Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake narkar da zuciyar yan mata.

Wani yarrrrr Islam taji tun daga tafin ƙafarta har zuwa babban ɗan yatsan ta, da sauri ta ja baya tana Banka masa harara gabanta na bugawa da sauri-da sauri.
Murmushi Aslam yayi tare da kamo hannunta cikin nashi ya ce"muje amaryar Aslam ko?"ya fada yana wani matsa mata hannu cikin salon mai tada hankali tare da kashe mata ido....


Manage please wayata ba caji ne.

Mrs babi ce
Anty mammy.
[9/30/2022, 12:05 PM] Abk: _____________Murmushi Aslam yayi,tare da kamo hannunta cikin nashi yace "muje ko amarya Aslam"ya fada yana wani matsa mata hannu cikin salon sa mai tada hankali tare da kashe mata ido.
Sosai Islam ta runtse idanunta,sakamakon yadda yake matsa hannun nata,cikin salo mai wuyar fassara wa,wani irin yanayi take ji ajikinta,dan haka da sauri ta fizge hannun ta,tare da balla masa harara tace "malam karka ƙara taɓani bana son iskanci"ta fada cikin ɗaure fuska tana nufar ƙofar fita daga falon.

Murmushin mugunta yayi tare da bin bayanta yana mai faɗin"da gaske bakya son iskanci?lallai aiki ya ganki dan kuwa niɗin cikakken dan iskane,kuma zakiga salo-salo na iskanci iri-iri,dama ai saboda kina son iskancin kika ce saikin aureni,kuma Indai iskanci ne kinsamu yarinya"ya fada dai-dai lokacin sun kawo wajen motar sa,mai shegen kyau da tsada.
Tsaki Islam tayi tare da tsayawa jikin motar ta na masa kallon sama da ƙasa"ai dama ba sai ka faɗa ba,nasan kai ɗin riƙaƙƙen dan iska ne,sai dai wallahi ka sani,zan aure ka ne badan wannann tunanin ba,dan kuwa koda wasa kace zaka taɓani,wllh zakaga yadda ake bala'i"ta faɗa cikin tsiwa tana murguda baki.

Murmushin gefen baki Aslam Yayi,tare da cije lips ɗin sa na ƙasa,cikin ransa yace "yarinya aiko mutuwa zanyi baki isa in nemi wani abu ajikin ki ba,bare kiyi tunanin zanyi sex dake,Allah ya tsareni"amma azahiri buɗe motar yayi ya shiga tare da faɗin"Allah ya kaimu lokacin zanga abinda zakiyi innazo hawa kanki "ya fada kai tsaye ko ajikinsa.
Kallon sa Islam tayi baki buɗe,dan ita kam kalmar tashi tayi mata nauyi,wai inyazo hawa kanta?sai kace wata doki.
Banza tayi dashi tare da buɗe gaban motar ta shiga.wani sanyi ne haɗe da ƙamshi mai daɗi suka ratsa hancin ta,har saida ta lumshe idon ta,kafin ta buɗe tare da jingina bayan ta da jikin kujerar.

Kunna motar Aslam yayi,tare da barin harabar gidan,fuskar sa aɗaure sosai,wllh shi har kunya ma yake ji agansa da wannan yarinyar, Ai ajinsa sai ya zube,adaina ganin girman sa,haka kawai yana zaman sa lafiya za'a ƙaƙaba masa wannan alaƙaƙai ɗin,wacce basu san daga ina ta fito ba,shi Daddy ma ba ruwansa da sanin asalin ta,kawai burin sa yayi aure,shine yake son hada zuri'a da ita.
ɗan juyowa yayi ya kalli Islam,wani bakin ciki ne ya ƙara turnuƙe masa zuciya,ganin yadda take wani hura hanci kamar wata tsiya, ji yake kamar ya shaƙeta ya huta.

"A'a wai ya haka ne?meye kuma zaka wani rinka satar kallo na?wllh kurwa ta kurr,inkai maye ne kaci kan ka,haka kawai da wanne zanji?ga wannan marin da motar keyi na gardawa, duk ya dameni, ji nake kamar nayi amai,kuma bazaka barni da wannan bala'in haka ba,saika kafamin wannan idanun naka,masu kama da kana jin barci?to bana son kallo ehe,ni.....

Bata sami damar ƙara sa wa ba,sakamakon buge mata baki da Aslam yayi cikin fushi.
"Wllh idan ki ka ce zakimin rashin kunya anan zane ki zanyi in cillar dake agurin nan,banza fitsararriyar yarinya kawai"Aslam ya fada cikin fushi yana jifan Islam da mugun kallo.

Islam kuwa kallon sa kawai take tare da riƙe bakin ta,ranta yayi mugun ɓaci.
"Wllh bazan yafe maka ba,mugu kawai,haka kawai kasanya wannan hannun naka mai kama da shebur ka kwaɗamin abakina? Allah saiya saka min wllh"ta faɗa cike da jin haushin sa.
Shima cikin jin haushin yadda take masa rashin kunya,ko tsoron sa bata ji yace "wllh idan baki rufemin baki ba zan yi maganin ki ne agurin nan,wawiya daƙiƙiya marar hankali kawai uban waye yace da kishigo motar?tunda qarin gardawa take?saidai inkece gardiyar da tasanya motar wari,dan kuwa ke kin ma fi bunsuru wari"ya fada cikin mugun fushi yana figar motar da mugun gudu.
Ji kake ƙummm!!
Kan Islam ya bugu da jikin kujerar,da sauri ta dafe kan nata tare da runtse ido.
"Wllh duk baƙin cikin ka sai dai kayi ka barni amma nidai nan gani nan bari,kuma bazan fasa faɗin kai mugu bane,dan ba tsoron ka nake ji ba wllh sai Allah ya saka min kuma wllh ni bana wari koda ban sanya turare ba,dan Ni bana amfani da banzan turare na ƙasar nan ma "Islam ta fada afusace idanun ta na kawo ruwa,Amma tsabar taurin rai irin na Islam tayi saurin maida hawayen .

Hannu Aslam ya sanya akaro na biyu ya ƙara buge mata baki har saida lips ɗin ta ya fashe.
Kuka Islam ta sanya tana mai kallon jinin data gogo daga lips dinta,cikin kuka da jin haushi ta kama dukan Aslam tana faɗin "Allah ya isana mugu,kalli yadda ka fasamin baki?wllh sai na rama,bashi ka ɗauka azzalumi kawai"Islam ta fada cikin kuka tana dukan gefen kafadar Aslam.
Tsayar da motar Aslam Yayi dai-dai sun kawo bakin store ɗin,wanda yake mallakina Aslam ɗin ne,dan haka haɗe hannayen ta yayi guri ɗaya tare da zaro manyan idanunsa da sukayi jaaa,saboda ɓacin rai yace "wllh idan baki nutsu ba zan miki dukan tsiya cikin motar nan,kuma in jefar dake anan gurin bani da asarar komai,banza maƙarya ciya,gidan uban wa kike shafa turaren kasar wajen ? Gara ki min shiru ,ki nutsu,dan nan ba gida bane,inkin ga dama ki fito "yana faɗin haka ya warɓar da hannayen nata tare da ɓude motar yayi ficewar sa.
Bakin ciki kamar ya kashe Islam,wllh bashi ya ɗauka,saita baƙanta masa kamar yadda ya baƙanta mata itama,kuma wllh duk baƙin cikin sa, saiya siya mata ƙayan nan,kuma wllh lodar kayan zatayi dan yayi asarar kudin sa.tana gama wannan tunanin tayi saurin fitowa tare da bin bayan sa, tana share hawayen da ya maƙale gefen idon ta,dama kukan nata ba wani hawayen kirki.

Lokacin data fito harya kusan shigewa cikin store ɗin,dan haka da sauri ta cimma sa, tana balla masa harara.

Juyowa yayi ya kalle ta cikin yatsina yace "ashe dai zaki fito ƙaramar tsagera"
"Ai badan kai na fito ba,ra'ayin kaina ne yasa na fito"ta faɗa cikin tsiwa tana murguda masa baki.
Banza yayi da ita suka shiga cikin store ɗin,aikuwa nan da nan ma'aikatan gurin suka fara gaida Aslam,cikin girmamawa da nuna farin cikin su,dan ya jima baizo gurin ba,komai ta online yake gudanar wa.
Taɓe baki Islam tayi ganin yadda suke ta wani girmama Aslam,
Cikin jin haushin su tace "aikin banza wahalallu marasa aikin yi,ku rasa wanda zaku girmama haka sai wannan saƙaƙon,mtssss"ta buga uban tsaki tana riƙe ƙugu.

Sukan basu fahimci inda zancen nata ya dosa ba,amma shikam oga Aslam, Sarai ya gane da shi take,banza yayi da ita gudun karta tsinkashi gaban ma'aikatansa,
Ɗaya daga cikin ma'aikatan gurin mata ya umarta akan ta raka Islam ta zabi abinda take bukata.
Shi kuma ya shige wani ɗaki.

Aikuwa cikin girmamawa matar wacce zatayi sa'ar jannat tace "to ƙanwata muje ko"ta faɗa cikin sanabe tana kallon Islam da murmushi.

Wani banzan kallo Islam ta wurga mata kafin tace "ke dalla Malama bana son iyayi,wacece ƙanwar taki?kinga nayi kama da ƙanwar ki?kije can ki nemi ƙanwar ki ba Islam ba,bana son shishshigi,ki wuce kawai kiyi abinda aka saki"Islam ta fada cikin yarfi.
Aikuwa sosai budurwar nan taji kunya tare da haushin Islam, dan ma ba mutane agurin, ita tunanin ta Islam ƙanwar Aslam ce,ita kuma aduniya tana bala'in son Aslam, shine take son kama ƙafa da Islam ɗin,saidai taga wannan yarinyar bata da kunya.dan haka simi-simi ta ja babban kwando tare da yin gaba Islam tabi bayan ta.

Ba ƙaramin kaya Islam ta debo ba, dan kwandon ma saida yayi kaɗan ta riƙo wasu ahannun ta.
Budurwar nan sai hararar Islam take ,ba damar yin magana dan tana tsoron rasa aikin ta.
Haka suka zo gurin biyan kudi aka lissafa, kuɗi sun doshi dubu dari uku da hamsin,dan kaya masu tsada Islam ta zabo,wasu ma ba amfani zatayi da suba,kawai ɗiba take tana zubawa cikin keken,banda gayyar ƙananan kaya data lubgo,da kayan cinye -ciye.

Koda aka fadawa Aslam kuɗin kayan mamaki yayi sosai,amma bai nuna damuwa ba,ya basu atm yace su cira, duk da sun nuna ba sai an karbi kudin ba,amma yace a'a su cire kawai.
Haka aka loda kayan cikin Boot ɗin motar Aslam.
Ta jima zaune cikin motar tana ta cin chocolate ɗinta,data ɗauka cikin waɗanda ta lubgo,kafin Aslam ya shigo cikin motar.
Kallon ta yayi yadda ta ke cin chocolate ɗin ta hankali kwance.
Kafin ya jinjina kai ya tada motar.haushi fal cikin ransa.

Maimakon suyi hanyar gida sai kawai Aslam ya wuce gurin shagunan sa,da ake dinka zallar hulunan sawa, masu kyau da tsada,suna tafiya ta buga wani uban tsaki wanda yasan ya Aslam saurin juyowa ya kalle ta.
Cikin haɗe rai tace "kaga malam dan juya kamaidani wancan shagon,dan nayi mantuwa,naga wata alawa kuma ban ɗauko ba" ta faɗa kamar tana bashi umarni.

"Saboda ubanki ne ya bani kuɗin ko?baki san zafin neman su ba kika kashemin kudi wajen kwata million sannan yanzu kice in koma zaki ɗauko alawa,ai ko da kuɗin babanki na gina store ɗin baki isa ki sani na koma baya ba"ya fada cikin ɓacin rai.

Sai lokacin Islam ta san wai ashe gurin ma nashi ne.duk da zagin uban ta da yayi, ya matukar ƙona mata rai amma saita haɗiye ɓacin ran tace "kash!! Wai kana nufin gurin ma namu ne?amma me yasa baka faɗa min ba? Ai wllh da yau duk wanda taje siyayya gurin bazai biya ko sile ba,amma ba komai za'a tara gaba, abu namu maganin akwabemu,bari nayi saurin shanye waɗan nan uban alawowin dana ɗebo in yaso saina sake sabon shiri"ta fada cikin murmushi idon ta akan Aslam,Wanda yayi galala yana kallon ikon AllahWato ma ita abinda tayi bai dame ta ba,wata barnar take ƙoƙarin sake yi masa?hmmm,ya ga da uban da zata dawo store ɗin.
Ƙyale ta yayi baice mata komai ba,dan gani yake magana ma da ita ɓata lokaci ne,dan haka yayi mata banza,tana ta neman maganar ta,har ta gaji tayi shiru ganin bazai kula ta ba,haka tayi ta shan chocolate ɗin nan,data shanye zata ɗauki wata.

Har suka zo gaban manyan shagunan nashi,buɗe motar yayi tare da ficewa,kuma ya kulle motar,koda Islam tayi yunkurin fitowa ,akulle taji ƙofar,tsaki tayi tace "aikin banza ya kulle motar,ko nufin sa inyi zaman jiran sa anan?kamar wata baiwar sa?to uban me ma zaiyi agurin nan,maimakon ya kaini gida shine ya wuce yawon karuwancin sa dani,dan gurin nan da da gurin karuwai yayi min kama,gashi nasan janbu yana can yana nema na"ta fáda tana wani taɓa baki tare da gutsirar chocolate ɗin ta.

Shikuwa Aslam,Yana zuwa shagon suka gaisa da ma'aikatan sa ,cikin mutunta wa da girmamawa,kai tsaye ya wuce babban office ɗin da yake zama idan yazo.
Office ne haɗaɗɗe mai kyau,harda ƙatuwar katifa ta huta wa,dan haka,bayan sun kama lissafin kuɗi da managern sa na gurin,kan karifar ya haura tare da kwanta wa, tunani kala-kala cikin ransa,yanzu idan ya auri yarinyar nan,ya makomar auren nasu zata kasance?shin akwai ƙa'idajjen lokacine da zai sake ta ko kuma zama zasuyi tayi har abada?amma ta yaya zama zaiyi ahaka?bata sonshi,shima baya sonta?Allah yasa anayin auren suga iyayen ta, sukuma suce basu yarda da aurar musu da yarinya da akayi ba,dan haka dole ya sake ta,shikenan komai zai zo masa cikin sauƙi, ya zama dole gareshi ma ya fara neman iyayen nata cikin sirri,ta yadda zasu bayyana cikin sauri koma kafin ayi auren,amma ta yaya zai zauna da mace kuma ba tare da yana samun nutsuwa da ita ba?shidai bazai taba zubar da girmansa yazo gurin wannan abar da sunan neman hakkin sa ba,tabb!! ALLAH ma ya kiyaye wannna ranar.
gashi yayi alƙawarin bazai ƙara ƙetare gonar da bata saba,duk da shi iyakarsa romance ne,amma yaga illar yin hakan,kuma ya tuba, Wanda Yayi abayama Allah ya yafe masa.
Haka Aslam yayi ta saka da warwara cikin ransa,yana cikin haka barci ɓarawo yayi gaba dashi.

Islam kuwa tun tana cin chocolate ɗin nan cikin marmari, har tazo ta fara gundurar ta, gaba ɗaya ta zubar masa da bawon chocolate har Kan seat din da yake zama,kuma duk dan neman magana tayi,ta ɗora ƙafar ta akan gaban motar.
Tsaki ta farayi ganin har lokacin bai dawo ba,sai masifa take ita kaɗai cikin mota,Bama wanda yasan da mutum cikin motar,tunda irin baƙin glass ɗin nan ne ajikin motar.
"Aikin banza kawai,yazo ya shanya mutane cikin wannan akwalar motar tasa ya tafi yawon karuwan cin sa,wllh zai dawo ya sameni,saiya bani bayanin inda ya tafi ya barni cikin wannan gwangwani nasa,anfaɗa masa Ni mai gadi ce?mugu kawai "Islam ta faɗa cikin jin haushi kamar ta kwalla ihu,dan kusan awarta ɗaya cikin motar bai dawo ba.
Wasa-wasa Islam fa tayi awa kusan uku cikin motar,ga yunwa da ciwon ciki dake damun ta, dan ba shan wasa tayiwa wannan chocolate ɗin ba,gashi dama ƙarshen wata ne,riƙe take da cikin ta tana juya kai,dama irin wannan lokacin tana shan wahala idan zatayi period,bare kuma yanzu ta haɗa da zaƙi.
Sai murƙususu take rike da cikin ta,tun tana daure wa,har ta fara kuka tana ambaton sunan Allah"innalillahi wayyo Allah cikina,zan mutu! wayyo baya na la'ilaha'illallahu muhammadar rasulullu, Wayyo Allah na, cikina !ciki!!abinda Islam ke ta faɗa kenan tana rike da marar ta dake azabar ciwo kamar zata balle tana kuka.
Gashi wannan lokacin ba malamin ta,dama shike bata magani da ta fara wannan ciwon.
Yanzu kuma ba mataimaki sai Allah,inka ganta saita baka tausayi,nan da nan lokaci ɗaya tayi ramar dole kamar marar lafiya
Aslam kuwa bai farka daga wannan nannauyan barci ba,saida aka fara kiran sallah,ahankali yayi miƙa tare da karanta addu'ar tashi daga barci tare da buɗe idonsa.
"barci nayi kenan?"ya fada cikin cool voice,kafin ya mike ahankali,ya shiga toilet,alwala yayi bayan ya kama ruwa,ya fito,saida ya gabatar da salla yana zaune kafin ya tuno da Islam cikin mota.dafe kai yayi da sauri yana runtse ido,harga Allah ya manta da ita, da sauri ya duba agogon Rolex dake hannunsa,kusan awa huɗu yayi yana barci, subhanallah,idan wani abu ya same ta cikin mota fa?ko kuma tana buƙatar yin wani uzurin? Wayyo sam baiji daɗi ba,dan bashi da nufin cutar da ita irin haka.da sauri ya mike ya zari wayar sa da car key Yayi waje cikin hanzari.
Yana zuwa ya buɗe motar yana kallon inda take zaune,
Cikin tsoro da firgici ya shiga cikin motar tare da zaro ido ya kallon islam cikin tsoro.
Dan zuwa wannnan lokacin tuni Islam ta sume tsabar zafin ciwo,hannun ta rike da marar ta,ta ɗora kanta akan seat ƙafafun ta dire aƙasan motar.
Cikin tsoro da hanzari Aslam.ya dagota yana jijjiga ta, cikin tashin hankali ya fara kiran sunan ta karon farko arayuwarsa" ke ISLAM !buɗe idonki mana,menene ya sameki?Islam !Islam!!ya faɗa cikin ruɗu yana jijjigata, innalillahi karfa yarinyar nan ta mutu?me zai cewa su mommy? "ya salam" ya faɗa yana haɗata da jikin sa ya rungumeta tsam yana jin wani irin zafi cikin ransa.....

Muje zuwa masu karatu


Mrs babi ce
Anty mammy.
[10/1/2022, 9:03 PM] Abk: ____________"Ya Salam,ke !Islam tashi mana,menene ya sameki?am sorry I don't mean to do that,barci ne ya ɗauke ni, Islam Please wake up"Aslam ya faɗa cikin damuwa yana kallon fuskar ta,wacce hawaye ya gama bushewa.
Ko motsi Islam batayi,sai yadda ya juya ta kawai take binsa,cikin hanzari ya maidata kan kujera tare da ɗaura mata seat belt ya kunna motar tare da janta aguje yayi asibiti da ita.
Yana zuwa asibitin ya kira family doctorn su cewar yana tafe da petient.
Doctorn yace masa ya shigo da ita office ɗin sa kawai.
Aikuwa yana facking ɗin motar, ya buɗe ya fito,sannan ya zagayo inda Islam take ya ɗauke ta cak! Kamar yar tsana ,dan sam Islam bata da nauyi.
Kai tsaye ya nufi office ɗin doctorn da ita.
Kwantar da ita likitan yace yayi akan wani gado dake office ɗin,kwantar da ita yayi tare da tsayawa yana kallon ta,bai taɓa jin tausayin ta irin na yau ba,kuma sam bai ji daɗin abinda ya same ta ba.

Tambayar sa likitan yayi mai ya sameta har ta suma,
"Doctor I have no idea kawai na ganta asume bansan menene yayi silar suman ta ba,kawai ka duba ta"cewar Aslam Yana kallon likitan.
Ruwa likita ya fara ɗaura mata,kafin ya fara ƙoƙarin ganin numfashin ta ya dai dai ta.
Cikin nasara kuwa ta farfaɗo,saidai tana farkawa ta tashi da ciwon marar.dafe marar ta tayi tana kuka."wayyo Allah marata zan mutu,Aslam kazo ka kaini gida,wayyo Allah na"abinda ta tashi dashi kenan tana murƙususu,jikin ta har rawa yake.
Da sauri Aslam ya riƙe hannun ta yana faɗin"sorry Islam yanzu zamu tafi gida,kuma maran naki zai daina ciwo kinji"ya fada cikin tausayawa ganin yadda take ta haɗa zufa jikinta na rawa.
Allura likitan yayi mata,dan ya gane meke damun ta,kuma yana tunanin ko tasha kayan zaƙi ne.yana mata allurar kuwa cikin ƙanƙanin lokaci marar ta lafa mata sosai,ta daina murƙususun.tayi lamo kan gadon idonta arufe,ba abinda take rayawa cikin ranta,sai irin matakin da zata ɗauka kan Aslam.
Can suka koma kan kujera shida likitan yana faɗa masa,ai period ne zai zo mata,kuma da alama ta sha zaƙi, sannan irin hakan tana kasancewa ga ƴan matan da basu san maza ba,wasu magani yana musu aiki,wasu kuma dole sai idan anyi musu aure sun tara da namiji,kafin suke daina wannan ciwon marar.

Shiru Aslam Yayi Yana sauraron likitan har ya kammala bayanin sa,ahankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da yiwa likitan godiya,sannan ya buƙaci arubuta musu magani su tafi gida,tunda jikin nata da sauki,gashi tun safe suka fito yanzu kuma yamma tayi.

Haka likita ya rubuta musu magunguna,dai -dai lokacin kuwa,tuni ruwan da aka sa mata ya ƙare,likitan ya cire mata.
Cikin sanyin murya da tausayi Aslam yace "zaki iya tashi ne,ko ina taimaka miki?
Banza tayi dashi kamar bataji me yace ba,dan mugun haushinsa take ji matuka,wato tasan da gangan ya barta cikin mota,kuma ya kulle,dan kawai ya tsane ta, yana kuma son ta mutu,badan Allah yasa da kwanan ta agaba ba aida tuni ta sheƙa,zaiyi bayani ne wllh"ta faɗa cikin zuciyar ta tana mai ci gaba da kwanciyar ta.
Ba irin maganar da Aslam baiyi mata ba,amma tayi biris kamar batajin sa,ƙoƙarin ɗaga ta yayi ganin bazata tashi su tafi ba,
Amma sam taƙi yarda ya taba ta,ɗaya kawo hannu zata buge hannun .yasan haushin sa take ji,amma ai shima bada son ransa yayi mata hakan ba,shine take wani neman raina masa hankali dan taga yana lallaɓata,nan take shima ransa ya ɓaci,cikin tsawa yace "ke dalla malama ki tashi mutafi,In kuma anan zaki kwana sai nayi tafiya,dan ina da abubuwa masu muhimmanci agabana" Aslam ya fada cikin fushi yana hararar ta.
Ko ci kanka Islam batace masa ba,kuma batayi yunƙurin tashi ba.hakan ya karasa hasala Aslam,sai huci yake ransa ya gama ɓaci.
"Kayi mata ahankali Aslam,kasan yarinya ce kuma bata da lafiya , bari nayi mata magana "cewar likitan yana dafa kafadar Aslam tare da kallon Islam ,wacce ke kwance ko motsi batayi.
Murmushi likitan yayi yana mai cigaba da kallon Islam dan lokaci guda yaji ta kwanta masa cikin ransa, kyakykyawa da ita mai saurin shiga rai.
Ahankali ya matsa kusa da gadon da take kwance, ɗan leƙa fuskarta yayi,dan ta basu baya.cikin taushin murya da sigar rarrashi ya fara mata magana"
" Sannu ko, Ƙanwa ta,yi hakuri ki daure ki tashi,In kuma kina jin ciwo ne saiki faɗa min, In baki magani kinji?yi haƙuri daure ƙanwa ta"likitan ya fada cikin taushin murya sosai.
Hararar likitan Aslam Yayi,aransa yana cewa "ji banza yadda yake wani maƙale murya kamar wani mace,wawa kawai"Ya fada cikin zuciyar sa yana harara likitan da yaji haushinsa ya kamashi lokaci guda,ganin yadda yake yiwa Islam magana kamar wani saurayin ta.
Aikuwa ahankali Islam ta yunƙura tare da zama akan gadon kafin ta sauƙo daga kan gadon ahankali,fuskar nan Tata amatuƙar ɗaure.ta nufi ƙofar fita daga office ɗin ta fice.
Binta sukayi da kallo dukan su,Aslam wani bakin ciki ne yake nuƙurƙusar zuciyar sa,wato shida yayi mata magana tayi banza dashi, saboda ta maidashi ɗan iska,amma wannan garan yana mata magana ɗaya, tabi umarnin sa, lallai ta raina shi,ko gidan uban wa ma tasan wannna banzan da har zataji maganar sa sama da tashi.rai bace shima ya nufi ƙofar office ɗin da takardar maganin ahannunsa.
"To Aslam Allah ya sawake agaida gida,Please akula da petient sosai saina zo dubiya"likitan ya fada cikin murmushi yana kallon Aslam dake barin office din.
Ko ci kanka Aslam baice masa ba yayi waje da sauri,tare da buga ƙofar da ƙarfi,ji kake buumm ! Ƙofar tayi ƙara.
Saƙare likitan yayi yana bin ƙofar da kallo,meye kuma ya ɓatawa Aslam Rai haka?ko dai ɓacin ran yarinyar ne yasashi wannan fushin?any way,koma dai menene shiya shafa,shikam yaga mata,kuma zaibi sawu,dan yarinyar ta tafi da imanin sa, masha Allah ga diri.
Aslam kuwa cikin ransa yake faɗin"shege, gidan ubanka zaka zo?wllh duk randa naga wannan shegen agidan mu da sunan yazo gurin Islam,saina ci uwarsa,daga zuwa ya duba ta shine yake wani shishshige mata.
koda ya ƙarasa Islam bata cikin motar,mamaki ne ya kamashi,to ina kuma ta tafi?ko wane gurin tayi kuma?kamar wanda akace ya duba hanyar fita daga asibitin,aikuwa ya hango Islam har ta kusan ficewa daga asibitin.
Dafe kai yayi tare da lumshe idonsa,to gidan uwar wa zata?wa tasani anan?wannan yarinyar nema take ta zame masa matsala arayuwa,salon tayi wani gurin ta ɓata,ace da gangan ya batar da ita,ta ja masa damuwa.
Shiga yayi cikin motar tare da bin bayanta,lokacin har ta fice daga asibitin,ƙafar ta ko takalmi babu,ta miƙe kwaltar tana tafiya abinta.
Gabanta yasha da motar tare da tsaya ya buɗe mata ƙofar motar, alamun wai ta shigo.

Ko inda motar take Islam bata kalla ba,ta zagaye motar taci gaba da tafiyar ta.ƙara tarar gabanta yayi tare da buɗe motar yace "bazaki shigo bane ko yaya"ya fada cikin faɗa da ɗan tsawa.
Sake kaucewa tayi tare da ci gaba da tafiyar ta duk da yadda takejin jikin ta ba kwari,gashi marar ta na mata ciwo kaɗan -kadan, amma ta gwammace tafi aƙasa,akanta shiga motar sa
.cikin haushi da ɓacin rai Aslam ya fito yayi kanta,yana zuwa bai jira wata-wata ba ya sure ta ya juya gurin motar da ita.
Dukan sa Islam keyi cikin haushi da kunar rai tana zille wa,tare da faɗin.
"Dalla malam ka sake ni, bana son iskanci,Wanda kaje kayi bai isheka ba shine zaka rinƙa tabamin jiki,dalla saukeni bazan shiga motar taka ba,banza mugu kawai" abinda take fadi kenan cikin ɓaci rai tana dukan sa da son kwacewa.amma riƙon da yayi mata bazata iya kwacewa ba,har ya sanyata cikin motar ya kulle tare da zagayawa mazaunin driver ya shiga shima. kuka mai tsanani Islam ta sanya tana tureshi tare da dukan ƙirjinsa.
"Ka budemin na fita bana so !bana so" abinda take fadi kenan Muryar har sarƙewa take.kana jin yadda sautin kukan ke fita kasan taji zafin abinda Aslam Yayi mata matuka.duk yadda yaso riƙe hannayen dan ta daina ƙoƙarin dukansa, kin yarda tayi,bori kawai take masa cikin mota tana kuka da kai masa duka,ganin haka yasashi kawai ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam-tsam.ta yadda dole ta haƙura da dukan nasa tayi lamo kan faffaɗan ƙirjinsa tana kuka mai sosa zuciya.

Lumshe ido Aslam Yayi Yana sauraron kukan tana,yana jin ba daɗi cikin zuciyar sa.duk da irin yadda yake jin ya tsane ta,amma dole yaji ba daɗi cikin ransa,tunda shine silar wannan kukan Nata.
Islam kuwa ta riƙe gefen rigar sa ƙam _ƙam tana kuka sosai harda shashsheƙa.....


Hmmmmm masu karu anya kuwa waɗan nan mutane ?
Muje zuwa dai.

Mrs babi ce
Anty mammy.
[10/2/2022, 10:02 PM] Abk: _____________Islam kuwa riƙe take da gefen rigarsa tana kuka mai shiga zuciya.kusan minti goma suka ɗauka cikin wannan halin,kafin ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinsa,jingina bayanta tayi jikin kujera tana share hawayen dake zubowa daga idanunta.
Kallonta Aslam yayi fuskar sa ba yabo ba fallasa,kafin ya tada motar suka nufi gida.
Kafin su ƙara sa gida ya tsaya ya sai magungun da likita ya rubuta masa, tana zaune cikin motar bata uhmm,bare uhm -uhm. Sai zuciyar ta dake ƙara cika da tsanar Aslam.da tunanin ɗaukar fansa.
Haka ya dawo da ledar magungunan ahannun sa,ya ja motar suka tafi.
Saida Yayi facking ɗin motar sannan ya ga wayarsa dake ta kawo haske,dan a silent ya saka ta.kira rututu yawanci na mommy ne, dan haka kiranta yayi tare da karawa akunnen sa bayan ya gama facking.yana tsayawa Islam

Please Login or Register in order to submit comment