Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wata uku"Daddy yace "kuma dai shine kuma ka yarda?"Mahmud yace "to ya zan yi tunda amaryar ta zamana ƴar rigima" Daddy yayi murmurshi mai sauti yace "to Allah kai mu ya sa alkhairi zuwa wannan lokaci Ammi ɗin ka ta ɗau nauyi ba za ayi hidimar biki da ita ba"Mahmud yace "kai haba?kar dai ace ciki ne da ita?"Daddy yace "ban tabbatar ba amman alamu sun nuna"ya faɗa ya na shafar kumatun ta,wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Mahmud yace"to sai an jima akwai abinda zan yi"Daddy ya katse kiran ya maida hankalin sa gun sahibar shi ya na bata kulawa.






Laulayi mai tsanani Ammi ke yi wannan ya sa Daddy ya tafi Mai Jan Gero ya tawo da ƙanwarsa Yusira ta na yiwa Ammi ƴan aikace-aikace wannan abu ba ƙaramin baƙanta ma Atine rai yayi ba musanman da ta lura kulawar Daddy ga Abbasi ta soma yin ƙasa.
Ganin wankin hulla zai kai ta rana ya sa ta fara biyar malumai burin ta cikin jikin Ammi ya zube,sai dai ya ƙi zubewa ya na zaune daram duk da irin harin da ake kawo mata ta mafarki wani sa'in har azahiri sai a rinƙa bata tsoro tun ta na ganin abu ita ɗaya har Yusira ta fara gani ita ma wannan ya sa Inna ta dawo gidan kwancakwakwam da zama.
Suratul Baƙara Inna ke sakawa safe da marice wannan ya sa gidan ya dawo normal,haka Ammi ta cigaba da rainon cikinta wanda ya samu soyayyar uwar miji da ƙanwarsa da shi kansa mijin .
Inna irin mutanen nan ne uwanda ba sa shakka sannan ta na da ilimi sosai na addini ɓangare guda kuma zamanin Kakani da Iyaye an yi harakar aljannu wannan kenan.
Cikin Ammi na cikin wata na biyar Mahmud yayi aure ,tun daga lokacin ya canza ba kasafai ya ke zuwa gidan Daddy ba saboda ya samu matar mai irin aƙidarsa ko kuma nace cutar hassada dan kuwa ita ke zuga sa ta na cewa ya na aikin mi har abokinsa ya fi shi kuɗi ya kamata shi ma ya ƙoƙarta ya kai kamar Daddy shi kuma da ya ke sakarai ne sai ya ke ɗaukar huɗubarta ya je ya na duƙushi gaban bokaye.
Lokacin haihuwar Ammi da yayi ta haifo ɗanta namiji mai kama da uban shi,ƙiri-ƙiri Atine ta fitar da hassadar ta na cewa "ko ba'a son ka a haife ka a farin iyee duk wanda za'a haifa bayan Abbasi na ya ke dan haka kar ma ayi mani gwalgi"Ammi ba ta tankata ba sai Inna ce ta shiga masifa mai shige da nasiha da kuma hannun ka mai sanda.
Sosai Atine ta ji tsoron furucin Inna a zuci tace "kar dai Inna ta gani lokacin da na keci tsumman in shiga uku?amman wlh ko ƙasa da bisa za su haɗe sai na kaiwa boka wannan ƙyalen ke da haihuwa kuma sai ta lahira"ta na gama zancen zucinta ta ja hannun Abbasi suka shige ɓangaren su.
Ranar suna aka raɗa masa da sunan Mahamadu amman su na kiran sa da Mahomet.
Mahomet na cika shekara ɗaya da ƴan watanni matar Mahmud ta haihu ta samu ƴa mace wacce aka raɗa ma Balkisu to daga wannan lokacin ne Daddy da Mahmud suka fara takun saƙa ,kowane da ra'ayin shi wanda ya sha banban da na ɗan uwan sa.




Mahmud kasuwar saffarar ƙwaya ya yiwa Daddy tayi shi kuma yace ba zai yi ba wannan dalili ya fara yin kayarsa shi ɗaya duk da ba haka ya so ba,so yayi in sun fara ya haɗa ma Daddy tarkon da zai ƙare rayuwar sa gidan yari.






Ruwan sanyi da jus da fruits ne gaban su amman rigimar da su ke ta hana su ci "har abada ba zan taɓa mara ma rashin gaskiya ba, Mahmud ka tsaya ka yiwa kan ka hisabi tun nan duniya sanadin kai yaran mutane sai haukacewa su ke amman kai ko a jikin ka sai ma sabbin kalolin mugayen ƙwayoyi kake kawowa wlh in ba ka bari ba zan tona ma asiri"Daddy ke faɗa cikin ɗaga murya,kukan kura Mahmud yayi ya shaƙe Daddy yace "ai sai in ka na da ran za kaje ka tona min asiri amman in na zama ajalin ka ai shikenan"Daddy ya fuzge ya hankaɗe Mahmud yace "in ba ka yi ajalina ba ni nayi na ka ta hanyar gurgunta rayuwar ka da muguwar fuskar ka"daidai nan Mama Balkisu ta shigo "subahanallah!mi mijina ya yi maka kake son kashe sa?"Daddy bai tanka ba ya fice ,nan Mahmud ya shiga zana mata ƙarya da gaskiya ita kuma ta yarda ta na mai sake jin wata irin tsanar sa.




Daddy na zuwa gida sam ya kasa nutsuwa da wannan lamari na Mahmud,da Ammi ta lura ta tambaye shi lafiya yace babu komi.
An yi haka da kwana biyu aka nemi Mahmud aka rasa,har gida Mama Bilkisu ta zo da kukan ta .
"Dan Allah in kai ka sa a ɗauke min Mijina ka taimaka ka sa a sake shi na roƙe ka"da mamaki Daddy yace "wane mijin na ki wai Mahmud?"cikin kuka tace "wa ni ke da dama in ba shi ba,tun ranar da kuka yi wannan fitsaniyar nace ya zo ya baka haƙuri saboda furucin ka na sai ka kashe sa bai zo ba sai jiya yace min zai zo wajen ka shikenan ban ƙara ganin sa ba"da alamar tashin hankali Daddy yace "wai gaske kike ko wasa?"cikin sake tabbatarwa Mama Bilkisu ta rantse da Allah.
Daddy fita yayi zuwa police station ya shaida masu ɓatan abokinsa domin kuwa duk lambobinsa ba sa shiga.
Tsawon kwana biyu ƴan sanda na bincike amman shiru kake ji,tun daga wannan lokacin Daddy ya ɗaukewa Mama Bilkisu duk wani nauyi kama da abinci zuwa suturu.






Bayan wasu shekaru
Tuni Mama Bilkisu ta manta da Mahmud amman ta ƙi ta yi aure sai ma wani dogon buri da ta ɗora kan Balkisu wacce jefi-jefi sukan je gidan Daddy.
Yau ma hakan ce ta faru su na zaune zaman biki na Yusira wacce aka ɗaura ma aure yau,shagali ake sosai su Ammi su ne gaba.
Mahomet da Abbasi an yi wanka an saka kaya iri ɗaya,a lokacin Abbasi na da 11year da wasu watanni yayinda Mahomet ke cikin 10years.
Bayan sallar Asar aka raka amarya gidanta wanda ke can Madarumfa,sosai Mahomet ya sha kuka kafin a tafi da shi.
Inna na gida kwance ta rinƙa jin motsi ɗakin Daddy,har za ta tashi sai kuma ta share ta cigaba da laziminta.
An ɗauki tsawon lokaci kafin ta ga fitowar Mama Bilkisu daga ɗakin jikinta sai tsuma ya ke,da sauri Inna ta lumshe ido tayi kamar ta na barci har sai da ta fice sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Daddy.
Takardu ne duk zuzube a ƙasa da alamu bincike tayi a ɗakin,Inna ta duƙa ta gyara wajen tsaf har za ta rufe drower idonta ya sauka ga hoton Mahmud cikin mugun yanayi fuskarsa duk jini da alamu dukan sa ne aka yi.Ɗauko hoton tayi ta na son gane ko wanene amman ta kasa saboda kamaninsa sun canza sosai,taɓe baki Inna tayi tace "ko ina ya rakito wannan na san bai wuce labaru ne na jarida"ta maida hoton ta ajiye kafin ta koma falo.
Bayan kwana biyu kamar yadda Daddy ya saba ya tafi gidan su Mama a tsakar gida ya tarar da Balkisu ta na rubutu da ƙasa ta na ganinsa ta rugo ta rungumesa ta na cewa "oyoyo Uncle"ya na dariya yace "ina Mamar ki?" "Ta na ɗaki ta na kuka"da sauri Daddy ya wuce sallama a bakinsa,ido jawur ta ɗago ta dube sa sai kuma ta ƙara fashewa da kuka "subahanallah lafiya kike ta kuka har haka mi ke faru?"Balkisu tace "wai Baba ta tuna haka tace min jiya "nasiha ya fara yi mata amman ci kanka ba tace masa ba har tashi jiki a sanyaye zuciyarsa sai bugawa ta ke da ƙarfi.
Tun daga wannan rana abu ya canza in ya zo ba tayi masa magana sai dai yayi hira da Balkisu,tun abun na damunsa har ya saba.




Bayan shekara ɗaya tuni an maido Yusira wajen haihuwa.
Yusira ce zaune Inna na fama shafa mata ruwa a goshi ko ta samu sauƙin naƙudar da ta ke,an ɗauki lokaci sosai duk matan gidan na kanta Atine ta zuba wani turare cikin garwashin wuta ko minti biyu ba'a yi ta haifo ƴar ta macce.
Ido biyu ta ke ganin wani abu kamar dodo ya na shan jinin haihuwar da ya zuba,gefe kuma Atine ce ke wangale mata baki wanda babu haƙora sai wani ƙaton halshe mai yanka-yanka kafin kuma ta fice daga ɗakin.
Kalmar shahada ta shiga jerowa ta na son rumtse idonta amman abu ya gagara har sai da rai yayi halin sa,faɗar tashin hankali da Inna ta shiga ɓanar bakina.
Mahomet wanda tun ɗazu ya ke bakin ƙofa saboda an hana su shigowa idonsa da kuma kunnensa suka jiyo masa abinda babu wanda ya gani sai shi,bai faɗa ma kowa ba sai bin bayan Atine da yayi wacce ta fito afujajen kamar wacce ta yi ma sarki ƙarya.




Jingina yayi da bayan ƙofa bayan idonsa sun gane masa kayan tashin hankali wanda suka fara juya kwanyar sa,da sauri ya ƙara kasa kunne jin kukan Atine ta na cewa "na shiga uku malam mutuwa?dama kallon da na ga ta na yi min mutuwa ce za tayi ? Innalillahi wa'inna iley raji'un malam ba mu yi haka da kai ba,miyasa tun farko ba ka gaya min har da kisan kai ba?"motsin da taji ne ya saka ta yin shiru ta nufo ƙofar sam Mahomet bai san da zuwan ta ba sai yaji ta na tambayar shi lafiya? "Tsoro ni ke ji an shigo da makara cikin gidan mu wai Tantie Yusi ta rasu"ya ida maganar ya na fashewa da kuka, Abbasi ya shigo ya na kuka shi ma Atine ta jawo su duka su biyun ta rungume ta na jin wata irin nadama ta zo mata a nan take ta ƙudurta a ranta ta tuba daga yin shirka.




Cikin ƙanƙanan lokaci aka yi ma gawa wanka akai kaita makwancin ta na gaskiya bayan zuwan mijinta da wasu ƙwararakin dangin sa,jaririya kuma an yi mata wanka da ruwan zafi an saka mata kaya tare da kaɗa mata madarar gwangwani.
Lokacin da Atine tayi tozali da jinjirai kuka tayi ta yi ta neman yafiya a zuci ta na jin ta wani iri....
[22/02 à 09:49] Mrs SADAUKI 💫: *PAID PAGE 29-30*




*Littafin kuɗi ne ki biya ki karanta hankali kwance ƴar uwa ba tare da kin shiga haƙina ba ki biya 200₦ kacal ki sha karatu in kin shirya kin tuntuɓe Ni ta WhatsApp* +22795045822




MATAN ALBARKA HERBAL MEDICINE


INA KUKE ISASUN MATA MASU AJI MASU DARSJA DA GIRMA MU MATSO KUJI GA GYARA NA MUSSAMN NA ISASUN MATA MASU AJI


INA MAI MATSALAR SAURIN KAWOWAR MAI GIDA KI ZO GA HADIN NE DA KAI ZAKU SAMU QARFI DA ISASHEN RUWA
MAI FAMA DA BUSHEWAR GABA
MAI BUDEWAR GABA
MAI QAIQAYIN GABA
MAI FITAR RUWA BA KAN GADO
INA MAI SO TA MATSE MUNA DA MAIDA TSOHUWA YArinya
Kuma muna gyara amare gyaran da zai shekara a jikin su ina masu jego
Kuma ga naku gadin ISASUN MATA
Muna gyara dukan matasalolin mata na cikiy Dana waje kedai ki tuntubemu a wanna nombar kuma muna wa,azin aure 08163199051


Sign manager c,e o maman shukura


________________




Tun bayan rasuwar Yusira rainon jaririyar da ci sunan Maryam ya dawo ga hannun Ammi ita ke kula da ita har ta girma.
Tsawon shekaru goma gidan ya zama wani iri saboda Daddy ya zama mijin Hajiya sai abinda Atine tace ake yi,kama daga kalar abincin da za'a girka irin shigar Daddy zai yi in kuma wata sabga ta tashi ita ke zaɓarwa kowa abinda zai saka.
Tun Inna na sharewa har ta kai ta tanka,ran Atine ya ɓace nan Daddy ya shiga yin masifa wannan ya fusata Inna ta koma mai jan Gero da zama,hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya yiwa Atine ba duk da kuwa duk yadda ta so Daddy ya so Abbasi sama da Mahomet abu ya cuttura shiyasa ta ɗauki tsanar duniya ta ɗora masa.




A yanzu shekarun Maryam goma cif a duniya,ta na sakewa tayi walwala in Mahomet bai gidan saboda yadda ta ke mugun tsoronsa ba kamar Abbasi ba da ya ke janta wasa tare da nuna mata ƙauna.
Maryam na zaune Ammi na tsefe mata kitso sai kuka ta ke ta na wani noƙe kai, Mahomet yayi sallama da sauri ta haɗe kukan ta na mai tusa kanta tsakiyar ƙafafun Ammi.
"Ihun minene ni ke ji Ammi?"Mahomet ya tambaya ya na mai zama kan salo,Ammi tace "mutumniyar kace mana ka san yadda ta tsani a taɓa kanta"tsuki Mahomet ya ja yace "shine ta ke ta wannan ƙugin kamar wacce ake ma zarar rai ?"Ammi ba tace komi ba sai sallamar Abbasi da ta amsa ta na mai cewa "har ka dawo?" "Eh Ammi in ji dai ba ta yi kukan ba?"Ammi ta yi dariya Abbasi ya cigaba da cewa "a'a Ammi faɗa min in dai tayi kuka na koma da biscuit ɗina da na sawo" da sauri Maryam ta goge hawayen ta juyo ta na kallon Abbasi da murmurshi kan fuskarta ta miƙa masa hannu tace "to bani "ya maƙe kafaɗa yace "na ƙi ga idon ki na sun yi ja alamun kin yi kuka,kin ga kawai sai na ajiye ma kai na"Maryam ta fara bubuga ƙafafu tace "Ni dai ka bani please ai kai kace Ammi ta kwance min kitso to in da har ba ka bani ba sai na ƙi yarda ayi min sabo"
Mahomet ya ja tsuki yace "sakara ƙazama kawai,to wa kika yiwa can ke kika sani kiyi ta zama da wari"ya na gama faɗa ya miƙe ya nufi ɗakinsa.
Abbasi yayi murmurshi ya miƙa mata yace "ungo zauna a ida kwance kitson sai na kai ki wajen gyaran gashi"da murnarta ta karɓa Ammi ta ida kwance mata kafin ta saka yaɗo ta wanke mata shi fes wannan ta bar Maryam ɗin tayi wanka.








Tun daga nesa ya ke ƙare mata kallo yadda Ammi ta take mata gashi a tsakiyar kai da shushu kalar rigar jikinta,sai tayi tsaf gwanin sha'awa.
Miƙa yayi kafin ya ƙarasa cikin kasalar barci da ba ta ida sakinsa ba "Mary ɗauko min fura cikin frigo"Mahomet ya faɗa ya na mai zaunawa,da sauri ta miƙe jin maganar sa, ta ɗauko kenan za ta bashi kamar wacce aka ture ta faɗi ƙasa kwacaaaa furar duk ta ɓata ma Mahomet jiki.
Wani irin rumtse ido yayi ya na jin sanyi furar na ratsa fatar jikinsa ta na shiga ɓargonsa,tashi tayi jikinta tuni ya fara karkarwa tsabar tsoro.
Buɗe idonsa yayi ya sauke su kanta,ta fashe da kuka tare yi motsi da baki alamun ta na son yi magana amman ta kasa kawai sai tayi demi tour za ta gudu gun Ammi talaɓaɓiya ta kwasheta tayi luuu za ta faɗa kan table glass cikin azama Mahomet ya tarota da hannunsa wanda yadda ta faɗo ya saka hannunsa yin ƙara.
Kwarantsin Maryam ya saka Ammi leƙowa daga kitchen,da sauri ta ƙaraso ta na "subahanallah!mi ne ke faruwa?wa zubar da fura?"
Mahomet wanda ya ke fafutukar jan hannunsa ya kalli Ammi kafin ya watsawa Maryam harara,da sauri ta koma bayan Ammi ta na shafar hawaye.
Wajen Ammi ta gyara tsaf kafin ta dama ma Mahomet fura,ya na sha ya na gangame fuska kamar wanda aka yi ma doli.
"Ammi wai dan Allah miye cikin kwanyar Maryam ?sam ba ta da nutsuwa duk yadda ni ke son saita mata saiti amman sai ta kauce mtws..."
Ammi ta dube sa da kyau kafin ta shafi kan Maryam wacce ke barcin wahala tace "da sannu za ta koma ta zama yadda kake so,abinda ya kamata kayi kawai shine haƙuri da sannu komi zai warware" ya ja wata doguwar ajiyar zuciya kafin ya lumshe ido, juste 20years ne da shi amman zuciyar sa na ɗawainiya da muguwar soyayyarta wacce bai san ta yaya,yaushe hakan ta faru ba.








Washegari
Ya kama Monday duk sun fito cikin shirin zuwa école,dining su ka hau dan yi breakfast amman Atine ta yi gâcher abun sai masifa ta ke.
Daddy wanda tun tsawon shekaru goma da Atine ta ɗauki rôle ɗin sa ta miji ya kalleta da kyau yace "kin ga Malama wannan karon ko mutuwa za ki babu fashi,aure tuni an ɗaura sai maganar tarewa kuma ba lalle ki san yaushe za ayi ba abu guda ne zan iya yi maki shine kayan kashe laifi "
Ammi tace "aure?yaushe ka yi auren Alhaji ?" Ya bata amsa da "sati biyu da suka wuce"
"Allah sa alkhairi ya kuma bamu zaman lafiya"cewar Ammi kafin ta fara zuba ma kowa abinci kamar kullum, Daddy ya amsa da "amen ya Rabb ai ke na san ƴar aljanna ce,kuma ke zan iya faɗa maki wace amaryar"
Ƙuuu Atine tayi ta koma ɗakinta,kan gado ta faɗa tare da fashewa da kuka a fili tace "Allah nayi maka alƙawarin ba zan sake zuwa wajen Malam ko boka ba shine Alhaji ke son mayar da ni ruwa Allah kar ka bani ikon cutar da wata halittar bayan Yusira"nan ta cigaba da rera kuka ta na saƙe-saƙe.
Tun daga wannan rana Daddy ya raba masu kwana ya ƙi kuma yarda ya sanar da su wace amaryar sai dai in ranar kwananta ne ya je can, wannan abu ba ƙaramin ciwo ya ke yi ma iyalinsa ba dan kuwa Abbasi da kansa ya je ya shaida ma Inna canjin da Daddy ya kuma samu dan wannan lokacin dukan hankalin shi ya koma gidan amarya.
Takanas ta Kano Inna ta zo maraɗi juyin duniya Daddy ya ƙi kawo amarya sun ganta sannan yace ba zai haɗe su ba, wannan ya fusata Inna ta tafi da Maryam ta cigaba da zama wajenta.




Bayan wasu shekaru
Tuni su Ammi sun gano Wace ce Daddy ke aure, Atine har gida ta je ta wanke uwar Balkisu da masifa a ƙarshe da ta dawo gida Daddy ya ɗirka mata shegen duka.
Jin abinda ya faru ya saka Balkisu shiryawa yau tun da wuri ta je gidan,tun a bakin ƙofa ta tsaya ta na ƙare mashi kallo.Sanye ya ke da ƙananan kaya na gudu farare uwanda su kayi matuƙar fitar da zatin sa da haibarsa ta ɗa namiji,ajiyar zuciya ta sauke ta na jin wani sanyi na mamaye zuciyarta saboda tsimin soyayyar da ya motso mata.Duk masifar da ta zo da ita sai taji ba ta iya yi kawai sai ta koma gida,zuwa bayan magrib Daddy ya zo ya yi mata sallama kamar kullum duk ranar da ba girkinta ba.
Jiki na ɗan rawa tace "sweety wlh tsoro ni ke ji please a samo wanda zai rinƙa taya ni kwana "Daddy ya shafi kumcinta yace "kin cika tsoro wlh to ni yanzu a ina zan nemo maki?"ta yamutsa fuska tace "ga ƴaƴana nan ko Mahomet ai sai ka turo sai ya rinƙa kwana nan falo"ba tare da wani tunani ba Daddy ya kira Mahomet ya kwatanta mashi gidan ya zo.
Baƙin ciki kamar zai kashe Mahomet jin wai tsoro yasa zai rinƙa tayata barci,babu yadda ya iya haka Mahomet ya rinƙa tayanta kwana.
Tun daga ranar Balkisu ta kuma kamuwa da son Mahomet da wata muguwar sha'awar shi,da zarar ta kwatanci yayi barci sai ta fito falo tayi ta kallon sa.
Hakan ya faru na wajen kusan shekara guda,zuwa wannan lokacin Mahomet ya kusa gama karatun shi.






Da sanɗa ta fito daga ɗakinta zuwa falo,cak ta tsaya ta na kallon yadda jikinsa ke motsawa alamun mafarki ya ke.
Balkisu ba ta san lokacin da ta ƙarasa inda ya ke kwance bisa doguwar kujera ba,hannunta ta kai kan D ɗin sa wanda hakan yayi sanadiyar tashinsa daga barci.
Sosai Mahomet yayi ƙoƙari wajen tsira da mutumcin sa a matsayinsa na mai tashen balaga,kuka Balkisu ta fashe da shi ta fara gaya masa kalaman soyayya wanda ya sa ya ɗauke ta a mahaukaciya.
Tun da wannan abun ya faru Mahomet ya hana kwanyarsa shaƙat,imagine ya ke ta yaya matar uba za ta nemi ɗan sa har tace ta na son sa?babban tashin hankali sa shine kullum sai Balkisu ta zo neman ra'ayinsa tun ya na sharewa har sheɗan ya fara ƙawata masa ko ya yarda.
Yau ma haka Balkisu ta sako sa gaba doli sai sun yi ko da romance,ture ta yayi ya nuna ta da yatsa yace "in ke mahaukaciya ce to ni da hankali na, sannan wlh in ba ki bari zan gaya ma Daddy kuma daga yau ba zan sake kwana nan gidan ba"Balkisu ta katse sa da "wlh Mahomet ba ka isa ba,kai nawa ne dan haka doli kayi min abinda ni ke so, zo ka ka yi min"ta ida zancen ta na mai ƙoƙarin jawosa ya ɗauke ta da mari ya ɗungujeta yace "mahaukaciya je a duba kwanyar ki likitar mahaukata,fasiƙa da ba ta san mutuncin kanta ba har kike sha'awar yin zina da auren ki"ya na gama faɗa ya buɗe ɗaki ya fice ya barta duk da kuwa dare ne.
Washegari juyin duniya Daddy yayi amman Mahomet ya ƙi faɗa masa abinda yasa yace ya gaji a tura Abbasi,saboda yadda Daddy ke sonsa yasa ya barsa sai Abbasi ya fara zuwa ɗayan biyu kuma Balkisu ta kore sa.






Kalmar mahaukaciya da ya ambata mata ya ƙi fita daga ranta har ta kai ta shaida ma Mamar ta ita kuwa tayi aniyar ɗaukar mataki a kai inda ta ke tabbatar ma da Balkisu "ki kwantar da hankalin ki zai gane ba ke ce mahaukaciyar ba ranar da ya zama garwaye biyu sai ya zo da kansa neman mafita ya baki haƙuri kawai zai samu kansa,wlh na rantse maki bakin magana ma zai yi masa wuya bar shi bai san wacece ke da matsayin ki a guna ke dai kawai ki jure da auren Alhaji da sannu za ki ga ribar da za mu samu"sam Balkisu ba ta tsammaci Mama za ta cutar da Mahomet ba ne sai da taji wai an kwaso sa daga can makaranta an maidosa gida saboda ya na abubuwa na maras hankali.






Tsabar shiga shock ya sa sai da aka kwantar da Daddy,sosai Mahomet ke haukan cikin kaya surutu in ya fara yi kamar an kunna radiyo.
"Mama miye haka?mi kika yi ma Mahomet ya ke hauka?"Balkisu ta kira Mama ta na kuka, Mama ta sheƙe da dariya tace "ke kwantar da hankalin ki ba haukan ƙwarai ya ke ba juste na wani lokaci ne,an raba masa kwanya biyu ne ta yadda ba zai tantance shi waye ba sannan an saka mugun tsoron ki a ran shi tunda kin ƙuƙe sai kin same sa commandé ɗin sa za ki yi duk abinda kike so zai yi"jin wannan zance ya saka Balkisu jin ranta fes.
Tunanin yadda za ta ɓullo ma lamarin tayi amman ta rasa hanyar da za ta samu Mahomet kawai sai tace Daddy ya game su gida guda,shi kuma da ya ke masifar sonta ya ke kawai sai ya fara gini inda a ƙarshe ya haɗe su gida guda.wannan kenan.






★★★ *CIGABA*




"Wuuu!kai ita ce?eh ita ce,ita ce hhh wuuu!"Mahomet ke zaune ya nanatawa hannun sa riƙe da wata ƙatuwar tabzaha ya na ja kamar wani zakiru,abincin da aka ajiye masa ya ɗauka ya juye gora ruwa guda kafin ya kafa kai ya na sha zuwa can kuma ya saki kwanon ya miƙe kamar wanda aka tsikara.
Babu kowa falon hakan yasa ya fice ya nufi ƙofar fita,ƙaƙar-ƙaƙar ya gama katanga duk tsayin ta ya haye sannan ya dire ya shiga gari.
Cikin jubji ya shira ya fara tsince-tsince ya samu wata bag irin ta yara ƴan makaranta,rataya ta yayi a kafaɗa duk abinda ya samu sai ya kaɗa ciki har sac ɗin ta kusa cika.
Wata riga ya gani duk ta yayage tayi dauɗa ya ɗauka ya saka kafin ya kutsi kasuwa,Bara ya fara yi wasu su bashi kuɗi wasu kuma abinci.
Jin kamar ya gaji ya sa shi samun wuri kusa da mai sayar da lemu ya zauna,ruɓaɓen lemu ya ɗauka ya fara sha ko ɓawon bai cirewa haka yayi ta sha can kuma ya miƙe ya nufi mai ruwan sanyi ya ɗauko guda ya shanye ya kuma ɗaukar wasu ya shanye a na ukun ne ya tara hannu alamun roƙo,yaron mai tallar ruwa ya ɗauki biyu ya bashi ya karɓa ya koma inda ƙatuwar jakar kayansa ta ke.Ya na shanye ruwan ya kwanta da ƙasa sai barcin gajiya,ya ɗauki lokaci kafin ya tashi ya saɓi jaka ya nufi gida.




Shigowar sa ya saka Abbasi ya nufo sa da sauri ya na

Please Login or Register in order to submit comment