Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tare da kama hannun mommyn ta tarike cikin nata, murmushi takeyi,amma kana gani kasan na karfin hali ne,to ta yaya ma zata iya kwantar da hankalin ta?ta yaya zata kai zuciyar ta nesa?sam koda tayi ƙoƙarin yin hakan,bazata iya ba,amma zatayi duk maiyi ta takura zuciyarta wajen kawar da kanta akan duk abinda Aslam zaiyi.dan haka cikin murmushi take cewa"na gode mommy,kuma in Sha Allahu zanyi amfani da duk abinda kika faɗa min"ta faɗa hakan cike da kwarin gwuiwa.
Murmushi mommy tayi tace "da kyau ƴata, Allah yayi miki albarka ,ya kare ki da dukkan nin sharrin abin ƙi"cewar mommy cike da jin daɗi.

"Ameen mommyna"
Islam ta fada.
Nan Islam ta fara nunawa mommy part din nasu,albarka ta sanya musu kafin suka koma can part din mommy sukaci gaba da hira.

Kasancewar Aslam gudu yayi ahanyarsa ta zuwa gidansu husna,dan ji yayi kamar ana azalzalar zuciyarsa dan yaje ga husnan.hakan yasa bai wani jima ba ya isa.
Yana zuwa dama tuni an sanar da mai gadi zuwan nashi,dan haka kai tsaye ya wangale masa ƙofar get ɗin ya shiga.
Husna najin ƙarar motar tayi wani uban tsalle tana ƙara duba kanta cikin madubi.
Tana sanye cikin wata matsatstsiyar doguwar riga,Wacce ta kama jikinta sosai,dagyar take nunfashi,ga uwar zugudar ta nan tayi shirim acikin rigar.
Cike da ɗoki ta ce "mommy yazo wllh kinji ƙarar motar sa can "ta faɗa cikin tsantsar farin ciki tana kallon mommyn ta dake zaune bakin gado,hannun ta riƙe da wata yar kwallaba da wani kalar ruwa blue aciki.

"Ke dalla ki kama kanki mana,ko so kike ya gane dama kin ƙagu yazo gareki ne?maza ungo wannan turaren ki shafa agoshinki da tafin hannun ki"cewar mommyn Husna tana mika mata kwalbar.
Karba Husna tayi cikin rawar jiki ta buɗe ta tsiyaya ta goga akan goshinta cikin sauri,dan Allah-Allah take taje gareshi.
"Mommy bazaki gane bane wllh,ina cikin farin ciki ne,dan ina ƙaunar Aslam sosai araina"ta faɗa tana mike mata kwalbar,bayan ta gama shafawa.
Wayar ta ce ta fara ƙara alamun ana kira.da sauri ta zari wayar tana murmushi.
"Mommy kingani harya kira "ta faɗa tana dagawa .
"Barka da isowa jarumina"
Ta fada tana wani fari da ido kamar tsohuwar karuwa.
Acan bangaren kuma Aslam ji yayi kamar ya suma dan daɗin jin muryarta,cikin zaƙuwa yace "kiyi hanzarin fitowa,dan nayi tozali da kyakykyawar fuskar nan taki ko naji daɗi cikin raina"
Wani shegen daɗi ne ya mamaye zuciyar Husna cikeda zumuɗi itama tace "gani nan zuwa gareka autan maza"tana faɗin haka ta ajiye wayar tareda rungume mommyn ta tana tsalle"wllh mommy Yayi mugun kamuwa,kinji kalaman da yake faɗa min kuwa?kai gaskiya mommy ki ƙarawa boka kudi"Husna ta fada tana barin dakin cikin sauri ta nufi ɗakin baki, dan ta bada umarnin yana zuwa a kaishi can.an gyara dakin sosai sai ƙamshi yake,ga kayan makulashe da aka tanada tun kafin yazo,an jerasu kan center table.
Murmushi mommyn Husna tayi,aduniya ba abinda yake so irin taga Husna na farin ciki.
Dan haka zata iya yin komai dan farin cikin tilon yar Tata.
Da sallama Husna ta shiga ɗakin saukar bakin,Tana wani tafiya tana girgiza jikinta,wanda yake aƙame kamar wani icce,ba inda yake motsawa kamar jikin maza.
Idonta akan Aslam tana sakar masa murmushi.
Kasaƙe !!Aslam yayi yana kallonta,domin tayi matukar yi masa kyau a idanunsa,gani yake kamar wanda aka sake ƙerata, ga wani shu'umin ƙamshi daya shaƙa daga gareta,wanda azahiri idan mutum yaji wanna ƙamshin tsaf zaiyi amai,amma shi da yake asirce yake,ji yayi baitaba jin ƙamshi mai daɗi irin na wannan turaren dake jikinta ba.
Lumshe ido yayi tare da budewa yana zuba mata wani finannen kallo.
Cikin rangwada ta ƙaraso kusa dashi sosai ta zauna.fari tayi masa da ido tana faɗin"Barka da isowa babban bakona" murmushi Aslam Yayi tare da gyara zama yana kallon Husna ,ji yake kamar ya maidata cikinsa.
"Barka dai moyiyata,abar alfaharina,kinga yadda kika haske dakin nan kuwa gaskiya wannan kwalliyar tayimin kyau sosai ,dole na biya kudin "ya fada yana mai kallonta da lumsassun idanunsa.

Murmushi tayi kafin tace "kaine ka ƙarawa dakin haske bani ba,domin kayi kyau matuka,kuma ba saika biya wannan kwalliyar ba,domin anyi tane dan kai "
Ajiyar zuciya Aslam ya sauke kafin yace"gaskiya ina komawa gida ,zan sanar da daddy azo nemamin auren ki,dan bazan iya kai nan da sati guda,ba tare da na mallakeki matsayin matata ba"Aslam ya fada yana kurbar lemun da Husna ta bashi,wanda yasha magungunan surkulle kala kala.

Daɗi da Farin ciki kamar ya kashe Husna,tace "Indai ta bangare nane bani da matsala ,domin nafi kowa son kasancewa dakai,kullum hakan shine burina,dana koma zan sanar da Daddy na Nima"ta faɗa tana wani kashe ido kamar tsohuwar mayya.
Sun jima suna shira,dan har saida akayi magrib,sannan Aslam ya tafi, saidai duk yadda Husna taso Aslam Yayi romancing ɗinta Sam yaki,yace sai sunyi aure saidai kissing din hannunta da yayi kawai. Amma shima da gyar ya iya barin gidan dan ji yayi zai iya kwana tare da Husna yana kallonta.

Lokacin daya koma gida,su mommyn Islam sun tafi.
Daga mommynsa sai Islam da granny da kuma hanan zaune afalo,kowa da abinda yake yi.
Islam na zaune tana tunanin har yanzu Aslam yana can tare da wannan ƙatuwar bijimar, hankalinsa kwance,ita ya barta da ciwon rai da tarin damuwa.

Da sallama Aslam ya shigo cikin Falon cike da nishaɗi,akan fuskarsa,saidai kuma deep down Yana jin wani irin ɓacin rai da ciwo cikin zuciyar sa,wanda baisan na menene ba,kuma bazai iya furta wa ko nuna ɓacin ran nashi ba.
Zama yayi akan kujera,sam bai kula da Islam ba,dan tana kan kujera ne can gefe guda ta kwanta kamar mai barci,yayin da granny ke zaune tana kallon Film ɗin da ake haska a arewa 24,

"Aslam harka dawo?"
cewar mommy cikin kulawa.

"Wllh mommy na dawo,da gyar ma ta bari na taho,gaskiya mommy da zaran daddy ya dawo ki sanar dashi aje ayi magana iyayen Husna,dan so nake ayi komai da wuri,wllh bakiji yadda nake jin yarinyar cikin raina ba"Aslam ya fada cike da shaukin soyayya yana ɗora kansa akafadun mommy.

Murmushi mommy tayi,tana mai shafa kan Aslam ,tare d cewa"ai Ni kaina bana son adauki lokaci,tun da dai duk gida ne,anjima nan zanyiwa Daddyn ku magana,In yaso konan da jibi ne,sai aje agama magana ko ya kikace granny?"mommy ta faɗa tana kallon granny.
Jinjina kai granny tayi tana cewa.
"Ja'irin yaro ba daga ganin yarinya kabi ka rikice,to Gara kam ayi komai cikin lokaci agama,Dan Nima yarinyar ta kwanta a raina sosai,tana da hankali sannan bata da rawar kai zamansu zasuyi lafiya da islam"

Ajiyar zuciya Aslam Yayi Yana mai kallon granny yace"granny nifa banki ace yau ma akawo min ita matsayin matata ba,dan wllh bakiji yadda nake jin so da ƙaunar ta cikin zuciyataba"
Aslam ya fada yana wani lumshe ido cike da farin ciki.

"To wllh dai kayi adalci tsakanin matan ka,karka auri wannan kace zaka wulaƙanta min jika,wllh ba yadda zanyi ba,kasan halina sarai,bana tsoron mu ba hamata iska da mutum ehe"granny ta faɗa tana tafa hannu da hararar Aslam.

Shikuwa murmushi Yayi Yana mai faɗin" ina Ni ,ina wannan dambe naki granny? Kwantar da hankalinki,ai kowa da matsayinsa,ita Islam ƙanwata ce, jinina, wannan kuma masoyiyata ce abar sona, dan haka kowa zai zauna a matsayinsa"
Ya faɗa yana mai gyara zamansa,sannan ya cire hular da ke kansa ya juya da nufin ajiyewa akan dan table ɗin dake gefen kujeru.
Carab idanunsa suka sauka akan Islam,wacce ke kwance kamar mai barci,sai dai azahirin gaskiya kallo ɗaya zakayi mata kasan idanunta biyu,duba da yadda jikinta ke ɗan rawa,sannan tana sauke wani irin numfashi da sauri-da sauri.
Sosai kalaman Aslam ke yawo cikin kwakwalwarta,lallai ta yarda ta kuma aminta Aslam baya ƙaunarta,agabanta yake faɗin irin waɗannan kalaman akan wata?ba ko kunya bare kara?wato ita amatsayin kanwa take agareshi,waccan itace abar ƙaunarsa.
Wai shin me yasa ma zuciyarta tayi mata rashin adalcin kamuwa da son Aslam ne?me yasa ta yarda ta auri Aslam?

Shikuwa Aslam ji yayi jikinsa yayi sanyi,dan kuwa harga Allah baisan cewa Islam tana falon nan ba,da bazaiyi wadan nan maganganun haka ba,koba komai ita ɗin matarsa ce ,kuma dole taji ba daɗi,duk da yasan bawai sonshi take ba,amma dai bai kamata ya fadi irin wannan kalaman agaban taba.kuma yasan tabbas taji duk abinda suka tattauna dasu mommy.

Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai,kusan minti biyu yana kallon yadda jikinta ke rawa,tana sauke numfashi,ahankali ya kai hannunsa tare da dafa kafaɗunta.
Islam kuwa kamar wanda aka ɗora mata wuta, tayi sauri zabura tare da ture hannunsa daga jikinta,wani irin kallo mai cikeda ma'anoni kala kala take jifansa dashi, kafin ta mike cikin hanzari ta bar falon.part dinsu ta nufa cikin sauri,
Kai tsaye ta wuce dayan dakin ta sanya masa key .
Zama tayi bakin gado jikinta yana rawa,wani irin masifaffen kuka ne ya kwace mata mai matukar zafi da ƙona zuciya.da ƙarfi kukan ya kufce mata ba tare da ta shiryawa hakan ba,cikin sauri ta sanya hannunta ta toshe bakinta,dan hanawa sautin kukan nata fitowa,duk da hakan baiyi wani tasirin hana kukan fita ba.
Kuka take sosai tana jin tausayin kanta,na kamuwa da don wanda bata ita yake ba,mutumin da yayi zurfi cikin soyayyar wata,son da baya hanashi faɗin yadda yake ji game da masoyiyarta tashi gaban kowa,ciki kuwa harda ita dake matsayin matarsa.
Mmn
Aslam kuwa yana ganin ta tashi shima yayi saurin biyota,dan yasan bai kyauta mata ba, saidai kafin ya ƙaraso tuni ta rufe kofar.
Tsaye yayi abakin ƙofar yana kallon ta.
Har zuwa lokacin da yaki ta fashe da wanan kukan mai zafi.
Runtse idonsa yayi yana jin kamar an watsa masa dalma cikin zuciyarsa,sosai yake jin zafin kukan nata cikin zuciyarsa,sam baya son jin ta ko ganinta cikin damuwa.amma ba yadda zaiyi,zuciyarsa cike take da kaunar Husna,kuma baya jin zai iya fasa auren ta.

Jin yadda Islam ke kukan kamar zata shiɗe ne,kuma bata da niyyar dainawa,yasashi fara buga ƙofar yana kirana sunanta.
"Islam !Islam!! Islam!!!
Please ki buɗe kofar nan muyi magana,an sorry Islam,dan Allah ki daina kukan nan,wllh zuciya zata buga bana son jin kukanki ko kaɗan Please Islam"ya fada cike da damuwa kamar zaiyi kuka.
Wani malolon baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Islam,wai baya son jin kukanta?kuma zuciyarsa zata fashe?kuji rainin hankali fa? Ita zai maida karamar yarinya hmmmm wllh daga yau tayi alkawarin ta daina yarda koda zama suyi guri ɗaya da Aslam,bare ya Sami damar taba jikinta,tunda ta gane ba sonta yake ba,jikinta kawai yake muradi.
Banza tayi dashi taci gaba da kukanta,har saida taji kanta na neman yi mata ciwo kafin ta hakura.
Alwala ta dauro tayi sallar ishsha.
Sannan ta kwanta.

Aslam Yana kwance adakinsu, saidai sam ya kasa barci,sai juyi yake yi tunanin Islam,ga wata irin faduwa da gabansa keyi,da zarar ya fara tunanin Islam,sai yaji gabansa ya faɗi sosai, sai kuma Husna ta fado masa.
Haka dai yayi ta juyi zuciyarsa ba dadi har gari ya waye.

Koda gari ya waye Islam tana shiryawa tayi saurin fitowa daga part ɗin.
Gaba ɗaya haushin yan gidan take ji,dan tana ganin duk da amincewarsu Aslam yake ƙoƙarin kara auren,dan haka bata shiga koda part din mommy ba,tayi fitowar ta daga gidan sanye da uniform ajikinta.
Bata da ko sisi bare ta hau adaidaita.
Haka ta kama hanyar makarantar aƙafa.

Aslam Yana tashi ya nufi dakin da Islam ya kwana,dan da asubama saida ya zo yayi mata magana amma tayi banza dashi.ganin dakin abuɗe yasa shi gane ta fice kenan.

Da sauri ya fito shima,baba mai gadi ya tambaya ko yaga gilmawar Islam?nan yake sanar dashi yanzun nan ta fice da uniform ajikinta.
Dafe kai yayi tare da runtse ido,yanzu ta yaya zata iya zuwa wannan makarantar mai nisa aƙafa?
Da sauri ya shige motarsa ya fice dan bin sawun ta.

Aikuwa saida yayi tafiya mai ɗan nisa kafin ya hangota,tana tafe cikin nutsuwa,wanda damuwar da take ciki suka ƙara sanyaya mata jiki,hakan yasa take tafiya ahankali.
Shan gabanta yayi da mota tare da budewa ya fito .

"Dan me zaki fito kice zaki tafi school aƙafa?me amfanin motocin gidan? Haba Islam me yasa kike son azabtar da kanki ne"ya fada cikin sigar rarrashi yana kokarin kamo hannunta.

Da sauri ta ja da baya tana maida hannunta baya.harara ta banka masa tana faɗin"karka sake kace zaka taɓani,domin an wuce wannan lokacin,kuma ina ruwanka dan zan tafi makarantar aƙafa? Shin kafarka ce ko tawa"Islam ta faɗa cikin fushi tana hararar Aslam.

Murmushi Aslam Yayi yana mai faɗin"na ji koma me zaki ce shigo muje na kaiki,kinga akwai nisa,bazaki iya zuwa aƙafa ba kaf....."
"Bazan shiga motar taka ba"Islam ta katseshi cikin daga murya tana hararar motar.
Sanin da yayi wacece Islam,yasanyashi,shammatar ta ya sureta ya tura cikin motar.
Da sauri ya kulle tare da dannan key bayan ya shiga shima.
"Malam ka budemin kofa in fita,ko dolene sai an shiga motar taka?"Islam ta faɗa cike da jin haushin yadda ya tilasta mata shiga motar.
"Ki fita mana ai ban hanaki ba ko"Aslam ya fada ba tare da ya kalleta ba .
Ƙofar motar ta kama kici-kici dan budewa,amma ko motsi ƙofar batayi,tsabar haushi kawai ta sanya kuka.
Shiru Aslam yayi baice mata komai ba har suka karasa cikin makarantar.
Tsayawa yayi tare da kallon ta,sosai wllh yake jin tausayinta,bayajin daɗin ganin ta haka.
Ahankali ya kira sunanta"Islam, Please ki fadamin meke damunki? Me yasa kike jin haushina kwana biyu?"
Ya faɗa yana kallon fuskarta,wacce take fayau ba ko mai bare kwalli,sai sheƙi take kamar fuskar jarirai.
"Budemin mota zan fita"Islam ta faɗa idonta na kallon window.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauke,wato bazata bashi amsa ba kenan?
"Tambayar ki fa nake Islam,ki sanar dani meke damun ki? Men.....
"Kai ke damunta Aslam! Ka takurawa rayuwata,dan Allah ka gyaleni in huta kaje kayi rayuwarka,nima ka barni nayi tawa"Islam ta faɗa cikin masifa da tsantsar kishi,wanda kallo ɗaya zakayi mata ka gano hakan.

Kallonta kawai Aslam yakeyi,ya gane tana jin haushi ne akan batun Husna,amma dole tayi hakuri dan bazai iya fada auren Husna ba.
Cikin sigar rarrashi yace"yanzu kina ganin hakan shine dai-dai?ta yaya zaki ce in barki kiyi rayuwarki?Nima nayi tawa?ok shine jiya kika kulle kanki adaki kikaƙi fitowa ?wannan shine matakin da kika ɗauka akan abinda Allah bai hana ba?aure fa zanyi ba wani mugun abuba.
Aslam ya fada yana kallon ta.
Runtse ido Islam tayi,dan maganar da takeyi dashima yanzu,ji take kamar ta shaƙe shi,
"Aslam ka budemin kofa in fita,an faɗa maka wani banzan auren da zakayi ya dameni ne?wllh in kaso kaje ka auri hudu,inyaso nika bani takarda ta,dan kasan dama baka gabana bare naji haushin auren ka kona ɓata raina,Ina Dana sanin yarda danayi ne na auri mutum irin ka wanda baisan menene kara ba" Islam ta faɗa cikin masifa kamar zata cinye Aslam.

Shikuwa Aslam bakin ciki ne ya turnuke masa zuciya,wato bata damu dashi Bama,duk wannan abun da take tana nufin bawai kishinsa take ba?wato ya auri hudu ma,In yaso ita ya bata takardar ta bata damuba?
Cike da ɓacin rai ya dannan securityn motar ta buɗe yace "fita !"da ɗan ƙarfi cikin ɓacin rai.

Taɓe baki Islam tayi kafin ta fice daga motar,ko waiwayensa batayi ba ta shige cikin ajinsu.

Shikuwa Aslam ransa abace yaja motar,dan me Islam zatace bata damu dashi ba,kenan duk abinda yake mata ita Bama sonshi take ba?ƙwafa yayi tare da figar motar da gudu.

Kamar yadda mommy ta faɗa kuwa, balance ta kasance,ta sanar da daddy batun Aslam da Husna,abin mamaki kuwa ba musu ba komai ya amince,nan take ya kira abokansa su biyu,yasanar dasu akan zasuje nemawa Aslam aure da yamma.
Dan mommy ta sanar dashi granny ma ta amince .duk da haka saida yaje suka tattauna akan maganar.

Washe gari kuwa akaje aka nemawa Aslam auren Husna,ba bata lokaci suka gama komai,nan da sati biyu za'ayi auren.
Lokacin da za'aje neman auren,daddy ya nemi abban Islam akan suje tare ,amma baya ƙasar,hakan ya hanashi zuwa,saidai yayi musu fatan alkairi.

Murna gurin Aslam kuwa ba'a magana ,bare kuma uwar gayya Husna.
Lokacin da labarin ya sami Islam,bata nunawa su mommy komai ba,tayi fatan alkairi garesu,sannan ta bar falon.
Kai tsaye ta nufi lambu,can saman bishiya ta haye ta kwanta tare da lumshe idanunta.xuciyarta naci gaba da tafasa kamar garwashin wuta...

Hmmmm muje zuwa masu karatu.

Anty mammy ce
Mrs babi.
[10/25/2022, 4:52 PM] Abk: 71/72
____________Saman bishiya Islam ta haye,tare da kwanciya jikin wani reshe ta lumshe idanunta.
Zuciyarta na ci gaba da tafasa kamar ana izamata wuta.tana rungume da janbu ajikinta,kamar wata marainiya haka take jin kanta.

So take ta kawar da damuwarta,ta cire batun auren Aslam daga cikin ranta,amma abin nema yake yafi karfin ta,dama haka kishi yake?lallai kishi zai iya hallaka mutum,domin a yadda take jin zuciyarta na bugawa, to idan batayi wasa ba lallai gab take da fashewa.
Ko kaɗan bata ƙaunar wannan husnar,dan ita zuciyarta ma bata amince da itaba,ga dukkan alamu bata da gaskiya,dan tana kallon ta taji hankalinta ya tashi.

Nan gurin dai Islam tayi kwanciyarta tana ta fama da raɗaɗin zuciya.

Da daddare bayan an kammala cin abinci,wanda Islam cakala kawai take,dan bata wani jin dadin abincin abakinta.
Aslam Yana zaune yana kula da yanayin ta,duk da ta bata masa rai dazu,amma ko kaɗan baya jin dadin ganinta cikin wannan yanayin,kamar ba Islam ɗin daya sani ba,mai neman tsokana da tsiwa,duk ta maida kanta shiru-shiru bata hira,bata tsokana,yanzu seniorityn ma ta daina,duk abun nata ya zama sukuku.
Su mommy kuwa hirarsu kawai suke,ta yadda za'a hado kayan lefen Husna,da irin abubuwan da za'a sanya acikin lefen,za'aje flazar Aslam gobe adebo kayayyakin acan.
Da abin ya ishi Islam kuwa,
Mikewa tayi daga kan danning table ɗin,dan bazata iya jurar sauraron wannan hirar tasu ba.
"Ina kuma zaki Islam ana cin abinci?"
Mommy ta faɗa ganin Islam ta mike.
Ahankali Islam ta kalli mommy kafin tace "mommy barci zanje nayi na gaji "ta faɗa tana mai kawar da kanta dan gudun su gano damuwar dake cikin ranta.
"To Islam kodai kishi kikeyi ne?naga ana zancen kayan auren kishiyarki zaki gudu ɗaki,wllh dai karki zama raguwa dan ninan da kike gani jaruma ce ba komai ke daga min hankali ba"granny ta faɗa tana watsa hannaye.

Wani kallo mai cike da jin haushi Islam ta jefawa granny kafin cikin murya mai dauke da ɓacin rai tace"Kodama dai kishi halitta ne,amma kisani bazan tsaya ina bata lokacinna wajen kishin wanda baya gabana ba,ina ruwana da zancen ku da zai dameni, kawai ina jin rashin daɗi ne,ta yadda ahalina suke fifita soyayyar wata akaina,wanda tsabar son da suke mata agabana suke hirar kaunarta garesu,sun ma manta cewar yarsu ce ni.
Amma karki damu granny,Islam rainon dawa ce,Ni kadai na dama na tashi,kuma zan iya rayuwata Ni kadai"
Islam na kaiwa nan a maganar ta ,ta nufi hanyar part dinsu cikin sauri.
Sosai jikin su mommy Yayi sanyi,gaskiya abinda suke mata sam basu kyauta ba,amma sun rasa menene abinda ya rufe musu ido,har suke mantawa Islam jininsu ita za'a kawowa kishiya,kuma kasancewar Islam aguri, baya hanasu yin hirar husna.koba komai sa tayata jimami idan basu hana auren ba.
"Kai wllh sai yanzu nake jin tausayin Islam,yarinyar nan tayi kawaici akan mu,kullum zancen mu Husna bata taɓa yin magana ba sai yau,amma dole tayi hakuri,ta saba da hakan tunda dai itama husnan gab take da zama yar gida"cewar granny cikin jimami.

Mommy kuwa kallon Aslam tayi,wanda yayi zaune riƙe da cokali ahannunsa yana kallon Islam,tunda ta fara magabata ,harta kammala.
Shi kansa baya jin daɗin yadda ake hirar agabanta,amma abinda ya lura da yan gidan nasu,sun kamu da son Husna sosai suma,har basa iya boye soyayyar da suke mata.
"Aslam kaje ka rarrasheta Please,dan ranta ya ɓaci"mommy ta faɗa cikin sanyin murya.
Tashi Aslma yayi tare da bin bayan Islam ɗin.
"Gaskiya mommy ba'a kyauta wa Islam agidan nan,gaba ɗaya kana kallon Islam kasan tana cikin damuwa,kullum baku da zance saina Husna Ni wllh husnan nan bata wani min ba ko kaɗan,abu shirin kamar kayan wanki"Aman ne ke wannan maganar cikin ɓacin rai,yana ajiye cokalin hannunsa yayi hanyar ɗakinsa. Dan sosai yake tausayawa Islam da wannan auren da yayan nashi ke ƙoƙarin yi,
Kallo kawai suka bishi dashi,kafin grannyn tace "ja'irin yaro,kuma ahaka zata zama antyn ka ko kana so ko baka so,ai baka fimu son Islam din ba,ba yadda zamuyi ne,tunda aure sunnar ma'aikin Allah ne"

"Allah nima tausayi Islam take bani,duka -duka ma yaushe akayi bikin nasu?amma yaya zai kara mata wani auren, Ni wllh idan mijina zaimin kishiya bazan zauna ba,saidai mu rabu"hanan ta faɗa tana turo baki.
"To hanan muma fa tana bamu tausayin,kawai muna son karfafa mata zuciya ne,amma kishiya kam ai kowa ya sani ba daɗi"cewar mommy tana ci gaba da cin abincin ta,can kasan zuciyarta kuma tana jin tausayin Islam.

Islam kuwa tana zuwa falo ta zauna akan kujera,abin yana matukar bata mata rai,yadda danginta suke nuna soyayya kiri-kiri akan husna sama da ita,sam basa tayata kishi,gaba ɗaya yanzu gidan ya fita daga ranta,ba abinda take bukata illa tajita jikin mommyn ta,tayi kukanta son ranta,koba komai tasan zata samu nutsuwa.
Kuka take cikin sauti marar ƙara,lallai duniya juyi -juyi,wai yau ita islam,itace ke zaune tana kuka akan damuwa?kuma bata da hanyar magancewa kanta damuwar.
Duk wannan Aslam ɗin ne ya jawo mata,wllh yanzu jima take ta tsaneshi ,bata son ko kusa da ita yazo.
"I hate you Aslam,na tsaneka"ta faɗa cikin muryar kuka tana shura kafa.
Karab!! Kalamanta suka sauka akan kunnen Aslam,runtse idonsa yayi da ƙarfi,dan ji yayi kamar ta caka masa mashi cikin ƙahon zuciyarsa.ya tsani yaji tana furta irin waɗannan kalaman akansa.

Fuska ba walwala ya shiga cikin Falon,zama yayi dan nesa da ita ya tsira mata ido,gaba ɗaya ta sauya,kamar ba Islam ba,har wata yar rama tayi.
Ahankali yace
"Ya kamata ki daina wannan kukan Islam,bakya tunanin zai iya haifar miki da wata matsalar?haba Islam gaba ɗaya kin sanya kanki cikin damuwa kin zama kamar bake ba,Please ki dawo Islam ɗin dana sani abaya,nafi son ganinki ahaka "

Aslam ya fada cikin yanayi na damuwa.
Ita kuwa Islam ko ci kanka bata ce masa ba.
Cikin damuwa yace "Islam ,me kike so nayi miki yanzu?ya fada cikin sanyin murya.
Da sauri ta juyo tana kallonsa,wanda da tayi banza dashi taki kallon inda yake,
Cikin zubar hawaye tace "so nake inkoma gidan mu,gurin mommy na"ta fada hawaye naci gaba da zuba kamar an bude fanfo.

Kallonta yayi na dan wasu sakwanni,yace "idan na kaiki gidan anty shikenan?shikenan zaki daina kukan?"ya fada yana kallon idanunta da suka danyi ja,zai kaita taga antyn,yasan zata ji sassauci cikin zuciyarta.inyaso saiya dawo da ita .
Cikin tsiwa da harara tace
"Wannan kuma bai shafe ka ba,kaga malam, nifa tafiya ta zanyi dan zan iya zuwa da kaina ba neman taimakon ka nakeyi ba, kawai inason ya kasance kaine ka amince min da kanka Dan mommy na ta tasan bada kaina nazo ba"ta faɗa cikin masifa tana mikewa tsaye.
"Shikenan to,kiyi hakuri shirya muje na kaiki da kaina,In kuma ba haka bazaki je ko ina ba,zan kira mommyn in faɗa mata bada amincewata zaki zo ba" ya fada yana kallon ta .
Dan jimm tayi na wani lokaci,kafin ta mike
Daki ta shiga jim kaɗan ta fito riƙe da mayafinta,ko magana batayi masa ba,tayi waje abinta.
Girgiza kai Aslam Yayi kafin ya bi bayanta.
Shiga tayi cikin motar ta zauna fuskarta ahade ba alamun fara'a ko kaɗan.
Haka suka nufi anguwar su mommy.

Yana ta Jan ta da magana amma tayi banza dashi.suna cikin tafiya kuma Husna ta kirashi a waya,jikinsa har rawa yake wajen daga kiran nata.
"Hello ranki ya dade gimbiyar mata"ya fada kamar an fizgi maganar daga bakinsa.

Ta can bangaren kuwa,juyi Husna tayi akan gadon ta, tare da lumshe ido sakamakon jin daddaɗar muryar Aslam dake ratsa sannan jikinta .
"Tare da kai autan maza angon Husna "ta faɗa cike da shauki.
Cikin murmushi Aslam yace "ya ake ciki ne gimbiya ta?
Husna kuwa cike da shagwaba tace"idanuna ke buƙatar ganin kyakykyawar fuskarka agabansu"
Ajiyar zuciya Aslam Yayi tare da cewa"kisa aranki ganinan har na zo gareki masoyiyata,domin nima nawa idanun na mararin kallon kyakykyawar fuskarki"ya fada yana ɗan juya sitiyarin motar cikin nishadi.

Tuni wata bala'ey'iyar zuciya ta gama ciyo Islam,wanda Bama tasan lokacin data fizge wayar daga kunne Aslam ta doka ta da ƙasan motar ba,cikin hucin ɓacin rai ta fara magana"wllh kayi karya Aslam,niba lalatacciyar mace bace,wacce zaka wulakanta yadda kaso ba,baka da wannan matsayin na kiran budurwa agabana kana faɗa mata kalaman soyayya,idan bana gurin kaje ku cinye juna da kalamai ma bai dameni ba,amma baka isa ka tozarta ni ba "Islam ta faɗa numfashinta na cikowa kamar zata shiɗe.

Ikon Allah,wllh gaba ɗaya Aslam yama manta da cewar Islam na cikin motar nan,tunda Husna ta kirashi, kuma haka ke kasancewa dashi,Aduk lokacin da yake tare da husna kota kirashi,komai ma mantawa yake dashi,yanzu ma tana kiransa ya mance da wata Islam cikin motar,hakan yasa yayi ta sakin magana son ransa.sai da Islam ta warce wayar sannan

Please Login or Register in order to submit comment