Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanya tare da zare rigar jikinta ya zama daga ita sai bra da wando short nicker iya gwuiwa.
Duk abinda yake tana jinsa,amma saboda yadda take jin zafin zazzaɓi ko yunƙurin hanashin batayi ba.sai kare ƙirjinta da tayi da hannunta ahankali.
Kallonta kawai yayi yana jin tausayinta sosai cikin ransa.
Haka Aslam Yayi ta tsoma towel ɗin nan cikin ruwan yana shafa mata ajikinta.
Banda nishi ba abinda Islam keyi, idonta akulle.ya jima yana shafa mata ruwan ajikinta har saida jikin yayi sanyi.ba jimawa kuwa barci ya ɗauke islam.ɗaukarta yayi tare da kaita daki kan gado ya kwantar da ita sannan ya fito.
Haka suka kwana yana kula da Islam sosai,hatta abinci abaki yake bata,da tayi wani motsi zaice meke damunta?sosai Islam ke mamakin iya kula da marar lafiya na Aslam,ashe yana da kirki ?yana da tausayi?dubi yadda yake tattalinta kamar wata ƙanwarsa.sosai take jin daɗin hakan kuma.
Ko Yau da safe ma bayan ya haɗa mata ruwan wanka tana kwance yazo ya zauna kusa da ita.ahanakali ya kira sunanta"Islam" cikin taushin murya.
Buɗe ido Islam tayi tare da saukesu akansa.dama ba barci take ba.
Ahankali ya kai hannunsa saitin wuyanta ya taba yaki koda zazzaɓin,ba zazzaɓi ajikinta hakan yasa yaji daɗi,murmushi yayi mata yace " sannu, meke damunki yanzu?
Ahankali Islam ta lumshe ido tare da girgiza masa kai alamun ba komai.
Hannunta ya kamo ahankali yana dubawa,ba kumburin saidai alamun ciwon,dan jiya ya sa mata magani dama agurin.ahankali yake shafa hannun nata mai tsananin taushi,
Lumshe ido Islam tayi saboda yadda tsikar jikinta ta zuba lokaci guda,ji tayi kamar yana mata tafiyar tsutsa,dan haka cikin sanyin jiki ta zare hannunta.
Kallonta yayi yace "ya kamata kiyi wanka saikici abinci da magani,ga ruwa can na haɗa miki"ya fada yana kallonta.
Jinjina kai Islam tayi tare da yunkurawa ahankali ta tashi zaune,tana riƙe da bargon data lullaba dashi,dan ba riga ajikinta,daga ita sai bra.
Fahimta Aslam Yayi kunyar tashi take ahakan.
Dan murmushi yayi yace "ki tashi mana kin riƙe bargo kodashi zakiyi wankan ?"
Ya fada yana ƙoƙarin cire bargon.
Da sauri ta kara ƙanƙame bargon tare da turo baki tace "Bafa riga ajikina ,kuma ahakan zan tashi ?"ta faɗa cikin sanyin murya tana karya wuya.
Murmushi yayi kafin yace "to menene dan mata ta tashi gaban mijinta ba kaya?
Nan gaba ma Ni zan saka miki kayan da kaina"ya fada yana ɗan kallonta kasa _ƙasa.jiya wato saboda bata da lafiya ne yasa ta tsaya ya cire mata rigar,hmmm zaki tsara yarinya duk sanda kikazo hannuna.ya faɗa cikin zuciyarsa.
Kallonsa tayi itama tare da ɗan buɗe baki,irin na mamakin nan.amma bata ce komai ba kuma bata tashi ba.
Ganin da gaske bazata tashi ba ne,yasa ya miko mata babban towel yace idan kina bukatar wani abu kiyimin magana ina falo"yana faɗin haka yayi waje.
Sosai Islam ta bishi da kallo,hakika sai yau tasan ashe Aslam Yana da kirki,yadda take zaton sa ba haka yake ba,murmushi tayi tana daura towel ɗin sannan ta shiga toilet.
Tana fitowa ta ga kaya akan gado,harda inner wear nan ta sanya bayan ta shafa mai da turare.saidai bata sanya bra ba,kuma bata zuge zif ɗin rigar ba,saboda ciwon bayanta yasha iska sosai.
Tana kammalawa ya shigo dakin,ganin harta shirya yace "ya kikasa riga kuma ban sami ki maganin ba?
Shiru tayi bata ce komai ba,dan haka kawai taji tana jin nauyin sa yau din.
Ƙarasowa yayi ya kama hannunta ya zaunar da ita kan stool ɗin dake gaban madubi,sannan ya ɗauki maganin,ba tare da ya sauke mata rigar ba yake shafa mata maganin tunda zif ɗin azuge yake.
Shiru Islam tayi idanunta alumshe,sosai take jin daɗin yadda yake shafa mata maganin,saitaji kamar susa yake mata.harya kammala idonta alumshe yake.
Kallonta yayi yadda ta wani lumshe ido alamun tana jin dadin abinda yake mata.
Tsintar kansa yayi da jin dadin hakan shima.saida yayi dan murmushi sannan ya ranƙwafo da kansa saitin kunne ta yace" ya dai ?ko kina jin daɗin yadda nake taba bayan naki ne inci gaba?dan naga kamar baki san na kammala shafa maganin ba"
Da sauri Islam ta buɗe idonta tare da zarosu waje,sai kuma ta turo baki cike da jin kunya ta tashi daga kan stool ɗin tana mai cewa"Ni wllh ba wani daɗi danake ji ba,kawai zafine yasani kulle idona,karkamin sharri"ta faɗa tana barin dakin. Dafe ƙirji tayi cike da jin kunya,da gaske fa bata san ya gama shafa mata maganin ba,ko me take tunani oho?
Shikuwa Aslam dariya yayi tare da ajiye maganin,yana jin wani daɗi cikin ransa, shidai kai tsaye bazaice ga abinda yake ji game da Islam ba, amma yasan yanzu yana jin tausayinta sosai,sannan baya son ganinta cikin damuwa,gashi idan basa tare yayi ta tunanin ta kenan.
Hmmmm muje zuwa malam Aslam.

Yau koda Aisha tazo makaranta, haka tayi ta neman Islam amma bata ganta ba,sosai yarinyar ta shiga damuwa,har aka tashi bata da wani walwala.ko abincin ta ƙinci tayi,ta saba Islam ke bata a baki suna hira tana ta shirmen ta da bata labarin yan gidansu.
Dan haka akan hanyarsu ta koma wa gida kawai takama kuka,duk rarrashin da driver Yayi mata taƙiyin shiru,har suka isa gida,nan mommyn ta ke tambayar ta dalilin kukan, cikin kuka tace"mommy yau antyna batazo makaranta ba,Kuma dama jiya naga kamar zatayi kuka,sannan jikinta da zafi"ta faɗa cikin muryar kuka.
Ahankali kyakykyawar matar mai nutsuwa da cikar haiba, ta zauna kusa da ƴar Tata tare da rungumeta ajikinta,sannan ta fara magana"kiyi hakuri uwata kinji,antynki zata zo makaranta gobe,may be wani abunne ya hanata zuwa"
"Mommy kullum antyna sai tazo school bata fashi sai yau, nidai mommy ki kaina gurinta"A'isha ta faɗa cikin kuka.
Shiru mahaifiyar Aishan tayi,dan tasan rigima irin ta A'isha,idan ta kafe akan abu to zai wahala ta sauka.dan haka cikin dubara tace "yanzu ki bari sai gobe, idan kinje makaranta Kinga antyn naki bata zoba,to sai muje gidansu mu dubata ko"
Cike da jin dadi yarinyar ta gyada kai tana dariya.nan dai mahaifiyar Tata ta bata abinci taci akayi mata wanka.

Bayan kammala cin abinci Islam ta koma kan kujera ta zauna,magunguna Aslam ya dauko tare da nufota, tana ganin haka ta haɗe fuska tare da kawar da kanta gefe,alamun bata so.
Shikuwa kusa da ita ya zauna har suna gugar jikin juna,bare maganin yayi tare da buɗe ruwa yace "oya haa"ya fada yana bude bakinsa.
Shagwabe fuska Islam tayi cikin shagwaba tace "Ni wllh bana son wannan maganin ɗaci gareshi"
Ta fada tana matsawa nesa da Aslam.
Matsowa Yayi shima tare da cewa"idan kika tsaya kika sha ahankali bazakiji ɗacin sa ba,maza karbi kisha"ya fada yana sake miƙo mata maganin.yunkuri tayi da nufin sake guduwa,yayi saurin rukota ya rungumeta agefen hannunsa na dama tare da tura mata maganin abakinta,sannan ya kafa mata bakin jarkar ruwan.
Dole tasa Islam haɗiye maganin nan,saidai yana cire gorar ruwan ta fara karin amai.
Cikin sauri ya ɗago fuskarta ,ganin da gaske amanzatayi kawai ya haɗe bakinsu guri ɗaya .

Muje zuwa masu karatu.

Mrs babi ce anty mammy.
[10/14/2022, 8:37 PM] Abk: __________Ganin da gaske Islam amayar da maganin nan take ƙoƙarin yi,shikuma baya son tayi Aman maganin.dan haka kawai sai ya haɗe bakinsu guri ɗaya.
Luf kakejin Islam ta kwanta jikin Aslam tare da maida amanta, dan tuni ta daina kakarin aman.
Shikuwa Aslam kissing din baƙinta yake cikin shauƙi da tausayawa,dan shi da nufin tsayar da Aman Yayi mata haka,amma sai abin nasu ya zarce ba zato ba tsammani kawai yaji Islam ta kamo harshen sa tana masa wani irin tsotsa mai sanya zuciya narkewa,zaro ido yayi cike da wani irin tsantsar farin ciki marar misaltuwa,haƙiƙa yayi matuƙar jin daɗin wannan respond din da Islam tayi.bai taba tsammanin zata iya biye masa ba.
Cikin azama da farin ciki Aslam ya ƙara kamo kan Islam yana kissing ɗin ta cike da nishaɗi,Islam ma na maida masa martani,wanda sam ba ma tasan tanayi ba,ita dai kawai yanzu tasan tana matuƙar son Aslam Yayi kissing nata koya taba wani sassa na jikinta,tana matuƙar jin daɗin hakan.
Sunyi nisa sosai banda romancing ba abinda Aslam keyiwa Islam,gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa,sai nishi yake,jikinsa har rawa yake,ita kuma Islam ko kaɗan batayi yunkurin hanashi ba.

Ƙararrawar da ake ta bugawa aƙofar part ɗin nasu itace tayi silar katse musu wannan farin cikin da suke ciki.
Tun ɗazu Aslam kejin bugun ƙararrawar amma yayi shiru abinsa.
Saida hankalin Islam ya kai mata kunne ya can ƙofar taji karar, sannan tayi saurin raba jikinta dana Aslam,tana sauƙe numfashi da gyara rigarta.
Da sauri ta miƙe ta nufi bakin ƙofar dan budewa,Aslam dake jin kansa yana yawo cikin sararin samaniya yayi saurin cafkar hannunta,idanunsa alumshe yana girgiza mata kai.alamun karta buɗe tayi zaman ta.
Zare hannunta tayi tace "naji kamar Muryar granny fa"ta faɗa tana nufar ƙofar dan an ƙara buga ƙararrawar.

Tana budewa kuwa sukayi ido hudu da granny,cikin murna Islam ta rungume granny tana faɗin "oyoyo granny na,shigo daga ciki mana"ta faɗa tana kamo hannun granny zuwa cikin falon.
"Ai gani nayi tun jiya banganki kinzo can gurin mu ba,shine nace bari dai ninazo na duba ko lafiya,idan kuma kina buƙatar wani taimako saina taimaka miki naga yau ma baki tafi can makarantar ba"cewar granny tana zama akan kujera.
Zama Islam tayi kusa da granny tace "wllh granny jiya nayi zazzaɓi ne after school shiyasa ban zoba,amma yanzu nake shirin zuwa dama"Islam ta faɗa tana murmushi.
Aslam Yana zaune banda hararar granny ba abinda yake,kawai tazo ta katse masa jin dadin rayuwa,yanzu bashi da tabbas ɗin sake samun wannan damar nan gaba.
Kallon sa granny tayi tare da yatsine fuska tace "to ɗan tijara da kake hararata dan nazo gidan ka,wllh baka isa ka hanani zuwa gidan nan ba,dan kuwa jikata na nan ehe ,kuma wllh kasan Ni, kasan halina dan In zage mu ba hamata iska ba wani babban abu bane agurina" granny ta faɗa cikin gatsine da fuska.
Ita dai Islam dariya kawai take tana kallon kaka da jikan nata.
Hararar Aslam ya ƙara bankawa granny kafin yace"ai wllh kekam kin cika katsewa mutum hanzari,yanzu da kikazo mana da wannan sassafen me zaki mana?ko kuma sa ido kikazo?ya fada aƙufule dan da gaske yaji haushin yadda granny ta katse masa hanzari sosai.
"Kai kasani ja'irin yaro marar kunya,dan nazo gidan ka shine kake jin haushi,wllh daga yanzu inna ga dama nan zan dawo da zama ma baki ɗaya,inyaso naga yadda zakayi marar kunya kuma yau anan zan wuni"cewar granny itama tana hararar Aslam.
Wani kallon me kikace Aslam yayiwa granny kafin yace "lallai ashe wanda ya mutu zai dawo,wato kizo ki hanani hutawa nida gidana ko,kiyi ta samana ido nida matata,wllh ban yarda ba. Sai kuma ya sassauta murya yana magana cikin rarrashi kinga matar kiyi hakuri ai dani dake bata ɓaci kije ki huta anjima da kaina zan rakota gurin ki haba tawan"Aslam ya fada cikin salon rarrashi .

"To ai kaine Asalamu dan nazo gidan ka kake min tsiya,dama Ni ba zama zanyi ba,ƴata na dubawa,kuma ma naga kamar abinda nake tunani bai faruba, dan haka bari na tafi"granny ta faɗa tana mikewa.suma mikewar sukayi,Aslam Yana jinjina tsurku irin na granny wato zuwa tayi tagani ko yayi making luv da Islam ne,yasa tun jiya basu ganta ba?hmmmm ƴar sa ido kenan.

Har bakin ƙofa suka raka granny.ga mamakin Aslam sai yaga Islam na ƙoƙarin bin granny.cikin sauri ya janyo Islam tayo baya.ɗan marairaice fuska yayi yana raɗa mata"ina kuma zaki?"
Cikin dan basawar Islam tace "zanbi granny part ɗin mommy"
Kallonta Aslam Yayi yace "to nan ɗin me yayi miki?keda baki da lafiya Please ki zauna ko zuwa yamma ne sai kije"ya fada yana ɗan haɗe fuska.yama za'ayi tace wani zatabi granny? bayan gashinan yana zaune agida kuma saboda ita.
Cikin wani salo na jan aji Islam tace "Ni bana son zama nan Ni kadai ne,gara can ɗin cikin mutane kuma nafi jin daɗin zama acan"ta faɗa tana ƙoƙarin tafiya.
Lallai ma yarinyar nan,kenan shi ba mutum bane? Wato bata jin dadin zama tare dashi ai kuwa wllh ba inda zata.
Dan haka cikin kama kai yace"wuce mukoma cikin gida bazaki bita ba"ya fada yana bata hanya fuskarsa ba wasa.
Turo baki Islam tayi tana dan bubbuga kafa cikin kukan shagwaba take cewa"Ni wllh saina je Ni bana son zama anan Ni kadai"ta faɗa cikin salon ta mai hargitsa tunani ko ina na jikinta motsi yake,kai kace da gangan take motsawar.
Saƙare Aslam yayi yana kallon Islam,dan ba ƙaramin tafiya tayi da imaninsa ba,ganin bazai iya jure kallonta tana neman gigita shi ba,kawai ya sungumeta yayi cikin Falon da ita.
Kan kujera yayiwa kansa masauki, ita kuma ya zaunar da ita akan cinyarsa.
Sai wani narkewa take ajikinsa tana kukan shagwaba.
Shikuwa Aslam kamar wani sokohaka ya rungumeta ajikinsa yana shafa kanta.
"Is ok baby kiyi shiru ba nace anjima za kije ba?kinga yanzu safiya ce ki zauna ki huta,kuma ina gida bazanje ko ina ba,zan zauna in tayaki hira kinji?Aslam ya fada cikin wata ƴar ƙaramar murya mai cikeda taushi,shi kansa baisan ya iya irin wannan Muryar ba saiyau.
Cigaba tayi da shura kafa kamar wata yarinya yar goye tana faɗin ita wllh saita je gurin mommy,shikuwa Aslam ya wani shashance sai rarrashin ta yake tana kan cinyarsa ya rungumeta ajikinsa kamar wani zai kwaceta.
Shiru Islam tayi tare da ƙara shiga jikin Aslam,tana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi ajikinsa.can kasan zuciyarta kuma tana jin wani irin sanyi da daɗi,ji tayi kamar su dawwama cikin wannan yanayin,har cikin zuciyarta takeji Aslam,batasan me yasa idan tana tare dashi yanzu,jinta take kamar wata yarinyar yar goye,sannan tana jin farin ciki sosai cikin ranta.
Bangaren Aslam shima jinsa yake kamar wani sarki,Aduk lokacin da yake tare da Islam,barin ma kwana biyun nan,yana yawan samun kansa da tunaninta ko kuma yayi ta murmushi yana tuna rigima irin ta Islam,ko fita yayi Allah-Allah yake ya dawo gida ya ganta.sosai yake jinta har cikin zuciyarsa.
Shidai bazai ce sonta yake ba,amma yasan yana matukar son ganinta cikin nishaɗi sannan baya son ɓacin ranta.
Gyara kwanciyarta Islam tayi tare da rungume Aslam ta baya batare da sanin tayi hakan ba.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Aslam ya saki tare da kaiwa goshinta sunbata.
Buɗe ido tayi suka ƙurawa juna ido na kusan minti biyu,kafin Islam ta ɗan turo baki tace "me yasa kayi kissing ɗin forehead ɗina? "
Ta fada cikin turo baki .
Murmushi yayi kafin yace "sabona nawa ne,ina da ikon yin kissing ɗinsa,bama shiba ko Ina ajikinki mallakina nane,so ba laifi bane dan nayi kissing din forehead ɗinki"ya fada idanunsa akan lips ɗin ta yana wani lumshe ido.
Turo baki tayi tace "nidai a'a jikina nawa ne bana kowa ba"

"Kin tabbata da abinda kika faɗa?"cewar Aslam .
Dan murguda baki Islam tayi kafin tace "eh mana da jikin na waye idan ba nawa ba?nike da iko da kayana saina so wani zai taba"ta faɗa tana wani fari da ido.
Dariyar gefen baki Aslam Yayi cikin zuciyarsa yake fadin"aikuwa yanzu zan nuna miki nike da iko da jikin naki,zanyi maganin ki yarinya.
Ba tare da wata -wata ba Aslam ya ɗago Kan Islam ya manna bakinsa kan nata.
Cikin dan yunkurin bogi ta fara ƙoƙarin kwacewa,saidai kawai taji hannun Aslam inda batayi tsammani ba,zaro ido Islam tayi tana rarraba su,jin yadda Aslam ke yamutsa mata hazo. Tun tana ɗan motsin ƙwacewa har ta saki jikinta itama ta biye masa suka lula duniyar romance.


Koda Aisha taje makaranta washe gari bataga Islam ba har aka tashi,hakan ya sanyata cikin damuwa sai haɗe rai take tana son kuka, ranar ya Hisham ne yazo ɗaukan ta,matashine da bazai wuce 16 yrs ba,Amma jin dadi da huta yasa idan ka ganshi zakayi tunanin ya haura 20 ma. kyakykyawa dashi kamar Aisha.
Tana ganinsa ta tafi da gudu ta rungume shi tana kuka"shafa kanta yayi tare da durƙusawa daidai tsayinta kafin yace"babyna menene ?fadamin ke dawa kike kuka?ko kunyi faɗa da antynki ne?Hisham ya fada cike da kulawa yana shafa kan yarinyar.
Cikin muryar kuka tace "ya Hisham yauma antyna bata zoba,Ni dai ka kaini gurinta"ta karasa da karawa kukanta sauti.
Shiru yayi yana kallon yarinyar,yasan irin ƙaunar dake tsakaninta da antyn nata,dan haka cikin sigar rarrashi yace" to kiyi shiru daina kuka zamuje ki ganta,amma sai munje gida kinyi wanka kunci abinci,sai mu tafi tare da mommy kinji?"ya fada yana ɗago kan A'isha.
Jinjina kai tayi tana share hawayen idanunta tace "thank you ya Hisham I luv you"ta faɗa tana rungumeshi.
"Luv You too my sweetheart"shima ya fada cike da ƙaunar ƙanwar tashi.
Tunani ya fara ta ina zasu samo gidan su Islam,dan yasan mommy ma bata san gidan ba.yana tsaye yana ɗan kallon farfajiyar makarantar saiga wata ɗaliba ta fito,da alama dai moninta ce.
Da sauri ya karasa gurinta yana tambayar ta ko tasan Islam? Aikuwa yar budurwa taga kyakyakywan yaro cikin iyawa tace bata santa wacce Islam ɗin yake tambaya ba yayi mata bayani yadda zata gane.nan ya kira A'isha dan tayiwa budurwar bayani.
Aikuwa kasancewar kusan kowa yasan Islam da Aisha,hakan yasa budurwar na ganin Aisha tace "ok Islam antyn Aisha kake nufi?
Da sauri ya gyada mata kai alamun eh.
Cikin yanga da kwarkwasa ta bashi address ɗin gidan su hanan ,dan tasan gidan tunda hanan kawarta ce sosai.
Godiya yayi mata sannan ya ɗauki Aishan suka tafi gida.

Aikuwa la'asar nayi, mommy ta kira wayar Abba ta sanar dashi batun zuwa gidan su antyn A'isha ,nan yace sai sun dawo,kuma ya bada sallahun ayimata tsaraba mai kyau ,ace daga Abban A'isha.

Ƙarfe hudu da minti arba'in 4:40 pm suka isa ƙofar gidan su Aslam,cikin rantsatstsiyar motar su,bisa jarogancin Hisham,zo kuga murna gurin A'isha ,kamar zatayi me acikin mota sai tsalle take suna mata dariya,sun lodowa Islam tsara kala-kala.
Mai gadi ne ya buɗe musu ƙofa bayan sun sanar dashi sunzo gurin masu gidan ne.
Yayi musu iso mommy tace su shigo ciki.
Da sallama suka shiga cikin Falon,Wanda mommy,granny da kuma hanan ke zaune suna hira da kallo,Aman baya nan ya fita yawonsa.
Amsawa su mommy sukayi gaba ɗaya tare da kai kallonsu bakin ƙofar,cikin azama mommy da granny suka mike tsaye baki buɗe suke kallon matar dake tsaye cikin tsantsar shock da mamaki tana kallonsu...

Wacece wannan matar ?
Muje zuwa masu karatu.

Anty mammy ce.
[10/17/2022, 12:53 PM] Abk: __________Azabure mommy da granny suka mike tsaye,tare da kafe matar dake tsaye bakin ƙofa cikin shock da ido.
kallon -kallo aka fara tsakanin matar da kuma su mommy.jikin granny Banda rawa ba abinda yake ta kasa cewa komai sai kallon matar kawai take,itama matar idonta na Kan granny,ganin abin take kamar almara,ahankali ta lumshe idonta tare da hadiya wani yawu mai ɗacin gaske,sannan ta buɗe idonta yayin da wasu hawaye Masu matuƙar zafi da ciwo suka zubo daga idanunta.
Cikin rawar murya mommy tace "Saratu! Ke ce nake gani ko idanuna ne ke min gizo"ta faɗa tana ƙara murza idanunta dan tabbabar da abinda suka gane mata.
Kuka sosai Saratu ta sanya tana mai jijjiga kai,nan take abubuwan da suka faru abaya suka fara dawo mata tamkar an kunna amajigin kallo.
Cikin kuka mai tsanani tace "nice anty Aisha,nice ba gizo idonki keyi ba"ta faɗa tana takowa cikin Falon da sauri tana jin wani irin raɗaɗi cikin zuciyar ta.
Gaban granny tazo ta durƙushe cikin matsanancin kuka ta kama ƙafar grannyn tana faɗin"bansan da wane baki zan nemi yafiyar ki ba uwata,domin nasan cewa niɗin mai laifice agareki,kin bani tarbiyya kin kula da rayuwata,amma nabiyewa son zuciya da ruɗin soyayya na tafi na barki,banyi tunannin wane hali zaku shiga ba,amma wllh nayi hakan ne dan ceto rai,dan Allah ummata ki yafe min ki gafarceni "Saratu ta fa ɗa cikin kuka mai tsuma zuciya.
Awannan lokacin granny ma kuka take,yayin da can cikin zuciyarta take godewa Allah daya dawo mata da ɗiyarta abin sonta,wacce ta rabu da ita shekaru masu tarin yawa,yau gata agabanta sun ga juna kafin ta bar duniya.ahankali granny ta sanya hannu ta ɗago Saratu dake kuka kamar ranta zai fita,hannu ta sanya ta share mata hawayen idanunta kafin tace "na jima da yafe miki Saratu,ban rikeki cikin zuciyata ba,kullum fatana ki dawo gareni yau Allah ya cika min burina Saratu na yafe miki"granny ta faɗa tana mai rungume ƴarta ajikinta.
Kuka suke sosai cike da kewar juna,mommy na tayasu,Hanna tana tsaye tana kallon ikon Allah,kamar dai Hisham da A'isha,suma mamaki suke ina kuma mommy tasan wannan matar da suka rungume juna suna kuka.
Sun jima suna koke-koke kafin suka zauna kan kujera.
Kallon granny Saratu tayi tace "umma ina yayana?matar yaya yaranmu nawa yanzu?ta faɗa tana juyowa ga mommy.
Cikin murmushi mommy tace "yaranki hudu,Aslam,Aman,jannat sai kuma hanan"ta faɗa tana nuna hanan.
Ahankali ta dafa kan hakan tace "Allah sarki sannu yata niɗin mamanki ce kinji"ta faɗa tana rungumar hanan.
Kallon su Hisham granny tayi,kobata tambaya ba tasan wannan jikokin ta ne,dan haka cikin murmushi tace "ku ƙaraso mana yan jikokina Ni kakar kuce, nice na haifi mahaifiyarku"granny ta faɗa tana mai miƙa musu hannu alamun su taho.
Ahankali Hisham ya ke takowa,cikin farin cikin da ya tsinci kansa,koba komai yau yaga dangin mahaifiyarsa,kullum dama Faransa kenan.Aisha kuwa da gudu tazo ta haye kan cinyar granny tace"kece kakata?jinjina kai granny tayi tana shafa kan A'isha tace "nice kakarki yarinya "
"Amma me yasa baki taba zuwa gurin mu ba,muma bamu taba zuwa ba,kullum mommy sai tayi kuka tana son ganin ki,abba ne yake rarrashinta"A'isha ta faɗa tana ɗan marairaice fuska irin na tausayin nan.
Shafa kanta granny tayi tace daga yau bazata ƙara kuka ba,zakuyi ta ganina tare da ku".
Nan dai suka zauna suna ta alhini da nuna kewar juna,sun ma manta da batun zuwa gurin Islam da sukayi.
Tuni mommy ta kira daddy ta bashi labarin daya sakashi tsantsar farin ciki,nan da nan ya nufo gida.
Haka ma Hisham ya kira Abbansa ya sanar dashi,sunga ahalin mommyn su.nan shima yace yana hanya.

Islam kuwa suna can suna shan barci ita da Aslam,bayan sun gama romancing juna,wanda Aslam yaso ya angonce awanna lokacin amma Islam taƙi yarda sam,ta nuna masa tsoro take ji kuma lokacin hakan baiyi ba.
Da gyar Aslam ya samu ya daidaita kansa,tare da rungumarta suka kwanta,jikinsa sai rawa yake,hakika yana matukar cutuwa,shi dama gashi Allah yayi shi da sha'awa mai ƙarfi sosai,kuma yanzu baya bin matan banza bare yace zai sami nutsuwa acan garesu.haka suka kwanta barcin wahala yayi gaba dashi.
Duk da Islam taji tausayin sa sosai,Bama yadda taga jikinta na matukar karkarwa,idanunsa har ruwa suke,amma haka ta waske,bata son sakar masa jikinta ,saita gama fahimtar inda ya dosa,ita kam ta gama yarda azuciyar ta,cewa ta kamu da son Aslam,kuma shima tana ganin zallar soyayyarta cikin idanunsa,amma tana son saiya furta mata da kansa,kafin ta sakar masa jikinta.da wannan tunanin itama barci yayi gaba da ita.

Ahankali Aslam ya buɗe idonsa da sukayi masa nauyi,kallonsa ya kai kan Islam wacce ke kwance kan ƙirjinsa tana barci,ba kaya ajikinta sai bargon da suka rufe jikinsu dashi. Shafa kanta yayi yana jin wani abu na taso masa can ƙasar zuciyar sa game da ita,saidai har yanzu ya kasa gane menene wannan abun.kissing koshinta yayi tareda murmushi . Cikin nutsuwa ya mayar da ita kan follow kafin ya tashi ya nufi toilet,ruwan wanka ya haɗa musu sannan ya fito.
Ɗaukar ta yayi caak!bai zame da ita ko inaba sai cikin abin wankan daya cika da ruwa.
Da sauri Islam ta buɗe idonta tana kallon inda take.
Turo baki tayi tana ƙara yin kasa cikin ruwan ,dan kar Aslam ya kalle mata jiki .
"Nifa barci nakeyi shine zaka kawo Ni nan?wllh ka mayar dani ba yanzu zanyi wanka ba"Islam ta faɗa cikin shagwaba tana turo baki.
Murmushi yayi yace "haba baby lokacin salla yayi fa ,zamu makara "ya fada yana janyota jikinsa.
Haka sukayi wankan nan,tun Islam na nokewa har tasaki jikinta,ganin shi ko kaɗan baya wani jin kunyarta.saima wasa da yake da sassan jikinta.
Bayan sun shirya sunyi sallane, Aslam yace zai je super market,ya duba yanayin yadda gurin ke tafiya.
Islam kuma dama part din su mommy zata shiga.
Tare suka fito cikin yanayi na nishadi da farin ciki,suna tafe suna dan hira yayin da hannunsu ke sarke dana juna.
Kai tsaye part ɗin mommy suka nufa.gab da zasu shiga Islam taji an rungumota ana ihun "antyna oyoyo antyna "
Cikin zaro ido da tsantsar farin ciki Islam ta buɗe baki kafin ta ɗago A'isha,wacce fitowar ta kenan daga cikin Falon da nufin zata dauko teddyn ta amota kawai ta ga antynta.
"Babyna kece yau agidan mu? Waye ya nuna miki?keda wa kuka zo?"Islam ta faɗa tana rungume A'isha.
Cikin zumuɗi A'isha tace "nida mommy na da ya Hisham,kuma anty kinsan me?Islam ta girgiza kai tana kallon A'isha.
Riƙe haba yarinyar tayi cikin iyayi tace "mommyn mu ta rungume wata tsohuwa tana kuka,shine tsohuwar tace wai ita kakarmu ce,suna can ma suna ta hira kuma abban mu ma yace zaizo"yarinyar ta

Please Login or Register in order to submit comment