Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu lafiya"
Hajiya Atine ta ja tsaki tace "ayi mu gani in tusa na hura wuta,aikin banza aikin wofi yaro ya yaje yayi shaye-shayen sa za'a liƙawa aljannu ina ce kwanaki gangaren Unwala aka samo sa ya na sha wiwi wa ya sani ma har da yaran mutane ya ke ƙwaƙulewa"ta na gama faɗa ba ta ida rufe bakinta ba Ammi ta wanketa da mari daidai nan kuma Alhaji Issufu ya sallamo tare da kunno kai Abbasi na take masa baya.






Hajiya Atine abun nema ya samu daman hakan ta ke so ta faru kawai sai ta ɓare baki ta na kuka,tare da cewa "Ammin Mahomet ni kika mara?daga faɗin gaskiya ?ai shawara na baki ban ce doli sai kin yi aiki da ita ba kuma Allah na gani ba da wata niyya na kira Mahomet mahaukaci ba sai dan takama doli amman ba komi"ta ida maganar ta na sharar ƙwalla tare da ƙoƙarin fita.






Alhaji Issufu wanda fuskarsa tayi ja saboda ɓacin rai yace "Hajiya je zauna"babu muso Atine ta zauna,ya maido dubansa ga Ammi wacce ta ke kallonsa "ke kuma ina son sanin mi tayi maki kika mare ta saboda na ji ƙarar marin balle ki ce sharri tayi maki"babu tsoro ko shakka Ammi tace "eh ƙwarai kuwa na mareta saboda ba zan bari ta tozarta min Ɗa ba tare da yi mashi sharri mafi muni "da sauri Hajiya Atine tace "miye na sharri daga nace jiya Abbasi ke faɗan ciwon Mahomet kamar shafar aljannu shine fah na zo mata da batun Malamin nan da ya yiwa Ramlatu aiki ya fitar da aljannun da suka hanata aure yanzu haka fah an yi auren har da albarkar yara shine Ammin Mahomet ta rufe ni da masifa wai ɗan ta ba MAHAUKACI ba ne da na matsa kawai sai ta kwaɗa min mari"ta ƙarashe ta na fashewa da wani irin kuka kai kace mutuwar uwa ko uba aka shaida mata.






Ammi tsaye tayi ta na kallon Atine ta na mai jinjina ƙarfin makircinta da yadda ta iya drama kai kace ƴar wasar kwaikwayo, Alhaji ya dubi Ammi yace "miye laifinta a nan dan ta nuna maki hanyar alkhairi?zo ki rama marin da tayi maki"da sauri Abbasi ya matso yace "Daddy kar ayi haka tunda ta riga ta faru kawai abar zancen ka yi masu nasiha kawai,kai fah shugaba ne in kace ta rama to wata masifar ce za ka kuma kunnowa sulhu ya kamace ka"
Atine ta miƙe ta na jin wani gululun baƙin ciki dan ta san tunda Abbasi ya saka baki to fah maganar sa Daddy zai ɗauka "Ni na tafi Abbasi ka karɓan abincina tunda dai a tare mu ka yi girkin balle a hana ni"ta faɗa ta na mai ficewa Abbasi ya dube ta da kallon mamaki dan ya san ƙarya ta gilla saboda a part ɗin ta ya barta lokacin da zai tafiya ɗaukar Daddy aéroport.






Kitchen Ammi ta shige dama jus ne ta ke ɗurawa a budo dan ta gama komi.Mahomet wanda tun ɗazu ya kasa yin komi ya kalli Daddy da idonsa da ke nuna zallar tsoro,gajiya da kuma begen mahaifin na sa.Hannuwa Daddy ya buɗe kamar wani ƙaramin yaro ya ƙarasa inda ya ke tsaye tare da faɗawa jikinsa, Daddy ya zagaye bayansa da hannuwansa ya na sake saka sa ƙirjin sa.Sanyayar ajiyar zuciya Mahomet ya fara saukewa ya na jin wata nutsuwa na shigar sa kafin wasu hawayen farin ciki su zubo masa ,a zuci yace "Allah kai ne abun godiya ina sake gode maka bisa ni'imar da ka yi min wacce ba kowa ka baiwa irin ta,ni ɗin na kasance tamkar ruwa da ƙanƙara ne wani gun nayi tauri wani gun kuma da taushi.A baɗini na sani mai lafiya ne kamar kowa amman a zahiri mahaukaci ne ni wanda kai kaɗai ka san miye sirrin da ya ɓoye wanzuwata a ruwa biyu."ƙara rungume mahaifinsa yayi wanda duk duniya bai da kamarsa,saboda sai in ya na tare da shi ne kawai ya ke sanin ainahin shi ɗin wanene ya ke kuma samun nutsuwar yin tunani daidai da na masu cikakken hankali.






"Mu je ka faɗan yanda ka yi kewata"cewar Daddy ya na zame sa daga cikin jikinsa ya zaunar da shi kan salon kafin shi ma ya zauna ya kamo tafukan hannun Mahomet.
Murmurshi yayi ya dubi mahaifin sa yace "Daddyna..."sai kuma yayi shiru ya ɗaga kai ya kalli Abbasi wanda ya ke tsaye rataye da jakar Daddy ya harɗe hannuwa ya na kallon su.Kamar wani ƙaramin yaro Mahomet ya turo baki ya na kallon Abbasi wanda ke masa dariya,wacce kuma ba ta rasa nasaba da yadda sangartar Mahomet ɗin ta motsa.
Daddy ya dubi Abbasi yace "Abbasi ba mu wuri za mu yi magana da farin cikina"Abbasi na dariya ya ajiye jakar ya shiga kitchen ya tarar da Ammi tsaye ta na sharar ƙwalla.A gabanta ya tsaya ya marairaice fuska yace "please Ammi ki yi haƙuri dan Allah ni na san sharri Hajiya tayi maki,dan Allah ki ƙara haƙuri ki bar biye mata "kai kawai Ammi ta jinjina tare da ɗaukar plate ta zuba masa abinci.






A falo kuwa murya ƙasa-ƙasa kamar ta munafuki Mahomet ya fara magana "Daddy nayi kewar ka sosai,a kullum idona su na kan hanya da tsumayen ganin ka,zuciyata ta raunata sai ni ke ganin tamkar in babu kai babu Mahomet wani sa'in kuma sai naji tamkar kai ne innuwata wacce zan raɓa na ji sanyi"shiru Daddy yayi ya na kallon farin cikin na sa don duk duniya babu abinda ya ke so sama da Mahomet in ka fidda Inna ita ma ɗin dan ta kasance uwa mahaifiya gare sa.




Rasa mi zai ce yayi kawai sai ya jawo sa zuwa jikinsa,lamarin Mahomet na basa tsoro sosai haɗi da mamaki.Bayan Daddy babu wanda Mahomet kan iya yin fira da shi tunda wannan cutar ta same sa,in kaji yayi magana to ba mai tsawo ba ce.
Ammi ta fito ta dire tray bisa table tamkar babu abinda ya faru ta tsiyaya lemu ta zuba a cup ta ɗan duƙa kaɗan tace "sannu da zuwa Abbansu fatan kun sauka lafiya?"murmurshi Daddy yayi ya karɓi kofin yayi Bismillah ya fara sha ya na jin sanyi biyu na ratsa zuciyar na farko yadda Ammi ta kasance mace tagari komin suka yi faɗa ba ta hana shi abinci ko kuma haƙin kwanciya,na biyu kuma daɗin ɗanɗanon lemun gami da sanyin sa.
Sai da ya kai rabi sannan ya ɗora kofin a bakin Mahomet ,sannan yace "alhamdullah uwa tagari"Abbasi ya kalli yadda Daddy ke mu'amula da su Ammi ba kamar yadda ya ke yi ba in ya je can part ɗin su wato ɓangaren Hajiya Atine.A zuci yace "baƙin halin Hajiya ya sa haka"a zahiri kuwa cewa yayi "Ammi zan wuce ina abincin Hajiya ɗin?"miƙewa Ammi tayi ta koma kitchen ta zubo masa a kula kafin yayi sallama ya fita.






Tamkar wasu sabbin aure masu ɗan jinjiri haka suka saka Mahomet tsakiya su na cin abinci cike da soyayya da ƙaunar juna.






★★★ *MAI JAN GERO*




Cikin gunguni Maryam tace "Ni fah na gaji da wanke pant da tsumman nan ,sabida Allah kamar wata ƙazama kullum cikin wankin jini"ta ida maganar ta na matse wani ƙyalen atamfa wanda Inna ta bata ta na yin ƙunzugu da shi.
Ta na gama wankan ta fito ta ɗaura alwala kafin ta wuce ɗaki,pant da ƙyalen ta shanya bisa ƙarfen gado sannan ta ɗauki wani busashen ƙyale gami da pant tayi ƙunzugu kamar yadda Inna ta koya mata.
Tapis ta shimfiɗa ta saka hijabi,har ta fara iƙama taji Inna na cewa "au!wai dama ba ki gama jinin ba shine na gan ki ɗazu ki na sallah asubahi?"da sauri Maryam ta juyo ta na kallon Inna wacce ta dawo daga gidan buki.
Rau-rau tayi da ido tace "har yanzu ya na zubowa"Inna tace "shine kuma kike sallah ba tare da kin gama ba?"Maryam ta ɓata fuska tace "in ya na zubowa ba'a yin Sallah?" "Eh mana sai ya ɗauke kin yin wanka tukunna sannan ki koma yin Sallah"
"Shine kuma kika ƙi faɗa min kika bar ni ina ta aikin banza?"cewar Maryam ta na zare hijabi.
Inna tace "ah toh ni na san digin garin wai baƙuwa da tayi kashi cikin moɗa,na zata kin gama ne da na ga kin yin wanka da asuba zan ce ko na tsarki ne kika yi"
Maryam tace "wankan tsarki?"Inna ta ce "ungo dubala da jus in kin canye sai na yi maki bayani"karɓar ledar tayi ta ajiye kan gado tace "a'a yi min yanzu"
Inna ta fara yi mata bayanin daga lokacin da mace ta fara yin jinin haila ta girma kuma in namiji ya taɓata ciki za ta yi,sannan in an gama ana yin wankan tsarki nan dai ta koya mata komi.....








*Ga masu son yin payement ƙofa a buɗe ta ke, 200₦ ƴan Niger 300f duk wacce ta san ba ta shirya saya ba dan Allah kar ta min magana*
+22795045822






Jikar Rabo ce 😎
[07/02 à 12:44] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```


Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR* 🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻






*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*


```MRS SADAUKI 💫✍🏻```


_______________________




Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*




*PAGE* 7-8




Fitowarta daga wanka kenan taji sallamar bakin ƙofa,bokitin ta ajiye ta gyara zaman hijabinta kafin ta leƙa.
A tsaye ya ke hannunsa riƙe da fararen zomaye🐿️ mata da miji,ya na ganinta ya washe baki yace "Mairo ta ai na zata ba za ki fito ba"sai ta ɗan sunne kai tace "ah haba miyasa za ka yi wannan tunanin?" Rabe ya miƙo mata zomayen yace "wlh Mairo sai ni ke ganin kamar Inna ba ta son soyayyar mu da ke shiyasa ni ke jin tsoro"kallon zomayen tayi tace "Ni fah tsoronsu ni ke,ina kuma ka samo su?"yace "sayo su nayi domin ke,kin san yau sallar masoya shine na kawo maki cadeau"har ga Allah Maryam taji daɗi hakan yasa ta miƙa hannu ta damƙi cikin ɗaya da sauri ta saki jin taushi.
Rabe yayi dariya yace "kunnuwa za ki kama saboda Zomo duk jikinsa tsoka ne babu ƙashi"ta ɗan ja da baya tace "to in fah na katse masa kunnuwa ,a'a ni dai gaskiya ba zan iya riƙewa ba"dariya yayi yace "to mu je na kai maki su cikin gida sai na saka maki su cikin akurkin kazar da na baki kafin na kawo kajin"hanya ta basa ya shigo ya saka su cikin keji wanda ainahi dama shi ya kawo shi da yayi mata alƙawarin kaji sama da shekara ɗaya kullum yau gobe zai kawo.






Ya na saka su ya rufe yace "zuwa an jima zan kawo maki karas da salati sai ki basu"Maryam tayi murmurshi tace "na gode sosai matuƙa Allah bar zumunci"Rabe har ya washe baki jin ƙarshen furucinta yasa ya gimtse yace "zumunci kuma Mairo?ko har yanzu ba ki fara sona ba?"
Ƙofar shiga ɗaki ta nufa ta na mai cewa "yanzu dai sai an jima kar Inna ta tarar da kai ka sa ta doke ni"ba don ran Rabe ya so ba ya bar gidan cike da zullumi.




Gefen gado ta zauna ta fara shafa mai ta na mai cewa "ah yo toh ina dalili ka sa ni yin ƙarya sabida Allah a rubuta min zunubi,ban sonka amman ba zan faɗa ma ba kar ran ka ya ɓace amman nan da ɗan lokaci zan bar ma garin gaba ɗaya Allah dai ya bani BEPC ina samu zan koma gidan Kawu Issufu"ta na gama shafa mai ta saka kayanta ta haye gado ta fara tunanin rayuwar da za ta yi a Maradi.
"Ko yaya zan kuma kasancewa?an ce jarabatu bai da lafiya yanzu ƙila ba zai takura ni ba mtws da wasu ido na sa irin na kwartaye"Maryam ke sambatu ita ɗaya sai kuma ta bushe da dariya tace "oh Maryam ko ina kika taɓa ganin idon kwarto?"sai kuma tayi shiru ta na tunani "kamar dai irin na Mahomet masu shegen kaifi sai yayi ta kallon mutane kamar maye"ta faɗa ta na mai lumshe ido.








★★★ *MARADI VILLE*




Alhaji Issufu wato Daddy shine hakimce bisa kujera ta alfarma ya na latsa waya yayinda matan sa su ke zaune ɗaya waje suna jiran jin abinda yasa ya kira su.
Sai da ya ɗauki lokaci ya na aiki da wayar kafin ya ajiye ya dube su cikin bada umarni yace "an kammala gida an yi komi zan turawa kowacenku 1million ta sayi abinda ta ke buƙata zan haɗe ku gida guda da Bilkisu (ɗayar matar sa wacce ke wani gida daban)sannan falo guda ne ni zan zuba kujeru da duk abinda ya dace ban son rigima ko kuma tsiyar gumi duk wacce ta nemi tayar min da hankali zan sallame ta tunda ba auren zobe mu ka yi ba"tunda ya fara magana suke kallonsa Hajiya Atine tace "to ai wannan rashin adalci ne wato ita ga matar so shiyasa ba ka kirata ta zo nan ba in ya so duk wannan jawabin ka yi shi gabanta amman da ya ke ba ka son ranta ya ɓace shine..."ɗagan ta hannu yayi yace "kin fi kowa sanin Balkisu ba ta iya shirmen da kuka iya ba,kuma déjà na sanar da ita yanzu haka ma har ta fara kai kayanta.Abu guda ni ke son na gaya maku wannan banzar kishin ku ajiye sa a nan saboda matata baturiya ce ba ta son kwaramniya"ya na gama faɗa ya tashi tsaye tare da ɗaukar wayar sa ya nufi waje inda Abbasi ke zaman jiran sa cikin mota.
Hajiya Atine ta dubi Ammi tace "kin ji wani rashin adalci ko?yanzu hakan da yayi daidai ne?"Ammi ta miƙe tace "ai sai haƙuri tunda kuma ya riga ya yanke hukunci"Atine tace "ai kamata yayi ki yi masa magana tunda ke ce babba, wannan abu sam babu adalci shiyasa banzar yarinyar nan ta ke wani jiji da kai ta na hura hanci sama saboda ta ga ya fifita ta sama da mu"Ammi dai ba ta biye ta ba ta dawo ɓangarenta ta fara shirin komawa sabon gida.








Abbasi da Daddy hanyar Mai Jan Gero suka kama cikin tafiyar da ba za ta wuce awa ɗaya ba suka isa.Tun a bakin ƙofa su ke jiyo masifar Inna sallamar da su ka yi ma ba ta amsa ba,Maryam na ganin Daddy ta rugo da ɗan gudunta ta na shafar ƙwalla tace "Kawu dan Allah ce ta bar min zomaye na kar ta fitar da su"Daddy ya riƙo hannun ta suka ida shigowa ciki sai a lokacin Inna ta ɗago ta kalle su.
"Ka na fa ganin yarinyar nan ta raina ni ai yau saura kaɗan ta aika ni lahira ƙila da ka tarar ana zaman zana'iza ta"
Abbasi ya kece da dariya yace "Inna ki mutu har a kaudo ki duk ba mu sani ba?ai mu ne fark..."kallon da Daddy yayi masa ne ya sa shi yin shiru.
"Mine ne ya faru?"Daddy ya tambaya,Inna tace "ah toh mi ma a bai faru ba,ka na gani yarinyar nan da kwashe-kwashe ta je ta jajiɓo min zomaye kingin kaɗan na kare ƙafa ina shigowa cikin gida na gane maka abu da dogayen kunnuwa farare ƙal kamar Mala'iku sun nufo ni ita ma ta kwaso da gudu ta na ta shiga uku Inna taimaka,na zata mugun abu ne nayi jifar ƴan bori na faɗi ƙasa wai ashe nufin ta na taimaka kar zomayen su tsere"
Tun daga Daddy har Abbasi dariya suka shiga yi, Daddy yace "miyasa kuka fiddo su?wai ina ma kuka samu zomaye?"Inna ta kaiwa Maryam ranƙwashi tace "wannan za ka tambaya"Daddy ya maido dubansa ga Maryam, rau-rau tayi da ido ta ƙi faɗa.




Tabarma Inna ta shimfiɗa masu suka zauna,nan fah aka fara gaishe-gaishe.Maryam ta kawo masu ruwa sai wani sunne kai ta ke yi kamar ta na gaban surukanta har abun ya baiwa Daddy dariya yace "Maryam sai yanzu aka tuna da tabi'ar?har yanzu kunyar nan ta ki ta na nan ashe ta Fulani"Inna tace "ta sakalci dai,jiya ma haka ta sunne kai gaban saurayi kai kace ubanta ne"Daddy ya ɓata fuska yace "saurayi kuma Inna?shine kike barinta ta na zuwa zance karatun fah?"
Inna tace "ita ke fita da kanta,ina su Mahamadu da mamarsa?"Inna ta juya zancen Daddy ya ɗan nisa yace "su na nan lafiya na baro su suna shirin komawa sabon gida"jin furucin sa yasa Inna ɓata fuska ta juye kai.
Daddy yace "dan Allah Inna ki yi haƙuri ki koma can Maradi ko dan cigaban karatun Maryam"
"Babu inda zan je Maryam kuma ga ta nan sai kun dawo amman ni ba zan zauna da matanka ba su na yi min shegantaka iri-iri kamar sa'arsu"Inna ke faɗa cikin jin haushi.
"In shaa Allah hakan ba za ta kasance ba Inna na yi maki alƙawari kuma zan gindiya sharaɗi duk wacce ta ɓata maki rai a kan auren ta"cewar Daddy,Inna tace "a'a ba za ayi haka ba,ku je kuyi zaman auren ku "Abbasi yace "haba matar dan Allah ki tashi ki shirya mu tafi"sigar da yayi magana yasa Inna yin dariya tace "abu kamar lakuru ai ko tafiyar ce ba yau ba"Abbasi yace "ai kam yau ƙafata ƙafar ki har Maradi da shirin tafiya da ke mu ka zo"
Inna tace "a'a sai dai ku tafi da Maryam ni zan zo daga baya"Abbasi ya riƙo hannun ta yace "ki min alƙawari?"kai ta ɗaga masa kafin ta zubo masu abinci Maryam kuma ta fara shirya kayanta.






Sai marice liƙis suka baro Mai Jan Gero suka nufo Maradi ko da suka shigo gidan tuni an fara kiraye-kirayen sallah magrib.Part ɗin Ammi Maryam ta wuce bakinta ɗauke da sallama amman sauran ta tsaya cikin maƙogwara ganin Mahomet gaban tv daga shi sai gajeren wando fararen cinyoyinsa duk a fili ga gargasa duk ta luluɓe su.
Rawa ya ke irin ta yadda ya ga mutanen ciki na yi,dariya Maryam ta tuntsire da ita ta na sake kallon yadda abarsa ke yin ƙasa da bisa a zuci tace "ƙaton banza ji kamar wani mahaukaci sai rawa ya ke kuma a haka"Muryar Ammi taji ta na cewa "wa ni ke gani kamar Maryamun Inna"sai a lokacin ta bar kallon Mahomet wanda tunda ya ji dariyarta ya tsaya cak ya na kallonta zuciyarsa na dokawa.




"Ina wuni Ammi "Maryam ta faɗa ta na mai ƙarasawa,"lafiya lau ya gida ina su Inna da fatan duk ku na lafiya ?"
"Lafiya lau tace a gaishe ki ma"Maryam ta faɗa ta na mai zaunawa,Ammi tace "ina amsawa ya aka yi kika gane gidan?dan rabon ki da nan an kusa shekara ai"
"Tare mu ke da su Daddy da kuma Abbas sun wuce masjid ne"Maryam ta bata amsa, Ammi ta ce "shiyasa je ki bedroom ki yi wanka ina zuwa"miƙewa tayi Mahomet ya raka ta da ido ya na jin wani haushin ambaton sunan Abbasi da ta gyara da Abbas.
Hannunsa Ammi ta jawo tace "mu je ka tafi ɗakin ka"murya na ɗan rawa yace "zan yi sallah"da murna Ammi ta raka sa ɗakinsa sai da ta tabbatar yayi alwala har ya fara sallah ta baro gun.






Pompo Maryam ta buɗe ta shiga yin wanka kamar ba gobe,ta ɗauki sama da minti talatin sannan ta fito ta yi sallah magrib.
Ta na nan zaune Abbasi ya shigo mata da akwatin kayanta,ta gefen ido ta ke ƙare masa kallo ta na jin sanyi na ratsa ta mai garwaye da shauƙin sa.
Ya na ajiyewa ya juya ya fita Maryam ta bi bayansa da kallo, Allah na gani tun ta na ƴar ƙarama ta ke dakon son Abbasi wanda ta kasa ɓoyewa har ya kai ya gane amman tsabar iya yi ya nuna kamar bai sani ba.








Goshinsa na ƙasa sama da minti goma ya na kwarara addu'a kamar ba gobe,hawayensa sai ambaliya suke su na jiƙa tapis.Can ya ɗago yayi tahiyar sallah ya salamce yayi tasbihi ya karanta *Allahumma ajirni minal naar*⁷ *allammma inee a'uzhu bika minn azabil ƙabar,wa minn azabi jahanam,wa min fitinatul masihi dajal*³ ya kawo Ayatul Ƙursiyu ya shafe jikinsa ya na jin sa garau cikin hankalinsa.








★★★ *NIAMEY*




"Ƙasa..ƙwas"haka sautin takalmin ta suke fitarwa,sai girgiza jiki ta ke manya mazaunanta da breast na tsallo kamar za su fasa ɗamamar rigarta su fito yayinda dogon gashin ke kaɗawa.Tunda ta shigo jinin kowa ya koma ga akaifa sai gaisheta su ke ita kuma ta na wani basarwa,har ta kai bakin office ɗinta ta juyo ta kalli délégué wanda shine ke kula da duk wani abu na ma'aikatar.
"Ka zo."shine abinda ta faɗa ta na mai shigewa ciki,muƙut ya haɗiye wasu yawu ya na jin wani abu mai ɗaci cikin ransa.
Ko zama ba ta yi ba ya shigo a daƙile yace "ga ni"ba tare da ta juyo ba tace "ya ka gama tunanin ko yaya?"cikin jin haushi yace "eh nayi gaskiya ba zan iya saɓawa mahallacina ba,ban taɓa yin zina ba kuma ba zan fara a kan ki ba "juyowa tayi ta ƙure sa da manyan idonta wanda aka ƙarama gashi tace "ba ka isa ka bijirewa umarni na ba délégué doli ka biya min buƙatata,kai ne namiji na farko da Farida ta taɓa jin sha'awar sa "
Délégué yace "ba zan yi zina ba muddin ina cikin gulbin hankalina na gaya maki tun farko ki sake tunani"
Cikin karya murya tace "sha'awar ta ka fah na kai ta ina?" "Kiyi aure"shine abinda délégué ya furta,ɓata rai tayi tace "bai cikin tsarina ban na gaya maka ban taɓa sanin mace ce ni ba sai da na ɗora idona kan ka"ta ida maganar ta na mai takowa inda ya ke......






*Littafin kuɗi ƴan Nigeria 200₦ ƴan Niger kuma carte airtel ta 300f za ku turo wadda ta shirya saya ta yi min magana ta WhatsApp* +22795045822








Jikar Rabo ce 😎
[09/02 à 15:24] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```


Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR* 🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻






*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*


```MRS SADAUKI 💫✍🏻```


_______________________




Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*




*PAGE* 9-10




Caraf idonsu ya sarƙe cikin na juna,wani irin sarawa kan délégué yayi ya na jin sa wani iri.
Murmushin mugunta Farida ta saki daidai lokacin da ta ƙaraso gab da shi har su na jin hucin juna,dukan hannuwanta ta ɗora saman fafaɗan ƙirjinsa ya sauke numfashi ya na mai ƙara sanya idonsa cikin nata.
Lips ɗin shi ta fara shafawa da ɗan yatsanta wanda ya sha faux ongles (akaifun kanti)da sauri ya lumshe ido ya na jin wani sauyi wanda bai san taƙamaimai na miye ba.Shi dai bai jin sonta amman a shirye ya ke da bin duk umarnin ta,"kiss me"ko gama rufe baki ba ta yi ba délégué ya sauke bakinsa kan laɓanta.
A hankali ya tura halshensa cikin bakinta ya fara jujuya shi kafin ya yiwa hannuwansa bisa manyan mazaunanta.Wani yarrr Farida taji hakan yasa ta ɗan ƙankamesa,shi kuma har jikinsa ke kyarma ya na mamatsa ta haɗi da embrassé ɗin ta.An ɗauki lokaci kaɗan kafin ta raɓa gefe ta na mayar da numfashi,karon farko kenan a rayuwarta da ta taɓa kasancewa da namiji duk tantirancin ta iya gidan rawa ne da shan giya amman namiji bai taɓa burge ta ba balle so délégué ma haka kawai taji ta na sha'awarsa musamman manyan taɓansa baƙaƙe masu kauri.




"Zauna a nan"cewar Farida ta na mai jawo masa kujera,kamar wanda yayi maye haka délégué ya zauna.Ta ƙasan ido ta ke ƙarewa babbar hallitar sa kallo wacce ta ɗan kumburo ta jikin wandon sa,numfashi ta sauke ta na jin wani feeling gami kuma da tsoron haɗuwar su a bed.
Gorar ruwa ta basa ya sha nan ya sauke ajiyar zuciya zufa na tsatsafo masa,babu jimawa ya ji nutsuwar sa ta dawo.Ya kalli Farida yace "ina son komawa akwai aikin da ni ke son ƙarasawa koko ki na da buƙatar wani abu?"kai ta girgiza masa ta na jin wani sanyi na ratsata tace "no je ka RDV ɗin mu sai gobe a hotel Larewa ka zamana cikin shiri" kai ya jinjina alamun ya ji sannan ya fice.
Ɗan tsalle Farida tayi gami da ƴar rawa tace "waiii ! Yayi Malam ka iya aiki ai na zata kwalli nan ba zai yi ba"ta na

Please Login or Register in order to submit comment