Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi mata ciki"
"Ah to ita ma ai ba imanin ne da ita ba shikenan dara ta ci gida"Tantie Yusura ke faɗa.






A ɓangaren Mahomet kuwa tuni ya fara aikinsa na haƙon zinariya,wanda tsantsar ilimi ne kawai ke aiki.Duk ƙarshen wata ya na zuwa ganin gida ,in kuma ya na Agadez duk dare na Allah sai sun yi waya da Maryam wacce a kullum ta ke yi masa kukan kewar sa.
Yanzu wata huɗu kenan da Mahomet ya fara aiki amman tuni rayuwarsu ta ƙara canzawa sosai ya ke samun kuɗi wanda ya saka masu babban buri.






A kwana a tashi babu wuya wajen Allah tuni Dr Halima an yi haihuwar farko inda ta samu Twins duk maza,murna gun Abbasi ba'a magana duk da kuwa ba wannan ba ne haihuwar shi ta farko dan tuni ita ma Farida ta haihu inda su ke samun kulawar Hawali wacce ta bada gudunmuwa sosai na ganin ƙawarta ta ba ta tozarta ba haka ma babyn wacce aka saka ma Hawa'u an ɗauki duk wasu matakan tsaro dan kar ta kamu da cutar ƙanjamau.
Farida ce zaune a bakin matelas ta na daidaita ƙafafun robar da Hawali ta sa aka yi mata, gundululun ta saka ma wata safa sannan ta ɗora ƙafar robar.Ta na gamawa ta tashi da tashi tsaye kai kace ƙafafunta ne,bakin mirror ta ƙarasa ta kalli kanta a take wasu hawaye suka zubo mata.Duk da ta kasance a gidan président hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba wanda kuma tsananin damuwa da ƙunci ne ke damunta.
Aka turo ƙofa,Laila ce mai kula da little Hawali .Saurin goge hawayen tayi ta ƙirkiro murmurshin doli ta karɓi yarinyar wacce ke barci an shirya ta tsaf cikin wasu ƴan kanti,"Madame tace in kin shirya driver na jiran ki"cewar Laila,kai kawai Hawali ta gyaɗa kafin ta goye yarinyar ta yafa mayafi ta ɗauki jaka.








A falo ta tarar da Hawali ta haɗe cikin gizner wacce ta zame mata kusan kayan jikinta a kullum, murmurshi ɗauke da fuskarta tace "exellency sannu da hutawa"Hawali ta ɗago ta dubi Farida ita ma ta sakar mata murmurshi tace "yauwa Barka da fitowa,na canza shawara ya kamata Laila ta raka ki shiyasa nace ta je ta shirya sai ku tafi tare"
Shiru Farida tayi kafin tace "miyasa har yanzu ba ki yarda da ni ba?wlh Allah ba zan taɓa baiwa Hawa nono ba nayi maki alƙawari can ma duk saboda ina a ruɗe ne amman ai yanzu na samu nutsuwa"
Hawali ta girgiza kai tace "ba wai saboda wannan ba ne kawai a'a,kin ga Homo/takwara ba ta wani saba da ke sosai ba kawai kuje tare da Lailar tunda ba jimawa za ku yi ba"
Ko kafin Farida tace wani abu Laila ta fito cikin shirinta ta na jaye da ƙaramin akwatin kayanta,miƙewa Hawali tayi duk suka fito waje.
Daidai bakin mota ta raka su sai da ta shafa kan Hawa wacce tuni Laila ta karɓe ta kafin ta dawo ciki su kuma driver ya fice da su zuwa aéroport.










***MARADI VILLE






Kasancewar yau weekend ce yasa Abbasi bai tafi aiki ba,su na zaune shi da Atine yayinda Twins Hassan and Hussain ke zaune daga gefe suna wasa.
Dr Halima ta fito daga kitchen ta na sanye da riga da siket na less wanda suka yi bala'in karɓar ta,dining ta nufa ta jera abincin da ta gama ta na jin Atine wacce suke kira da Hajiya na jera mata sannu haɗi da sa mata albarka saboda tunda aka kawo Dr Halima suke zaman lafiya.






Sallama suka ji a bakin ƙofa,Dr Halima da ke kusa ta karɓa haɗi da basu izinin shigowa.
Cak Farida ta tsaya ta na ƙare masu kallo kafin tayi ƙarfin halin cira ƙafarta ta ida shigowa ciki.
Abbasi ƙurrr ya kafeta da ido ya na kallo ya na jin tsohuwar soyayyarta na motsa mashi,Atine kuwa kawar da kai tayi gefe duk da ita ma ta nada mugun hali amman yanzu ai ta tuba.






Ganin sun yi tsaye Dr Halima ta shanye mamakin zuwan na su tace "ku zauna mana bari na kawo maku abun sha"sai bayan sun zauna ne Farida tace "ina wuni Hajiya?"Atine ta waigo ta amsa fuska a ɗan sake,nan kuma suka gaishe da Abbasi kafin Laila ta miƙa masa Hawa wacce ta buɗe ido tarau kan mahaifinta.




Kumatun ta ya shafa ya na jin wani tausayin ta,yanzu yarinyar ta na cikin wata kusan na goma amman sai yau kawai ya ganta.
Dr Halima ta kawo masu jus mai sanyi suka yi godiya suka karɓa,gefe ta zauna ita ma ta na jin wani tausayin Farida wacce ta aje duk wani jiji da kai da izza.


Dr Halima tace"yaushe garin?"Farida ta mayar da ɗacin da ta ke ji haɗi da kishi tace "yanzu mu ka sauka ai,driver da ya kawo mu daga aéroport ya na waje"ta faɗi hakan ne dan tabbatar ma da Dr Halima a jirgi ta zo har yanzu da sauran gatan ta.
Abbasi yace "ayya shine kuka baro sa waje?"Farida tace "eh da ya ke yanzu za mu wuce"Atine tace "kamar dai ana korar ku?ai ku bari ku ci abinci ko?" Duk yadda Farida ta so zillewa su bar gidan dan takaici amman sai da Atine ta tsayar da su suka ci abinci hatta driver ma sai da ya shigo ya ci.
Ba su yi wata hira ba sosai suka wuce gidan gwamna dama a can ne za su sauka,sosai suka samu tarba mai kyau daga wajen matar shi da masu yi mata hidima.




Kukan da ba ta samu ba ta yi ba ne ya kubce mata yayinda ruwan pampo suka fara dukan jikinta,sosai ta ke jin raɗaɗin ganin Dr Halima da mijinta wanda yanzu duk duniya babu wanda ta ke so sama da shi sai dai kash wutsiyar raƙumi ce yayi mata nisa.






Tuni Laila ta yiwa Hawa wanka ta kaɗa mata madara ta sha a nan barci ya ɗaukesu su biyun.Farida na fitowa ta shirya cikin kayan shan iska ta kwanta luf kan shimfiɗa ta na tunani da wannan barci ya ɗauke ta mai cike da mafarkan ƙarya,ko da ta farka sai taji haushin tashin da tayi saboda ta san in ba a mafarki ba babu yadda za'a yi ta ƙara zama ƙarƙashin innuwar aure kuma da Abbasi.






Washegari
Haka Farida ta ja Laila suka wuce gidan Daddy sosai suka yi mamakin canzawarta,neman gafarar su tayi suka kuwa ce sun yafe mata.Maryam wacce aka yi katari ta zo ganin gida sosai suka yi hira da Farida wacce rabinta duk ƙarfafa ma Faridar gwiwar ne ta na nuna mata girman ƙaddara wacce mutum bai iya kauce mata.Sosai Farida taji daɗin zuwan nata can,sai kuma yanzu ne ta gane tabbas tayi babbar asara da ba ta ƙulla hulɗa da Maryam ba tun farkon shigowata familyn.
Lokacin da ta tafi gidan Abbasi ma neman gafarar tayi kafin ta sa a sauko da akwatin kayan Hawa,ta na kuka ta na ƙari ta baro ma Abbasi Ƴar sa wacce tuni Atine ta ɗauki nauyin kula da ita.
Lokacin da Farida suka shiga jirgi dan komawa Niamey sosai taji kewar ƴar ta sai dai babu yadda za ta yi,ko da suka isa Niamey tuni an zo ɗaukar su.
Kamar yadda suka tsara har da Hawali aka zo tarbanta,daga hilin jirgi direct gidan su Farida suka yi tsinke.
Escort sai take ma Hawali baya suke har cikin gidan,a zaune suka samu Mama a falo ta na ganinsu ta je ta kirawo Papa.Ba su wani sha wahala ba iyayenta suka karɓi tubanta tare da yi mata nasiha mai ratsa jiki inda Papa ke cewa "duniya makaranta ce yanzu dai ko rayuwar ki da ta Hawali sun ishe ki ISHARA,a kullum burinki ki zamo sama da ita ya zamana kin fi ta sai dai Allah ne ke yi ba mutum ba.A ta dalilin son zuciyar ki kin rasa miji,ƙafafu uwa uba lafiya to ina son wannan ya zame maki darasi daga yau ki koma ga Allah"banda shashekar kukanta ba ka jin komi,nan dai Hawali tayi masu sallama ta tafi.




Washegari
Sai ga motoci kayan abinci aka sauke haɗi akwatunan kayan Farida,sosai su Papa suka ji daɗin haka inda suka kira Hawalin suka yi mata godiya.








Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Farida kullum ta na cikin kaɗaici duk da kuwa kusan kullum ta na tare da Ɗiyarta ta waya su na appel video da Dr Halima wacce ita sam ba ta riƙe Farida a rai ba tsakani da Allah ta ke kula da Hawa.
Wanka Farida tayi tsaf ta shirya,a falo ta tarar da Mama bayan ta gaisheta ta fice zuwa asibiti karɓar magani wanda ta ke zuwa ɗauka duk ƙarshen wata.
Yau ma ta tarar da layi,ta na nan zaune kamar an ce ta juya idon ta ya sauka kan délégué wanda ya ke cikin layin maza na masu karɓar maganin ƙanjamau.




Da mugun mamaki cikin ɗaga murya tace "délégué... ?"da sauri ya waigo dan muryar ta raɗau ta sauka cikin kunnen shi,fitowa yayi daga layin ya nufo ta mamaki ɗauke da fuskar shi yace "wai Dr Farida ce?"kai kawai ta gyaɗa masa ta na jin wata irin kunya ganinta da yayi cikin layin ƴan HIV .






Wayar shi ya fiddo dalleliya yace "saka min lambar ki"babu muso ta saka masa,ba tare da sun ƙara cewa komi ba ya koma layin shi.
Ya rigaita amsa hakan yasa ya zauna zaman jiranta, ta na fitowa yayi mata alama da hannu cike da kunya ta ƙarasa inda ya ke jingine da motar shi.






Ciki suka shiga yayi driving na su,inda a hanya ya ke bata labarin irin gurɓataciyar rayuwar da yayi a baya kawai dan Allah ya nufe sa da kuɗi yayi ta yawo da matan banza ya na ɓata ƴaƴan mutane har Allah ya jarabce sa da SIDA.
Har gida ya kawota,Farida za ta bashi labarin kanta ya ɗaga mata hannu yace "duk na san komi saboda can ma'aikata yadda kika san kaladan haka ko ina ake hirar ki har cire ƙafafun ki da aka yi,yanzu abinda ni ke so da ke in kin shiga gida ki zauna kiyi tunani da kyau in kin amince cikin satin nan azo ayi maganar komi a ɗaura mana aure"da "toh in shaa Allah"ta amsa kafin ta shiga gida.








Labarin délégué ta baiwa Mama cike da murna Mama tace "to ai babu wata matsala gwara ku yi auren zai fi tunda dukan ku séropositif ne"murmurshi kawai Farida tayi dan ta tsani ace ita séropositif ce.
Da dadare Mama ta shaida ma Papa,shi ma sosai ya nuna farin cikin sa hakan yasa Farida ta shaida ma Délégué yadda suka yi da iyayenta .
Cikin sati guda kacal aka zo aka yi magana aka ɗaura aure,auren da kusan Hawali ta fi kowa jin daɗin sa dan ita ta ɗauki nauyin kayan ɗaki.




Watan auren su Farida ta samu ciki,tuni aka fara ɗaukar masa matakan tsaro na kariya.Sosai suke nuna soyayya ga junan su tamkar uwanda ba su da cuta mai karya gangar jiki,a yadda suke gudanar da rayuwar su in ka gani sai sun baka sha'awa.
Lokaci zuwa lokaci Farida ta kan je palais in Hawali na gida,wani sa'in ma har gida driver ke zowa ya ɗauke ta.


Auren Farida a bakin Adamu Abbasi ya same shi ,shi ma Adamun yayi aure har da yaran sa biyu.
Hawa na cika shekara biyu babu wasu ƴan watanni Farida ta haifo ɗanta namiji wanda ya ci sunan Abbas.
Su Dr Halima da Maryam sai da suka tafi biki haka ma Abbasi ba'a barsa a baya ba,ya je yayi ɓarin kuɗi dan sosai ya yiwa takwaransa sayaya.
Da za su tawowa ne suka baro ma Farida Hawa,sosai kuma ta ji daɗin haka saboda ganin Ƴaƴan ta su ke mantar da ita duk wata damuwa.






A ɓangaren Hawali kuwa sosai hankalin ta ya kwanta musamman yanzu da Kalil ya dawo hannunta saboda matar da Deeni ya aura kullum cikin gallaza masa ta ke shine a ƙarshe ya kawo mata shi.Sosai rayuwar Hawali tayi haske ta na samun kulawar mijin ta Jamal wanda ya haska duniyar ta ya maisheta mutum,ya gina ma iyayenta gida mai doron zabo a Tillabery ya bata jarin kasuwanci kuma.




****MARADI




Bayan wasu shekaru
Tuni Tantie Yusura ta sake aure,Inna kuwa ta koma Mai Jan Gero inda ta ɗauki riƙon Yusu wanda tuni ya shiga makaranta.
Maryam ce ta fito hannun ta riƙe da kaji wanda Rabe ya aiko mata jin wai ta zo garin duk da kuwa idonsa na son ganin ta amman ya ƙi zuwa.
Bayan Boot ta saka kajin ta na ɗaga ma Inna da hannu wacce Yusu da Abdallah suka sata tsakiya,Mahomet wanda ya riga ta fitowa dan tuni ya ke zaune cikin mota ya na jiranta.Vitre ɗin mota yayi ƙasa da shi ya na kallon yaran na sa wanda duk duniya bai da kamar su,murya a ɗan raunane yace "shi ma Abdallahn ta riƙe sa ne ko miye?"da sauri Maryam ta dube sa tace "eh yace zai zauna ne "cike da jin haushi ya kawar da kai,Inna da ke bakin ƙofar gida ta na kallon su tace "uwar mi ce ya ke cewa?"Maryam ba ta ce komi ba ta shige mota ya ja su.






Su na zuwa gida ya shige ɗakinsa,jikin Maryam ne yayi sanyi duk sai taji babu daɗi.Part ɗin ta ta wuce,wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa.
Ɗakinsa ta nufa,a zaune ta tarar da shi ya na duba syst dab da shi ta zauna ta ɗora kanta kan kafaɗar sa.Bai kulata ba ya cigaba da aikin sa,ta turo baki ta kai hannu ta na daddanna system ɗin.Tsayawa yayi hakan yasa tace "kayi haƙuri"ba tare da ta kalle shi ba,"haƙuri?da aka yi mi?"ya tambaya,amsa ta bashi "da na baro Abdallah can wajen Inna "ɗan ture ta yayi yace "a'a dan mi ai Ɗan ki ne tunda kin yanke hukuncin barin sa a can miye nawa?"a yadda ya yi maganar za ka gane ya na cikin fushi.
A shagwaɓe tace "dan Allah kayi haƙuri Allah zan haukace "Mahomet ya miƙe yace "daidai kenan sai mu yi ta haukan a tare dama mijin ki mahaukaci ne kin ga sai mutane su ce *MATAR MAHAUKACI* ta haukace "da sauri ta tashi ta na dire-diren ƙafafu haɗi da kukan shagwaɓa "Allah kar ka sake ce min matar mahaukaci tunda dai mijina lafiyar sa lau"da sauri Mahomet yace "a'a inda lafiyar sa lau da ba za ki bayar da yaron sa riƙo ba alhalin kin san nan da wani week..."saurin huging na shi ta baya tayi hakan ya sa shi ƙyalewa.






Lokacin da ya juyo ƙuri suka yi ma juna,kafin ya ɗan busa gashin idonta da sauri ta lumshe ido.A hankali ya ranƙwafo ya sa bakin sa cikin nata,halshen sa ya zura ya fara shan yawunta.
Jikinsa ta ƙara shigewa kafin ta ririƙesa da dukan hannuwan ta,tsawon lokaci kafin ya cire bakin sa ya ɗago haɓarta ya na dubanta da idon shi suka canza launi.Da sauri tayi ƙasa da kai,zip ɗin rigarta ya ja tare da yin ƙasa da rigar,da sauri ta faɗa ƙirjinsa saboda har kullum ta na jin kunyar Mahomet.Kan bed ya direta ya fara sarrafa ta,har zai shigeta ya fasa da sauri ta buɗe idonta jin ya kwanta kusa da ita ya na sauke numfashi.
Ido cikin ido suke kallon juna,kafin ya ɗaga mata gira ita kuwa ta turo baki ganin haka Mahomet ya rage masu hasken ɗakin kafin ya ziyarce ta.










Haka rayuwa ta cigaba da kansacewa yau daɗi gobe akasin sa, ɓangaren Dr Halima sosai ta samu nutsuwa zumuncin su da Maryam ya ɗore sosai kamar yadda ya ke wajen Hawali da Farida wacce aka naɗa shugabar mata ta masu HIV .


Taron buɗe asibiti M.M AGAJI ya tara dubbunan likitoci da iyayen su,likita ce ta azo a gani wace ta tara ko wane ɓangare na kiyon lafiya.
A gaban ɗumbin mutane Mahomet ya taimaka ma Maryam ta datse ɗan ƙyalen da yayi masu iyaka da shiga harabar asibitin,taɓi aka yi Mahomet ya ja hannunta suka shiga, Daddy da Ammi da su Tantie Yusura da Inna ma suka shiga kafin sauran jama'a .
Atine sosai taji haushin ganin asibitin Mahomet ta fi ta Ɗanta Abbasi amman da ta tuna hassada babu kyau sai tayi ta Istigfari,su Dr Halima da Abbasi sai duba waje suke suna yaba kyawun sa gami da yin addu'a.
Mahomet kuwa hannun matar sa ya jaye suka silale wani ɗaki,Maryam ta waro ido tace "Chouchou wai miye nufin ka mun baro baƙi a can fa"wani irin jawota yayi yace "babu ruwana da su uzuri ne ya taso dan haka a taimaki patient please Dr "dukan wasa ta kai masa a ƙirji ta na cewa "babu wani patient wayo ne kake son yi min"cak ya ɗauke ta ya ɗorata kan wani ɗan madaidaicin gado ya na mai cewa "ina son zama patient na farko da za'a duba matsalar shi ne"Maryam na murmurshi tace "to bari na fara gwada alƙalamin ka in har dagaske ya shiryar karɓar traitement ɗin Dr Maryam "fuska ya shagwaɓe yace "ai kuwa dai tamkar ya ji ki har ya fara..."saurin kai bakinta tayi kan lips ɗin shi tayi shi kuma yayi baya da su ya zamana ita ke bisan sa,har zai cire mata kaya yace "bari dai na rage hasken ɗakin ta yadda ƴan gulma ba za su ganin mu ba"Maryam ta turo baki tace "wlh kuwa kamar ka sani Mrs SADAUKI na nan ta laɓe ta na ɗaukar duk abinda mu ke ta na kaiwa can *MATAR MAHAUKACI* PAID"Mahomet ya waro ido yace "kai haba wannan tonon asiri har ina,kice duk ta tonare mu?"Maryam tace "sosai fah ba ka ga Halimatu tun daga Diffa ita da M Shakur ta Katsina da Lawiza suke sauraren kalar soyayyar mu ba?"da sauri yace "ke an yi fah haka dan kuwa haka na ritsa Queen Fulani ta na gulmata wai ashe har dukan ki na taɓa yi lokacin da ina hauka?"Maryam ta ƙyalƙyace da dariya tace "ai kuwa dai Mrs Shugaba da M Yusuf Dabo sai da suka ta yi min dariya, Princesse Aichatou da wasu ɗaiɗaikun FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS kawai suka tausaya min"Mahomet ya jawota yace "ke haba dan Allah?ki na nufi Real Aïcha da Sajida da Najaâtou Haladou duk ba su cece ki ba?" Baki ta kwaɓe tace "ai fah sai kayi ba su ne ƴan *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR 🇳🇪* ba?to duk dariyata suka yi"Mahomet ya ɓata fuska yace "ok tunda ma haka ne bari na ida kashe duk hasken ɗakin gaba ɗaya ,Mrs SADAUKI ba za ki sake leƙen asirin mun ba tunda har mun gano ki mi za mu ce Qalbi?"yayi maganar ya na tambayar Maryam haɗi da sake janyota ya manna jikinsa sosai a tare suka sauke wata sanyar ajiyar zuciya suna masu furta "Alhamdullah!"


To Ni ma Mrs SADAUKI 💫 a nan Ni ke cewa:


*ALHAMDULLAH !!!*




A nan na kawo ƙarshen labarin matar mahaukaci,godiya ta tabbata ga Allah mai kowa kuma mai komi da ya bani ikon gama sa lafiya.Ina godiya da dukan masoyana na gode sosai da kuka kasance tare da ni kuka fidda kuɗin ku kuka sayi book ɗina,na gode sosai da kuka nuna soyayyar ku gare ni😍😍😍 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment