Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na biyoka inda kake kwance ko?nida kai waye ya fara kwanciya akan gadon?saika buɗe idonka kaga a inda kake kwance,kai dai kawai ka biyoni kan gado kana son amfana da jikina,shine zaka kama borin kunya,kuma nikam bazan taɓa amincewa da kai ba ehe"cewar Islam itama cikeda jin haushi.
Cikin hanzari Aslam ya kunna hasken dakin,mamaki ne sosai ya kamashi,ganin da gaske akan gadon yake,to yaushe ya dawo kan gadon?ko dai aljanu ne suka dawo dashi?shidai iya sanin sa bai dawo kan gadon nan da kansa ba. Da sauri ya juyo yana kallon Islam,wacce take kallonsa cikin yanayi na harara.
"Yaushe na dawo kan gadon nan?ko dai kece kika dawo dani?saboda kina son na taba miki jiki kiji daɗi,Ni kuma ki barni cikin azaba ko? muguwa kawai"
Ya fada yana sauka daga kan gadon cike da ɗan jin kunya,dan ya fahimci tabbas shi da kansa ya dawo kan gadon.kai tsaye toilet ya shige yayi wanka cikin sauri dan tuni gari ya fara haske,anan cikin dakin ya shimfida sallaya ya tada sallah.
Tashi Islam tayi itama tana turo baki ta nufi toilet tana faɗin "haka kawai mutum yana zamansa anzo za'a takurawa rayuwarsa da wani taɓe taɓen jiki"ta faɗa tana shigewa toilet.yana jinta dan da ƙarfi ta fadi hakan.
Alwala ta dauro tare da fito ta zari yafi zatayi salla.
Cikin tsawa Aslam yace"ke!!!ahaka zakiyi sallar?saboda ke wawiyace ?"
Harara ta balla masa kafin tace"to ayaya kake so nayi?"ta faɗa tana watsa hannu.
"Bayan kin gama lallatseni kinji dadi kuma saikiyi salla ba tare da kinyi wanka ba?saboda ke kikafi kowa ko?"ya fada yana hararar ta.
Turo baki tayi kafin tace"Allah ya kiyaye,Ni ba wani daɗin dana ji bare nayi wanka,kai dai dakajin ai kayi "ta faɗa tana turo baki.

"Ai Ni lafiyayye ne shiyasa idan ma naji daɗin,amma ke da yake dutse ce shiyasa baki jiba, saidai ƙoƙarin turomin wannan manyan breast ɗin naki da kike da sunan in taɓa miki su"Aslam ya fada idonsa akan Islam.

Buɗe baki Islam tayi da zaro ido, kafin tace"yaushe na turo maka ka tabamin?wllh kaji tsoron Allah,Ni ina ruwana da wannan abun da zan wani ce ka tabamin,kuma wllh niba dutse bace,kamar yadda kake lafiyayye nima haka nake"ta faɗa tana juya ido tare da murguda baki.
Kallonta Aslam Yayi cike da jinjinawa ƙuruciya irin ta Islam,kafin yace "oho dai koma menene wllh saikinyi wankan tsarki kafin kiyi salla,ɗan karya kike kice min ba abinda kikaji,yadda kike ta min shishitu da nishi kuma kice bazakiyi wanka ba"ya fada yana mai tsare Islam da ido.
Ƙara turo baki Islam tayi,kafin ta jefar da mayafin ta nufi toilet,Dan kuwa gaskiyar Aslam ne lokacin da taje yin alwalar pant dinta sai floshing ɗin sa tayi,saboda yadda ya jike,sai abin ya bata tsantsani.
Wankan tayi tana ta mita kafin ta dauro towel ɗin Aslam,ƙato ta fito.
Koda ta fito bata sameshi adakin ba,dan haka doguwar jallabiyar alama ta sa, sallar tayi kafin ta ɗan shafa mai da turare,sannan ta ta cire rigar ta maida towel ɗin,komawa kan gadon tayi tare da kwanciyar ta.

Aslam kuwa bayan ya idar da sallar,motsa jiki ya fita,daga nan ya wuce part din mommy Dan ya gaisa da su.

Sai wajen bakwai ya dawo part din nasu,kwance ya ganta akan gado tana barci,tsabar tsiya irin ta Islam daga ita sai wannan towel ɗin ta kwanta,gashi duk ya tattare ya koma cinyar ta.kawar da kansa yayi tare da shigewa toilet ,wanka yayi sannan ya fito,bargo ya ja ya lulluɓe jikin Islam dashi yana hararar ta,dan idan yana ganin ta ahaka ,bazai iya komai ba,gani yake da gangan take wasu abubuwan ma.
Haka dai ya shirya cikin sauri ya fito falo,nan ya samu an kawo musu abinci,dan haka ya zauna yaci ya koshi,sannan ya ɗan kishin gida akan kujera,nan da nan shima barci yayi gaba dashi.

"Mommy please kuyi wani abu da wuri,wllh zuciya gab take da tarwatsewa,ina son Aslam,Ina ƙaunar sa kuma kunfi kowa sanin haka,amma kuka ƙiyin wani abu har saida ya auri wata, wllh mommy komai na iya faruwa dani idan aka kara daukan lokaci ban mallaki Aslam ba"husna ke wannan maganar cikin zubda hawaye,sam ta kasa samun nutsuwa tun lokacin da batun auren Aslam ya zo gareta,dan taci burin auren Aslam,kuma ta sanar da Daddyn ta shi take son aure,sannan yayi mata alƙawarin yin magana da Daddyn Aslam ɗin akan batun auren nasu.kawai kuma sai jin daurin auren sa tayi.
Cikin sigar rarrashi,mahaifiyar Tata ke share mata hawayen,kafin tace"husna nasha faɗa miki ki daina damun kanki akan batun Aslam,aurene kamar kin aureshi kin gama,koda baya so,akwai Abinda nake jira ne,kawai ki zubamin ido,nayi miki alƙawarin ba abinda zaki nema cikin duniyar nan ki rasa"mommyn Husna ta fada cike da yaƙini.
Rungume mommyn nata Husna tayi cikin darinyar kuka tace "na sani mommy na,nasan Indai kina duniya bani ba shan wuya,mommy ki haɗashi da bokan ki,ta yadda zai ji ba wacce yake so aduniya sai ni"Husna ta fada cikin ɗoki.

"Ki sa aranki,sai Aslam ya soki kamar ransa,ke dai abinda nake so dake ki daina sa damuwa cikin ranki,ki kwantar da hankalin ki kawai"cewar mommyn nata.
"To mommyna"Husna ta fada cikin farin ciki dan tasan mommyn nata sarai.

Koda dare yayi Aslam,kin shiga ɗakin yayi,ya tafi can ɗayan dakin ya kwanta,saidai sam barci ya gagareshi, haka yayi ta juyi akan gado,ƙarshe dai ba yadda ya iya dole ya dawo dakin da Islam ke kwance haka ya haye kan gadon ya juya mata baya. Kusan minti ashirin da kwanciyar sa amma ya kasa barcin,sai tsaki yake ,dan ji yayi idan bai rungumi Islam ba bazai iya barcin ba.cikin haka ne kuma Islam tayi juyi tare da rungumeshi ta baya.
Wani ɗan zabura yayi dan bai zata ba kawai yaji ta rungumeshi.
Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da juyowa ahankali ya janyota kan ƙirjinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana jin kamar wanda aka cire masa damuwa.hannunsa akan mazaunan ta yana shafawa haka barci yayi gaba dashi.

Asuba nayi kuwa yayi saurin tashi ya bar ɗakin, dan kar Islam ta kamashi.
Karfe bakwai Islam ta gama shirin ta na zuwa makaranta,fes da ita sai ƙamshi take.ta fito zuwa falon nasu,inda Aslam ke cin abinci.zama tayi tare da sanya hannu ta ɗauke tea ɗin daya ke sha ta fara kurba,Binta yayi da ido yana kallonta,baice mata kala ba,dan yasan neman magana take.wani kofin ya ɗauka ya haɗa wani tea ɗin ya fara sha.
Har suka gama karyawa ba wanda ya kula wani cikinsu.
Shiya fara mikewa yace "kiyi sauri ki gama ina jiran ki amota"yana faɗin haka yayi waje.

Hararar bayansa tayi tana mai faɗin"ji yadda yake magana kamar wani boss,waishi adole irin mijina ɗin nan ko?hmmm zakayi bayani ne yaro"ta faɗa tana ajiye kofin hannunta.nan gurin ta bar kayan da sukaci abincin tayi ficewar ta.saida taje lambu taga janbu,dan akwai kofar da zata kaika lambu ta cikin part ɗin nasu.farfajiyar gidan ta fito bayan ta je gurin su mommy .
Yana cikin mota azaune fuskarsa aɗaure sai tsuka yake,dan ya gaji da jiran ta.

Cikin takun ta mai daukar hankali ta nufi motar tashi.tana zuwa ta bude gidan baya ta zauna.kamar wata Hajiya.
Haushi ne ya ƙara kama Aslam,yace "dalla malama fito ki dawo gaba,koni drivern ki ne?ya fada ahasale.
Cikin gadara Islam ta ce"kaga malam,karka min ihu ai ban tilasta ka saika kaini makaranta ba,kai ka gadama,dan haka saika zubamin ido kawai,Ni anan nayi niyar zama "ta faɗa tana wani fari da ido.
Afusace Aslam ya buɗe motar tare da fitowa.inda take ya zagayo ya buɗe,fincikota yayi da ƙarfi ya fito da ita ya bude gaban motar sa ya jefata tareda ƙullewa.
Da ƙarfi yana motar yana huci.
"Wllh idan ka karya min hannu ba yarda zanyi ba saina rama"Islam ta faɗa cikin raunin murya kamar zatayi kuka.
Banza yayi da ita har suka isa makarantar .
"Fita"ya fada akausashe.
Banza tayi dashi kamar bata jiba,kuma taki fita.
Kallonta yayi ya kara maimaitawa "fita nace"nan ma tayi masa shiru tana turo baki.
Yasan halin Islam sarai,idan baiyi mata da gaske ba saita ɓata masa lokaci,kuma akwai inda zashi.
"Wllh idan baki ficemin daga mota ba,zanyi maganin ki nasan abinda kike so,saboda jiya banzo nayi miki ba ko?"ya fada yana ɗan buɗe idonsa.
Sam Islam bata gane manufar sa ba,dan haka cikin tsiwa tace "tunda ka gane abinda nake so,ai saikayi min,amma wllh kasan nima ba gyale ka zanyi ba,dan ban.....
ina kafin ta ƙara sa kawai taji Aslam ya janyota jikinsa tare da manna bakinsa kan nata.
Zaro ido Islam tayi waje,dan sai yanzu ta fahimci abinda yake nufi,cikin sauri take ƙoƙarin tureshi amma ta kasa, kissing dinta kawai yake cikin kwanciyar hankali,nan da nan jikin Islam ya kama rawa,ta kasa koda motsi,sai lumshe ido da tayi tana karbar sakon Aslam,saida yayi mai isar sa kafin yayi ta maza ya zare bakinta daga nata,gaba ɗaya baya sukayi tare da jingina da jikin kujera idanunsu alumshe.
Ahankali Aslam ya buɗe idonsa tare da kura mata ido,sosai tayi masu akyau,lips ɗin ta sai sheƙi yake.
"Ya ?hakan yayi miki ko kina buƙatar kari ne?"Aslam ya fada cikin ƙaramar murya dai-dai saitin kunne islam.
Wani yummmmm Islam taji tsikar jikinta ta zuba,da sauri tayi baya,tare da buɗe motar asukwane tayi waje.bayan ta zari jakarta,da sauri tayi cikin dalibai bata ko waiwaye.

Murmushi Aslam Yayi tare da ƙureta da ido,har ta bacewa ganin sa.
Haka kawai yake jinsa cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa.
Cike da kasala yana motar sa ya bar makarantar.

Muje zuwa.[10/12/2022, 1:21 PM] Abk: ____________Murmushi Aslam Yayi tare da ƙureta da ido,har ta bacewa ganin sa.
Haka kawai yau yake jinsa cikin farin ciki marar misaltuwa.kunna motar yayi cike da kasala, tare da barin harabar makarantar.
islam kuwa kai tsaye ta wuce gurin assembly,bayan an kammala komai aka fara shiga aji,ita kuwa kai tsaye ta wuce ɓangaren yan primary dan duba A'isha.cikin class ta Sami yarinyar ana musu karatu,dan haka daga waje ta tsaya tare da daga mata hannu,dan A'isha kusa da kofa take zaune,cikin farin ciki yarinyar itama ta dagawa Islam hannu tana dariya.
Alamu Islam tayi mata na tayi karatu sosai zata dawo anjima kafin tayi mata bye bye ta juya bangarensu.
Tana shiga class ɗin wata ƙawar hanan mai suna maryam,ta buga uban tsaki tana mai faɗin"haka kawai mutum ba dan kowa ba sai faɗin rai,wllh mukam ba'a isa anuna mana jiji da kai ba,dan munsan komai"ta faɗa cikin daga murya tana kallon islam.haka take mata kullum,burinta kawai Islam ta kulata dan haushin Islam take ji,saboda tafisu ƙoƙari.
Islam kuwa, bata kula kowa cikin ajin nan,dan gaba dayansu taga masu rainin hankali ne,gasu da son dizga mutum,ita kuma bazata dauki rainin hankali ba,yanzu zata balla yarinya ba ruwanta.dan haka duk da taji abinda Maryam ta faɗa sai tayi kamar bata jiba,ta nemi guri tayi zaman ta.
Dariya suka kwashe da ita wata daga cikinsu tace "kai Maryam,ke matsala ta dake tsoro ne dake,inba haka ba kifito fili ki fada mana da wa kike "
Cikin isa da gadarar rashin kunya Maryam tace "wa zanji tsoron?yar riko agidan mutanen ? Allah ya kiyaye,to bari kiji da waccan Islam ɗin nake saime?"ta faɗa tana nuna islam.
Runtse ido Islam tayi cike da jin wani irin zafi cikin zuciyarta.lallai yau zata koyawa yarinyar can hankali,zata san wacece Islam,ba tsoron su take ji ba.
"Hahhhhh lallai Maryam kin cika wallahi,ai nayi tunanin tsoron faɗin suna kike"yarinyar dazu ta faɗa.
"Ai kinsan ni Maryam bana jin tsoron ko wanne shege makarantar nan,wllh idan mutum yayi min wani gani_gani yanzu zansa ayiwa yarinya tsirara atiti kuma wl......

Kau !kau!!kau!!! Kake jin ƙarar saukar maruka akan kumatun maryam,wanda ya dauke mata ji da gani na wasu ƴan daƙiƙai.
Ihu ta kwalla da ƙarfi tana dafe duka kumatun ta "wayyo na shiga uku an watsamin acid akumatuna,na shiga ukuna Ni Maryam, wayyo Allah na"abinda Maryam ke faɗi kenan cikin ihu da razana,dan marin a bazata yazo mata.
Cakumo wuyan rigarta Islam tayi tare da kwara kanta da bango nan take jini ya fara zuba daga hancin maryam.islam ta shaƙar mata wuya,cikin muryar gargadi ta fara magana"dan ubanki Ni ba sa'ar yinki bace,nafi ƙarfin ƙaramar tsagera irin ki,sai manyan kwari,kada tsautsayi yasa kice zaki shiga gonar Islam,zaki sha wahala matuka arayuwarki,banza shashasha mai siffar karuwai"cewar Islam tana hankada Maryam,
Cikin masifa wannan ɗayar yarinyar ta taso tana mai cewa islam"ke Islam meye hakan?ko kasheta kike sonyi ne?dallah malama kauce kiba mutane guri"
Ai afusace Islam tayi kan yarinyar nan tana duka ta ko ina.duk yadda a kaso rabasu, sam Islam taki yarda sai dukan yarinyar take kamar ta sami jaka.
Ajin ya cika danƙam da yan kallo,wasu suna jin daɗin dukan da Islam tayiwa su Maryam,dan sun addabesu dama cikin school ɗin,wasu kuma suna jin haushin Islam ɗin.
Saida principal yazo da sauran malamai kafin aka iya raba faɗann nan.shima da gyar Islam ta saki yarinyar,gaba ɗaya ta fasa mata baki da hanci,Maryam kuwa dama tuni jini ke zuba daga bakinta da hancinta.
Kai tsaye principal yace su biyoshi office.
Koda sukaje office faɗa sosai principal Yayi musu, kafin ya koma kan Islam yayi ta zaginta,sannan yace sajant yayi mata bulala ashirin masu zafi.
Haka sajant ɗin nan ya kama dukan Islam,cike da mugunta,dan dama yana fatan Allah ya kawo su wannan ranar yana matuƙar jin haushin Islam.
Gaba daya hannun Islam da bayanta ya kumbura,bayanta yayi raɗo-raɗo da shatin bulala,hannunta kuwa wani gurin ma ya fashe.sannan principal ya sata share wani guri mai girma,da gyar take iya daga tsintsiyar saboda yadda hannunta ke mata ciwo.tana gama sharar ta dawo,nan ma saida suka gama ci mata mutunci sannan aka sallame ta,tsabar takaici da ciwon rai,na rashin adalci da aka mata,bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba,can bayan class ta koma tana kuka sosai.tana cikin wannan kukan yaji an dafa kanta.da sauri ta juya ɗan ganin ko waye,cike da ɗoki da mamaki ta sake fashewa da kuka,har da shashsheka.
Ba kowa bane ya dafa ta face malaminta, tayi kewar sa fiye da tunani,rabon da yazo inda take tun lokacin daya bata shawarar auren Aslam,tayi ta tunannin Ina ya shiga ?ko shikenan ta daina ganinsa?
Murmushi yayi mata tare da cewa"kiyi hakuri Islam,haka rayuwa ta gada,yau fari gobe tsumma,ya zama dole ki koyi hakuri da kawar da kai akan abubuwa,ba komai bane idan akayi maka zaka ɗauki mataki akai, Allah yana son mai hakuri"ya fada yana kallon islam.
Jinjina kai Islam tayi,so take ta tambayeshi ina ya shiga?amma ta kasa yin magana kamar kullum.
Murmushi yayi yace "nasan kina son kice Ina na shige kwana da yawa bana zuwa gurin ki ko?
Da sauri Islam ta jinjina kai .
"Wani gagarumin aikine ya sameni, Islam,yanzu haka nazo inyi miki sallama ne sai kuma Allah ya dawo dani,ki rike mijinki da gaskiya,kiyi masa biyayya,sannan kizama mai hakuri akan komai, Allah yayi miki albarka,Ni zan tafi saina dawo,amma zan dauki lokaci mai tsawo kafin dawowa ta,kizama jaruma mai fuskantar dukkan ƙalubalen ta"yana kaiwa nan yayi mata murmushi tare da bacewa.
Ta jima agurin tana share hawaye kafin ta tashi ta koma class.lokaci ɗaya zazzaɓi ya rufeta sai karkarwar sanyi take,su Maryam anyi musu dressing agurin da sukaji ciwo,suna zaune sai hararar inda Islam ke zaune ta kifa kanta suke.hanan kuwa tana mai gargaɗin su akan su kiyayi Islam,dan tun kafin su fara tsokanar ta saida tayi musu gargaɗi amma suka ƙi jinta.
Har aka tashi Islam na kwance bata ɗago kanta ba,duk malamin daya shigo saidai yayi karatunsa ya fice,dan Islam bata fahimtar komai.
Gaba ɗaya yan class din har Hanan haka suka fice suka bar Islam kwance akan desk.ita kuwa Aisha tana can taki tafiya tun ɗazu tana jiran zuwan Islam,dan tasan lokacin tashin su nayi,Islam zata fito suyi sallama,kafin Aishan ta hau mota su tafi.to yau taji shiru,tun ɗazu drivern ta yazo daukar ta amma taƙi tafiya sai taga Islam.
Tana ganin an tashi seniors ta fara murna tana dariya saidai gaba ɗaya wucewa suke bataga Islam ba.cike da damuwa akan fuskarta ta nufi ajin su islam,leƙawa ta farayi tana duba Islam,aikuwa can ta hangota kwance akan benci,da sauri ta karasa cikin class din tana kiran "anty! Barci kikayi ashe?antashi tun ɗazu ina ta neman ki, tashi mu tafi kowa ya tafi gida"A'isha ta faɗa tana dafa islam.jin Muryar A'isha ya sanya Islam ɗago da kanta,wanda idanunta sun kumbura sunyi jajur dasu. Murmushin karfin hali tayi,tana shafa kan Aishan, jikinta sai rawa yake ta mike tare da ɗaukar jakarta,sannan ta riƙe hannun Aisha suka fito.ahankali suke tafiya,dan Islam ji take kamar zata faɗi jiri ne ke neman kayar da ita.
Kai tsaye bakin motar da ake ɗaukan A'ishan ta kaita,sannan tace cikin Muryar marasa lafiya"Baby kije gida kinji sai gobe,ki gaida mommy ki"ta faɗa tana ɗagawa A'isha hannu.
"Anty yanaji muryarki tana son yin kuka?ko wani ne ya dake ki?A'isha ta faɗa tana wani gwabe fuska kamar zatayi kuka.
Girgiza kai Islam tayi kafin tace "kinga Ni ba wanda ya dakeni mura nake bye"ta faɗa cikin murmushin ƙarfin hali.
Haka drivern yaja motar suka bar makarantar.
Ahankali ta juya da nufin samun guri ta zauna,dan taga Aslam bai ƙaraso ba, saidai nata juyawa taji jiri ya debeta, luuuuu tayi zata faɗi kasa,saidai kafin ta kai ga faduwar akayi saurin tare ta.
Ahankali Islam ta buɗe idonta dake rufe, dan ganin wanda ya tare ta,ido hudu sukayi da Aslam,Yana kallon ta cike da tsoro,dan zuwansa kenan ya hango ta tana ƙoƙarin faduwa ta dafe kanta,shidai bazai ce gata yadda yayi ba,kawai ya tsinci kanshi ne a gurin.dan ji yayi zuciyar sa ta buga da mugun ƙarfi tsoro ya ziyarci zuciyarsa.
Kallon juna sukayi na tsawon lokaci,tana riƙe ahannunsa,gaba ɗaya yaga tayi wani iri,da alama ma kuka tayi sannan ga jikinta nan zafi kau.cikin sanyin murya mai taushi yace "me ya sameki?maimakon Islam ta bashi amsa, sai ji yayi ta kankameshi tare da sakin kuka mai ciwo.
Sosai jikin Aslam Yayi sanyi,dan Islam bata taɓa masa irin hakaba, lallai duk abinda ya sata wannan kukan babba ne.
Rungumeta yayi shima yana shafa kanta."is ok ba gani ba ,kiyi shiru ai gani nazo ina tare dake"ya fada yana shafa kanta,kafin ya nufi mota da ita.
Koda ya zaunar da ita kan kujerar, kuka take marar sauti.haka ya ja motar suka nufi gida.ta can daya kofar sukabi zuwa part ɗin su, gaba ɗaya zuciyar sa ba daɗi,tausayin Islam kawai yakeji ta ko ina ajikinsa.haka ya kamota suka shiga cikin Falon nasu,suna zuwa ta kwanta tare da kanƙame jikinta,dan sanyi takeji sosai.zama yayi kusa da ita yana shafa kanta cikeda tausayawa yace"sannu kinji ?bari na baki magani zazzabin zai sauƙa"ya faɗa yana kamo hannunta.
Ɗan ƙara Islam ta saki tana kwace hannun dan kuwa ciwo yake mata.da sauri Aslam yakai kallonsa kan hannun nata.
Zaro ido yayi cikeda tashin hankali yana kallon yadda hannun ya kumbura yayi jajur ga wani gurin afashe.
Da ƙarfi yace "WHO did this to you?"ya fada cikin tashin hankali da ɓacin rai.
Kallon sa Islam tayi cikin hawaye,amma ta kasa magana.
Lumshe ido Aslam Yayi,yana jin zuciyar sa kamar zata fashe ,wane mahaukaci ne yayi mata wannan dukan da har ya fasa mata hannu?wllh ko waye yau saiya yabawa aya zaƙinta.
Buɗe ido yayi ahankali da ƙoƙarin kawar da ɓacin ransa, ahankali ya kamo hannun nata yana kallo,wani irin zafi yaji cikin zuciyar sa,kallonta ya sake yi ya ce"ISLAM ! ya furta sunan nata cikin tashin murya.
Kallonsa tayi itama da kunburarrun idanun ta."meya sameki?waye yayi miki wannan dukan?me kikayi masa?"ya fada cikin sanyin murya.
Hawayene ya shararo daga idanun Islam kafin ahankali tace "kullum sai sun tsoakane Ni,bana kulasu,shine yau suke cemin yar riko mai jiki dakai,nikuma na gaji da yadda suke tsokana ta shine na dakesu,principal yasa wannan shegen sajant ɗin yayi min duka gaba ɗaya ya fasa min baya da hannu"Islam ta karasa cikin yanayi na shagwaba.
Ƙura mata ido Aslam Yayi tunda ta fara maganar ta har ta kai ƙarshe,wannan wane sankaran ne ?wane marar hankalin ne yayi gangancin dukan islam?matar sa,wacce igiyoyin auren sa ke kanta,koshi bai dake ta ba dai wani wawa?lallai zai gane shi ƙaramin mahaukacine.
Hannu yasa ya tada Islam zaune,sannan ya cire mata hijabin dake jikinta,ta tare da wani bata lokaci ba ya zuge zif ɗin rigar ta ya sauke kasa.
Da sauri ya runtse idanunsa sakamakon yadda yaga bayan na Islam yayi ruɗu -ruɗu duk ya farfashe.
Wani irin nishi yake cike da tsantsar bala'i da ɓacin rai.
Mikewa tsaye yayi cikin matsanancin ɓacin rai yayi waje da sauri.
Islam kuwa maida rigar ta tayi tare da kwanciya .
Kai tsaye Aslam ya hau motar sa ya figeta da gudu,Allah ma yasa mai gadi na kusa yayi saurin buɗe mata get.kana ganin yanayin da Aslam ya fita kasan akwai bala'i
Kai tsaye ya nufi makarantar su Islam.

Masu karatu nidai ba ruwana wllh,nayi nan.

Anty mammyn kuce.
[10/13/2022, 12:54 PM] Abk: ___________ Kana ganin Yanayin da Aslam ya fice da motar kasan akwai bala'i.
Kai tsaye makarantar su Islam ya nufa cikin wani mahaukaci gudu kamar zai tashi sama.ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi gaban sajan ɗin nan,zuciyar sa banda tafasa ba abinda take.
Cikin Sa'a kuwa yana zuwa ya samu gaba ɗaya malaman suna nan,dan kuwa suna meeting me yau.ko rufe motar baiyi ba ya fito cikin fusata,office ɗin principal ya nufa kai tsaye.aikuwa gab da zai shiga,saiga sajan ɗin nan ya nufoshi da buta ahannunsa,ɗaya hannun kuma riƙe da zanbaɗediyar dorina.
"Malam ina zaka ne?kada ka shiga principal suna cikin meeting ne, saidai ka jira su fito"cewar sajan kenan yana ƙarasowa da ɗan gudu,dan kar Aslam ya shiga office ɗin.
Cakk Aslam ya tsaya tare da juyowa,kallon sajan ɗin yayi tun daga sama har ƙasa,wani ƙazamin kucaki dashi,dagani wannan ko aji bai taba shigaba,amma shine zai kama masa mata yayi mata irin wannan bahagon dukan.
Cikin fusata Aslam ya nufi sajan ɗin yana faɗin "kai waye?waye kai cikin makarantar nan?meye matsayin ka?"ya fadi haka ne dan tabbabar da cewa shine sajan ɗin,ɗan karya hukunta wanda baisan komai ba.
Cikin washe baki sajan ɗin yace "ai matsayina makarantar nan shine,cin uban tangararrun yara,waɗan da basa jin magana,dan ko dazu saida na zane wata fitinanniyar yarinya,na farfasa mata baya da hannu...
Wani wawan mari da Aslam ya ɗauke sajan dashi, saida ya kusan hantsilawa,bai gama dawowa cikin hayyacin sa ba,yaji saukar wasu maruka, ba jiran wani dogon bayani Aslam ya fara dukan sajan kamar an aikoshi.gaba ɗaya sajan ya rikice ya dimauce, dukan shi kawai Aslam keyi ta ko ina,shikuma yana kwance ya kasa koda kare kansa.
Ganin Aslam na neman kashe shi ya sanya shi fara ihu da iya karfinsa.
Shaƙar wuyansa Aslam yayi ya haɗashi da bango yana faɗin"kasan ko wacece yarinyar daka daka?kasan irin haukar da kayi?kai jahilin inane zaka mata wannan dukan kamar wani ka sami jaka?wllh yau saina daure ka,zan ga uban da ya sanya ka wannan haukar.
"Na tuba ranka ya dade,ayimin afuwa,wllh bazan sake ba kayimin rai,wayyo Allah principal ku fito ku ceceni, zai kasheni"abinda sajan ɗin ke faɗi kenan cikin azabar shaƙar da Aslam Yayi ma.
Da gudu Principal da malamai suka yi kansu,ganin yadda sajan ke shure shure yana neman mutuwa. Shikuwa Aslam ya shaƙar masa wuya sosai banda huci ba abinda yake.
Dagyar suka kwace sajan daga hannu Aslam,sai dai zuwa lokacin tuni sajan ya suma.
Cike da ɓacin rai Aslam ke tambayar Principal dalilin da yasa aka yiwa Islam wannan dukan?
Shidai Principal haƙuri kawai yake ba Aslam,Dan ya tsorata da yanayin na Aslam,yadda ya fusata.
Da gyar Principal ya shawo kan Aslam,akan karya kai kara shima saida ya kira daddy da baya ƙasar,kafin ya ce Aslam ya bar maganar,sannan ya haƙura bayan ya buga musu gargaɗi.dan da cewa yayi ma zai sauya mata makaranta,daddy ne ya hana.
"Wllh !wllh!!wllh!!! Ko kallon banza ban amince asake mata cikin wannan makarantar ba,bare baƙar magana ko ta kai ga duka,dan ba ankawo ta bane dan wasu ƙartin banza su daketa, kunci Sa'a daddy ya hanani,da saina kai wannan makarantar kara"Aslam ya fada cikin fushi yana barin gurin.
Har zuwa wannan lokacin daya yiwa sajan mugun duka baiji zuciyarsa tayi sanyi ba.gani yake bai ramawa Islam dukan ta ba.haka ya dawo gida zuciyarsa ba daɗi.inda ya bar Islam nan ya dawo ya sameta.tana kwance idonta arufe,zama yayi kusa da ita yana kallon ta cike da tausayi,ji yake kamar ya dawo da zazzabin zuwa jikinsa.
Ahankali ya sanya hannunsa ya taba wuyanta.har zuwa lokacin jikinta zafi sosai.
Buɗe ido tayi ahankali ta kalli Aslam kafin ta maida idon ta ta rufe,sai juya kanta take,da alama dai tana jin jiki.
Tashi yayi ya nufi cikin daki,jimm kaɗan ya fito ɗauke da towel, sannan ya shiga kitchen ya ɗauko wata yar roba mai fadi,ruwa ya dauko mai sanyi amma ba sosai can ba cikin firji ya zuba cikin robar.
Dawowa yayi ya zauna kusa da ita.
Hannunsa

Please Login or Register in order to submit comment