Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar wani shabiyu sha uku har sadeeq yashigo besaniba.


"Inyee! Wannan washe haqoran duka menene?" Inji sadeeq cikin sigar tsokana

Dagowa yayi yana kallonshi tareda zabga mashi harara still fuskarshi dauke da murmushi.


Qarasowa yayi da tray din tea din tareda direwa a bedside locker ya zauna kusada shi yana cewa
"Wato ni inacan ina faman hada maka tea harda qonewa amma kai kananan kana dariya kai kadai ko? Tell me what's funny" yafada Yanajin dadin yanayin daya ganshi

"Am..in..love" yafada kamar mai koyon magana yana qara rungumar pillon

Waro idanu sadeeq yayi cikin mammaki, dukda yaga alamun son saudart a idanunshi be ta6a tunanin zai furta dawuri hakaba


Tsalle yayi yadawo kusada shi kan gadon

"Maimata inqaraji dan uwa, kamar ban fahimci zancenkaba" yafada cikin sigar waqar sambisa.

Murmushi Ashraf yasaki mai tsadan gaske yana dan mintsinin sadeeq Wanda har saida yadan saki qara.

"Yes am in love......I love her" yafada cikin shauqi

"Wayyo dadi kasheni! Dunkum din abokina is in love! Yeah! Oya Jo soapy soapy, tashi muyi rawar soapy, tashi muyi rawar soapy, soapy soapy!" Yafada yana miqewa Yana rawar soapy din.

Wurga mashi pillow Ashraf yayi yana dariya sosai

"Kai dan iska ne ko?" Yafada yanada dariya

"Yan iska ba, inyee gaskiya saudart ta ciri tuta, wannan washe baki haka? Rabon da naga kana irin wannan dariyar har mantuwarma ta mance"

Dariya Ashraf yasakeyi yana girgiza Kai
"Kaifa dan iska ne"

"Na yarda, wato shiyasa dazu aka kusan sheqeni ko? Haryanzu wuyana ciwo yake na rantse"

Dariya Ashraf yayi mashi yana cewa
"Maganin mai shiga sabgar mata da mijinta kenan"

Bude baki yayi yana toshe wa

"Inyee ni kake fadawa haka? Lallai Bari na koma gefe naita kuka"

Dariya Ashraf yayi kawai sannan yadan girgiza Kai yanayinshi na chanza wa

"Meye kuma?"

"Ta tsaneni" yafada cikin wani yanayi

"A'a bata tsaneka ba"

"Ta tsaneni kaima kasani"

"Amma ai kai k koyamata tsanar ka din, why not ka koyamata sonka?"

"How?"

"By showing her love tsantsa"

Girgiza Kai yayi

"Banjin zata saurareni"

"Zata saurareka mana, kawai all you need to do is ka sauke wannan shegen girman kan naka dabeda amfani ka yaqo zuciyarta"

Dariya Ashraf yayi yana shafa gemunshi

"Nikuma banason abinda zai ta6a Mani jin kai na, yaya za'ayi kenan?"

Harararshi sadeeq yayi sannan yace
"To saika cika form din wahala don kai dashi kun qulla abota kenan"

Dariya kawai yayi bece komai ba

"Yanzu sha tea din kasha magungunan"

Babu musu yaziro kaffafun kasa ya amshi tea din yana sha ahankali

"Ummy fa? Yakamata ta sani" inji sadeeq

Dagowa Ashraf yayi daga kofin bakinshi yana kallonshi

"No"

"No? Sokake taji abakin wasu?" Inji sadeeq

"Fushi zatayi kasan halinta, insha Allah ni dakaina zan gayamata amma sai komai ya lafa"

"Komai ya lafa kamar ya?"

"Sai saudart tadawo gareni"

"Amma baka gudun taji waje?"

"Wazai gayamata? Saudart bazata gayamata ba I know, tsohon ta ma bazai faraba, nima bazan fadaba saidai ko kai zaka fadi"

"Hmm to Allah ya kyauta, ga magungunan kasha ka rama sallolinka insamu inkoma gida."

Saida yasha magungunan shi sannan ya rama sallolinshi sannan yadawo ya zauna suka dan ta6a fira sannan sadeeq yatafi bayan yagama quleshi da tsokana.


Dawowa yayi ya zauna kan daya daga cikin kujerun falon yana kishingidawa murmushi kwance a fuskarshi.

*I love you*

*I love you so much... SAUDART*...✍️


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲





Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




060




Ranar zaune yakusan kwana, sai saqa da warwara yake na yadda zai 6ullowa saudart, wani abun har mammaki yake bashi don ko a mafarki be ta6a tunanin zai ware wani kaso cikin lokutanshi masu amfani ya asarar dasu akan tunanin mace ba amma gashi har hana idanunshi barci yake don tunanin yadda zai 6ullomata.



Washegari sai 11:00am yafarka saboda Rashin samun isashen barcin dabeyiba jiya Wanda saida yayi sallar asuba sannan barcin ya daukeshi.

A gaggauce ya fada toilet don yin wanka da brush.

Fitowa yayi bayan wasu yan mintuna ya shirya cikin wasu ash colour suit ya feshe Jikinshi da turare.


Fitowa yayi yana gyara necktie dinshi yanufi motarshi.

Shiga yayi ya tadata sannan yafice daga gidan.



Opposite din bakery dinta ya parka motarshi yana kallon mutanen daketa karakaina a wajen.

Ya Dade cikin motar yana kallon wajen batareda yasan me ya kamata yayi ba.

Can yaga wani yafito daga bakery din da alamun daya daga cikin ma'aikatan ne.

Saurin bude kofar yayi ya fito ya tsaya gefen motarshi yana kallon mutumin dake qoqarin ketaro titin zuwa bangaren da Ashraf yake.


Saida ya qetaro yana niyyar wucewa Ashraf yayi saurin dakatar dashi.

"Ehmm barka" inji Ashraf yana dakatar dashi

Juyowa mutumin yayi yana kallonshi da alamun Rashin ganeshi sannan yace
"Barka dai"

Hannu Ashraf yabashi sukayi musabaha sannan yace

"Erm madam nanan kuwa? I mean saudart"

Girgiza Kai mutumin yayi yana cewa
"A'a rabonta da Bakery dinnan tun Friday, lfy?"

Murmushi Ashraf ya sakarmashi

"No lfy lau, dama aikoni akayi wajenta ne, amma idan babu damuwa kozan samu number ta?"

Kallon Rashin yarda mutumin yashiga binshi dashi Wanda yasa Ashraf jin duk ya tsargu da kanshi.

"A'a banida numberta, idan order kukeso ko wani abun kana iya shiga ciki kasamu P.A dinta amma babu mai number ta" yana kaiwa nan yawuce yana waiwayenshi don hakanan yaji be kwanta mashi ba.

Shima Ashraf binshi yayi da kallo harya wuce sannan yasa hannu ya shafi kanshi yana hurar da iska.

"This is gonna be tough" yafada yana saka hannayenshi a aljihu yana qara kallon bakery din.

Ganin tsayuwar batada amfani yasashi shiga mota yabata wuta yabar wajen.


Direct company dinshi yawuce, anan yayi assigning din wani daga cikin guards dinshi kan ya cigaba da saka idanu a bakery dinta duk sanda yaganta yayi alerting dinshi.

Yakuma yi assigning din wani a unguwarsu akan yasaka idanu a gidansu saudart duk sadda yaga fitowarta yayi alerting dinshi.


Komawa yayi jikin kujera yana jujjuyawa ahankali yana jinshi empty, Yanajin kamar yarasa wani 6ari nashi mai matuqar muhinmmanci.

Ranar babu wani aikin dayayi bayaga tunaninta, abin har tsoro yake bashi don gani yake kamar qaramashi Sonta ake akowace daqiqa mai wucewa.





Wasa wasa kwana uku kenan da assigning din masu saka ido akan saudart amma babu wani labari mai dadi.

Kullum amsarsu daya ce, basuga fitowarta ba.

Ashraf yashiga cikin tsananin damuwa, damuwarshi dayace anya lafiyarta qalau kuwa? Idan yayi la'akari da yadda suka rabu a haduwarsu na qarshe sai yaga kamar ba lafiya.

Duk yabi ya susuce, kodayaushe wayace a hannunshi yana jiran akirashi ace anga fitowarta amma shiru, idan kuma yagaji shi yabuga amsar duk dayace, babu ita.


Duk wannan budirin da'ake sadeeq na gefe ya zuba mashi idanu, don shi abun ya daina bashi mammaki yanzu saima takaici.

Yaya za'ayi ace kana tsananin son ganin mutum kuma kasan inda yake amma ka kasa zuwa ganinshi saboda wani dalili naka na banza?

Hakan yasashi bude kwandon shara ya sakashi ciki ya rufe ya cigaba da harkar gabanshi acewarshi idan kaji ana rakani kashi to ba zawo bane.



Yau Saturday babu aiki don haka yau gidansu ya wuni yana hutawa.

Kwance yake yana waya murya qasa qasa da alamu da masoyiyarshi yake wayar.

Da sallama Ashraf yashigo looking so pale, kallo daya zakayi mashi kasan yana cikin damuwa don duk yazama wani iri, gashi nan dai.

Dagowa sadeeq yayi ya amsa sallamar sannan ya cigaba da amsa kiranshi hankali kwance.

Samun kujerar dake dakin Ashraf yayi ya zauna ya jingina da kujerar yana dafe kanshi dake dan Sara mashi.

Sadeeq na ankare dashi amma ya share yacigaba da wayarshi batareda ya kulashi ba, shima Ashraf bece komai ba sai lumshe idanun dayayi hannu dafe dakai yana sauraron wayar sadeeq.

Ada idan yaganshi yana waya irin haka has yake bashi yana yi mashi kallon marar aikin yi amma yanzu jiyake dama shine ke wayar da muradin ranshi, abar kaunarshi, Saudart.


Haka yaita jiranshi harya gama wayar batareda ya katseshi ba ko yanuna 6acin ranshi akan shareshin dayayi hasalima kalaman sadeeq din yake sauraro yana mammakin ina ya iya wadannan kalamai haka.


Dagowa sadeeq yayi yana kallonshi sannan yadan ta6e baki

"Ya dai? Naga you look pale"

Bude lumsassun idanunshi yayi ya kalleshi sannan ya maidasu ya rufe batareda ya tanka mashi ba.

"Mtcheew dan wahala kawai" inji sadeeq yana daukar remote zai kunna kallo

Bude idanunshi yasakeyi ya kalleshi sannan cikin sanyi yace
"Please banson hayaniya karka kunna"

Wani kallon uku saura kwata sadeeq yayi mashi sannan yace
"Dalili? Dakinka ko nawa? Kaji qarfin hali"

Sauke ajiyar zuciya Ashraf yayi yana dan rolling din idanu

"Sadeeq dama haka kake? Dama kai maqiyina ne bansaniba? Ni atunanina idan ina cikin damuwa saika fini shiga damuwar amma am mistaken"

Sadeeq da tunda yafara magana yake antayamashi harara yaja tsaki yace

"To ni me zan maka? Ashraf taurin kanka yasa nafara tantamar da irin qashin da'akayi namu kan akayi naka, kana wahala zuciyarka na wahala amma kasan yadda zaka kawo qarshen wahalar ka kasa, saboda wani banzan dalili naka can" yafada cikin jin haushi

"But am trying ko? Duk hanyar danasan zan ganta inabi kaima kasani" yafada kamar zaiyi kuka

"Nidai tawa ta sameni, dafarko ina zaman zamana hankali kwance banida damuwar komai amma tunda tashigo rayuwata ta sauya komai, gashi yanzu ta tafi tabarni da jinya gashi kai da nake tunanin zan dan samu sauqi a wajen ka kaima ka juyamin baya" yaqarashe zancen yana dafe Kai.

"Mtcheew kai ka siya ai, muddin bazaka sauke girman Kai ba bakaga komai bama, ita saudart din allurace da zata bace bakasan inda zaka ganota ba? Kasan inda zakaje ka ganta kawai baka shirya ganinta bane" yafada yana maida hankalinshi kan kallon dazai kunna

"I can't, bazan iya taka gidan mutumin nanba, zan iya zuwa koma inane inganta amma banda wannan gidan" inji Ashraf yana dan huci.

"Why? Ai ba wajen shi zakajeba, wajen Matar ka kaje, ni banga wani Abu aciki ba"

"Ni nagani, the first and worst mistake dina shine sanyota acikin deal dina, da bansata aciki ba da ko saninta banyiba bare har wannan masifar ta hayeni" inji Ashraf yana cije le6an qasa.

"Yes Ashraf, Allah ne ke nuna mana kurenmu, yakuma nuna mana aure ba abin wasa bane, dukda rama sharri da sharri ba haramun bane anfison a ramashi da alhairi, amma mu saimuka nemi ramawa fiyeda yadda akayi mana, muka kuma saka Wanda bata jiba bata ganiba kuma muka dauki abu mai martaba irin aure muka maidashi wasa shiyasa muka rufta aciki" inji sadeeq shima cikin sanyi.

"And you warned me, ka gargadeni akan hakan amma ni idanuna sun rufe fansa kawai nakeson dauka gashi yanzu muntashi ba wan ba qanin saima masifar danake ciki, wlh danasan yadda zan cire Sonta a zuciyata danayi hakan ko na huta, kullum kamar qaramani Sonta akeyi, with every passing minute, second, breath jinake kamar qara huramani wutar Sonta ake, am helpless, bansan yaya zan tunkareta ba, bansan Kalmar dazan yi amfani dashiba, bansan komai ba, all I know is I love her, I so much love her" yafada cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.

Cikin tausayawa sadeeq ya dawo kusada shi ya zauna tareda dafa kafadarshi

"It ok bro, insha Allah komai zaizo da sauki, ka riqe addu'a kuma kaima kayi trying best dinka, ka ajiye komai kayi fighting for your love, insha Allah saudart alhairi ce a rayuwarka shiyasa tun farko ka sakota aciki, insha Allah zakayi dariya watarana.."


Ringing din wayar Ashraf ce ta katsesu.

Saurin saka hannu yayi ya fiddo wayar jin ringing tone din Ummy ne Wanda contact dinta kadai yasama tone din.

Janye hannunshi sadeeq yayi daga kafadarshi yana kallonshi yayinda shikuma ya daga ya kara a kunne yana sallama.

Ganin yanayin fuskarshi na chanzawa yasa sadeeq kuramashi idanu da alamun tambaya

"Ummy.. Lafiya?" Inji Ashraf cikin Rashin fahimta.

Bansan ko me ummin tace ba sai gani nayi wayar takawo haske alamun an katseta.

Ahankali ya sauke wayar daga kunnenshi fuskarshi dauke da ayar tambaya.

"Lafiya?" Inji sadeeq daketa kallonshi tundazu

"Ummy ke Neman mu" Ashraf ya amsa absentmindedly tunani kala kala na yawo a qwanyar shi.

"Meyasa?" Inji sadeeq

Miqewa Ashraf yayi
"Muje amma she don't sound normal".

Shima miqewan yayi ya Dora t-shirt akan singlet dinshi yasaka takalmi suka fita.

Sallama sukayima umman sadeeq dake falo akan zasu dan fita su dawo sannan suka fice da motar Ashraf.



A harabar gidansu Ashraf sukayi parking suka fito.

" sadeeq wani Abu na faruwa, inaji a raina something bad is happening" inji Ashraf yana kallon hanyar cikin gidan

"Babu komai insha Allah, mushiga nasan babu komai sai alhairi" inji sadeeq cikin qarfafa mashi gwiwa.

Haka suka jero kamar yadda suka saba sadeeq ya Danna door bell sukayi jigum suna kallon kofar.

Bayan yan daqiqu sai gani sukayi an murda kofar an bude.

Baby ce ta bayyana fuskarta adagule alamun something is happening.

Saurin qaqalo murmushi tayi tana kaucemasu tana gaishesu.

Yau babu Wanda yasamu halin amsawa saboda fargaba don haka shiga sukayi atare suna sallama.


A falo suka hango Ummy zaune kan one seater fuskarnan babu fara'a tadago tana amsa sallamarsu tana masu wani irin kallon daya kada hanjin cikinsu.

A sanyaye suka qaraso suka zauna qasan tsadadden rug din dake tsakiyar falon suka sunkuya kai.

Itama baby dawowa ciki tayi ta zauna kan kujerar dake nesa dasu ta zauna tana kallonsu

Tare suka gaidata cikin sanyi kallo daya zakayi musu kasan suna cikin fargaba sosai.


Kallo tashiga binsu dashi batareda ta amsaba hakan yasasu sunkuyar dakai kasa

"Ina matarka?" Ummy ta jefo masu tambayar a bazata.

Hakan yasa duk suka dago kai gabadaya suka kalleta sai kuma suka kalli juna.

Maida kallonsu suka sakeyi kanta sannan Ashraf cikin inda inda yace
"Ni?"

Batace komai ba sai tsareshi da idanu datayi Wanda hakan ba qaramin sanyaya mashi jiki yayiba.

Sunkuyar dakai yayi sannan ya bude baki yace
"Tana gida"

"Ka kirata tazo yanzu" tafada commandly

Dagowa yayi yasake kallonta yanason karantar yanayinta

"Ummy.. Wayarta a kashe.. Take"

Dan murmushi Ummy tasaki mai kamada na takaici sannan ta kalli baby tace
"Kirata"

Jiki a sanyaye baby ta Ciro wayarta ta kira number saudart sai gashi tashiga suna kuma ji saboda hands free tasata.

Har tayi ringing dinta tagama ba'a dagaba.

Maido kallonta Ummy tayi kansu sukayi saurin sunkuyar dakai.

"Ina matarka Ashraf!"

Gamm ya runtse idanunshi tashin hankali qarara a fuskarshi.

Tunda yake Ummy bata taba kiranshi da sunanshi ba sai yau.

Nan take zuciyarshi tafara bugawa abnormally gumi na tsatsafo mashi.

"Nace where is your wife!!" Ummy ta daka mashi uban tsawar da bata ta6a yi musu ba.

Nan take baby tafashe da kuka tana toshe bakinta shikuma Ashraf yadago yana kallon Ummy idanunshi sunyi jajur.

"Ummy.."

"Shut up!" Ta katse sadeeq din a tsawace

"Kabari nadawo kanka tukun" tafada a fadace

"Now answer me, ina matarka?" Ta maida akalar tambayar kan Ashraf.

Bakinshi yabude zaiyi magana amma yakasa sai 6ari da bakin keyi.

Be Ankara ba yaji an wurga mashi takardu a fuska sun watse a gabanshi

"What is this?! Nace meye wannan!" Ta tambaya a tsawace

Bin takardun yayi da kallo nan take Jikinshi yadauki rawa...✍️



Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Aslm fans🙋🏻‍♀️ sorry kunjini shiru kwana biyu, wayatace tasamu mtsl😟 amma yanzu komai yayi daidai.

Masu cigiya, masu kira da masu text duk nagode da qauna😍😇
Allah yabar zumunci🤲





Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)










Bin takardun yayi da kallo nan take jikinshi yadauki rawa.

Shima sadeeq takardun yake kallo fuskarshi fall mammaki zuciyarshi na bugawa.

"Nace meye wannan!!" Suka sakejin muryarta tsakar kansu.

Kasa dagowa Ashraf yayi daga kallon takardun sai binsu yake da kallo kamar yau yafara ganinsu.

"Ummy... we can explain.." inji sadeeq cikin kwantar da murya

"Explain? Kenan wannan gaskiya ne?" Tafada cikin sanyin murya tana kallonsu most especially Ashraf daya kasa dagowa, idanunshi sun kada sosai

"Yes ummy...amma.."

"Ya sallam!" Inji ummy tana komawa dabaya ta zauna akan kujera jagwab tana dafa kai, tashin hankali qarara a fuskarta.

Da sauri Ashraf ya rarrafa gabanta yana kamo hannunta data dafe kanta dashi
"Ummy?.. ummy am sorry, am so sorry"

"Sakarmin hannu" tafada cikin sanyin murya.

Qara qanqame hannun yayi yana cewa
"No ummy, Dan allah kiyi haquri ummy, please" yafada muryarshi na rawa rawa, jiyake kamar yafashe da kuka ko zai samu sauqi.

Idan akwai abinda ya tsana duniyarnan to 6acin ran ummy ne, kullum cikin taka tsantsan yake wajen ganin ya faranta mata rai amma yau tashin hankali da 6acin ran dayake hangowa a idanunta yasashi jin kanshi so guilty.

Baby kau na gefe tana sheshekar kukan dataci, bata ta6a ganin ummy da yaya a wannan yanayin ba, hakan yasata jin wani iri ga baqin labarin da hankalinta yakasa dauka daya riskesu.


Shima sadeeq rarrafowa yayi kusada ashraf cikin sanyin jiki.

"Ummy munyi kuskure amma Dan allah ki sauraremu, please" yafada shima kamar zaiyi kuka.

"Let go of my hand" ummy tasake cewa in a cool mode wanda hakan yaqara tada hankalin Ashraf

"Ummy.."

Fizge hannunta tayi a fusace daga riqonshi sannan ta miqe tsaye tana nuna masu kofa da yatsa.

Tashi baby tayi tayi sama dagudu tana toshe bakinta cikin qoqarin hana kukan daya kufto mata fitowa.

"Out!!" Tafada a tsawace.

Kasa ko motsawa Ashraf yayi daga kneeling position dinshi, jikinshi yayi liqis jiyake kamar babu sauran lakka ajikinshi.

"Nace kufita and never come back again! Get out!" Tafada cikin qaraji.

Hakan yasa sadeeq saurin tashi don yasan halin ummy idan ranta ya 6aci, dawuya kaga 6acin ranta amma idan ranta ya6aci batada kyau.

Kamo ashraf dake durqushe haryanzu yayi dakyar suka miqe.

Dago kai ashraf yayi ya kalleta da idanunshi dasuka yi jaa, siraren jijiyoyi jajjaye duk sunfito akan farin idanun.

"Ummy am.."

Daga mashi hannu tayi sannan ta nunamashi kofa.

Babu musu suka juya su biyun kowanne kamar zakaran da aka tsoma cikin ruwan zafi suka fita.

Komawa ummy tayi ta zauna tana dafe kai zuciyarta a jagule.




Cikin mutuwar jiki kowannensu ya kama murfin motar yabude yashiga.

Tada motar sadeeq yayi sannan yabata wuta suka fita daga gidan.


Tafiya suke amma babu mai cewa uffan kuma babu mai niyyar maganar, kowanne da tunanin daya addabi ruhinshi.


Ahaka suka isa gidan Ashraf din, ko gama daidaita parking din beyiba Ashraf ya 6alle murfin motar yafita.

Binshi da kallo sadeeq yayi sannan ya ida gyara parking din shima yafito.


A falo ta taddashi kwance bisa kujera two seater, kanshi akan hannun kujera daya kaffafuwanshi akan daya sun sauko qasa, hannu daya dafe da kai yayinda idanunshi ke a lumshe.

Dauke kai sadeeq yayi yawuce dining area, yabude fridge din wajen taciro gorar ruwa da cups yadawo cikin falon.

Zama yayi kan kujerar dake gefen ashraf sannan ya tsiyaya ruwan a cup sannan yayi tapping din kafadar ashraf.

Bude idanunshi yayi dakyar ya dago ya kalleshi yaga ruwa yake miqomashi.

Maida idanun yayi ya rufe batareda yako motsaba.

"Kasha Ashraf, you'll feel better" inji sadeeq a tausashe.

Shiru yayi kamar bazai motsaba saikuma ya bude idanu ya miqe zaune ahankali ya miqa hannu ya amsa cup din ruwan ya kafa kai.

Saida yashanye sannan yasake miqama sadeeq ya amsa yasake cikawa yabashi ya amsa yaqara sha sannan ya ajiye cup din kan stool din gefen kujerarshi yakoma ya kwanta.

Ajiyar zuciya sadeeq ya sauke sannan yace
"Ashraf?"

Banza yayi dashi

"Ashraf katashi, we need to discuss this"

A kwancen dayake batareda ya bude idanuba yace
"Babu abun tattaunawa anan sadeeq"

"Ofcourse akwai, dole musan wa ya gayawa ummy wannan abun"

Murmushin gefen baki yayi wanda shikadai yasan yayi abinshi

"Ni dakai munsan wanda yafada, meye na wahalarda kanmu? Bansan har haka tadauki abinba, telling my mother without my consent?"

"Saudart? No bazata iyaba" inji sadeeq

Shiru ashraf yayi besake cewa komaiba

"Ashraf.."

"Dan allah kayi haquri ka kyaleni, please.. i need to be alone..please" yafada yana dafe kanshi.


Shiru sadeeq yayi yana kallonshi, yasan yadda yakeji kuma ya tausayamashi, komai sai juyemasu yake from normal to abnormal.
Yasan yadda suke da ummy, yasan dole abin yayi affecting dinshi sosai.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miqe yana cewa
"Ok, zanje gida amma please take it easy on yourself"

Bece komaiba kamar yadda be bude idanunshi ba.

Dafa kafadarshi yayi yana dan murzawa
"Be strong" yafada cikin qarfafa gwiwa sannan yajuya yafita.


Ahankali ya bude idanunshi bayan yaji fitarshi ya saukesu a p.o.p din falon

Yau ummy ke fushi dashi? Yau ya 6atawa ummy rai? Garin yaya be ta6a tunanin wadannan abubuwan zasu bayaba tinda farko? Yana iya jurar komai amma banda fushin ummy, bazai iya jurewaba samm.






********************************

Driving yake tunannuka kala kala na yawo akanshi.

Haryanzu yakasa yarda cewa Saudart zata iya gayawa ummy komaiba, yanaji ajikinshi ba ita bace.

Karya motarshi yayi awani round about ya dauki hanyar gidansu Saudart.


A opposite din gidan yayi parking sannan yafito yana kallon gidan.

Tsallakawa yayi yazo bakin gate din yafara bubbugawa.

Saida ya bubbuga sau hudu sannan yaji motsi daga ciki.

Tsayawa yayi yana kallon yadda karamar kofar gate din ke motsi alamun budewa akeyi sannan kofar ta bude fuskar maigadin ta bayyana wanda kallo daya zakamashi kasan buzune.

Murmushi sadeeq yayi yana miqamashi hannu yana mashi sallama.

Shima miqamashi hannun yayi yana amsawa yana mashi kallon rashin sani.

"Erm.. dan allah ko madam nanan? Saudart nake nufi"

"Eh yananan, lfy?" Inji buzun cikin gur6attacciyar hausanshi

Murmushi sadeeq yayi
"Eh lfy lau, dan allah kamin sallama daita, kace sadeeq ne, abokin mijinta"

Kara karemashi kallo buzun yayi sannan daga bisani yace
"To..to, amma ki tsaya nan bari na fadamashi, ki tsaya" saiya rufe kofar sannan yashige ciki don sanarda madam saudart.



Zaune take a falo kan one seater ta doro kaffafunta a kan kujerar tana filing din akaifunta na hannu, kanta dauke da earphones dinnan da ake dorawa akai tana sauraron cool music cikin low volume.

Kallo daya zaka mata kaga tadan fada, ga hasken data qara wanda hakan yaba fatarta damar fitowa sosai cikin blue black din roba gown din dake jikinta.

Sallamar maigadin dataji yasata dagowa daga abinda take.

Amsawa tayi cikin fara'a, duk kwakwarka baka iya gane damuwarta don allah yayita mai fara'a da yawan murmushi.


"A'a? Sannu mallam audu, kina lfy?" Tafada cikin sigar tsokana.

Washe baki yayi yace
"Wlh lfy lau hajiya, barka da hutawa"

"Barkanmu dai, wani abu kikeso?" Tasake tambayarshi cikin yanayin maganarshi fuskarta daukeda murmushi.


"A'a hajiya, kayi baqo ne"

Dan daga gira daya tayi

"Baqo? Waye?"

"Wai abokiyar maigidanki ne, wai saddiqu"

Dan ware idanunta tayi

"Sadeeq?"

"Eh"

"Shi dawa?" Ta tambaya still idanunta aware.

"Nidai ita kadai nagani"

Ajiyar zuciya ta sauke

"Yana ina yanzu?"

"Tana shan waje aradu, cewa nayi tajira in fadamaka"

"Ok..ok, kagane? Kaje kashigo dashi ganinan tafe"

"To angama" yafada yana fita don aiwatar da yadda tace.

"Sadeeq? Meya kawoshi?" Tambayar datayiwa kanta kenan.

Tashi tayi ta tattara tarkacenta ta haura sama tana cire earphones din kanta.

Doguwar hijabi kawai tazira ta zura takalmin soso sannan ta dauki wayarta tafito tana addu'ar allah yasa takardarta yakawo mata.





Tun daga nesa ta hangoshi zaune kan farar kujerar roba kusada parking space wata empty kujerar na facing dinshi.

Dauke kai tayi ganin shima ya dago yana kallonta ta qaraso wajenshi ta tsaya daga dan nesa dashi tana mashi sallama.


Cikin fara'a ya amsa yana cewa
"Sannu da fitowa *Mrs A.A*"

Jin sunan tayi wani banbarakwai amma saita basar tace
"Yauwa sannu"

Nunamata kujerar gabanshi yayi yana cewa
"Bismillah mana"

Itama kallon kujerar tayi kamar yanzu tasan daita sannan ta dauke kai tana cewa
"No need, hakanma am ok"

Miqewa shima yayi yana cewa "in that case nima bari na tashi yadda zamufi fuskantar juna"

Kauda kai tayi batareda tace komaiba

"Kin wuni lfy?" Yafada yana pocketing din hannunshi

"Lfy, yes? How may i help you?" Tafada tana kallonshi

Murmushi yadanyi yace
"Magana nazo muyi *Mrs A.A*"

Kallonshi tayi kafin tace
"Idan ban manceba, ba ta6a warning dinka akan dagantani da wannan sunan"

"Why? Ba sunanki bane? Ko ba matarshi bace"

Guntun tsaki taja

"Now get to the point, kazo da sign dinne ko da takardar?"

"Takarda? Tame?"

"Kafini sani" tafada tana kauda kai cikin son danne 6acin ranta

"Nazone don in tambayi dalilinki na aikawa ummy da takarda don nasan bake kikajeba dakanki"

Kallon rashin fahimta tayimashi.

"Takarda? What are you talking about?"

Ganin kamar bata ganeba yasashi cewa
"Kin gayawa ummy komai, dont you? Why zaki aikamata bayan kisan wannan is between us, mu kadai"

Tsayawa tayi tana kallonshi na yan sakanni sannan taja tsaki.

"Look, basan akan me kake magana ba, i thought kazo da takardata ne shiyasa kaga nafito tun farko.
Batun kaima ummy takarda ba aikina bane, why should I? Koda aika takardar zanyi to ta sammaci zan aiko maku ba kotu don am taking this issue down to court, it's better kaba abokin naka shawara akan mu warware komai a tsakaninmu salin alin ko kotu ta taimakamana wajen warwarewa"

"Court? Kinsan me hakan ke nufi? Zaku tonama kanku asirine a idanun duniya da kanku, kinsan abinda zai biyo baya? Kinsan abinda duniya zata fada akanku?" Yafada cikin ayar tambaya

"I dont care, as far as zan rabu da wannan mutumin duniyar ta dade bata fadi koma menene akaina ba" tafada in an I-don't-care manner

"Amma kinsan hakan zaiyi tarnishing din image dinku ko?"

"Yadaiyi tarninshing din image dinshi, am independent and not that famous, shifa? Kana ambatar A.A kowa saiya waigo don sunanshi, sunanshi zai 6ata a banza, zai shafama kanshi baqin fenti a bugamashi tambarin zalunci wanda bazai iya taimakon naqasa dashiba saiya nemi wani abu in exchange.

Court zata tuhumeshi da bribery, corruption and harrassment, labari zai yadu a duniya akuma wajen abokan huldarshi, zai samu karaya fiyeda tunaninka, now tell me waya kwan aciki?"

Ajiyar zuciya sadeeq yasauke sannan yace
"Saudart, why did you hate him that much? Allah nason bayinsa mai gafara, ki tuna koshi Allahn daya hallicemu muna mashi laifi mu nemi yafiyarsa

Please Login or Register in order to submit comment