qasa yadda yasan zataji yace
"Kowa nata hutawa sai matata akabari da aiki"

Dan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta janye idanunta ta cigaba da kallonta


Haka saudart taita fitowa tana jera dishes din dukda duk acikin qarfin hali takeyi saboda yadda take junta very uncomfortable saboda kallon dayake binta dashi

Saida tagama komai sannan ta qaraso falon adarare

Dagowa ummy tayi ta kalleta cikin fara'a tace
"Yauwa Yar albarka, kin gama ko?"

Murmushi tadan Saki tana sinne kai

"Sannu to, kije kiyi haramar zuhr naji anata Kira"

Kada kai tayi kawai, kamar zata wuce saikuma tadan juyo saitin ashraf daya maidata mirror tundazu.

Janye idanu tayi sanaddiyar hada idon da sukayi, cikin calm voice dinta tace "ina yini" tana dan russunawa

Wani farinciki ya ziyarci zuciyarshi nan take hakan yasakashi sakarmata murmushi yana cewa
"Lfy.. Sannu da aiki"

Bata amsa ba sai wucewa datayi tana jinta so uncomfortable saboda shigar dake jikinta dukda yanzu ta yafa gyalle Wanda dama aiki yasata cireshi a kitchen.

Saida ta haye sama sannan ummy ma ta tashi itama ta haura saman batareda tace mashi komaiba

Murmushi yayi sannan shima ya tashi ya nufi trolley dinshi yaja yafice yanufi apartment dinshi yana tafe yana cilla keys dinshi sama yana cafewa zuciyarshi fess.

Da sallama yashiga dakin jaye da trolley dinshi

Dakin bawani datti don ana gyarashi koda bayanan bare dama yan kwanaki yayi rabonshi da dakin.

Ajiye trolley din yayi kawai yanufi bathroom ya dauro alwalla a gurguje yafito don har Ana shirin kabbara sallar

Koda aka gama sallar yadan jima be dawoba.

Lokacin daya dawo duk suna dinning da alamu abinci sukeci.

Qarasowa yayi cikin takunshi na qasaita idanunshi kafe da saudart da kanta ke qasa tana jujjuya spoon dinta a abinci

Zuwa yanzu ta chanza shigarta zuwa deep blue Arabian gown buba wadda hannun yadan tsuke a daidai gwiyagun hannayenta, sai adon fararen tutar flowers da aka jera round din wuyan rigan, sai veil din rigar data yafa simply akanta.

Tayi kyau sosai dukda bawani kwalliya tayiba amma glowing din fatarta kadai abin kallone da sha'awa.

Saida ya qaraso sannan ya janye idanunshi akanta yana jan kujerar dake facing din saudart baya sannan ya zauna.

Dagowa yayi suka hada ido da baby dake shirin kai spoon abaki, wata uwar harara ya gallamata yana kada kai

Sadda kai tayi tana kumburo fuska

"Anan kikafi afki ai, a girka kici" yafada yana ziran plate at the same time yana cigaba da hararanta.

Qara turo baki tayi tadan saci kallon ummy taga abincinta kawai takeci hakama saudart dako dagowa bataiba

Hakan yasa itama maida kanta ga abincin tanaci a sanyaye don saitaji duk ya ficemata akai duk dadinshi.

Itadai saudart tin shigowarshi bata yarda taqara dagowa ba don tanajin yadda idanunshi ke yawo akanta abin har mammaki yake bata, kodai ya manta ummy na a dinning din ne.

Bata ida tsinkewa da al'almarinshi saida yaji yace
"dear serve me mana, yunwa"

Shiru dining din ya dauka don they're all confused sun rasa dawa yake

Gaban saudart yafadi jin yasake cewa
"Kinji wifey? Am hungry" ya qarashe maganar a shagwa6e kamar yadda yakema ummy

Daburcewa saudart tayi yayinda wata matsananciyar kunya ta lullu6eta.

Dagowa tayi ta saci kallon ummy taga kamar ma batasan dasuba don abincinta kawai takeci.

Hakan yasata maida kallon akanshi, kashe mata ido daya yayi sannan yace "kinji?"

Rasa inda zata sa kanta don kunya tayi, tashi tayi kamar wanda aka zarewa lakka tana Satan kallon baby Wanda ta sadda kai tana qumshe dariya da wutsiyar ido sannan ta bude warmern fried rice din kamar zatayi kuka

Turo mata plate din daya zara yayi yana qoqarin danne dariyarshi ganin yadda tayi da fuska da yadda take zuba abincin a daburce

"Yauwa ya Isa hakan" yafada yana janyo plate din sannan ya turamata glass cup daya yana cewa
"Saura drink"

Bata kalleshi ba ta dauki glass din ta bulbula smoothie din dayayi gwanin kyau aciki sannan ta zari wani glass din ta zubamaahi ruwan gora masu sanyi.

Duk tanayin wadannan ne a nonnoqe don wani irin kunyar ummy takeji wanda bata ta6a jiba.

Komawa tayi ta zauna tanajin kamar ta nitse don kunya

Shikau ko ajikinshi saima spoon daya saka a plate din ya debi spoon guda yakai baki.

Lumshe idanu yayi sakamakon karon da abincin yakaimashi harcikin qwalwa, abincin is so delicious kamar yadda look dinshi is so salivating.

"Hummm" yafada yana chewing din abincin ahankali ido a lumshe irin yakaimashi Karo dinnan.

Kasa qumshe dariyarta baby tayi wannan karon saida tafito tayi saurin dafe baki tanayi

Atare suka wurga mata harara ta gefen ido, fuskar saudart kamar mai shirin kuka, jitake kamar taita ihu don takaici

Itakau ummy ko alamun tasan abinda ke faruwa bata nunaba saidai can qasan ranta mammakin rashin kunyarshi take.

Cigaba da cin abincin shi yake hankali kwance yana wani lumlumshe idanu yana humming alamun yana enjoying din abincin

Baby kau dakyar take cin abincin saboda dariyar dake cikinta, musanmman idan takalli fuskar saudart dake blushing don kunya, Allah Allah take su ke6e ta amayar da dariyar cikinta


Saudart kau jitake kamar ta tashi tabar dining din saidai babu dama don tun farko saida ummy ta bigemata warning akan saita cinye wanda ta zuba, gashi ko Rabi bata ciba don tinda yashigo sai cin abincin yazama shiririta


Haka taita tsakurar abincin kanta a qasa feeling very uncomfortable kafin daga bisani ummy ta dauki ruwan gabanta tasha ta goge baki da tissue sannan ta miqe batareda tacema kowa komaiba.

Dan murmushi ashraf yasaki ganin tabar wajen tama hayewarta sama.

Sannan ya maido kallonshi kan baby data nutsu sosai yanzu tana cin abincinta.

Tamke fuska yayi sosai yana kallonta, hakan yasata sauke spoon din hannunta tana kallonshi idanunta rau rau

"Get lost" yafada fiska ba alamun wasa

Tashi tayi da sauri tana daukar plate din abincinta tafice daga dinning area din kamar zatayi kuka.

Saida yagama rakata da mugun kallo sannan yamaido dubanshi kanta.

Haryanzu kanta sadda yake sai jujjuya spoon take acikin abincin

Dora hannayenshi yayi saman table din ya buga tagumi tareda zubamata hazal eyes dinshi kamar yasamu mirror....✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[12/2, 1:42 PM] Aeesha umar aliyu: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻


Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)



094



Qin dagowa tayi dukda yadda takejinta a tsananin takure da kallon qurillarshi ya haifarmata.

Qurawa spoon din hannunta idanu tayi tana sauraron zuciyarta data sauya bugu.

"Saudart..."

Lumshe idanunta tayi ta budesu ahankali don taji kiran har tsakiyar kanta

Kallonta yacigaba dayi yanajin wani irin feelings akanta, jiyake kamar su dawwama a hakan

"Saudart..." Yasake kiranta saidai wannan karonma bata ko motsa ba saima hawayen dataji suna taruwa a idanunta wanda ta rasa ko namenene

"Kinyi kyau... Sosai" yafada yana dan murmushi still idanunshi kafe akanta

Still bata motsaba saima battling datake wajen maida hawayen dake neman zubomata wanda haryanzu batasan dalilin zuwansu ba.

Dan matsowa yayi jikin table din wanda hakan yaqara basu kusanci

Cikin muryar rada yace
"Shin wani yata6a fadamiki ke kyakyawace ta qarshe?"

Bejira amsarta ba sai kamo hannunta dake riqe da spoon dayayi ya riqe da hannunshi na dama ya dafe natan dana haggu yana binta da romantic kallo

Lumshe idanu tayi tanajin tsigar jikinta na tashi sosai

Sake qasa yayi da murya yana cewa
"You're the most beautiful creature that ever exist, and am the luckiest man that ever exist for having such glowing dem as my other half"

Dan matsa hannunta dake cikin hannayenshi yayi wanda saida ta sake tamke idanunta saboda yadda zuciyarta tayi zillo

"And I'll continue to thank Allah for granting me such rare, pure damsel with golden heart..."

Gyaran muryar dayaji daga bayansu ya dakatar dashi daga abinda zai sake cewa ya dan waiwayo don ganin waye

Saurin dauke kai tayi daga kallonsu tace
"Ehm.. Dama ummy ke kiran aunty"

Ganin kallon dayake binta dashi yasata saurin juyawa tabar wajen.

Tashi itama saudart tayi kamar wanda dama ke kan qaya ta zame hannunta daga cikin nashi ta gittashi tawuce batareda ta yarda ta dagoba.

Binta yayi da kallo yayi harta haye sama sannan ya saki slight smile ya maida kanshi akan abincin shi yanaci cikin nishadi.


Saudart kau tafiya take amma jinta take kamar ba a hayyacinta ba take don saida tayi dagaske don kartayi missing din steps tasamu ta ida haurawa sama

Direct dakin baby tashige don bazata iya facing din ummy ba ayanzu.

Taddata tayi zaune gefen gado ta jingina da jikin gadon waya kare a kunnenta.

Ganinta yasata katse wayar tareda sakin ihu mai tafe da dariya.

Saudart ko gefenta bata kalla ba ta zagaya ta dayan 6arin gadon ta kwanta tareda juyamata baya.

Dariya baby tasake fashewa dashi tana matsowa kusada ita tace
"Wuuuu! Love birds, gaskiya abin fa yabada show, wannan soyewa haka? I never knew yaya sharukhan ne sai yau, ca6 gaskiya ne da akace fear silent people, ca6!"

Itadai saudart ko iskar daya kwasota bata kulaba don ko juyowa batayi ba saima lumshe idanu datayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda be dawo normal ba


Haka baby ta tisata gaba da tsokana iri iri harta gaji don kanta ta shafamata lafiya.

Saudart bata tashiba saida taji ana kiran sallar la'asar sannan ta lalla6a ta tashi ta dauro alwalla tazo ta sauke farali sannan tasake komawa kan gadon.

Itadai bazata iya fadin taqamaimai abinda takeji ba saidai tana jinta haryanzu ba daidai ba ga magangganunshi daketa eoching a kunnenta plus qamshin turarenshi daya kasa barin hancinta, wadannan suka taru suka haifarmata kasala tayi lamo a gado bata ko son tashi.

Haka ta qarasa wuninta a daki don kunyar fitowa ta hadu da Ummy take plus batason haduwa da ashraf dukda batada tabbacin haryanzu yana gidan don ita batasan da zancen dawowarshi gidan ba


Zaune take kan sallaya wanda tagama sallar isha'i akai wayarta a hannu tana yan danne dannenta.

Jitayi an bude kofa amma taqi juyowa don atunaninta baby ce

"Daughter"

Saurin juyowa tayi jin muryar ummy saikuma ta maida kanta qasa tana gaidata a kunyace.

Amsawa tayi fiska a sake tana cewa
"Ya baki fito dinner ba?"

Tashi saudart tayi daga kan sallayar tana cewa
"Yanzu zan fito ummy"

"Ok" ta amsa a taqaice tana fita

Ninke sallayar tayi ta maidata ma'ajinta sannan ta zira takalmin soso ta fito.

Ahankali take taka stairs din tana tunanin yadda zata iya zama taci abinci cikin sakewa agaban ummy don haryanzu kunyarta takeji sosai, jitake kamar tace aqoshe take saidai tasan ba dama.

Qarasa saukowa tayi ta nufi dining din kanta qasa

Jin masculine scent din turarenshi yasa gabanta faduwa don she didn't expect it

Dagowa tayi ta kalli saitinshi saita hangi bayanshi kasancewar yaba hanyar shigowa bayane

Maida kanta tayi qasa tana mammakin why yau ya Dade betafiba, koko dawowa yayi? Tabbas dawowa yayi duba da chanza shigar dayayi don kayan jikinshi bana dazun bane.

Ida qarasowa tayi daukeda sallama a bakinta

Duk dagowa sukayi suna amsamata tareda zubamata idanu.

Jan kujerar dake kusada baby tayi ta zauna tana dan murmushin yaqe.

Sannu tayi ummy tareda amsa sannu da baby ke mata sannan ta cije ta dago dakyar ta kalleshi

Kamar kau yadda tayi tsammani idanunta suka fada cikin nashi don dama ita yake kallo

Janye idanunta tayi sannan ahankali ta gaidashi

Amsawa yayi yana sakarmata murmushin shi mai tsada, ba qaramin dadi yakejiba idan ta gaidashi, jinshi yake so uptop

Serving din kanta tayi sannan takoma ta zauna tafaracin abincin a hankali

Shiru dining din ya dauka idan ka dauke qarar cokalan daketa haduwa da plate

Yanzun ma kamar dazun atakure takecin abincin don duk motsin dazatayi saitaji alamun idanunshi akanta, ga yawan hada idanun dasuke wanda duk sadda suka hada ido saiya sakarmata wannan cool murmushin nashi, haka dai take tura abincin badon tanajin dadinshi ba don duk a darare takejin kanta.

Ganin taci fin rabi dakyar yasata dagowa ta kalli ummy

Itama ummyn dagowa tayi daga abincinta tana kallonta batareda tace komaiba

Marairaice fiska tayi sannan tace
"Ummy am full" cikin sanyin murya

Ga mammakin ta sai jitayi tace
"Ok daughter you can go"

Dadi taji wanda saida hakan ma ya nuna a fuskarta, daukar glass cup tayi ta sha ruwa kadan sannan ta goge bakimta da tissue ta miqe tareda dan satar kallonshi.

Gani tayi fuskarshi ta nuna alamun rashin jin dadin tashinta


Kauda Kai tayi tabar wajen tana sauke Ajiyar zuciya don Allah yasani a matuqar takure take awajen

Bata jima ba da komawa dakin ba itama baby ta shigo.

Sun dan ta6a fira da baby kafin barci yayi awon gaba da baby

Ganin haka yasata jawo wayarta takoma ta jingina da pillow data kara da jikin gado tashiga danne dannenta.

Sosai tayi missing din laptop dinta don wasu abubbuwan dole saida ita zatayi.

Tana cikin danne dannenta kira yashigo wayar

Qurawa number idanu tayi batareda ta dagaba yayinda bugun zuciyarta yafara sama


Haka taita kallon wayar harta yanke, ko seconds biyu ba'a qaraba wani kiran yasake shigowa.

Saida takusan tsinkewa sannan tayi qarfin halin daga wayar ta kara a kunnenta batareda tace komaiba

"Beauty.." Taji anfada daga dayan bangaren

Shiru tayi batace komaiba

"Hello? Are you there?" Yasake cewa

Qarfin halin bude baki tayi tace
"Yes? Who's this?"

Sautin murmushin shi taji kafin yace
"You know better"

Shiru tayi bata sake cewa komaiba

"Shine kika tashi dazun without my consent?" Yasake fada bayan wasu daqiqu

Dan wara idanu tayi tace
"Your consent?"

"You heard me" ya amsa a gajarce

Ta6e baki tadanyi batareda tasake cewa komaiba

"Bakice komaiba"

"Me zance?" Tafada tana Zamewa ta kwanta

"You tell me why you leave without my consent ko kiyi apologising for that" yabata amsa

Dage giranta tayi alamun 'dagaske?' Sannan tace
"Bye.. Am sleepy"

"Are you kidding me" yafada da sauri jin alamun zata katse wayar

Dakatawa tayi don jin abinda kuma zai sake cewa

"Don't tell me kin manta da deal dinmu"

"Deal?"

"Kinji kenan, am waiting"

"Waiting for what?"

"Our deal, you promised zaki hadamin coffee kikawo apartment dina dazun, don't you?" Yafada yana lumshe idanu don sosai yakejin dadin wannan little conversation din nasu


Itakau saudart mammaki nema ya kamata, ita sai yanzu ma ta tuna dawani deal, lallai ma

"Kinyi shiru"

"Hmm wane coffee kake magana akai? Ni bànsan abinda kake magana akai ba"

Murmushi yasaki yana shafa kwanttacen sajenshi yace
"Really? Ko kinsan promise is a debt? Musanmman ma nawa promise din cos bana yafe bashi"

Daga kafadu tadanyi sannan tace
"Bye"

Bata jira cewarshi ba ta katse kiran

Maganar da ashraf ke shirin yine ta maqale jin an yanke kiran.

Sauko wayar yayi yabita da kallo cikin mammaki sannan ya kada kai.


Kashe wayar gabadaya tayi sannan ta aza kan bedside locker ta kashe wutan dakin tabar dim light don bata iya barci cikin duhu sannan ta janyo bargon da baby ta lullu6e dashi itama tashige ciki tana sauke Ajiyar zuciya

Addu'ar kwanciya ta karanta ta tottofa sannan ta qara qudundunewa a bargo tana lumshe ido


Cikin barci taji kamar kofa na motsi, ahankali ta bude idanunta dasukayi nauyi don barci ta kalli saitin kofar a kasale.

Ganin tayi kamar inuwar mutum hakan yasa taji gabanta ya fadi.

Qara bude idanuwanta tayi don tabbatarda abinda tagani din gaske ne.

Ganin shadow din na nufo gadonsu yasata qara lahewa a gadon zuciyarta na racing sai qoqarin karanto addu'o'i take amma takasa saboda yadda ta tsorata

Baby kau batasan wainar da'ake toyawa ba saboda she's fast asleep gashi Allah ya horemata nauyin barci

Zufa ke tsatsafo mata takoina gashi tana tsoron yin kwakwarar motsi don kar 6arawon yaganta kamar yadda ta dauka

Saida yazo gaban gadon sannan taga yaja ya tsaya kamar mai tunani saikuma taga ya nufo 6aran datake kwance

Rawa jikinta ya dauka yayinda tashiga karanto duk addu'ar dayazo zuciyarta, abin mammaki kuma takasa ihu sai mazari kawai datake daga kwance

Ganin yazo dab da ita yasata tamke idanunta tana sauke numfashi sama sama cikin tsananin kidima

Jitayi an matso dab da ita sosai har tana iya jiyo saukan numfashin mutumin akanta hakan yasata dauke numfashi cikin sadaqatwa

"My coffee.." Taji anyi wishpering a kunnenta

Bata motsa ba bata kuma saki numfashin ba

"Nasan kina jina, fulfill your promise" yasake fada yana hurama fuskarta iska


kamar wanda aka tsikara tayi saurin miqewa zaune tareda danna plug din kwayakwan wutan dakin, take dakin ya gauraye da haske

Karo idanunta sukayi dashi zaune a bedside lockern dake gefenta hakan ya haifarmata da mummunan faduwar gaba don ko kadan bata tsammacci ganinshi ba don ita duk atunaninta yana can gidanshi

Jada da baya zatayi yayi saurin cafko hannunta, bude baki tayi zatayi ihu yayi saurin dora yatsarshi manuniya akan lips dinshi alamun tayi shiru

Kasamcewar a mugun tsorace take yasata saurin hadiye ihun tana kallonshi a tsorace

"Bani coffee dina sai intafi" yafada still riqe da hannunta

"A.A?.." Tayi wishpering cikin son gasgata shi dinne

Daga mata gira daya yayi yace
"Yes?... I told you Ai bana yafe bashi, you promised zaki kawomin coffee idan na 6uya , so nacikamaki alqawarinki kema ki cika nawa"

Yanzu kau ta tabbatar da shine don har qamshin turaren nashine wanda dazu tsoro yahanata jinshi, amma me yakeyi agidan nan at this hour of the night?

Huremata idanu yayi tayi saurin lumshe su
"Kallon fa?" Ya tambaya yana daga mata gira daya

Dan Satan kallon baby tayi dake qudundune cikin bargo batasan me duniyar take ciki ba sannan ta dago ta kalleshi tana dan frowning face dinta

"Ka cikani please, am sleepy"

"My coffee" yabata amsa batareda ya saketanba

"Zan Maka ihu ummy tazo and you know she won't take it slightly with you" tafada threateningly

"Go ahead, zanfi kowa jindadin tazo ta iskemu hakan maybe hakan sesa tasan I need my wife"

Dan wara idanu tayi kafin takuma maida fuskar puppy face

"Please ka kyaleni, this is not right" tafada tana qoqarin kwace hannunta

"Menene ba daidai ba?" Yafada still riqe da hannun

"Everything, please leave me alone am sleepy" tafada kamar zatayi kuka

"Idan kinaso in kyaleki ki hadamin coffee dina kikaimin apartment dina"

"But dare yayi for crying out loud" tafada tana yarfe hannuwa

"And I won't leave without my coffee for crying out loud" yafada shima cikin yanayin data fada

Sauke Ajiyar zuciya tayi tace
"Ok kasaki hannuna tukunna"

"Ki gudu?"

"Zuwa ina?"

"Oho but I assure you kina yunkurin guduwa zan daukeki cak wlh bazan direki koina ba sai cikin mota and direct gida zan kaiki saidai ummy ta farka taga babu ke, kuma try me and see" yafada in a very serious tone

Tsayawa tayi tana kallonshi a mammakince, ganin zai iya yasata sauke Ajiyar zuciya tace
"Alright naji sakeni"

Babu musu ya sakarmata hannu yana kallonta without blinking

Dan murza ankle din hannunta tayi sannan ta bude baki dakyar tace
"Yanzu me kakeso nayimaka?"

"Simple.. Just make my coffee ki kaimin apartment dina shikenan"

"Ok zanyi maka gobe i promised"

Wani kallo yayi mata
"Are you kidding me?"

"Please.. Kaga yanzu dare yayi and ummy na iya jiyomu ta tashi and you know what the result will be, I promised gobe insha Allah zai zama first thing tomorrow morning, I promised"

"Hmm, I need my coffee now not tomorrow miss, idan ma ummy kikeji yanzu am sure she's fast asleep kuma aiba hayaniya zamuyiba... You know what? Da wannan 6ata lokacin damuke da yanzu kin manta da kin hada kin dawo kin kwanta, all I know is yau bazan kwanta ba saina sha coffee dina" yafada firmly yayinda cikin zuciyarshi Dariya kawai yakemata ganin yadda take kallonta in confusion

Dafe kanta tadanyi cikin rasa abin yi ga takaicin baby dake kwance kamar gawa wai ace duk abinda ake bataiba saikace mai barcin mutuwa?

Dagowa tayi ta kalleshi taga shi dinma ita yake kallo yawani jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta kamar ya samu mirror

Sauke Ajiyar zuciya tayi nannauya sannan ahankali tace
"Ok"

Murmushi yasaki sannan yamiqe tsaye yace
"Let's go

Badan ranta yasoba ta ziro qaffafunta qasa ta sauko.

Sleeping gown baqa ce a jikinta mai kauri wanda takaimata har qasa sai hular net ja dake kanta wanda ta cusa duka gashinta aciki.

Gwada mata hanya yayi ganin batada niyyar wucewa hakan yasata gittashi ta wuce ya bita abaya

Maimakon tanufi qofa saita maida akalar tafiyarta ga wardrobe din dakin ta bude taciro long milk colour hijab dinta tazira sannan ta nufi qofar fuskarnan hade kamar zatayi bindiga, binta yayi yana murmushi yanajin kamar ya rungumota ta baya ya dauketa in a bridal style yakaita har kitchen din.

Kamar munafukai haka suke sanda wurin sauka stairs din, saudart agaba hannunta tattare da gaban hijab dinta dake jan qasa shikuma biye a baya suna tafiya sadaf sadaf.

Suna gab da sauka qasa hijab dinta ya tadeta tayi gaba zata fadi.

Saurin riqo hannunta yayi ya janyota jikinshi ya tallabe

Ajiyar zuciya ta sauke don ta sadaqar faduwa zatayi

Dagowa tayi daga jikinshi ta sakarmashi harara mai cike da jin haushi sannan taqara sa hannu ta tattaro hijab din ashraf na tayata sannan suka cigaba da tafiya sadaf sadaf kamar qwarrarun 6arayi dasuka qware wajen sanda...✍️
Aeesha umar aliyu: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)



095



Ahaka suka samu suka ida saukowa falon wanda yake dirim sai dan dim light blue colour dayadan haska falon

Direct kitchen suka nufa, ashraf ya bude kofar ya matsamata ta shiga sannan yabi bayanta tareda maido kofar ya rufe.

Kunna kwan wutan kitchen din yayi ya hangota daga can nesa tana kallonshi

Daga mata gira daya yayi alamun kallon fa?

Janye idanu tayi ta kalli wani 6arin kafin tace
"I think basai an rufe kofar ba"

Daga gira daya yayi kafin yace
"Kinaso tsautsayi yasa ummy ta sauko ta hango kitchen din da haske? Inkuma bakiso dan sai a bude kofar a kashe wutan saina haska phone dina" yafada yana yunqurin kashe wutan kitchen din

"No, ka barshi kawai" tayi saurin dakatar dashi da hakan sannan ta juya tanufi inda qaramin electric kettle yake ta fiddoshi ta dauraye sannan ta zuba ruwa ciki tayi plugging dinshi jikin socket


Duk abinda take yana nan zaune kan fridge yana binta da kallo duk inda tayi yanajin wani nishadi a zuciyarshi

Haka saudart taita kiciniyar hada coffee din saidai duk abinda take fuskarnan a kumbure take kamar mai shirin yin bindiga yayinda can qasan ranta take danasanin nacewa datayima ummy akan tabarta tayi girkin

In less than 10mins tagama hada black coffee din ta juye a mug ta Dora a saucer ta azasu bisa wani qaramin tray sannan ta dauka tajuyo tanufoshi dasu.

Kallon dai dayake mata ya cigaba dayi harta qaraso wajenshi ta Dora dan tray din saman fridge din kusadashi sannan ta juya zata wuce

Cafke hannunta yayi hakan yasata tsayawa batareda ta juyoba

"Ina zaki bayan baki gamaba?"

Juyowa tayi ta gallamashi harara batareda tasan sadda tayi hakan ba tace
"Menene kuma? Kace na hadamaka coffee na hada, what again?"

"Menene deal dinmu? Zaki hada coffee kikaimin apartment dina ko ba hakaba? Nan yayimaki kama da apartment dina?"

Wani malolo ya taso ya tokarewa saudart maqoshi, fizge hannunta tayi afusace tasake juyawa zata wuce

Shan gabanta yayi saurin yi yana cewa
"Where did you think you're going?"

"Look mallam wai what's wrong with you ne? You said I should make you a cup of coffee, nayi kuma yanzu saika qirqiro wani abin? What exactly did you want from me?" Tafada atsakankanin haqoranta cikin fushi fuskarta na dayi jaja jaja

"I want you to fulfill our deal, meyasa kika amince bayan kinsan you can't do it? Ni ba ruwana, I want my coffee in my room, final"

Tsayawa tayi tana kallonshi tinda yafara harya kai aya sannan tayi Ajiyar zuciya tace
"If not?"

Matsowa yaqara yi dab da ita sannan yace
"If not mu kwana anan"

Kallonshi takeyi, a yanayin dayake bataga alamun wasa ba a tattare dashi kuma taga alamun zai iya din besides ita zata kwan aciki don bashida asara Sam

Juya idanuwanta tayi tana cije lips kafin tace
"Ok I

Please Login or Register in order to submit comment