Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bokan yake,saboda aɗan saman wani dutse yayi dakin nashi.kuma mota bazata je ba.

Yana ganin mommyn Husna ya sanya dariya mai sauti yana nuna ta da isgar dake hannunsa.
Zama tayi tana mai hararar bokan,dan afusace tazo gurin nashi,saboda ya karya musu alkawari, ba wani aiki da yayi musu,kawai yayi ta amfana da jikinta ne ya yaudareta.

"Boka meyasa zakayi mana haka?me yasa zaka ci amanata?ashe baka yi mana aikin da kace zakayi ba? Kaci amana ta boka,yanzu haka mijina yana kulle,duk wani laifi daya aikata aboye yanzu ya fito fili,ansan dashi wllh kaci amanata makaryacin banza mugu kawai Allah ya isa tsakaninmu da kai"mommyn Husna ta faɗa cikin ɓacin rai da mugun jin haushin bokan.

"Wata irin hatsabibiyar dariya bokan ya sake sanyawa,kafin ya turɓune fuska,kallon mommyn Husna yayi da jajayen idanunsa yace cikin tsawa"ke la'ananniyar Allah,mushirika mai bin bokaye,ki sani kinyi kuskuren fada min bakaken maganganu,yau zaki yabawa aya zakinta, da kin dauka duk mai bin boka yana karewa lafiya ne?wannan shine karshen rashin bin Allah da duk wasu masu irin tunaninki suke riskar kansu,Ni kaina nasan karshe na bazaiyi kyau ba, dan haka ina fatan akashe mijin naki ma,sannan kema kiyi mutuwar wulaƙanci"ya kai zancensa yana mai fashewa da dariya.
Hawayen bakin cikine suka fara zubowa daga idanun mommyn husna
"Allah ya isana boka,Allah ya tsine maka albarka,mugu mai dulmiyar da mutane marar tsoron Allah,In Sha Allahu tun aduniya zaka gone gurmus shegen mutum, kuma bazanyi mutuwar wulaƙanci ba,saidai ka gani akanka"mommy ta faɗa tana mai mikewa dan barin dakin.saidai taku biyu tayi,taji an fizgota tare da maka ta da ƙasa.
Ihu mommy ta kwalla na azaba,kafin tayi wani yunkuri kuma tuni boka ya haye ruwan cikinta yana ƙoƙarin zare wando.

Kokawa suka fara da mommyn Husna,amma ina saida ya kaima abinda yake so,tana ji tana gani bokan nan yake sex da ita cikin wulaƙanci da mugunta.
Hawaye ne kawai ke zubowa daga idanunta,cikin wannan kuka ta lalubo wannan kwarangwal ɗin kan mutum ɗin dake ajiye gefen gurin zaman boka,bata jira komai ba ta rabka masa a keyarsa.
Wani wawan ihu bokan ya kwalla wanda Saida dajin ya amsa,sannan ya fadi nan gefenta jini na malala daga ƙeyarsa,sai shure Shure yake.

Cikin hanzari da tsoro mommyn Husna ta mike tare da zubawa aguje,tana zuwa ta shige motarta tana kuka wiwi jikinta sai rawa yake.

Tuki take cikin rashin nutsuwa kamar ma bata cikin hayyacinta,tana cikin tukin taga wani ƙaton zakara, wanda girmansa ya kai raƙumi,sannan da ƙaho ɗaya akansa ,ya tunkarota da gudu.
Ihu ta kwalla maimakon addu'a,aikuwa tuni kan motar ya kwace mata, taje ta bugu da wata ƙatuwar bishi,nan motar tayi ta wuntsilawa ta na dukan bishiyoyi.kan kace kwabo motar tayi taga raga, inda mommyn Husna tayi kaca kaca da jini ƙafarta ɗaya ta cire kanta ya fashe ta gefe kamar wanda aka sare shi. Wannan shine karshen mommyn Husna ,ta mutu mutuwa ta wulaƙanci da tozarxi.
(Allah kasa mufi karfin zuciyarmu,ka hane mu aikata shirka ameen).

Wasu masu wucewa ne suka ga hadarin inda sukayi saurin sanar da yan sanda akazo aka tafi da gawar mommyn Husna wanda aka tattara sassan jikinta cikin akwati.

Kan kice me tuni labarin hadarin ya watsu cikin garin.
Ana ta fadi gidan talabijin da kuma lambar motar da aka gano da ƙyar. Aikuwa ahauce Husna ta nufi asibitin da aka kai gawar mommyn ta.
Tana ganin gawar ta shaida mahaifiyarta,nan take ta fadi asume.

Labari ya iskewa su daddy haka suka rankaya asibitin cike da jimami inda suna zuwa suka tarar da an kawo jannat haihuwa.

Kafin su gama cukucukun karbar gawar jannat ta haifi diyarta mace kyakykyawa .


Haka suka dauki gawar suka je suka gudanar da jana'iza aka kaita makwancinta,saidai muce Allah yasa mu dace.
Koda labarin mutuwar ya riski Alhaji musa,kuka yayi tayi kamar karamin yaro yana tuba ga ubangijinsa.Hankalinsa yayi mugun tashi game da mutuwar matar tasa,gashi ko gawarta bai sami gani ba,dan lokacin da aka zo dashi tuni an binne ta, shima saida Daddyn Aslam ya, sanya baki aka barsa' kabarinta kawai ya gani,yaso kwarai akaishi yaga yarsa amma,ina sam yan sandan nan sunki,dan sunce case dinsa babbane kuma suna tsoron ko wani plan din ne suka hada dan inyaje asibitin ya gudu .

Haihuwar jannat itace ta ɗan sanyaya musu zuciya,game da damuwa da alhini da suke ciki, inda suka cika da murna samun baby.

Husna kuwa koda ta farka,kamar zararriya haka ta koma kuka take tana ihun mommyn ta,(to Husna sai muce Allah ya bada hakurin rashi....

Mrs babi ce
[12/31/2022, 8:09 AM] Abk: 105/106
____________Husna kuwa koda ta farka,kamar zararriya haka ta zama,kuka take kamar ranta zai fita tana kiran mommyn ta. Idan ka ganta awannan lokacin,dole ta baka tausayi.
idanunta sunyi luhu luhu,da kyar take iya budesu,mutane sai bata hakuri suke,amma ko sauraraonsu ma batayi bare tasan me suke cewa. Daga karshema danne ta likitoci sukayi tare da yi mata allurar barci,dan bata cikin hayyacinta.

Koda aka shiga kotu kuwa,sam Daddyn Husna bai musa tuhumar da akeyi akansa ba,dan kuwa gaba ɗaya yanzu,ya sare duniyar ma ta fita akansa,kullum cikin kuka yake,gashi yana matukar son ganin yarsa,ko zai ji sanyi cikin ransa,sam baya magana saidai kuka yayi ta istigfari da neman yafiyar Allah.
Lokacin da za'ayi zaman kotun daddyn Aslam da kansa yaje ya taho da husna daga asibiti.dan itama kullum cikin kuka take tana cewa akaita gurin Daddyn ta.
Lokacin da aka shigo da Daddyn nata taga yadda ya koma,yayi baki ya rame sannan idanunsa sun kumbura alamun kuka da rashin barci.
Wani irin tausayin sa ne ya kamata,batasan lokacin da ta sanya kuka ba.shima Daddyn nata yana ganin husnan kukansa ya ƙara tsananta, wanda da dama saida suka ba mutane tausayi.

Kasancewar daddyn Husna bai musanta akan tuhumar da ake masa ba, kuma bai wahalar da Shari'a ba,sannan Daddyn Aslam ya nema masa sassauci akan hukuncin da za'a yanke masa,hakan ya sa alkali ya yankewa Daddyn Husnan hukuncin daurin rai da rai.
kuka sosai Daddyn Husna keyi lokacin da za'a tafi dashi kurkuku,yana rungume da yarsa,ji yake kamar zuciyarsa zata fashe,damuwa, danasani da takaicin irin rayuwa da kuma tarbiyyar dasuka ba Husna yana mai damun zuciyarsa,sam lokacin da suke bata dukkan wata dama da take nema ta yin abinda taso,basuyi tunanin zuwan wnanan rana irin ta yau ba,gashi Dukansu sunyiwa Husna nisa,nisan da bazai basu damar gyara barnar da sukayi abaya ba.
Cikin matsanancin kuka Daddyn Husna ke faɗin"ki yafe min Husna,ki gafarceni Husna,mun cutar da rayuwarki, mun bata miki tarbiyya,ta yadda bakya gane mai kyau da marar kyau,mun ɗoraki akan tafarki marar kyau,yau gashi mommy ki ta tafi ta barmu,nima kuma zanyi miki nisa, nisan da koda munga juna bashi da wani amfani,domin ba abinda zan iya miki,Husna bani da kowa Ni Maraya ne,amma ban riƙe maraicina ba,na sanya kaina cikin rayuwa marar kyau,sannan mahaifiyarki bata da alaƙa mai kyau da danginta, nasan bazasu riƙe mana ke ba,Husna nayi dana sani da Allah wadai da rayuwata,ban zama uba na gari ba Husna ki..kik....
kuka ya hana Alhaji Musa ƙara sa maganar da yake son fadawa husnan.

Itama Husna tana ƙanƙame da mahaifin nata,inda take wani irin Kuka mai tsananin ban tausayi,kai bakace itace husnan nan marar mutunci ba,dan duk rashin imanin ka,saika tausaya mata.kuka kawai take tama kasa magana sai neman shidewa take.

Daddyn Aslam,Daddyn Islam,Aslam,dakuma Aman,gaba ɗayansu saida suka tausaya wa su husna,dama wanan shine ƙarshen maci amana ai.

Cikin kuka Daddyn Husna ya riko hannun Husna zuwa gaban Daddyn Aslam,
"Alhaji nasan na cutar da kai,ban zamo mai saka alkairi da alkairi ba,amma dan Allah ina rokon ka,ka taimakawa rayuwata ka kulamin da Husna,dan nasan zuciyarka ba ba irin tamu bace,kai adali ne mai manta sharrin wani agaresa.
Husna bata da kowa ahalin yanzu sai kai,sai Allah"ya kai zancensa yana mai sunkuyar da kansa hawaye kuwa kamar an bude fanfo.

Ƙwallar data ciwa Daddyn Aslam ido ce ta sami damar zubowa,sakamakon rufe idanunsa da yayi.hannun Husna ha kamo tare da dafa kafadar Daddyn Husna yace"In Sha Allahu Musa zan kula maka da diyarka,kamar yayan cikina,zan zame mata uba kuma zan cike mata gurbin ku data rasa"ya fada cikeda tabbatarwa.

Kara karfin kukansa Daddyn Husna yayi,yana mai faɗin"na gode alhaji,na gode Allah ya biyaka, ka yafe min Alhaji,kaima Alhaji Abubakar Ina neman yafiyarka"

Yan sandan da zasu tafi da Daddyn Husna ne suka fara jan hannunsa mai ankwa dan tafiya.

Ihu Husna ta sanya tana mai bin Daddyn nata da gudu "wayyo daddy karka tafi ka barni,wayyo Allah na daddy ka dawo bani da kowa saikai da mommy ita ta tafi ta barni,kaima zaka tafi ka barni, wayyo Allah na"kalaman da Husna ke faɗi kenan tana bin motar da aka sanya Daddyn ta ciki.
Da kyar Daddyn Aslam ya rike ta yana rarrashinta.
Koda suka dawo gida sosai granny ta fara fadan me ya kawo Husna gidan? Sanar dasu komai daya faru daddy Yayi,amma firr granny tace Husna bazata zauna dasu ba.

Karshe dai da kyar suka shawo kanta ta yarda akan mommyn Islam zata tafi da ita can gidan ta.


Anyi sunan jannat inda aka sanyawa yarinyar khadeeja,suna kiranta da Nana.

Bayan wani lokaci,komai ya lafa,rayuwa ta dai -dai ta,inda Aslam da Islam suka buɗe sabon babin soyayya mai cikeda aminci,tausayawa tare da jinkan juna .
Aslam ya kammala ginin tamfatsetsen gidan sa,wanda faɗin kyau da tsaruwar da yayi ba'a magana,yau kwanansu uku da tarewa agidan,suna zaune afalo,inda Aslam Yayi matashin kai da cinyar Islam,ya kafeta idanunsa masu cikedazallar soyayyarta, dan hure masa ido tayi tare da yin fari da idonta tace "Ni kaga malam karka gano muni na da wanann kallon"ta faɗa cikin salon jan hankali.

Murmushi Aslam Yayi tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin. Yace
"Akullum Islam ina ƙara godewa Allah daya mallaka min ke matsayin matata,kedin alheri nace kuma sanyin idanuna ,ina godiya ga Allah Islam "ya fada sounding so happy.

Ahankali Islam ta saki ƙayataccen murmushi mai sanya zuciya zurmawa cikin kogin soyayya. Kafin ta ɗan marairaice fuska tace
"Saidai har yanzu na kasa baka dawwamammen farin ciki,ta hanyar haifa maka yara kamar yadda kake fata da buri,abin yana matukar damuna zaujee"Islam ta faɗa idanunta na cikowa da hawaye.yau kimanin shekara guda kenan da aurensu, amma har lokacin Islam bata sami ciki ba,abun yana matukar damunta,dan tasan yadda Aslam ke matukar son yara.

Dan haɗe rai Aslam yayi tare da sanya hannu yana share mata hawayen daya gangaro da idanunta kafin yace "zaki fara ko? Kinsan bana son irin wannan maganar,ai bake kika hana kanki samun cikin ba,Allah ne bai ga damar bamu ba,ko kina son yiwa Ubangiji butulcine ?ya fada yana mai kallon fuskarta .
Cikin sauri Islam ta girgiza kanta,alamun a'a.
"To ki daina faɗin wannan maganar kinji?ki godewa Allah daya yiki matsayin musulma,kuma ya baki rai da lafiya,idan muna da rabo zamu sami haihuwa,maza ki share hawayen nan,bana don ganinsu suna sanyani damuwa kinji?"ya fada yana mai shafa kumatunta.

Jinjina kai tayi tare da sanya bayan hannunta ta share hawayen dayayi saura a idonta.
Sannan ta kalli Aslam ashagwabe tace "to Ni ka goyani ka kaini lambu gurin janbu" ta faɗa tana wani langabe kai irin na shagwaɓaɓɓun yaran nan.

Murmushi Aslam yayi tare da mikewa tsaye yana mai jin kaunar Islam ta ko wacce kafa dake jikinsa,yana matukar son yadda take shagwaba idan suna tare,hakan yana sanya shi nishadi sosai.

"Angama yan matana maza tashi ki hau,In kai ki duk inda kike bukata"ya fada yana mai ɗan ranƙwafawa yadda zataji daɗin hawa bayan nashi.

Cikeda farin ciki da doki Islam ta mike tare da hayewa bayan nashi,shikuwa ya nufi garden da ita.

Sosai garden din nasu ya kawatu matuka,dole idan kana gurin kajika cikin nishadi da farin ciki.
Jikin bishiyar ayaba ya ajiye ta,dan yasan can zasu taradda janbun.
Kallonta yayi lokacin data sauka daga bayan nashi,tana sanye da wando iya gwuiwar ta,sai wata yar karamar riga mai hannun best,kayan sun kamata sosai, sunyi mata kyau.
Dan ƙanƙantar da ido Aslam yayi kafin yace "madam,wai menene sirrin ne?
Kallonsa tayi cikin rashin fahimta tana shafa bayan janbu daya sauko da gudu sakamakon hangota da yayi.
"Sirrin me fa"ta faɗa da son jin karin bayani.
"Cike da salonsa na son sanyata Farin ciki ya sanya hannunya ya kamo hips ɗin ta yace "waɗan nan abubuwan nawa fa sai ƙara bajewa suke,sannna wannan kayan laushin suma sun kara girma da kyau, ya fada yana shafo breast dinta da suka cika rigar atsatstsaye.ke gaba dayan ki ma fa kin canza kin zama yar lukuta meye sirrin ne?

Turo baki Islam tayi,kafin tace "kaine sirrin mana,kulawarka ce akansu ta kai yadda suke bukata,amma kwana biyun nan girman nasu karuwa yake sosai dayawan kayana sun min kaɗan "ta faɗa tana dan shagwabe fuska.
Shiru yayi yana kare mata kallo,anya kuwa Islam ba ciki gareta ba?
Kamo hannunta yayi yace Islam when kikaga period dinki?
Ɗan shiru tayi tana nazari,idan bata manta ba,kimanin wata biyu kenan bata gani ba.
"I think tun last two months"ta faɗa tana kallonsa.

Cikin tsantsar farin ciki taga ya sureta yana juyi da ita .
"Alhamdullah Islam I think you are pregnant" ya fada cikin farin ciki.

Itama Islam ɗan zaro ido tayi,sam ta manta cewar idan mace bataga period dinta ba,zai iya zama ta samu ciki ne.
Ba wani bata lokaci kuwa suka shirya sai asibiti.
Binciken Farko ya nuna Islam na dauke. Da ciki har na tsawon wata biyu.
Masu karatu, zo kuga murna wajen su Aslam.
Faɗin irin murnar da sukayi ma bata lokaci ne. Haka suka dawo gida suka fara rainon cikinsu.

Cike da so da kulawa suke rainon cikin,inda gaba ɗaya aslam ya maida hankalinsa akan Islam,kome zatayi shike mata,baya barinta tana motsi mai ƙarfi,
Gashi cikin nata saiya fara sanyata laulayi mai zafi,komai taci saita mayar dashi,kullum zaka ganta kwance jikin Aslam,tana zuba tabara son ranta.
Shikuwa da tace wai zaice me kike bukata?me za'ayi miki?kingaji da kwanciyar ne?
Haka dai ire -iren waɗan nan tambayoyin zaiyi ta jero mata,har saitace ba komai.
Hannunsa kuwa kullum yana cikin rigar Islam yana shafa cikinta.

Kaf dangi ba wanda baisan Islam na da ciki ba, dan waya suka rinkayi suna sanar da yan uwa.
Mommy Islam da suka kirata ma dariya tayi tayi musu ganin yadda suke ta bata labarin cikin.
Lokacin da grannyn tazo ganin Islam,dole ta sanyata zama agidan,dan ganin yadda Islam ɗin ke shan wahala,kamar ba ita ba,ta zama shiru shiru ta ɗan rame,saidai tayi fari sosai ta kara kyau.

Saida cikin ya kai wata biyar sannan ta daina laulayin, sai ci kamar gara,koda yaushe cikin ci take.

Yauma kamar kullum,suna zaune afalo,yayinda Islam tayi matashi da cinyar Aslam, tan cin yalo,shikuma Yana nasa aikin wato na shafa cikinta.
Kamar wacce aka mintsina ta tashi zunbur .
Da sauri Aslam ya riko hannunta yana faɗin"lafiya pretty ?menene?ya fada adan ruɗe yana kallon jikinta.
Kallonsa tayi tare da ɗan zaro ido kamar wacce take cikin mamaki ko al'ajabi tace "ji nayi kamar ana Min zillo acikina"ta faɗa tana ɗan riƙe mararta saitin dataji motsin.
"Da gaske pretty?Aslam ya fada yana mai ɗora hannunsa inda ta ɗora nata.
Aikuwa cikin Sa'a shima yaji cikin yayi motsi har sau biyu.
Da sauri ya ɗago kai suka haɗa ido da Islam,kawai sai suka sanya dariya cikin farin ciki.
Kunne Aslam ya ƙara acikin nata yana mai faɗin"hi baby ya kike?mom and dad luv you so much"ya fada kamar wanda yake magana da mai wayo.

Dariya Islam tayi tana mai shafa kan Aslam din.
Grannyn ce ta fito daga ɗakinta tana faɗin"wai nikam dariyar me kuke yi ne ?tun ɗazu nake jiyo babatun dariyarku"
Ta faɗa tana ƙarasowa cikin falon,.
Sai lokacin ta hango hannun Aslam akan cikin islam.
Tafa hannu ta fara kamar wacce taga wani abun mamaki kafin tace "yanzu kai kuwa wannan yaron bazaka bar wannan masifar taka ta shafa cikin matarka ba?shikenan baka da aiki sai kayi ta lalubewa yarinya ciki?ke kuma ki zauna kina masa dariya ke adole miji yana son cikin ki ko? To wllh kiyi ahankali in ba haka ba,wannan da tsabar jarabarsa saiki kara samun wani cikin"granny ta faɗa tana harararsu.
Dariya suka sanya tare da tafawa .Aslam yace "yau nake ganin ikon Allah,wai mutum da abunsa dan ya taba kuma ake sa masa ido?nifa wllh kobaki zo ba zan iya kula da matata, haka kawai kinzo kina ta faman samana ido "ya fada yana ci gaba da shafa cikin Islam cikeda tsokanar granny .

"Nazo,kuma bazan koma ba har sai Islama ta haihu sannan mutafi gida wanka,In yaso ka zauna ka cinye kanka"cewar granny.
Wani kallon me kikace Aslam Yayi mata kafin yace "tab wllh ba wanda zai kaimin mata wani wanka,duk ruwan gidan nan bai isheta wanka ba sai an kaita gida?a'a wllh garama kiyi tafiyarki tun yanzu,dan ba inda zata"Aslam ya fada cikin yanayi na jinki nake.

"Ja'iri marar kunya wato so kake abar maka ita agidan,salon shekara na zagayowa ta sake haihuwa ko? To baka isaba kayi tsururu ruwan randa"ta faɗa tana riƙe ƙugu.
Dariya sosai taba Aslam ganin yadda ta dage da gaske tana faɗa.
Islam ma dariya take kasa-ƙasa.

"Au dariyama kake min ko?to ka tsaya in ƙaraso gurin da kake wllh saimun raba raini dakai,dama jikina yayi min nauyi "grannyn ta faɗa tana nufo Aslam.
Da sauri ya tashi tare da sanya dariya yana mata kwalo.ita kuwa ta dage saiya tsaya sun raba raini.
Haka yayi ta zagaye falon yana wahalar da yar tsohuwa,data gaji saita zauna tana faɗin "zaka zo ka sameni ne ja'iri.tana zama agurin ta kama barci.
Cikin dariya Aslam yazo ya ɗauke Islam suka gudu daki suka bar granny anan.

Cikin Islam na cika wata tara da yan kwanaki ta haihu,cikin nasara ba tare da ta sha bakar wahala ba,ta haifi yaranta biyu,mace dana miji.

Masu karatu kuzo kuga murna gurin su Aslam,dashi ake karbar Barka,ko kuma sai yan Barka sunzo ake karbo yaran agurinsa.
Ranar suna aka sanya musu sunan mommyn Aslam da Daddyn Islam.
Wato A'isha da Abubakar inda ake ce musu haneef da haneefa.
Yaran sun taso cikin kulawa da soyayya inda gaba daya haneef ya dauko halin mahaifinsa na son girma da manyance.
Haneefa kuwa halin Islam gareta saidai ita akwai iyayi da tsiwa.
Kowa na son yaran gasu da shiga rai.

Rayuwar Husna agidansu Islam rayuwace mai tsafta abin so,domin mommyn Islam na bata kulawa sosai .
Yanzu ta nutsu ta daina duk wata mummunar harka,kullum cikin shigar kamala zaka ganta da hijabinta.
Ta shiga islamiyya kullum bata aiki sai karatu da istigfari ,cikin haka ta sami wani malamin islamiyyar tasu zata aureshi.
Matansa biyu da yara goma.amma ta amince zata aureshi.


Bayan shekara biyar zuwa shida Islam na hango cikin haɗe dakinsu.
Sanye,take da doguwar riga abaya tayi rolling da babban dan kwali hannunta riƙe da rigar likitoci wato lapcot,yayin da Aslam ke gefenta yana tajewa haneefa gashin kanta.
Haneef kuwa yana yiwa arfat yar kimanin shekara daya da watanni wasa.sai dariya take.

Cikin yanayi na shagwaba Islam tace"zaujee nikam na kammala shiryawa,ku nake jira,wllh idan kuna shiryawa bata lokaci ne daku"Islam ta faɗa tana ɗan turo baki
Kallonta Aslam yayi yana mai faɗin "sorry Madam prettyna yanzu zamu kammala"
Ya fada yana mai haɗe hannayensa guri daya.
Haneefa ma kallon ammin nasu tayi tare da dan marairaicewa tace "preetyn daddy kefa ƙawata ce amma bazaki bari agama min kwalliyar gashina ba?ta faɗa tana wani kashe ido ɗaya.

Turo baki Islam tayi kafin tace "to ai kune zaku batamin lokaci bayan kunsan yau muke passing out "ta faɗa tana karyar da kai tare da kallon haneef.
Shima ita yake kallo ganin yadda take kamar zatayi kuka,

Cikin yanayin faɗa irin na yara yace "
Preetyn daddy kawai mu tafi mu barsu,nima na gaji"ya fada yana kamo hannun Islam.

Kuka haneefa ta sanya tana faɗin "daddy wai zasu tafi su barmu"
Cikin sigar rarrashi yake shafa kan yarinyar yace "barsu uwata,idan suka tafi muma bazamu je dasu park ba"ya fada yana kallon haneef dan yasan shine mayen zuwa park.
Shiru yaron yayi yana kallon Daddyn nashi.kafin yace"daddy zamu jiraku fa amma kuyi sauri, kaga preetyn ka zatayi kuka"ya fada yana kallon fuskar Islam,wacce ta wani kwabe fuska kamar zatayi kukan gasken.

Murmushi Aslam yayi tare mikewa yace to bari na rarrasheta "ya fada yana kallon Islam tare da kashe mata ido yace "nasan me kike so fa,amma kinga nan akwai yara muje dakina in rarrasheki acan"
Ya fada yana kashe mata ido.

Zaro ido tayi tare da kallon haneef daya kuresu da ido,tace "nidai ba ruwana wllh kana kallon dan jaridar ka yadda ya kasa ya tsare yana daukar rahoto"ta faɗa cikin dariya.
Shima dariyar yayi yana mai shafa kan yaron yace "haneef dan jaridana"
"Daddy me yasa bazaka rarrashi preetyn ka anan ba sai kunje daki?haneef ya fada yana kallon Daddyn nashi da son jin karin bayani.

Kallon juna Islam da Aslam sukayi kafin Islam ta toshe bakinta tana dariya tace "saika bashi amsa"

"Yarona ,zan bata sweet ne aɗakin nawa dan tayi shiru kartayi kuka kaji?"ya fada yana shafa kan yaron.
Haneefa ce ta sauko riƙe da wata yar mitsitsiyar jaka sai faman sabata ake tana saukowa tace "daddy Nima inason ka bani sweet din"

Cikin dariya Islam tace "a'a saidai ya siyo miki taki daban ,wannan sweet ɗin ta pretty ce kawai"
Dariya Aslam ya sanya yana mai daukar arfat karamar diyar tasu.
"Kuzo kuyi hoto maza"ya fada yana ɗora haneefa akan cinyarsa.
Islam ta zauna kefensa ta dauki haneef, suka fara hotuna.cike da farin ciki da annashuwa.

ALHAMDULILLAH.
Wannan shine karshen littafin rainon dawa,kurakuren dake cikin sa Allah ya yafe mana,gyaran kuma Allah ya bamu ikon yin amfani dashi.

Sannan ina mai baku hakuri masoyana masu bibiyar wannan littafin na rainon dawa,sakamakon tsaikon da akayi ta samu,wanda ba dabi'ar rubutuna bane,idan na fara littafi bana tsayawa saina kammala.amma an sami tangarda sosai akan wannan littafin.ina neman afuwarku, hakan bazata sake faruwa ba in Sha Allah.
Ina kaunarku Aduk inda kuke,domin kune ni,saida ku nake jin dadin rubutuna.
Allah ya sadamu agidan aljannar firdausi.

Ina sonku bil hakki har cikin zuciyata.
Sai mun haɗe cikin sabon littafina mai suna
SIRRIN ƁOYE.

Labarin littafin na daban ne salonsa daban yake karku sake baku labari
Ga kaɗan daga cikinsa.


Ɗanɗano daga littafina na gaba wanda zai zo muku nan gaba In Sha Allah.

Yarinyar ce wacce akiyasin shekarunta bazasu gaza sha biyar zuwa sha shida ba.
Zaune take kan tarin wata ƙasa da aka zubeta gaban wani ginin laka,da alama kasar ginin gidan da take kusa dashi ake.
Kuka take sosai kamar ranta zai fita,
Ahankali ta kara rungume jaririn dake hannunta,aƙokarinta na kareshi daga sanyin da ake zabgawa cikin tsakiyar daren,wanda ba komai jikin yaron sai wani yalolon zani data lullubeshi dashi.

Banda haushin karnuka ba abinda kake jiyowa.
Cikin tsoro take waige -waigen gefen ta sakamakon jin ƙarar takun mutane da tayi.
Wannan kenan.



"Waikai al'ameen baka da wani aiki sai na sex? An faɗa maka niɗin jakar ka ce ,ina laifi sau biyu fa kake kusantata Aduk watan duniya,ina ce ko sati biyu bakayi da kusantar tawa ba, shine yanzu ka lallabo ina barci na ka tasheni? To wllh ba abinda zanyi maka"

"Please baby ki taimaka min mana,idan banzo gurinki ba ina kike so naje?kefa matata ce dan Allah ki taimaka min ,wllh ina cikin wani hali "

"Ina ruwana kaje duk inda zaka je ma bai shafe ni ba, taimako daya zanyi maka shine ,kaje ka jika kanwa da lemon tsami kasha.....


Wai ya batun yaron nan da na ce ku sanar da iyayensa su turo million goma?
Idan basu turo ba lallai kusanar dasu inda zasu dauki gawarsa.

"An gama ranki ya dade,su kuma wadannan yaran da muka dauko jiya ga sun damemu da kuka
Ya kike ganin za'ayi musu?

"Ku sanya musu kwaya mai ƙarfi cikin ruwa ku basu,ta yadda hankalinsu zai gushe.


Hmmmm masu karatu me kuka fahimta da wannan littafin?

Kudai ku biyoni sannu kan hankali ɗan jin warwarar wannan ƙulle ƙullen.

Mrs babi ce
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment