Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaishetaba tajuya ahankali tayi kwafa zanyi maganinki yarinya. takarasa gaban mirrow takara feshe jikinta da turarukanta masu kamshi dakuma tsada sannan tajanyo wani dan karamin gyalen kalan rigan ta yafa niko nace da babu gwara ba dadi amma wannan gyalen meya rufe Safeena? takun takalminta shiyaba Sageer daman dago dakanshi zuwa ga hanyarda yakejin karar dasauri yadukarda kanshi. Tsabar faduwarda gabanshi yayi, this girl is crazy yazata fito ahaka gaban auncle niko nace tofa mutum da matarshi?
Ba abinda yake aika mata dashi sai mugun kallo. Koda taja kujera tagaida kowa amma batako kalli gefenda yakeba cos she haté him da shida wannan fitsararriyar yarinyar duk zata saita musu zama basu san wacece Safeena ba har aka gama cin abincin ba abinda Sageer yaci amma bawanda yalurada halinda yake ciki. Har kowa yawatse dasaurinshi yamike yafada dakinshi taredã daukar makullim motarshi cos he needs some fresh air yana fita wani restourant yanufa yai odar fresh milk da cheese cake yasha gaba daya yakasa ganema kanshi har wayarshi tai kara yasa hannu yadauka hello dude can dayan gefen yusuf ne yace wat is wrong dude bangane makaba ne wannan karon?tunjiya da muka rabu i thought zaka nemeni amma shiru yanzu kuma nazo gidan baka nan meke faruwa? Noting kawąi stress ne but am fine yanzu kana ina ?yace kajirani gani nan zuwa yanzu yai cutin wayar tareda mikewa yabiya bill din sannan yawuce

Yana isowa suka shige cikin gidan yana tura kofan falon yayi saurin komawa baya tareda cema yusuf muje garden dude saboda ganin safeena da yayi tana kishingide akan kujeranda kesaitin shigowa falon yana tafe yana cewa dis girl is crazy baisanma maganar tafito ba saida Yusuf yace wai Menal sai sannan yasan maganar tafito yasamu kanshi dacewa eh ita metayi maka ne wannan karon don Yusuf yasan yanda Menal keson shigema Sageer, yace wai yamaganar wannan bussines din na texas dude yace yana tfy yanada akeso don muna samun incomes sosai ok dude wannan yarinyar tadamenifa tanaso inbata numbanka wanda takeda bayashiga so gşky nidai nabata, why dude yarinyar nan mayyace wlh rabona da ita tun a paris ok yanzudai kayi hakuri ka saurareta kasani wannan karon koku daidaita. Ya daure fuska dawaye zandaidaita wannan yarinyar da batada natsuwa kainifa natsani mace mai shishshigi dayawa fa ok but meye laifin humaida kawai sonka takeyi plss dude. Ok mubar zancen haka

Abangaren Safeena kuwa gabadaya ita rayuwar tayimata wani iri koda gidansu bawasu mutane bane but tasaba fita koda shoping ne but yanzu kuma ba hali saboda an dauretã da wannan aurenda miji ko kallo baka isheshiba, wai ahakane rąyuwarta zata cigaba wai ahaka źata cigaba da zama da wa innan mutanen masu girman kan tsiya anty nena batada lokaci dama itama aiki take zuwa saimasu kula da aikin gidan wa inda da sungama sunkoma gefensu.


*Godiya gareku fans kucigaba da biyoni yanzu muke shiga labari*
[2/19, 1:55 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵

Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar


editing
(Firdausi mai Nasara)

*_inagodiya gareku fans wa inda kekirana ta waya da kuma masu yimin mãgana ta watsp duk ina godiya agareku Allah yabar kauna*

4⃣
Ahaka rayuwar taketa tafiya, waňda ayau Safeena tasamu kusan sati daya acikin gidan Alhaji mu azzam. Ahankali take fahimtar rayuwar kowa dake cikin gidan, su Al ameen sun saba da ita sosai don duk rashin son hayaniyarta yaran sunshiga ranta. Sai menal wadda har yau gaisuwa kawai kehadasu, wanda baidamu Safeena ba kokadan don batason raini daman, agefen Alhaji kuwa bawai bayason kula matarshi bane aa. Saidai yana ganin tayimai karama dayawa ko lokacinda mahaifinta yamai maganar don bazai iya kinyarda bane, sai don yana ganin girman mutumin

Sageer kuwa rabonshida shigowa cikin falon tun ranar farko, don bayason gasgata zuciyarshi don yana ganin bai daceba amma shikadai yasan irin halinda yake ciki yana azabtuwa, bacci kuwa saidai barawo' saukinshima yafara zuwa office da abin zai mai yawa, yanzu hakama yana zaune acikin office dinshi zuciyarshi na tunzurashi da komawa gida. jiyake idan har baiga wannan yarinyarba yau akwai matsala , yau sati daya rabonda yasata a iđo
Zunbur yamike yadauki key din motarshi. wani gefe na zuciyarshi na tanbayarshi meye kake tunani sageer? yazakayi haka me kakeso ka aikata?amma ina baijin yau zai iya hakura gaskya
Yana isa cikin get din gidan yaga motar Alhaji mu azzam yace aunčle meyadawo yi gida yanzu? Ahaka dai yakarasa ciki, yana shiģa yayi dana sanin dawowarshi gida. Saboda mugun ganinda yayi, Safeena tana sanyeda dogon wandon jeans blue da kuma farar tshirt ajikinta ga gashinta takamashi atsakiyar kanta , tasako jelar fuskarta tasha make up tasa janbaki maroon abinka da farar mace ga hips dinta sunfito sosai ga t shirt dinma ta mugun kamata komai yafito tana fitowa daga kofar sashenta shima Alhaji nafitowa daga nashi gefen wanda hankalin sageer yamugun tashi saboda bayason Alhaji yaganta ahaka, kujimin fa readers mutum da matarshi. dasauri yakarasa cikin falon yatari auncle diň. Sageer mekadawo yi gida by this time ?yana me duba agogon hannunshi. nayi mantuwane nazo indauka kaifa naganka agida?nima mantuwar nayi kuma yanzu dama nakeson kiranka don nasamu urgent call munada comprence meeting a yola so zanbi jirgi karfe shabiyu.yaushe zaku dawo? May be gobe ko jibi duk yanda takama ok Allah yakiyaye, yana gamawa yasakai waje shikuma yafada dakinshi tareda yin ajiyar zuciya mai karfi najin dadin auncle baiganta ahaka ba,
Wayarshice tayi kara yadauka tareda cewa hello auncle yaçemai don Allah kafadama sauran yaran da kuma Safeena nayi tafiya ina sauri ban sallameta ba,
Ita khadija tasani. Ok zànfada mata yafada akasa lance sann yakatse wayar, harya gyara kwanciyarshi kome yatuna yamike da sauri yafito, yanufi gefen safeena wadda ita ko lokacinda yashigo bata ko lurada shiba wucewarta tayi wurin lambu tana danna waýarta tunda ba abokiň hira.

Kõda ya kwankwasa baiji motsiba yakara shiru Ahankali yatura kofar yashiga cikin dakin wani kamshi mai dadi yabugi hancinshi yaduba ko ina tsab tsab amma baiga alamar tana cikiba
Yana fitowa yayi harabar gidan acan gefen lanbu ya hangota zaune tana waya gamai ba fulawoyi ruwa ga masu aiki sunata aikinsu, azuciye yakarasa wurinda take zaune yatsaya zuciyarshi natafasa,
Yace mekikeyi anan? Cikin hasala dasauri tadago kai don ganin waye yake mata íhu haka don tasan bamai gidan bane. Kallonshi takeyi da mamaki don ita tama manta dashi agidan, yakuma cewa dakefa nake magana. mekikeyi anan Ahaka? bakida hankaline kome? Yazaki fito waje da wannan shigar kuma gamasu aiki suna kallonki, meyasa kike wulakanta jikinda yakeda muhimmanci? baki da hanci harda ido tasaki tana kallonshi tareda cewa ikon Allah. Kaikuma waye kai da kakemin ihu haka akai bakasan natsani hayaniya ba, how there you shout at me like this? zuciya takuma ciyoshi yace , i no u don't care har waje ma zaki iya fita Ahakan, wai wayekai ma tukun? ninasan bakai kake aure naba ko mijin da ya auroni bazai zo yanamun ihu har haka ba cikin fushi yace wuce muje ciki, kinajina ki wuce karki bari inkuma mai maitawa duk masu aikinma tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah ganin idon mutane yasa tadauki wayarta tashige tareda zabgamai muguwar harara,
Har tashiga tana me tunanin wannan wane irin mutum ne ko shine megidan saihaka, zanyi maganinshi. Shikuwa yana shiga side dinshi yafada kangado yana fitarda numfashi mai karfi shikadai yasan halinda yake ciki juyi kawai yakeyi agado wannan yarinyar tanaso tamin illah meyasa take wannan shigar mutane naganinta meyasa take bari wanda yakamata da wanda bai kamataba suna ganin tsadadden jikinta?

yana kwance baisan lokaci yayi hakaba saida yaji kiran sallar ázahar yatuna yabar office tun shadaya.
Wai meyasa nadamu da wannan yarinyar meyasa ma namata magana? Karfa tarenani ôh shit ya naushi iska tareda miķewa yafada bathroom yasheko wanka tareda dauro alwala.

Yafito daureda towel menal tafado dakin da gudu bros, saida yadaka mata tsawa bana fadamiki kirika nocking kafin kishigoba ta tsaya taname kallonshi shikuma yana goge jikinshi dawani towel yace kije falo kijirani ínshirya jikinta yayi mugun sanyi sannan tace tom tareda juyawa tana mekara jin feelings sosai a zuciyarta . Agaskiya yakamata Sageer yasancewa tagirma itafa tanajiň da soyayyarshi aka haifeta. tana bala in sonshi har cikin zuciyarta shiyasa ko lokacinda Humaida budurwar shi ke zuwa take jin tatsaneta sosai duk da lokacin bata wuce ten years ba,
Ahankali tafada kan sofa tareda furta i love him somuch har lokacinda Aunty nena ta dawo tasameta afalon batasaniba ta fada tunani saida ta tabata tareda cewa yar gidan Aunty mekike tunani haka inatã magana yau ba lecture ne naganki agida ? Yanzu nadawo Aunty you are welcome tace tank u inasu Al ameen? Basu isoba driver yaje dakko su.
Ok bari inkintsa in fito muyi lunch takarbi jakarta tareda rakata dakinta sannan tafito,
Saida sukazo lunch Anty nena ke fada mata megidan yayi tafiya saida taji wani iri ace mijinda kake aure baida lokacinka. Koda auren bawai yadameta bane amma ko yaya yaka mata yakula da ita itama fa mutum ci tana son kulawa har suka gama Sageer bai fitoba dama tun ranar farkon zuwan Safeena yadaina cin Abinči a dining saidai akaimai side dinshi. Ko yauma menal ce ta kaimai sannan tatsaya adakin yanaci tana gyaramai dakin har yagama takwashe komai shikuma yazari key tareda fita daga gidan direct gidansu Yusuf yawuce dayake dan gidane kai tsaye yashige ciki tareda yin sallama Mamy na zane wato maman Yusuf yakarasa yagaisheta ta amsa cikeda fara a tace nayi fushi sai yau kaga damar zuwa gaisheni? Yace kiyi hakuri mamy abubuwan ne sukayi yawa. tace Allah yataimaka yace Ameen mutumin naciki ? Eh yanzu yàshigo shima ka karasa ciki. yashiga yasamu Yusuf din wanka yazauna jiranshi yana fitowa yace yau ina kashiga naje office dinka baka nan? Yace nadanyi mantuwa ne nakoma gida. Amma nazauna kusan awa daya ina jiranka. Oh sory ina fatan bawata matsala ko yace babu kawai inaso muyi wata magana ne.
[2/19, 2:01 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYAYYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵

Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
Maman Ammar


editing
(Firdausi mainasara)

*_wannan shafin nakune yan grp din feenerh fans kucigaba da posting ina yinku*

5⃣
Har Sageer yadawo gida yana tunanin maganarshi da Yusuf

Meyasa Yusuf yake tunanin zai iya auren Humaida yama zai bashi irin wannan shawarar
Shifa yanzu inhar bazai samu macenda yakesoba tofa ya hakura da auren

Yusuf bazai taba fahimtar halinda yake cikiba yana azabtuwa tundaga raʼnarda yafara dora idonshi akan wannan yarinyar gabadaya zuciyarshi bata fada mai gáskiyà.

Shifa yana bukatar inma bacci yakeyi yasamu wanda zai farkar dashi don yandã yakejin zazzafar soyayyarta dakuma mugun kishinta.

Fitinarda kecikin zuciyarshi bai tunanin akwai mai iyamai maganinta. Sai Allah. Yawatsa ruwa yafi sau goma bayan dawowarshi amma har yanzu bai samu peace of mind ba saida yasanyã kaya yafito falo ko Ällah zaisa ýaganta ko sanyi yaji aransa.


Koda yãfito duk suna falon tareda yara Ammar nakusa da ita yana zuba mata surutû Al ameen kuma yana tareda Anty Nena
Kamshin turarenshi yasa duk suka dago kansu domin sun fahimci waye mai isowar harda ita Safeenar ma cos taji kamshin ajikinshi dazu
Saida gabanta yabuga tsabar kwarjininda yamata saiyau takare mai kallo dakyau yana sanyeda riga amles dakuma tree quter ajikinshi sajen nan yana sheki yana takowa Ahankali irin na isassun maza dasukejin sunkai.

Cikin minti dabai wuce biyu ba takare mai kallo for the first time data taba jin wani namiji yaburgeta arayuwarta,

Yaran suka nufesu dagudu suna mai oyoyo bros Anty Nena tace son dama kana gida? Eh wallahi Aunty nadan hutane,
Ya zauna daidai saitin kujerar datake zaune

Ita kuwa Safeena tunda takalleshi gabanta kemugun faduwa saboda wani irin kallo dayayi mata wanda takasa fahimtar, meyeke nufi

Menal kuwa tasowa tayi daga kujerar da take zaune tadawo kusa dashi tanamai wani irin firirita wanda shi gabadaya hankalinshi na kan Safeena.


Wai ita wannan yarinyar batada kaya sai kananan kaya. duk da shima bawai yanason manayan kayan bane amma yaga alamar wannan abin nata yafara yawa.

Ahankali tadago kanta cikin sa a yajefeta da kallon da shikadai yasan ma anarshi, dasauri ta dauke kanta tareda mikewa gaba daya, tanacema Anty Nena zanshiga ciki indan kwanta Anty Nena tace ok saikin fito Ahankali take tafiya wanda duk ta motsa saika dauka da gayya take kada jikin nata wanda kuma ba haka bane nature ne , Sageer kuwa ai kusan suma yayi, saida yaji wani irin mugun shock acikin jikinshi har tsakiyar kanshi.


Yakai wajen minti biyar baidawo dai dai ba, saida Menal tace mai bros wannan karon baka kaimu shoping ba tunda kazo yaushe zamu fita? Anty nena tace to sarkin yan make up kayan kwalliya ko? duk wa inda dadynki yasiyo miki basu isheki ba saikin wani bashi aiki ko? Cikiņ shagwaba tace Anty please kibari yakaimu. Anty tace ni na isa ince kar yayanki yakąiki shoping gaki nan gashi ai,


Yace zamuje little sis but not today. tace sai yaushe yace tomorrow' ok bros tank u tareda rike hannun shi Ahankali yatashi tareda komawa čikin dakinshi. Yanashiga yafada kan gadoʼnshi ba abinda yake tunani irin surar Safeena da kuma fuskarta yana tuna yanda lips dinta yake kyalli dazu saboda lip glos dinta tashafa saiyaga tafi kyau ma ahakan dabatasa janbaki ba ganin yanda dan bakinta yayi wani smooth Hmmmm yayi doguwar ajiyar zuciya tareda mika mai karfi,

Ahanķali yatashi zaune daya tuna da wani abun saikuma hankalinshi yatashi tunawa dayayi Safeena fa matar Auncle dinshi ce gwara yacirema zuciyarshi Abinda yariga yasan yamai nisa. In banda sharrin zuciya ma tayaya zata kwallafa gamatar aure? Yanaushi iska zuciyarshi nazafi tana tafar fasa' baimasan wane irin tunani zaiyiba kuma bayajin zai iya furtawa kowa wannan lamarin saboda yazama kamar yaci amanar auncle dinshi,

Why why why yafada tareda dafe sashen zuciyarshi tunawa dayayi da irin halaccin da Alhaji Mu azzam yamai arayuwa, tundã yatashi baisan kowa nashiba shiyarikeshi kamar dan uwanshï na jini. dan koda iyayenshi suka rasu baida wani wayon sanin yan uwansu duk da Alhaji na fadamai cewar saboda dukiyarda mahaifinshi yatara yan uwanshi keson ganin bayanshi shiyasa yadankama Amininshi saboda yasan zaikula dashi kobayan ranshi.


Wannan mutumin ne dayamin komai arayuwa shine zuciyata take son matarshi ta aure hawaye masu mugun zafi suka dinga zubowa ta idanunshi. Nafarko yana tsanar ķanshi na biyu rashin iyaye na uku baisan makomar rayuwarshiba wannan shiné tashin hankalinshi don ko ita Safeenar ma tagane wane irin kallo zatayi mishi impact ma yafahimci yarinyar tatsaneshi amma meyasa zuciyarshi zata yimai haka tun yana hawaye har yafara kuka mąi sauti bawanda zai lallashe shi yana cikin wannan halin ne yaji anturo kofar ďakinshi tareda sallama. Sanin muryar mai shigowar yasashi saurin goge hawayen ida nunshi wanda tarigada tagansu .


da sauri takaraso kan gadon tareda cewa meyasameka bros meyasa kake kuka meyafaru dakai? Menal ce kejero mai wa innan tanbayoyin don hankalinta yatashi. bata taba ganin jarimin yayanta ba yana koda kwalla amma yau ace yana kuka meye zaisa bros kuka har haka? tace bros tell me what is wrong? yace noting kaina keciwo dukda bata yardaba haka tamike taje takawomai panadol xtra tace bros gashi kasha kanzai daina ciwo, yakarba taje tabude mini firij diñda yake dakinshi ta dakko goran ruwa tabude mai yasha, tareda cemata tanks little sis tadan matse fuska am not little bros ka kalleni mana wallahi nagirma. Saida tabashi dariya yanda tayi maganar , itama taji dadin yanda yadan saki jikinshi,


Washe gaři, da mugun zazzabi Sageer yatashi saboda kwana yayi da ciwon kai da kuma cikinshi haka yakwana juyi har Asuba dakyar yayi sallah yäkoma yadunkule,

Har kowa yayi break fast bai fitoba saida Menal tamike zata hadamai takaimai Anty Nena tace taje kartayi latti don ita kawai driver kejira su Al ameen na motar. tace ok Anty Nena namikewa wayarta tayi kara Alhaji Mu azzam yakirata cewar yana kiran Sageer wayarshi bata shiga akashe lafiya kuwa tace lafiya kalau Amma bari tagani yace no balokaci tashirya tawuce office nashi akwai wasu documnt da zataba secretery dinšhi sunada baki don bazai samu dawowa a yauba tayi sauri ta zari key din motar ta tareda kwankwasa
Kofar Safeena tafito tace don Allah taduba Sageer takuma hadamai breakfast dinshi zatawuce don bazata dawo yanžuba sai antashi aiki tace ok badamuwa duk da bataso wannan sakon ba.



Ta isa dining tahadamai komai sannan tanûfi hanyar dataga yake fitowa

*bazan taba daina gode miki ba my sis FIRDAUSI MUHAMMED MAI NASARA Allah yakara miki basira yakuma kaimu ranar aurenki*
[2/19, 2:04 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYAYYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵


Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
Maman Ammar


*kuyi hakuri fans da wannan tsaiko danayi na wannan shafin sanadiyyar rashin danayi amma yanzu Alhamdulillah zandora dãga inda natsaya insha Allah.*

*_hafsat nasan kinfi kowa matsuwa dacigaban wannan littafi gashinan kyauta nabaki shafin nakine*_

6⃣
Tana isa cikin dakin ta hangoshi cikin blanket yana rawar sanyi tsabar zafin zazzabin da yashigeshi, da sauri takarasa cikin dakin tareda yin sallama tajanyo center table ta ajiye abincin sannan takarasa tayaye blanket din tareda tanbayar meyasameshi?
bakada lafiya ne? Shikam kamar amafarki yaji muryarta yabude idonshi ahankali don yahasgata ko da gasken ita ce. Yatashi Ahankali tareda yaye bargon gabadaya duk da jikinshi ba karfi amma ganinta acikin dakinshi kuma har täna damuwa da yananyinda taganshi aciki yasa yaji dadi sosai acikin zuciyarsji.
saurin juyamai baya tayi ganin ba riga ajikinshi kuma dagashi sai tree quater shikuma baifasa mamakin shigowaŕta har cikin dakinshiba. bata juyoba tace ga abincinka nan nakawomaka still ba aikin dayakeyi saina kallonta jiyaķe dama da dama yadan rungumeta ajikinshi kozaiji dan saukin abinda yakeji acikin zuciyarshi.

Baimasan lokacinda tafita adakinba yakalli abincinda tace takawo mai yamike yashiga bathroom yawanke bakinshi sannan yafito yazauna yabude abincin tareda kurbar tea dinda tahada mai haka kawai yaji yamai dadi sosai koba komai ita takawomai don haka kobayaso zaici saida yaşhanye tea din tas sannan yamike ya fada bathroom yawatsã ruwa don yaji dadìn jikinshi yäna fitowa bai tsaya ko mai yashafa ba yazira jallabiya yafito don ba abinda yakeso irin yakuma sata a idanunshi don yanaji ajikinshi itace maganin damuwarshi gaba daya.
Safeena kuwa koda takoma dakinta kasa zama tayi kawai ta tsinci kanta da damuwa da halinda ta ganshi aciki. tasamu kanta da fitowa falon tazauna tana kallon kofar dakinshi kawai kamardaga sama taga fitowarshi da tamike tana tanbayarshi yajikinka kaji sauki itama saida tayi dana sanin nuna damuwarta haka.
Amma shi yaji dadi har cikin zuciyarshi tayi saurin komawa tazauna tareda dauke kai.
Yace naji sauki sosai musamman danaga abinda nakeso dasauri takuma kallonshi yayi kamar bashi yayi maganarba tareda samun wuri ta saitinta yazauna. Yana mai kallonta da kuma jindadin yanayinda suke ciki inama zasu dauwama Ahaka dagashi sai ita.
Yana cikin tunanin sukaji sallama cikin minti daya naga fuskarshi ta canja gaba daya daga walwala zuwa bacin rai saboda ganin wadda tashigo falon bakowa bace face Humaida budurwada keson Sageer tun tuni ita kuma Safeena batasan waceceba ganin tanufi wurin Sageer tareda fadin baby na yasa tafahimci bakuwar tashice saikuma taji ranta ya mugun baci komai yasa ? Nikam nace oho mata.
Ta zauna Ahannun kujerarda yake kai tareda rikemai hannu. Oho baby nayi missing dinka sosai wallahi meyasa baka daukar kirana nakiraka yafi akirga amma kaki responding why? Yasaki siririn tsaki tareda fadin she spoil my mood acikin zuciyarshi yakuma kalli kujerarda Safeena take ta bar wurin , nan take yaji kamar yashake Humaidan tsabar jin haushin katsemai jindadin da yake ciki.
Cikin fushi yace me kika zoyi ne agidan mu? Tace nazo ganinka baby. Yace ok kinganni tashi muje inraka ki ko no baby yanzufa nazo why not muje dakinka ko hira natayaka yace no tanks zanyi bacci please muje inraka ki waje.
Baby korata kakeyi? Yace nop kawai ina bukatar space kaina ke ciwo. Oh sory my dear bari intafi. Amma yaushe zakazo gidan mu? Yace zanzo kije kawai inzanzo zankiraki

Please Login or Register in order to submit comment