Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaci tace "Abbas ni kake gaya ma magana?"Abbasi ya hayayaƙo mata yace "eh ɗin an gaya maki ke wace ce?"tsabar baƙin ciki Farida ta zube a sume.
Cike da tashin hankali ya ciciɓeta ya shiga da ita wani ɗaki wanda an yi shi ne domin duba lafiyar shi ne kawai halin en cas.
Kan bed ɗin ya shimfiɗeta,Dr Halima wacce ke bayan sa ya baiwa umarni "Hubby kirawo min Maryam"fita Halima tayi ta na juya kalmar Hubby a zuci ta ke tambaya "ko dai dagaske shine ɓoyayyen masoyi?"ta na shiga Infirmerie duk suka juyo su na kallonta ita kuwa ba ta kula su ba dan ta lura tuni Barira ta shaida masu shine gulma ke ciciyar su.








Hannun Maryam kawai ta jawo ita kuma ta fara tambayar ta lafiya,sai da suka fito waje ne sannan Dr Halima ta gaya mata abinda ke faruwa.
Ɗakin da Farida ke ciki suka shiga,dubata suka yi ta dawo daga sumen da tayi Maryam ta ɗibi jininta ta fita zuwa labo tsawon lokaci kafin ta dawo ta na murmurshi ta miƙa ma Abbasi takardar sakamakon tace "congratulations na kusa zama Tantie Farida na da ciki na wata biyu"kamar almara haka Abbasi ya ji furucin karɓar takarda yayi ya na dubawa kafin ya gwale idon Farida wacce ke barci ta na sauke ajiyar zuciya da huci.
Dubawa yayi ya ga tension ɗin ta ya hau,kanta ya shafa yace"kin cika rigima ne babyna"da sauri kuma ya juyo sai ya ga ashe su Halima sun fita,ya sauke ajiyar zuciya.








"Hum!kin ga kamar almara ashe DG ne ɓoyayyen masoyi"cewar Halima,Maryam tayi murmurshi tace "ina taya ki murna domin duk wacce ta samu Abbasi matsayin miji ta huta dan dai kawai Allah ya jarabe sa da matar ƙwarai ne amman Abbasi bai da wata matsala"Halima tayi dariya haɗi da kai ma Maryam dukan wasa tace "wai matar ƙwarai,to miye na sakayawa kawai kice ƴar iskar mata ni kuma ko kallo ba ta ishe ni ba sannan yanzu ma na ƙara jin son sa dan tunda ni ke kishiya ba ta taɓa ɗagan hankali ba"Maryam ta ja baki tace "sai kuma fah ni sgiyasa da nace ki auri Abban Yusu kika ƙi amincewa"Halima ta harareta tace "ke yanzu in nace maki zan auri Abban Yusu sai ki yarda?"Maryam ta ɗaga kafaɗu tace "mi zai hana kuwa?kin ga kuwa da daidai kenan tunda yanzu na tsufa sai na bar maki miji ku sha amarcin ku har sai na haihu nayi arba'in"
Halima ta girgiza kai tace "eh na ga alamu ki na buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa"a sanyaye Maryam tace "dan ina *MATAR MAHAUKACI* ko?"da sauri Halima tace "Innalillahi wlh ba da nufi nace ba,dan Allah kiyi haƙuri wlh tallahi ban faɗi haka da wata manufa ba"
Maryam tace "laaa!bai fah komi nima kawai zuwan zance ne ai yanzu ya warke,kin san kuwa kishiyar ki ce ta fara kirana da *MATAR MAHAUKACI* ?"
"Dagaske wai?"Halima ta tambaya
Maryam tace "wlh kuwa lokacin an kawota ta na amarya sai ciwonsa ya motsa shine fah ta jefe ni da kalmar"cikin sanyi Halima tace "ayya dama su mutane haka suke babu lafazi mai daɗi,ni fah har yanzu ban ida yarda da Abban Yusu yayi rashin lafiya ba"
Maryam tace "ki shirya ki zo gidana sai na kunna maki videos bikin "
Halima tace "wai yaushe ne za ku koma sabon gidan?"Maryam ta bata amsa da "wai sai na haihu,kin sa kuwa babu abinda ba a saka ba kawai komawa ce za mu yi Abban Yusu yace ina haihuwa daga likita za'a yi tsinke da ni can"
Halima tace "Allah sauke ki lafiya,wlh in dai kika haifi mace sunana za'a saka mata"Maryam tayi dariya tace "ai kuwa ko dan ta samo jarumta da ƙawa zucin ki zan yi haka"nan dai suka cigaba da hira kafin Maryam ta koma ɓangaren su.










Sai da aka ɗauki lokaci sannan Farida ta farka, Abbasi ta ga zaune gefenta da sauri ta haɗe rai shi kuwa cikin murya rarrashi yace "please ki bar fushin nan kar ya taɓa lafiyar babyn mu"yayi maganar ya na kai hannu bisa mararta.


Kallon ban gane ba ta yi masa yasa shi gwada mata result,tsabar murna yasa taji duk wata damuwarta ta kau.
Taimaka mata yayi ta sauko daga gadon ya ja ta suka fita,ko inda Halima ta ke ba ta kalla ba sai wani shishige ma Abbasi da ta ke yi.
"Zan tafi na kai Madam gida duk wanda ya zo nema na in urgence ne ya tardo ni gida,uwanda ni ke da haɗuwa da su kuma a yau na soke zan tafi gida"cewar Abbasi ya na kallon Dr Halima ido cikin ido "to in shaa Allah DG prompte rétablissement à Madam"da sauri Farida ta buɗe ido jin wai Halima na cewa Allah ya bata lafiya harara ta watsa mata tace "ina ruwan ki da cikina?"
Abbasi yayi gaba da ita yace "yaushe kika ji ta ambaci cikin jikin ki sabida Allah?" Farida ta turo baki.
Key ɗin motar ta ya karɓa suka shiga yayi driving na su zuwa gida,a shagwaɓe tace "Allah bb na tsani waccan baƙar sakatariyar kawai ka sallame ta"Abbasi ya girgiza kai yace "da tayi maki mi?" "Hum!ai dama na san haka za kace tunda yanzu ma har da wani tankata kayi ka na gaya mata inda za ka je"
"To bbna ai saboda ita ke kula da lamurran office ɗina ne sannan please ki kwantar da hankalin ki ni na ki ke ɗaya ban son ki na damun kan ki bari na kira Hajiya na sanar da ita"rufe ido tayi da tafukan hannu wai a doli ta ji kunya ne.








Wata irin buɗa Atine ta saki ta fara taka rawa ta na cewa "komi da lokaci amarya zo taso ki bi bayan mijin ki,wacce ba ta da gata in ta rasa yanzu za ka ji shewar maƙwabta to ku cewa ƴan gulma su zo suji abun murna ya same ni ɗan Ɗan guda-guda shi ma zai zamo Abba nan da ɗan lokaci"
Inna wacce ke zaune ta na shan kunun da Ammi ta dama mata tace "to sakara sai aka ce maki in Allah ya baka wata ni'ima waƙa ake yi da habaici?mtsw ai sai kiyi sujudar shukur ba wai wani banzar habaicin ki ba maras kai"
Cak Atine ta tsaya "to Inna abun murna ya same ni sai na fasa rawa?ina ce a gaban ki Alhaji ke nuna banbanci kullum cikin sayo ma Yusu kayan wasa ya ke alhalin ba wani adana su ake yi ba nima yanzu ai zan yi jikan sai na ga ta gori"
Inna ta jujuya kai haɗi da taɓe baki tace "ai kin bari har a haifo cikin ko?"ba tare da shakka ko jin ɗarrr ba Atine tace "haifo sa ma za'a yi saboda wannan ya fi ƙarfin dodon tsafin matsafa"
Mahomet wanda ya ke can saman bene ya na kallo da kuma jin komi yace "dodon da kike tsafi wanda kika taɓa baiwa jinin ɗaya daga cikin ahalin mu?"
Da sauri Atine ta ɗaga kai ta na kallon Mahomet,shi kuwa a harzuƙe ya fara saukowa daga matatakala ya sauko ƙasa fuska tamau yace "ko kin manta na tuna maki?"
Sallamar Daddy ce ya sa duk suka dubi bakin ƙofa ,"ya na ga duk kun yi cirko-cirko mi ke faruwa?"Daddy ya tambaya ya na kallon Ammi wacce ke feeding Yusu da ƙaton biberon ɗin sa.




Da ido tayi masa alama wajen Atine da Mahomet,hakan yasa Daddy ƙara tambayar"Hajiya mi ke faruwa?"ƙyaf-ƙyaf tayi da ido ta na kallon Alhaji .
Mahomet ya saki murmushi yace "matar ka ce ke yiwa Ammina habaicin suna da dodon tsafi saboda taji tarihin iyaye da kakannin Ammi a baya sun yi tsafe-tsafe shine ta ke tsoron Ammi ta salwantar da cikin sarakuwar ta wato matar Abbasi ga dodonnin tsafi kamar yadda ita ma ta taɓa baiwa na su dodon jinin...."sai kuma Mahomet ya ƙyale .




Daga can gefe Inna ta saki murmurshi sai kuma wata guntuwar ƙwalla ta zubo mata,Ammi kuwa zantukan Mahomet sun ɗaure mata kai dan sam ta kasa fahimta uwa uba Daddy.
Mahomet yayi murmurshin gefen baki yace "matar Alhaji ki sanar da su abinda ke faruwa kafin ni na sanar da su,saboda in ke kika faɗa da kan ki abun zai zo maki da sauƙi ko kin manta sharaɗin ne?"ya ida maganar ya na ɗaga gira cike da shaƙiyanci.




Zubewa Atine tayi ƙasa jiki na kyarma sam ta manta da wani zance wai shi yarjejeniya balle kuma kuskuren baya,tamkar wace aka jona da courant haka duk illahin jikinta ke rawa wanda hakan ya ɗaga hankalin Daddy da Ammi Inna kuwa ko a jikinta dan kuwa ta san an rina wai an saci zanen mahaukaciya.








"Ok tunda ba za ki faɗa ba bari ni na shaida masu abinda ke faruwa,shekarun baya da suka wuce Hajiya ta..." Da sauri Atine ta kamo ƙafafun Mahomet ta na girgiza kai,wani babban al'amari shine juyewar bakin Atine lokaci guda kuma yawu suka fara yi mata zuba saboda tsabar kaɗuwa tension ɗin ta ce ta taso lokaci ɗaya.








Baki a jirkice tace "Ni ce! Ni ce na salwantar da Yusira "sai kawai tayi shiru jin ƙaramin farcenta na ƙafa ya na motsi kamar zai fita.
Ammi ta miƙe da sauri kanta na sarawa yayinda Daddy ke tambayar "wace Yusura?"
Miyau na zuba dalalaaa a bakin Atine tace "ƙanwar ka mahaifiya gun Maryam"ta na faɗar haka numfashinta ya tsaya cak sakamakon azabar da taji ruhinta na yi mata.








Tamkar wasu zararru haka duk ahalin suka yi ,likitoci kuwa su na can su na fama da Atine da ta farfaɗo kuma sai ta koma tsabar furgici sai ambaton sunan Yusura ta ke.
Abbasi wanda Daddy ya sanar da kuma hankalin sa in yayi dubu to ya tashi,shi ma shiga yayi cikin ɗakin da ake duba Atine.
Wani irin kuka ne ya kubce masa ganin yatsun ƙafarta na hagun duk sun ƙindile sun koma irin na kutare tuni kuma ƙafar ta fara canza kamani,Daddy,Ammi da kuma Inna suma duk shiga suka yi saboda sunan su da Atine ke kira.
Mahomet kuwa ya na can zaune cikin masallacin asibitin ya na wuridi, murmurshi kan fuskar shi wanda ya ke nuni da samun nasara.






Cikin muryar ta da ta canza tace "na salwantar da rayuwar Yusura yanzu kuma lokacin dawowarta duniyar mu ne yayi ni kuma zan koma kamar ita dan Allah dan Annabi kuce tayi haƙuri ba da niyyar bada ranta nayi ba kawai dai Ɗan cikinta na bada su kuma sai suka yi masanya"
Abbasi ya tambaye ta "su suwa?"amsa ta bashi "dodonni,wayyo ga su nan za su tafi da ni Mahomet dan Allah ka bari,ya na addu'a eh addu'a"ganin kamar abun ya taɓa mata hankali yasa Abbasi cewa ayi mata allurar barci ana yi mata nan ta ke barci ya ɗauke ta.








Wajen Mahomet Daddy da Abbasi suka nufa ganin haka Ammi da Inna ma suka fito.
"Kayi ma Allah da Annabi ka tsayar da wuridin nan ka zo ka ida fahimtar da mu taƙamaimai abinda ke faruwa,sam mun kasa gane zantukan Hajiya tace Yusura ta bada alhalin kowa ya san Yusura ta mutu ne wajen haihuwa"ba tare da Mahomet ya juyo ba yace "ba ta mutu ba"
Daddy yace "kamar ya ba ta mutu ba?"
Mahomet ya taso ya fuskance su yace "Tantie Yusura ba ta mutu ba ta na nan da ranta kuma za ta dawo gare mu daga lokacin da Hajiya ta bayar da sacrifice"a kiɗime Abbasi yace "sacrifice?kamar dai matsafa wane irin sacrifice kuma?"Mahomet yayi murmurshin gefen baki yace "ƙwarai kuwa tsafi ne,saboda lokacin da Hajiya ta tafi gun bokan idonta a rufe suke wannan ya sa ba ta gane boka da doguwa ya ke aiki ba,sun yi da ita a basu jinin haihuwa wanda ya ke nufin yaron da aka haifa ganin an kawo Tantie Yusura haihuwa shine tace abu ya zo gidan sauƙi.Ammi in ba ki manta ba Hajiya Atine ita ta nace kan abar Tantie Yusura ta haihu gida ta na ta kushe likitoci akan yanzu ba su kulawa da patient?"Ammi ta gyaɗa kai dan kuwa an yi haka.


Mahomet ya cigaba da cewa "lokacin da ta fara naƙuda sai Atine tayi turare wanda lokaci guda kuma haihuwar ta zo gadan-gadan,jinin haihuwa na fara zuba dodon da ya ke zaune cikin kwalbar turaren nan ya fito ya fara lasa a zumar ya gama da jinin jaririn da aka haifa sai dai kash aljannun da ke jikin jaririyar har sun fi sa hatsari wannan yasa suka juya akalar zuwa ga Tantie Yusura wacce kuma tsawon shekara da shekaru suke da na sanin ɗaukarta da suka yi saboda jininta ya ƙi shayuwa a gare su"
Inna ta goge hawaye tace "ta yaya jinin Yusura na zai shayu dama?yarinyar da tsanani imani da tsarin Allah sun ratsa jini da tsokar jikinta,tun ta na ƙarama wasu sukan ce sun zata waliyiya ce wannan al'amari ya faru ne saboda tonon asiri da kuma darasi da ƴan baya"
Abbasi yace "yanzu duk ba wannan ba kai ya aka yi ka sani? wannan ai zancen banza ne dama na jima da sanin ba ku ƙaunar mahaifiyata"
Mahomet yace "no ɗan uwa ba haka ba ne,ai bin bayan Ammin ka nayi har ta isa ɗakinta ina kallonta in ba ka manta ba kai ma ka tarar da ni ka zo ka na kuka an shigo da makara gidan mu?"shiru Abbasi yayi.
Ammi kuwa tuni ta ke kuka, Daddy fuskar sa tayi ja tsabar ɓacin rai da kuma furgici"ina mafita a nan Mahomet?"


"Mafitar dai ɗaya ce ita ce wadda na gaya maku shine Atine ta bayar da sacrifice in ba haka ba za su ɗauke ta su sauko Tantie Yusura tunda lokacin barinta yayi,yanzu ya zama doli Atine ta bayar da Abbasi ko shi ɗan cikin wanda shigar sa ne komi ya dagule ko kuma ta bayar da ruhin ta shawara ta rage ga mai shiga rijiya"........
[08/03 à 12:38] Mrs SADAUKI 💫: ```BONNE FÊTE DE LA JOURNÉE DE FEMMES A VOUS TOUTES MES CHÈRES FANS,GODIYA DUBU DA KUKA KASANCE A NAN GIDAN INA MAKU DUK BARKA DA SALLAR MATA TA DUNIYA```




*49-50*






"Innalillahi wa'inna iley raji'un,wai ka nufin doli sai jinin ɗan Adam?"Abbasi ya tambaya, Mahomet yace "haka take!jinin wani bare kuma wanda ba sashen Atine ba sam ba zai yiyu ba"ihun Atine da cika duk illahirin asibitin ne yasa su duk suka dugunzuma wannan karon har Mahomet.
Cike da alhini Dr yace "ta rasa duk yatsunta na ƙafafu sannan kamar ƙafafun sun fara bushewa matsalar kuma har yanzu mun kasa gane wace cuta ce ke damun ta dan kuwa wannan sabuwa ce,shiyasa na rubuta maku takarda sallama wacce za ta baku damar fita da ita ƙasar waje "Daddy ya karɓi takardar ba tare da yace komi ba.




Bisa gadon maras lafiya aka turota sai ihu ta ke ta na kiran "kar ku tsotsen jini wlh ba zan bayar da Abbasi na ba shine farin cikina gwara ku ɗauke ni"da sauri Abbasi yace "a'a Hajiya kar ki mutu ki bar ni na bayar da cikin jikin Farida a matsayin fansa"ko ida rufe bakin sa bai ba Atine ta miƙe ras da ita sai uban gumi ta ke haɗawa.
Kuka Abbasi ya fashe da shi mai ciwo, fuskar Daddy tayi ja sosai cikin ɓacin rai dan kuwa yanzu ya tabbatar da mugun halin Atine "kin san dama lokacin da zan ƙara aure kiyin shirmen da na cire igiya ɗaya na kuma mayar da ke a take,to yanzu na ida tsinke sauran biyun kai kuma sai ka tafi da uwar ka ta gama zama a gidana kuma"Daddy na gama faɗar haka yayi gaba sauran iyalan sa suka take masa baya.






Abbasi ya na kuka ya na ƙari ya ɗauki Atine a mota suka wuce gidansa,su na shiga ya tarar da Farida kwance ta na murƙususu.
Da sauri ya nufeta ya na kiran sunanta,ririƙesa tayi ta na jin wata irin azaba na karta mata a mara.Idonta tuni sun yi ja tsabar azaba, Atine kuwa gefe ta zauna ta na kuka haɗi da da na sani marar amfani.
Ihu Farida ta ƙurma jin kamar an zuɓuce wani abu ta ƙasanta kawai sai jini ya biyo baya,tun daga nan ba ta sake sanin inda ta ke ba sai ganinta tayi kwance kan gadon asibiti hannunta ɗaure da drip.
Ido ta lumshe ta na son tuna abinda ya faru amman ta kasa doli ta haƙura,a haka barci ya sace ta.










GANGAREN MAWALIYA wani yanki ne da ke cikin garin Maradi inda ruwa ke kwantawa lokacin Rani da kuma Damina.
Wuri ne da mafi akasarin matasan yankin kan zuwa ɗebo ruwa,wankin kaya da kuma wanka.
Kamar walƙiya haka suka ga matar kwance a bakin ruwan,kanta a yamutse yayinda suturar jikinta ta ke jagab da ruwa.
Kewaye ta mutane suka fara yi kan kace wani abu duk wajen ya cika da mutane maza da mata,wasun suma matan aure ne.
A ɗan tsorace kowa ke kallonta yayinda wasu suke bada shawarar a kira ƴan sanda,haka kuwa aka yi babu jimawa ƴan sanda suka ƙaraso.
Wani mai jarumta cikin su yayi addu'a gami da jaye hannunta wanda ta rufe fuskarta da shi,da sauri wasu suka yi baya saboda tsabar haskenta da kuma kyawun ta.




A hankali ta fara motsa bakinta "alhamdullah lazhi ahyana ba'ada ma amattana wa'ileyhi nushur!"ta gama faɗa sai ta buɗe idonta uwanda suka yi mata nauyi sosai.
Tashi tayi zaune ta na kallon mutane kamar wata sabuwar hallita,ido ta rufe ta kuma buɗe cikin sanyin murya tace "dan Allah ku kai ni gidan mu"
"Wlh mutum ce ga shi nan ta na magana"
"Baiwar Allah na san ɓata ne tayi"
"Anya ba mahaukaciya ba ce?"
Wannan sune kaɗan da abinda mutane ke faɗa,cikin motar ƴan sanda suka sakata kafin su wuce da ita police station.






Kaf illahirin gidan rediyo na Maraɗi aka sa sanarwa yayinda kuma masu yin shela ma ba'a bar su baya ba,dan kuwa ta kasa tuna unguwar da ke.
Faruwar wannan lamari da yadda aka gabatar da sanarwar yadda aka tsinci matar ya saka wasu zuwa har comsariat ,ciki kuwa har da Dr Halima da Maryam sai dai an hana mutane ganin ta doli duk suka haƙura.
Daddy ne da Mahomet a gaban d.p.o su na yi mashi bayani haɗi da nuna masa hoton Yusura tun ta na budurwa,tabbas kamaninta ba su ɓace ba sai dai ramar da tayi ne kawai.
Fiddota aka yi ta na ganin Daddy ta tsaya ta na yi mashi kallon ƙure,"tabbas wannan ɗan uwana ne duk da an ja shekaru dayawa"ta faɗa a zuci kafin ta zo ta rungume sa.
Ajiyar zuciya Mahomet ya sauke ya na jin wata nutsuwa,lambar Maryam ya kira sai dai har ta katse ba ta ɗaga ba.
Bayan sun yi godiya gami da yiwa d.p.o kyauta suka wuce gida,banda kuka babu abinda duk ahalin su ke yi musamman Inna .
Mahomet ma sai da ya koka,kamar wata yarinya haka Inna ta taimaka mata tayi wanka sabulu sannan na ruwan addu'o'i wanda tun lokacin rashin lafiyar Mahomet ba su taɓa yankewa ba.








Da sallama Maryam ta shigo gidan,tsayawa tayi ta na kallon mutanen falon yadda suka wani tattaro hankali da nutsuwar su suka baiwa baƙuwar fuskar cikin su.
Mahomet ya taso ya jawo hannun Maryam ya kai ta har gaban Yusura wacce ke kallon Maryam.
"Tantie Yusura kin ga Maryam ɗin nan"cewar Mahomet shi kuwa Yusu ƙafafun Maryam ya ririƙe ya na cewa ta bashi biscuit.




Rungume ƴar ta tayi kafin ita ma Maryam ɗin ta zauna,ta na sauraren labarin.


"Abu na farko da ya bani mamaki yadda duk kuke kuka haɗi da yi min fatan rahamar Ubangiji,daga nan ne na gane tabbas mutuwa ce nayi kamar yadda ake gaya mana a makaranta shi mamaci ya na jin duk maganar da ake.Sai dai lokacin da ake yi ma gawa wanka sam ba ni ba ce,wata gawar ce daban dan ni ina gefe wata mace mai jajayen kaya ta kulle min hannuwa haɗi da riƙe ni saboda ina son zuwa gun ku,a gabana aka fitar da gawar da kuke ma ɗauka tawa ce aka sallace ta.Ana shigar da gawar cikin mota dan zuwa maƙabarta wannan mace ta ja ni izuwa wata duniya wace ke can NAHIYAR MATSAFA (Mai Ƙosai)"Yusura na kawowa nan ta tsagaita da maganai ta goge ƙwalla sannan ta cigaba da cewa "gari ne mai girman gaske wanda aka yi ma ado da ƙwanƙwamar kawuna mutane wanda tsabar firgici zai sa gan su kamar wasu FATALE(Princesse Aichatou),a haka mu ka shiga babban birnin jikina duk a mace sai dai zuciyata cike ta ke da zikirin Allah.Gidaje ne a ƙalla sun kai goma wanda ya fi girma can mu ka nufa ta na gaba ina bin ta a baya,tun bakin ƙofa na fidda rai da zan rayu saboda ƙafafu da sauran gangar jikin da na ga wasu mata na dadatsawa ana ɗorawa a tray..."ƙarar da Maryam ta saki ne ya saka su duk tawowa gunta Tantie Yusura kuma ta ƙyale ita ma ta nufi Maryam ɗin wacce wasu ruwa ke bin ƙafafunta.






"Ina ga fah haihuwa ce poche des eaux ce ta fashe"cewar Ammi ,da sauri Mahomet ya fita ya gyara zaman mota tuni Ammi ta kamo Maryam ta fito da ita yayinda Inna ta shiga ɗaki tattaro kayan haihuwa.








Labour room aka kai Maryam ko da suka isa asibitin,allurar ƙarar volume ɗin naƙuda aka yi mata.
Tsawon lokaci cur ta na ciki kafin Allah ya sauke ta lafiya,nurs ta fito da murmurshi tace "an samu baby boy"Ammi ta karɓo sa ta na mai miƙa ma Inna ita kuwa ta baiwa Mahomet ta na cewa "Ammin su ya kamata ki koma gida ki shaida masu ta haihu sai ki dafa ruwan zafi"
Ammi tace "toh bari na leƙa na ga jikin Maryam ɗin sai na wuce"




Ko da Ammi ta shiga ta tarar ana yi mata kwalwar jini,sai rumtse ido take nurs guda na matsa mata cikinta ɗaya kuma na saka hannu ta kwalyewa da sauri Ammi ta fito ta na jin tausayin Maryam ɗin.








Mahomet ya sauketa gida kafin ya koma asibiti,ta na shiga ta tarar da su zaune Yusura na jan tabzaha haka ma Daddy yayinda Balkisu wacce ta dawo daga ɗan sheƙenta ta na zaune ta na shan jus mai sanyi.
"Ya ta sauka?"Daddy ya tambaya kai Ammi ta ɗaga ta na murmurshi tace "na ƙara samun wani mijin"tayi maganar ta na shafar kan Yusu wanda ya sha kuka saboda ba a tafi da shi asibiti ba.
Kofin da ta ke shan lemu ta saki ya faɗi ƙasa a take ya tarwatse,ko ta kanta Ammi ba ta bi ba ta shige kitchen Yusura na take mata baya.
"Minene haka Balkis? haihuwa fah ta Allah ce ke ma in kin yi haƙuri wata rana sai labari"cewar Daddy cikin son kwantar ma da Balkisu hankali saboda shi a tunanin sa rashin ita ba ta haihu ba ne kawai matsalar bai san kishin wata ta haifa ma abun ƙaunarta Mahomet yaro ta ke ba.








Ƙwalla ta goge kafin ta duƙa ta fara tattare glass ɗin, Daddy kuwa fita yayi zuwa masallaci dan sallah magrib tuni ta gabato.
Gumba Ammi ta fitar da cikin frigo,sai da ta saki sannan ta dama kunu.
"Yau duk hankali ba kwance ba shiyasa ko girkin dare ban yi ba"cewar Ammi ta na juye ruwan zafi cikin wani ƙaton tarmus.
Tantie Yusura tace "ni kuwa yanzu na manta girki balle nayi"Ammi tayi dariya tace "kar ki damu ai ba'a rasa abinda za'a ci ba,zan sa Mahomet ya je restaurant ya sawo"nan da suka cigaba da yin hira har suka gama ɗan abinda suka haɗa ma mai biƙi.










Tsaf aka gyara Maryam aka kaita ɗakin hutu,sai da ta shayar da yaronta wanda Mahomet yayi mashi huɗuba da Abdallah sannan ta kwanta.
"Yaron nan fah da ni ya ke kama"cewar Inna ta na goge masa baki,da sauri Mahomet yace"haba Inna da wannan buɗaɗen hancin na ki?"
"Hancin uwar ka ne buɗaɗe"cewar Daddy wanda ya ke shigowa yanzu,su Ammi da ke bayansa suka sa dariya.






Mahomet ya sosa ƙeya yace "Daddy wai jaririn da ita ya ke kama" ,Tantie Yusura wacce ta karɓi yaron tace "Allah kiyaye uwata ta fi shi kyau ma kawai ta faɗa ne dan kuji daɗi kuce Ɗan ku mai kyau ne"nan dukansu suka dara kafin Ammi tace "Maryam tashi ki sha kunun tun da zafin sa"
Da "toh"ta amsa ta na janye Yusu wanda ya zo ya tsaya kusa da ita kamar zai koma ciki.
Ammi ta janyesa tace "to daga yau laƙuwa ta ƙare sai dai ka yi ma Inna "da sauri Inna tace "a'a ya dai yi maku ni ina côté sabon Ɗan"
Yusu ya taɓe baki zai yi kuka Mahomet ya ja sa suka bar asibitin.








Washegari


Bayan an sako Maryam daga asibiti ƴan barka suka

Please Login or Register in order to submit comment