Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mance, haka sukaita firarsu cikin tsananin so da shaquwa yayinda hakan ya gusarmata kaso 60 na 6acin rai da kuncin datake aciki.

Qarshe ma tare suka hau hada yan kayyayakinta dazata dasu gidan mamyn, daddy na mitar zata tafi ta barshi shi kadai, zaiyi missing dinta sosai. Itadai sai dariya take mashi tana fadin abinda duka yan kwansji zatayi tadawo kuma itama ai zatayi missing dinshi.

Haka dai suka qarashe yinin cikin farinciki da jindadi.


A bangaren ashraf kau tunda yashiga daki be saukoba sai wajajen magrub yafito suka hadu da kawu ibrahim da shima gobe insha allah zai koma suka wuce massalaci.

Koda aka gama sallar basu dawoba can suka xauna jiran isha'i inda a dan wannan lokacin kawu ibrahim yaita yimashi nasiha da shawarwaru masu amfani wanda sosai ashraf yaji dadinsu don sun taimaka mashi wajen dan ragemashi abinda yakeji a zuciya.

Saida suka gama isha'i sannan suka shigo gida inda direct dining suka nufa.

Saida yaci ya qoshi sannan ya miqe yaima kowa saida safe sannan yayi hayewarshi sama.

Koda yakoma dakinshi cigaba yayi da tunanin daya katse dazun yana nazarin shawarwarun da sadeeq da kawu ibrahim suka bashi ayau.

*Ashraf nasan saudart bawai ta yarda zata zauna dakai bane don son ranta, ta yarda ne don batada za6i, ashraf wannan damace allah ya aramaka don ba kowanne mutum allah ke sake bashi damaba, ashraf take your time, don't play with your opportunity, yanzu damarkace na koyawa saudart sonka, ta mato akanka, ka tsundumata tsundum acikin kogin sonka, don't play with your chance, opportunity come but once*

Maganar da sadeeq yafadamashi daxun kafin yatafi ya dawo mashi a qwanya.

*Babana Allah ya azurtaka da mace tagari mai tarbiyya, kayi kokarin riqeta dakyau, karka bari tasake kufcemaka a karo na biyu don ba lallai bane allah yabaka irin wannan damar ma, ita zuciya tana muradin mai kyautata mata ne, ka kasance mai kyautatawa iyalinka zakasha mammaki* maganar kawu ibrahim yadawomashi.

Ya dauki lokaci mai tsawo yana tunani wanda kuma ke qaramashi qarfin gwiwar samun saudart.

Tabbas dafarko yayi kuskure ya bari girman kanshi yakusan kaishi yabaro amma ayanzu ya shirya damarar yaqo zuciyar saudart, saiya koyamata sonshi yadda duk numfashinta saita shaqa da sonshi ne, zai ajiye komai ya gyara abinda ya 6ata da kanshi.

Fatanshi dai allah ya tallafamashi yakawomashi komai cikin sauqi.


πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

Washegari wajajen 12:00pm saudart ta isa gidan mamy.

Saida ta tsaya suka gaisa da maigadi kamar yadda suka saba sannan ta shige ciki janye da dan qaramin trolley dinta.

Gidan shiru kuma tasan hakan be rasa nasaba da saboda yaran na makaranta ne, tasan mamy kadai ke gida, koyaya zata tarbeta? Tambayarda taiwa kanta kenan.

Danna doorbell tayi tana jinginar da trolley din gefenta.

Saida ta danna sau uku sannan taji muryar mamy na amsawa daga ciki sannan tajiyo takunta na nufo kofar wanda hakan yaqara mata fargaba.

Budewa akayi fuskar mamy ta bayyana.

Turus mamy tayi tana kallonta daita da trolley dinta da ayar tambaya a fuskarta.

"Mamy barka da rana" inji saudart tana dan murmushi

Kaucewa mamy tayi tana bata hanya don tashigo tana amsa gaisuwarta.

Kama trolley din tayi tashigo tana jaye dashi mamy tarufe kofar tabiyota tana kallonta still da ayar tambaya.

Zama saudart tayi kan daya daga cikin kujerun falon feeling uncomfortable da kallon da mamy ke binta dashi.

Itama mamy zama tayi dan nesa daita tana kallonta.

Zamowa tayi tashiga gaidata cikin girmamawa.

Amsawa mamy tayi babu yabo ba fallasa.

"Su abdul basu dawo makaranta ba?" Injita trying to sound free

"Eh basu dawoba" inji mamy a taqaice.

"Ayyah shiyasa gidan yai wani shiru" tafada tana murmushi.


Shiru yadan ratsa falon can sai mamy tace
"Ya naganki da trolley?"

Dan murmushi tayi shyly sannan tace
"Zan dan tayaku zamane mamy"

Dan ta6e baki mamy tayi tace "ok saiki kai kayan sama ki huta, bari nakoma kitchen" daga haka ta miqe tai wucewarta kitchen din.

Tashi tayi itama ta haura sama kamar yadda mamyn tace ta ajiye kayanta a dakin datake sauka anytime idan taxo kwana gidan sannan ta warware nadin gyalen jallabiyarta tabar hula kawai akanta ta sauko qasa ta wuce kitchen itama.

Sau daya mamy ta waigo ta kalleta takuma juya ta cigaba da abinda take.

Qarasowa saudart tayi ta amshi wuqar hannun mamyn, ba musu ta sakarmata ta koma wajen tukunyar dake saman gas cooker tana budewa itakuma saudart tacigaba da chopping din carbbage din a chopping board.

Haka dai sukai aikin kamar kurame babu mai magaba cikinsu gwara gwara saudart tana dan tambayar wani abin idan zatayi itakuma ta amsa a taqaice da alamu dai bata huce ba.

Cikin qanqanin lokaci suka gama saudart taita kawosu dining area itakuma mamy ta haye sama.

Saida saudart ta gyare kitchen din kamar ba'ayi girkiba ciki sannan itama ta haye sama don watsawa.

Wajajen biyu tana zaune kan sallaya bata dade da ida sallah ba taji hayaniyarsu abdul alamun sun dawo kenan.

Shafa addu'o'inta tayi sannan tamiqe ta linke sallayarta ta ajiye samsn bedside locker ta cire hijabinta ta adanata sannan tayi hanyar waje.

Su abdul nata gwadama mamy sums dinsu dasukayi a school sukaji tafiyarta.

Duk dagowa sukayi suna kaΔΊlonta a mammakince don basusan tana gidanba.

Dagudu sukayo wajenta har suna rige rige.


Fasa yar qara tayi tana dan qanqame jiki ganin yadda suka nufota don yadda suka taho dinnan tsab su zibe dukkansu.

Illai kuwa saigashi suna qanqameta suka tafi gabadaya suka zube.

Su aminullah da kamal me zasuyi banda dariya don kamal harda riqe ciki.

Mamy ma saida ta murmusa sannan ta dauke kai.

Tashi saudart tayi tana turo baki tana dungurinsu ganin sun kadata kuma suna mata dariya.

Haka suka taho suka w
qaraso falon suna ta dariyar.

Nan suka shiga gaidata tana amsawa tana tambayarsu ya school.

Tuni abdul yaje ya amshe littafinshi daga hannun mamy yakawoma saudart sai washe baki yake yau yace duka sums dinshi

Yabonshi saudart tashigayi tana fasa mashi kai shikau kan sai kumbura yake yana washe baki.

Ganin hakan yasa su kamal fara tsokanarshi saudart na kareshi.

Ganin abin nasu bana qarewa bane yasa mamy umartarsu suje su chanza su sauko suci abinci.

Babu musu duk suka haye sama harda saudart dake goye da jakkar abdul da habeeb.

Ita ta taimakawa qanannun suka chanza sannan suka sauko qasa suka wuce dining.

Saudart ce tayi serving dinsu suka zauna suka faraci silently bayan kowa yayi basmalah...✍


Ummin fasihuπŸ§šπŸ»β€β™€οΈ

πŸ‘°πŸ»πŸ€΅πŸ»AUREN KWANGILAπŸ€΅πŸ»πŸ‘°πŸ»
(Contract marriage)




081



Da suka gama cin abincin duk sama suka haye don shirin islamiyya while saudart ta tsaya gyara inda suka 6ata ta tattara abinda suka 6ata tayi kitchen dasu don wankewa.

Tana gamawa itama tabisu saman don taimaka masu wajen shiryawa, anan ne suke tambayarta yaushe zata koma tace musu tananan sai tayimusu sattitika.

Zo kuga murna wajensu don sosai suke qaunar yar uwar tasu, haka dai suka kammala shirinsu suka fito gabadaya har wajen motarsu.

Shiga duk sukayi driver ma yashiga maxauninshi ya tada motar yaja su Abdul na dagama saudart hannu.

Saida suka fice sannan ta sauke ajiyar zuciya murmushi a fuskarta, dan lokacin nan datayi dasu ba qaramin tasiri yayi ba wajen gusar da damuwarta, sosai take jinta cikin nishadi.

Juyawa tayi takoma ciki, bata iske kowa falo ba hakan yasata hayewa sama don gabatarda sallar asr don wasu massalatan ma harsun gama.


Tana zaune kan sallayarta taji knocking din kofa, shafa addu'ar tayi sannan ta miqe ta dauke sallayar ta dora saman bedside locker sannan tanufi kofar.

Tana budewa taga mamy tsaye bakin kofar tana kallonta.

Murmushi tasaki sannan ta matsa don bata damar shigowa.

Shigowa mamy tayi dakin itakuma ta maida kofar tarufe sannan itama ta shigo.

Samun wuri mamy tayi a gefen gadon dakin ta zauna sannan ta nunama saudart dake tsaye gefenta alamun itama tazo ta zauna.

Babu musu ta tako ta zauna inda mamyn ta gwadamata ta zauna ta sauke kanta kasa.

Shiru ne yadan ratsa dakin kafin mamy ta kawar da shirun ta hanyar cewa
"Saudart..."

Dagowa saudart tayi ta kalleta batareda ta amsaba

"Gayamin gaskiya, meyasa kika amince da cigaba da zama da mijinki?" Ta tambayeta tana tsareta da idanu.

Dan murmushi saudart tasaki tana sauke idanunta sannan ta girgiza kai ahankali.

"Look, ba maganar kurame zakiyimin ba, ki bude baki kiyimin magana" inji mamy

"Babu komai mamy, kawai gani nayi hakan yafi, tunda allah yakawo fahimtar juna atsakani bekamata kuma mu butulcemashi ta wannan hanyar ba, afterall kowa nada laifi a wannan case din this will serve as a lesson to us" tafada vatareda ta yarda sun hada idanu da mamyn ba.

Shiru mamy tayi tana nazarinta don kwata kwata bata gamsu da dalilantaba

"Saudart kin amincene....saboda ni?" Ta tambayeta ahankali idanunta kafe a kanta.

Dagowa saudart tayi ta kalleta saidai kuma takasa cewa komai sai hawayen da ke qoqarin taruwa a idanunta.

Sadda kai tayi qasa tashiga girgiza kai ahankali alamun A'a

"Saudart look at me.. nace kin amincene ki cigaba da zama da wanda bakiso ne saboda ni?"

Bata kalletan ba sai amsa mata datayi asanyaye da

"Mamy nariga na fadamaki dalilina"

Kamo hannunta duka mamy tayi tana matsowa kusada ita sosai

"Then look into my eyes and say it" tafada tana kallonta

Kasa dagowan tayi sai hawayen dasuka silalo mata suka digomasu a hannu.

"Kenan saboda ni kika yarda?" Inji mamy asanyaye.

Kasa amsawa saudart tayi sai hawayen dasuke saukomata ahankali.

Tasan wannan ne karo dabiyu ta zata cuci kanta arayuwa, nafarko tayine saboda daddy, mahaifi kuma jajirttace akanta yanzu kuma saboda mahaifiyarta mai qaunar cigabanta.

Bazata iya jure ganin mamy cikin damuwa da 6acin rai ba bayan tasan tanada hanyar magancesu, bazata ta6a bari mamy taji kamar batada wani matsayi awajenta kamar yadda tafada kwanaki, tana iya sadaukar da farincikinta ga mutanen nan biyu muddin su zasu samu farincikin don tasan suma sun sadaukar da fiyeda hakan akanta.

Ta yarda zata cigaba da zama da ashraf ne don gujewa 6acin ran mamy, ta yarda ne don mamy ta daina tunanin batada matsayi a wajenta bane. She sacrifice her happiness for her and she's ready to do more sacrifices for her muddin hakan zai sata farinciki.


"Saudart why? Kinsan abinda kikayi kuwa? Kin yarda ki zauna da wanda bakiso na tsawon rayuwarki? Saboda me? Saboda nayi blunting ranan cikin fushi? You should have know i don't mean all i've said, 6acin rai ne kawai yasani fadin wadansu abubuwan amma shine zaki tafka kuskuren dakikayi a farko?"

Itadai shiru tayi sai hawayen da haryaunzu be bar gangarowa ba.

"To bazai yiwuba, indai saboda ni zakiyi zaman cutuwa to tun wuri a warware wannan abun, cos baxan iya jurar ganinki kina rayuwar qunci ba"

Sai a sannan ta dago kanta jin yadda mamy ke magana seriously.

"Mamy.." tafada ahankali saikuma tayi sniffing tasa hannu ta share fuskarta sannan tasake cewa

"Mamy duk ba wannan ba nake buqata ba yanzu, addu'arki nafi buqata, bamu saniba wataqila hakan shiyafi alhairi, na yarda da farko saboda daddy dukda banaso amma a sakamakon hakan daddy ya sake re-uniting da mutanenda zumuncinsu ya dade da watsewa, yanxu kuma na yarda saboda ke saboda farincikin ki nasan bazan ta6a danasaniba, insha allah alhairi zai biyo bayan wannan ma kamar koma fiyeda wancan. So mamy batin tada magana bata tasoba, addu'arki kawai zata zama gata agareni"

Kallonta kawai mamy keyi cikin tausayawa, tasan saudart diyace mai biyyaya tasan abinda ya faru ba laifinta bane maiyasa 6acin rai ya rufemata idanu ta gayamata irin magangganun data gayamata? Tasan bata qaunar 6acin ranta kuma kullum cikin taka tsantsan take don gudun 6acin ranta meyasa takasa tunawa da hakan alokacin?

Jawota tayi vatareda tace komaiba ta rungume.

Luff saudart tayi a kafadar mamy tanajin wani dumin dadi na ratsata wanda har hakan saida ya wanzar da murmushi a fuskarta.

"Allah yayimiki albarka saudatu, allah kema yabaki 'ya'ya masu biyayya masu gudun 6acin ranki wadanda zakiyi alfahari dasu duniya da lahira"

Qara lafewa saudart tayi jikinta cikin jindadin addu'ointa tana amsawa da amin

"Allah yasa hakan shizai fiyemaki alhairi allah yasa kici ribar haqurinki"

"Amin mamy na" inji saudart murmushi fall fuskarta.

Ahankali ahankali mamy kemata nasiha gameda haquri da zamantakewar aure tana nusar daita nauye nauyen dake kanta na haqqin abokin zamantakewar auren nata.

Itadai saudart batace komaiba sai lafewa datayi jikinta tana sauraronta magangganun kuma nasamun matsuggunni a can qasan zuciyarta.

Ta dauki lokaci mai tsayi tana mata nasiha da shawarwarru inganttatu wanda hakan yayi nasarar kashe jikin saudart murus.

Daga qarshe tace "yanzu meyasa kika dawo nan harda uwar trolley? Sokike baban naki yaga kamar ni na huremiki kunne?"

Murmushi saudart tayi tace
"To mamy dama waya huremin kunnen?"

Dunguremata kai mamy tayi tana tashi tsaye tace
"Oho dai nidai babu ruwana is better kizo ki koma"

"Mamy shifa yace inzo" tafada a shagwa6e

Ta6e baki mamy tayi ta bude kofa tana cewa
"Kanku dai akeji bari naje nasan yanzu wadancan lasfikokin zasu dawo daga islamiyya su kuma rikita gidan da hayaniyarsu" ta fice.

Ajiyar zuciya saudart ta sauke bayan fitar mamy takoma ta jingina da kan gado.

Sosai takejin wani irin dadi da nishadi a zuciyarta tasan muddin iyayen nata zasu cigaba dayimata addu'a to bazata ta6a ganin ba daidai ba a rayuwarta.

Komawa tayi ta kwanta tana hasaso yadda zamansu zai kaya da wanda bata ta6a jin ko digon sonshi a zuciyarta ba, saidai ta qudura a ranta koma menene bazata ta6a barin tsanarshi ya hanata neman aljannarta ba awajenshi, zatayimashi biyyaya bakin gwargwado don neman aljannarta amma bazata ta6a budemashi kofar zuciyarta ba bare sonshi yashiga.


Kusan tare Abba dasu Abdul suka dawo da marece, shima abba yayi mammakin ganinta kuma yaji dadi sosai dayaji tazo tayasu yan kwanaki ne.

Da daddare haka suka baje a falo sunata kwasan fira suna dariya wanda firar yau tafi ta kullum dadi saboda kasancewar saudart acikinsu, saudart nada baiwar da idan tana waje sai an gane kuma komin qanqantar lokacin dakukayi tareda ita idan ta tafi saita barku da kewarta, that's her vibe.

Sai da lokacin kwanciya yayi sannan kowa ya haqura akaje aka kwanta.

Tana komawa daki kuma suka dasa da daddy dake can cikin kewarta sai qorafi yakemata wai ta tafi ta barshi, saida barci yafara cin qarfinta sannan sukayi sallama ta kwanta.

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–


Yau kwana uku kenan da dawowar saudart gidan mamy.

Zaune take kan kujera, kaffafunta a saman kujerar ta takure waje daya idanunta kafe da wani english novel dake hannunta mai taken *ice and fire*.

Ta shagala sosai a karatun novel din don sosai labarin ya qayatar daita don sai sakin murmushi take akai akai.

Ringing din wayarta ne ya katse mata karatun tasa hannu ta daukota batareda ta janye idanunta daga kan novel din ba.

Dagawa tayi ta kara a kunne batareda ta kalli screen din ba tayi sallama.


Lumshe idanu yayi a dayan 6angaren ya bude cikin wani irin yanayi sadda muryarta ta dakar mashi dodon kunne. Batareda yace komaiba.

Jin shiru yasata duba screen din taga baquwar number ce hakan yasata dan yamutse fuska ta maida wayar a kunnenta tace
"Hello?...hello?" Amma shiru ba amsa

"Mtcheew network problem" tafada tana katse kiran ta ajiye wayar tacigaba da karatunta.

Furzar da iska yayi daga bakinshi yana dan murmushi sannan yasake dailing din number.


Wani dogon tsaki taja wanda har saida su habeeb suka juyo daga kallon dasuke suna kallonta.

"Kema ki koma ciki mana ki daga wayar dama tayaya zakiji ana kallo?" Inji mamy da itama tana falon tana danna wayarta.

Miqewa tayi batace komaiba ta nufi sama tana daga kiran da harya kusan tsinkewa.


"Hello?..." tafada tana shigewa dakinta.

Shiru!

"Look nifa banjin komai, idan ansan baza'ayi magana ba adaina bugowa mana idan kuma network ne kindly send sms dukda banga alamun network dinne ba" tana kaiwa nan ta tsinke kiran ta maida wayar silent tanajan tsaki ta fada kan gado tana cigaba da karatunta.


Sauke wayar yayi daga kunnenshi yana murmushi jin ta tsinke wayar. Jin muryarta kadai ba qaramin nishadi yasashi ba.

Komawa yayi ya jingina da kujerar office dinshi yana kallon number tata wanda dakyar yasameta a wayar baby daya sace jiya da daddare.

Shiga yayi wurin saving din contact yayi saving din number da *other half* yana murmushi.


Bude kofar office din da'akayi yasashi dagowa ya kalli kofar still murmushi a fuskarshi.

Sadeeq ne yashigo looking so tired don kallo daya zakamashi kasan ya kwaso gajiya don tie dinshima a safsafce yake.

Dan hade rai A.A yayi yana kallonshi harya je wajen qaramin fridge din office din ya dauko ruwa mai shegen sanyi yadawo ya zauna ya 6alle murfin yashiga kwankwada.

Tsaki ashraf dake binshi da harara tundazu yayi yace
"Nifa na rasa gane kanka kwana biyun nan, saidai kazo office da safe bayan azahar you are nowhere to be found sai gab da za'a tashi sannan ka lalla6o kadawo, gidan uban wa kake zuwa on duty" yafada yana hararanshi.

Banza sadeeq yayi ya kyaleshi har saida yaga bayan ruwan sannan yayi cilli da goran yana komawa yana balancing akan kujerar dayake akai.

"Kutt.. wlh kaje ka dauke kasa a waste basket wannan wane irin wulaqanci ne?" Yafada yana ajiye wayar hannunshi.

"Mtcheew headache ne kai wlh" inji sadeeq yana tashi zaibar office din.

Saurin tashi ashraf shima yayi ya nufi inda yayimashi jifa da goran ya dauka yadawo ya cusamashi a hannu yace
"Tafi da abinka kuma kayi gaggawar rubutomin note akan inda kake zuwa yawon gantalinka na yan kwanakin nan ko kaga takardar sallama wlh"

Kya6e baki sadeeq yayi yanufi kofa hannunshi maqale da goran ruwan da ashraf ya cusamashi yana cewa "mad oo"

"Zakasan mad oo idan banga note dinba first thing tomorrow morning" inji ashraf yana kwafa.

Bude kofar yayi yafita yamaidota da karfi ya rufe.

Girgiza kai ashraf yayi kawai yana murmushi sannan yakoma wajen desk dinshi yana kaikaye stuff dinshi don lokacin tashin nasu yayi cikin zuciyarshi kuma yana wondering ina sadeeq ke zuwa yan kwanakinnan da rana don abin yafara damunshi, mutum kamar tsinke saidai ka nemeshi ka rasa?

Haka ya ida kammala kayanshi ya fito daga office din yanajin wani nishadi a zuciyarshi duk sadda yatuno muryar saudart dayaji dazu acikin kwanyarshi.

Shigewa yayi cikin motarshi ya tada yafice daga company din feeling very lively...✍


Ummin fasihuπŸ§šπŸ»β€β™€οΈ

πŸ‘°πŸ»πŸ€΅πŸ»AUREN KWANGILAπŸ€΅πŸ»πŸ‘°πŸ»
(Contract marriage)



Story written by Ashaanty loveπŸ’–
(Ummin fasihu)






082




Washegari jumua't babbar rana.

Ashraf ne da sadeeq cikin mota suna kan hanyarsu ta dawowa daga sallar jumu'a.

Sadeeq ne ke tuqi while ashraf na danne danne a waya.

Sosai ya shagala da abinda yake a wayar don bema lura da sadeeq ya dauki wata hanyar ba saida sukayi nisa sosai sannan ya ankara.

Kallon waje yayi yana yatsine fuska sannan yajuyo ga sadeeq yace
"And where are you taking us to?"

Ta6e baki yayi yace "sai yanzu ka lura"

"That's not the answer to my question" ashraf ya ansamashi yana harararshi

"Inda kake complaining ina zuwa zan kaika kaima" sadeeq ya amsa mashi yana shan wata corner

"Ina kenan?" Inji ashraf

"Gani ya kori ji" inji sadeeq batareda ya kalleshi ba.

Be sake cemashi komaiba sai maida hankalinshi dayayi kan wayarshi yana scrolling information on *how to make a girl fall for you* dayayi browsing.


Jin tsayuwar motarsu ya dawo dashi daga duniyar karatun daya lula, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dago idanunshi daga kan phone din yashiga bin inda suke da kallo cikin mammaki.

"Ina ne nan?" Yafada still yana bin harabar da kallo cikin mammaki

"Idanunka sun fara ciwone halan?" Inji sadeeq yana bude murfin kofar sannan yafita.

Shima fitowa yayi yana qara bin environment din da kallo.

"Waye be lafiya?" Inji ashraf yana kallon sadeeq

"Kaidai muje" inji sadeeq yana yin gaba.

Maida wayarshi a aljihu yayi sannan shima ya maramashi baya yana wondering waye be lafiya aka kwantar dashi asibiti.


Saida suka biya office din wani Dr sannan suka fito gabadaya da Dr din suka nufi wani ward, shidai ashraf binsu kawai yake batareda yasan wazasu je ganowaba.

A bakin wani ward suka tsaya Dr din yabude kofar yashiga sadeeq yabishi sai lastly ashraf da shima ya maramasu baya very eager to know what's happening.

Daga farko be dago wacece ba saida yakusan kaiwa bakin gadon sannan ya ganeta wanda hakan yasashi tsayawa cak daga tafiyar dayakeyi yana kallonta.

Itama kallonshi take agalabaice da alamu dai tana jin jiki ga wasu hawaye dasukayi forming a idanunta dasuka fada ciki.

Juyawa yayi batareda 6ata lokaciba ya nufi hanyar fita don baxai juri ganintaba don zuciyarshi wani irin suya take.

"My.... my please don't leave...please" tafada cikin muryar kuka.

Beko saurareta ba ya cigaba da tafiya harya isa bakin kofa yakama handle zai bude yaji tace
"Please don't leave without forgiving me, nasan mutuwa zanyi, please forgive me" tafada cikin kuka sosai.

Tsayawa yayi hannunshi kan handle din kofar batareda yajuyo ba.

Ganin hakan yasata cigaba dacewa

"Am so sorry my... na cuci kaina, beebah ta cuceni, nabiyewa son zuciya da hudubar muguwar qawa nafada hallaka, please forgive me"

Shiru yayi yana sauraronta zuciyarshi na zafi, duk ya tuna kazafin dataje tayimusu wajen ummy saiyaji kamar yaje ya shakureta a inda take.

Cikin sheshekar kukan dabai fita tacigaba dacewa

"Ashe beebah ba masoyiyata bace? Ta kaini ta baro, A.A nasan bani cikin mata masu kyawun hali, nasan bana cikin masu isashiyar tarbiyya.

Ashraf nasan kasoni ada, kasha yunkurin nunamini hanyar gaskiya amma nayi wasa da damata na 6ata wayauna na biyewa rudin qawaye da rayuwar turai na lallata alaqar dake tsakaninmu.

Ashraf tunda nafara ganinka a uk nakamu da matsanancin sonka wanda hakan yasa naji idan ba kaiba babu wanda zan iya rayuwa dashi amatsayin mijina.

Hakan yasani tattalin kaina da mutuncina don kai ganin kai kamili ne.

Duk iskancina ban ta6a wuce romance don nasa a raina kai kadai zanba kaina saboda na samama kaina mutunci awajenka bayan aurenmu.

Ranar daka ganni da chris muna kissing har hakan yayi sanadin rabuwarmu, aranar nashiga tashin hankali sosai kuma nadama tashigeni amma na nade tabarmar kunyata da hauka don ganin zan wulaqanta a idanun jama'a.

Daga lokacin natuba daga romance life saidai kaqi kabani wani damar.

Nabi duk hanyar danasan zanbi inshawo kanka amma kaqi saurarata.

Alokacin da labarin aurenka ya riskeni na shiga tashin hankali sosai.

Tun a lokacin naso tada bori amma beebah ta hanani acewarta asannu zamu warware komai.

Na biyemata nakuma yarda daita saboda duk duniya banida qawa kuma aminiya data fita.
Ita tayi convincing dina takaini wajen wani boka da nufin shiga tsakaninku kai da matarka yakuma cusa maka tsananin sona yadda zakaji bazaka iya rayuwaba batareda niba"

Shiru tayi sakamakon kukan dayaci qarfinta.

Izuwa yanzu ashraf yajuyo yana kallonta ya jingina da kofa hannayenshi harde da qirji shima sadeeq ita yake kallo shima jingine da bango.

Babu wanda yacemata uffan har taci kukanta mai isarta sannan ta tsagaita don kanta sannan tacigaba dacewa

"Bansan wannan ne hanyar lallacewar rayuwata ba, bansan kaini zatayi ta baro ba.

Ataqaice dai the man demand for my virginity domin samun biyan buqata ta.

Dafarko naqi yarda don banga amfanin auren ba bayan nayi loosing din abinda zai kankaromin mutunci awajenka ba amma sai sukayi convincing dina dashi da beebah cewa aikin da za'ayimaka bazai baka damar tantance am virgin or not ba, kawai dai burinka a lokacin ka mallakenine kuma bazaka ta6a barinaba har abada.

Ina sonka kuma banida burin daya wuce in mallakeka na har abada hakan yasa magangannunsu sukayi tasiri azuciyata nabada kai"

Sniffing tayi ahankali sannan tacigaba

"ranar nayi loosing pride dina ga dirty tsohon nan, nayi kukan takaici sosai saidai beebah na kwantarmin da hankali cewa yanzu you're mine forever.

Shiru shiru har aka kwashe wata banji alamun nasaraba saima canjin danakeji ajikina cos am always sick.

Hakan yasa na tsare beebah da qorafi nan ta kwantarmin da hankali tareda cemin akwaima hanya mafi sauqi dazamu warware aurenku batareda munjira bokanmu ba.

Nan tagayamin tasamu information awajen helen cewa aurenku is based on contract.

I was shocked alokacin don abin yazomun a bazata, nan na buqaci evidence tace tasa helen tasamo mana akan yarjejeniyar huge amount of money.

Hakan yasa nadanji dama dama saidai me? Bayan kwana biyu jikina yayi worsening.

Dakyar na iya kai kaina hospital inda aka gwadani aka bani result din daya giggita rayuwata.

Result ne na juna biyu wanda ya nuna inada jaririn ciki sai kuma cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS.

Ina gama karantawa na yanke jiki nafadi saidai nasake bude idanuna naganni akan gadon hospital.

Nayi kuka sosai nayi baqinciki marar misaltuwa.

Qarshe dai na lalla6a dakyar nakai kaina gidan beebah.

Sosai na burkuce mata don gani nake tawa tazo qarshe kawai.

Dakyar ta rarrasheni ta nuna haryanzu is not too late wajen mallakarka, ta fiddomin takardun datasamu wajen helen na yarjejeniyar aurenku takuma kitsamin yadda zan maku makirci wanda dolene umminka tasa ka aureni

Banida za6i, a lokacin banida kingin burin daya wuce in mallakeka kafin inmutu hakan yasa nazo har gidanku nayi maka kazafin danayimaka.

Bayan wannan ranar kuma zazzafan zazza6i yakuma lullu6eni ga laulayi daga qarshe beebah tabani shawarar terminating din cikin.

I dont have choice don alokacin inajin jiki sosai haka takawoni wannan asibitin don zubda cikin.

Wanda garin zubda ciki akasamu matsala mahaifata ta ta6u.

Tunda takawoni hospital yau kwana goma kenan ban sake ganinta ba, ina cikin matsanancin hali gashi tagudu tabarni, banida kowa, bansan ta ina zanfara contacting din yan uwana ba.

Beebah ta cuceni A.A, taci amana ta, tasani tafka kuskuren da bazan ta6a iya gyarawa ba.

Please forgive me ashraf, ka yafemin kona dan ji sauqin abinda ke damuna, ka yafemin ko allah zai sassautamin halin

Please Login or Register in order to submit comment