Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farko arayuwarta tayi kwalliya,ba ƙaramin kyau kuwa tayi ba,ita kanta batasan cewar ta iya kwalliya haka ba sai yau.wasu sabbin riga da siket ta dauko wanda bata taɓa sanyawa ba ma,ta sanya.cif suka zauna ajikinta,kamar ajikinta aka dinka.
Haba hips ɗin nan yayi ɗam_ɗam cikin fisis siket din. Ga yar rigarta mai bala'in kyau,Brest cube ɗin nan yayi cas atsaye ƙam kamar zai tsokanewa mutun ido.
Lol.
Kasancewar bata iya daurin dan kwali ba,sai kawai ta daure uban tulin dogon gashin kanta,ta sake jelar baya .sannan ta daura ɗan kwalin ta soke shi ta gefe.haba sai ya bada wani style mai matukar kyau.
Islam da kanta saida ta yaba kyan da tayi.
Murmushi tayi tunowa da Aslam da tayi,ko yaya zaiganta idan ya dawo?ko zaiji dadin kwalliyar da tayi domin shi?
Turare ta fesa ajikinta mai daɗin ƙamshi.sannan ta sanya flat shoe ta nufi part din mommy gurin mommynta.

Gidan cike yake da jama'a ana ta hidindimu.
Duk inda Islam ta ratsa sai an bita da kallo,Masha Allah kawai wasu ke cewa,wadanda suka san Husna kuwa suna mamakin ta yaya Aslam Yana da wanna matar zai auri Husna?
Ba ƙaramin daɗi mommyn Islam da granny sukaji ba,ganin Islam ta sake har tayi wanna kwalliya mai kyau kuma ta shigo cikin jama'a.
Nan sukayi ta rarrashinta da kalamai masu dadi.
Kuma ba laifi ta saki jikinta ba kamar yadda take yi daba, kuma ba komai ke kara karfafa mata gwuiwa ba sai maganar da Aslam yace zai sanar da ita mai muhimmanci,tana kyautata zaton maganar zata faranta mata rai,dan kuwa yanayinsa ya nuna hakan.
Lokaci zuwa lokaci zakaga tayi dan murmushi,Bama idan ta tuno yace itace farin cikin sa,kuma abin tunaninsa.

Kasancewar anyi walima bayan daurin auren,hakan yasa Aslam bai dawo da wuri ba,sai wajen azahar.
Wanda zuwa wannan lokacin Islam ta fara sarewa akan anya kuwa zai dawo.
Tana zaune kan gadon granny ta buga uban tagumi,hancinta ya shaƙo mata daddaɗan ƙamshin Aslam.
Lumshe ido tayi gabanta na faɗuwa.
Ahankali Aslam ya ƙaraso kusa da Islam ya zauna,hannu ya sanya ya zare mata tagumin yana kallonta.
Itama ɗago kanta tayi tana kallon shi.
"Masha Allah Islam ɗita,kinyi kyau matuka kwalliyar ki ta haskaka min zuciya "Aslam ya fada yana riƙe hannun Islam.
Murmushin farin ciki ne ya kwacewa islam,idanunta akan Aslam tace "kace zaka fadamin magana mai muhimmanci idan ka dawo,tun ɗazu nake jiranka"Islam ta faɗa cikin zazzafar muryarta.

"Ina sane Islam ban manta ba,amma tashi mu koma part din mu,saina fada miki acan"cewar Aslam Yana kama hannunta suka fito daga part ɗin mommy zuwa nasu.
Mutane sai kallon su suke,ana ƙus-ƙus.

Kai tsaye ɗakinsa ya shigar dasu.abakin gado ya zaunar da islam,shi kuma ya janyo stool din gaban madubi ya zauna.
Hannunta ya kamo ya rike cikin nashi yana ɗan murzawa ahankali.
Hannun nasu Islam ta bi da kallo,kamar yadda shima Aslam ke kallon hannun nasu dake sarƙe dana juna.
Ahankali ya ɗago kansa yana kallon Islam,kafin ya kira sunanta cikin wata kalar voice"islam"ya fada ahankali.
Wanda saida tsikar jikin Islam ta zuba yummmm, sakamakon yadda harafin sunan nata ya fita daga bakinsa.
Ahankali cikin faduwar gaba Islam ta ɗago kanta ta zuba masa kyawawan idanunta.
Kallon juna suke kamar yau suka fara ganin juna.
Saida ya sauke ajiyar zuciya kafin ya fara magana kamar haka"Islam,bansan ta yaya zaki karbi magana ta ba,bansani ba ko zaki yarda da abinda zan sanar dake yanzu ba,amma nikam na sani har cikin zuciyata haka abin yake.ya dan yi shiru yana sauke ajiyar zuciya,tare dakai hannun Islam bakinsa ya sumbata. Kafin yaci gaba---"islam tun lokacin baya da Bama shiri dake,kina cikin raina,lokuta da dama nakan zauna na bata lokaci wajen tunanin ki,saidai a wancan lokacin ina daukan hakan ne amatsayin kiyayyar dake tsakanina dake,shine dalilin da yasa nake yawan tunaninki,kullum idan ban ganki ba bana jin dadi,ina shiga wani yanayi na damuwa.
Na gwammaci in ganki koda zamuyi faɗa,kece mace ta farko da take kallon cikin idanuna tayi min rashin kunya,kuma ina kasa ɗaukan mataki akanta,kece mace ta farko da idan nayi niyyar yi mata wani mugun abu nakanji bazan iya ba.
Kece mace ta farko data fara kiritamin tunani sakamakon ganin surarta,kece mace mafi ƙarancin shekaru dana taba mu'amalantar ta har nake tsayawa muyi jayayya,kinsan me yasa ?
Saboda inyi ta sauraron muryarki,duk da raina yana ɓaci da irin zafafan maganganun da kike fadamin matsayina na wanda na girmeki,amma ina jin dadin sauraron muryarki,dan ita ke sanyani farin ciki.
Islam bazan taɓa iya cutar da ke ba,koda kuwa ke zaki cutar dani,sannan bana iya jurar ganin wani yana cutar dake,kinsan halin da na shiga lokacin dana kulleki cikin mota?ya fada cikin yanayi na damuwa da jimami.
Kallon sa kawai islam keyi ta kasa cewa komai,mamaki take sosai cikin ranta.duk wannan abubuwan da suke faruwa tsakaninta da Aslam,kenan shi hakan daɗi yake masa?kenan baya jin haushin yadda take masa rashin kunya?
Ci gaba yayi da maganar sa"ji nayi kamar In shaƙe kaina ,sosai naji haushin kaina da kaina,sannan abun da ya kara sanya Ni cikin damuwa, shine yadda mukaje asibiti naga kinki yimin magana,kuma kin saurari likita,wllh awannan lokaci ji nayi kamar In kashe shi,sosai naji haushin ki wanna lokacin.

Sannan lokacin da wannan shegen sergant ɗin ya dakeki, hmmmmm.ya sauke ajiyar zuciya mai cike da ɓacin rai.kafin ya dan matse hannunta yace "ina fita kai tsaye makarantar ku na wuce,wllh badan sunzo da wuri ba zan iya kashe shi, yadda nake jin zuciyata na tafarfasa.
Islam duk waɗan nan abubuwan da suke faruwa bansan asalin meke damun zuciyata ba sai yanzu,Islam zuciyata acike take da tarin farin ciki Aduk lokacin dana tunaki kona ganki"
Shiru Aslam Yayi tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana sumbatar hannunta .
Kallon ta yake ido cikin ido,fuskarsa ɗauke da murmushi mai kayatarwa.sannan yace
Islam yau zan bayyana miki sirrin dake zuciya ta,koda kuwa bazaki karbe shiba,hakan zai rage min raɗaɗin da nake ji game da ke acikin zuciyata.
Islam ina matukar sonk....ƙarar da wayar shi ta dauka ne ya katsar dashi daga maganar da yake,cikin sauri ya dauko wayar tashi.kan kuce me tuni jikinsa ya dau karkarwa,cikin hanzari ya daga wayar yana mai karawa akunnensa.

Kafin yayi magana Husna tace "Honey kayi sauri kazo zamuje gurin dinner kasan yau za'a kawo ni gareka"
Cike da faduwar gaba Aslam ya ce"yadda kika ce hakaza'ayi Madam,ganin zuwa yanzu"
Yana faɗin haka ya ajiye wayar,jikinsa dai rawa yake ,ya nufi toilet.
Cike da mamaki Islam ke binsa da kallo,anya kuwa Aslam Yana cikin hayyacinsa?kodai bashi da lafiya ne?yanzun nan fa yake faɗa mata kalamai masu sanyi,yake sanar da ita irin yadda yake jinta aransa,amma daga kiran waya yama manta da abinda yake?
Kodai karya yake faɗa mata dama?
Yanzu kiran waccan shashashar yafi masa muhimmanci akan faɗa mata abinda ya sanya mata rai akai?
Nan da nan ran Islam ya ɓaci hankalinta ya tashi sosai,me yake son cewa aƙarshen maganarsa?so yake fa yace yana sonta,amma wannan kamar ta katsar dashi.
Tana nan zaune Aslam ya fito daga toilet cikin hanzari yake shiryawa.inda yake cewa islam"Please Islam kiyi hakuri idan na dawo zamu karasa maganar tamu,yanzu ina sauri wani uzuri mai muhimmanci ya sameni"
Ya faɗa yana feshe jikinsa da turare bayan ya kammala sanya wata zazzafar shadda mai shegen kyau.

Kallonsa kawai Islam ta tsaya yi zuciyarta kamar zata kama da wuta.cikin fushi za zafin zuciya Islam ta sauko daga kan gadon ta nufi ƙofa.

Binta Aslam Yayi da kallo kafin ya fara kiran sunanta,amma ina ko inda yake bata kalla ba tayi waje cikin fushi.


Muje zuwa masu karatu.

Please kuyi hakuri na jina shiru kwana biyu,kunsan yanayin jikin sai ahankali .

Idan a jini shiru ayimin afuwa 🙏

Na gode.
Anty mammy ce
Mrs babi.
[10/30/2022, 7:47 PM] Abk: 77/78
____________Binta Aslam Yayi da kallo,kafin ya fara kiran sunanta.
Ko inda yake bata kalla ba,bare yasa ran zata tsaya.
Ficewar ta tayi cike da ɓacin rai,lallai wannan husnan tayi nisa cikin zuciyar Aslam,ita ta rasa me yasa duk irin yadda Aslam ke yin wani abu mai muhimmanci,da zarar ta kira shi awaya yake zama kamar wani sakarai,ita gani ma take kamar tsoron husnan yake,har wani rawar jiki yake idan ta kirashi awaya.

Cikin dakin ta ta shige tare da fizge dankwalin kanta ta jefar dashi,ta fizge ribom ɗin ma ta jefar shi aƙasan dakin tana hararar sa kamar shine yayi mata laifin.
Ji take ahalin yanzu idan da zata ga wanna n Shegiyar Husnan,saita shaƙe mata wuya ta mutu kowa ma ya huta.
Dan taga alama nema take ta rabata da farin cikinta,tun kafin ta shigo gidan kenan,ina kuma ga ankawota cikin gidan?
Dole ta zage itama,ta kowane hali ta ga cewar husna bata rabata da mijinta ba.
Tana zaune tana jiran Aslam ya shigo dan ya rarrasheta. Saidai shiru shiru bai shigo ba,hakan tasa ta mike tare da fitowa daga cikin dakin.
Shiru ba motsin Aslam aɗakin nashi,kodai tafiyarsa yayi?Islam ta faɗa cikin ranta.
Da sauri ta shiga ɗakin nashi,aikuwa baya ciki.
cike da mamaki da mutuwar jiki ta zauna abakin gadon dakin tana kafe kayansa daya cire da ido.

Shikuwa Aslam tana fita yaji wani irin ba dadi cikin ransa,so yake yaje ya bata hakuri,amma yana fitowa ya tsinci kansa da wucewa kofar fita kai tsaye.ba tare da ya ko kalli dakin Islam ba.
Saidai can kasan zuciyarsa yana jin bai kyauta wa Islam ba,amma bazai iya ketare maganar ƙiran da Husna ke masa ba.
Dan haka ya wuce kawai akan idan ya dawo zai rarrashe ta.

Islam kuwa dataga zaman ba abinda zai kara mata sai ɓacin rai,saita tashi ta koma dakin ta,Dan kwalinta ta ɗauko sannan ta fito zuwa falo.tsaye tayi tama rasa me Yakamata tayi.
Ta nan tsaye saiga mommyn ta ta shigo part din,Dan taga ficewar Aslam.
Dama tun dazu hankalin ta yana kan Islam ɗin.
Tana ganin yanayin da Islam ɗin ke ciki,tayi saurin ƙarasowa cikin Falon.
Dan taga kamar bata cikin hayyacin ta ma.ta kure guri ɗaya da ido alamun tayi kisa cikin tunani.
Nan dai mommyn ta ƙaraso tare da kama hannun yarta suka koma cikin dakin ta.
Nan tayi ta mata nasiha da bata shawarwari masu amfani.

Misalin ƙarfe takwas na dare,motocin kawo amarya sukayi jerin gwanon zuwa gidan su Aslam,inda anan amarya ma zata zauna kafin Aslam ya kammala ginin tanfatsetsen gidan sa da yake ginawa.
Ba karya idan ka ga dakin Husna kasan yar gata ce ta gaske. Dan ankashe kudi mahaukata wajen kayata mata dakunan ta zuwa kitchen.

Lokacin da suka kawo amarya Islam na zaune adakinta ita da sauran yan uwansu da suka zo bikin.
Tun daga yanayin da suka shigo gidan kasan ba arziki,dan sai yada habaici sukeyi.haka dai suka gama rashin mutuncinsu suka bar amarya ita kadai adakinta.

Haka ma yan uwan Islam suka rarrasheta sannan suka barta.
Mommyn Islam ma sosai tayiwa yarta nasiha da addu'oin zama lafiya kafin ta bar gidan.
Kuma anan aka bar A'isha dan debewa Islam kewa.

Islam na zaune ita da A'isha,ta rungume yarinyar ƙam ajikinta,zuciyarta na mata zafi sosai,inda Allah ya taimakata ma shine,addu'ar da take cikin zuciyarta.

Ba jimawa ango ya shigo cikin gidan,kai tsaye ya nufi dakin Islam,dan so yake ya ganta,tun ɗazu itace aransa.
Harya kama handle din kofar dakin zai bude ya tsinkayo Muryar Husna "honey ! Ina kuma zaka shiga?bayan kasan yau da gobe da sati guda ma duka nawa ne ?ta faɗa cikin yanayin shagwaba tana nufoshi.
Lokacin har ta sauya kaya daga less din da aka kawo ta dashi zuwa wasu tsinannun nighty,Wanda suda babu ba maraba.gaba ɗaya rabin na shanunta awaje yake.
Da sauri Aslam ya juyo yana kallonta,dan baiyi tsammanin jinta agurin nan yanzu ba.
Murmushi ya sakar mata cike da jin wani irin shaukin ganinta da yayi ahakan, duk da ba wani fasali bane da ita,amma agurinsa gani yayi kamar tafi kowa kyan ƙira da zati.
Nan da nan tsohon tsuminsa ya tashi.
Saidai can cikin ransa yana mamakin yadda daga kawota yau har ta iya yin irin wanna shigar kuma ta fito har babban falon part din nasu.
Saidai idonsa ya rufe dan haka sakin handle din kofar yayi tare da nufota,hannunsa riƙe da ledojin kaji.
Cikeda tafiyar jan hankali Husna ta nufi cikin Falon tana Gara goga turaren dake hannunta a tsakanin ƙirjinta.
Nan take kuwa Aslam ya shaƙi wannan turare,tuni tunaninsa ya gushe ya nufi Husna arude.
Rungume ta yayi sosai ajikinsa yana sakin ajiyar zuciya.
Ba kunya bare kawaici Husna ta lalubo bakin Aslam ta jefa nata ciki ta fara missing dinsa kamar zata cinyeshi.
Abinka da wacce ta jima tana neman wanna damar.
Nan shima ya biye mata suka fara lalube juna,cike da zaƙuwa.

Islam kuwa tana zaune rungume da A'isha taji kamar ana taba kofar ɗakinta.hakan yasa ta kasa kunne amma bataji an shigo ba,saidai tana iya jin maganganu ƙasa-ƙasa, dan haka kwantar da A'isha tayi tare da nufo ƙofar ta fito zuwa falon.
Wata irin faduwa da gaban Islam yayi, saura kaɗan ta fadi kasa.sakamakon arba da su Aslam da tayi suna neman amarcewa afalo.

Da sauri ta dafe bango tare da saurin juyawa ta koma daki.banda bugawa ba abinda gabanta keyi.
Dafe ƙirjinta tayi cike da tarin baƙin cikin abinda idanunta suka gani.lallai na miji ɗan kunama ne,kalli yadda ya barta anan yaje yana lalube wata.
Zama tayi bakin gado ta janyo A'isha jikinta,kawai kuka ya kwace mata.
Sosai ta ƙanƙame A'isha kamar zata karya ta ajikinta,har saida Aishan ta fara mutsu-mutsun tashi kafin ta sassauta mata rikon.
Kuka take ahankali marar sauti,saidai gaba ɗaya jikinta rawa yake.

Su kuwa su husna da gyar Aslam ya kwaci kansa yana haki,idanunsa gaba ɗaya sun rine sun kankance.kamar yadda na Husna ya koma jajur, da gani Husna irin jarababbun matan nan ne masu kokarin tsotsewa na miji ruwan jikinsa idan suka tarfa shi.
Sai wani layi take tana kara kamo Aslam.
Hannunta ya kama suka nufi dakin ta.bayan ya dauki ledar kajinsa.

Suna shiga ya zaunar da ita abakin gado kafin ya nufi kitchen da kansa ya dauko plate da kofuna.
Tana zaune sai mutsu-mutsu take tana tattaba ƙirjinta.
Dibar musu tasu yayi kafin ya dauki leda ɗaya yace "amaryata bari na kai wa Islam wannan na dawo yanzun nan"ya fada yana shafa uban nonuwanta da sukayi rigija cikin rigar barcin.
Yamutse fuska tayi tare da haɗe rai tace "a'a fa bana son shiga hakki honey ka ajiye mata afalo mana ka kiranta tazo ta dauka" ta faɗa cikin haɗe rai tana turo baki kamar shantu.

Dan jim aslam yayi yana kallonta,ganin yadda ta bata rai sai yaji ba dadi,dan haka ya ajiye ledar yana mai cewa"to my love ya kike so ayi"ya fada yana zama kusa da ita tare da rungumeta ta gefe.

"Kawai ma bani na kai mata da kaina inyaso ma saimu gaisa da ita"ta faɗa tana daukar ledar bayan tayi wani tunani cikin ranta.

Ko kaɗan Aslam bai so hakan ba,Amma ji yayi bazai iya mata musu ba.dan haka yana ji yana gani ta dauka ta nufi ƙofar fita daga dakin,cikin wannan shigar tata,ba kunya ba tsoron Allah.

Runtse ido Aslam yayi tare da kwanciya rigingine,sosai yake jin ba dadi cikin ransa,so yake yaje yaga Islam ya rarrasheta,dan yasan zuwa yanzu tana nan cikin damuwa da tashin hankali,ko kuka ma take waya sani.

Husna kuwa kai tsaye ta haifa dakin da take tunanin shine na Islam,kallon wulaƙanci take bin dakin dashi kafin ta taɓe baki ta shiga can uwar dakan ba ko sallama.
Kasancewar Islam ta juya bayanta ne,hakan yasa tayi saurin share hawayen ta jin an bude kofar,dan atunaninta Aslam ne.saidai kuma wani irin warin turarene mai ƙarfi da ya ziyarci hancin ta.
Hakan yasa ta gane ba Aslam bane Dan haka da sauri ta juyo,idanunta suka sauka akan fuskar Husna.
Nan aka fara kallon kallo.
Cike da rainin hankali Husna ke kallo islam, tana wani tabe baki da girgiza jiki.

Islam kuwa kwantar da A'isha tayi tare da mikewa tsaye itama,ƙugu ta kama tare da kanƙantar da ido tace"ke uban me ya kawo ki dakina?har kikazo kina min girgije -girgije kamar bishiyar mangwaro da wannan jikin naki na garada"
Islam ta fadi haka cike da rashin tsoro.

Husna kuwa buɗe baki tayi da mamaki tana kallon Islam,lallai yarinyar bata da kunya,har ita take fadawa waɗannan maganganun kai tsaye ba tsoro?itane mai kama da bishiyar mangwaro?aikuwa dole taci uban yarinyar nan wllh.
Cikin ɓacin rai da jin haushin abinda Islam ɗin tayi mata tace "ke dan uwarki Ni kike fadawa wannan maganar?saboda baki da kunya?ko ba babba agidanku ne"
Husna ta fada cikin hayayyaƙowa islam kamar zata daketa.

"Saidai uwarki dan ubanki,wllh idan kika ƙara zagina zaina ci uwarki ,karuwa marar kamun kai banza kucaka,kuma wllh ki ficemin daga daki kokuma yanzu nayi maganin ki"Islam ta fadi cikin zallar masifa tana nufo Husna.
Husna ma cikin masifa da ɓacin rai tace "lallai yarinyar nan wuyanki ya isa yanka,wllh zaki gane baki da wayo,zaki san kinyiwa Husna rashin kunya"ta faɗa tana jefar da ledar kazar dake hannunta tayi waje,kafin Islam ta ƙaraso. Dan taga yarinyar tsayayyace, kuma da alama zatayi karfi.
Ƙwafa Islam tayi tana mai tura ƙofar ta da ƙarfi tace "shegiya tsohuwar guzuma,da kin tsaya kinga danyen kai wllh"
Ledar kazar ta dauka ta feho ta falon sannan ta kulle ƙofar ta ta koma cikin dakin.
Kwanciya tai tare da rungume A'isha ajikinta,ranta abace sosai.Aslam ya nuna mata iyakarta,wato kazar ma saidai matarsa ta kawo mata?saboda ga mayunwaciyar kaza ko?hmmm duk zatayi maganinsu ne.

Husna kuwa cike da ɓacin rai ta koma ɗakinta buguzun -buguzun.
Tana shiga ta nemi guri ta zauna tana hura hanci.

Da sauri Aslam ya taso yazo gareta yana tambayar lafiya ?Meya faru da ita take bata rai.
"Wannn yarinyar ashe bata da kunya?harni zata kalla tana fadawa magana son ranta?wllh saina koya mata hankali agidan nan,yauma Sa'a taci ina cikin farin ciki amma d saina ci uwarta wllh"ta faɗa cikin huci tana kumbura baki.

Hmmmm shi dama Aslam yasan za'ayi haka,dan dai Husna bata san wacece Islam ma,amma da bazata tunkareta bama.
Cike da son kwantar mata da hankali ya janyota jikinsa yana faɗin"haba babyna karki bari ɓacin rai ya bata mana wannan ranar mana.ki barta kawai kishine ke damunta kawai.amma zan ja mata kunne karta ƙara yiwa babyna rashin kunya"ya fada yana janyota jikinsa tare da fara bata tsokar kaza.

Nan dai suka ci sukasha,tun agurin Husna ta haye cinyar Aslam tana masa salo iri-iri,nan dai aka fara damben arziƙi.
Abin mamaki mai makon aji ango yana zuba sanbatu da surutai,a'a wannan kam amarya ce ta kwace wannan fagen,dan ihu ta rinkayi tana sunbatu da zantuttuka iri -iri.
Kana ji kasan bana zafi ko ciwo bane na jin dadi ne.yayin da ango kuwa gaba ɗaya kansa ya kulle,dan shikam kawai yana yi ne ,amma badan yana jin dadin abun ba, maimakon yaji farin ciki da nishaɗi ma,a'a sai wani irin kunci da ɓacin rai daya mamaye zuciyarsa,duk da bai taba kusantar mace haka ba,amma yasan cewa Husna ba cikakkiyar budurwa bace,dan kuwa kai tsaye yaji ya shigeta ba wani gargada.
Hakan na nufin ba shine wanda ya fara kusantar Husna ba.
Sosai ransa ya ɓaci ,saidai bazai iya tuhumar ta ba ko kaɗan.
Haka ta gama haukanta da sumbatu, yana jinta.
Bayan komai ya lafa ne Husna ta jirkice can gefe tana sharbar barci,yau taji zumar da bata taba dandanar irin taba,ta samu abinda rai da zuciyarta ke so.

Kallonta kawai Aslam keyi,ransa abace sosai ,daga karshe ya tashi ya shiga toilet Yayi wanka sannan ya dawo ya kwanta tare da juya mata baya.
Can cikin dare yana barci kawai sai jin mace yayi ta haye kansa tana ƙoƙarin zare masa wandon dake jikinsa.
Ranar dai Aslam yaga abinda yafi karfinsa,dan gaba ɗaya Husna ta hanashi barci minti kaɗan zai jita ajikinsa.har gari ya waye.
Gaba ɗaya jikinsa ciwo yake,shiba da jin dadiba amma shine da shan wahala.
Wanka ma tare sukayi,bayan sun shirya suka fito falo,sai wani maƙale masa take,shikuma yana riritata kamar jaririya, amma cikin ransa wani irin kunci da ɓacin rai yake ji.
Ga ciwo da kansa keyi.

Muje zuwa

Mrs babi ce
Anty mammy.
[11/9/2022, 11:23 AM] Abk: 79/80
_______________Gaba daya jikin Aslam ciwo yake,shiba da jin dadi ba amma shine da shan wahala,sai yazama tamkar shine amaryar, Husna kuma angon.
Wanka ma tare sukayi,inda badan yayi da gaske ba,a toilet din ma so tayi ta far masa,yana gocewa.
Haka dai sukayi wanka suka fito,bayan sun shirya ne suka fito babban falo,sai wani maƙale masa Husna keyi,duk ta hanashi sakat, shikuma sai riritata yake kamar wata jaririrya, duk da yadda yake jin zafi da radaɗi gami da ƙunci cikin zuciyarsa,haka yake biye mata yana riritata.
Islam kuwa bayan sunyi sallar asuba ita da A'isha,kwanciya suka ƙarayi, sai wajen bakwai na safe kafin suka farka.wanka tayiwa Aisha tare da shiryata cikin wasu riga da wando na jins masu kyau,sannan ta daure mata gashin kanta mai uban yawa.da yake mommyn Islam dibo musu kayansu tayi suka ajiye agidan saboda biki.
Islam ma cire kayanta tayi tare da sanya rigar wanka,wacce ta tsaya mata iya gwuiwar ta,rigar fara ce mai ɗan kauri.
Kanta ba ko huta bare dan kwali,hakan ya ba gashin kanta damar bazuwa gadon bayanta yayin da wani yake zubowa yana ɗan rufe mata fuska,saita sanya hannu ta kawar dashi.
Bayi take ƙoƙarin shiga,A'isha tace ""anty zan sha yoghout"
Juyowa tayi tana kallo yarinyar kafin tace "to jirani nayi wanka saina dauko miki afalo,kinga Ni bani da yoghout anan"ta faɗa tana juyawa dan shigewa cikin toilet ɗin.
"Ni anty ki dauko min kafin kiyi wanka,yanzu zansa"A'isha ta faɗa cikin yanayin murya mai nuna tana son yin kuka,dan A'isha mayyar yoghout ce,bata da wani aiki saina shan yoghout.
Juyowa tayi tana kallon yadda yarinyar ke murza ido da son yin kuka,ahankali ta tako zuwa gaban yarinyar tace "to kiyi shiru karkiyi kuka kinji?bari na dauko miki"ta faɗa tana shafa kan A'isha tare da nufar ƙofa.

Kai tsaye ta bude kofar da zata sadaka da babban falon,ko kaɗan bata kula da su Aslam dake zaune akan kujera ba,wanda Husna ke ta faman kissing bakin Aslam, ta wani zauna rigija akan cinyar sa.
Cikin takunta mai cike da ɗaukar hankali ta nufi ƙaton fridge din dake cikin falon,budewa tayi tare da dauko ƙatuwar jarkar yoghout,sannan ta rufe ƙofar fridge din ta juyo.
Carab idanunta ya sauƙa cikin na Aslam,Wanda tun fitowarta ya ƙureta da idanuwansa,kallonta yake cike da tsantsar so da kauna,yayin da wutar sha'awarta ke ƙara ruruwa cikin zuciyarsa,nan da nan yaji asalamiyyar sa ta fara hanƙoro,ba ƙaramin kyau da shigar dashi cikin shauƙi ganin Islam cikin wannan shigar yayi ba.

Da ƙarfi gaban Islam ya buga sakamakon ganin su da tayi ahaka,nan da nan ta karajin haushin Aslam cikin ranta.Wata uwar harara ta banka masa,taka tsaki mai karfi tare da juyawa cikin sauri ta nufi ɗakinta.
Lokacin ne kuma Husna ta kalli Aslam,Dan gaba ɗaya ta fahimci hankalinsa baya kanta,sannn taji ƙarar tsaki,inda taga Aslam yabi da kallo itama tabi,cike da jin haushi da bacin rai take kallo Islam,da irin yadda take tafiya tana juya jikinta kamar wata tarwada.
Cikin wata murya wacce ita adole shagwaba takewa miji tace"honey ! Kana ganin yarinyar nan,ta shigo mana ba sallama,da sassafen nan,sannan tana yiwa mutane tsaki,kuma bata gaida kowa ba kamar wasu sa'o'inta?gaskiya bazan dauki wannan rainin ba,daga yau karta ƙara shigowa falon nan dai-dai wannan lokacin,ai iskanci ne wannan, da son riskarmu cikin wani yanayin dan tasan duk wata mata mai matsayi yanzu tana tare da mijinta"ta kai zancen ta tana wani kwantar da kanta akan ƙirjin Aslam,tare da shafa kwantaccen gashin dake kwance akan ƙirjinsa.tana bugawa Islam harara.

Ɗan kallon ta Aslam Yayi,kafin ya maida idanunsa kan,Islam,wacce tayi tsaye riƙe da jarkar yoghout ahannun ta, jin abinda Husna ke faɗa.
Juyowa tayi suka haɗa ido da Aslam,hannunta ta sanya wanda ba komai acikinsa,tare da riƙe ƙugunta tana jiran jin amsar da Aslam zai bayar.

Shikuwa cikin kwantar da murya kamar wanda yake jin tsoro husnan yace "baby ki barta kawai,kinga nan babban falone,kuma dole kowa acikinku zai shigo yayi wani uzurin.ki kwantar da hankalin ki,ki barta ta rinƙa shigowa tayi uzurinta"ya fada yana shafa gefen fuskarta,aƙoƙarinsa na kwantar mata da hankali.

Taɓe baki Islam tayi cike da jin haushin amsar da Aslam ya bayar,wato dai idan ta fahimta fa kamar tsoron Husna yake?
"Gaskiya honey nikam za'a takura min,haka kawai da sassafen nan,mutum yana hutawa da mijinsa adameshi da sintiri?nikam kawai ka hanata shigowa falon nan"Husna ta fada tana turo baki da juyar da kanta alamun tayi fushi.
Kafin aslam yayi magana Islam ta rigashi.
"Da yake nan ɗin gidan ubanki ne, shine zaki ce karna ƙara zuwa falon nan ko?
To bari kiji koshi mijin naki matsoraci wanda yake yiwa mace biyayya,bai isa ya hanani shiga duk inda nake so agidan nan ba,kuma wllh ina gargaɗin ki,ki fita hanyata, dan wllh idan kika cika min ciki saina koya miki hankali.banza mai siffar akori kura,anƙi agaidakin kiyi duk abinda zakiyi "Islam na kaiwa nan azancen ta bankawa Husna harara tayi juyawarta ta shige dakin ta.dama ta kusan shiga ɗakin.
Wani

Please Login or Register in order to submit comment