Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanya hannunsa yana shafa soft lips ɗin ta,kafin yace "wai meye ne yau naga kina wani jamin aji?inaga fa dole sai na nuna jaruntata ayau,dan na tsinka ajin nan"Aslam ya fada yana ɗora bakinsa kan na Islam.
Sosai Aslam ya zage Yana saukewa Islam hadda, gaba dayansu sun fice daga hayyacin su,Aslam Ya gigice sosai da irin salon da Islam ke nuna masa yau,cikeda buƙatuwa yake ƙoƙarin angoncewa, saidai ƙam yaji Islam ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kai,alamun a'a.
Cikin ɗimuwa da buƙatuwa yace "why Islam ?me yasa bazaki barmu muji daɗin auren mu ba?meyasa kike azabtar da zuciya da gangar jikin mu?Please kiyi hakuri ki bari na samu nutsuwa dake,wllh idan kika barni haka zan shiga wani hali"Aslam ya fada cikin wata irin murya mai kamar zaiyi kuka.banda tsuma ba abinda jikinsa keyi.

Ita kanta Islam tana tsananin bukatar kasancewa dashi,saidai har yanzu bai cika sharuddan da zai sa ta amince masan ba,bata san menene cikin zuciyarsa game da ita ba,bata sani ba ko iya jikinta yake so,dan haka tayi alkawarin bazata bari ya kusanceta ba,har sai ranar daya furta mata kalmar so da kansa.
Dan haka cikin sauri ta tashi tare da janyo rigarta ta sanya tace "kayi hakuri bazan iya mallaka maka kaina ba"ta faɗa cikin sanyin murya.
Da ƙarfi aslam ya runtse idanunsa,yana jin wani irin zafi cikin zuciyarsa,me yasa Islam zatayi masa haka?shin bata san irin azabar da yake ji bane?
Ahankali ya buɗe idanunsa da suka gama rinewa yace"Please Islam ki taimaka min awannan halin da nake ciki komai zai iya faruwa dani,ki daure ki bani hakkina dake kanki nifa mijin kine kuma kinsan ina da hakki akanki"Aslam ya fada cikin yanayi na marairaita yana riƙe mararsa.
Girgiza kai Islam tayi tare da saukowa daga kan gadon ta nufi ƙofa "kayi hakuri bazan iya ba"tana faɗin haka tayi waje.
Hannu Aslam ya dunkule tare da kaiwa bango naushi.ji yake kamar ana zazzaga masa fetur acikin zuciyarsa.sosai ransa yayi matuƙar ɓaci,wani irin haushin Islam yayi masa dirar mikiya.
Wato bata damu ba, koma meye zai sameshi ya sameshi ko?shine tayi ficewar ta ta barshi cikin wannan halin? In sha Allah daga yau,bazai ƙara neman hakkinsa agurin ta ba,taje tayi duk abinda zatayi dashi.duk lokacin dataga dacewar ta bashi ,ta bashi dan kanta.
Tsabar ɓacin rai nan take yaji baya jin sha'awar ma ahalin yanzu,wanda kafin wannan lokaci ji yake kamar zai mutu dan sha'awa.
Bayi ya shige ya watsa ruwa kafin ya dauro alwala yazo ya kwanta,zuciyarsa cike da jin haushin Islam.

Islam kuwa dakin A'isha ta shige ta kwanta bayan ta.
sosai take jin ba dadi cikin ranta,tasan bata kyauta ba abinda tayi,amma dai tana da nata dalilin nayin hakan.
Tana kwance amma zuciyarta tana gurin Aslam,tunani take ko wane hali yake ciki yanzu?ko yaji haushin ta akan abinda tayi masa?
Juyi tayi ahankali tare da janyo A'isha ta rungumeta ajikinta.
dan ko kaɗan bata jin dadin kwanciyar,ta riga ta saba kwana akan kirjina Aslam.
Haka tayi ta juyi sai can barci yayi gaba da ita.
Shima dai Aslam anashi bangaren hakan ce ta kasance,sai juyi yake yana tsaki, ƙoƙarin cire tunanin Islam yake daga zuciyarsa,amma ya kasa ko yaya ya juya ita yake ji ajikinsa,daga karshe ma tashi yayi ya dauro alwala ya kama nafila,san can cikin dare shima barci yayi gaba dashi.

Washe gari kuwa da sassafe ya bar gidan,inda ya sanar da mommy akwai wani meeting daya taso masa na gaggawa shiyasa ,zai tafi.

Islam kuwa makara tayi kasancewar week end ne ba school,gashi ta jima batayi barci ba,dan haka sai wajen bakwai ta tashi.
agurguje tayi wanka tare da alwala,bayan tayi salla ta tashi A'isha itama tayi,sai murna A'isha take ganin tare suka kwana da natyn ta.
Kai tsaye Islam ta fito falo,idonta akan dakin da Aslam yake,so take taje taga ya ya kwana,amma tana jin nauyin yin hakan.
Dan haka kitchen ta bi mommy bisa rakiyar A'isha.
Bayan sun gaisa ne Islam ta tsaya tana kallon mommy tana ta ƙoƙarin haɗa breakfast.
Kallon ta mommy tayi kafin tace "Islam bazaki tayani aikin ba"ta fada fuskarta ɗauke da murmushi.
Ɗan zaro ido Islam tayi kafin tace"tab Ni kuwa mommy me na iya?nida saidai kawai inga abinci a ajiye,aikina kawai ci"ta faɗa tana ɗan taɓe baki,idonta akan mommy.
Murmushi mommy tayi kafin tace "aikuwa dole ki koyi girki, kodan mijin ki,bazai yiwu ace kullum saidai kuci na gida ba,wani lokacin yana buƙatar girkin matar sa shima,dan haka matso ki gani"
Tare da Islam dai mommy sukayi girkin nan,Islam sai murmushi take tana jin dadi,ashe haka yin girkin yake da daɗi?aikuwa zata dage da kowa .
Lokacin da Islam tasan tun safe Aslam ya bar gidan, abin baiyi mata daɗi ba,kuma tasan haushinta yake ji,duk sai taji haushin kanta takeji,meyasa ta tafi ta bar dakin?koba komai data tsaya ta rarrasheshi ai,tunda dai kusan koda yaushe hakan ce ke faruwa.

Haka suka gama komai suka rankaya gidan mommy.

Husna ce zaune kusa da mahaifiyar ta,tana mata bayanin yadda zatayi amfani da maganin data karbo daga gurin boka.gefe guda mahaifinta ne shima yana sauraron bayanin da ake mata.
"Ki tabbata ya shaƙi ƙamshin wannan turaren,sannnan karki sanya wannan kwallin sai kinyi gab da shiga gidan,da zarar kin sanya, to ki sunkuyar da kanki ƙasa,karki yarda ki kalli kowa sai kinji Muryar Aslam.
Shikuma da zarar ya shaƙi wanan turaren zaiyi ya son ku haɗa ido dashi,da zarar kun haɗa ido kuwa shikenan aiki ya gama,kuma shida matar nan tasa sai wulaƙanci da cin mutumci,ke kuwa,sai batun aure,dan boka ya tabbatar min da cewar har yanzu bai tara da matar tashiba, ke kuma da anyi auren ku,kiyi duk yadda zakiyi ki hanashi kusantar matar dan kuwa duk lokacin daya kusanceta,shikenan asirin zai lalace,kuma sakinki zaiyi boka ya fadan hakan"ta kai aya tana mikawa Husna wasu kwalabe guda biyu.
Karba Husna tayi cike da farin ciki tana mai rungume mahaifitar Tata tace"kai mommy wllh kin gama min komai arayuwa,In babuke bansan ya zanyi ba ,na gode sosai mommyna"ta faɗa tana dariya .
Mahaifin ta yana zaune sai murmushi yake,shi kansa yana jin dadin yadda matar tasa ke kula da al'amuransa, da zarar abu ya shige masa duhu,tana zuwa gurin bokanta shikenan lamari ya zo karshe.
Tashi Husna tayi tace "bari naje na shirya mommy "ta faɗa tana nufar ɗakinta da gudu rigija -rigija da uban nonuwa kamar kayan wanki.

Suna zaune gaba dayansu afalon,ana ta hira,kowa na gidan yana cikin Falon in Banda daddy da yayi fitar sassafe,sai kuma Aslam,hankalin Islam gaba ɗaya yana can wajen tunanin ina Aslam Yayi?tashi tayi tsam ta nufi part dinsu ba tare da sun fargaba.dan ta kasa jurewa rashin ganin Aslam ɗin.
Tana shiga part ɗin taji kamshinsa mai sanyin daɗi,lumshe ido tayi tana mai sakin murmushi,tasan yana ciki.ahankali ta taka zuwa cikin dakin nasu.
Da sallama ta tura ƙofar dakin ta shiga.
Yana kwance ,ya bawa kofar baya,yana sanye da dogon wando da riga kanana kayane masu kyau , kallo ɗaya idan kayi masa zakayi tunanin barci yake,nan kuwa idonsa biyu,yana jin sallamar Islam yaji wani sanyi cikin ransa,amma so yake ta nuna mata yayi fushi da ita.dan haka yayi kamar barci yake.
Sallama Islam ta sake yi amma taji shiru.
Ahankali ta taka cikin sanda ta nufi inda yake,leƙa fuskarsa tayi,taga barci yake.
Ahankali ta sauke ajiyar zuciya tana mai bin fuskarsa da kallo,masha Allah Aslam ba karamin kyakykyawa bane,komai nashi kwanin burgewa,hannunta ta daga da nufin shafa fuskarsa,amma saita maida hannu.tayi haka kusan sau uku,kafin ta daure ta ɗora hannunta kan sajensa tana shafawa ahankali.kallon lips ɗin sa tayi wanda suka yi pink sosai kamar ya shafa janbaki,ahankali ta furta "so cute "kafin ta Dora baƙinta ahankali Kan nashi bakin tayi masa kiss ahankali .
Saura kaɗan Aslam ya fallasa kansa ,saboda yadda kiss din nata ya shiga jikinsa,amma ya daure.kallonsa taci gaba dayi tana murmushi,kafin ta mike ahankali cikin sanda zata bar dakin.
Carab !!taji an riko hannunta.zaro ido tayi sosai gabanta na mugun bugawa,badai idonsa biyu ba?ya Salam"ta faɗa tana runtse idanunta da ƙoƙarin zare hannun ta.
"Ina kuma zaki?bayan naga kamar baki gama abinda kikeyi ba"ta tsinkayo muryar Aslam.
Dafe ƙirji tayi da sauri, shikenan wllh yana jin duk abinda nayi masa,wayyo ni islam ya zanyi da kunya?ta faɗa tana mai runtse idonta sosai.
Jawo ta Aslam Yayi ta dawo gabansa,ƙureta yayi da ido,yana kallonta,sosai yake jinsa cikin nishadi idan yana kallon fuskarta.islam kuwa ta kasa bude idonta bare ta kalleshi.
Ahankali ya ɗago fuskarta yana kallon bakinta.ji yake kamar yayi ta kissing dinta,Amma yayi alƙawarin sai lokacin da taso hakan da kanta.
"Buɗe idonki"ya fada cikin muryarsa mai daɗin sauraro.

Ahankali Islam ta buɗe idonta ta sauke akan fuskarsa.
Murmushi yayi mata kafin yace"meye najin kunya? dan kinyi kissing lips ɗin mijinki?ko laifine yin hakan?ya fada yana saukowa daga kan gadon, dan idan yaci gaba da zama kusa da ita,to tabbas zaiyi watsi da alwashin daya dauka.
Turo baki Islam tayi tace "nifa dama zuwa nayi in faɗa maka mommy tazo"ta faɗa tana wani ƙaryar da wuya.
Murmushi yayi yana mai kama hannunta yace "to muje can ɗin"
Tare suka fito riƙe da hannun juna,suka nufi part din su mommy.
Suna bude kofar falon ,wani irin ƙamshi ya doki hancin Aslam,Wanda nan take yaji kansa yayi mugun sarawar da saida ya dafe kan nashi yana mai runtse idonsa.
Kallonsa Islam tayi tace "lafiya"tana kallon yadda lokaci ɗaya yanayin fuskarsa ya sauya.
Girgiza kansa yayi yace "ba komai muje"
Haka kawai yaji yana son ganin Husna, yau ɗaya,wacce shi yama manta da ita sam,amma yau kam ji yayi yana son ganinta.

"Ya aslam ina kwana"yaji muryar Husna ta doki dodon kunnen sa.
Da sauri ya kai kallonsa inda take zaune,aikuwa carab,idanunsu suka sarke cikin na juna.
Wani irin abu yaji ya cakeshi cikin ƙahon zuciyarsa,lokaci guda ya daina ganin kowa agurin sai Husna.
Nan take yaji wata muguwar soyayyar Husna ta shiga zuciyarsa,ba shiri ya saki hannun Islam yayi gurin da Husna ke zaune yana sakar mata murmushi.
Cike da mamaki Islam tabi hannun ta daya saki da kallo,kafin ta bishi da kallo shima.

Wacece wannan ɗin ?
Islam ta faɗa cikin wani irin zazzafan kishi,tana kallon yadda Aslam ya zauna kusa da husnan.

To fa muje zuwa masu karatu.

Nagode sosai da addu'ar ku gareni,
alhamdullah naji sauki sosai,Allah ya bar kauna.

Anty mammy ce.
[10/22/2022, 12:42 PM] Abk: 67/68
"Wacece wannan ɗin" Islam ta faɗa cike da wani irin zazzafan kishin da taji ya taso mata lokaci ɗaya.tana kallon Aslam wanda ya zauna kusa da Husna yana sakar mata ƙayataccen murmushi.
Cikin haɗe rai Islam ta karasa cikin Falon,ta zauna kusa da mommynta ba tare da tace komai ba,saidai kallo ɗaya zakayi mata kasan ranta abace yake.
Su mommy kuwa hirarsu suke hankali kwance,basu kawo komai aransu ba dangane da zaman da aslma yayi kusa da Husna,

Aslam kuwa ji yake kamar ya maida Husna cikinsa,dan wani irin so da kauna yaji yana yi mata marar misaltuwa.
Kafeta yayi da ido yana kallonta,ita kuwa cike da kissa ta ɗago idanunta tana kallonsa tare da yi masa fari da ido tace "kai yaya Aslam ya haka da kallo ?"ta faɗa tana wani juya ido kamar mujiya.
Shikuwa Aslam ji yayi kamar wanda ta jawo zuciyarsa,wani irin kyau yaga ta ƙara masa cikeda wata murya mai dauke da tarin ƙauna da shauƙi yace"badan kar kice nayi karya ba,sai ince ban taba ganin macen data kaiki kyau ba,ke ɗin ta musamman ce domin sosai nake kinji cikin raina"Aslam ya fada yana aika mata wani sihirtaccen kallo mai cike da ma'anoni kala-kala.
Wani irin dadine ya cika zuciyar Husna, lallai aikin boka yayiDomin ga alamu nan sun nuna hakan,dubi yadda Aslam mai ji da kai da rashin sakin fuska,yake ta zuba mata tsadajjen murmushinsa?kuma agaban matar sa,wayyo daɗi.
Cike da kissa tace "kai yaya Aslam Banda zuga fa?niɗin ina naga wani kyau?kawai dai kana fadane dan naji daɗi"ta faɗa tana kafe shi da ido.

Murmushi ya sake yi akaro na barkatai,kafin ya gyara zama yana kallon ta,cike da kallon ƙauna yace "ai Ni a idona kinfi kowa kyau,kuma bana ganin kowa sai ke,dan haka zanzo gidan ku ma anjima sarauniya"ya fada yana mai jin wani sonta na ƙara shiga zuciyarsa.yayin da agefe guda kuma yake jin wani ƙunci acikin zuciyarsa.
Saura kaɗan Husna ta sanya ihun tsabar murna,lallai tsafi gaskiya ne,yanzu da mommyn tasan da wannan aikin,ta barni nake ta shan wahala da soyayya?Husna ta fada cikin zuciyarta.
Tana mai kallon Aslam kamar ta cinyeshi take ji dan so.

Duk abinda sukeyi,hankalin Islam na kansu,wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ke azabtar da zuciyarta,ji take kamar zata kama da wuta,wannan wane irin cin fuska ne Aslam ke mata?gaba ɗaya yama manta cewar tare suka shigo falon,kuma agabanta yake fadawa wannan banzar irin wannan kalaman?domin duk abinda suke fadi akan kunnen ta,dan sam bata sauraron abinda su mommy ke faɗi.wacece wannan matar wai?meye alakarta da Aslam?ga dukkan alamu dai sun jima da sanin juna,kuma daga yadda suke kallon juna zaka fahimci masoya ne na hakika, tab lallai akwai babban rikici kenan.
Ahankali Islam ta sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya,lokacin da Husna ta mike Aslam ma ya mara mata baya,sallama tayiwa su mommy cike da kunya,
Amsawa sukayi tare da cewa ta gaida mommyn ta.
To tace tana mai sunkuyar da kanta.
Kafin ta matso kusa da inda Islam ke zaune,murmushi tayi sannan ta kalli Islam tana mata murmushin nata na rainin hankali tace"yan mata ykk"ta faɗa tana daga mata yan yatsun ta biyu.
Wani kallon zanci uwarki ,Islam tayi mata tare da sakin tsaki mai ƙarfi ta kawar da kanta.murmushin jin dadi Husna tayi tana faɗin,yarinya bakiga komai ba,saima na shigo gidan nan,wllh saina hanaki shan ruwa,bakin ciki saiya kasheki da irin abubuwan da zaki gani.
Azahiri kuma kallon Aslam tayi wanda ya kafeta da ido kamar zai cinyeta tayi,kafin tace " ya Aslam wannan yarinyar fa?ba sanya agidan nan ba"ta faɗa tana kallon Islam .

Kallon Islam shima yayi kafin ya dan taɓe baki yace "ƙanƙara ce karki damu da ita" ya fada idonsa akan ta.
Murmushi tayi tana mai kashewa islam ido ɗaya tace "ok bari na tafi ya Aslam kar mommy tace na dade,dama zuwa nayi mu gaisa kuma na ganka"ta faɗa da ɗan daga murya yadda Islam zataji.
Aikuwa tajin, gabanta banda faduwa ba abinda yake,kallonta takai ga Aslam jin amsar da ya ba husnan.
Dakuma wacce yake bata yanzu.
"Muje to na madam na rakako da kaina,dan bana son ki wahalarmin da kanki,amaryata"yana faɗin haka suka yi waje.
Binsu Islam tayi da ido kamar wata zautacciya,amarya ?amarya kuma ?shine abinda take ta nanata wa cikin zuciyarta.
Gaba ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa, ita Bama ƙanwar tashi ɗaya ce bane ya fi daga mata hankali, kamar kalmar amaryata.
kallon su mommy tayi banda hira ba abinda suke,su sam basu san wainar da ake toyawa ba.
Ahankali ta yunƙura ta bi ƙofar da zata sadaka da part ɗin su ta bar falon.
Tana zuwa ta shige cikin dakin nasu ta kwanta.wani irin zafi zuciyarta keyi,wanda bata san lokacin data fashe da wani kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya ba.
Meyasa Aslam zaiyi mata haka?me yasa zai fifita son wata?, agabanta yake nuna zallar kulawa da soyayya ga wata?koba komai yayi mata kara,duk da tasan dama ba sonta yake ba,ya fadi hakan abaya yafi aƙirga,amma saboda rashin wayo da hankali irin nata,har ta bari soyayyarsa ta shiga zuciyarta.jin daɗinta ɗaya ma da bata mallaka masa jikinta ba,da shikenan ya cutar da ita ta ko ina.
Kuka take sosai akan gadon nasu ta tura kanta cikin fillow,ba abinda take ji cikin zuciyarta face tsanar wannan matar mai manyan nonuwa kamar guga.

Shikuwa Aslam saida suka jima suna tattaunawa da Husna, kafin ya buɗe mata mota tashiga.yana jadda da mata zuwanshi anjima.
Ita kuwa sai wani rawar kai take da zumuɗi,haka sukayi sallama ta ja motar ta bar gidan.

Tsaye Aslam Yayi agurin yana bin sawun tayoyin motar Tata da ido,wani yanayi yake ji cikin zuciyarsa marar daɗi,sannan yana tunanin kamar yayi wani abu ba daidai ba.
Ahankali ya dafe kansa dake sara masa kaɗan -kaɗan,kai tsaye ya nufi part ɗinsu Dan ya Dan kwanta.
Yana shiga ɗakin ya jiyo shashshekar kukan Islam,gabansa ne ya fadi sosai,dan sai lokacin ya tuna da ita.
Kuma yasan tare suka shiga part din mommy Amma bazai iya cewa ga lokacin da suka rabu da juna ba.
Da sauri ya karasa bakin gadon tare da zama kusa da ita sosai,cike da karaya ya sanya hannun sa ya dagota gaba ɗaya yana kallon ta.
Islam ma buɗe ido tayi, jin an tabata, karab idanunta ya sauka akan na Alsam, wani irin mugun haushinsa taji ya darsu cikin zuciyarta.
Dan haka azafafe ta fizge jikinta daga nashi tana mai balla masa harara kamar idanunta zasu faɗo.

Mika hannu yayi da nufin sake kamota,tayi saurin ja da baya tana faɗin"karka sake ka tabani wllh,kaje can ita da take da muhimmancin daya fi nawa ka taba ta,amma bani ba"ta faɗa cikin muryarta dake rawar kuka.
Kallonta Aslam Yayi tare da sassauta murya yace "Please mana Islam menene kuma?me nayi miki?ya fada cikin marairaita kamar zaiyi kuka,dan shi wllh yama manta menene abinda ya faru,bare yasan wane laifin yayi mata,dan yasan duk abinda ya sanya Islam kuka haka,to babbane.
Wani shegen kallo Islam ta wurga masa cike da jin haushinsa tace "ban sani ba nima,nace ka gyaleni dan Allah wai dole ne saika kulani?kaje can ku ƙarata da waccan mai nonuwan kamar guga,amma wllh karka sake damuna mugu kawai"ta fada tare da juya masa baya tana ci gaba da kukanta.babban abin ahushinta maimakon taji ta daina sonshi,sai kawai takejin wani irin sonsa na fizgarta jima take tana bukatar ya rungumeta ajikinsa.

Kallonta Aslam yake cike da wani irin tausayinta,sosai yake jin ba daɗi yadda take kukan nan,shi baisan me yayi mata ba bare ya bata hakuri.
Ahankali ya haura kan gadon zuwa inda take,zama yayi abayanta tare da sanyata atsakanin cinyoyinsa,kafin ya sanya hannunsa ya rungumo ta baya.
Kansa ya dora akan kafafunta tare da sauke ajiyar zuciya yace "am sorry Islam,koma me nayi miki kiyi hakuri,bada sanina bane bani da burin sanyaki cikin damuwa ki yafe min Islam am sorry"ya fada Asaitin kunnenta .
Runtse idonta tayi da ƙarfi tana sakin ajiyar zuciya,so take ta kwace jikinta amma zuciyarta sam ta ƙi bata goyon bayan yin hakan.
Sai kukan data sake saki marar sauti.

Shikuwa Aslam har cikin ransa yake jin kukan nata,ƙara rungumeta yayi sosai ajikinsa,yana mai kissing ɗin dokin wuyanta cikin ƙoƙarin sa na mantar da ita damuwar dake ranta.
Lumshe ido Islam tayi tana mai jin yadda yake kissing ɗin wuyan nata so romantic,ta so ace hakan na faruwa ne da dinbin soyayyarta cikin zuciyarsa,sai dai kash!!! Ba soyayyarta azuciyarsa ko kaɗan,yana son yin amfani da damar sa ne dan samun biyan buƙatarsa.
Tunanin hakan da tayi yasa ranta ya ƙara ɓaci,
Da sauri ta tureshi daga jikinta tare da sauka daga kan gadon tayi waje.
Binta kawai yayi da ido,lallai akwai Abinda ke damunta, kuma yana da alaƙa da shi.amma to menene haka yayi mata?wanda ya ɓata mata rai sosai har tayi fushi?
Falon ya fito yaga ko nan ta koma amma sai yaga ba kowa cikin Falon.dan haka ya koma cikin dakin ya kwanta.

Islam kuwa kai tsaye tana fitowa tayi garden,can taje ta haye kan bishiya tare da rungumar janbu ajikinta.
lallai soyayya masifa ce,lokaci ɗaya ta sanya Islam tayi wani laushi ta koma kalar tausayi sosai.

Da gudu Husna ta shiga cikin ƙaton falon nasu tana kwalla kiran sunan mommynta.
"Mommy !mommy!!mommy!!!har sau uku.
"Mommy wai kina ina ne ?kizo kiji abin daɗi da sanya farin ciki,wllh aikin boka yana ci.mommy na kusa zama matar aure" Husna ta fada tana rungume mommynta data ke saukowa daga saman bene, sakamakon kiran yar Tata datajiyo.

Cikin farin ciki mommy ta rungume yar Tata tana faɗin"Ni dama na san Indai kinyin aikin nan dai-dai,to ba Aslam ba, ko ubansa ne wllh sai ya soki,fadamin ya akayi?"cewar mommy cikin dariya tana zama kan kujera tare da kama Husna ma ta zauna.
Dariya Husna tayi tare da faɗin"wllh mommy bakiga yadda Aslam ya ruɗe ba,gaba ɗaya kamar wani sakarai ya koma daga ganina,agaban matar sa fa, ga su mommy Amma ya bar matar yayi gurina ya zauna kinga yadda yake rawar ƙafa?kuma bawanda ya ce wani abu,ke mommy da yamma ma zai zo yace"Husna ta kai zancenta tana buga cinya da taɓe baki cikeda farin cikin samun nasara.

Dariya mommy tayi tana mai cewa"ai ba wanda zaice wani abu dama,dan dukkan su saida nasanya boka ya rufe musu baki akanki,koda anyi auren ma,sai yadda kikaso zakiyi agidan,saidai ki kula dan boka yace itama matar tashi hatsabibiyar kanta ce,asiri baya cinta,sannan idan ta fiye kebewa da Aslam ɗin ma,to na jikinsa ma karyewa zaiyi"

"To mommy yaushe zan barsu su kema ɗin ma? ai wllh kullum muna tare dashi bazan bari ko dakin ta ya shiga ba,mommy afara shiri dan Allah anjima zai zo fa"Husna ta fada tana mikewa tsaye,bari nima naje na fara shirin tarbar masoyi"ta faɗa tana nufar ɗakinta da gudu rigija-tigija.

Dariya mommyn tayi tana mai jinjinawa aikin boka,tace "ai wllh na yarda da boka dari bisa dari,duk abinda ya faɗa tabbas saiya tabbata.

Sai wajajen azahar sannan Islam ta dawo part din nasu,shima salla take son yi,ta ɗanyi wanka.
Lokacin data shigo Aslam Yana kwance yana barci.kasancewar yanayine na sanyi,hakan yasa Aslam ya dan takure jikinsa.
Kallonsa Islam tayi tana jin wata zazzafar kaunarsa na ratsata,har zata wuce,amma ta kasa ganin yadda ya takure jikinsa, ta gane sanyi yake ji.
Dan haka ta dawo kusa dashi tare da ɗaukar ƙaton bargo ta lullubeshi sannan ta wuce toilet.
Wanka tayi tare da ɗauro alwala.agurguje ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ko sallar bata tsaya yiba,dan bata so ya farka daga barcin ya ganta.
Part din mommy ta wuce ,anan tayi sallar ta sannan ta zauna sukaci abinci tare da ci gaba da hira da mommynta da granny.

Aslam kuwa yana cikin barci yaji kamar wanda aka soka masa mashi cikin zuciyarsa,azabure ya farka yana kiran sunan husna.
Hakan kuma ya faru ne sakamakon kiran sa da mommyn Husna tayi ,ta cikin wata kwaryar tsafi da boka ya bata.
Cikin azama ya tashi ya shiga toilet,wanka yayi agurguje yayi Sallah,sannna ya shirya cikin wata ubansu shadda mai kyau da tsada.
Yayi kyau sosai sai ƙamshi yake zubawa.

Part din mommy ya nufa cikin hanzari,
Duk suna falon azaune suna hira.
Mommyn Islam ce ta ce"kai mashá Allah dana,daga nan sai ina kuma ?irin wannan kyau haka?"ta faɗa cikin murmushi.
Murmushi Aslam Yayi shima kafin yace "wllh antyna gidan su Husna zani, shine nake sauri kartayi ta jirana.
Dammmmm!!!gaban Islam ya buga da karfi,har saida ta dafe ƙirjin nata .ɗago kai tayi ta zubawa Aslam ido, shikuwa ko kallon ta ma baiyi ba.
Ɗan jimmm mommyn Islam tayi kana kallonta kasan bataji daɗin amsar daya bata ba,amma saitayi murmushi tace "to agaisheta "ta faɗa tana kallon Islam.
Wacce tayi kasaƙe tana kallon Aslam ɗin.sosai taji tausayin yar tata ya kamata,dan abinda ba dadi sam.
"Mommy na wuce saina dawo"Aslam ya fada yana kallon mommyn sa.
"To Aslam ka gaidamin da ita sosai,da mommynta"ta fada tana cin apple.
Da mamaki Islam ta kalli mommy,kenan da saninta ma Aslam din zai tafi zance?
Bata gama wannan mamakin ba taji granny na faɗin"yarinyar kirki mai kunya ba,nima kace Ina gaisheta sosai,sai mun zo"
To kawai Aslam ya iya furta wa dan tuni yayi bakin ƙofa cikin sauri.
Kallon juna Islam sukayi ita da mahaifiyarta,wacce ke kallon yar Tata tun ɗazu cike da tausayawa.
Lumshe ido mommyn Islam tayi tana mai ƙoƙarin kwantar wa da yar Tata hankali tace"Islam baki nuna min dakin naki ba fa !maza tashi muje ki nuna min"ta faɗa tana kamo hannun Islam ɗin.wacce ke zaune kamar butun-butumi.
Binta kawai Islam keyi amma zuciyarta kwata -kwata bata tare da ita.
Su granny kuwa sai hirar Husna suke da yaba halinta.

Muje zuwa.

Mrs babi ce
Anty mammy.
[10/24/2022, 11:41 AM] Abk: 69/70
Suna zuwa part din su Islam,mommyn ta ta zaunar da ita akan kujera,kallonta tayi cike da tausayawa,itama Islam kallon mommyn nata takeyi, tana ji kamar ta kurma ihu.
Cikin kwantar da murya mommy ta fara magana tana shafa kan Islam.

"Islam ita rayuwa da kike gani a sannu ake bin komai,kuma ba duk abinda mutum ke so yake samu ba,ki zamo mai juriya da kawaici akan dukkan al'amuranki,sai kiga kinci ribar abun nan gaba,kada ki bari wani abu ya sanya kiji haushin mijin ki ko yaya ne,yana da dama da ikon yin duk abinda yake so,domin addini ya bashi wannan damar.
Ko menene zai faru kada ki damu kanki, kiyi ta addu'a komai yayi zafi maganin sa Allah,kuma idan kika mikawa Allah lamarin ki,zakiga nasara arayuwarki"mommy ta kai ƙarshen zancenta tana mai kallon Islam.
Ahankali Islam ta sauke

Please Login or Register in order to submit comment