Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu da wani nisa da juna .
Daidai lokacin da Aslam ya tura ƙofar falon.idonsa ya sauka akan husna,wacce ke zazzagawa mommynsa rashin kunya tana faɗin"wllh ko kina so ko bakya so saina koma dakina,dan ba wanda ya isa ya rabani da mijina, tsabar mugunta ke taki yar tana can agidanta ,shine ni kika kashemin nawa auren,wllh ki sani kamar yadda kika sa aka sakeni kema sai nayi silar da zaki bar gidan nan kuma..... Wani irin yunkuri Aman yayi cikin zafin nama da mugun bacin rai,ya fizge rikon da mommy tayiwa hannunsa,ya tunkari Husna gadan -gadan.
Saidai kafin ya karasa inda husnan take ,sai ihunta kawai suka jiyo,gaba ɗaya hankalinsu yayi kanta,dan ganin abinda ya sanyata ihun nan.
Islam suka gani ta maƙure Husna ajikin bango,ta shaƙe mata wuya da hannunta daya,yayinda dayan hannun kuma take dukan bakin husnan dashi.

Aslam ma cikin zafin nama da ɓacin rai ya ƙaraso cikin Falon,dan tuni Islam ta rigashi shigo lokacin da taji abinda Husna ke fadawa mommy....

Kuyi hakurin jina da kukayi shiru kwana biyu,abubuwa da dama sun faru dani,amma alhamdullah yanzu komai ya dai daita.
Ina fatan zakuyi min afuwa🙏🙏🙏

Luv You all guys 💞

Mrs babi ce
[12/23/2022, 9:05 PM] Abk: 99/100
______________Aslam ma cikin zafin nama da ɓacin rai ya tunkari Husna,saidai ganin yadda Islam ke wassafa ta yasashi tsayawa tare da harɗe hannayensa aƙirji.
Kallonsu kawai yake yana jin Islam na ƙara burgeshi sosai,sannan yana jin tsanar Husna na mamaye zuciyarsa .
"Ashe rashin mutuncin naki ya kai kina zagin Mommy?kinyi ƙarya wllh saidai idan bana gurin,amma baki isa ki zagi babba agabana ba,wllh dole na koya miki hankali, Ni rainon dawa ce,bana daukar rainin yan iska irin ki"islam ta fada cikin huci.

Ita kuwa Husna sai zare ido take tana kawar da kanta daga bugun da bakinta kesha wajen Islam.
Ihu mommyn Husna ta kwalla tare da tunkude Islam da iya karfinta. Wanda hakan ya sanya Islam ɗin faduwa tare da buge hannunta jikin kujera. Da ƙarfi ta runtse idonta,ɗan jin yadda hannunta ya bugu sosai,ga wani radadi daya ziyarci hannun nata.
Da sauri Aslam ya dagata tare da kamo hannunta wanda ta bugu ajikinsa.
"Sannu bakiji ciwo ba sai ko?kinsan idan akace mutun ya ci kai ,to zai iya komai ma"saidai..ya fada tare da dan ja mata hannun .
Ɗago kai yayi tare da zuba idanunsa akan mommyn Husna wacce ta tallafi husnan dake kuka bilhakki,ga gefen bakinta afashe.
"Na shiga uku mommy ta fasamin baki,wllh bazan yarda ba saita biyani bakina shegiya mai ƙarfi kamar doki"Husna ta faɗa cikin kuka da asaranci.

"Banza ƙatuwar wofi yanzu Husna ki tsaya wannan yar yarinyar da haihuwar kaji kin haife ta,tayi ta mazge miki baki?Kamar ta samu giginya?wllh kinbani haushi "mahaifin Husna ke faɗin wannan maganar cike da jin haushin yadda yarinya karama ta kama Husna tana lodarta kuma agabansu,sannan ita ta kasa koda yunkurin kwatar kanta ne.

"To dazaka ce ta baka haushi,baka ganin shigar sauri tayi mata?wannan abun dama shiryayye ne,an shirya hakan tun kafin zuwanmu,amma wannan Shegiyar ta isa ta daki Husna koda wasa ma bare har taji mata ciwo"mommyn Husna ta faɗa itama cike da jin haushin mijin nata,na bayar da yar tasu da yayi gaban maƙiya,dan ita ta jima da sanin cewar husna bata da ƙarfi ko kaɗan sai tsabar kuri.

"Hehehehe Islam kinyimin dai dai wllh haka ake son dan halak, idan yaji ana cin zarafin iyayensa sai inda karfin sa ya kare,ku kuma maza-maza ku bar gidan nan,tun kafin. Mu naɗa muku na jaki wallhi"
granny ta faɗa tana wani dunƙule hannu kamar yar dambe.

"Wllh ba inda zamuje sai yan sanda sunzo sun kama mana ku,dan kuwa kun cutar damu,dole hukuma ta dau mataki,maza Alhaji ka kira yan sanda,ka sanar dasu cewar ga wasu ahali suna kokarin kashemu"mommyn Husna ta faɗa tana mai bashi umarni.
Aikuwa cike da bin umarnin nata ya dauko waya yana kiran yan sandan.
Ran mommy sosai ya ɓaci da irin wannan tozarcin da suke ƙoƙarin yi musu.kallon mommyn Husna tayi tana mai cewa"yanzu Hajiya yan sanda zaki kira mana?da mutuncin mu da komai?"
"Kwarai kuwa dole yan sanda suka ma ku wllh,dan bazaku ci banza ba mugayen mutane kawai.
Cikin ɓacin rai Aslam yace"Please mommy ki barsu,su kira sojoji ma ba yan sanda ba,ai ita hukuma ba mahaukaciya bace, da tunani suke aikinsu,ba cikin jahilci ba"ya fada yana mai kawar da kansa ransa abace.

"To takadari,marar kunya da tarbiyya,muna matsayin surukan ka kake neman zagin mu ko? Saboda baka san da'a ba,sannan ina son sanin dalilin sakin da kayiwa yarmu yanzun nan" mommyn Husna ta faɗa cikin gadara da isa.

Wani banzan kallo Aslam ya watsa mata,kafin yace "saboda bana sonta,bana ƙaunar ta,sannan bata da tarbiyya,bayan haka awancan lokaci saki daya nayi mata ko?ya fada yana mai dage gira guda daya kafin ya kalli husna wacce ta yi galala tana kallon Aslam din cike da fargaba.kafin ya dora da cewa" to kisani Ni Aslam na datse sauran igiya guda biyu ta aure dake tsakanani da ƴarki ,daga yau ba wata alaƙa ta aure atsakina da ita"
Aslam ya fada kai tsaye yana mai kallon cikin idon mommyn husna,wanda itama tayi saƙare tana kallon Aslam ɗin,mamaki,al'ajabi da kuma dana sanin faɗin maganar da tayi,sun dabaibaye mata zuciya.
Husna kuwa wani wawan ihu ta kwalla wanda yayi silar da daddynta ya shigo cikin Falon da gudunsa,dan yana waje yana yiwa yan sanda kwatancen gidan,kasancewar gidansu Aslam ba boyayyen bane yasa yan sandan suka gane cikin sauƙi.
"Meya faru kuma?sake dukanta akayi ko me?"mahaifin Husna ya fada yana mai zare ido.
"Wayyo Allah na,na shiga ukuna ,daddy ya sake sakina saki uku kenan wayyo rayuwata na shiga ukuna Ni husna,mommy kin cuceni kin lalata min rayuwa, kin rabani da mijina,meyasa kika faɗa masa wannan maganar ?gashinan ya sake sakina, wllh bazan yarda ba ,ba inda zani bazan rabu da shiba,wayyo Allah daddyna" Husna ta faɗa cikin kuka mai sauti tana yarfe hannu.
"Ahayye nanaye !!!Allah na gode maka,Asalamu ka cika ɗa, yau ka nunawa tsagerun nan kana son iyayenka.wllh kayi dai-dai,Allah yayi maka albarka.
Maza afitar mana daga gida gayyar
tsiya"granny ta fada cikin nishadi da annashuwa.

Hanan ma ba karamin dadin wannan sakin taji ba,shikenan sun yarda kwallon mangwaro sun huta da ƙuda.
Aman ma sosai yaji yayan nashi ya burgeshi,dan sai jinjina kai yake yana murmushi.
Islam kuwa kallon Aslam tayi da ɗan marairaita afuskarta,shikuwa ya ɗan lumshe mata ido alamun rarrashi.
Kafin kowa ya ƙara cewa wani abu,saiga jiniyar motar yan sanda yuyuyuyu!ta shigo farfajiyar gidan.
Wanda shigowar motar yayi dai -dai da shigowar motar daddy,ko farking baiyi ba motar Abban Islam ta Kunno Kai cikin gidan.
Cike da mamaki daddy ya fito daga motarsa yana tambayar yan sandan lafiya?cikin girmamawa sukayi masa bayanin ankirasu ne akan ana ƙoƙarin yin kisan kai agidansa, dan haka suka taho da gaggawa,kuma idan ba damuwa suna son shiga dan ganin abinda ke faruwa.

Ajiyar zuciya daddy Yayi,dan yasan komai,tunda ya kira hanan tayi masa bayani,saboda kasa daurewa yayi,gashi ya hadu da tsaiko akan hanyarsa ta dawowa gida .

Cikin kwarin gwuiwa daddy yace" ba damuwa zaku iya shiga"
"Wai yaya meke faruwa ne agidan nan?
Mommyn Islam ta faɗa cikin damuwa tana riƙe da hannun A'isha.
Kallonta daddy Yayi kafin yace wata yar hatsaniya ce tsakanin Aslam da surukansa,shine suka kira mana yan sanda"ya kai zancensa cike da takaici.
Zaro ido mommyn Islam tayi tana mai faɗin "yanzu yaya abin harya kai ga yan sanda ?"
Jinjina kai daddy Yayi yana mai faɗin"sam ban san Alhaji Musa zai iya min wannan tozarcin ba,da mutuncina da komai agari ya kiramin yan sanda?hmmmm ba komai,mushiga daga ciki Abubakar "daddy ya fada yana mai kallon Abban islam dake tsaye shima cikin mamaki.

"Kayi hakuri Alhaji, kasan mutanen yanzu sai ahankali,ba kowa yasan ya dace ba"cewar Abban Islam kenan suna mai nufar cikin Falon .

"Yawwa officers kun ƙaraso?ga masu laifin nan ku kamasu"Daddyn Husna ya fada yana nuna su mommy gaba dayansu.

"Cike da son gasgata muryar da kunnensa yajiyo masa yace "Alhaji Musa"
Da hanzari shima Daddyn Husna ya juyo dan ganin mai kiran sunan nasa,dan ya ba kofar baya .

Tsoro,mamaki,fargaba da kuma razani sune suka dirarwa Daddyn Husna lokaci ɗaya,sakamakon haɗa ido da Alhaji Abubakar da yayi.
Cikin rawar murya yace "Alhaji Abubakar,kaine kana raye dama ,baka mutu ba?Daddyn Husna ya fada cikin mugun tsoro da firgici.

"Ina nan da raina,Allah ya ƙaddara nida ahalina muna da sauran shan ruwa adoron duniya,sannna ya kubutar damu daga zalunci da cin amanarka,me nayi maka nida iyalina?me muka tsare maka wane ci gaba muka dakushe maka aduniya daka yi yunkurin ganin bayanmu"Daddyn Islam ya fada cikin yanayi dake nuna yana jin zafin abinda ya faru dashi abaya.

Cikin inda inda da in ina,Daddyn Husna ya fara kame kame yana faɗin"dan.... Allah kakkakayi hakuri Alhaji Abubakar,ka manta da komai,duk abinda ya faru abaya,sharrin shaidan ne,kuma Ni bance su kashe kuba, nace kawai su daukomin takarda ,amma kayi hakuri "Daddyn Husna ya fada yana haɗe hannayensa jikinsa sai rawa yake.

Gaba dayan falon yayi tsit,kowa sai kallon Daddyn Husna da Abban Islam yake,gaba ɗaya sun sanya su a duhu,domin basu fahimci me suke nufi da kalamansu ba.islam cikin ranta take faɗin kodai wannan shine mutum daya so kashe mu?
Maganar mommynta ce ta katse mata tunaninta.
Inda mommyn ke fadin
"Wai Alhaji kana nufin wannan shine Alhaji musan daya sanya a kashemu ta hanyar sa mana wuta? Mommyn Islam ta faɗa cike da mamaki .

"Kwari kuwa shine Alhaji Musa,abokin kasuwanci na,wanda ya biyewa son zuciya da eudin duniya,yaci amanata,ya turomin yan ta'adda har cikin gidana dan su kasheni nida iyalina.

Salati gaba dayan dakin suka dauka,kowa yana al'ajabi da mamakin rashin imanin Alhaji musa.

Mommyn Husna da Husna sunyi tsilli-tsilli.husna kuwa mamakin mahaifin nata take, bata taba zaton zai iya kashe mutum ba.

Kuka granny keyi tana tafa hannaye,"ohh,yanzu dama kaine kake kokarin kashemin ya da iyalanta?sannan ka turo yarka dan ta hana jikata sakat agidan aurenta?Allah ya toni asirinku annamimai yan sandoji,kuna dai ji da kunnen ku,dan haka ku kama mugu"
Tuni yan sanda suka yi kan su hunsa da nufin kwamushesu.
Kuka Husna keyi tana ƙanƙame mommynta,
Haka aka tusa ƙeyar su gaba dayan su har husnan zuwa folice station.
Mommyn Husna sai zage zage take tana fadin anyi musu sharri....

Muje zuwa.
[12/24/2022, 8:59 PM] Abk: 101/102
______________kuka sosai husna keyi tana ƙanƙame mommynta, ita bazata police station ba.
"Wayyo Allah Aslam ka taimake ni,Ni matarka kace,dan Allah karka bari su tafi dani na shiga uku"abinda take fadi kenan tana kuka wiwi tare da miƙawa Aslam hannu.

Shikuwa Aslam gaba ɗaya mamakin mahaifin Husna ya gama cika masa ciki,yanzu wannan mutumin rashin imanin sa ya kai har ya iya sanyawa a kona mutane da ransu? Lallai dan adam sai ahankali,mutane sam ba amana.yayi dana sanin auren yar wannan macucin maha'inci azzalumi,inda ya godewa Allah ma, da bai hada zuri'a dasu ba.
Wani ƙasƙantaccen kallo ya watsawa Husna,kafin yace "har abada bana fatan koda haduwa dake ahanya,bare wata alaƙa ta hadamu, karki ƙara kiran sunana domin na yanke duk wata alaƙa dake tsakanina dake,kuje ku girbi abinda kuka shuka acan Ni yanzu matata ɗaya ce kuma ita zataci gaba da kasancewa matsayin matata har abada domin aurena dake ƙaddara ce wacce ta riga fata"Aslam ya fada yana mai riƙe hannun Islam tare da nunawa Husna.
Ita kuwa Husna sai Ihun kuka take kamar ranta zai fita tana faɗin ba laifinta bane,dan Allah karya rabu da ita.haka aka fitar da Husna daga gidan zuwa motar yan sanda,

Mommyn Husna sai zage -zage take tana faɗin akyalesu,basu aikata komai ba ita da yarta,akama alhaji shine mai laifi.

Saida Dan sandan ya daka mata tsawa yana mai faɗin ta shiga taitaiyinta,su ba abokan wasanta bane,sannan tayi shiru.dan ta san hukuma ba wasa.
Gaba daya sun fito farfajiyar gidan suna kallon yadda ake kokawa da Daddyn Husna,kan shi bazai bi yan sanda ba,saidai ya taho amotarsa.su kuwa sunce bazasu kyaleshi ba,saiya bisu.

Daddyn Aslam kuwa sam ya kasa magana ma,dan cike yake da mamakin abokin nashi,yadda rashin imaninsa yakai ya iya kashe rai,ba daya ba harda na kananan yara Kuma ma ƙanwarsa ?

Ana ƙoƙarin tura Daddyn Husna mota ne,wayarsa ta shiga ruri, nan ya fara kokarin dauko wayar daga aljihunsa,saidai kafin ya dauko wayar,tuni Aslam ya zura hannunsa cikin babbar rigarsa ya dauko wayar.dan yana zargin wani abu akan Daddyn Husna game da harin da aka kaiwa daddynsa da Aman kwanaki wanda Allah yasa Islam ta cecesu. Yana duba wayar kuwa saiga
Sunan jaga ya fito baro-baro akan fuskar wayar.hakan ya sanya shi ƙara karfafa zargi sa akan Daddyn Husna,dan dagani sunan nan bana mutanen arziƙi bane.

Tuni gaban Daddyn Husna ya fadi, tsoron sa ya ƙara bayyana,dan kuwa jiya sukayi da jaga akan zai bashi cikon kudin aikin daya sanya su, na bibiyar mahaifin Aslam,Dan su gano ta yadda zasu kawar dashi.amma yaƙi cika masa kudin ajiyan,dan yace baya cika masa aiki idan ya sanya shi dan haka bazai biya kudin aikin ba,
Wanda hakan ya fusata jaga yace,idan har Daddyn Husna yayi saken kin cika masa kudinsa zuwa washegari,to wllh saiya dauki mataki mai ƙarfi akansa.
To yanzu ma kira yayi dan ya sanar da Daddyn Husnan ya saurari hukuncin da zai dauka akansa.

"Aslam karka daga wannan kiran,dan Allah karka daga,wllh shidin mai kisa ne,kuma zai iya yin komai akan kuɗi,sannan wannan wayar sirrina ne karka daga"Daddyn Husna ya fada cikin yanayi na firgita da tsoro,dan yana tsoron kar wani asirin ya Kara tonuwa.
"Aslam ka daga wayar,ka sanyata a sifika kowa yaji,dan na tabbata wannan kiran daga mutanen dayake sanyawa aikin kisan ne"Daddyn Aslam ya fada cikin bada umarni.

"A'a Alhaji dan girman Allah karka sanya yaron nan ya daga wayar nan,wllh akwai gagarumar matsala Gara ku kaini police ɗin cikin wannan motar ayimin hukuncina,akan ku daga wayar nan,sirrina ce"Daddyn Husna ya fada cikin firgici da tsoro fiye dana da.

Jin irin yadda ya tada hankalinsa ya sanya Aslam saurin daga kiran,wanda harya kusan tsinkewa.

"Kai Alhaji Musa ,Ni zaka mayar dan iska?kaƙi cika min kudin aikina, sannan wayata ma saika ga dama zaka daga?to wllh nafika akuyanci,baka isa ka sanyamu aiki kuma kaki biya ba,kai kanka ka sani wancan lokacin har videon yadda muka sanya motar Alhaji kabeer hatsari da hoton gawarsa saida muka nuna maka,amma da yake ehh Allah yayi da sauran shan ruwansa bai mutu ba.kuma tunda ga wancan lokacin.kasanya mu muke bibiyar rayuwar sa,Allah yana kubutar dashi, mun samo maka mafitar yadda zaka iya kashe shi yanzu,shine zaka juya mana baya?karya kake wllh jaga cikakken dan tasha ne ,wllh saina zo har gidan ka,agaban idonka zanyiwa yarka fade,da matarka,sannan inba yarana suma su aikata su,kafin in kashe su kisa mafi muni agaban idonka.
Wannan shine hukuncin maci amana irinka "jaga yana gama faɗin wannan maganar ya kashe wayarsa.

Gaba daya mutanen dake gurin,sandarewa sukayi cikin shock,bama ya Daddyn Aslam,zuciyarsa tayi rauni matuka hankalinsa ya tashi sosai,jikinsa kuwa tuni ya kama rawa,saida Aslam yayi saurin rikeshi yana faɗin"ka kwantar da hankalinka daddy everything will be ok"ya fada yana jingina mahaifin nashi da jikinsa.
Cikin dacin zuciya Daddyn Aslam ya kalli Alhaji Musa,wanda ya sunkuyar da kansa,tunda jaga ya fara magana,sai yanzu yake dana sanin kin biyan jaga cikon kudinsa.
Da yanzu asirin sa bai tonu ba.

"Yanzu Alhaji Musa,dama kaine wanda ya sanya akasheni akan hanya ta nida ɗana?
Sannan kaine wanda ke son ɗauke takardar dana sanya hannu akan maƙudan biliyoyin kuɗaɗen mutane? Wannan shine sakamakon janyoka danayi jikina?ashe da gaske makashinka na tare da kai?shin wannan Shine sakayyar da zakayi min Musa? Shin ka manta ahalin dana daukoka? Kana almanirinka na daukoka na sanya ka jikina,nayi maka aure na baka gida na inganta rayuwarka,sannan na sanya ka cikin harkokina,na aurawa dana yarka,duk wannan alkairan da nayi maka da kisa zaka sakamin ? Bayan kayi ƙoƙarin kashe ƙanwata da mijinta ,tare da ƴaƴansu? Me kake nema Alhaji Musa? Me zaka ajiye aduniyar ?"Daddyn Aslam ya fada cikin wata irin murya mai kama da zaiyi kuka.

"Alhaji sharrin shaidan ne dana zuciya,kuma Ni wllh karya ma wannan yaron yake min,bansanshi ba kawai yana son ya...

Tasss!!!Daddyn Aslam ya ɗauke fuskar Daddyn Husna da mari mai matukar shiga jiki.
"Rufemin baki macucin banza maci amana maha'inci officers ku tafi dasu muma muna tafe bayanku, dan bada bayani"daddy ya fada yana huci.
"Alhaji dan Allah kayi hakuri wllh sharrin zuciya ne ka gafarceni"
Abinda Alhaji Musa ke faɗi kenan yana zare ido.
"Ku daukeshi daga gabana officers" daddy ya fada cikin fushi.
Aikuwa yan sandan ma cike da tsanar su Daddyn Husna suka tasa ƙeyarsu zuwa police station,Dan sun Sha mamakin cin amana irin na wannan bawan Allah.

"Kuka sosai granny ta sanya tana tsinewa musa"Allah ya isa tsakanina da mutumin nan,ashe shine yayi kokarin kashemin yayana har biyu, wllh sai munyi shari'a dashi azzalumi kawai"
Rarrashinta su mommy sukayi tayi hartayi shiru,sannan suka koma cikin Falon cike da jimami,gaba dayansu zama sukayi zuciyoyinsu cike da alhini da kuma ƙara godewa Allah, daya bayyana musu wannan gaskiyar,suka gano cewar suna zaune da mugayen mutane tsawon lokaci ba tare da sanin su ba.
Ajiyar zuciya daddy ya sauke mai ƙarfi,kafin yace "alhamdullah,Allah shine abin godiya,domin cikin hikima da taimakon sa muka gano wannan gaskiyar da ta jima aboye, tabbas,Alhaji Musa ya cutar da mu,ya ha'incemu,amma Allah shine zaiyi mana sakayya akansa,na daukeshi tamkar dan uwana na jini,na maidashi babban abokina,kuma abokin shawarata,amma yaci amanata"daddy ya fada cike da karyewar zuciya.

"Dama haka halin dan Adam yake ,wanda ka yarda dashi,ka bashi amana shine yake cinyeta,yanzu ka duba ka gani menene baka yiwa Musa ba?ba kallon kai ba,nima tamkar da haka na daukeshi,
Haka muka ƙi jininmu muka nuna son nashi,ta hanyar aura mata Aslam,Ni wllh sai yanzu nake tunanin anya ba asiri sukayi mana ba?
Dan awannan lokacin wllh ji nake tamkar na daukota na dawo da ita gidan nan matsayin matar Aslam,Amma yanzu sam bana jinta cikin
raina "cewar granny kenan tana taɓe baki.

Girgiza kai daddy Yayi tare da kallo Daddyn Islam yace "ya kamata muje can police station ɗin ko?ya fada yana mai mikewa tsaye.

"Haka ne Alhaji karsuyi ta jiran mu,dan wannan case ɗin babban ne "cewar daddy Islam shima yana mikewa tsaye.

"Aslam ka tashi muje kaima dan akwai bayan da za'a bukaci ji daga gareka"daddy ya fada yana mai kallon Aslam,dake zaune kusa da islam hannunta cikin nashi.

Mikewa Aslam yayi tare da sakin hannun Islam,yace "to daddy "sannan ya kalli Islam yayi mata murmushin kwantar da hankali,dan yaga gaba ɗaya jikinta yayi sanyi kamar ba Islam dinsa daya sani jaruma ba.
Ahankali yace "idan kina jin barci ki kwanta anan,idan mun dawo zan tasheki mu koma part dinmu,sannan ki kwantar da hankalinki kinji?"
Ya fada yana mai kafeta da idanuwansa masu sanyata jin kasala.

Jinjina kai kawai tayi ba tare da tace komai ba,dan jikinta asanyaye yake sosai.
Haka su Aslam suka rankaya zuwa police station din...

Muje zuwa.
Mrs babi ce
[12/27/2022, 7:50 AM] Abk: 103/104
_______________Jinjina kai kawai Islam tayi ba tare da tace komai ba,dan jikinta gaba ɗaya asanyaye yake sosai,ashe duk tsawon wannan lokacin suna tare da mutumin da yaso halakasu ita da nahaifanta?sannan kuma shine wanda yaso kashe yayan mahaifiyarta sannan surukinta? Wannan fa shine ake kira rashin sani ,wanda yafi dare duhu.

Haka su Aslam suka rankaya police station da su daddyn,yayinda aka bar Aman agida,Dan ya kula dasu mommy,tunda gaba dayansu jikin kowa yayi sanyi.

Koda suka je police station din,sun tarar dasu Daddyn Husna da Husna tare da mommynta akulle.
Inda mommyn Husna sai masifa take akan ita da diyarta basu da laifi,abudesu.
Shikuwa Daddyn Husna yana zaune yayi shiru yana kallon yadda diyarsa ke kuka sosai,tunda gurin da aka kullesu yana kallon juna ne.

Bayan su daddyn sun gama bada bayani ne Daddyn Aslam ya bukaci da a fito da su husna,dan su kam basu da wani case dasu.
Hakan ta sanya aka fito dasu Husna akan sharadin bazasu bar garin ba har zuwa sanda za'a mika Alhaji akotu, sannan zasu zauna bisa kulawar yan sanda saboda furucin su jaga.
Koda aka fito dasu Husna,sai kuka take tana rokon Aslam ya maidata ɗakinta, shikuwa ko kallo bata ishe shi ba.
Saboda dattako irin na Daddyn Aslam,har rarrashin Husna yake akan tayi shiru ta daina kuka.

Haka dai su husna suka tafi gida bisa rakiyar yan sanda guda biyu.
Suma su daddyn suka dawo gida.

Su daddyn Islam basu jima da dawowa ba,suka tafi nasu gidan suma.

Aslam ma Bangaren su suka koma shida Islam,tunda dare yayi.
Gaba daya Aslam baya cikin yanayi na jin dadi,damuwa ta bayyana sosai akan fuskarsa.
Suna kwance akan gado shida Islam,inda yake rungume da ita asaman ƙirjinsa,bayanta yake shafawa ahankali yana tunanin ta yaya ya auri yar mutumin daya so kashe masa haifi da antynsa? Shifa badan yasan cewar ba ta yadda za'ayi ya zauna da Husna gida ɗaya ba tare da aure ba,to da saiyace shi baisan lokacin da aka ɗaura musu aure ba.
Jinda Islam tayi shirunsa yayi yawa ne yasata ɗago kanta ahankali ta kalli Aslam,aikuwa ta cikin dan hasken dimm light ɗin dakin ta hango fuskarsa, idonsa biyu ba barci yake ba,saidai kana gani kasan yayi nisa a kogin tunani.
Shiru tayi tana tunanin abinda zatayi masa dan kawar masa da damuwar dake ransa.
Tana son faranta masa,saidai tana tsoron wahalar da zata sake sha.
Amma ya zame mata dole awannan lokacin ta kuka da Aslam.
Dan haka cikin nutsuwa da ɗan dari-dari ta matsar da fuskarta saitin bakinsa.
Kawai jin bakin Islam yayi cikin nashi.
Aikuwa abinka da mai neman kuka,kuma aka jefeshi da kashin shanu.
Ba jiran wani abu Aslam ya karɓe bakin Islam,nan dai suka fara ƙoƙarin faranta ran juna.

Yau ma dai Islam taji ajikinta,saidai ta daure sosai dan ganin Aslam ya samu nutsuwar da ta kamata.
Aikuwa ya samu nutsuwar da ta ɗauke masa duk wani damuwa dake ransa.
Bayan komai ya lafa yana rungume da Islam ajikinsa,albarka kawai yake sanbado mata, yayin da yake jin so da ƙaunarta na ƙara nutso cikin zuciyarsa.
Fata yake Allah yasa yayi ajiya ajikin Islam daren jiya.

Washe gari da safe aka mika case ɗin su daddy zuwa kotu.inda aka sanar dasu ranar Monday za'a fara zama ɗan saurarar case ɗin nasu.

Kai tsaye suka wuce dan ganin Daddyn Husna,har zuwa wanann lokacin Daddyn Aslam Yana jin ba dadi game da kulle Daddyn Husna da akayi,dan kuwa indan ta tashi ne wllh yafe masa zaiyi,dan yana ganin cewa Alhaji Musa baida kowa sai shi,shine ya zame masa uwa,uba,yaya kuma aboki.
Dan Alhaji Musa Maraya ne baida uwa baida uba.
Dan haka yake jin damuwa sosai cikin ransa na ganin Alhaji Musa cikin kurkuku.

Koda aka fito dashi daga inda aka kulleshi, sosai Daddyn Husna ya tausaya masa,ganin yadda jikinsa yayi dukun dukun,sannan ga dukkan alamu baici komai ba,kamar ma dukansa akayi,dan da kyar yake taka ƙafarsa.

Allah sarki daddy cike da zafi da jin ciwo azuciyarsa yake kallon Alhaji musa yace "yanzu Musa wannan itace rayuwar daka zaba wa kanka?wannan shine abinda kake burin ganin kanka ciki?me yasa musa?me yasa ka aikata wannan danyen aikin?kasan yadda nake ji cikin zuciyata ganin ka ciki wannan halin? Musa ka cuci kanka,ka lalata rayuwarka,me yasa baka cemin kana bukatar wannan kudaden na baka su ba?meyasa baka yi tunani Ba kafin aikata wanann danyen hukuncin?na dauke ka matsayin dan uwana amma kaci amanata Musa, yanzu ga abin da gari ya waya"
Daddyn Aslam ya fada muryarsa na rawa.

Kuka Alhaji Musa ya sanya mai ciwo,sai yanzu yake dana sanin ƙoƙarin cutar da Alhaji kabeer da yayi tayi,lallai wannan mutumin, mutumin kirki ne kamar yadda ya sani tun baya,yanzu duk wannan abinda ya faru,amma yana nuna tausayawarsa akan sa.
"Dan Allah Alhaji kayi hakuri,hakika na cutar da kaina na zalunci rayuwata,na zamo mai son zuciya da kwadayin abin duniya,wanda suka sa na manta da menene zai iya faruwa dani nan gaba, dan Allah Alhaji ka yafe min"Alhaji Musa ya fada cikin kuka yana haɗe hannayensa alamun neman yafiya.

Shi kansa Daddyn Islam yaji tausayin Alhaji Musa,amma ya kamata ahukuntashi,domin ya cutar da al'umma sosai.

Haka suka tafi suka barshi yana ta kuka,wanda suma saida sukayi kwalla.
Mommyn Husna kuwa kwana tayi tana kitsa abubuwan da yawa cikin ranta,bata bari gari ya waye ba,ta saci jiki ta fice daga gidan,kawai sai jin karar tashin mota yan sandan nan sukayi.
Ƙoƙarin Binta sukayi,amma ina tayi musu nisa,dan ko ganin ƙurar motar ta basuyi ba.
Haka suka hakura suka dawo gidan, inda suka tarar da Husna zaune ta hada kai da kwuiwa tana kuka.

Kai tsaye mommyn Husna ta nufi gurin bokanta,tafiya mai nisa tayi kafin taje gurinsa.
Ahargitse ta shiga dakin da bokan yake,sai haki take,dan sai kayi tafiyar kasa kaɗan zaka je inda

Please Login or Register in order to submit comment