Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ɗauka ta zuba ruwan zafi ta saka Lipton ɗaya sannan ta fashe ɗanyen ƙwai guda ta kaɗa ta zuba zuma sai da ta rumtse ido tare da daɗe hanci sannan ta shanye.
Ammi murmuje kawai tayi saboda kusan kullum dama sai sun yi darama da Inna ta ke sha yau kuma tayi da kanta,ƙaton plate ɗin da zuba frite ta buɗe ta ɗauki ɗaya ta ci saboda bakinta babu daɗi "ki zuba ma mijin ki na shi ki kai masa can ɓangaren ku"ta tsinkayo muryar Ammi ,babu muso ta hahaɗa komi ta aza a tray ta kai masa.
Tsaye ya ke bakin gadon Yusu ya na tofe sa da addu'a *A'uzhu bi kalmatillahi taamati min sharri ma kalaq* .
"Barka da shan ruwa "ta kuma faɗa juyowa yayi ya na kallon ta kafin yace "haka ake yi ma miji Barka da shan ruwa babu huging babu komi alhalin ya wuni da ƙishi?"wuya ta rausayar tace "ayya Abban Yusu ni fah sam ban san haka ake yi ba"
"To yanzu tunda kin san yadda ake sai ki zo kiyi"ya faɗa ya na ɗan ɗaga mata gira,jiki babu ƙwari ta zo ta rungume sa tace "bne rupture"ya kwaɓe fuska kamar wani ƙaramin yaro yace "bne rupture qui?" Sai da ta juya ido tace "Abban Yusu mana"ɗan tureta yayi yace "ban so a sake min suna"yadda yayi maganar a shagwaɓe ya bata dariya sai tace "to Chouchou na" "waiii!"ya faɗa tare ɗaukar ya fara juyi da ita gabanin ya sauketa yace "wash kin sa ƙuguna ciwo kin zama ƴar lukuta gaskiya sai an biya ni ɗaukar da nayi maki"Maryam ta saki murmurshi tace "bari nima na ɗauke ka"kai ya girgiza yace "no!mu je dai ki taya ni wanka"bai jira cewar ta ba ya ja ta.
Kamar wani ƙaramin yaro haka ya shige cikin baignoire ita kuwa ta shiga yi masa wanka soso da sabulu kai kace Yusuf ne ta ke yi ma wankan.
Kukan Yusu ne ya sa ta barsa ta fito,ɗaukar sa tayi ta koma bakin bed ta fara shayar da shi.Mahomet na fitowa direct wajen su ya nufa kusa da ita ya zauna ya kai hannu ya laƙace kumatun yaron yace "ka hana ayi ma Daddyn ka wanka ko?"kamar wanda ke jin magana haka ya tsaya da shan nonon ya na ɓangala dariya.Hannu ya kai ɗaukar sa Maryam tace "bar shi ya gama kai ma ga abincin ka can ka ci" "ke ma ai abinci ce"ba ta kula sa ba hakan yasa ya miƙe ya na dariya.
Ko da ya shirya frite ɗin ya zuba masu,ta shimfiɗe Yusuf yace bai san wannan ba doli ta ƙarasa da shi ta zauna su na ci Mahomet na yi mata hirar tun lokacin ta na ƙarama da yadda ya ke sonta.
"Shine kuma kake muzguna min kake nuna ba ka ƙamnar gani na?"cewar Maryam, murmurshi yayi ya ɗauki frite wanda ba'a sa masa komi ba ya saka a hannun Yusuf sannan yace "gata ni ne yi maki ai,saboda duk wacce ta tashi cikin sangarta to mijinta da ƴaƴan ta ne da wahala.Da farko dai kin ga in mijin ya shigo sai ya rasa wa zai yi ma wasa uwar ko ƴaƴan?"dariya Maryam tayi tace "to ai dukan mu kai ne shugaban mu"bai ce komi ba saboda kiran sallah isha'i da ya ji,toilet ya shiga yayi alwala "ki shirya tarbar mijin ki da zarar ya dawo yau B.S.B.S"a shagwaɓe tace "Yusu fah bai yi barci ba"har ya kai bakin ƙofa yace "ki san yadda za ki yi da shi"ya na gama faɗa ya fice,tashi tayi ta sauka ƙasa ta kai ma Inna shi kafin ta zo tayi sallah ita ma,ta nan na zaune ya shigo direct wajen maɓalin wuta yayi ya kashe hasken kafin ya zo ya sukuce ta.












A ɓangaren Farida kuwa tunda ta ga Abbasi ya fara take-taken kula ƴan mata ta buga ma malam Jaye waya,magani ya aiko mata ta Bus taje ta karɓa.Kullum sai ta barbaɗa ma Abbasi shi cikin abinci da ruwan wanka,muɗus ya bar maganar ƴan mata ya fara bauta ma Farida duk abinda ta ke so shi za'a yi maganar kuɗi kuwa kai kace account ɗin ta ce saboda yadda ta ke bishasharta da su.






Ta na kwance Abbasi na yi mata tausa wayarta ta ɗau ringing,ɗagawa tayi ta na ce "hello matar soja "daga can ɓangaren Hawali tayi dariya tace "auren soja ko kata'i ƙawa ko zaman kirki ban yi,yadda kika san doki haka Jamal yayi sukuwa a kaina saboda kawai zai tafiya mission "dariyar ƙeta Farida tayi tace "ya yi min daidai ai gobe sai mu ga ta jajanta cewa Abban Kalil raggo ne"da sauri Hawali tace "ƙawa ban gaya maki ba ai Abban Kalil ya dawo har ma ya je Tillabery ya karɓo Kalil gun Anyya wai na taimaka ko saboda yarona na koma gidan sa "Farida ta ja tsuki tace"ke ƙyale ɗan iska bayan ya gamo yawon dandin shi wa ya sani ma ya kwaso cutar HIV"
"Ki bari kin kuwa san yadda ni ke tsoronta har sunanta ban ƙaunar ji,haka jiya da na tafi awo sai da aka min ibar jini"
"Awon mi?"Farida ta tambaya ta na mai tashi zaune,Hawali ta bata amsa "awon ciki mana kin san ya shiga 3month"zuciyar Farida ce ta tsinke a take taji wani abu na yi mata yawo cikin maƙogwaro wanda ta kasa tantance na miye.
"Yanzu Hawa ki na da ciki shine ba ki faɗan ba har ya kai 3mois?ok daga yau na san zaman da ni ke da"ƙit Farida ta kashe waya ta na jin wasu zafafan hawaye na zubo mata .
Abbasi ya shiga bata haƙuri da kwantar mata da hankali,hawayen ta goge tace "Hubby ka na ganin Hawali ma da tayi aure bayan na mu ita ma ciki ne da ita"kawai sai ta fashe da kuka.
"Ya Salam !"Abbasi ya furta kafin ya jawota zuwa jikinsa ai Farida kamar jira ta ke sai ta ƙara sautin kukan,a haka ta lalube numéro Mama bugu biyu ta ɗaga jin kukan Farida ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba.
"Mama kin ji Hawali ma ciki ne da ita"cewar Farida bayan ta tsagaita kukan "to shine mi dan Hawali na da ciki?tun farko da nace kar ki sha maganin hana haihuwa ki bari har kiyi ta farko ya kika ce min?cewa kika yi a'a ba yanzu ba ke ba ki shirya aje yara ba da yarintar ki su zo su mayar da ke tsohuwa to ga irin ta nan mtsw "Mama ta kashe wayar dan ita ma a can ɗin ba wani jin daɗi ta ke ba tunda Papa ya tashi tsaye da kare kansa daga sharrin ta na zuwa gun maluman tsibo sam ta kasa juya shi yadda ta ke so.


Zuciya na tuƙuƙi Farida ta tashi ta shige bedroom sannan ta saka key ta rufe, toilet ta shiga ta wanke fuskarta kafin ta kira Malam Jaye ta sanar da shi burin ta .
Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta furta "Hawali in kin san wata ai ba ki san wata ba wlh,doli na raba ki da cikin jikin ki kowa ya rasa wato yanzu hankalin ki ya kwanta ba ki da matsalar komi sai ni yanzu kawai ke cikin damuwa"ganin Hawali na cigaba da kiranta yasa ta saka number liste noire ta yadda ko ta kira ba za'a samu ba.










Washegari
Maryam na kitchen za ta ɗora ruwan wankan Yusuf ta jiyo ihun Balkisu ,da sauri ta nufo falo sai kuma ta tsaya cak zuciyarta na halbawa da ƙarfi sakamakon jin furucin ta "ba laifina ba ne Mama ce ta saka ni dan Allah Alhaji ka tashi kar ka mutu ka bar ni Innalillahi wa'inna iley raji'un na shiga uku na lalace na kashe shi"kalmar ƙarshen ce ta saka Maryam yin wani gigitacen ihu mai haɗi da ƙara wacce ta janyo hankalin duk illahirin jama'ar gidan.




Balkisu na ganin su ta ƙaraso ta na nuna Maryam sai ta nuna Daddy wanda kumfa ke fita ta bakin sa,a kiɗime Mahomet ya kira mai gadi suka ciciɓi Daddy aka wuce da shi asibiti sai dai ko kafin a kai ya bar motsi......
[02/03 à 09:17] Mrs SADAUKI 💫: *41-42*








"Innalillahi wa'inna iley raji'un"Mahomet ke nanatawa ya na kallon fuskar Daddy wacce tayi fyau,su na zuwa asibiti aka shiga da shi ciki.
Tuni Abbasi ya zo, Mahomet ya tambaya amman ya yi mashi shiru ya kasa tambaya saboda tsaka mai wuya da ya ke ciki na ƙazafin da Balkisu ta ke ƙoƙarin ƙaƙaba ma matar sa.


Fiye da minti talatin kafin Dr ya fito fuska babu walwala da sauri Mahomet ya tare sa ya na tambayarsa "Dr da ransa?"Dr ya gyaɗa kai da sauri Mahomet ya sauke ajiyar zuciya kafin Dr yace "sai dai hanjin cikin sa sun samu matsala doli sai an yi masa opération hakan kuma ba zai yiyuwa ba doli sai ƴan sanda sun saka hannu saboda alamu sun nuna caise ɗin kisa ne"
Abbasi wanda dama tun a gida Atine ta shaida masa komi yayi waje da gudu bai tsaya ko ina ba sai police station,babu jimawa kuwa suka zo hannun suka saka bayan ƴan tambayoyi kafin su wuce can gida.
Kamar yadda Balkisu ta shaida ma ƴan gidan haka ta miƙe ta na cewa "tun bayan dawowar Alhaji daga masjid ya zauna nan ya na tilawar alƙur'ani ni kuma ina gefen sa zuwa can sai Maryam ta fito ta nufi kitchen ,ganin haka Alhaji yace na karɓi alƙur'ani na maida ɗaki ko da na dawo sai na tarar da shi ya na kakari yayinda ita kuma ta na tsinkayo ni tayi sauri ta ruga kitchen sai bayan taji ihuna kuma sai ta fito"a yadda ta ke jawabin ta na kuka kamar ranta zai fita za ka ɗauka gaskiya ne.
Maryam ita kuwa har tayi kukan ta gaji idonta sun bushe,sai da ta ga an saka mata ankwa kawai sannan wasu hawayen suka ziraro mata ta na kallon su Inna da Ammi wanda suma kukan su ke.






A can asibiti kuwa tuni an fara aiki , Mahomet sai sintiri ya ke sam bai san abinda ke faruwa ba sai da Ammi ta je asibitin ne ta ke shaida masa.
Kafaɗun Ammi ya riƙe ya na jijigata cikin fitar hayyaci "ta yaya har kuke tunanin Maryam za ta iya aikata haka Ammi ?miyasa kuka bari aka tafi da ita?har yanzu kun kasa gane makircin Balkisu ne da manufarta?"sai kuma ya sake ta ya na ganin sam hakan da yayi bai kyauta ba,ya dunƙule hannu ya naushi iska kafin ya nufi hanyar fita nan suka ci karo da Abbasi riƙesa yayi yace "Mahomet ..."ture sa yayi ya na harar sa kafin ya wuce babba comsariat ta Maradi.
Da ya tambaya ya na son ganin ta sam ƙin fiddota suka yi sai da ya nemi alfarma a kai shi ya ganta ko da daga cikin grillage ne.
Maryam na zaune bisa wata cakusasar tabarma wacce tsabar wahala ta sa duk ta cashe,ta na ganin Mahomet ta miƙe tsaye ta nufo daidai inda ya ke tsaye,hannu ta ziro ta tsakanin ƙarafunan ta na kuka ta girgiza kai tace "wlh ba ni na kashe shi ba ƙarya ta ke sharri ne ta haɗa min"Mahomet ya matse hannunta yace "na sani zuciyar mai kyau ce kamar yadda mamalakiyarta ke da kyau,ko kiyashi na san ba za ki iya cutarwa ba balle mutum wanda ya kasance mahaifi a gare ki.Ki kwantar da hankalin ki zan fitar da ke",
Ta na kuka tace "Yusu na gida ba su bari na ɗauko sa ba please karɓo min Ɗana"jingina Mahomet yayi da grillage ya juya mata baya ya na jin wani abu na sukar masa zuciya,hannunta ta kai ta sarkaye cikin sa kafin cikin muryar rauni tace "Please Mamet" "zan kawo sa "ya bata amsa "to ka juyo ka kalle ni mana"
"Ba zan iya ba zuciyata tayi rauni sosai "
"Dan Allah chouchou kar ka karaya Allah na tare da mai gaskiya kuma duk abinda ka ga ya faru dama ya ƙaddara haka"da sauri ya juyo,hawayen kumatun ta ya shafe kafin ya tafi dan tuni ɗan sandar ya fara shaida masa lokacin da aka basa ya ƙare.










Wani kuka mai ƙarfi ya kubce mata ganin mijinta uban ƴaƴan ta ya tafi ya barta a nan,daga can bayanta taji an ja tsuki.
Waigowa tayi ta dubi matar wacce a ƙalla za ta kai sa'ar Ammi .
Kallon da ta ke jefo mata kawai ya tabbatar mata da ba ta da mutumci, muryarta ta tsinkayo ta na cewa "ke zo nan"babu muso Maryam ta ƙarasa.






"Yi min tausar har sai nayi barci tunda ke kika tashe ni da wannan ruɓaɓen bakin na ki"cewar matar ta na mai gyara kwanciya,tausar Maryam ta fara yi mata ta na tunani game da matar can taji tace "ƴaƴa na biyu a duniya ba su kula da ni shiyasa ni ke cin bashi sosai har ya kai an saka min uwar rikici dan ba biya ni ke yi ba,rabon ayi na ci kayan wata mata da ta zo karɓar kuɗin mu ka kece da faɗa a ƙarshe na buga mata murfin tukunya a kai maganar da ni ke yi maki yanzu ta na babba asibiti ko rai ko mutuwa ke kuma laifin mi kika yi?"matar ta faɗa a ƙarshe kuma ta tambayi Maryam babu muso ta shaida mata duk yadda aka yi.
Tashi tayi tace "kan uban can!"








***NIAMEY




Hawali ce zaune kan salon sai faman fyace majina ta ke ta na kuka,yayinda ta cigaba da kallon Sheikh Bashir Ghana inda ya ke wa'azi kan alƙiyama da irin azabar da Allah ya tanada ma mushrikai.
Ta na nan zaune ta lumshe ido a zuci ta ƙudirta aniyyar ta tuba kenan ita da zuwa gidan malam ko boka sai kuma a lahira in akwai,tashi tayi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fara jera sallah ta na kuka wiwi tare da neman gafarar Ubangiji .
Suratul baƙara tayi daloading ta kunna ta na jin wani sanyi na ratsa zuciyar ta,kira ya shigo wayar ta ɗaga ganin Jamal ne.
Bayan sun gaisa ya ke shaida mata sun isa ƙasar Mali lafiya,barka tayi mashi da fatan Allah tsare har zai kashe yace "sai na ji kamar ki na cikin damuwa"da sauri tace "babu komi kawai kewar ka ce ni ke"yayi murmurshi yace "ragguwa yanzu da kika ga ba ni nan ko?to in shaa Allah ina san juyowa nan da 2week akwai wani abu mai muhimmancin da zan yi"cikin shagwaɓa tace "na zata gobe za ka ce shine har 2week?"dariya yace "d'ici 2semaines ɗin ma c'est pas sûr Madam kawai ki taya ni da addu'a Allah sa abun ya zo mana da sauƙi,ya na babyna fatan ya na lafiya?"Hawali ta shafi marar ta sannan tace "yayi kewar Daddyn sa"
"Kice masa ya ƙara haƙuri kaɗan in Daddy ya dawo har sai ya gaji da ziyarar sa"nan dai suka cigaba da hirar su ta masoya.








Da daddare haka Hawali ta kamo tashar sunnah tv ta na sauraron wa'azi daga nan barci ya ɗauke ta abun ka ga mai ciki.
Wani hayaƙi mai launin duhu ta gani a bakin ƙofa ya na son shigowa amman ya kasa,daga can bakin ƙofar kuma ta ke jin ana ce ma Ɗan cikin ta ya fito da sauri ta dafe cikin ta na addu'o'i haɗi da kuka amman sai barazanar rabata cikin ake.Firgigit ta farka,zuciyarta ta dafe ta na ƙara tuna abinda ta gani cikin mafarki.Cike da tsoro ta kira Jamal ta shaida masa,shi kuwa yace ta je tayi alwala tayi sallah ta nemi kariya daga sharrin magauta hakan kuwa tayi tun daga ranar kuma ta mayar da karatun Alqur'ani abokinta su na waya da mijinta ya na ƙara encourager ɗin ta, ɓangaren guda kuma har yanzu ta kasa gwada kiran layin Farida amman ba ta samu.








****MARADI




Kwana biyu kacal da faruwar wannan al'amari duka ahalin sun shiga ruɗu da tashin hankali,an yi aikin Daddy amman har yanzu bai farka ba haka babu wanda ake bari ya shiga.Ɓangaren Maryam kuwa tuni suka saba ita da Lami ta ɗauke ta kamar ƴar cikinta,gefe guda kuma tuni aka fara azabtar da Maryam ta hanyar sakata share filin comsariat wankin banɗaki da sauran su.
Mahomet ke kai mata abinci bai barin ta ci na ƴan kaso,juyin duniya tayi amman har yanzu bai kawo mata Yusu ba.
Tun zuwanta sai yau kawai su Ammi suka zo,kallon su ta tsaya ta na yi sam ta kasa cewa komi dan ta lura kamar sun yarda da ita ɗin ce aikata haka.
"Maryam ba wai rashin so ko kuma yarda ba ne yasa ki ga mun ƙi zuwa inda kike,a'a sai dai wani dalili na can daban ga Yusu nan dai an kawo maki yau duk da na san ko ke ba za ki so a bar sa nan ba"cewar Ammi ta na miƙa mata yaron wanda ke ta barci.
Karɓar sa tayi ta shafi kumatunsa,wani tausayinsa taji yau kusan kwana biyu bai samu nonon uwa ba balle ɗumin jikinta.
Inna dai na zaune ta kasa ma magana ,Ammi tace "Maryam ba ki ga Inna ba ne?"Inna ta goge ƙwalla tace "ta yaya za ta ganni alhalin ɗaukar maƙiyiyarta ta ke yi min?"da sauri Maryam ta ɗago tace "ko ɗaya Inna sai dai ina mamakin yadda kuka bari aka kawo ni nan ba tare da yunƙuri ko ƙaryata zancen da kuka san ko da ban cikin hankalina ba zan aikata sa ba"tayi maganar cikin kuka.


Ammi tace "dukanmu mun sani sarai sai dai hakan da mu ka yi shine zai bayyanar da gaskiya kin ga yanzu Balkisu a tunaninta Alhaji ya mutu so mu ke ta saki jikinta ta tona ma kanta asiri da kanta"Maryam tace "Ni fah surutun ta yasa na fito da sauri sai faɗin ta kashesa ta ke yi,amman abinda na lura da shi kamar saka ta ne aka yi ba da son ranta ba"shiru dukan su suka yi kafin Inna tace "babu komi Allah shi zai saka maki ko nisanta ki da yaron ki da tayi shi kawai babban haƙi ne balle na kisan kai"duk hirar da suke wani ɗan sanda na nan ya na sauraren su ba tare da sun sani ba.
Har za su tafi Lami ta ƙaraso ta ajiye bokitin da ta gama baiwa flowers ruwa ta gaishe da su Inna suka amsa cikin sakin fuska.
Karɓar yaron tayi ta na girgiza irin wasa jika da kaka ai kuwa ya farka,ta cigaba da yi masa wasa ya na ɓangala dariya ta miƙa ma Maryam shi tace "ki aza shi ga nono bari na je na gyara makwancin mu,ɗazu aka nunan sabon ɗakin mu inda kin gan sa gudan makeke har da ƴan matalu"dariya Inna tayi tace "Ƴata miye amfanin girman ɗaki tunda ba na alkhairi ba ne kuyi fatan dai Allah fidda ku daga wanga baƙin wajen"
Duk suka amsa da "amen" Lami ta wuce yayinda Maryam ta fara shayar da yaron ta.










A asibiti kuwa mai gadi ne ya shigo da wani dattijo wanda duk yayi furfura ga uban gemu da ya tara,bayan sun gaisa da su Abbasi yace "na je can gidan ku na farko aka ce kun tashi nan aka gamo ni da wani ya kawo ni sabon gida sai kuma na tarar babu kowa sai mai gadin ke faɗan Issufu ne babu lafiya"Abbasi ya amsa masa "eh wlh ya na ciki yanzu haka Dr mu ke jira ya bamu izinin shiga yace mu jira sa"dattijon ya jinjina kai.
Can Dr ya leƙo yace "Bismillah"ai kuwa suka runguɗa,a kwance suka tarar da Daddy ya rame sosai yayi haske.
Da sauri ya tako inda Daddy ya ke kwance yace "Issufu?"Daddy yayi murmurshi yace "welcome back Mahmud sai yau Allah yayi nufin ƙarasowar ku?"Mahomet yace "Daddy wane Mahmud ɗin?"
"Baban Balkisu Uba mahaifi" cak suka tsaya su na kallon juna Balkisu da kuma Mama uwanda shigowar su kenan su na addu'ar Allah basu iko su ƙarasa kashe Daddy kafin ya tona masu asiri.
"Mahamud?"Mama ta faɗa shi kuwa ya juya ya na kallon mata ma fi soyuwa a rayuwar sa....
[03/03 à 13:55] Mrs SADAUKI 💫: *43-44*




Hayaniya da koke-koken su ya saka Dr shigowa fitar da su daga ɗakin aka bar Mahomet shi kaɗai,hannun Daddy ya riƙe yace "ya jikin na ka ?ka na jin wani canji kuwa?"Daddy ya lumshe ido ya na jin wani sanyi na ratsa sa sannan ya buɗe su yace "alhamdullah!ina takwara na?"
Mahomet ya sunne kai dan bai son ɗaga ma Daddy hankali "ya na can tare da mahaifiyar shi"ya faɗa dakyat
"To a kawo min shi nayi missing na shi sosai"Daddy ya faɗa ya na mai massaging hannun Mahomet da ke cikin na sa.
Da "toh Daddy"ya amsa kafin ya jefo wata tambaya "amman Daddy miyasa ba ka faɗa ma iyalansa ya na raye ba ka ɓoye masu?"Daddy ya bashi amsa "saboda inda ya ke da shi da matacce sunan su ɗaya,ka bari in na fita daga nan duk zan faɗa maku komi"shiru kawai Mahomet yayi.






Turo ƙofa aka yi tare da shigowa,Inna ce da Ammi.Cike duk da murna su ke tambayar sa jiki ya na amsa masu "to ai yanzu shikenan tunda ka farfaɗo sai ka faɗa ma ƴan sanda ba Maryam na ce ta so kashe ka muguwar matar ka ce dan haka a sako min jika ta"cewar Inna .
Da mamaki Daddy ya tambaya"Maryam ɗin na hannun su?"Ammi ta basa amsa da "eh! Bilkisu tace wai ita Maryam ɗin ta baka guba ka sha shine ƴan sanda suka kamata"
Daddy ya kalli Mahomet da sauri yace "yi haƙuri Daddy dan kar na tayar maka da hankali ne"Daddy yace "ok tashi ka je can police station ɗin ka tawo da ɗan sanda guda nayi mashi bayani"da murna Mahomet ya fita.








A harabar asibitin ya ga Mama sai kuka ta ke yayinda Bilkisu ke taya ta, Mahmud kuwa ya koma gefe ya na kallonsu dan shi ya zata kukan murna su ke.
Tsuki Mahomet ya ja ya na jin wata tsanar duka ahalin kafin ya wuce,babu jimawa suka zo shi da ƴan sanda wanda ganin su ya kaɗa hantar su Mama.






Cikin halin ciwo Daddy yace "ku saki baiwar Allah ba ta san komi ba,ku kama mahaifiyar Balkisu ita ta tsara komi in na ƙara samun lafiya zan yi maku bayanin komi"haka kuwa aka yi Mahomet ya yiwa ƴan sanda jagora har wajen Mama.
Da mugun mamaki Mahmud ke kallon su,a ruɗe ya fara tambaya "lafiya?mi matata tayi maku da za ku kamata?"
Mahomet ya bashi amsa "saboda ta so kashe mutumen da yayi ma rayuwarta da ta ƴarta halaci,duk tsawon shekarun da Daddy ya ɗauka ya na kula da su hakan bai sa tayi farin ciki ba sai ganin bayansa da ta ke son yi ta dalilinta ga shi an saka masa hanji roba .Ku tafi da ita."Mahomet na gama faɗa ya juya.






Mahmud kuwa zaman ƴan bori yayi tsabar tashin hankali ya kafe Balkisu da ido alamun ya na son jin ƙarin bayani dan alamu sun nuna ta san komi.
"Wlh Abba ba laifina ba ne Mama ce ta ban wani magani na saka ma Alhaji a tea tace min da zarar ya sha to sai yadda nayi da shi komi yawan kuɗi kuma zai bani ashe guba ce ta saka"wani gigitacen mari Abbas ya ɗauke ta da shi kafin yace "miƙe maza"tashi tayi jiki na ɓari,kamar wata ƙaramar yarinya haka ya kama hannunta suka fita ya tsayar da adaidaita jin ya ambaci comsariat ya saka Bilkisu ƙara ɗaga murya ta na kuka tare da bashi haƙuri.
Da isar su ya ce ma ƴan sanda a haɗa da ita a kulle, Mahomet wanda ya ke tsaye kusa da Maryam yayi murmurshi dan tun farko ya so a haɗa da ita sai dai gudun ɓacin ran Daddy ne.
Lami har da kukan ta jin Mahomet ya ɗauki nauyin zai biya duk bashin da ake binta,in kuma lokacin fitar ta yayi zai zo su ɗauke ta dan tuni matar da ta ji ma ciwo ta dawo hayyacinta.








Sai da suka tafi gida tayi wanka ta ci abinci kafin ta shirya Yusu, Mahomet ya wuce da su asibiti.
Daddy ya karɓi Yusuf ya na yi masa wasa sosai ya ke son yaron,Atine da Farida uwanda su ke zaune daga gefe baƙin ciki kamar zai kashe su .
Maryam na son yi ma Farida magana irin na tsakanin matar ƙane da magajin nan amman babu dama Farida sai cika ta ke ta na batsewa a doli ta shafa ma kanta lafiya.












Satin Daddy biyu a asibiti aka sallamo shi,tun daga nan rayuwar gidan ta koma wata iri saboda zuwa yanzu

Please Login or Register in order to submit comment