Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ta zowa ciki kuwa har da ƴan Madarumfa dangin mahaifin ta wanda suka zo da biyu jin wani sabon al'amari wai Yusura ba ta mutu ba.




A can ɓangaren Farida kuwa sam ba ta san abinda ke faruwa ba saboda cikin ikon Allah ko da ta tashi jinin ya bar zuba haka kuma Abbasi bai shaida mata da zubewar cikin ba.
Wata irin kulawa ta musamman ya ke bata wacce ta danne haushin dawowar da taji yace Atine za ta cigaba da zama gidan su.
Wasu manya-manyan safar ƙafa Atine ta saka a ƙafafu kamar tsohuwar kuturwa,abinci ta girka masu wanda Farida kawai ta ci su kuma sun kasa ci saboda zullumi.






Kamar za tayi kuka haka ta ke magana da Mama ta na cewa "zan zo sati mai zuwa in shaa Allah please kar ki gaya ma Papa na san in yaji hana ni zai yi"daga can ɓangaren Mama tace "to Allah kai mu,nace Farida in jin dai ba wata matsala ba ce?"sai da ta ɗan yamutsa fuska tace "Mama ina da début ne(ciki) kuma kawai sai naji ina sha'awar garin Niamey"
"Allah mun gode maka,kin ga abinda ni ke faɗa ma ki ko Farida ? Allah ne ya karɓi addu'a ta amman da bari kika yi har ya kai haihuwa sai ki zo in ya so ki haihu nan"da sauri ta ce "a'a Mama ban iyawa wlh sati guda ma ki ka ji nace saboda in ƙara samun ƙarfin jikina ba dan haka ba da tuni na zo,ina dalili an kwaso gayyar tsiya an kawo min cikin gida"Farida ke faɗa ganin innuwar Atine bakin ƙofa......
[10/03 à 12:36] Mrs SADAUKI 💫: *51-52*






Da sauri Atine tayi baya ta na goge ƙwalla,ɗakin da aka sauketa ta koma ta na jin zuciyar ta na wata irin suya sai dai babu halin yin faɗan.Bakin katifa ta zauna ta rabka uban tagumi a zuci tace "duniya kenan!duniya juyi-juyi yau ni ce ake faɗa ma baƙar magana ba tare da na ɗau mataki ba,duk wannan abu ni na jawosa rabon ayi na tafi gidan boka ashe silar kuturcewata ce"ta ida zancen zucin ta na mai duba ƙafafunta uwanda ke cikin safar ƙafa.
Gundululun faratun ta shafa ta na ƙara jin haushi fiye da na farko, turo ƙofa aka yi Abbasi ne gaishe da Atine yayi kafin ya ɗora da faɗin "Maryam ta sauka an samu baby boy sannan Tantie Yusura ma ta dawo"a yadda ya ke maganar kawai za tsinkayo zuciyar shi na cike da rauni kawai jarumta ce ya ke.
Sunne kai Atine tayi ta na jin kunyar Ɗan ta, Abbasi ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da magana cikin sigar nasiha "Hajiya kin ga abinda na ke guje maki nan tun farko,ranar nadama saboda ita gaskiya ko mutum ya binne ta cikin ƙasa to tabbas wata rana za ta fito.Yanzu dai ko wannan zama da safar ƙafai ya isa ya zame maki darasi da kuma nadama,dan haka ki fara Istigfari ki nemi tuba gun Ubangijin ki"kuka Atine ta fashe da shi wiwi kamar wacce aka aiko ma da mutuwar uwa ko ta uba,sai da tayi mai isarta sannan ta ɗago ta kalli Abbasi wanda ya ke tsaye bakin ƙofa tun shigowar sa.
"Na gode sosai Ɗana in shaa Allah zan yi duk yadda kace,ka rubuta ka ajiye Atine ta sauya ta rikiɗa mutumniyar ƙwarai ba kamar ta can baya ba sannan zan jure karan tsana da tsangwama"da sauri Abbasi yace "haba Hajiya wa zai tsangwame ki?nan fah gidana ne kuma da ni da duk abinda da na mallaka ƙarƙashin ikon ki su ke"
Wani farin ciki ne ya luluɓe zuciyar Atine wanda ta kasa ɓoyewa har sai da tayi murmurshi tace"Allah maka albarka je ka gun iyalin ka dare yayi"sallama yayi mata ya wuce gun Farida .
Ta na ganinsa ta taso ta tarbe sa, yau wata irin soyayyar shi ta ke hakan yasa tayi ƙoƙari sosai ta ja ra'ayinsa suka raya daren duk da Abbasi ya nuna bai so haka ba.








Washegari
Abbasi da Farida suka zo barka,tamkar babu abinda ya faru haka ya gaishe da su Ammi .
Farida sai shan ƙamshi ta ke musamman da ta ga Dr Halima zaune kusa da Maryam, Abbasi ya matso ya karɓi jaririn daga hannun Dr Halima ya na sakar mata murmurshi.
Addu'a ya yi masa kafin ya ɗauki matar shi ya maida ta gida,ko da ya tafi office ya tarar da har Halima ta riga shi.
Kallon-kallon suka fara yi kafin ta turo baki gaba,kai ya girgiza yace "to kuma mi nayi?"
"Komi"ta bashi amsa,ya ja kujera ya zauna ya tsura mata ido "ni ka bar kallona"ta faɗa a shagwaɓe shi kuwa ya maƙe kafaɗa yace "sai kin ce ki na sona"ta waro ido yace "eh sosai kice Abbas ina son ka"


Dariya tayi tace "naji zan faɗa ba yanzu ba amman"ya marairaice fuska yace "Please!"da sauri tace "no yanzu ina aiki ne ka jira har na gama"ai kuwa Abbasi ya gyara zama bai bar gun ba har sai da Halima ta furta masa kalmar so dakyat.








Ana gobe biki su Mahomet suka koma sabon gidan su wanda ya sha kyau har ya gaji sai dai na Abbasi ya fi shi girma.
Sosai ƙawayen Maryam suka zo duba gida masu taya murna na yi ƴan baƙin ciki irin su Rahila sai da suka samu abun kushewa cikin gidan.
Ranar sunan kaf ƴan ma'aikatar su Maryam sai da suka zo biki in ka fidda Farida wace girman kai ya hana ta zowa,a cewarta duk yaran mijinta ne ba girmanta ba ne taje ta zauna cikin su.
Sai da Maryam tayi arba'in sannan Inna ta koma can gidan Daddy.




Ɓangaren Farida kuwa sai shirye-shiryen zuwa Niamey ake tafiyar da ta so yi tun tuni amman Allah bai nufa ba sai yanzu.
Ta na zaune ta na shirya kayanta a valise Abbasi ya shigo hannunsa riƙe da plate ɗin jalof wacce Atine ta girka masu,wani ƙazini ne ya bugi hancin Farida da sauri ta tashi ta shiga toilet ta fara kelaya amai kamar za ta fitar da hanjin cikinta.
Fuska ta wanke da baki kafin ta fito ta na wani layi kamar wacce ta sha giya saboda jiri,da sauri ta toshe hanci ta na kallon Abbasi wanda shi ma ita ya ke kallo mamaki cike da fuskar shi.
"Dan Allah ka fita ka ci abincin ka waje ban son warin shi"Faridar ta faɗa ta na jan numfashi,da sauri kuwa Abbasi ya fita sannan ya dawo.A kwance ya tarar da ita sai wani sauke ajiyar zuciya ta ke,wuyanta ya taɓa yaji rau.Text ya aika ma Dr Halima babu jimawa kuwa ta zo,duk da Farida na cikin halin jinya bai hanata harar Dr Halima ba wacce ke dubata haɗi da yi mata allura kafin ta fice ta koma asibiti.




Murya kamar za tayi kuka tace "yanzu sabida Allah Abbas ka rasa wacce za ka kira ta duba ni sai maƙiyiyata?wai ma ba wannan ba ina ka samu lambar ta?"bai tankata ba sai ma sumar kanta da ya shiga shafawa ya na mai cewa "babyna ina ga fah doli a ƙara ɗaga tafiyar nan har ki warware kafin nan cikin jikin ki yayi ƙwari"Abbasi ya faɗi haka saboda Dr Halima ta shaida masa Farida ta samu shigar ciki ne.






Baki ta turo gaba tace "a'a wlh ni kam tafiya zan yi can in naje nayi jinyar"
"A'a ba zan bar ki ba,saboda za ku wahala sosai"ya na gama faɗa ya tashi ya fice ba tare da ya jira cewar ta ba.






Kuka Farida ta fashe da shi saboda yanzu duk wani iya shege na ta ba ta iya juya Abbasi yadda ta ke so,a kullum sake nuna mata ya ke ya isa da gidan shi.
Waya ta jawo ta kira Mama amman har ya katse ba ta ɗauka ba,cike da jin haushi ta miƙe ta nufi falo ta fara zage-zage "ina dalili ina mafari ƙaddarar jalof ta tsiya ta tado min da rashin lafiya har ya jawo zan fasa balaguro,dama na san an daɗe ana baƙin cikina to gani nan bari nan."Atine na jin abinda Farida ke faɗa yasa ta fito daga ɗaki ko kafin ta kai ga tambayarta lafiyar ta kuwa?sai kawai Farida ta ɗora waya a kunne kamar mai appel ta na cewa "mutu ka raba takalmin kaza in ma wani munafurcin ne kike ƙullawa to sai dai ya koma kan ki,zama daram a gidana tunda mijina na sona ba zan kula da wata banza ba ta zo ta kashe min aure kamar yadda ta kashe na ta iyeee!kuma..."marin da Atine ta ɗauke ta da shi ne yasa ta cin burki ba tare da ta shirya ba,ta buɗa baki za ta magana Atine ta ƙara mata wani sannan ta nunata da ɗan yatsa tace "ki shiga hankalin ki nan ba wajen ba ne,ke cikin ƴan iskan ma ke ce Auta ni kuma uwar su ce.Ke in ba dan duniya ta juya min baya ba har kin isa na zauna innuwa guda da ke?au!ke nan baƙin cikin zamana a gidan Ɗana kike? lokacin da na haife shi ki na ina?nayi wahala da shi har ya zama abun ƙwarai kawai yanzu kai tsaye kike son raba ni da shi?to da ni da ke shege ka fasa duk yawon biyar bokayen ki da malumai ke ko rabina ba ki kai ba kuma ki jira Abbasin zai zo zan nuna ma ki na fi ki cikakken iko a kan sa" Atine na gama faɗa ta koma ɗaki ta bar Farida shaye da mamaki sam ba tayi zaton Atine masifafiya ce har haka ba.










Maryam ce zaune ta na gyara ma Abdallah kwanciya,Mahomet ya shigo kamar an jefo shi.
Da sauri ta miƙe ta faɗa jikinsa ta na cewa "oyoyo baban Abdally"ƙugun ya zagaye kafin daga bisani ya cirata sama ya na juyi da ita,sai da yayi mai isar sa sannan ya direta ya na cewa "albishirin ki?"sai da ta ɗan riƙe sa saboda juwa ba tasake ta ba sannan tace "goro fari tasss"Mahomet ya ɓata fuska yace "no ban son goro a bani abincin ruhina kawai"dariya tayi tace "to ai dama ni ta ka ce"
Ya laƙace mata hanci yace "na samu babban aiki za'a riƙa biyna a ƙalla one million a wata ɗaya"zaro ido Maryam tayi tace "wai gaske?"kai ya jinjina mata sannan ya ɗora da "in shaa Allah zuwa gobe zan wuce Agadez a can ne zan yi aikin"Maryam ta ɗan ɓata fuska tace "to ni fah ina za ka bari na?"
"Nan gida mana ai zan rinƙa zuwa duk ƙarshen wata"jiki a sanyaye tace "to Allah sa alkhairi"ya amsa da "amen"kafin yace "muje ayi min wanka"










"Innalillahi wa'inna iley raji'un !"shi kawai Daddy ke maimaitawa ya na kankamar Balkisu wacce ke ta buge-buge da ihuce-ihuce.
Jiki na ɓari Ammi ta nufi ɗakin Inna a zaune ta tarar da ita ta na canza ma Yusu kaya "Inna ki taso Balkisu ce ke ihu duk ta farfasa kayan gidan hannuwanta sai jini suke zubarwa"cewar Ammi hankali tashe,zama Inna ta gyara tace "tsuntsun da ya ja ruwa ai shi ruwa ke duka,kin manta zancen malam ne na cewa duk ranar da aljannun suka samu garara sai sun koma jikin wanda ya haukata Mahomet?"Ammi ta gyaɗa kai Inna ta cigaba da cewa "da farko na zata Atine ce tayi aikin lokacin da naji mugun aikin da ta aikata kan Yusura sai daga baya ne na gane aikin Balkisu ne dan haka taje can ta ƙarata da su"
Ammi ta marairaice fuska tace "duk da haka Inna ya kamata ki taso"Inna ta riƙe haɓa tace "kin ji ki da wani batu to zuwa na mi zai hana ?aljannu dai ne duk wanda ya nemo su wajen shi suke zuwa tunda ta nemo kayanta ai shikenan"




"Inna tashi mu tashi"cewar Yusu Inna kuwa ta miƙe tace "yanzu kuwa ɗana mu je,mu gidan ma za mu bari Mai Jan Gero zan je nayi ziyara"






Inna ta kama hannun Yusu suka bar gidan ko kallon inda su Daddy suke ba tayi ba ya ƙulle hannuwan Balkisu ya na yi mata addu'a.
Abu kamar wasa sai ga Balkisu ta fara hauka mai digi,maluman duniya an kawo amman aljannun sun ƙi magana,Mama da Abba kamar za su yi hauka haka Daddy ya basu ɗiyar su saboda ba zai iya zama da ita ba.Bakin Balkisu bai rufuwa kullum cikin bada labarin ita ta haukata Mahomet ta ke,tun ana ƙulleta cikin gida har Mama ta gaji ta barta ta na fita yawo da wannan damar matasan unguwa ke tausheta su biya buƙatar su.






A can gidan Abbasi kuwa tsaka mai wuya ya shiga saboda Atine tayi tsaye ta buga kai da ƙasa sai ya sallami Farida,haƙuri ya shiga bata ya na cewa "Hajiya dan Allah kiyi haƙuri ki bari ta zauna ko dan saboda sabon cikin da ke jikinta"Atine ta karkaɗa ƙafa tace "to ta ci albarkacin cikin amman duk da haka sai ka ƙaro aure in kuma ka ƙiya Allah ya isa nonana da ka sha".....
[12/03 à 03:53] Mrs SADAUKI 💫: *END*






Ba ƙaramin tashin hankali Farida ta shiga ba lokacin da ta ga maganar auren Abbasi ta kankama amman har yanzu ba ta san wace ce amarya ba.Ta na ji ta na gani a doli Abbasi ya kai kuɗin aure babban baƙin cikinta kuma ɗaya tayi ta buga lambar malam Jaye amman ta ƙi shiga,da wannan ƙarin haushin yasa ta tattare ta tafi Niamey duk da cewa Abbasi ya hanata.
Da isarta can kwana ɗaya kawai tayi ta nufi Gamkalé unguwar su malam Jaye,tun a bakin ƙofa ta ga canji saboda babu clients kamar kullum.
Ya na ganinta ya tashi zaune ya na wasar baki,zama Farida tayi ta na duban shi kafin tace "malam gani na zo da ƙafafuna tunda ka ƙi ɗaukar kirana"
Malam Jaye ya gyara zama yace "ba ƙin ɗauka nayi ba wayar ce na ajiye gaba ɗaya saboda harakokin sun yi min yawa,ba na da isasshen lokaci shiyasa na ware rana ɗaya ta hutawa ba ki ga yau babu kowa ba?"
Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "haka ne na lura,yanzu ni dai ka yi min abinda ya kawo ni ina cikin wani hali tsangwamar Uwar miji ga shi kuma zai yi min kishiya"nan Farida ta shiga labarta masa yadda rayuwar gidan aurenta ta ke ciki tun dawowar Atine.
Bugun ƙasa ya fara kafin ya ɗago yace "eh gaskiya Uwar mijin ki ba ta da mutumci dan kuwa mugun halinta ya rabota da gidan ta sannan kamar yadda tace maki ɗin sosai ta ke da hatsabiban Malamai masu yi mata aiki ,gaskiya tunkarar ta abu ne mai wahala"
Kuka Farida ta fashe da shi tace "dan Allah ka taimake ni kasa a fasa auren nan sannan ita ma Uwar mijin kayi mata sihirin da zai sa ta bar min gidana"shiru malam Jaye yayi kafin yace "abu ne mai wahala gaskiya amman in kin matsa doli nima ki biya min buƙatata tunda aikin na da hatsari sosai "Farida tayi saurin katse sa da cewa "ba dai zina ba?"kwanciya malam Jaye yayi yace "hanya a buɗe ta ke in kin ji ba ki iya ki tashi ki tafi"shiru Farida tayi ta na tunani kafin daga ƙarshe tace "na yarda"




Ƙurya ɗaki suka shige malam Jaye ya turmumushe ta son ran sa har sai da ya gaji sannan ya barta,Farida kuwa da toshe hanci da tsirtar da yawu haka ta biya masa buƙatarsa.
"Ki je gida kiyi barci ina nan da ke auren nan zai watse ko ƙaunar jin sunan wata mace ba zai ƙara son ji ba,ita kuwa Uwar shi za mu haukatata ta can bi duniya kowa ya huta,ba zan amshi kuɗin aiki ba wannan karon sai buƙata ta biya "da murna Farida tayi godiya ta tafi bakin titi ta samu taxi.




Dariya malam Jaye ya tuntsire da ita yace "hegiya to nima masu taimakon nawa sun watse sun bar ni,yo ina na ga aljannun da zan yi aikin da su hhhh"ya tuntsire da wata dariya ya na shirin kwanciya kenan yaji cacaniyar mutane ko da ya fito daga ɗaki sai ya ga duk gidan ya kama da wuta yayinda kuma daga can waje mutanen da ya ci kuɗin su ya yaudare su ba tare da yayi masu aiki ba suke ta zagin sa.
Malam Jaye na ji ya na gani ya zauna wuta ta toye sa ƙurmus ya zama toka.






Farida na bisa hanya ƴan sanda suka tsayar da taxi ɗin su da wasu sauran mutane,mutanen cikin taxi ɗin ne wata ta ja tsuki tace "dama na san an rina tunda naji ana sanarwa matar Son exellence Jamal za ta yi fita gari zuwa unguwannin talakawa"
Da sauri Farida tace "ki na nufin saboda ita ce aka tsayar da mu?"matar ta bata amsa da "eh mana,ba ki ga duk an baza ƴan sanda ba sai katse wata matar gwal mtsw"matar ba ta ida rufe bakinta suka fara jin jiniyar motoci da sauri Farida ta buɗe marfin taxi ta fito ta tsaya tsakiyar kwalta duk da kuwa ƙoƙarin hanata da wani ɗan sanda ya ke.




A haukace driver ya ke gudu duk ƙoƙarin sa na taka burki abu ya gagara sai da ya bi ta kan Farida ya darje mata ƙafafu uwanda suka fita tak ɗaya tamkar fitar taya.






Motar da Hawali ke ciki ita ce ta biyu suna zowa suka tsaya,sojoji na take mata baya haka ta ƙarasa inda mutane suka yi cincirindo.
Ido ta waro lokacin da idonta ya sauka kan fuskar Farida wacce ta ke a sume ,durƙasawa tayi har gefen rigar gizner ɗin ta ya shiga cikin jinin da ya ke kwance a kwalta.
Ba ta san lokacin da hawaye suke tsatsafo mata suna zuba kan fuskar Farida,cikin kuka ta fara kiran "ƙawata?ƙawa Farida dan Allah ki tashi kar ki mutu ki bar ni"janyeta aka yi lokacin da motar asibiti ta ƙaraso.
Zagayen unguwannin talakawan da Hawali ba ta yi ba kenan,asibiti suka tafi babu jimawa aka shiga duba ta musamman yadda aka gani ta samu rakiyar First Lady.






Har dare Farida ba ta farfaɗo ba,ita kuwa Hawali a doli ta koma gida.
Labarin accident ɗin Farida ya game Niger sarai tuni an faɗa a labarai wanda ta nan ne su Mama da Papa suka samu labari da su kansu su Abbasi.










Bayan kwana biyar
Tuni Farida ta dawo hayyacinta tayi arba da sabon tashin hankalin fitar ƙafafunta wanda ya haifar mata da ƙaramin hauka,Hawali kuwa ta na bakin ƙoƙarin ta duk da uban zagin da Farida ke aika mata mai cike da tsantsar hassada.




Tuni Abbasi ya zo Niamey dan doli,ya so yayi jinyarta sai dai babu halin yin haka a matsayin sa na shugaban asibitin sa ga kuma shirye-shiryen aurensu da Dr Halima.


Sati biyu yayi a can kafin ya juyo maraɗi, Mama ita ke jinyar Farida yayinda Hawali ta ɗauki duk nauyin kula da su ɓangaren harakar kuɗi.






Ranar da Farida ta cika wata uku,tuni ciwon ya fara warkewa,babu laifi yanzu ta rage zage-zage sai ma hankali da ta maida kan Ɗan cikinta wanda cikin ikon Allah bai zube ba.
Safiyar da Hawali ta zo dubata ne ta riske su cikin tashin hankali wanda ba komai ya haifar da haka ba sai cutar ƙanjamau da aka tabbatar Farida na da ita ranar da aka fara yi mata awon farko.
Dan doli Abbasi ya sake dawowa saboda kiran gaggawa da Hawali ta sa aka yi mashi,jininsa aka auna aka tabbatar da lafiyar shi lau.
Cikin kuka Farida ke yi masu bayanin inda ta ke zaton ta samu H.I.V wato ga malam Jaye,tuni kuwa Hawali ta tura bataliyar sojoji dan ƙwamuso shi sai dai kash ƴan unguwa sun ƙona shi.






Farida na jin haka tayi ihu ta na cewa "wayyyo na shiga uku na lalace shikenan ba zai yi min aikin ba,dan Allah ku kai ni gidan wani malamin wlh in Abbas yayi aure mutuwa zan yi"
Abbasi wanda haushi da takaicinta duk sun cika shi,jin wai da igiyar aurensa taje ta kwanta da wani ƙaton banza.
Ƙanƙance ido yayi yace "ai kuwa sai dai ki mutu dan kuwa tuni Dr Halima ta shigo gidana yanzu haka ta na ɗauke da cikina,kuma ki sani na sake ki saki uku in kin haife min yaro zan zo na karɓe sa kar ki shayar da shi guba"ya na gama faɗa ya ajiye mata takardar sakinta.






Papa ya ja Mama suma suka bar ɗakin bayan Papa ya tabbatar ma Farida sun yarda ta taje can ta nemi wasu iyayen amman ba su ba,cikin kuka ta diro daga kan gadon sam ta manta ma da har yanzu ƙafafuwan ba su warke ba sai da ta ga suna fitar da jini.






Da sauri Hawali ta duƙa ta rungumeta tare da fashewa da kuka tace "ƙawata duniya ce ke haka,duniya juyin waina yau in ta na yayin ka gobe sai ta sake ka ta kama wani,a baya mun yi kuskura sosai shine na zuwa gidan boka wanda ban ƙara yarda ba sai da aka naɗa Jamal shugaban ƙasa nan na gane malam Jaye ba malami ba ne ɗan tsibo ne.Sannan lokacin da na samu cikin Ahmad duk a mafarki a nuna min komi,nayi neman ki dan na nusar da ke muhimmancin abota amman ban samu ba har gidan ku naje na tarar da su Papa sun tashi doli na haƙura.Dan Allah abinda ni ke so da ke kiyi haƙuri ki sa ma zuciyar ki dangana,sannan ki ƙudirci tuba tun yanzu ni kuma nayi maki alƙawarin zan kasance tare da ke har ƙarshen rayuwa"






Hawayen Farida ne suka tsaya cak jin kalaman Hawali "ƙawa duk irin cutar da nayi maki amman har yanzu ki na jin sona a ranki?kuma dagaske kin yafe min?"
Hawayen da ke kan kumcinta Hawali ta share mata kafin tace "bai komi bari na kirawo Dr ya duba ki "da sauri ta riƙo hannun Hawali kafin tace "dan Allah ki sa a cire min cikin nan ban so na haifo yaro mai irin cuta ta"
Hawali tace "a'a ai ba zai zo da ciwon ba ko kin manta akwai prévention ?"Farida ba tace komi ba Hawali ta fita ta kirawo Dr aka mayar da ita kan gado kafin a duba ta.










**** MARADI




Dr Halima ce zaune ita da Maryam wacce ta kawo mata ziyara, videos biki suke kallo yadda aka gabatar da bikin Dr Halima ɗin da Abbasi.Video na kaiwa ƙarshe sai wata ta shigo ashe na bikin Farida ne lokacin da aka yi party.
Dariya Maryam tayi tace "ashe ki na da shi"tayi maganar ta na kallon tv inda aka wano Mahomet duk ya ririƙeta kamar za'a ƙwace ta.
Dr Halima tace "eh wlh ashe Hubby ya na da shi,jiya na kalli video wlh in an ga Abban Yusu ba'a cewa bai da lafiya"
Maryam tace "a'a fah ana ganewa dubi yadda ya manne min,duk inda na yi ya na biye da ni"
Sallamar Atine ce ya katse su,da sauri Maryam ta miƙe ta karɓo Abdallah wanda tun zuwan su ya ke hannun Atinen "ki basa ya abincinsa, bawan Allah ya sha barci "cewar Atine da murmurshi Maryam ta karɓe sa ta na cewa "ai kuwa dai"kafin ta zo ta zauna.










A can gidan Daddy kuwa yau sosai suka ji dawowar Inna wacce tayi zamanin ta a Mai Jan Gero,wanda kuma tayi hakan ne dan baiwa Ammi da Daddy damar shaƙatawa tunda yanzu ita ɗaya ta rage cikin matan.
Yusu na kwance jikin Tantie Yusura wacce ke basu cigaban labarin nahiyar matsafa,da ɗan mamaki Ammi tace "yanzu wai dagaske naman mutum su ke ci?"
Tantie Yusura tace "Allah kuwa ,dama yadda tsarin ya ke su baiwa doguwa jini su kuma su ci naman to ni inda Allah ya yi min iyaka da su saboda ina yawan yin Azkar haɗi da karatun Alqur'ani.Lokuta da dama sai an shirya ni cikin kayan yanka sai shugaban matsafan yace wannan nemanta bai ciyuwa har yanzu mu ƙara bata lokaci"
Daddy yace "wlh har yanzu ina jin tausayin ki cikin raina,yadda kika yi rayuwa cikin aljannu to wai ake ma ki na yin sallah?"murmurshi Tantie Yusura tayi kafin tace "a sace ni ke yi saboda ko a can akwai mutanen da su na zaune ne kawai dan doli,akwai matar da ke taimakona"


Ammi tace "to wane irin abinci kuke ci ?"ta bata amsa da "irin wanda ake ci nan,sai dai babu nama"Inna ta tashi tace "dan Allah ku bar maganar nan tunda dai Allah ya kuɓuto mana ke,su kuma uwanda suka gina ramen muguntar sai su yi ta zama ciki"cike da jimami Daddy yace "wlh kuwa Inna kamar kin sani jiya-jiya nan na gamu da Balkisu tsakiyar kasuwa ta na hauka tuburan aka kuma samu maras imani

Please Login or Register in order to submit comment