Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin ihun ɓacin rai Husna ta sanya tana mikewa tsaye.
"Kan kazakazar uban nan,honey kana jin abinda yarinyar nan ke fadamin?zagina fa tayi?wllh yau saina ci uwar uwarta agidan nan,shegiya dangin tsiya wllh na tsani wannan yarinyar"cewar husna kenan cikin daga murya tana ƙoƙarin bin Islam ɗakinta.
Da sauri Aslam ya riko hannunta,sosai ransa ya sosu da zagin da tayiwa Islam,koba komai ai tasan Islam yar uwarsa ce,kuma idan ta zagi dangin Islam,tamkar nashi ta zaga.ransa ya ɓaci sosai,amma kash!! bazai iya nuna mata ɓacin ransa afili ba.
Dan haka cikin kwantar da murya da rarrashi yace"haba baby Dan me zaki kula wannan yarinyar?bata da hankali fa ai kinfi karfin yin faɗa da ita,kiyi hakuri kodan ni, kinga ƙanwata ce bata da kunya nima bana kula ta bare ke"ya fada yana janyota jikinsa bayan ya zauna.

"Wllh honey bazan yarda wannan Shegiyar mai kama da aljanu tana min rashin kunya ba,aini ba sa'arta bace"ta faɗa cikin huci tana hura hanci.
"Sorry baby ki kwantar da hankalin ki,yanzu kije ki shirya zanje nayi mata magana,zan ja mata kunne akan karta ƙara miki rashin kunya, idan kuma tayi min ba dai-dai ba jikinta ya fada mata"Aslam ya fada yana ɗan haɗe ransa dan ta yarda da gaske hukunci zaiyiwa Islam.

Shashashar kuwa cikin farin ciki tace wllh jeka kayi mata duk hukuncin daya dace na rashin kunyar da tayi mana shegiya mai dogon hanci kamar biro" Husna ta fada tana mikewa tsaye,ɓatar -ɓatar,rigija rigija ta nufi ɗakinta tana faɗin"karfa ka dade kuma idan ka shiga,sannan ban amince koda kallon da zaisa taji daɗi kayi mata ba"ta faɗa tana kallonta dai -dai lokacin da taje kofar ɗakinta.
Ɗan haɗe fuska yayi kafin yace "Allah ya kiyaye waccan yarinyar zan wani tsaya yiwa kallon da zataji daɗi?wannan ai saike ginbiyar mata "ya kai ƙarshen maganar yana sakar mata ƙayataccen murmushi.
Wani fari tayi cikin jin daɗi kafin tace "yawwa honey na,kayi sauri ina jiranka"ta faɗa tana shigewa cikin dakin.

Bin ƙofar Tata Aslam Yayi da kallo,haka kawai ya tsinci kansa da jin wani irin haushinta cikin ransa,tsaki yayi tare da nufar dakin Islam.
Yana shiga falon yayi arba da ledar kazar daya siyo jiya ,har lokacin tana nan ayashe agurin da Islam ta wurgar da ita, gadai falon da alamun an gyara,amma ledar ko tabata ma ba'ayi ba. Kallon yabi falon dashi, A'isha ce ita kadai zaune tana shan yoghout dinta.
"Oyoyo yaya Aslam"ta faɗa cikin dariya tana dirowa daga kan kujerar tayi gurinsa tare da rungumeshi.
Murmushi yayi yana shafa kan yarinyar,yana sonta sosai dan kusan komai nata irin na Islam ne, hatta yanayin murmushinta saidai kawai Islam tafiya kyau sosai.
"Oyoyo Easha, kin tashi lafiya?"

"Lafiya kalau yaya,ina matar taka?ance aurenka akeyi "ta faɗa tana kallon fuskarsa.
"Murmushi yayi tare da cewa"kina son ganin ta ne?"

Da sauri tace "eh yaya ina son ganinta,yanzu ta zama antyna itama"ta faɗa cikin murna.
"Murmushi yayi yace "to ina anty Islam take?
"Tana cikin daki tana wanka"ta bashi amsa tana kurbar Yoghout dinta.

Shiru yayi tare da kallon ƙofar uwar dakan islam kafin yace"to ki zauna anan,bari na dubota,inna dawo sai muje kiga dayar antyn naki ko?"ya fada yana shafa kanta.

Dariya tayi cikin murna tace"to yaya ina jiranka,ka dawo yanzu fa!"
Jinjina kai Aslam Yayi tare da tashi ya shige dakin Islam.
Wani daddaɗan ƙamshine ya ziyarci hancinsa,wanda saida ya sanya shi lumshe ido,ahankali ya buɗe idon nashi yana bin dakin da kallo.ko ina agyare fess, ba kowa cikin dakin,sai ƙarar ruwa da yaji daga toilet.dan haka zama yayi abakin gadonta tare da jin wani irin sanyi da nutsuwa na ratsa sassan jikinsa.

Islam kuwa tana kammala wankan ta ta daura wani dan guntun towel,Wanda da kaɗan ya wuce mazaunan ta ta fito.
Fuskar nan tayi fayau, sai sheƙi take,sam ba alamun wasa akan fuskarta,dan fuskar Tata ahade take.
Domin har zuwa lokacin tana jin haushin Aslam da matarsa cikin ranta,sannan tana jin wani irin kishi na yadda ta gansu afalon dazu.Hakan saiya haddasa mata damuwa sosai ta yadda kwata-kwata ta kasa walwala.
Shikuwa Aslam kallo yabita dashi lokacin data fito,tun daga zara-zaran yatsun ƙafarta ya fara kallonta,har saida ya dire idannunsa akan santala -santalan cinyoyinta masu tsananin kyau da ɗaukar hankali,sai sheƙi suke,ga Dan damshin ruwan dake jikinsu,hakan ya kara musu wani yanayi na sanya mutum cikin shaukin kallonsu, wata ajiyar zuciya Mai haɗe da shashsheƙa Aslam ya sauke,kafin ya ɗago idanunsa,wanda suka fara sauya kala daga fari zuwa ja,ya sauke su akan tudun na fulaninta, wanda take ƙoƙarin cire towel din Dan sanya inner wear ,ai tuni Aslam yaji yawunsa ya tsinke,nan da nan yaji tsikar jikinsa na zubawa,lumshe ido yayi tare da huro iska mai sauti daga bakinsa.
Sai lokacin Islam tayi saurin ɗago kanta tare da saurin maida towel din data fara warwarewa.
Idanunta ne ya sauka akan Aslam,Wanda ya buɗe idonsa dake cike bukatuwarta yana ɗora su akan fuskarta.

Islam kuwa kara haɗe fuska tayi sosai kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa,duk da cewar taji daɗin ganin nasa sosai,dan idanunta cike suke da son kallon kyakykyawar fuskarsa,saidai sosai take jin haushinsa.

"Malam Meya kawoka dakina ?ta faɗa cikin ɗaure fuska tana zabga masa harara.
Lumshe ido Aslam ya karayi,dan sosai yake jin sa cikin kasala,sannan jin muryarta ya ƙara saukar masa da wata kasalar.
"Laifine dan miji yazo dakin matarsa?
Ya maida mata amsa.

Harara ta ƙara balla masa kafin tace "can dai kaje gurin waccan mai kama da giwar,itace matar ka,ba niba"ta karasa tana murguda dan karamin bakinta dake sheƙi.
Ahankali Aslam ya turo harshen sa tare da lasar lips ɗinsa da suka bushe yanzu-yanzu.sannan ya gyara zamansa tare da kara kanƙantar da idanunsa yace"ok kin bar mata Ni kenan ko?
Ya faɗa cikin wani salo na jan hankali.
Da sauri Islam ta kawar da kanta daga kallon cikin kwayar idanunsa,dan wani irin zuummmm take ji ajikinta idan tana kallon nasa.kafin tace "oho maka kai ka sani,nidai ka tashi ka ficemin daga daki,dan bana buƙatar ganin ka agabana,kaje gurin wacce kake so da ƙaunar, wacce take da muhimmanci agareka,kuma kake shakkar ta baka son ɓacin ranta,dan ina da buƙatar kasancewa Ni kadai "ta faɗa cikin zafin zuciya da ɓacin rai.
Wanda kana jin yadda kalaman ke fitowa bakinta kasan cike take da ɓacin rai.
Kallonta kawai Aslam keyi,dan duk yadda take motsa bakinta,ji yake kamar ya kama lips dinta ya cinye koya huta da yadda zuciyarsa ke tsananin bukatar shansu.
Cikin yanayi na kokarin kwantar mata da hankali yace
"Islam me yasa kike faɗin irin wannan maganar agareni ne?ko kin manta Ni mijinki ne?kuma ina da damar da zan zo inda kike akoda yaushe. Tun jiya nake fama da tunaniki, da son zuwa inda kike ,shin ke bakya son ganina ne?"ya fada yana ɗan karkatar da kansa cikin kalar tausayi.

Wani haushine ya ƙara kama Islam,wai tun jiya yake son zuwa inda take,lallai Aslam ya Raina mata hankali wllh.afusace ta juyo tana watsa masa wani kallon ka raina min hankali.tace
"Ai nasan tun jiya kake son ganina dama,shiyasa ka kasa zuwa inda nake ka aikomin wannan jakar matar taka marar kamun kai,saboda ga mayunwaciyar kaza shine ka bata ta kawomin,kai baka da lokacin zuwa inda nake da kanka,wllh duk ranar da tsautsayi yasanya matarka ta sake zuwa cikin dakin nan,saina sauya mata kamanni,kasani kuma idan nace zanyi to sainayi"tana kaiwa nan ta zauna gaban madubi ta fara shafa manta.
Tunda ta fara magana Aslam yake kallonta,tabbas yasan bai kyauta mata ba,domin kamata yayi ya hadasu duka ajiyan yayi musu nasiha,sannan ya rarrashi Islam,amma sam baiyi hakan ba,saidai ba yadda zaiyi,ba laifinsa bane shima.baisan abinda ke damunsa ba,Aduk lokacin da Husna ta shigo gabansa,mantawa yake da komai.

Ahankali ya tashi ya nufi inda Islam ke zaune.kan lokar madubin ya hau ya zauna tare da kafeta da lumsassun idanunsa, ita kuwa sosai ta daure fuskar ta tare lakuto mai ta fara shafawa ajikinta cikin nutsuwa.
Saida ya dau lokaci yana kallonta kafin ya kamo hannun da take shafa man ya rike cikin nashi.
Kallon -kallo suka fara yiwa juna kafin ya fara magana cikin kwantar da murya"am sorry islam !!wllh bani da nufin bata miki ko cutar dake,abinda ya faru jiya ma is an incident ,Amma wllh kinji ma rantse miki dake na kwana cikin raina,Islam duk abinda nakeyi bana mantawa dake,kina cikin zuciyata,saidai i don't now what wrong with me,Ina kasa aiwatar da abubuwan da suka dace Aduk lokacin da Husna ke tare dani,Islam kiyi hakuri dani"ya kai zancen sa yana mai kissing hannun Islam.

Hmmmm!!! Wato a takaice dai so yake ya sanar da ita yadda yake tsananin kaunar Husna,shine yake faɗa mata asaye ko?idan yana tare da husna yakan manta da komai dake kansa?
Cikin zafin nama Islam ta warce hannunta tare da mikewa tsaye.cikin hucin ɓacin rai take cewa"shikenan,ka koma inda take,kaje kayi ta mantawa da nauyin dake kanka, idan yaso ma ka cinyeta tsabar so,nida baka so kuma ka kasheni,amma daga yau karka ƙara koƙarin faɗamin yadda kake sonta bai shafe ni ba, inka so ma daga yau karka ƙara tunawa da wata Islam,dama nasan ba sona kake ba ai,basai ka fadamin hakan zan tuna ba"Islam ta kai zancenta hawaye na zubowa daga idanunta,tsabar bakin ciki da ɓacin rai.
Juya bayanta tayi tana mai ci gaba da kukanta marar sauti,wanda tayi iya kokarinta wajen hanashi zuwa,amma ina !!saida ya kwace mata.

Da ƙarfi Aslam ya runtse idanunsa, zuciyar sa zafi take masa sosai,shifa bada wata manufa ya fada mata hakan ba,ya fada matane dan ta fahimci ba laifinsa bane,zuciyarsa ke sashi ya aikata hakan,kuma bada son ranshi ba.amma Islam tayiwa maganarsa wata irin fahimta.
Saukowa yayi daga kan madubin ya zagayo gabanta kamar zaiyi kuka yace "Please Islam try to understand me mana,ba abinda nake nufi kenan ba,kuma waye yace miki bana sonki?kefa yar uwata ce,wllh Islam yadda na damu dake azuciyata bazai misaltu ba.dan Allah ki fahimceni"ya fada yana riko hannunta.
"Ni ka sanar min hannu,kaje can gurin waccan giwar da kake so ba ruwana da kai nima"Islam ta faɗa cikin kuka da Muryar shagwaba tana ƙoƙarin kwace hannunta.
Ganin yadda take ƙoƙarin kwace hannun nata yasanya Aslam janyota ya mannata da ƙirjinsa.

Gaba ɗaya atare suka sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi,yayin da Islam taci gaba da rera kukanta cikin kasa-ƙasa da sauti.
Shi kuwa Aslam Yana rungume da ita tsam ajikinsa kamar wani zai kwace masa ita.har cikin ransa yake jin sautin kukanta,yayin da yake jin tamkar ana disa masa dalma idan hawayen nata ya zubo.

Husna kuwa tana can kwance akan gado tana jiran miji ya dawo ta kara tara masa gajiya,sai kace wata harija,wai amarya ce ahakan.
Shiru -shiru bai dawo ba,da tana ta dariyar lallai Aslam Yana can yana cin uban marar kunyar can,waya sani ma ko dukanta yake?kai gaskiya aikin boka fa yayi, ƙarshe ne,aikuwa zata fadawa mommynta su koma dan ayi maganin waccan Shegiyar marar kunyar.
Saidai har ta kira mommynta suka gama maganar su ,amma Aslam bai dawo ba,sai kuma ta shiga wani tunanin,karfa take tana nan shikuma yaje ya kusanci yarinyar can aiki ya lalace?kan uban can,ai da mugun hanzari ta mike har tana neman faduwa,da gudu-gudu ta nufo dakin Islam.
Tana zuwa falon ta tarar da Aisha zaune tana wasanta.
"Laaaaa anty yanzun nan yaya yace zai kaini gurin ki idan ya fito daga ɗakin anty"A'isha ta faɗa cikin murna tana nufar Husna.
Husna kuwa cikin jin haushi da tsanar yarinyar ta tunkudeta can gefe tana mai cewa"shegiya gayyar tsiya karki taɓani dan ubanki,niba antyn ki bace,ina Aslam din yake?"ta faɗa cikin tsawa tana zarewa A'isha ido.tare da ɗora mata kafa a cikinta.

Tsoron Husna ne ya kama Aisha sosai ta sanya kuka mai sauti tana faɗin"wayyo anty kizo kigani tana zaremin ido,zata dakeni cikina anty"yarinyar ta faɗa jikinta sai rawa yake tana kwance aƙasan kafar husna.

Da sauri su Islam suka rabu da jikin juna ,jin ƙarar da A'isha keyi,alamun naiman taimako.
Har rige-rige suke wajen fitowa dan ganin abinda ya sami yarinyar.

Zaro ido sosai Islam tayi lokacin da idanunta suka sauka akan ƙafar Husna dake kan cikin A'isha.....


Hmmmmm,masu karatu muje zuwa.

Na gode sosai da addu'oin alkairi da samun sauki da kuke tayi min,wanda suka kirani da wanda sukayi min online,da wanda sukayi azuciyarsu.
Allah ya bar zumunci,ya kuma kara mana lafiya.

Duk masu juna biyu Allah ya saukesu lafiya.

Anty mammy ce
Mrs babi.
[11/20/2022, 11:20 AM] Abk: 81/82
___________Zaro ido sosai Islam tayi,lokacin da idanunta suka sauka kan ƙafar Husna dake kan ruwan cikin A'isha.
Wani irin numfashi Islam take saukewa mai tsananin zafi da suka,gaba ɗaya jikinta ya kama rawa nan da nan idanunta suka kada sukayi jaaa tamkar wacce aka watsawa barkono acikinsu.
A'isha kuwa tana ganin Islam ta kara sautin kukanta tana mika mata hannu "wayyo antyna kizo ki daukeni zata dakeni ƙafarta nauyi zata fasamin ciki"abinda yarinyar ta faɗa kenan cikin kuka tana riƙe da ƙafar Husna.
Aslam cike da mamakin rashin hankalin Husna yake kallonta,yadda ta riƙe ƙugu tana girgiza ko ajikinta kamar ba dan mutum ta ɗorawa ƙafa ba. Cikin dakiya yace "Husna meye hakan kikeyi,?yarinya ce fa karama ,kike taka mata ciki baki tunanin wani abu ya sameta?" Aslam ya fada yana mai kallon husnan.kafin Husna tayi wani yunƙuri kawai sukaji Islam ta kwalla wani kara cikin mugun ɓacin rai ta nufi Husna gadan gadan.ba wata-wata tana zuwa ta sanya hannunta tare da angije Husna da mugun ƙarfi,ji kake rigijib,Husna ta fadi kasa, ƙafarta ta bugu da jikin ƙofar dakin.
Kukun kura Islam tayi tare da afkawa Husna.
Dukan ta take ta ko ina tana zabga mata lafiyayyun maruka da naushi kamar wata yar caskale.
Gaba ɗaya tunaninta ya gushe,ba abinda idanunta ke haskowa sai kafar Husna akan ruwan cikin A'isha.
Ƙafar ta Husna islam ta cafko ta baya tare da lankwasawa da mugun ƙarfi.
Ihu Husna ta kwalla cike da azaba tana kiran "wayyo Allah Aslam kazo ka taimakeni,zata kasheni,wayyo kafata wayyo bakina na shiga uku,wllh ba mutum bace wannan zata kasheni wayyo mommyna"abinda Giwa Husna ke faɗa kenan tana kokarin ture Islam daga kanta, amma inaaa!! Islam ta zage sai gibgarta take kamar ta sami jaka.
Banda naushin bakin Husna da bata lafiyayyun maruka ba abinda Islam keyi.

Ganin da Aslam yayi ana shirin yin kisan kai ya sanya shi zaunar da A'isha akan kujera,wacce ya dagata lokacin da Islam ta angije Husna tare da rungumeta yana rarrashi.
Da sauri ya nufi Islam wacce ta shaƙewa Husna wuya tana dukan bakinta.
Husna sai kakari take tana shura kafa,dan ko kare kanta ta kasayi, domin ba karamin duka take sha agurin Islam ba.
Da sauri Aslam ya ɗago Islam daga kan Husna yana mai faɗin"Islam barta haka mana zaki kasheta fa "
Tureshi Islam keyi tana ƙoƙarin komawa kan husna,wacce tayi ragwab akwance tana tari,dan tama kasa mikewa bare ta gudu.
"Ka kyaleni,wllh yau saina ci uwar azzalumar matar nan,haka kawai take ƙoƙarin kashemin Aisha,me tayi mata?wllh saina illata ta"Islam ta faɗa tana kaiwa Husna kafa.
Da sauri Aslam ya janye ta yayi ɗakinta da ita.yana zuwa ya turata ciki tare da kulle ƙofar ,dan yaga da gaske Islam kamar zararriya haka ta koma,kuma idan ya barta ba karamin illata Husna zatayi ba.
A'isha na zaune jikin ta sai rawa yake tana kuka,Aslam yazo ya mika mata makullin dakin Husna yace"sorry eeshan mommy,daina kuka kinji?bari na kai anty asibiti na dawo,idan kinga mun fita saiki budewa anty kofa "Aslam ya fada cikin yanayi na rarrashi tare da tausayin yarinyar.
Karba A'isha tayi tare da cewa"yaya Ni gurin mommyna zani,ka kaini gurin mommy"ta faɗa atsorace tana kallon inda Husna ke kwance.
Kafin yayi magana suka jiyo Islam tana buga kofar kamar zata karya tana faɗin"ka budemin kofar nan kona ballata,wllh bazan yarda ba idan wani abu ya sami ƙanwata, A'isha zoki budemin kofar nan kinji"Islam ta faɗa cikin daga murya tana buga ƙofar.
Tsoro sosai ya kama A'isha sai rawar jiki take tana kuka tare da kallon Aslam.
"Karki budeta yanzu kinji eeshan mommy?ki Bari saina fitar da anty saiki bude kofar.
"Yaya tsoro nake ji,dan Allah ka kaini gurin mommy"yarinyar ta faɗa cikin kuka.
"To kiyi shiru bari naje na dawo "ya fada yana mai ɗago Husna dake kwance sharab tana kuka ta kasa tashi.
"Wllh bazan yarda ba saina ɗauki mataki akan wannan yarinyar,kana kallo tayi min dukan Kawo wuka kamar ta sami jaka,wllh saina fadawa daddy na ya dauki mataki,wannan ba ita kadai ke wannan dukan ba ,harda aljanu "Husna ta fada lokacin da Aslam ya taimaka mata ta mike tsaye.
Saidai fa tana mikewar ta kwalla ƙara tana faɗin"wayyo kafata na shiga uku ta karya min ƙafa "ta faɗa data neman zubewa a ƙasa.
Da kyar dai Aslam ya fitar da ita daga dakin zuwa nata dakin,dan ya fahimci fa Islam tayi mata targade ne akafar.
Hanan ce tazo kawo musu abinci ta tarar da wannan hatsaniya,inda bayan ta ajiye kulolin abincin sai ta shiga ɗakin Islam,nan ta tarar da A'isha tana ta kici-kicin bude Islam tana kuka.
Da sauri ta karasa gareta tana tambayar ta meke faruwa?
Nan Aishan tace" anty hanan ki buɗe anty,Ni bazan iya ba"ta faɗa tana mika mata makullin dakin.
Karba hanan tayi tare da buɗe kofar.
Tana budewa Islam dake bakin kofa ta fito.
Da hanzari ta janyo A'isha wacce ta ƙara tsorata ganin fitowar Islam,atunanin ta zata daketa ne tunda taki budeta"anty dan Allah kiyi hakuri yaya ne yace karba buɗe sai sun fita,dan Allah karki dakeni"A'isha ta faɗa gwanin tausayi,jikinta sai rawa yake.
Rungume yarinyar Islam tayi tsam ajikinta tana jin wani hawaye mai zafi na tausayin yarinyar yana zubo mata.cikin kwantar da murya tace "kiyi shiru Aishana,ba dukan ki zanyi ba kinji?ki daina kuka ƙanwata"Islam ta faɗa tana zama tare da kara rungume A'isha.
Zama hanan tayi kusa da Islam tace "yar uwa meke faruwa ne ?"ta faɗa tana dafa kafadar Islam.
Ajiyar zuciya Islam tayi tare da labartawa hanan komai.
Sosai hanan tayi mamakin haukar Husna,yanzu wannan yar yarinyar zata takawa ruwan ciki?
Sosai tayi ta rarrashin Islam saida taga hankalinta ya ɗan kwanta sannan ta bar part din.
Tana zuwa kuwa ta sanar dasu mommy abinda ke faruwa abangaren su Islam.
Aikuwa cike da ɓacin rai granny ta fara ɓaɓatu da masifa.
"Wllh bazan yarda da wannan zalunci ba,ashe haka yarinyar nan take?har nawa Aishan take dazata taka mata ciki?wato so take ta kashe ta ko? Wllh bazan amince ba zuwa zanyi inji dalilin dukan , wando ma zan saka koda zata kaimu da dambatuwa da yarinya ehe " granny ta faɗa tana nufar kofar fita daga falon.mommy da hanan suka rufa mata baya.
Mommy na fadin "kiyi hakuri granny abi komai ahankali"dan
Ita dai mommy bataso suje bangaren nasu yanzu da safen nan ,amma tana gudun abin da zai biyo baya.dan haka dole tabi bayan grannyn.
"Saboda ba yarki aka yiwa dukan Kawo wuka ba ko?muguwar mata,dama na jima da fahimtar ki ai sam ke baki da imani to wllh ki kiyayeni,dan kema ba tsoronki nake ji ba"granny ta faɗa cikin masifa tana hararar mommy.
"Allah ya huci zuciyarki granny"shine kawai abinda mommyn ta faɗa tana bin grannyn da tayi gaba abinta.
"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bayar abiyaki?muguwa "granny ta fada tana tura ƙofar falon nasu Aslam.

Aslam kuwa yana zaune riƙe da hannun Husna dake kwance akan gado,fir taki yarda suje asibiti dan tace ta yaya daga kawota gidan aure jiya-jiya kuma yau a ganta asibiti da raunuka?
Ita wllh ba inda zata je.
Shikuma yana rarrashinta akan suje kodan ciwon dake jikinta ga ƙafa nan har ta aune.
Ita kuwa sai wani kuka take tana juya kai cikin kuka.
Kai tsaye granny ta shigo babban falon tana kiran "ina kuke?gaba ɗaya ku fito naji dalilin dukan da akayiwa A'isha?
Granny ta faɗa cikin daga murya.
Islam ce ta fito riƙe da hannun Aisha wacce ta sha kuka sai ajiyar zuciya take,dan ta tsorata sosai.
Da sauri granny ta riko hannun yarinyar tana duba jikinta cike da tausayi tana faɗin"Allah sarki yar malaikar Allah,yanzu idan ba rashin imani na wannan yarinyar ba ,meye abin duka ajikin wannan yarinyar?harda su taka ruwan ciki? Salon taje ta fasa mata kindini.(wai tana nufin kidney) saida hanan tayi murmushi ita da mommy.
"Ke kuma Islam kika tsaya kina kallonta zata kashe miki ƙanwa dan asara baki tattaka mata ruwan cikin ba ita"granny ta faɗa tana hararar Islam.
Shiru Islam tayi dan zuciyarta zafi take mata sosai ,ganin Aishan taci gaba da kuka.
Aslam ne ya fito da sauri, yana tunanin ya akayi granny tasami labarin abinda ya faru?cikin yanayi na nuna ba abinda ke faruwa yace "granny, keda wa kike ta ɓaɓatu da safen nan?mommy meke faruwa naganku gaba ɗaya?ya fada yana kallon mommy.

"Kaji ja'irin yaro ko?wai tambaya ma yake meke faruwa irin baka san abinda waccan matar taka ta aikata ba ko?
Granny ta fada tana buga masa harara.

"To granny me akayi?dan Allah karki zo ki tada min hankalin gida da sassafen nan,mu ba abinda ke damun mu"ya fada cikin haɗe fuska.
Aikuwa nan granny ta hau fada kamar zata aro baki,mommy dai sai hakuri take bata.
Har cikin dakin Husna ta shiga tayi mata kashedin dukan A'isha nan gaba, abinda ya sanyaya mata zuciya ma ganin husnan da tayi kwance alamun dai Islam ta dauki mataki kenan.
Husna kuwa sai wani yatsina take tana hararar granny da juya ido.
Haka granny ta fito tana ta masifa ta fice da A'isha ahannunta.

Mommy ce tayi musu nasiha sosai akan zaman lafiya,fir Husna taki fadin cewa Islam ce tayi mata duka harda su targade,tace faduwa tayi atoilet.
Gani take wannan ai abin kunya ne ace wannan yar yarinyar ce tayi mata dukan tsiya,amma wllh bata daki banza ba,zata rama .
Wannan ma shigar sauri tayi mata bata shirya ba shiyasa.
Bata san cewa su mommy sun fita sanin wacece Islam ba ,dan kuwa sun san aikin tane wannan.
Sosai hanan tayi dariya tana mamakin asaranci irin na Husna ,wai Islam ce tayi mata wannan dukan haka.

Haka dai Aslam ya samo mace mai gyara ta gyarawa Husna kafar ta,ƙatuwar banza haka tayi ta ihu gaban mommy,lokacin da ake gyara mata targaden.

Yau kimanin wata guda kenan da daura auren Husna da Aslam,abubuwa sun faru da dama wasu masu dadi wasu akasin hakan,cikin marasa dadin kuwa harda kasa kusantar Islam da Aslam yakeyi,Dan yanzu duk yadda ya kai da son kusantar ta to Sam asalamiyyar sa bata tashi,saita kwanta luf,abin yana matukar damunsa,tunda ba haka ke faruwa dashi ba idan yana dakin Husna,kalau yake mu'amalantar ta.
Amma idan Islam ce,saidai yayi iyakar yinsa,amma bazai iya komai ba.

Tun abin baya damun Islam harya fara damunta sosai,gani take kamar da gangan yake jagwalgwala mata jiki ya barta.
Kullum gani take rainin hankalin Aslam Kara yawa yake,dan ko ranar kwananta saidai ya saci jiki cikin dare ya shigo dakin nata,kuma ba biyan bukata.

Haka Husna zata fito falo tayi ta falli idan taga Islam,tayi ta mika tana jikinta ciwo jiya Aslam ya wahalar da ita.
Shikuwa yayi ta basarwa Dan baya son Islam ta ji ba dadi.
Ahankali munanan halayen Husna suka bayyana gaba ɗaya ga yan gidan,har dashi kansa uban gayyar,wato Aslam.
Sam bata iya komai ba,hatta dakin ta saidai shi ya gyara mata,kaya kuwa inda ta cire nan take jefarwa,ga rashin kunya,ko kaɗan bata girmama mommy da granny,sai taga dama take zuwa ma su gaisa,shima atsatstsaye.
Gaba ɗaya ta fice daga zuciyar ahalin gidan,ba wanda ke son ta ahalin yanzu sai Aslam.
Wanda shima son na dole ne,sosai yake jin tsanar ta cikin ƙasa zuciyarsa,amma baya iya nuna mata koda akan fuskar sane.

Islam sun kammala makarantar su ta secondary cikin nasara,inda tafi ko wane dalibi kaykykyawan sakamako,gaba ɗaya A ta samu.saidai muce Allah ya bada sa'ar zuwa wata makarantar.

Yau ta kasance ranar juma'a, Islam na zaune afalonta yayin da janbu ke tsalle-tsallen sa akan kujera.gaba ɗaya damuwa ta hanata sakat,kullum tunanin halin da suke ciki ita da Aslam take,ta kasa gane menene abinda ke damunsu, to kodai basu da lafiya ne?kai amma idan da hakane ai itama Husna bazai iya kusantar ta ba,amma ba wata alama ta baya kusantar husnan"kodai nice bani da lafiya?"
Islam ta faɗa afili cikin damuwa.
Ahankali Aslam Wanda tun ɗazu ya buɗe kofar Tata ya tsura mata ido amma bata san da zuwan shiba ma,tsabar nisan da tayi cikin tunani.
Shigowa yayi cikin dakin ya zauna kusa da ita.
Juyowa tayi da ɗan sauri ta kalleshi,dan bata ji zuwansa ba kwata -kwata.
Kallon juna sukayi na dan lokaci kafin Islam ta kawar da kanta gefe guda tare da turo baki tace"ya hakane wai? Saikayi ta zuwa kana min labe kayi ta tsoratani "ta faɗa tana ɗan murguda baki.
Murmushi yayi tare da rungumeta ta gefe yace
"Matsoraciya kawai,da kin ɗauka Husna ce tazo zaneki kome?ya fada cike da tsokana yana ɗan murmushi.

Da sauri Islam ta ɗago daga jikinsa tana mai

Please Login or Register in order to submit comment