Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakuri wannan shekarar bashi da kudi,to uwar gida next week zasu tafi,daga nan yace su wuce dubai zasu siyo kayan sawa ita da yaranta.
Ai dan baki sani bane idan uwar gida tana da hankali tana da biyayya duk wata Amarya ko balarabiya ce ko dangin uwar mu ce baturiya bata isa ta kwace fada a wajen uwargida ba,ya aure ki kawai sabo da ya samu sabon jini kullum ki bashi taskira uwar gida kuma ita ce da shi.
Ki daina jiji da kai Aunty Amal bakya gabansa kuma yanzu so kike ki haihu baki samu ciki ba sabo da gado kin damu sai kin haihu to ciki ne dake ammaAllah ne yasan abinda zaki haifa,idan baki yarda ba kije ayi miki test, dama ke mayyar sex ce da zaki taho ma sai dai me tunbi yazo kuka yi na ban kwana,yace babu kamarki a ransa, kika taho kina murna karya yake wlh.


Amal gwiwar ta ce tayi sanyi jin abinda Sahil ya fada tasan basa karya,tace amma wlh idan na koma sai anyi tashin hankali,yanzu Alhaji Rabiu haka zai min,Sahil yace katon kwado kina ce masa Baby, Kuma dan yayi miki ke din ba har wajen malami kawarki ta rakaki ba wai zaki mallake shi,Islaha tace kinga Zayna muje ciki wannan yaron munafuki ne,Aljanunsa kaf munafukai ne,Ibrahim yana ta dariya abinsa yasan halin su Sohail shi yasa yayi shuru kar su tona masa asiri.


Sohail ne ya fito yana duba Maheera bata nan ya duba kitchen Islaha ce kadai ciki tana girki yace girki kike? Tace yanzu na fara Aunty Zayna ce tace farfesu zamu yi musu da white rice and stew wai Aunty Amal tazo sannan wai na dafa mata kan rago ka ganshi an kawo yanzu fresh da shi,Sohail yace yau babu wanda zaici abinci a gidan nan sai dai su fita waje suci mu kadai ne zamu ci mu koshi ni,ke,Sahil da Maheera, suna kallo zamuyi party sai dai su bar gidan nan suci abinci a waje,nidai zan dafa musu ko dan aikin Maheera kar ya kubuce,Sohail yace bazai dafu ba abincin yau ko me za a dafa indai a gidan nan ne bazai dafu ba,Islaha bata yarda ba yana fita ta fara girki,ruwan ma yaki tafasa bare a zuba shinkafa wuta ci take ci take a gas amma idan aka taba ruwan sanyi karara,Islaha ta dinga dariya ita kadai a kitchen,komai ta dora bazai yi ba sai dai a taba aji sanyi,har ta kwashe awanni ta gaji ta maida komai fridge ta fito.


Tana fitowa taga Sahil da Sohail sun shugo da ledoji niki niki,Sahil yace kowa yaje yayi wanka yau akwai party, suka shiga wanka,Maheera ta hade cikin wani material dinta na sallah me kyau,Islaha ta sa riga da skert yan kanti sunyi mata kyau kamar ba gobe,Sohail kuwa da Sahil kana nan kaya suka sha masu kyau wando jean fari riga ruwan toka me rubutu blue a gaba,palo suka fito kawai suka samu Ibrahim,Amal,Adnan da Zayna a dining suna jiran abinci daga wajen su Islaha.


Ido suka bude ganin Su Sohail da su Islaha duk sun sha wanka sun fito da abinci a leda sun dora a center table,Sahil ya bude ya fito da su hot pizza,shawarma,burger, kaza ta sha gashi katuwa a bankare gashin amarya,ga kuma wata kalar shinkafa ta larabawa da katon kifi yaji hadi,ga hadin salat a gefe da lemon tsami,ga ruwa ga lemuka da fruits salat abin ba sauki.


Suka baje komai a center table,Amal har tana dariya irin taga mahaukata ta dakawa Islaha tsawa ke yarinyar nan dalla kawo mana abincin mu,Islaha tace yarinya tana bayan uwarta,Adnan a fusace suka yo kan Islaha,Ibrahim yace dan Allah ku kyaleta su Sohail ne suke zuga su,ai su Sohail zaku ci uba da waccen bakar munafukar Maheera sune suke zigata,ai ita yarinya ce me hankali.


Adnan yace ko sonta kake yi ne? In kana sonta kayi magana ta karfi kudi zai siyar maka ita ai,Amal tace ko dan su Sohail ma sai na so ya aureta naga ta tsiya,bari mu kyaleta zasu ga tsiya kudi zaiyi aiki ai talakawa ne iyayenta zasu ji yaren kudi.


Amal ta sake cewa kawo mana abinci,Su dai sunga suna kuskus basu san me suke cewa ba,suma su Sohail aljanun basu fada musu ba,Islaha tace yanzu kika yi magana da kika bini a sannu,to abinci wlh yaki dafuwa na dade ina abu daya ko me na dora ko zafi bayayi bare ya tafasa,Sohail yace kuma nine nace yau mu kadaine zamu ci abinci a gidan nan ba abinda zai dafu.


Zayna tace na yarda wlh ni na gani rannan,Amal ta mike ta shiga kitchen din da kanta ta dora tukunya ta dade a haka ruwan sanyi ta sauke ta fito ta zubawa Sohail rankwashi tace dan iska marar mutunci,kunyi asarar halinku,shuru suka mata tace kuzo muje eatery muci,suka mike,Maheera ta kunna kida ta ware uban volume wai party zasu yi Sohail ya samu aiki.
Sahil yace wata ta zauna cinyata safe waje ne.


Kida na tashi suna ta ciye ciyensu abin dariya ko wacce makale kusa da daya,hauka tana motsawa Sohail yace ayi musayar kawa,Maheera ta koma kusa da Sahil,Islaha ta koma gefen Sohail,Sohail kuma sai kishi,yaga Maheera sai kallon Sahil take tana murmushi me kayatarwa kuma tana sani tayi tunda shi yace ayi musaya.


Sohail idonsa na kanta ya saki baki yana kallonta haushi ya kama shi yace a ransa ai kuwa sai na baki haushi yau,ya ballo kaza yace da Islaha ungo kici,Islaha ta bude baki ta yagi nama tana taunawa ta kwabe fuska kamar zata yi kuka wai duk cikin dadi ne,tace Aunty babar Khalisat ina nan dadi zai kashe ni ta furta da sigar kuka ka rantse kuka take sharba harda yarfe hannu.


Maheera wani bakin kishi ya kulleta a rai,Islaha tana ta mata inkiya da nuni ta fahimta ba da gaske bane amma haushin Sohail ya kashe Maheera tace a ranta ai hauka ma tana iske hali,halinsa ne wlh sai na rama ta dakko Shawarma itama ta fara bawa Sahil a baki yana ci,Sohail ya kame ya zama gunki da lemo a hannunsa,ransa ya baci,Islaha ta mika masa a baki shima yana ta ci amma wuri daya ya tsurawa ido yana bacin rai,duk da yana kokarin dannewa sabo da Sahil ne.
Sahil kuma yana ta nunawa Islaha ta daina taki ji,Har ya gaji ya kura mata ido yana cewa uhm uhm...uhm...uhm wai ta daina ga kida kamar zai fasa gida suna ta dumurmusar abinci suna cusawa juna haushi kowa yana ta ramuwar gayya ba ga mazan ba ga matan sun biye su,ana party amma kowa haushin kowa yake ji anyi musayar mata.






Free page
400 ne


0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank


'Yan Niger
+22790795939








AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸


26-30




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM.




Page naki ne
Umu Afrah




Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw












Sai dare Maheera ta mike tace zanje na kwanta bacci nake ji gobe gidanmu zanje ganin gida har yanzu ban samu naje ba,Sohail yace Allah ya kaimu,Islaha ta mike suka wuce ciki,bayan sun shige bangaren su Sahil ya kalli Sohail yace ya kamata Islaha fa ta koma wajen danginta ko yaya suke bai kamata kawai ta bar can ta yo nan ba,mata fa idan aka biye musu basu da hankali,dole sai ana sara ana duba bakin gatari,bai kamata tazo nan ta zauna ba kaga su Yaya su ba kaunar mu suke ba,Daddy kuma ba damuwa yayi damu ba bare yasan me muke yi,gwara Maheera tana da hujjar zama aiki suka dauke ta,Islaha kuwa sam ma Zayna bata bata wani aikin yi bare su biya ta, su fa ba damuwar su bace koma me zamu yi muyi kawai a duniya,uwar mu Mahaifiya har yau bata neme mu ba ma shima Daddy ko zancenta baya yi mana, indai da hali kawai ta tafi indai dan ni tazo ba ruwana ni dai.


Sohail yace hakane kuma amma yanzu ya za ayi da ita? bari na kira su kawai ayi a gaban kowa,kamar masu hankali yau haka suka yi magana.
Sohail ne ya mike ya musu knocking a kofar su Maheera.

Budewa tayi yace dan Allah ku dan zo zamu yi magana,Fitowa suka yi palo tare da zama.
Sahil yace abinda yasa na kiraku,Islaha akanki ne,duk duniya dan Adam baya rasa dangi ko ya suke,Islaha tace ae,yace yawwa ku mata watarana tunaninku gajere ne, Maheera ke aiki kike yi kina da dalilin zuwa nan,Islaha nayi tunanin za a bata aikin ma hakan bai samu ba sai dai amma tana tayaki na gida tunda ita basu biya ta ko sisi ba.


Magana ta gaskiya ni ba korarki zanyi ba Islaha nasan kina da dangi ko da baki da iyaye Wacce ta rike ki ta kore ki bai kamata ki taho wajena ba,kamata yayi ki koma Taraba wajen danginki,ni bana so ace zamana kike yi ni ba iskancin nan nake ba,gwara ma da yi nake sai a zargeni da hujja,ya kamata ki koma danginki shine darajarki, nima kinga babu me zargina,idan Daddy yazo su Yaya zasu iya hada mana sharri,ki koma danginki ba korarki nayi ba kawai ji nayi ba tsari haka sam,ba wani dan uwa da zaiji kina nan yaji dadi indai suna kaunar ki.


Sohail yace wannan haka yake maganarsa gaskiya ce tare muka yi shawara,nima na ziga shi mun tantance gaskiya.


Islaha murmushi tayi tace ba komai na fahimce ku,karku damu ina da dangi kuma Inshaallah zan tafi,Sahil ya kalleta yace sai naji tausayinki kuma Allah sarki,shuru tayi tace shike nan? suka ce ae tace to baku da damuwa indai nice.
Sahil ya kalli Islaha da tausayawa yace tausayi nidai.
Maheera ce tayi magana tace gaskiya bai kamata ba ina laifin ku bari mu kaita gidansu da kanmu,Islaha tace sai kace yarinya kema dai Maheera karku damu dan Allah.


Su Sohail kamar ba su suka yi maganar ba kawai sun ma ci gaba da uzuri suna duba waya suna dariya,Maheera ta mike suka wuce bedroom,Islaha tana shiga ta fara hada kayanta,Maheera tace ke yanzu maganar Twins zaki biyewa shirmen su ne fa.


Islaha tace abinda suka fada gaskiya ne Maheera,Sahil yana tubanin ni Karuwa ce wanda ba haka bane,nasan ranar da yake zargin ya ganni shine ranar da Aunty ta bani kaya na rashin mutunci tace sai na saka nabi Khalisat hotel ko ta koreni daga gidanta,babu yanda zanyi haka na shirya na bita,kuma ba abinda na aikata maganin bacci na saka masa a lemo ya sha da safe na fito na koma gida,nidai na tabbata a nan Sahil ya ganni, Abinda ya faru kenan ko Sahil ya ganni bazai wuce wannan ranar ba,kuma banga laifinsa ba domin duk wanda ya ganni a lokacin zai yarda ni karuwa ce sabo da shigar da take jikina.

Maheera tace to kuma sai kice zaki tafi haba Islaha,Islaha tace a daren nan kuwa zaki ga na tafi,Jakarta ta dauka Maheera ta riketa tace haba Islaha mene haka da daren nan zaki tafi.


Fisge jikinta Islaha tayi ta fice,Maheera ta biyota amma Islaha ta arce ma da gudu,ba kowa a palo ko compound haka ta fice abinta.
Ranar Maheera ko baccin kirki bata yi ba sabo da tafiyar Islaha.


Washe gari da safe ta fito tayi aikinta tana shirya dining Sahil ya fito,Maheera ta kalle shi tace Islaha ta tafi tun jiya da dare,dammm ya danyi a tsaye,yace ta tafi? tace ae a daren ta tafi,Sahil shuru yayi zama yayi a hankali a saman kujera.
Hankalinsa ya gama tashi gashi aljanun nasu yawanci abin da ba a damu da shi ba shi suke fada musu.


Tagumi ya zuba Maheera tayi tafiyarta tare da ci gaba da aikinta,Sohail ne ya fito zai tafi wajen aiki ya samu Sahil yayi tagumi,tambayarsa yayi yace me ya faru? Maheera fitowa tayi da plate dauke a hannunta ta furta Islaha ta tafi tun jiya da dare,kuma yanzu ba a sani ba gida ta tafi ko ba gidan ta tafi ba,a wanne halin take oho,tunda ba san can garin nasu mene ya hanata zuwa ba.
Sohail yayi shuru shima yace gaskiya ne bamu kyauta ba sai yanzu na ga illar hakan mun gode da tunatarwa Maheera.

Sahil ya mike tare da zama ya zuba tagumi yace sabo da zuciya shine ta tafi cikin dare idan aka sace ta fa,Sohail ya furta har na fara tunanin kudin fansar Islaha da zamu kai gashi ban fara aikin ba ina zamu samu kudin?
Sahil ya furta ai da Maheera kin fada min sanda ta tafi a daren zan bita da bulala me kyau zan rako har ta gida,Sohail ya furta
lallai bamu kyauta ba na wuce Office.


Maheera takaici ya kamata tace wlh badan aikin nan nawa ba sai nayi tafiya ta nima wannan ai ba daidai bane, na gaji da halinku
Sohail ya kusa kofa ya juyo sosai ya kalleta yace Allah ya baki hakuri,juyawa tayi ranta a bace.


Sahil baice komai ba har Sohail ya fita yana tunani,Amal ta fito da shirin komawa gidan mijinta dauke da akwatinta Adnan ya fito zai rakasu airport" tare da Ibrahim zasu tafi suka samu Sahil yayi tagumi ya zurawa waje daya ido baya ko motsi.


Kallonsa suka yi kawai suka tabe baki tare da wucewa abinsu.
Sai da ya gaji a haka sannan ya kwanta a saman kujera ya zubawa sama ido ba ci ba sha,har lokacin sallar azahar yayi bai san yayi ba,shi kadai a gida Maheera har ta shirya ta sanar da Zayna ta fito da kayanta tayi tafiyarta ko kulashi bata yi ba.


Da kyar ya mike ya dauro Alwala tare da gabatar da Sallah ya roki Allah ya bayyana Islaha sai da ya gama adduar ya koma saman kujera ya kwanta, a haka Sohail ya dawo ya iske shi,yayi sallamar duniya shuru shuru,sai da ya shugo yaga inda ya bar Sahil a nan ya same shi kuma ba bacci yake ba,Yana tsotsar Alawa me tsinke


Yace lafiya? gaba daya abinda muka yi bai dace ba,yanzu wa yasan inda take,ko an sace ta ma jiya da da dare wa sani,Sohail yace kasa ina tsoron kudin fansa Sahil


Sahil yace yau ko ruwa ban sha ba bare na iya cin wani abu,wannan abin ya tsaya min ba wai ni wai sonta nake ba ka gane,ni da bakina da nace ta tafi shine ya dameni,Sohail tashi yayi yace kuma gaskiya bamu kyauta ba gashi yanzu Maheera fushi take yi itama.
Kitchen ya shiga ya ebowa Sahil snacks da lemo ya kawo masa yace muci wannan Maheera fushi take yi bata ajiye mana abinci ba yau ina zan sa kaina.


Sahil kadan yaci ya koma ya kwanta ya dora da tunaninsa,gani yayi kwanciya baza ta kaishi ba ya mike tare da cewa bari naje na nemo ta a gari, ya fita kofar gida bakin gate ya tsaya yana kallon hanya a haka neman Islaha ya fita iya bakin gate,sai da aka yi kiran sallar Magrib sannan ya koma gida.


Islaha kuwa a tasha ta kusa kwana da asuba suna yin sallah ta shiga motar Taraba garinsu suka tafi tana motar tana ta tunani wai Sahil ya iya cewa ta tafi,Farcenta tasa a baki tana ci tana tunanin kawai a haka har suka isa Taraba.


Sauka tayi ta shiga motar kauyen su me suna Sharbe inda ba abinda ake kiwo sai dabbobi iri iri,kauyen ma kafin aje aiki ne,Allah yasa Aunty tana aikenta tana kaiwa dangi sakon kudi da kayan abinci,duk iskancin Aunty akwai taimakon dangi,duk yanda dan adam ya kai ga lalacewa baya rasa halin kwarai.
Wani sakarkarin gida Islaha ta sauka wanda duk garin daga ginin kasa sai Gidan kara da bukkoki irin na fulani,babu wani ginin bulon siminti ko guda daya a garin.


Islaha ta saba da birni bata kaunar ma ace ta dawo garin da zama kuma ko waye haka zaiji,ace ka taso a birni ka dawo irin wannan kauyen,gashi yan uwan nasu kawai su dai a basu kudi,wanda ya basu shine mutum,basa iya rike dan wani dangin su Islaha yawanci haka suke.


Gidan wata wacce suke kira da Lalai kanwar kakar su Islaha ce itace ta rage tana da rai a cikin dattijai dangi sauran duk da kwarinsu kuma ta fisu dama dama,duk ciki babu wanda zai iya rike Islaha.


Lalai ita kanta ta zaci Aunty ce ta aiko Islaha ta kawo musu kayan abinci da kudi,tana ganin Islaha hannu bibiyu ta tarbe ta tana murna tace marhabin ja'ira yau ma kinzo,Islaha ta shiga dan karamin dakin Lalai wanda sai gadonta karami sai kayanta irin na tsofaffi,gida kuma gidan kara ne gaba dayansa, Lalai ce kawai a cikinsa.


Bayan sun zauna ta kawowa Islaha tuwon masara da miyar kuka amma fa miyar da nama a ciki,Islaha taci ta koshi tayi wanka tayi sallah sannan ta zauna tana hutawa.


Lalai tana ta jira taji ance ga sako daga Aunty amma shuru,Lalai ta gaza hakuri Islaha tana mata hira tace Auntyn taku ce ta aiko ki? Islaha tace a'a Lalai,ta kore ni daga gidanta tace baza ta iya ba na tafi,ina zanje bani da kowa sai ku dole nan zan dawo ku rike ni.


Kirji Lalai ta dafe tace sabo da Allah a dora min nauyi ina tsohuwa ta,nima fa Abdulrazaqu shine yake ci dani,ba kudi ne dani ba,Allah ya gani fama nake da kaina,ga dangi nan da yawa su Gali,su shamsu duk su Allah ya hore musu suna da shi 'yan uwan uwarki ne na kusa ba na nesa ba ai sai kije can yafi.


Islaha tace kema fa kin san su Baffa Gali Lalai baza su min ba kuma ma ko sun yarda ai matansu basu da mutunci,sannan da dangin uwata dana ubana duk daya suke yan uwane gaba daya auren zumunci kuka hada,ke yanzu Lalai ba me rike ni bace? Kun fi so na shiga duniya,wallahi dole ku rike ni tunda nazo a yar uwarku ya zaku yi dani ba inda zanje.


Lalai tace inda rayuwa ta canja sabo da Allah gishiri ma yanzu ya zama masifa ni azo a zauna min nima fa yar Allah bani muci ce,Islaha tace nima itace ke dama ai bakya son mutane bakya so wani ya rabeki bare ya amfana dake.
Zan shiga duniya ne ya zanyi,Lalai tana ji tace to gaskiya bazan lamunci gandandan dake ba ki zauna irin yanda kuke yi a birni,da miji ya fito ki fitar kiyi aure a kaiki dakin mijinki ko da katifa ne,ga samari nan da yawa a dangi duk kaunar ki suke yi idan sunzo ki zabi daya,ba hauka ake ba da zaki zauna a gabana kin fini girma nono duk sun cika miki kirji bazan iya ba,kullum ina bude ido ina ganinki a haka bazan iya ba,wannan maguzancin bada ni ba baza kizo ki jawo min hawan jini ba.


Islaha tace naji zanyi kokari na fitar dan Allah ki kyaleni na huta da kudi na kawo miki ko kayan abinci ai da yanzu kin rasa inda zaki sa kanki dani sabo da murna.
Lalai ta furta nidai na fada miki ki fidda miji.


Islaha zata hau gadon Lalai ta kwanta kamar yanda ta saba idan Aunty ta aiko ta Lalai tace karki hau min gado ko ni ba kwana nake a kai ba sosai, kiyi shimfida ga tabarmar kaba can,Islaha bata ce komai ba ta dauki tabarmar ta shimfida tana cewa indai aka ce iyayenka sun rasu a wannan zamani ka shiga uku babu me iya rikeka sai daidai ku,haka ta sa rigar bacci ta kwanta.


Sahil sai dare ya tuna da waya ana kiran mutum a ciki,cikin dare ya dinga kiran Islaha ko dagawa bata yi ba,da ta gaji ma kashe wayar tayi gaba daya,Sahil kwana yayi yana gwada kira sai bacci barawo da asuba ya dauke shi.
Gaba daya gidan baya musu dadi sam Sahil ya rasa sukuni hakan sai ya damu Sohail shima ga Maheera tana jin haushin su duk Sohail ya damu kansa,tunda ta tafi ganin gida bata kira shi ba.


Wayar Sohail ce tayi kara ya duba,yana dubawa yaga Email ne aka turo sako,dubawa yayi sai ya ga an dauke shi aiki a kamfani personal assistant na matemakin manager aka bashi,ga Alert na kudi,sannan gobe yaje ya karbi motarsa da takardun gidansa
Sahil yana daki yanda yanzu yake zama baya so ma a kulashi,Sohail ne ya nuna masa,murna ya tayashi sosai,Ya fito ya turawa Maheera text ya sanar mata,tayi murmushi tace mashaallah.


Message ta turo masa congratulations! sai ka dage nan gaba ka zama manager din da kansa.
Karantawa yayi ya tura mata yaushe zaki dawo?
Reply ta masa da Jibi Inshaallah,ya furta Allah ya kaimu da baki kawai ya maida wayarsa Aljihu shi a dole ya bata amsa yace Allah ya kaimu,shuru taga ba reply nasa ta zubawa wayar Ido tana jira,shi kuwa ya riga ya fada da baki.


Maman su Maheera wacce take katuwa da ita me kiba kyakyawa ta kalli Maheera tayi murmushi tace Maheera wannan Sohail din da kike min zancensa ko da shi za ayi ne? Murmushi tayi,Mama tace wlh naji dadi da kika canja hali Maheera amma da kullum baki da aiki sai tsokana sai fada,Maheera tace hmm yanzu ai wannan aikin da nake samu ina yi kinga Mama dole nayi ladabin dole kar a samu matsala a kore ni,daga haka ban san sanda na canja hali ba gaba daya,yanzu ko kudi kika bani bazan yi abinda nayi da ba,nayi hankali, a baya ma ai da kuruciya.


Juwairiyya tace lallai Aunty Maheera Allah dai yasa kin daina kar kije ki samu miji kice zaki yi masa wannan mulkin kama karyar kice dole ke sai an miki yanda kike so,sai kin samu yanda kike so nasan hali,Ammar yace wlh kamar kin sani nima abinda nake so nace kenan,dariya suka yi Maheera ta mike ta bar dan karamin palon nasu dake gidan nasu gaba daya 2 bedrooms ne sai palo sai kitchen da toilet,daya bedroom din na Ammar daya Juwairiyya, Mama da Maheera,gidan daidai talaka.


Adnan ne ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya fito yana tafiya da kyar kasancewar baya cin abinci sosai sabo da tafiyar Islaha,yana kallo Amal ta tafi gidan mijinta ko magana,Zayna ko me zasu yi kanzil baya cewa.
Adnan yace ka wanke min motar? har ya gama maganar Sahil bai jin ma me yace ya tafi tunani,Hello....Adnan ya furta sannan a hankali ya dago kansa ya kalle shi,yace munce mun daina aiki muma aikin yi muke nema ku dauki ma'aikatan ku ya juya baya abinsa yana cewa ina cikin tunanina kawai ka dameni.


Adnan cike da masifa yace kaje ka wanke min mota tun wuri na fada maka,ko kulashi Sahil baiyi ba ya koma ya kwanta abinsa.


Ran Adnan ya baci sosai yau Daddy ya kira a waya ya daga bayan sun gaisa Adnan yace Daddy karar Twins na kawo maka yanzu kwata kwata sun raina mu baka isa kace suyi ba,babu abinda suke yi sai rashin mutunci,aikensu idan kayi zasu ce baza suyi ba direct,Daddy murmushi yayi yace to baka ganin ba kalau suke ba,Aljanun ne suka canja su,ai Daddy ba komai Aljanu zasu sasu suyi ba naga dai Aljanun sai lokaci lokaci suke zuwa kansu watarana ma sai ka rantse kalau suke,ko yanzu yanda suka

Please Login or Register in order to submit comment