Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta katse kiran yabi wayar da kallo tareda tura mata text


_please my happyness mu hadu ko a garden ne leter_

Ita duk yasata cikin wani yanayi yazatayi da wannan mutum wai ?dole ta takamai birki gaskiya yau

Karfe takwas na dare duk sun gama diner suna zaune Afalon har Alhajin gaba daya Anty Nena lamarin zaman Safeena da dan uwanta yadameta gaskiya yana shiģa hakkin yar mutane dole tayi wani Abu Akai


Suna wurin har Sageer yashigo baiji dadin yanda yasameta Afalon ba ga Auncle yagaida su tareda samun wuri yazauna Suna magana da Alhaji Anty tace Safeena muje daģa ciki

Zamuyi magana, saida gabanta yafadi sannan tamike shima sageer yaji wani iri meye Anty źata fada mata da sai sunshiga ciki

Suna shiga Anty cikin hikima take tanbayarta dakuma nuna mata cewar harda laifinta mijinta ya banzatar da ita cikin dabaru da kuma na siha ta koyamata dabaru da kuma nuna mata yanda zata janyo hankälin megidanta

Har tabata wata hadaddiyar humra tace tariga Amfani da ita idan zataje gurin Alhajin tunda suka wuce yarasa natsuwa saida yaganta duk jikinta asanyaye tashige dakinta tana tunanin mafita

Ta dade azauʼne tana saka da warwara kafin ta mike ta sheko wanka tashafe jikinta da mayuka dakuma turaruka masu kamshi daga karshe tasaka wata guntuwar nitie ta dora dogon hijab akai kafin ta tsaya tana tunanin

Taje ko karta je ?idan taki zuwa Anty zatace bata dauki shawarar taba haka ta janyo kofar tafito Alokacin bakowa haka tafara takawa cikin sanyin jiki zata nufi dakin Alhaji

Batareda ta shiryaba taji anfisgota cikin mugun zafinshi kafin tace me yasata cikin dakinshi cikin muguwar kaduwa da kuma tsoro take kallon yanda jikinshi ke rawa ga idonshi yakada yayi jawur


Duk ta tsure cikin fusata yace ina kike shirin zuwa Safeena? Yafada cikin kidimewa itama cikin kosawa ďa lamarinshi tace dakin mijina zanje cikin hasala yace mezakiyi acan?

Cikin bushewar zuciya tace zanbashi hakkinshi da yakamata inbashi tun farko cikin bugawar zuciya tareda zafin rai yace jikin naki zaki mallakâ mai?

Kafin kace me sai hawaye yafara bin kumatunshi cikin rage murya da kwantarda zuciya yace Safeena please don't wallahi inkin bashi kanki zan iya mutuwa ina kishinki ina bala in kishínki


Meyasa kike kallon idona ki fadamin zakiba wani namiji jikinki Safeena you are mine only please don't ke tawace cikin kasa da murya yakara matsawa kusa da ita zai riketa tace

Karka tabani yace why? Ni bankai namiji bane um look at me Safeena meye nakeyi wanda bakyaso tell me i will stop just tell me duk jikinshi narawa yake fada mata maganaŕ

Ga hawayenda yakeyi da duk yabatatausayi don itama tana sonshi amma yazatayi itafa matar aurece ta yaya zata rika biyemai idanshi idonshi yarufe ita da sauran hankalinta dole tayi controling kanta

Cikin ajiyar zuciya tareda kallon cikin idonta yace kina sona Safeena? Cikin kidima tace ni insoka ina matar aure? No way and please kafita hanyana ka hana ni sakewa

Har addu a nakeyi dama bantaba ganinka ba arayuwata katakurani ka hanani sakewa kabaŕni haka takarasa tana fitarda hawaye cikin sanyin jiki dakuma damuwa yake binta da kallo

Harta gama fadar abinda taga dama yana mata wani irin kallo cikin rashin kuzari yace shikenän jeki amma duk Abinda yasameni kece sanadi yabude mata kofar tafita sannan yakoma ciki tareda fara wasu hawayen masu zafi

Gaba daya bataji dadin kalamanda tafada maiba amma shine kawai mafita ita kanta tasan idan tace bata sonshi tayi karya shine dai dai da ita shiyaka mata ta aura sai yanzu tagane kuskurenta.

Dama Abinda Aunty Zaliha ke kokarin nuna mata kenan? Hmmm.

Washe gari har dare bata sa Sageer a idonta ba tayita sintirin yawo afalo har zuwa waje har wayewar gari duk ta damu saida kowa yafita tayi karfin halin zuwa dakinshi domin taga ko lafiya Amma kofar Arufe wanda ya nuna mata bama ya gidan

Yinin ranar kamar mara lafiya haka tawuni har wani zazzabi yafara shigarta tsabar damuwa da tunã ni koda mutanen gidan suka dawo dakyar tafito cikin dauriya Anty tace lafiya kuwa Safeena ?

Cikin sanyin jiki tace kanta keciwo tamata sannu Menal ma ta mata su Al ameen ma suka mata sannu Aunty

Menal ce tace Aunty bros tunjiya bai kwana agidaba ko yashigo yau? Cikin bugawar zuciya da tsoro tace Aa bai kwanaba? To ina yaje? Cikin zuciyarta take tunani

Wasa wasa har kwana uku shiru saida taji Aunty Nena tana fadama yara dazu ma sun hadu a office tasan cewa itace bayason gani bayan yasa mata sonshi sannan ne zai nemi kaura ce mata gaskiya bazata iya dauka ba

Allah kadai yasan halinda zucyarta take ciki kwana ukun nan dabata ganshiba cikin damuwa tafita garden tana zama tafara bin wayar hannunta da kallo tareda karanta messages dinda yake turomata kafin yayi fushi da ita

_ina kake ne?please come back i realy missed you.i love you too please come back tafada cikin damuwa_


Realy my pretty? Kamar daga sama taji muryarshi tamike akidime tareda kallonshi yana tsaye sanye cikin riga da wandon jeans yayi wani irin kyau, cikin shaukin so da kuma rufewar idanu ta nufeshi tana mai kallon don me zaka shiga hakki na daya wa

Cikin karyewar zuciya tana isa tafara dukan kirjin shi tareda fadin meyasa zakamun haka? Saida ka koyamin sonka sannan zaka juya min baya meyasa ka kaura cewa ganina kwana biyu?kasan halinda ka jefani kuwa?

Sageer why ?takarasa tana mai fashewa da kuka da kuma fadawa cikin faffadan kirjinshi batareda tayi tunanin ai HARAMUN bane tana matar aure soyyaya ta rufe mata ido har tamanta da rashin dacewar hakan

Duk tarukunkumeshi tana gursheken kuka kuma tana kan mai mitan meyasa zaigujeta ?meyasa zai wahalar da zuciyarta haka?

Cikin damuwa dakuma farin ciki yace relaxed my pretty am fine cikin kaďawar ido take kallonshi tana mai wani irin kallo tareda cewa yes i see you are fine, but what About me? Kasan irin halinda ka jefani kuwa ?

Yakuma janyota cikin rashin kuzari tareda mannãta akirjinshi yana shafa bayanta pretty Am sory kece kika nuna bakya sona zaki bama wani jikinki bayan kinsan ke mallakina ce dasauri ya kuma dagota tareda cewa

Pretty kinje dakinshi? Please yatabamin ke tell me? Kifadamin baki bari ya tabamin jikin nan nakiba yana fada yana kare mata kallo baby! Kin san irin halin da nashiga kuwa nima cikin kwana uķun nan

Daurewa kawai nakeyi amma banda wani choice ne bayan hakan kidaina min zancen wani namiji baby zuciyata zata buga inada mugun kishi musamman Akanki.

Bazan daure ganinki awajenshiba banason ganinki kusa dashi pretty shiyasa na daìna zaman gidan nan Amma kinsan bazan taba daina sonki ba sonki yariga yashiga cikin jini na tundaga ranarda nafara dora idona
Akanki

cikin murmushin tsokana yace ranarda nafara ganin Safeena real dinta ranarda ta hana ni bacci baby kinsan aranar nasan inada sha awar kasan cewa da mace baby look at your structure yana me bin jikinta zuwa kugunta da kallo dasauri tayi baya tareda rufe ido tunawa datayi Aranar daga ita sai towel Sageer yaganta

Dagudu tayi cikin gida tana maijin kunyar Abinda tayi Aranar dakuma yau batareda tasaniba tajitayi karo da mutum cikin hanyarta tashigowa falon cikin firgici ta ja da baya ganin wanda ke tsaye yana kuma binta da wani irin kallon da takasa gane me hakan yake nufi?


_Shin yaganta ne Ajikin Sageer ko yaji Abinda suķe cewa? ........_🖊

*SANNU BATA HANA ZUWA FANS MUJE ZUWA*
[2/19, 2:43 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)


💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar


*godiya mara adadi HARAMTACCIYA SOYYAYAR FANS Kunayin yanda yakamata*

_UMMU JIDDAH.. mema zance miki ne kincika masoyiya ta hakika Allah yabar mu tare Yaraya mana JIDDAH_


1⃣4⃣
Duk tarude Abinka da mara gaskiya ya kalleta yace ina zakije haka Safeena kiķe gudu haka?

Hmm Ajiyar zuciya tasauke saboda tagane baigansuba kafin tace wani Abu shima yashigo cikin falon sai takuma tsurewa,

Abinka danamiji sai yawani waske tareda rabewa zai wuce yana cewa sannu Auņcle, yabishi da kallo kafin yace son inason ganinka yanzu,


Yace ok Auncle da sauri ta karasa cikin dakínta tareda dafe kirjinta gudun abinda zai faru kodai Auncle yagansu shiyasa yake kiran Sageer ?


Suna zaune Alhaji mu azzam yakira Aunty Nena Awaya itama tazo duk sun natsu wanda shi Sageer ko Ajikinshi baya shakkar duk Abinda zai faru Ahalin yanzu.


Indai Akan zancenshi da Safeena ne saida Alhaji yace Khadija! tace na am.
Kinsan watan nin baya kafin Sageer yakoma new york nayimai maganar Aure Anan surin ko?

Tace kwarai yaya yace ok zaki tuna meya fadamin Alokacin? Eh yace kayi hakuri har yadawo nija gaba daya. Alhamdulillah yanzu yadawo.

Kuma idan ban mantaba kanada yarinyar da kuke soyyaya da ita cikin tsunkewar zuciya da kuma kaduwa yama kidime yarasa ta cewa.

Saida yakuma cewa inajinka son lokaci yayi da yaka mata ace ka ajiye iyalinkanka yanzu, tsabar rudewã yace ok Auncle zanyi tunani akai kaban kwana biyu ,

Badamuwa amma fa kasani ina nan Akan bakana idan kashirya sai in samu Aminina muje gidan su yarinyar ko ? Cikin dauriya yace na gode Allah yakara daukaka sannan yawuce

Aunty Nena tace yaya kana ganin yarinyar nan yakamata Ahadata da son kuwa? Meyasa kikace hakan ? Saboda naga ita take sónshi ba shike sonta ba

To ke kinganshi da wata yarinyar ne bayan itan? Aa amma yaya anawa tunanin da anbi ahankali ko.

Khadija ku mata lokuta da dama tunaninku sai Ahankali duk cikin maganar da kikayi baki ban wata kwakkwaran hujja ba

Shikanshi da baya sonta zai fàda Amma baice komai ba so kema kiyi shiru kawai, tace shikenan yaya Allah yashige mana gaba Ameen.

Duk wannan maganar da sukeyi Akunnen menal gaba daya hankalinta yatashi bros zai yarda da Auren Humaida?

To ita kuma fa?meyasa dady zai mata haka? Cikin matsanan cin kuka tasan yanzu dadynta zaice tayi karama da Aure Amma ita gaskiya tanason brothern ta


Duk da yanzu tashiga sixteen years amma dayake goyon hutu ce zaka dauķa takai twenty tsabar cikar da takeyi Ayanzu

Ita ta inama zata iya furtawa Sageer wannan zancen tasan ko banza kallonta yakeyi a karamar yarinya bare kuma har ya yarda Ya Aureta


Kuka takeyi irin mai ban tausayin nan gaba daya tarasa wanda zai taimaketa can ta tuna Safeena tamike da sauri zuwa dakinta

Tana kwance tun lokacinda tashigo dakin tana faman tunanin ya akayi ta kasa controling kanta ne wai har tabari yafahimci itama takamu

Hartakaita ga rungumeshi tafara istigifari cikin zuciyarta tana tuna yanayin datashiga lokacinda tafada cikin kirjinshi

Jitąyi kamar anyi mata rahama gabadaya taji kamar batada wata sauran damuwa Arayuwarta Hmm ta sauke Ajiyar zuciya mai sanyì tana cikin hakan

Menal tafado dakin cikin kuka tareda fadawa kan jikinta saida taji tsoro don bataji shigowarta ba cikin kidima tace Menal lafiya?

Meya sameki? Cikin kuka tace Aunty bros zaiyi Aure🙆‍♀ dum kirjin Safeena yabuga da karfi cikin firgici dakuma mugun tsoro tace bangane ba kimin bayani please

Cikin kukan take gaya mata komai Ai tashin hankalinda tashiga na Menal wasa ne kafin kace me itama sai kuka tareda rungume Menal

Kukan da Safeena keyi shiyasa Menal tayi shiru cikin matukar mamaki take kallonta tareda sakin baki tasan dai wannan ba kukan tausayinta take ba,

Gaba daya tamanta da wata Menal tausayin kanta takeji tunda Gwara Menal tana da hope Amma ita fa? Menal zata iya Auren Sageer ko A yau Amma ita fa?matar Aure ce da igiyoyin wani Akanta

Saida Menal ta dafa ta tareda cewa Aunty lafiya ? Sannan ta saita kanta tareda saurin wayin cewa tace natausaya miki ne Menal,

Cikin dauriya tace kiyi hakuri hakan bazai yuwuba ma bazai Aureta ba kinji ki daina kuka cikin mamaki tace Aunty Aini nayi shiru Amma ke mezai saki kuka har haka?

Tace banason ganin kukanki ne shiyasa tace ni ai nayi shiru kema kiyi shiru haka nan tana share mata hawaye _tofa wata sabuwa_

Aranar mutum uku sunkwana cikin damuwa ko barci barawo saida yabar Sageer da Safeena Menal dai ita ta runtsa Abinta tunda Auntyn ta tabata hope

Tunda sassafe yafita Agidan sai gidansu Yusuf shima saida yatsorata don rabonda su hadu tun Asibiti dasuka rabu da fada Akan me zai kira mai Humaida shikuma yace yayi saboda gujê mai fadawa halaka

Kuma koyanzu shiyazuga Auncle Akan zancen Auren Amma bai mai baýani bã kawai yafada mai yana soyyaya dawata baturiya don haka gwara Auncle yamai Aure kila zasu rabu


*Yusuf yabarota*koda yaganshi yasan kwanan zancen amma yamatse yace mai ya akayine Dude naganka da safiyar nan ?

Cikin rudu yace kaji me Auncle yace waifa in Auri Humaida wannan yarinyar yazatayi dani? bangane yazatayi dakaiba? Batada Abinda zai burgeni Ajikin macen da nakeso

Gabadaya bata cikin tsarin matar da nakeson Aura cikin mamaki Yusuf yace to kai meya hana tunfarko ka bude ido kazäba duk matan dake cikin Abujar nan ba wacce tayi maka?

Ai ba dole saika Aureta ba kawai ka bude ido kazabo matar Aure kafita hanyar wannan *HARAMTACCIYAR SOYAYYAR* daka jefa kanka ciki.

Cikin mutuwar jiki yace bazaka ganeba Dude na rasa ta yanda zanyi incireta Azuciyata how? Inason Safeena fiye da kaina Yusuf,

Yace naji what Abaut Menal itama kasani fa tana sonka duk dabata fadaba yanayinta kawai yanuna itafa? Mtsww yayi tsaki wanʼnan jaririyar

Sokakeyi inkashe musu yařinya? So ita Safeenar ce kadai kenan zata iya dakai Sageer ba araina mace duk kankantar ta tana iya daukar nauyin mijinta,

Bazaka taba fahimta taba Yusuf duk wata mace kallon da nakema irinshi nakema sauran mata banga macen da tataba burgeni ba sai safeena i love Safeena oñly

Hmm Yayi Ajiyar zuciya don Abin yafi karfinshi sai shiru har suka rabu bawata mafita da yasamu awurin Yusuf

Karfe goma na ranar da yake Asabar ne ba aiki duk suna gida har yaran Alhajima yana hutawa Adakinshi dàga Aunty Nena Sai Safeena da Menal Afalon yaran na leson

Humaida tashigo cikin yanga tareda sallama tana wani karkada jiki gajikin sai Ahankali ba Abinda yake motsi irin wanda ke haukata oga Sageer

Tana karasowa tasamu gefen Aunty tareda gaisheta Aunty ta amsa cikin sakin fuska tareda tanbayarta muta nen gidan sannan tadan wani juya tace masu Safeena hy duk ba wacce ta ko kuma kallonta

Hartagama fi ilinta ta ce Aunty Sageer yana ciki tace gaskiya bansaniba Am Menak ki duba min brothern ki ko yatashi cikin turo baki tace baya gidan tace banson shashanci banaji dawowarshiba dazu?


Bayanda ta iya haka tamike tashiga dakin yana aikin wato tunani tashigo tareda dauke kai bros Anakiranka kafin ma yace wani Abu tayi waje yabita da kallo yakai minti biyar kafin yafito

Cikin takunshi yana sanyeda amles din riga dakuma treequater duk farare gaba daya yatafi da hankalin mata ukun dake zaune Afalon kowacce na aika mai da nata irin kallon

Amma shi hankalinshi yatafi wurin rabin ranshi bakuwar ma bai gantaba yasamu wuri saitin da zai rika ganinta don gaba daya ganinta da yayi saiyaji duk damuwarshi ta yaye

Saida Humaida ta taso tazauna gab dashi tareda rike mai hannû sannan yaganta cikin kwarkwasa baby naji shiru shiyasa nazo inkara ganin jikinka cikin jin haushinta yace tnks

Itako Safeena Hmm jitake kamar tashaketa yanda ta wani rike mai hannu kamar zata shige jikinshi shikuma harara da kallon Akwai yaki mai zuwa take jefa mai Menal da Aunty tuni sunbar falon


Aunty cewa tayi irin wannan rashin kunya budurwa kibiyo saurayi har gida kuma ki na shigemai? Tom Allah yaraba mu da zamani


Cikin tsananin kishi ta mike tareda shigewa cikin dakinta ta banko kofar yana kallonta harta kule sannan yakalli Humaidan yace Wai yaushe zaki daina zubarwa da kankiAji kina zuwa nan gidan?

Nan fa ba turai bane kigane hakan kuma ni nasan Al adana ok so just go and tank you for d visit cikin rashin kuzari tareda rashin zuciya takeson takuma rikemai hannu ya mike yace muje cikin matse rai

Yata iya dole tawuce yana binta Abaya hartakai wurin motarta yabude mata tashiga duk A idon Safeena tana kallonshi ta window tana fita da motar yashigo cikin gidan

Hango shigowarshi datayi yasata fitowa daga dakin domin wani irin bala in kishin shida yatokare mata kirji jitake inbata tunkareshiba yanzu Akawai matsala.....🖊



*To Allah dai ya kyauta Safeena kishin Sageer*?Hmmm
[2/19, 2:50 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)


Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar



FAGEN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION


Gidan zaman lafiya, Aminci had'in kai da yardar juna insha Allah🤝

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*Bismillahir rahamanir rahim*



1⃣5⃣
Tana bude kofa yana tsaye afalon yana kallon kofar dakinta tayi tsaye tana mai kallon kenan da ģaske Auren zakayi?

Yace pretty zomuyi magana please kallonshi kawai takeyi cikin damuwa nan take wani matsanan cin kukan yakuma zuwa mata takoma ciki tareda kulle kofarta da key


Duk hankalin Sageer yagama tashi saboda ganin irin yaʼnayinda tashiga to meyasata irín wannan kukan?

Duk yakasa natsuwa yakoma dakinshi yadauki waya yafara kiranta tana kallon wayar taki dauka yakira yakai sau biyar batayi picking ba

Ya tura mata text kamar haka _(don Allah baby na kifito ko ki bude min kofa please_)

Ta bude tagani Amma tasan ba Abinda zai iya yi mata tariga tasan shikenan tarasa shi bazata taba Auren shiba tunda da Auren wani Akanta

Takara fasa wani irin kuka yanzu yazatayi ? Yakamata ko wani ne tafada mawa ko zata samu sauki da sauri ta mike tareda canza kayan jikinta

Gyale kawai taja tareda makullin mota kowa bata fada maba ta fice agidan har takama hanyar gidan sû ta tuna yau kila Abbu na gida

Kuma tasan halin ma haifinta kawai tawûce gidan Aunty zaliha,da kyar takarasa cikin gidan tana shiga falon wani sabon kuka ya kuma zuwa mata

Aunty zaliha dake kicin da gudu tafito tareda sakin salati tana tanbayar meya faru sister ta janyota suka shige ciki don kar megidan yaji ko kuma yaran

Saida ta bata ruwa mai sanyi ta karba ko tsiyayawa batayiba ta kwankwada sannan ta mika mata goran cikin damuwa Aunty zaliha tace sister lafiya meke faruwa?

Sai hawaye kebin kuncinta tace please kimin bayani yar uwa kin daga min Hankali sakin ki yayi ne?
Ta girgiza ķai kunyi fada ne nan ma tace aa tace to kifada min damuwarki

Ko kinada wata yar uwar bayan ni ? Tace aa to kifadämin cikin kuka tace Aunty na cuci kaina kirjinta yabuga dam kifadamin meya faru?

Aunty kitaba kirjina harbawa yakeyi kamar zai fita Wallahi Aunty ina sonshi bansan lokacinda nafara sonshiba Aunty ba laifina bane cikin kuka tace nashiga uku tareda fyace majina

Aunty zaliha tace to don kinfara son mijinki shine me ai hakan akeso meye na kuka kuma ai saita tuna cewar baran baramar datake son ta fada Abin kunya Ayi mata Aure da megida takuma so yaron gidanshi


Ba arziki ta saita kanta tafara share hawaye Aunty zaliha ta tanbayeta sister Akwai wani abune daban da yake damunki ? Don wannan kukan naki bawai nã soyyayar mijin ki bane kawai


Ta tattaro sauran natsuwarta tace Aunty bakomai kawai banajin dadine
Aunty tayi murmushi tareda cewa kodai kin halbu ne don naga kinyi wani fresh kindan rame Hope Abun baya baki wuya sosai?

Tace bangane ba Aunty tace zama kigane ke kinfaya zurfin cikin tsiya komai bakya iya bude baki fada ma kowa harni da nake yar uwar ki to shikenan taja bakinta ta tsuke don ita bata masan mezata cê ba

Haka dai ta koma kaņ gadon Aunty zaliha ta kwanta tace nidai bari inkarasa girkina mijina nagida kifito ku gaisa yana fälonshi tareda yaran tace ok

Tamike tareda goge fuskarta da wifer sannan tadan shafa hoda da wetlips sannan ta nufi falon mijin yayar tata tanayin sallama yaran suka rugo da gudu oyoyo momcy

Ta rungumesu tareda karasawa cikin falon tana gaida mijin yar tata cikin tsokana yace yau Ämare ne Agidan namu?

Murmushin karfin hali tayi kawai tace eh wallahi ya Aiki ya kwana biyu yace Alhamdulillah hope kinga Auntyn taki ? Eh tana zuwa bata gama rufe bakiba Aunty tashigo da tray

Ta ajiye sannan ta shinfida dadduma akasa tajera musu Abincin tareda ajiye plate tace to ku sakko muci abincin Anan yau tunda ga sister

Tace no ita ta koshi Aunty tace is ur fevourite fa sis tuwon shinkafa miyan danyen kubewa oya kisakko kici Abinci

Kowa nacin Abincin amma ita tsakura kawai takeyi duk zuciyarta ba dadi

Saĺlamar mai aikin Aunty zaliha taji tace lafiya balki ? Tace Ana sallama da megidan ne cikin sauri yace ok ina zuwa tareda wanke hannunshi ya mike ya fita

Baifi minti biyu ba yadawo cikin dakin jin sallamar da Safeena tayi bäyan ta mijin yayarta shiya daga mata hankali

Sageer tafada cikin kaduwa duk ta firgice jikinta yafara rawa Aunty tabita da kallon mamaki to ina tasan wannan kuma? Kafin tasamu Amsa megidan ya mai ison shigowa tareda nuna mai kujera

Dukarda kanshi yayi tareda gaida Aunty zaliha sannan ne mijinta yake cewa wai yazo tafiya da Safeena ne cikin tsabar tsoro da rashin gaskiya tace Aunty yaron Alhaji ne babba


Aunty dai jikinta yayi mugun sanyi duk tarasa wane irin tunani zatayi saida Megidan yace zaliha ki zuba mai Abincin mana kafin ita ma ta gama ko

Duk tunanin ta ya sauya tarasa ta ina zata dafa tace hope kana cin tuwo don naga bakon namu bature ne cikin zolaya yace haba ai nafison tuwo akan kowane Abinci

Cikin minti biyar yasaki jiki yanata kwasar tiwonshi ita kuwa bayan loma biyu bata kara kodaya ba tana tunani

Meya kawoshi nan wama yafada mai täna nan gidan ?ita kadai take tunanin ta saida yacinye tuwonda Aunty tasa mài tas sannan ya wanke hannu yanata tanbayar yaran sunan su

Suna fadamai Aunty tace sister wannan babyn namu gaskiya yazo duniya saimun rankwasheshi tunda ya hana min sister cin Abinda takeso

Da sauri ta sunne kanta cikin tsabar kùnya da kuma tsoro wai waya fada ma Aunty tanada ciki?ita da miji ko hannunta baitaba rikewa ba ta yaya zatace wai tanada ciki cikin rashin tacewa tace Aunty bari mutafi

Shikam Sageer duk inda tashin hankali yake yashiga cikinshi tsundum ciki? Safeena kedaciki? Wato tabama Auncle kanta har tasamu ciki ?tashin hankalin da yatsinki kanshi aciki baya faduwa

Har sukayi sallama da masu gidan yace ta bashi key din motar datazo dashi cikin daure fuska tamika mai yakarba suka fita yashiga ciki mazaunin driver ta bude gefen tazauna ýa ja motar tana mamakin

To shi ame yazo? Abinda bata saniba bayan fitarta yazo dakin nata yasamu bata kuma yaga ba mota daya acikin gidan sanin da yayimata ko ince Afahimtarda yayi mata batada kawaye

Don baitaba ganin wata kawa tazo da sunan wurinta tazoba ya lura batada son mutane sosai shiyasa zuciyarshi tabashi taje gidan yar uwarta da tataba zuwa lokacinda yabita abaya daga shoping

Kuma yana isowa yagã motarta shiyasa yakira driveř yace yatafi da tashi motar sannan yasa Akamai sallama da megidan

_Arayuwata amasu karfin hali bantaba ganin irin na Sageer ba_

Azuciye ya fisgi motar tareda daukar titi ko kallonta baiyiba gaba daya baya cikin hankalinshi

Itama ta dauke kanta tareda mayarwa gefen titin Amamakinta kawai saitaga ya dauke wata hanyar daban ya nufi gida ina kuma zai kaita tayi saurin kallonshï tace ina zaka kaini?


Baiko kalletaba ya kuma fisgar motar saida yaje wata unguwa can dabata ko san ina bane kafin yafaka akofar wani dan madaidai cin gida mai bala in kyau da tsaruwa kamar na turawa yayi horn mai gadi ya bude mai

Yasa kai cikin gidan batareda yatsaya amsa gaisuwar mai gadin ba yana fakawa yafito tareda ce mata fito cikin daure fuska tace ni bazan fitaba kaban key

Intafi gidana cikin fushi ya fisgota tareda kulle motar yace shige muje tace nifa ba inda zani malam kabani key din motar intafi gida yagadai zata bata mai lokaci cikin zafi yadauketa kamar wata baby

Tana dukan kirjinshi tareda cewa ka saukeni banason iskanci meye haka wai cikin fushi yace kimin shiru ko ranki yabaci yanzuñnan

Megadi yasaki baki yana kallon ikon Allah wacece wannan kodai megida ýayi Aure ne?

Suna šhiga cikin falon yadireta tabi falon da kallo cikin mamaki falon yamugun haduwa yaji kudi kamar ana rayuwa aciki Ahankali tadawo da kallonta gareshi yana mata kallon tuhuma


Safeena ciki ?cikifa ?Jikin naki danake tattalinshi kika mallakama wanda baisan darajar shiba?cikin fushi dason kularda shi

Please Login or Register in order to submit comment