Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganewa,Murmushi Sahil yayi tare da fisge hannunsa,Zayna dafe goshinta tayi tare da furta oups I'm sorry,Sohail yace sai kace kin rike wani bare he is my blood tare zamu aure ki fa mu biyu,Sahil yace InshaAllah ki kwantar da hankalinki matar 'yan biyu ce ke,Zayna ta zaro ido tasan kansu da motsi shi yasa dariya suka yi sannan suka shiga cikin gidan,Sahil ya koma mota ya zauna yana danna waya abinsa,yana jiran Sohail,Sohail lekowa yayi yace kazo ka kama min,bazan iya zancen ba sai kace ni kadai zan aure ta ai har da kai a ciki,driver yana jinsu yana ta dariya,yace au dama wai zance kuka zo nan? Kuma mace daya zaku aura ku biyu? Sahil yace ta ishe mu rayuwar duniya ya bude mota ya fice ya bar driver yana ta dariya.


Sohail suka shiga palo Zayna suna hirar school din su,Sahil yace I love you Zayna, Zayna ta zaro ido tace kaga saurayina fa,Sohail ya bata rai yace shima yana sonki ai tare muke son ki idan bakya sonsa nima bakya so na to shike nan na daina kulaki,Zayna tace sai kace akuya ce ni ta ya zan so maza biyu ni bazan iya ba,to shike nan nima na daina sonki wlh,Sahil a fusace ya mike kamar zai mare ta ya daki table sai da ta tsorata,yace da Sohail muje,Sohail ya mike yace kinwa kanki ki rasa mu karki sake kula mu.


Zayna tace to sai me aikin banza mahaukata da ku ma,nan a makaranta kake dalalar da yawu,dama dan kana da kyau nake kulaka amma me zanci da mahaukata,Sahil ne ya dawo ya rike Zayna ya kwashe ta da mari,ya fara dukanta sai da ya mata lilis tana ihu yan gidan su suka fito da gudu,Sohail ya jawo Sahil.


Maman zayna tace amma ku dai kunyi asara ai zaku aikata mahaukatan banza,kowa ya fito yana tambaya lafiya sai ace ai mahaukatan nan ne sai ace ohhh Allah sarki ai mahaukata ne a kyale su,su Sahil ko a jikin su dan ance musu mahaukata suka yi tafiyar su.


Sai dare suka koma gida , Mama suka iske Fada ta fara tace dan iskanci sai yanzu zaku dawo,Sahil yace wai Mama a koma bamu nono mana kawai a huta ace muna maza zamu fara university ba inda zamu je muyi dare sai kace mata,Sohail yana jinsu ya saka Earpiece dinsa zai toshe kunne,Mama ta rike kunnen sa tare da murdewa dariya ya hau yi dake yafi Sahil fara'a shi,bana so ne a samu matsala ku lalace,karatu zaku fara fa, kafadar Mama Sahil ya dafa kamar wata sa'arsa yace ba abinda zai faru, Mama tace Allah yasa,Abinci fa? Mun koshi mun ci burger dazu,tace to Good night ayi adduar bacci kar a manta.
Sam su Sohail basu taba tambayar ina maman su ba,ko wacece ba ruwan su ko zancen basu taba yi ba.


Bayan wasu watanni Sohail da Sihil aka kai su private University dake Germany suna can suna karatunsu amma dai sai dai result me kyau basu san komai na karatun ba har yanzu
Har suka shiga level 2 sannan suka zo hutu gida.


Suna zuwa hutu suka samu anyiwa Amal aure ta auri wani hamshakin me kudi dattijo ne gidanta daban,Adnan ma yayi aure an masa aure,ko fada musu ba ayi ba sabo da ana ganin basu da muhimmanci,basu da amfani a duniya haka mahaifinsu da sauran yan uwa ke gani,basu ma ce me yasa ba a fada musu ba sai murna ma da suka yi Adnan yayi aure da Amal,Mama Asmau itace komai dinsu a gidan sabo da ita ne ba a iya taka su.


Hajiya Asmau yau shiri suka yi ita da kishiyarta Nadia zasu je Kaduna bikin 'yan uwan Nadia a danginta dake ita yar kaduna ce,Asmau Kara zata yi mata,su biyu driver ya tuka a mota suka tafi cikin ikon Allah a hanya motar su tayi hatsari bayan tayi dugu dugu motar nan take ta kama da wuta,da kyar aka samu ma aka kashe wutar,babu wanda ya tsira a motar gaba daya sun mutu da Nadia da Asmau har driver,Alhaji Ali sai mummunan labari yaji,nan take ya fadi a sume aka kaishi asibiti.


Su Adnan kuka kamar ba gobe,su 'yan biyu ma basu san me ake yi ba suna daki suna game tunda Mama ta tafi basu fito ba,mutuwar ma sabo da iskanci ba wanda ya kula su Sohail bare a fada musu kawai ba mutane bane,Alhaji ya farfado da shi aka hada matan nasa wanda duk sun kone kurmus,sai sassan jikin su kadan,hayaniya da kuka ne yayi yawa Sohail ya mike sanye daga shi sai gajeren wando ya fito yana lekowa yaga mutane dankam mata sun cika ko ina na gidan.


Dawowa yayi ya saka jallabiya yace kai Sahil gida fa ana ta kuka an cika gida ko menene oho,Sahil yana ji yace kar fa abar nan ce tazo gidan nan yau,ai kuwa ina jin ma itace tazo din cewar Sohail,yace tabbas ta karaso bari muji wa tazo ta dauke,Allah yasa Umma Nadia ce,Sahil yace 3qtr ma zan saka dan iskan zaman makoki zanyi naji a jikina Umma Nadia ce,3qtr ya sha me tsada da tshirts dinsa wata grey,shi kuwa Sohail jallabiya ce fara a jikinsa,a jikin Mirror suka tsaya suna taje sumar su ,Sahil ya shafa man lebensu na maza me kyau,Sohail ya hau fesa turare sai da suka gama suka bude kofa tare da fitowa wai zaman Makokin Nadia zasu yi.

Mata aka zuba musu ido yuuuuuuuu kamar za a cinye su sabo tsananin kyawunsu,suna zuwa Main palo suka ga yan uwan Mama Asmau da yawa suna ta kuka,wani palon kuma yan uwan Nadia ne,Amal tana ta rusa uban ihu a cikin su,Sohail yace cikin rada da alama Umma Nadia ce,Sahil yace akwai rawar bungalo yau da galala,suka dawo ta parlon da yan uwan Mama suke domin sun fi sanin su,Sohail ne yaji ana cewa Allah sarki sune yaran Asmau wanda ta raina,Allah sarki sunyi rashi,Allah kaji kan Asmau, mutuniyar arziki,Sohail yaci wani wawan birki yace wa naji kuna cewa? Sai lokacin ya tuna ai tare suka tafi unguwa da Nadis, Yanda yayi maganar cikin tsawa da karaji sai da suka firgita,Sahil yaje ya rike wata tsohuwa cikin dangin Asmau yace wacece ta mutu? Dattijuwar tana hawaye tace Nadia ce da Asmau duka matan mahaifinku sunyi hadarin mota Allah ya musu rasuwa gasu can ana sallatar su.


Sohail yace wai Maman mu har da ita ta rasu? Suka ce ae,sumarsa ya hargitsa ba tare da ya sani bama,ya fara kokarin cire rigarsa da ya fesa mata turare yana hawaye nan take idonsa yayi jajir, Sahil kuka yake wiwi sosai yake kuka,ana ta basu hakuri,Dattijuwar tace sai hakuri,Sahil cikin karaji yace baza muyi hakurin ba,wallahi bazan hakura ba sai munyi kukan.


Da kyar da lallashi suka tashi suka nufi wajen makokin,Alwala suka yi suka bi sawu aka sallaci gawar Mama da Umma da su,ana sallar suna ta sharbar kuka sam basu iya sallar ba sai kace mata.


Sohail anzo daukar gawar babu kara sohail da Sahil suka ce a tsaya dan Allah suyiwa maman su addua amma baza mu yiwa Umma Nadia ba wlh suna hawaye ana jinsu suna cewa baza mu yiwa Umma Nadia ba,kowa yayiwa iya uwarsa,haka aka jira,suka tsuguna a saitin kanta sun dade suna hawaye suna yiwa Mama addua sannan suna gamawa su biyu kacal suka daga makarar Mama kowa yayi mamaki duk nauyin mamaci da makara,haka mutane suka kama amma basa jin nauyin sam su Sohail sun dauke nauyin amma kamar basu dauki komai ba,suna tafiya suna hawaye sai uban sauri kuma suke yi mutane sai da gudu gudu sauri sauri ake binsu,Nadia kuwa tana can karshen baya ana kiri kiri da ita,ana kaita bakin kabarin Sohail yayi sauri ya shige kabarin ya kwanta wai sai ya ji inda Mama zata kwanta,aka fito da shi da kyar yana cewa ni a barni na dana yana kuka abin tausayi, Sahil shima ya shige ya kwanta,da kyar shima aka fito da shi yana faman tirje tirje yana cewa sai na Dandana nima, ana musu fada,aka zo za a sa Asmau a makwancinta suka hana,suka rike aka yi aka yi suka hana har aka binne Nadia sun hana a saka Asmau,Sai da Alhaji Ali ya musu magana ya kira su sannan aka samu aka fara sata,Sahil da sauri yaje ya saka rigarsa da ya cire ya dukunkune ta ya saka a saitin kan Asmau yace ayi mata pillow taji dadin kwanciya,kwace rigar aka yi sannan aka samu aka kammala komai.
Sohail kuka sosai ya durkushe a kasa kuka yake ba ji ba gani,an gama komai amma Sohail yace mu baza mu tafi ba a nan zamu kwana sai munyi gadin Mama.


Daga ranar babu wanda ya kara ganin su Sohail suna dakinsu suna ta kuka da jimami suna tuna maman su Asmau da irin rayuwarsu da suka yi,girki da kansu suke wa kansu dama sun iya sosai suna taya Mama duk ta koya musu,bayan akwai masu aiki a gidan amma Adnan ya hana a basu su yan biyun abinci,za dai a zuba komai a store su dafa da kansu.


Bayan anyi kwana arba'in Mama komai nata anyi rabon gadonsa 'yan biyu ko handkerchief ba wanda ya basu,itama Nadia anyi nata yaranta duk an fiddawa kowa hakkinsa duk da ba wani abu suka tara ba,Alhaji Ali ko kadan baya saurarar su Sohail haka kowa na gidan,gasu sun zama manyan samari sosai.
Hutunsu yana karewa suka samu Daddy a part dinsa,tare da Adnan da Ibrahim suka iske su suna ta rubuce rubuce suka shiga da sallama,Adnan da Ibrahim suka wani daure fuska,Alhaji Ali yace ya akayi twins? Sahil yace hutun mu ya kare muna so mu koma school Daddy.


Adnan da Ibrahim suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya,Ibrahim ya kalle su shekeke yace wai school sai kace suna ganewa,Adnan yace babu me biya muku har Germany ku dinga yiwa mutane asarar kudi,me kuka sani,Alhaji Ali ne yayi magana yace ya isa,kai Sahil naga ma kafi dan hankali company na dake Abuja na damkawa Adnan da Ibrahim zasu dinga kula da shi suna aiki,kun san a cikin companies dina wannan na Abuja yafi ko wanne sabo da haka duk wani Business su zasu dinga juyawa,sabo da ina matukar kaunar Adnan,duk gidan nan ba wanda nake so sama da Adnan sai Ibrahim,Su Sohail harda murna Daddy yana son Adnan da Ibrahim su yaya ana kaunar ku cewar Sohail,Sahil yace mu kuwa bamu da kowa,Sohail yace kai muna da Allah mu ya ishe mu harda tafa hannaye,Sahil yace fam fam magana ta kare mune muke da Allah ya daga yatsa sama sannan yasa yatsan a baki yana tsotsa.


Adnan ya karbe zancen yace kai karku dame mu da shirme, da ku zamu tafi can kuna taimaka mana da aikin gida,gaku ai bai kamata mu dauki yan aiki ba,sai ku dinga wanke mana mota,shara da goge da girki komai dai kuma zamu dinga biyanku kudin kashewa haka sannan sutura baza ta gagare ku ba kowa zai sa wacce yake so,wajen kwana ma me kyau za a baku part komai,batun wata makaranta ba ganewa kuke yi ba ku hakura ku fara shiri jibi zamu tafi, Ibrahim yace wannan shine daidai Daddy shawarar da yaya Adnan ya bayar basa ganewa mene amfanin asarar kudi.


Sohail da Sahil basu ce komai ba kuma ko alama ransu bai baci ba hasalima ma da sauri suka ce to zamu shirya,Ibrahim yana harararsu yace kuje dan Allah aiki muke,suka juya suka bar wajen.
Suna komawa bedroom kuma suka fara shirin hada kayansu ko a jikinsu murna ma suke yi su.


Wacece Zayna


Zayna 'ya ce ga Alhaji Shehu asalinsu babur ne,babanta Alhaji Shehu yana da kanne mata da maza kasancewar shine babba sannan yan uwansa gaba daya suna kasuwanci ya zaunar da shi a Kano,shima daga zuwa cirani Allah ya azurta shi tun yana matashi har ya hadu da matarsa daya tilo yar fulani Hajiya Furera ita ya aura, Allah ya basu yara hudu,Imran shine babba,Saif sai Zayna ta uku da autar su Arfat suna kiranta da Baby.
Iyayensu mutanen kirki ne ga hakuri ga kyauta ga sanin yakamata,su Zayna sun taso cikin kulawa da tarbiyya kamar ba yaran me kudi ba haka suke,sun san me suke yi,nutsatsu da su sai dai suna da son me kudi.


Zayna kyakyawa ce ba laifi dai, ita ba fara ce ba tana da haske dai dai mashaallah, 'yar lukuta ce Zayna, bayan su Sohail sun daina kulata Allah ya hadata da yayansu Adnan taje shopping suka hadu,ta san shi yayan su Sohail ne amma ganin da kudinsa daga nan suka fara soyayya har ta aure shi wanda har yau su Sohail basu san Adnan Zayna ya aura ba.
Abuja din ma da zasu koma bada Zayna zasu tafi ba ita tana katafaren gidan mijinta sai dai ya dinga zuwa weekend ko watarana ta dinga zuwa can haka suka tsara,su Sahil sunce zasu je ganin amarya amma yace kar su je masa gida,haka Amal ma ta nuna bata kauna suje gidanta shi yasa suka hakura kawai.


Bayan kwana biyu Adnan da Ibrahim su a jirgi suka tafi amma su Sahil sai suka ce driver ya kawo su Abuja a mota,haka aka kaisu a mota .


Free page


1&2
500 ne.


0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank


Niger
+22790795939






AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: https://www.arewabooks.com/chapter?id=6683ec1256566fe605af16a3


🪸MUMMUNAR DABI'A🪸


6-10


Official


By
AsmaBaffa




Sadaukarwa ne ga 'Yata Tasnim




Pagae naki ne
Ummu Khinal




GARGADI GA MASU AUDIO BAN YARDA A SACI LITTAFINA A JUYA ZUWA AUDIO BA.




*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*








Su Sohail suna karasawa har asokoro wani mahaukacin gidane na alfarma gida ne na musamman wanda komai nasa ba karamin dukiya aka narkar ba wajen gina gidan ba,komai akwai na more rayuwa,Adnan suka gani yana hutawa zaune a wasu kujeru na hutawa masu kyau ya dora kafa daya kan daya yana latsa waya sannan yana kora ruwan lemo me inganci da kara lafiya a jikin dan Adam, kallon su yayi wani haushi ya kama Adnan sun fisu kyau da cikar zati da komai ma,baki ya tabe tare da mikewa,akwatunan su suka dakko tare da kallonsa "how far bro" suka furta.


A hasale yace kunga respect your self ni ba sa'anku bane kar ku sake kirana da wani bro,who is your brother? Dalla ku wuce muje ya ja wani tsaki tare da wucewa ciki suka bi bayansa suna murmushi ko a jikinsu,hirarsu ma suka fara yi,a fusace ya sake juyowa yace kai kun cika min kunne,shuru suka yi kawai suka haura sama ya nuna musu dakinsu hadadden gaske me dauke da makeken bed da toilet komai a kwai ciki,suna ajiye Jakar su bai bari sun huta ba yace ku fito na nuna muku gidan sannan na zana muku aikin ku,suka biyo shi kamar 'yan aiki.


Sai da ya nuna musu ko ina na gidan sannan suka koma palo,Sohail yace wash na gaji,Ibrahim ne ya shigo yana magana yace ai ba hutu ne ya kawo ku ba,kai bari kuji aikinku a gidan nan
Gyara gidan nan ku share ko ina ku goge,sannan kuyi mana wanki da guga, kuyi girki,ku wanke mana motoci kullum,bude gate da kullewa,komai da kuka sani na gyara gida da kula da shi kune zaku yi shi kunji,su Sahil suka ce sun ji,su kansu ganin basu san komai ba sun hakura da rayuwar, tunda ana kiransu da mahaukata gani suke basu da amfani a duniya,gani suke ba abinda zasu iya tabukawa a duniya,shi yasa suka hakura kawai tunda sunga kowa baya daukan su a mutane,kuma suma abinda suke yi da abinda suke ganin suna yi sai yasa suke ganin lallai ba daidai suke da kowa ba,suka riki aikinsu hannu bibiyu,sun zama 'yan aiki ta karfi, sun fara musu bauta ba ji ba gani har sun kai matakin samari na gaske ya isa ace sun kammala degree din su amma sun kare a bautar yan uwan su, sun kwashe shekaru biyu suna bauta musu.


Su Sohail sun girma sosai dan sunfi ma su adnan girman jiki da tsayi,kai in ba fada maka aka yi ba baka isa ka gane wane Sahil wane Sohail ba sai wanda ya mugun saninsu zai iya tantancewa shima ba ko yaushe ba,kansu daya,tsayinsu daya cif,kibarsu da jikinsu komai irinsu daya kai daya babu banbanci,sun ajiye saje da gemu madaidaici,gasu jajir da su,ga tsayi gasu su ba ramammu ba sannan baza ace suna da kiba ba,idanuwansu masu kyau farare tas,gasu da yalwar gashin gira da sumar kansu me kyau da baki sai sheki suke yi kawai,kana ganinsu kasan ba wahala a tare da su,sai dai suna bautuwa sosai, ko waye ya kalle su bazai so ya dauke idonsa a kansu ba,gasu da kwarjini da cikar zati,gasu da tsafta ta gaske ga daukan wanka tunda ana basu sutura da cima me kyau,komai iri daya suke yinsa,kawai banbancinsu Sahil yana da wushirya yar kadan shi kuwa Sohail baida ita banda wannan basu da banbancin da za a gane waye Sahil waye Sohail,halayyar su ma tazo kusan daya,Sohail yafi fara'a,Sahil baida wata fara'a sai dai in suna tare da Sohail kawai zaka ga yana dariya, 'yan mata kuwa basa tunanin ma sun kai mutanen da har zasu iya son mace bare su aure ta wannan yasa ma su ba ruwansu da mata basa harkar su.


Ci gaban labari


Ibrahim ne ya shiga kwalawa Sahil kira "Sahil" "Sahil" kamar zai fasa gidan,Sahil ya fito da gudu a gigice,dake su ba wahala sun gigice sun rude,sanye yake cikin gajeren wando da riga armless maroon,Ibrahim yana wani gadara ya sha wata azababbiyar shadda fara yana shining yace baka da hankali,jakin ina ne kai kalli takalmin da koge min,brown nace ka goge? Na fada maka meeting zanje black nace ka goge min amma ka goge min brown useless,karbi ka goge wannan,kuma idan 15mnt tayi baka goge ba wlh sai ka gane kurenka stupid,Jikin Sahil yana rawa ya karba yace kana nufin a goge wannan? a'a goshin uwarka zaka goge min,Sahil yace uwata ai bata nan ina zan ganta na goge maka goshinta? Dan Allah ka taimake ni ina zanga Mummy na goge maka goshinta? Kuma kasan Mama ta rasu,dama Mama tana raye wlh sai naje Kano na goge maka goshin nata,cike da mamaki Ibrahim ya tsaya sololo yana kallon Sahil,yau ya tabbatar Sahil basu da hankali,tsaki yaja yace "Sahil" yace na'am ka goge min takalmi zan fita, a goge dai ko kace? Sahil ya sake tambaya,Ibrahim ya hasala sosai ya sake dakawa Sahil tsawa ya juya ya tafi gogewa.


Adnan kuwa cikin shirinsa ya fito zai fita ya samu motarsa da yace zai hau da alama ba a wanke ta ba,Sohail ya dinga kwalawa kira,Sohail ya fito, yana zuwa Adnan ya fara bala'i kai dan uwarka wacce motar nace ka wanke? yace bakar na wanke,haka nace? ae cewa kayi na wanke maka fara kawai ni kuma na wanke bakar tafi kyau, Adnan ya zaro ido yace are you mad? Ni in saka abu ka canja min zabi,ba komai ai zaka aikata ai kafi kowa hauka da ciwon aka haife ka dalla bani key ya fisge key dinsa ya wuce ya shiga motarsa ya tafi,Sohail ya juya ya wuce kitchen ya duba ba abubuwa da yawa wanda yana bukata yayi amfani da su wajen girkin da zasu yi, yana shirin fita ya siyo kawai Ibrahim ya dawo ya kulle kitchen din yace tunda baku da hankali sai kunyi kwana bakwai baku ci abinci a gidan nan ba,sai dai ku siya da kudinku useless ya juya ya tafi,Sahil ya kalli Sohail suka yi shuru basu ce kala ba.


Yau haka suka yini basu ci komai ba a gidan gashi su Ibrahim a waje zasu ci hadadde abinsu,su kuwa basu ma da kudin ko sisi sabo da kawai komai sai dai su gani an siya musu har sutura ba a basu kudin su siya an maida su kamar yara,idan ma sunce a basu kudi baya wuce 1k, Sahil dazu kace zaka je shopping ina kudin? Sohail yace ai kasan kayan abincin dama idan munje su suke transfer da kansu sai dai kawai mu karbo a shagon,Sahil yace na tuna kuma gashi har yamma tayi likis wlh yunwa nake ji, fita zamu yi ko zamu samu wani abu,Sahil yace nifa na gaji da wannan rayuwar bro gidan nan zan bari na gudu kawai,Idan ka tafi ina zaka je? Wa kake da shi? Sohail ya tambaya,Kazo mu gudu kawai,Sohail yace ba inda zanje ni,ina zani bamu da hankali ance waye zai zauna damu a haka,Sahil yace to zan tafi na barka ni domin gwara naje na bautawa wasu wlh,Sohail yace a dawo lafiya ma dinga waya.


Tafiya suke yi kawai a titi har sai da suka bar layinsu suka bar unguwar ma baki daya,sai da suka shiga wata unguwar suka samu wani shago karami da shi kamar container ce ma har sun wuce Sohail yace muje kaga wata a ciki kamar zamu samu wani abu,dawowa suka yi da baya wata budurwa ce kyakyawa ajin karshe ta saka face mask tana zaune a ciki,tana danna waya,ganinta da suffar musulmi suka furta salamu alaykum cewar Sohail,Sahil kuwa ya hade rai yana gefe a tsaye.


Amsawa tayi sannan tace me za a baka? Sohail bai kulata ba, wani botikin gyada fari me murfi dake gabanta ya fara yin kida da hannu biyu yana kida da bokitin,ta tsaya tana kallon ikon Allah!


Dariya yayi ya tsaya yace to ya aka yi? Ya ake ciki? mene da ke na ci?


tace ga gyada,akwai biscuits,bread,cake etc gasu nan dai,Sohail ya kalleta suka hada ido"
dariya tayi yanda yake leke leke a wajen yana kalle kalle yana sosa gashinsa,"
yace bamu da kudi ne magana ta Allah bamu ci komai ba,ki taimaka ki bamu bashi in na samu zan kawo miki.
budurwar ta kare musu kallo tace guys kamar ku ace baku ci komai ba?
ke

Please Login or Register in order to submit comment