Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin yin rude na tuwon dare sukayi sallama farfajiyar makeken tsakar gidan nata,wanda aka yiwa gidan wani gyara na musamman aka shafeshi da sumunti yayi mul gwanin sha'awa,fuskarta qunshe da wadatacciyar fara'a ta aje muciyar hannun nata ta miqe
"Wai wai wai,amaryar muhammadu yau a garin namu,lallai yau farar asabar ce" dariya aysha take sosai
"Kai gwaggo,kamar bani zuwa?"
"A'ah to wannan zuwa na yammaci haka?,yaushe rabonki da takan ma" ta fada tana yin gaba suka bita a baya zuwa rumfar dake gaban dakinta wanda ke shimfide da tabarma da alama bata jima da tashi ba akai,lale take musu wanda tana shirin tashi ta debo musu ruwa ayshan ta dakatar da ita,da kanta ta isa bakin randar gwaggon taba debo ruwan cikin kofin silba
"Wannan randa taki gwaggo da tsahon rai take,har yanzu kuma sanyi yake bata fasa ba"
"Ai 'yar amana ce wannan randa ni kaina na shaida...." Bata kai aya ba yara suka fara sallama dauke da kwalaye a kansu
"Wai gahi,kayan indo ne inji wasu mutane a waje a mota" kallonsu aysha take sanda take takowa riqe da kofin sulbar ta aje gaba hanan tana kallon kwalayen,dukkansu na kamfaninsu khalipha ne donga tambarin kamfanin nan rubuce baro baro a jiki,tana tsaye tana kallon ikon Allah sai da aka sauke kwalaye guda goma cif,jakarta ta bude ta dauko dubu daya ta baiwa yaran su raba,suka amshe suna godiya suka cilla suka fice a guje yayin data qarasa saman tabarmar ta zauna tana kallon kwalayen.


Sam batasan da kayan ba har suka zo garin,daga gaya mishi tafiyar kenan zuwa turosun da yayi har yasa aka sayi kaya irin wannan
"Wannan bawan Allah wannan bawan Allah akwai hannun alkhairi,bamu da abinda zamuce saidai ubangiji ya albarkaci aurenku,ya baku zuriyya ta gari,ya yalwata dukiya da arziqi" gwaggo asabe ke fadin haka sanda ta duba kwalayen taga kayan da aka nade da sunanta,dubanta hanan tayi da sauri jin gwaggo ta ambaci aurensu
"Aur...." Da hanzari aysha ta mata alama da ido kan tayi shuru don Allah,hakanan hanan ta hadiye maganar tana duban ayshan cikin mamaki,dama ayshan matar aure ce amma basu taba sani ba?,to meye dalilinta na boyewa?,haka taci gaba da duban ayshan cikin mamaki,wanda ta lura da hakan itama,dariyarta take ta dannewa kawai,don tasan yau za'a sha cakwakiya kam,nan gidan gwaggo sukayi sallar la'asar.


Tana saman abin sallarta taja waya ta soma neman number din khalipha,don tun dazun hankalinta na wajensa,tana son taji yanayin da yake ciki,saboda hanan na wajen da gujewa yawan tsiyar data shirya yi mata saita miqe ta fita daga dakin sanda wayar ta fara ringing.


Har zuwa sannan yana kwance rigingine saman gadon nashi dafe da kanshi,a lokacin ya jiyo qarar wayar saidai sam bashi da kuzarin da zai iya tashi bare ya daukota,haka ga qaraci ringing dinta ta gama,har wajen sau uku tana kira ba amsa,hakan ya sanya a sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta rubuta masa gajeran saqo
_ya jikin naka?,ina fata dai lafiya,Allah ya qara afuwa yasa kaffara ne a gareka_

Sai data tabbatar yaje sannan ta juya don komawa ciki,sai taci karo da hanan dake tsaye harde da hannayenta tana kallonta
"Sannu mrs khalipha" dariya aysha ta sheqe da ita,don tasam cewa maganar nata cin hanan,don ba yadda zata yine yasa tayi shurh,qarasawa tayi ta kama hannun hanan din
"Me kike ci na baka na zuba?,abinda zamu kwana tare zaki ji komai"murmushi hanan tayi donta qagu taji labarin daga bakin ayshan,tana hango bala'in dacewar ayshan da khaliphan ne,ta hangi cewa wata iriyar soyayya ce ke riqe dasu duka su biyun mai tsayawa a rai
"Promise?" Ta tambayeta tana dariya dariya
"Nayi...muje mu qarasa gidan inna yelwa,itace ta haifi abbana"
"Uhmmm" hanan ta fada suna shigewa ciki.


Sanda suka fito da niyyar wucewa saitaga ashe dukka motocin na tsaye suna jiranta,cikin hanzari suka taso,mamaki ya rufeta,yanzu ashe dama wai suna tsaye,saita kasa shuru ganin kamar hakan bai dace ba,sam sai taji wani iri,suma fa mutane ne kamarta,ita din wace da za'a dinga bata wani tsaro da kulawa haka
"Ai da kunyi tafiyarku,idan yaso in zamu koma kwa zo ku maida mu,ai duka inda zanje ba mai nisa bane duk kusa suke da juna"
50

"duk yadda kika ce haka za'ayi madam,amma mu qarasa dake can gida"
"Shikenan" ta fada tana matsawa hanan ta soma shigewa sannan ta mara mata baya.


Tunda suka shigo layin mamaki ya cikata,saita kasa tantance gidan,don ba gidansu take gani ba,wani gida take gani mai dauke da ingarman katanga wadda duk girmanta mulmule take da sumunti da fenti mai kyau da daukar ido,sanda motar ta tsaya sanya kai kawai tayi cikin gidan cikin rashin qwarin gwiwa,don bata da tabbacin gidanne,hakanan bata da tabbacin jama'ar gidan har yau sune mazauna gidan.


Kamar ko yaushe mafi yawancin matan gidan suna qarqashin bishiyar da zamanta ga zame musu kamar al'ada,saidai a wannan karon bishiyar tafi kyau da qawata gidan fiye da lokutan baya,sakamakon siminti da aka yiwa ilahirin fadin gidan,sallamarta ita taja hankalin duk wanda ke zaune a wajen,gaba daya ido yayo kanta yayin da suka mimmiqe tsaye wasu sukayo gaba inda take
"A'ah,lale maraba sannu da zuwa"
"Maraba da matar allaji halifa"
"Sannunku da zuwa indo,indo mutanen birni"irin wadan nan kalaman dake nuna maraba da mutum su suka dinga furta mata,kowacce fuskarta wasai da fara'a,karo na biyu a rayuwarta da taga soyayya makamanciyar wannan.


Gaba daya suka dunguma dakin inna yelwa,wanda a yanzun ya zama babban falo da dakuna guda biyu a cikinsa,an sauya shi bayan gyaran da aka yi masa lokacin bikinsu,gaba daya mamaki ya cikata na waye ya iya irin wannan aikin a dukka gidan duk da kyau da yake dashi.


Tamkar inna yelwa zata goya ayshan haka ta rasa inda zata ajeta,kyakkyawar daddurma mai girma da taushi aka shimfide mata,kana ta umarci biyu daga cikin matan 'ya'yanta suje su dorawa ayshan wani abun
"karki wahalar dasu inna yelwa,mukam a qoshe muke"
"Ke ba irin cimar da kike zato bace" inna yelwar ta fada tana dariya,murmushi aysha tayi
"Allah mun qoshi inna,amma ban sani ba ko zuwa anjima"
"Toh ina zuwa" ta fada tana ficewa don ta bada sautu a samo mata fura da nono mai kyau,saboda ta sani indon mai son fura da nono ce a baya,saidai sum ranar kasuwa idan 'ya'yanta suka kawo haka za'a dama a rabawa kowa fana kallo bata da rabo duk yadda takai ga son furar,saidai ta sude a kofin wasu,sai tayi saurin kauda wannan tunanin daga zuciyarta,sau tari idan ta tuna saita dinga jin babu dadi ita kanta cikin ranta.


"Gaskiya aysha ke 'yar gata ce,kowa sonki yake?"
"Hmmm,hanan kenan" aysha ta fada tana dan qaramin murmushi,haka rayuwa take,a duk sanda kaga wani bawa cikin wata ni'ima saika yiwa kanka sha'awarta kota birgeka,harma wani lokaci ka yiwa kanka sha'awarta ba tare da kasan irin qalubalen daya fuskanta ba kafin yakai ga wannan bigiren.


Suna zaune aka kawo furar a dame an jefa qanqara a ciki ta dauki sanyi,bude faifan dake kai tayi,kallon furar tayi tana tuna wani lokaci can baya,sai taji gaba daya ta fice mata a kai bata bata sha'awa ba,saboda haka ta turawa hanan gabanta
"Bismillah sis kisha" ja hanan tayi gabanta ta soma shan abinta,ta mata dadi sosai saboda sanyi da suger data sha
"Ke bakya sha indo?" Inna yelwa ta tambayeta,murmushi kawai aysha tayi,a dacan baya wani lokaci daya shude,lokacin da take da buqatarta,lokacin da take sha'awa da qulafucinta aka hanata,hakan ya sanya a yanzu ma sam bata sha'awarta,bata baiwa inna yelwa amsa ba murmushi kawai tayi mata,sai jikin inna yelwan yayi sanyi,kwalin da tasa aka shigo mata dashi ta bude ta fidda tsarabar kowa ta lissafawa inna yelwan,fuskarta washe da fara'a take jerowa ayshan addu'a da fatan alkhairi,sai tayi zugudi kawai tana kallon innan,lafuzan da tunda ta budi ido tasan me duniya ke ciki bata taba jin makamancinsa a kanta daga bakinta ba,saidai ta jiyo akasin hakan
"Allah ya baki miji indo dan albarka,mijin da ina jin kaf zuriyata babu yarinyar da zata samu kamarshi,hannun kyayta Allah yayi masa,ki duba yadda duk wanda ke cikin gidan nan sai daya dandani arziqinki indo,ba shakka kedin mai qashin arziqi ce,ki qara masa godiya bisa aikin da yayi mana,ki duba kaf fadin karkarar nan babu gida ya namu dana kakanki salihu" mamakin khaliphan ya kamata,yaushe duka yayi wannan aikin?,cikin shi ko anni ba wanda ya taba nuna mata anyi ko a fuska,ya Allah,wadan nan wanne irin mutane ne masu kyakkyawar zucuya har irin haka da Allah ya hadata dasu?,dame ita kuwa ayshatu zata sakawa rayuwarsu?,khalipha...khalipha sunan data ringa maimaitawa kenan a ranta har zuwa wani lokaci,bayan hanan ta kammala sha suka nufi gidan mero.


Ta samu mai jego lafiya ita da yaronta,nan ta zauna suka kacame da hira,hirar da suka jima basuyi irinta ba,itama kwali guda ne na tsarabarta,itadai dukka mamaki take,waita yaya khalipha yasan kowa yasan kuma siyayyar data dace da kowa?,waye ya gaya mishi?.


Godiya mero ta dinga yi sosai,kaya ne turamen atamfofi da rigunan jariri masu kyau da tsada,hira suka dinga wadda suka jima basuyi irinta ba,sun tuna baya sosai,sun tuna abubuwa kala kala,na dadi da akasin haka,hanan kam tana waje suna hira da saddiq dinta,basu bar gidan meron ba sai qarfe kusan goma na dare,gidan inna yelwa suka koma,a sannan tuni har an saka musu shimfida,qatuwar katifa ce mai kyau da taushi da bargunan rufa.


Aysha na kwance rub da ciki tana danna wayarta yayin da hanan ke sakawa kanta hula suna shirin kwanciya
"Matar khalipha....baki gayamin ya akayi aka haihu a ragaya ba" murmushi tayi kafin ta kashe wayar ta aje,sannan ta dubi hanan sosai
"Muhammad khalipha mijina ne,munyi aure babu jimawa ya tafi qaro karatu nima nayo kust qaro nawa,yanzu haka aurenmu bai cika shekara ba,saidai mun kusa"
"Kai aysha,ashe duk solamu kawai kike,kuma ban taba ji kinyi maganarshi ba tunda muke dake" numfashi ta sauke tana kwanciya rigingine gami da lumshe idanunta kana ta bude
"Munyi aure ne ba tare da dukkanmu muna son junanmu,tausayi shine abu na farko daya jawo qulluwar aurenmu.....saidai bazan boye miki ba...." Aysha ta fada tana sake mirginawa ta koma rub da ciki saidai ta takore jikinta da gwiwar hannunta tana duban hanan
"Ina jin wani abu na daban akan khalipha wanda bansan meye shi ba,ina jin wata shaquwa aduk sanda muke tare,hakanan inajin wata kewa a duk lokacin da yayi nesa dani,ina jin tausayinsa a duk lokacin dana tuna gwagwarmayar rayuwarshi,akwai abubuwa da yawa da nakeji baqi a kanshi wanda bani da amsar meye su..." Murmushi sosai hanan ta saki wanda yafi kama da dariya
"Akwai ayar tambaya akanki aysha...saidai bazan gaya miki ba nima,kamar yadda kika jamin rai akan sanin kina da aure nima sainaja miki,saida safe" ta fada tana juyawa zata kwanta,dariya aysha tayi tana girgiza kai,bata ce da hanan din komai ba ta juya itama ta kwanta
Bata zata ba don har ta fidda rai taji muryar hanan din
"Aysha....koda baki soma son khalipha ba dab kike daki afka,dukkan abinda kike ji dangane da khaliphan ina kyautata zaton soyayya ce da qauna mai zafi" waiwayowa tayi gaba daya tana duban.hanan gabanta na dukan uku uku kamar taga khaliphan,gira hanan ta dage maya fuskarta qunshe da murmushi tana bata tabbacin abinda ta gaya mata
"Qwarai kuwa,shi so yakan iya farawa da tausayi,wani lokaci kuma daga faduwar gaba,tsoro,daduwar bugun zuciya a duk sanda taga abinda takeso din,yawan kallo,yawan shuru da nutsuwa a sanda kuka hada muhalli dashi,saboda haka nake miki albishir.....barka da zuwa duniyar soyayya" ta qarashe tana dariya,kai ayshan ta girgiza tana duban hanan fuskarta qunshe da murmushi
"Ban yarda da wannan sharhin naki ba malamar love" saita maida kanta ta kwantar
"Ki gama qi fadinki tsaf da kauce kaucenki,baki da wata makawa kan zancena,zaki ce kuma na gaya miki nan da wani qanqanin lokaci" itama hanan din ta fada tana gyara rufarta tare da gyara kwanciyarta,shuru aysha tayi tana sauraronta tana fidda boyayyen murmushi,
saidai can qasan ranta tana taraddadin rashin jin khalipha da bata yi ba har a sannan.


Washegari suna idar da sallar asuba ta zari slippers dinta tayi gidan suna koda akwai wani aikin da zasuyi a lokacin tabar hanan tana bacci,tasan yanayin yadda mutan qauye kesa asubanci,haka kuwa tayita cin karo da mata jefi jefi,tana tsayawa suna gaisawa,wanda hakan yana musu dadi sosai.


Sanda ta isa kuwa ana shirin yanka abun suna,ta gaisa da 'yan uwan mero dake rumfarta ta tsallake uwar daka inda meron take tana shiryawa,mero na dariya tace
"Indo baki manta da al'ada ba,na zaci birni tabi jikinki ai ba zaki iya wannan asubancin ba" dariya tayi ta amshi yaron da tuni anyi masa wanka an shiryashi tsaf cikin daya daga cikin rigunan da khalipha ya sako masa,kyau yaron yayi sosai dama kuma kyakkyawa ne,ya debo babarshi xam,sai taji ya bata sha'awa
"Tushiya masomin dawa mero,ta yaya zan manta usulina"
"Wannan gaskiya ne,aike indo kam Allah ya baki,duk yadda akaso ayi da rayuwarki Allah bai nufa ba,gashi da yake ke din 'yar qwarai ce irin halak daular da kika samu bata sanya kin manta da tushenki ba,bakya qyamatar kowa cikin 'yan garinku,kowa sanbarka yake dake" cewar iyalle kishiyar babar mero wadda ke shigowa dakin ta tsinci zancan da sukeyi,murmushi mero tayi kaman yadda yasha itama shi tayi,tana zaunw suna hira da mero harta kammala shiryawa,tayi kyau cikin atamfa abinta,tanajin an shigo da abun sunan za'a soma gyarawa ta ajiye yaron tana cire hijabin jikinta ta rataye
"A'ah ina zaki kuma?" Maro ta tambayi aysha tana dubanta
"Aiki mana"
"Wanne aiki duk ga mutane nan,kiyi zamanki muyi hirarmu karki bata jikinki,inake ina bakin murhu ma" dariya aysha tayi,duk basusan irin uban aikin data tashi ta saba dashi bane,hakanan bata taba samun sararawa ko salamar aiki ba sai bayan data auri khalipha
"Mero kenan,aikin kuma ai da yana kisa da ban kawo iwar haka ba,bata jiki kuma mero idan a kanki ne ba kayana ba har fatata zan iya batawa,idan kin manta halaccinki a gareni ni bazan manta ba,ke kadaice wadda ta tsaya dani a sanda duniya ta juyamin baya,kin manta randa muka fara qawance,ranar da 'yan uwana suka taddani bakin rafi zasumin duka kika qwaceni daga hannunsu?" Dariya mero kawai take tana girgixa kai,ba shakka alheri danqo ne baya faduwa qasa banza,ita ta mance yadda abun ya kasance amma har yau gashi ita indon bata manta ba
"Tunda sai kinyi jeki kiyi ki dawo muyi hirar" aysha na dariya ta fice,ko su sunso hanata amma ta karbe hanjin ta gyarashi fes ta kuma dorashi kan wuta,sai data gama suyar a sannan rana ta dan fito tacewa meron bari taje ta dawo ta duba baquwarta.


Sanda ta koma ta tadda hanan a bararraje ita da inna yelwa suna kwasar hira kamar sun jima da sabawa,har tayi wanka abinta ta kuma karya da lafiyayyen kunun gyada daya sha madara da kuma qosai,idanun inna yelwar a kanta tunda ta shigo take kaffa kaffa da ita,kiran daya daga cikin surukanta ta kira ta hadawa ayshan ruwan wanka
"Jeki abinci inna karima,zan iya hadawa da kaina" ta fada tana zare hijabin jikinta
"Banda abinki indo da kin bari ta hada mikin,inake ina jan ruwa yanzu" dariya ma maganar ta inna yelwa ta bata,bata mantawa akwao sanda take wani azababben zazzabi haka ta tasota gaba kan sai taja ruwan,data gaya mata tana jin jiri ne tace ko zata fada cikin rijiyar sai taja,haka kuwa akayi wanda da qyar tayi guga uku,tana cikin na hudun jiri ya debeta gugan ya koma rijiyar,ita kuma Allah ya kawo mero a dai dai lokacin ita ta riqeta,bata tankawa inna yelwar ba ta daura zani da hijabi ta fice abinta ta debi ruwanta cikin babban dakin girkin da aka yi musu taja ruwa ta sirka ta shiga bandakin da aka yi cikin daya daga cikin dakunan dake falon inna yelwar,wanda ta shaida mata shine nasu da zasu dinga sauka a ciki.


Tana zaune tana karyawa jifa jifa tana duban inna yelwa,wadda ta taqarqare tana faman jansu da hira,ita a yanzu bata yadda ba qaunarta take?,haka aysha kewa kanta wannan tambayar cikin mamaki,data gama tare suka fice da hanan,wannan karon maimakon gidan mero gidan inna kulu suka nufa,shima dai gidan tun daga waje tasan tabbas aikin khalipha ya sauka ta kanshi,sanda ta gansu ita dinma da yake ba baya bace wajen son abun duniya kamar zata goya ayshan,itadai kallon kowa take
"Mamarki kuwa ina zaton yau zata shigo garin" cewar inna kulu,da mamaki take duban innan,tunda suke bata taba sako mata zancan innarta a tsakaninsu ba sai yanzu,bata ce komai ba wanda hakan yadan sanyayar da jikinta saita sauya hirar,awa biyu kawai sukayi mata suka wuce gidan sunan,a can hanan ta sake abinta,ta dinga yiwa mejego da 'yan suna hoto,ita abun qayatar da ita yake,da yake su iyaye da kakanni 'yan haifaffun cikin gari ne,kusan bata da wani qauye da zata nuna tace na kakanninta ne.


Duk hidimar nan da ake hankali da tunanin aysha na kan khalipha,tana shirin tada sallar la'asar taji shigowar saqo,cikin hanzari ta sanya hannu ta dauko wayar tana dubawa

_ina cikin aminci da kulawar ubangiji,na gode qwarai da kulawa_

Haka kawai taji amsar bata gamsheta ba,amma don kada ta takura shi saita haqura ta tada sallarta.


A ranar suka koma makaranta da yammaci lis,wanda motocin daukarta ma su sukayi jiranta,tana jin zuwan umminta garin a sanda suke shirin ficewa daga takai din,saidai ko kusa ko alama bata kwantanta dosarta ba bare taje wajenta.


Koda wani satin ya kewayo taje gida weekend kuma gida taje wajen daddy,tayi sa'ar samunshi a gida kuwa,sun jima suna hira dashi sosai,wanda hakan ya baqanta ran mummy,irin ci gaba da sauyin da take gani tattare da ayshan ya soma tabata,saita tuna asma'unta,wanda kusan rabin wahalarta ta dawo wuyansu,bata tabaji aysha tace ehmmm dazai nuna tana cikin wani hali ba bare takai ga furtawa har duniya ta sani.


🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶

Qarfe biyar ne na yammacin ranar,suna zaune ita da mummyn ta a falon samanta,kayanta ne da suka zo daga lagos a bude suna lissafi ita da mummyn na kudaden kayan da sunan wadanda za'a rarrabawa.


Saman ya hawo yana amsa waya da alama shigowarsa gidan kenan,baiyi ko sallama ba ya ratso falon,suka hada idanu da mummyn,baiko nuna alamun ya santa ba ya samu daya daga cikin kujerun falon yayi zamanshi yana ci gaba da wayarshi,dif asma'u sukayi ita da mummyn ganin ya sanyasu gaba yana waya,sai daya kammala sannan yace
"Barka da yamma" yayi maganar yana latsa wayarshi ba tare daya nuna da mummyn yake ba,hakanan ta amsa saboda tasan da ita din yake,irin gaisuwar da ada idan yazo wajen asma'un yake maya kenan,banbancinta da waccar kawai yana kallonta yake gaidata,a sannan data danyi qorafi sai asma'un tace yanayinshi ne haka,haka mummyn ta qyale maganar ta biyewa son ran asma'un.


Mai aikinsu ya soma qwalawa kira,cikin mintina qalilan sai gata ta shigo,cikin girmamawa ta risina masa ya gaya mata abinda zata kawo mishi,dole mummy ta yiwa asma'u sallama,ganin abun na hamid ba girma ba arziqi.


Sanda mummyn ta fita mai aikin ta shigo ta shirya masa komai sannan ta fice,wata sabuwa kuma ya samo don tuni ya sallami wacar farkar tasa ya gaji da ita,idanunsa nakan kayan da salma ke lissafawa ba tare data ko dubeshi ba,lissafi yake cikin ranshi,so yake kawai ta kulashi suyi wani abu ta yadda zai samu damar cewa ta masa asarar wani abun ya debi lesunan gabanta ga kaiwa budurwarshi.


Tana sane taqi kulashi,don a yanzu ta gaji da hamid ta gaji da aurenshi,kamar ita asma'u tana ganin bai cancanci ta rayu da hamid cikin irin wannan uqubar ba,tana da kyau,tana da gata tana da usuli,ba shakka hamid bai cancanci ci gaba da zama da ita ba.


"Ke...wato saboda wuyanki yayi kauri kina ganin mutane baki iya musu sannu da zuwa ba ko?,kuma saboda rashin tarbiyya a gaban babarki amma bata tsawatar miki kota nuna miki rashin dacewar abinda kika aikata ba" abinda bai sani ba shine,ita kanta asma'un dama hanya take nema,saboda hama ta miqe a fusace cikin daga murya tace dashi
"Dakata hamid,karka sake kiran uwata saboda ita din ba sa'arka bace,sannan rashin tarbiyya aikao za'a tambaya wannan,tunda baka iya zama da matarka ba kaga kuwa daga wajen tsoho aka...." Bata kai aya ba ya wanketa da wani lafiyayyen mari
"Karki sake ki qarasa,wanda kike shirin zagi shi ya bada kudin da kika gani kika maqale min"
"Ni ka mara hamid?,...."
"An marekin ko kina da abinda zakiyi?"kai take kadawa kuka kamar zai qwace mata
"wallahi zakasan ka mareni,ka mari aurenka,yau saika sakeni,saika bani takardata" wata wawiyar dariya ya saki yana jan tsaki,komawa yayi ya zauna saman kujerar daya tashi a kai yana kwance agogon hannunsa mai tsada ya sanya hannunshi cikin abincinsa
"Aikin auru kenan har abada,idan ma kina mafarkin zan sakeki ne to kinyi kuskure,don ni ba shashasha bane,nasan ciwon kudina" daga haka yakai abincinsa baki ba tare daya sake bi ta kanta ba.


Dakinta ta shige cikin kuka ta dauko jakarta da mayafinta ta fito,ko kallonta baiyi ba,itama hakan yayi mata dadi,saidai bata gane manufar sharetan da yayi ba sai data je bude qofa taqi buduwa,sai daga bisani ta gane muqulli ya saka mata,dawowa tayi gabanshi cikin hargagi ta tsaya
"Ka tashi malam ka budemin qofa,don wallahi daga yau na gama aurenka na gaji"
"Ni kuma yanzu na fara aurenki wlh,don ba more komai cikin abinda na kashe miki ba" wani qululun baqinciki ne ya taso ya tokareta,me yake nufi kenan?,yana son yayi mata qwalelen rayuwar da ta shiryawa kanta samu a gaba?,yana nufin fa bazai saketa ba,wanda hakan dai dai yake da cewa haramiyarta rayuwar da takewa kanta hasashe.
51
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶


A hankali yake ratsawa ta cikin layin nasu har zuwa qofar gidan da yake mallakinshi ne,kuma a halin yanzu yake zaune a ciki,yayi kyau sosai cikin qananun kaya wanda ya dira jibgegiyar rigar sanyi a kai,yana saka key yana shirin bude qofar gidan wayarshi tayi qarar shigowar saqo,basu jima da gama waya da anni ba wadda ta tashi zuwa saudiyya don tayi umara,wayar ya zaro daga aljihunsa yana dubawa,murmushi ya saki a hankali yana karanta abinda saqon ya qunsa,a qalla ya dauki wasu kwanaki bai.maida.mata da amsa,yayi kuma hakanne saboda ya auna yadda ta damu dashi,shin abinda zuciyarsa take raya masa haka ne?,wani irin yanayi da bai taba hasashen shiga irinsa ba akanta ya samu kansa,bashi da shakku kuma ko kokwanton cewa wannan ba komai bane soyayya ce,yadda yake ji din ya tabbatar da cewa ba qaramin kamu tayi masa ba,yaushe hakan ta kasance duka bazaice ba,yana tsoron kar yayi zurfi da yawa abun ya zame masa matsala,ya kasa samun goyon baya yadda ya kamata daga gareta.


Sosai saqon yayi masa dadi,don har ya shiga parlour din gidan maimaita karanta saqon yake yana murmushi kafin daga bisani ya samu wajen zama.


Daga bangarenta kuwa tana zaune gefan gadon anni bayan sun dawo daga rakiyarta airphort,wadda ta bar mata muqullin dakin nata a hannunta saboda ta tashi ne ran asabar sanda ayshan ke zuwa gida hutu,kasa aje wayar tayi daga hannunta sai juyata take tana jin wani iri babu dadi a ranta,batasan me yasa a duk sanda ta tura mishi saqo take kasa samun amsar sa ba,batasan dalili ba tana jin babu dadi sosai cikin ranta,ko wani laifi tayi masa?,damuwarta tana ganin ko bata rasa nasaba da qoqarin kyautata matan da yake yasa batason itama tayi masa wani abu da yake ba dai dai ba?,duk dai bata sani ba.


Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,jiki a sanyaye ta miqe ta soma kintsawa

Please Login or Register in order to submit comment