Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji tsoron ki?wllh ko kifice kona zazzabga miki mafi agurin nan"Husna ta fada tana daga hannunta kamar zata mari granny,sosai take jin haushin grannyn.

"Keeeeeh grannyn zaki mara?
Kakata?kuma acikin gidana?
lallai yau zaki bar gidan nan,kije gidanku akoya miki tarbiyya da ɗa'a .

juyowa sukayi gaba dayansu dan ganin mai wannan maganar.

Aslam ne ke fitowa daga dakin sa kunnensa suka jiye masa Husna na faɗin zata mafi granny,badan Yana gudun karya illata Husna ba,daba abinda zai hanashi dukanta.

Kuka Husna ta sanya cike da nadama tana mai faɗin"dan Allah kayi hakuri karka ce in tafi gida,wllh subutar baki nayi,bazan sake ba "
Ta faɗa tana mai hada hannayenta guri ɗaya alamun neman afuwa.
Ko inda take Aslam bai kallaba, sai kama hannun granny da yayi suka nufi dakin nashi.
Granny sai matsar kwalla take,ba'a taba mata rashin kunya irin na yau ba.
Zaunar da ita Aslam yayi akan kujerar falonsa,yana mai share mata hawayen yace "ya ce haba matar meye na kuka kuma?kiyi hakuri zanyi maganinta ne"
Cikin girgiza kai granny tace "wannan yarinyar ba yar arziki bace,wai nice tsohuwar kilaki,kuma Ni zata mara?wllh daka barni da zagewa zanyi mu doku"granny ta faɗa tana dukan taron hannunta.
Murmushi yayi yana mai cewa haba dai ai nine ya kamata na dauki mataki da kaina grannyna"
Haka dai yayi ta rarrashin granny yayin da islam ta fito itama suka rarrashi grannyn tare,inda take tambayar ina Islam taji ciwo,sukace bushewa tayi.

Husna kuwa cikin ihun kuka ta nufi part din mommy tana kuka..
[12/16/2022, 6:36 PM] Abk: 95/96
______________husna kuwa cikin kuka ta nufi part din mommyn Aslam.tana fadin
"Wayyo mommy kizo ki taimakeni Aslam yace intafi gidan mu akoya min tarbiyya,wllh Islam ce tayi masa asiri,itace ta karyamin nawa,shine Aslam ya daina sona,ya daina jin maganata, komai sai islam,wllh na tsaneta bana sonta"abinda Husna ke faɗa kenan lokacin data shiga part din mommy,Wanda fitowar mommy kenan daga kitchen.hanan tana zaune tana duba laptop dinta.
Da hanzari mommy ta ƙaraso gurin Husna tana mai riketa,ganin kamar ba acikin hayyacinta take ba yasa mommy ta zaunar da ita akan kujera tare da buƙatar hanan ta kawo mata ruwa.
Mikewa hanan tayi tana mai taɓe baki,dan ita wllh kwata -kwata bata son ganin husnan nan agidansu matsayin matar Aslam.dan bata da mutunci ko kaɗan.
Ruwan ta kawowa mommy cikin kofi.
Karba mommyn tayi tare da mikawa Husna kofin dai-dai bakinta akan tasha ko zata sami nutsuwa.
Amma saboda tsabar iskanci irinna Husna ta sanya hannu ta kaɓar da ruwan har saida ya jiƙa mommy.
Tana faɗin"niba shan ruwane ya kawoni ba kiyiwa Aslam magana yace intafi gidan mu,wllh kuma Ni bazan tafiba, dan kuwa waccan Shegiyar Islam ɗin ita ta sanya shi,asiri tayi masa,kuma wllh ƙarya take daga ita har wanda suke taimaka mata,bokana yafi nasu ƙarfi"Husna ta fada cike da rashin hankali da sanin me take cewa.
Galala mommy tayi tana kallo da sauraron abinda Husna ke faɗi,wato kenan asiri suke yiwa Aslam?shine take zargin Islam ma asirin tayi masa,lallai tayi sake wajen nemawa danta tsari,dole kuwa yanzu ta mike da yi masa addu'a akan mugayen mutane irin su husna.
"Kee Malama meye hakan ko bakya ganine?dubi yadda kika jika mata jiki da ruwa kuma da gangan kikayi hakan"hanan ta faɗa cike da jin haushin Husna.
Afusace Husna ta juyo kan hanan,tana faɗin"dan uwarki an zuba mata ruwan,ko zaki rama mata ne?marar kunya fitsararriya wllh idan kika ƙara shiga sabgata saina illataki"Husna ta fada cikin huci da masifa.
Buɗe baki kawai mommy tayi tana kallon husna,duk da tasan rashin kunya irin na Husna ,amma bata taɓa tsammanin zata iya zagin hanan agabanta ba.

Hanan kuwa cike da jin haushin zagin da Husna tayi mata, itama ta zaburo tace "wllh badai uwata ba,saidai taki,kuma wllh idan kika ƙara zagin uwata saikin gane kuren ki ban.....

"Ke hanan meye hakan?baki da kunya ne?agabana kike yiwa matar yayanki rashin kunya? tarbiyya dana baki kenan?"mommy ta faɗa cikin haɗe rai da yiwa hanan gargadi.

"Amma mommy kina jin abinda take fadamin itama?zagina fa take dan kawai nayi mata magana akan abinda tayi"hanan ta faɗa kamar zatayi kuka.
"To ki kyale ta mana ko ke ta jiƙa?ban son rashin kunya hanan"

"Ai gara ki barta ta nuna min rashin tarbiyyar tata afili,yo idan batayi haka ba, ai bazan san yar gadon rashin tarbiyya bace, kuma wllh dai -dai nake da kowane dan iska agidan nan"cewar husna kenan cike da rashin da'a da tarbiyya tana hararar hanan.

Cike da fara gajiya da irin yadda take yadawa mommy magana ta rashin kunya,mommy tace "Husna !ya kamata ki iya bakinki,kisan ne Yakamata ki fada, dan kuwa kome kike ce akan hanan,to damu kike"mommy takai zancenta tana kallon Husna da ɗan ɓacin rai akan fuskarta.
Husna kuwa taɓe baki tayi cikin gatsali da raini tace "ita yar taki bakijin abinda take fadamin ne?wllh ba wanda ya isa ya hanani maida martani akan duk abinda akayi min,dan kuwa nima yace kamar kowa,mutane ba abinda suka sani sai son kai da mugunta"Husna ta fada tana mai yatsina fuska da murguda baki.

Aikuwa amugun zafafe hanan tayi akan husna tana huci tare da faɗin"wllh baki isa kiyiwa uwata rashin kunya agabana ba,kedin banza baki isaba wllh"hanan ta faɗa cikeda masifar dataji ta taso mata yanzun nan.
Saidai kafin ta kai ga Husna mommy ta tare ta.
"Meye hakan ne hanan,baki jin magana ko?ki barta ai duk wanda ya raina iyayen wani,to nashi ya raina,kuma kowa yayi na gari,kansa"

"Kidai iya bakinki,karki sake ki zagi iyayena wllh,kuma Ni ban raina iyayena ba,can dai wannan Shegiyar yar taki, itace ta rainaku badai niba,kuji muguwar mata mai son kai, haka kawai kisani gaba kina ta yimin baki,uwata ce ke? A'a wllh banaso dan kuwa wllh niba......

Kau! Kau!! Kau!!! Husna taji saukar wasu zafafan maruka, masu matuƙar zafi da radaɗin daya haddasa mata daukewar ji da gani,na wani lokacin.
Wani gigitaccen ihu Husna ta kwalla,wanda bata gama fitar da ihun ba taji saukar belt ta ko ina ajikinta, ihu Husna keyi tana ƙoƙarin tashi daga faduwar datayi sakamakon marin da tasha,saidai ta kasa tashi, gaba ɗaya ta gigice ta rasa ina zata sanya kanta.dan ba tasan ma ta ina dukan yake sauka ba, jinsa kawai take from no whare.

Da sauri mommy ta riƙe belt din da ake zabgawa Husna,cikin ɓacin rai tace "meye hakan kake yi ?agabana kake dukan yar mutane kamar ka samu jaka? Wannan wane irin hali ne ka daukarwa kanka, agabana fa"mommy ta faɗa cikin ɓacin rai sosai.

Cikin zafin zuciya da mugun bacin rai marar misaltuwa,Aslam Wanda suka taho domin rako granny part din mommy,shida Islam,Dan ta dage ne saita zo itama shiyasa ya taho tare da ita, kuma tuni granny ta fahimci abinda ya faru da Islam,dan ta kula da yadda take tafiya ahankali kamar yar kaciya, duk da ta gasa jikinta sosai.
Haka granny ta sake bata kulawa ta musamman irin tasu ta tsofi, tayi murna sosai da farin ciki,tare da fatan Allah ya basu zuri'a dayyiba.
Zuwansu kenan falon cike da farin ciki suke tafe yana riƙe da hannun Islam,granny tana ta masa tsiyar bashi da kunya, kuma tana masa gargaɗin wllh ya bar mata jika ta huta.
Kawai kunnensa ya jiye masa yadda Husna ke zazzagawa mahaifiyarsa rashin kunya kamar sa'arta.
Baisan lokacin daya saki hannun Islam ɗin ba ya shiga falon da mugun sauri ya fara mata da maruka masu kyau,kafin ya zaro belt ɗinsa ya Dora dashi.

Huci kawai yake yana kallon Husna,ji yake aduniya ba wanda ya tsana sama da husna,zai iya jure zama da ita koda baya sonta,amma bazai taba daukar cin mutunci ga mahaifiyarsa ko ahalinsa ba.

Kuka sosai Husna keyi tana mai sosa jikinta, sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta,kallon Aslam tayi cikin kuka ta fara magana"wllh bazan yarda ba, akan wannan matar mai son kai zaka dakeni ?baka daki banza ba,mugu azzalumi,dan kawai ana sonka shine zakayi ta dukan mutane ?wllh zaka san ka dokeni kuma agaban wannan tsinanniyar matar taka dangin tsiya masu asiri,ke kuma ki jira kiga abinda zai biyo baya,wllh saikinyi dana sani.."
Zabura Aslam yayi cikin zafin nama zai kara yowa kanta mommy tayi saurin rikeshi tana tace"Aslam fice daga falon nan tun kafin raina ya ɓaci"ta faɗa tana mai tsare shi da idanunta ba alamun wasa.

Cike da ɓacin rai Aslam ya kalli husna yace na tsaneki,nayi dana sanin auren ki,kuma kije gidanku na datse igiyar aurena daya akanki.
Yana fadin Haka yayi waje, ko kaɗan bai so mommy ta hanashi sake gyarawa Husna zama ba,dan yaga bata saituba har yanzu.
Ganin yadda ya fita afusace, yasan ya Islam binsa da sauri tana ɗan ɗingisa ƙafarta.

Ihu Husna ta sanya tana ɗora hannunta aka"wayyo Allah na,na shiga uku ya sakeni Shegiyar kuma ta bishi, na shiga ukuna, wllh bazan barki ki huta ba Islam,sainaga bayanki tsinanniyar yarinya dangin tsiya"
"Keee yarinya ki iya bakinki fa, dan nan ba sa'anki, mune tsiyar kome kike nufi? Ai yayi daidai daya sakekin, marar kunya kawai, kuma ba abinda kika isa kiyiwa jikata wllh,Allah yafi karfin ku idan juninki asiri,wllh sai yanzu nake jin takaicin auroki da Aslam yayi,abu ba fasali ba komai,kalleki sai tsabar rashin kunya,wllh ba wani abu bane agurina in zage mu danbatu dake mu raba raini marar tarbiyya kawai.
Cewar granny kenan tana cin damara da ɗan kwalinta.
Kallon bata taki na ke ba Husna tayiwa granny kafin ta miƙe tsaye ta riƙe ƙugu"bani da lokacin ki yanzu tsohuwar duniya, ki jira in gama da jikar taki,kema zan dawo kanki,ba ke kadai ba ma,da duk masu son yimin shishshigi arayuwata.
Wllh duk saina ɗauki mataki akanku" tana gama faɗin haka tayi hanyar fita daga falon tiɓi -tiɓi.

"Aikuwa wllh barin gidan nan zakiyi tunda ya rabu dake, marar kunya mai siffar jakin dawa,wllh ban taba ganin fitsararriya yarinya irinki marar da'a ba"faɗa sosai granny keyi tana ba mommy labarin irin rashin albarkar da Husna tayi mata.
Hakuri mommy tayi ta ba granny tare da rarrashinta akan tayi shiru,dole ayiwa tubkar hanci.dan bataso Aslam yayi saurin furta sakin ba.

Islam kuwa cikin daki ta tarar da Aslam Yana kwance akan gado ya ɗora hannunsa akan goshinsa,inda idanunsa ke rufe.amma kallo ɗaya zakayi masa kasan ransa amatukar bace yake.
Ahankali Islam ta karasa cikin dakin, bakin gadon taje ta tsaya tana kallonsa tayi shiru ba tare da tace komai ba.
Buɗe idonsa yayi wanda suka kada sukayi jajur tsabar ɓacin rai, kallonta yake shima,tana tsaye kamar an dasata .
Mika mata hannu yayi alamun tazo gareshi.
Cikin sanyin jiki Islam ta kama hannun nashi tare da hawa kan gadon,akan faffaɗan ƙirjinsa yayi mata masauki tare da rungumeta tsam-tsam kamar wani zai kwace masa ita.
Ajiyar zuciya yake saukewa kamar wanda yasha kuka ya ƙoshi, sosai yake jin zuciyarsa tanayin sanyi daga suyar da take masa.
Islam kuwa tayi lamo akan ƙirjin nashi tana sauraron yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.
Hannunta ta sanya tare da balle maballin gaban rigarsa, kwantaccen yalwataccen gashin ƙirjin nashi ya bayyana,cikin nutsuwa da ɗan rawar hannu ta cusa hannun nata cikin ƙirjin nashi,ahankali ta fara shafa saitin zuciyar tasa cikin salo da hikima.

Tuni Aslam ya fara lumshe idanunsa,dan ji yayi kamar waiwayi take masa tare da zuba masa ruwan sanyi.
Cike da so da kauna Aslam ke shafa bayan Islam,yana jin wata irin muguwar kauna da sha'awarta na motsa masa.amma sanin ba dadi take jiba yasashi danne sha'awarsa tare da kara kankameta ajikinsa.
Ahankali ya furta "ina sonki Islam,kece farin cikina,maganin damuwa da ɓacin raina,kici gaba da kula da ni,ki kasance kusa dani akoda yaushe,ina sonki islam" ya fada cikin wata irin murya mai cike da shauki.

Wani irin sanyi zuciyar Islam tayi,soyayyar Aslam na ratsa dukkan sassan jikinta,ji take bazata iya rayuwa ba Aslam ba.cikin shaukin so da kauna tace "nima ina sonka mijina,zan kasance dakai har karshen rayuwata".
Ta faɗa tana mai kara shigewa jikinsa sosai.
Dadi da farin ciki ne suka baibaiye zuciyar Aslam.da sauri yace "da gaske kina sona kema ?
Ya fada cike da zumuɗi.
Jinjina kai Islam tayi tare da cewa"fiye da yadda kake sona"
"Alhamdullah na gode wa Ubangiji domin ya gama min komai arayuwata,ina sonki Islam "Aslam ya fada yana kissing din Islam ta ko ina.
Sabuwar wayar daya siyo mata ya dauko tare da saita mata komai ya bata.
Murna sosai Islam tayi tare da yi masa godiya.nan dai suka buge da soyewarsu.
I

Husna kuwa tana fita daga falon mommy, kai tsaye motar ta tashige ta figeta aguje.gidansu ta nufa tana zuwa ko kashe motar batayi ba ta nufi falon nasu tana kuka.
Iyayen ta gaba ɗaya suna zaune afalo,suna kitsa yadda surkulle su zai kasance,
Da kuka Husna ta fado musu cikin Falon tana faɗin "wayyo Allah na mommy wllh ya daina sona,dukan tsiya yayi min da belt bayan ya zabzabga min maruka.wllh bazan yarda ba ku daukar min mataki akan wannan dukan,kuma bazan bar mata shiba,asiri tayi masa"Husna ta fada tana mai fadawa kan mommynta.

Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba,ganin shatin belt ajikin Husna,nan da nan suka harzuka mahaifin Husna yace bazai yarda ba,dan koshi bai taba dukan yarsa ba bare wani aslam,
Nan take suka tashi gaba dayansu suka nufi gidan su Aslam...

To fa!!!
Ko wace wainar za'a toya? Oho ?
Muje zuwa .
Mrs babi ce.
[12/23/2022, 8:11 AM] Abk: 97/98
_____________Hankalin iyayen Husna ba karamin tashi yayi ba ,sakamakon ganin shatin belt da sukayi ajikinta,wanda koda wasa su basu taba koda yi mata tsawa ba bare duka.
Yau kuma gashi wani da sunan mijinta yayi mata duka harda belt,lallai bazasu yarda ba,dole su dauki mataki mai kwari akan wannan al'amarin.

Cikin zafin rai da matukar jin haushi,mahaifin Husna ke faɗin"Ni Alhaji kabeer zaiyiwa haka?Ni ɗansa zai yiwa yata irin wannan dukan kamar ya sami jaka?to wllh bazan laminta ba,shi baisan darajar wannan yarinyar yake ciba,shiyasa har yanzu yake raye? To lokaci yayi da zan aiwatar da ƙudurina akansa,wanda na daga masa ƙafa ada, tun lokacin daya sami damar tsallake tarko na farko,amma yanzu ninasan mai zanyi akan al'amarin nan"Daddyn Husna ya kai ayar zancensa cikin huci.

Mommy dake shafa kan husna cikin damuwa da sigar rarrashi,ce ta ɗago ta maida kallonta kan mijin nata,hakika ranta itama yayi mugun ɓaci,kuma wllh bazata yarda da wannan wulaƙancin ba,saboda Aslam Yana auren yar uwarsa,shine Hajiya A'isha ta zuba masa ido yana wulakanta mata ɗiyarta tilo kamar rai.
"Ai wllh idan ma kai baka dauki mataki ba,to Ni nan zan dauka,dan ban haifa musu yar dansuyi ta duka ba,akan me?kwanaki ma marinta yayi sai kace jakarsa? Maza ki share hawayenki yanzun nan zamu je dan daukan mataki akan wannan zaluncin meye ma abinda ya jawo dukan ?"mommyn husna ta faɗa tana sharewa Husna hawayen dake zuba a idonta.
Ita kuwa sai wani kuka take tana narkewa jikin uwar kamar wata sakara.
"Mommy akan wannan tsohuwar matar ta gidan fa da matarsa ya dakeni, dan kawai tamin shishshigi nayi mata magana,shine naje na fadawa uwarsa itama take min baki,nikuwa na gaggaya mata magana kawai sai jin saukar duka nayi ta ko ina"
Husna ta faɗa tana mai kallon uwar tata.

"Yo ai kinyi min dai-dai, nice nan na saki ,duk wanda ya kawo miki wargi ki nuna masa kurensa,idan ba lalacewa ba ma kina suruka kike yiwa matar danki katsalandan, da shishshigi kuma dan tayi magana kike mata baki? Shegiyar mata,ai duk tana haka ne dan tana duniyar,idan ta barta kinga shikenan kowa ya huta"cewar mommyn Husna tana miƙar da husnan tsaye.
Daddyn Husna kuwa tuni yayi waje dan fito da motarsa.
Haka suka dunguma zuwa gidan gaba dayansu, har uban,saboda rashin hankali,maimakon suyi bincike mai kwari kafin su san matakin dauka,kawai suka biyewa diyarsu.

Lokacin da suka je tuni anshiga sallah,dan haka kowa na gidan yana Sallah,aikuwa neman guri sukayi suka zauna a babban falon suna ta yada magana har alhajin kamar wata mace shima.
Mommy ce ta fara fitowa daga ɗakinta,da sauri ta ta ƙaraso tana faɗin sannunku da zuwa hajiya,Alhaji kune da magaribar nan?sannunku "ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.
Wani banzan kallo suke bin mommy dashi,inda mommyn Husna tace "dole kice haka mana,saboda bakiyi tsammanin Husna na da gatan da za'a bi mata hakkinta awannan lokacin ba, wllh kin bani mamaki Hajiya A'isha,ace kina gani wancan gantalallen dan naki, ya kama min ya yayi ta jibga kamar ya sami baiwa, sannan ya dunguma mata saki ,amma kika ƙyale shi ko ajikinki,saboda bakin hali da mugunta dan ba ƴarki akayiwa hakan ba ko?to wllh bazan yarda ba,ƙara zamu kai dole abi mata hakkin dukanta da kuma na sakin da yayi mata ehe"mommyn Husna ta faɗa cikin masifa tana zazzare ido kamar mujiya.
Shikuwa Daddyn Husna sai wani gyada kai yake yana hura hanci,saida matar ta kai kare maganarta shima ya dora da nashi yana cewa
"to in banda zalunci ma,husnan nawa take?da za'a sanya mata karfi wajen duka kamar wanda na kawo muku baiwa, sannan daga ke har mijinki kunyi shiru baku ce komai ba, to mukam bazamu yarda ba,dan kuwa Shari'a zamuyi daku" Daddyn Husna ya fada da ɗan daga murya yana wani baza malum malum kamar na Allah.

Mommy kuwa saroro tayi tana kallon ikon Allah gurin waɗan nan mutanen,ita tayi tunanin sunzo ne dan asasanta,ashe ba hakan take ba, bamamaki kuwa bai barta tace komai ba,sai kallonsu da take ɗaya bayan daya.tana kuma jinjina rashin dattako da hankali irin nasu.
Cikin sanyin murya da son kwantar musu da hankali,duk da taji zafin maganganun su,akan danta tace"ayya Alhaji da Hajiya,kuyi hakuri,tabbas anyi muku ba dai-dai ba, amma ina mai baku hakuri kuma yanzu haka jiran dawowar Alhaji nake,koda baku zo ba mu zamu zo har gida mu baku hakuri sannan shima Aslam zai zo ya baku hakuri,Husna ai tamkar ya take awajenmu,ba ta yadda za'ayi mu cutar da ita da gangan,ko mu bari ta cutu kuma muna kallo.
Yaran zamani ne sai haƙuri,ka haifi da ne baka haifi halinsa ba,amma ita husnan ai tana ji da ganin yadda na nuna masa ɓacin raina akan abinda yayi Kum...
"A'a wllh Ni karya kike min,banji ba kuma banga lokacin da kike nuna masa ɓacin ran naki ba,hasali ma ba kece kika haddasa komai ba?koba ke kika ja ya sake niba?"Husna ta tari numfashin mommy ta hanyar katse mata zancen da take cikin daga murya da rashin kunya.

Shiru kawai mommy tayi tana kallon Husna,zuciyarta na tafarfasa,amma tana ta kokarin danne ɓacin ranta,dan tana bukatar zaman lafiya ne.
"Yanzu Husna nike miki karyar? Mommy ta faɗa cikin sanyin murya.
Cikin rashin kunya Husna tace
"Ba ƙaryar kikayi ba?ko za'a hanani fadane?" Ta faɗa tana murguda baki.
"A to za'a hana yarinya fadar gaskiya ne?idan ba karyar kikayi ba,ai bazata fada ba"cewar Daddyn Husna kenan yana zare ido.
Sosai mommy take mamakin rashin kunyar Husna ,da kuma yadda iyayenta ke goya mata baya,gaskiya
Sai yanzu tasan Aslam baiyi dacen mace ba.sam ba yar gidan mutunci bace,kuma kome tayi gado ne.
"Wai hayaniyar me nake jiyowa ne tun ɗazu ina salla?wane karnukan ne suka shigo mana gida da magaribar farin nan?"granny ke faɗin wannan maganar,dan kuwa tana iya jiyo sautin muryoyinsu tana cikin ɗakinta,dan haka tana idar da sallar ta fito,idonta ne ya sauka akan husna dake wani yamutse fuska tana harare harare,tace "au! wannan marar kunyar ce?me ya dawo dake cikin gidan nan?ko kin dawo ne ki sake zage mu tas,kamar yadda kikayi dazu?to wllh ki shiga taitaiyinki,dan kuwa yanzu idan kika min rashin kunya,wllh jikinki ne ,zai gaya miki,marar tarbiyya kawai"granny ta faɗa cikin masifa da jin haushin da tsanar husnan.

"Eh lallai kuwa,Alhaji gadai gani agaban idonmu ma kenan, ina ga bayan idonmu,ka duba dai wannan mata tsofai tsofai amma kaji abinda take fadawa yar cikinta,wllh girma dai ya faɗi"

"Haba Hajiya ya kamata aringa sanin abinda za'a fada,koba komai agirmama furfurar mana"
Gaba dayansu juyawa sukayi dan ganin mai maganar.ba kowa bane face Aman, Wanda shigowarsa kenan yaji mommyn husna na faɗin waɗan nan kalaman ga granny.
Baya garin kusan wata guda kenan yana kaduna,sai yau ya dawo gida.

"To rashin kunya zakayi min kenan?marar tarbiyya to kasani dai dai nake da kai duk wani salon rashin kunyar ka,kasani tawa ta wuce nan"mommy Husna ta faɗa tana wani zaburowa kamar zata daki Aman.

"Ba rashin kunya zanyi miki ba,domin ba'ayi min wannan tarbiyyar ba,saidai ki sani bazan taɓa zuba ido ina kallon ki kina cin mutuncin ahalina ba,wllh sai inda karfina ya kare"Aman ya fada cike da haɗe fuska,dan ya fuskanci rashin mutunci mommyn Husna ke ƙoƙarin aikatawa.

"To muzuba Ni da kai,shege ka fasa dan halal sai yanka,wllh ko uwarka bata isheni ba, bare kai karan kada miya"cewar mommyn husna tana huci.
"Ba ita zakayiwa rashin kunya ba,Ni Yakamata kayiwa,tunda Ni na mijine nine zamu iya zagewa mu daku dakai,dan kuwa wllh nafika tashanci"
Daddyn Husna ne ya zo gaban Aman yana faɗin wanann maganganun,kamar wanda ya sami sa'ansa yake faɗa dashi.

Cikin ɓacin rai aman yace "wai mommy me waɗan nan mutanen sukeyi agidan nan ne?dan me zasu zo su tada mana hankali ? Mommy su fita dan kuwa raina ya fara ɓaci,komai na iya faruwa tunda gaba dayansu basu san girma ba"

"Aman ya isa kayi shiru kawai karka sake cewa komai"mommy ta faɗa tana mai riƙe hannun Aman, Dan taga ransa yayi mugun ɓaci,kuma komai na iya faruwa,dan aman yana da hakuri sosai,saidai bai iya zuciya ba,idan ransa ya ɓaci, har yafi Aslam faɗa.
"Dan me zakice yayi shiru?so kike ya zuba musu ido suna ci mana mutunci agabansa ya kasa daukar fansa?wllh bazai yiwuba, dan Ni ahalina ba asararre ko kaɗan,nina baka dama Amanu idan suka ce kule,kace musu casss-cararassss! ehe"granny ta faɗa tana tafa hannaye,tare da riƙe ƙugu.
Wasa wasa kirici su mommyn Husna ke son tayarwa acigidan surukan na yarsu,Dan kuwa cire malum malum Daddyn Husna yayi,wai zasu danbatu da Aman.
Hanan ce ta dauki wayarta ta kira daddynsu ta sanar dashi halin da ake ciki,inda yace gashinan zuwa yanzun nan.
Hankali tashe yayo gida dan ganin abinda ke faruwa.
Tana gama waya da daddynsu ta kira ya Aslam tace yazo gida ga iyayen Husna sunzo sai rashin mutunci suke.
Aikuwa cikin matsanancin fushi da ɓacin rai Aslam yayi gida,dan dama kira ya samu daga store dinsa na gaggawa,shine ya fita.

Duk wannan hatsaniya da ake yi cikin Falon mommy Sam Islam bata san wainar da ake toyawa ba,domin tana can bangaren su tare da malaminta,wanda zuwansa kenan ta bashi wannan tarkacen asirin nasu Husna.
Karba yayi tare da kallon tarkacen yana jinjina kai.kusan minti biyu kafin ya ɗago ya kalli Islam,yace "Islam ki godewa Allah daya baki kariya,amma wannan abun da aka kulla muku ba ƙaramin sihiri bane da zai farraƙa tsakanin ki da Aslam.
Ina son kici gaba da amfani da wannan maganin dana baki,sannan ki yawaita addua da neman tsari,
Allah zai kare ki da mijinki.ungo wannan kirinka shafawa ajikinki,bayan kinyi alwala,domin ahalin yanzu kishiyarki da mahaifanta zasu tashi tsaye sosai wajen ganin bayanki,dan kuwa abinda ya faru dazu yayi matuƙar kona musu rai,kuma ke suke ɗorawa laifin"malamin Islam ya fada yana mai mika mata wata yar tasa fara mai shegen kyau da sheƙi,banda ƙamshi ba abinda tasar keyi.

Duk da tasancewar malamin nata ba mutum bane,amma tayi mamakin yadda yasan abinda ya faru dazu.dan haka cike da ɗan mamaki tace "malamina,ya akayi kasan abinda ya faru dazu?alhalin baka zo gidan ba lokacin da abin ya faru?"
Islam ta faɗa tana ɗan gyara zaman ta.
Murmushi malamin na Islam yayi kafin yace "Islam Allah yana sanar damu abubuwa da dama,wanda ku baku sani ba,Ni rauhani ne kuma basarake,inada ƙarfin fikira sosai atare dani, ba wannan bama, nan da wani dan lokaci kaɗan wani al'amari zai faru mai girma na ban mamaki, kiyi ƙoƙarin hada mahaifin ki da mahaifin kishiyarki su hadu ido da ido.bayan haka Husna da iyayen ta suna cikin gidan nan ahalin yanzu"malamin Islam ya fada yana ɗan murmushi.

Jinjina kai Islam tayi cike da tunanuka iri iri,meyasa zata hada iyayen nasu ido da ido?meye alaƙar Abban ta da mahaifin Husna?
Dagowa tayi dan tambayar malamin nata,shikuwa cikin hanzari ya daga mata hannu yana murmushi kamar kullum.
"Kada ki tambaye Ni komai Islam,keda kanki zakiga komai,zaki samu amsar tambayar ki duk lokacin da kika hada mahaifanku guri ɗaya"yana fadin haka yayi mata murmushi tare da yin kalmar shahada ya zama farin hayaki ya bace.
Jimm Islam tayi azaune kafin ta ajiye tasar ta nufi part din mommy.inda tana fitowa suka hadu da Aslam Yana koƙarin shiga falon mommy.Tsabar yadda ransa yake ɓace,kallon Islam kawai yayi ya wuce cikin falon, ba tare da yayi mata magana ba.
Bin bayansa tayi tana tunanin meye ya bata masa rai haka?
Kusan tare suka shiga falon,dan

Please Login or Register in order to submit comment