Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansa ya ja tsaki ya shiga mota yace karki sa na aureki ta karfi gwara ma ki yarda ta salama.
Juyawa tayi ta tafi abinta,yaja mota ya wuce,tana shiga gidan Abdulrazaqu harda kifawa Islaha mari shegiya yar iska ina ji kika ce bakya sonsa wallahi sai kin aure shi,Islaha kumatunta suka tasa suka yi jajir, tana dagowa ta shammace shi ba zato ta yarfawa Abdulrazaqu mari itama tace ka isa ka mareni ba abinda na maka bazan aure shi ba, Abdulrazaqu dafe kumatu yayi yace ni kika iya mari? Ya jawo bulala Lalai ce ta rike shi tace kyaleta a hankali ake bi zata so shi ne sai a hankali.


Islaha tace ka dakeni ka gani wlh yanzu sai na kunna wayata na kira Sahil duk sai ya tashi garin nan Aljanune da shi da kun sani wlh,Lalai tace ta tabbata tana tafa hannaye Ibrahima baiyi karya ba ashe kuwa Mahaukacin ne kike so,Islaha daki ta shiga ta barsu nan suna ta surutunsu, kwanciya tayi ta fashe da kuka tace ai koma mene kaine ka jawo Sahil mutumin banza dan iska,ta dinga zagin Sahil,tunawa tayi aljanu suna fada musu abu kar su fada masa,tace dan kirki ne Sahil ga hankali,yana da mutunci,yaro na gari da shi.


Lalai da dare ta koma gidan Malamin ya sake buga kasa yace na fada bata ci ba,ta fiku wayo naman boyewa tayi ta jefar daga baya,Lalai tace to yanzu ya kenan? Wani garin magani ya bata yace bari mu bullo mata ta nan idan tana bacci ki barbada mata maganin a jikinta,sai tana bacci amma,Lalai ta karbo ta dawo tana zuwa ta duba daki babu Islaha babu dalilinta,ta duba ko ina na gidan bata nan,makwafta ta shiga da gidajen yan uwa duk bata nan,kuma babu jakar kayanta,Lalai wajen masu machine na haya taje ta tambaya ko sun ganta,wani a ciki yace yanzu na dawo nine na kaita tasha can ta cikin birni inda ake shiga motar Lagos.


Lalai tace gidan Auntyn zata koma da sauki ai zamu kira a waya muji idan tana can sai mu tura Ibrahim can sannan har maganin ma zai kai gareta sai ta soshi.
Islaha kuwa tana zuwa mota ta cika ta shige zuwa lagos sabo da a garin tafi sanin mutane da yawa zata samu wajen zama ko aikin yi.


Ibrahim haushin Islaha taki sonshi gani yake kamar Maheera ce take zigata a tunaninsa suna waya dole a boye,sai ya kara tsanar Maheera ya uzura mata,ita kanta Maheera din sonta yake ita ya fara so amma jarabar Sohail tafi karfinsa,yaga Sohail ya zurfafa bashi da mutunci kuma akan Maheera zai iya batawa da kowa,Kawai sai ya dakko wata mace dattijuwa Igbo me suna Madam Oge ya kawota a sabuwar me aikinsu,Maheera ya samu a bedroom ya shiga kai tsaye yace mun sallame ki a aiki ki tattara ki koma gidan ubanki munafuka,mun dakko kwararriya,sannan Zayna ma da kike gani gobe zata koma kano wlh kika ki tafiya sai na lalataki,gwara ma ki tafi tun muna sheda juna.


Maheera ta kalle shi tace an fada maka dan ku nake zaune? Akwai dalilin zamana kuma yanzu ma ni nafi karfin nayi muku aiki Sohail yayi kudi tun yaushe ma yace na daina nice nace zan yi amma badan shi ba zan zauna, kuma dama dan shi nake yi sabo da ina kai masa Office kula nake da abina kai kuwa sai walagigi kuma bazan so ka ba Islaha ma tafi karfinka,har abada baza ka samu kamar mu ba kalle ni kalli Islaha ta juya a gabansa tace kaga komai yaji to sai Sohail da Sahil,a hakan su muke so ba ku ba.
Ibrahim yace har kudi ne da Sohail din? Nawa ya tara? Har yaushe ya fara aikin? Sabo da an bashi yar mota da bata fi ta aiken cefane ba,sai gida irin na gwauraye,kudin kuma nawa ne? Kudin cefanen wani ne a rana daya,Maheera tace ae a hakan dai kake son yan matansu kuma kwalele sai ma kaga anyi biki.
Ibrahim yayi murmushin takaici yace aje a haifo dolaye masu suffar yan ruwa, maza tun daga ranar da zaki samu cikinsa laulayinki shine Zana Zero kin dinga zana zero kenan har ki haihu.


Inshaallah matarka ce zata zana kuma sai naga dama zan tafi yanzu ma sai na kai masa abinci,Tsaki yaja ya juya yace ana korar ku kuna likewa ban taba ganin talakawa irinku ba.
Maheera ta dade bata kai binci Office ba sai yau ta shirya girki iri iri ta shirya abinta taci kwalliya cikin abayar da Sohail ya siya mata wata pink Egyptian tayi kyau tana kamshi ta fito dauke da abincin a katuwar wledoji har biyu,Adnan ta wuce a compound yana hutawa ya harde yana danna waya yana kallo ta fice,ya bita da kallo shi kanshi Maheera tana tafiya da imaninsa,ko baka so sai ka kalleta komai nata dagwas daidai da ita.


Juyowa tayi ta kama Adnan yana kallonta da sauri ya dauke kansa,Maheera ta juya tayi tafiyarta,tana zuwa building din tun kafin ta fito a taxi ta kira Sohail a waya ya fito,fitowa yayi sanye da gajeren wando da tshirts maroon,hannayensa a aljihu ya fito yana murmushi.
Yace Sweet yau ma baza ki shigo ba? Sunan ya mata dadi tace me kace? baya ya juya yace nima na manta,tace to juyo mana,ya juyo yace kunyarki nake ji yau,yau ma baza ki shigo ba? Kai ta daga masa tana murmushi,kallonsa tayi tace ina kayan da ka fito da su ai ba wannan bane,yace aiki ne yayi yawa na cire dama wannan suna mota ai,fuskarsa ya kawo jikinta yana shinshinawa yace ya naji turare? me taxi ya gama shanyewa bazan ji ba sai da aka gama jinsa a duniya zaki wani zo nan,Dariya Maheera tayi tace kai malam Sohail,harararta yayi yace kinga ta inda muke fada dake ki dinga fada min malam sai kace wani tsoho ya furta da shagwaba,dariya ta sake yi tace to na daina.


Yau banyi aiki ba babu abinda na iya na manta aikin Office din,haka aka kyaleni zaman kashe wando nake yi,ai Alhaji Saminu ya sani baida damuwa,bazai damu ba,Ya damu mana ina ruwana ni cewar Sohail,Maheera tace wai Sohail idan anyi aure me akeyi ne da kace zaka aureni? dariya yayi yace nima ban sani ba ai kece zaki fada min shi yasa zan aureki tunda kin fini sani,Maheera tace ato nidai nasan baka san komai ba yanzu haka zamu yi auren? tunda ke kin sani ai ba damuwa ya furta yana gyara mata mayafinta,yace tafi gida to kawo abincin an gode miki,idan ka tashi daga aiki kazo ka kaini gida yau zan koma gidanmu,Sohail yace kin hakura da aikin? tace ae na hakura gwara muyi auren kawai,amma Sahil fa shi auren? Sohail yace zaiyi mana shima kika sani ma ko yazo ya fini samun kudin,Karki damu ko ma mene ai komai nawa nasa ne Accnt dinmu duka kowa yana iya amfani da na kowa duk abinda yaga dama zai iya yi nima haka,nafi so muyi auren tare da shi amma shi yace ta Islaha yake yi yanzu inda zai ganta yake tunani.


Maheera tace kai ka tabbata so na kake a matsayin matar aure? Sahil yace a'a kinki nake yi, Karki dameni,to kace you love me bazan fada ba na gaji kullum sai nace I love you ni na gaji i hate you zance,Dariya tayi tace anya Sohail ba lafiya kake samu ba? Watarana fa magana kake fada min ko?
Sohail yace kanki ake ji dai, wannan kayan fa?ya tambaya.
tace Kai ne ka siya min ko ka manta?


Sohail yace shi sam ba shi ya siya ba,sai idan wani ne ya siya miki kike min karya,Maheera baki ta bude tace kai fa ka siya min wallahi amma kace ba kai bane,to yaushe na siya? kawai ki dinga fakewa sabo da ina da dan kudi komai na gani a jikinki sai kice nine na siya miki,Maheera ta zaro ido tace to a tambayi Sahil ai yana wajen ka bani,ai ba a karya a gabanmu to ki sani Sahil yana Office dina yanzu haka tare muka zo da shi, Maheera tace a kira shi din.


Wayarsa ya dauka ya kira Sahil ya fito,ya kalli Maheera yace ai ban gane ki ba ashe kece kinyi kyau da yawa ne,Sohail yace kaima ka fada wai nine na siya mata kayan nan wai kana wajen ma,Sahil ya karewa kayan kallo yace a'a Maheera kawai dai ki fada masa gaskiya idan kece ma kika siya ai normal ne na mene zaki kala masa sharri kice shine ya siya miki kaya,Maheera ta tsaya kamar gunki baki bude tace Allah ya kyauta ta ajiye abincin ta juya zata tafi Sohail ya fisgo hannunta a ina kika samu rigar? Amana ta zaki ci? ka siya min abu kazo kana masifa kai ba kai bane me zan maka,ko kaga ina kula wani,sannan bani da iko kaga abu a wajena sai kace lallai wani ne ya bani ai,sabo da kaga mu bamu da kudi shine zaka dinga min haka.


Sahil yayi dariya yace yawwa Maheera karki kyale shi wlh rainaki zaiyi ,to kai kana kallo me zaka ce ta harare ka fa,sai ka kyaleta? Sohail baya son fushin Maheera yace to naji ni na siya shike nan a bar zancen jira na maida ke gida,Maheera ta juya tana tafiya zata yi tafiyarta wani me mota yayi slow a kusa da ita ya sauke glass kasa yana binta a hankali yana mata magana,Sohail kamar walkiya sai ganinsa suka yi yazo wajen ya rike hannun Maheera suka ci gaba da tafiya a haka yana mata magana yace Sweet I love you,kallonsa tayi tasan jarabar kishinsa ne ya kawo shi,Me mota yana ta magana anki kulashi tafiya yayi kawai,yana tafiya Sohail yace dan iska kawai, ya tare mata taxi harda biyan kudin motar ya saka ta a mota,tana shiga ya leka ciki yace naji riga ni na siya ko ba ni bane nine shike nan magana ta wuce,murmushi tayi abinta tace bye.


Office ya wuce suka ci abinci harda wasu ma ma'aikatan,Sahil yace ka kira Daddy kace a tura a nemo auren Maheera kawai ka huta da wannan kaunar idan ka ajiyeta a gida ai ka huta,Sohail ne ya dauki wayarsa ya manta rabon da ya kira Daddy a duniya shima Daddy haka,yana kira Daddy ya daga yace wai Sohail yau ba jiran gaisuwa yace ya akayi sohail?


Sohail yace Daddy kiranka nayi ayi min aure kawai,Daddy yayi dariya ya furta to kana da budurwar ne? Sohail yace ae ina da abata kuma ta yarda su suka ce ma na tura sabo da haka aje ko kuma na kai masallaci al'ummar Annabi su daura wallahi idan baka yarda ba sai nace ni maraya ne bani da uba kawai a daura min,Daddy yayi mamaki yace to ku wanne aiki zaku iya bare ta kai ga aure Sohail waye zai yarda ya baku yarsa sannan ita budurwar amma marar galibu ce ko?


Sohail yace lallai wato mu ba mutane bane? Daddy yace ba haka bane ai gaskiya ce sabo da lalurarku,to a hakan na samu kuma ko ka yarda ko baka yarda za a daura aure,Daddy yace gaskiya ban yarda bada yawu na ba, bada sa hannuna ba a zalunci yar mutane.


Sohail yace ni da amincewa ta da yawu na harda hawayena na kara ciki, ba yawu ba harda gumin jikina da yake tsatsafowa wlh sai dai kaji an daura ni dama bance kasa yawunka ba,idan zaka zubar ka zuba a shara a aurena kar a samun yawu ya kashe wayarsa.
Daddy yace Allah ya sawwake to a haka a bawa mutum aure da ya za a rike mace a haka nima ana min magana gatsal.

Sohail kuwa yana kashe waya ya sanar da Sahil abinda Daddy yace,Sohail yace gobe weekend ai mun san Jigawa din har garin su kawu Nafiu muje mu fada musu a bamu ko mutum biyu ne nima na sha babbar riga da hula muje a nemo maka auren inda hali a daura ma daga baya a kai amarya ko ya kace? Sohail yace ai dama kaine waliyi na karka sake wani ya karbar min aure dangi marasa mutunci ba wanda yake ta tamu duk rabu da su ana zuwa naka nine wakilin ango suje su karata da furfurar su.


Washe gari kuwa Flight Sahil ya biya suka ware jigawa,daga can suka shiga mota taxi har garin danginsu,gidan Kawu Nafiu suka dira,Kawu Nafiu yana zaure ya gansu katsam,yace yau yan biyu ne a gidana?


Sohail ko zama basu yi ba yace badan Allah muka zo ba,ba zuwa gaisheka muka yi ba,dama ai kaima baku damu da mu ba cewa kuke bamu da lafiya,Sahil yace dole ce tasa muka zo.
Kawu Nafiu inda sabo sun saba jin shirmen twins,yace to ku shigo muje ciki,Sohail yace a'a barmu a nan dakin matarka kamar mashekarin Jaki, wata baban bola da ita,tana yi mana wani gani gani ita su Adnan take so baza mu je ba.


Kawu Nafiu yasan matarsa kazama ce ta gaske kuwa dakinta sai me dauriya,yace to ku zauna,zama suka yi a gefen tabarma,yace meke tafe daku? Aure Sahil ya furta kafin ya rufe baki sun bada amsa,kana da budurwar ne? Ae duk muna da ita amma tawa tayi zuciya yanzu an rasa inda take ko jiya Allah sai da nayi kuka ko Sohail bai sani ba,Kawu ina jin jiki soyayya nake tana ta bani wahala kalleni duk na tsiyace na bushe na kekashe,dan Allah kawu kuyi min addua kafin zuciyata ta buga,Sunanta Islaha,kawu Ko kai ka ganta sai ka so ta sai munyi takara da kai,amma kana gani zan kasa ka na aure ta.


Kawu dariya ya dinga yi yace Allah Sahil? Sahil an sosa masa inda yake masa kaikayi yace yarinya ce kai Kawu gangariya, great girl,ta Sohail kuwa kasan Dawisu? Kawu yace ae yace to Dawisu ce,sabo da haka ayi gaggawar aurar da Sohail tasa tana hannu yanzu.
Sohail ya fara karin bayani yace yar mutunci ce kawu ko kai sai ta baka tarbiyya,kawu zaiyi magana Sohail yace dakata kawu karka ga kana da furfura kaima fa kuskure kanayi tunda ko kai baka damu da mu ba,kana nuna mana banbanci sannan matanka biyu zaluntar daya kake yi,Abu sabo da tana da hakuri shine kake zaluntarta amma Zulai marar mutunci amma kafi tsoronta badan Allah bama yi mata abu kake yi,kaga Maheera ta baza tayi haka ba.


Kawu yasan hali Allah yasa ba a gaban matan suka fada ba,Sabo da haka tana so na ina sonta iyayenta sunce a tura dangi kuma da uba ake ado dole aga dangin ubana shi yasa ma nazo amma badan haka ba wlh baza muzo ba,to me zamu zo muyi maka,Kawu yace to mahaifinku ya yarda? Ko bai yarda ba sai kunje cewar Sahil,da kudinmu muna da aikin yi yanzu da gida da mota zamu iya,ko gidanka sai mun rike ku ba tare da mun girgiza ba,kullum kuma sai anci nama ba ma garau garau ba,amma karka sa rai bafa rike ku zamuyi ba sisi baza ku samu ba kuje Adnan su baku.


Kawu yace to ni yanzu naje mahiufinku bai yarda ba,Sohail yace kayi masa magana ai yana jin maganarka wlh kawu idan baka je sai an kwana ana zuba ma bulala yau kaji na fada maka sati za ayi kullum da dare sai an zaneka gwara ma kaje kawai ka lallaba shi kuma kuna zuwa ni bana son wannan kudin kaza kudin kaza kawai ayi balance na komai a fada min.


Kawu yace wai da gaske kudin kuka yi ne? Sahil yace zancen kake so Kawu ka tambayi dangin Maheera idan kaje sai da suka lalace da kudinmu,tun a waje suke ci,Sohail yace Kanwar Maheera yarinyar nan Juwairiyya har ta fara gurun wuya sabo da yanzu komai suna da shi ba tunanin an dora da rana ana tunanin na dare,Kawu dariya yayi yace kun kyauta,Sahil yace zamu baka kudin mota kai da Kawu Tukur kaje ka samu Daddy kwandala ba mu ce a taimaka mana ba,kawai aje a nema mana,kuma nine wakilin ango.


Kawu yace to madalla za aje gobe Inshaallah nasan yana gida,idan ma baku je ba jikinku zai fada muku cewar Sohail,ya zaro damin kudin a aljihu ya balle wrapper guda yace gashi,sabo da Allah dai sauran ka kashe kuma kayi adalci a gidanka kar ka sake da kudinmu ka siyawa Zulai tsire ka kyale Abu da tuwo,Kawu hannu na rawa ya karba yace na gode za aje inshaallah za a daura ma.


Mikewa suka yi suka ce ka kira su Abu mu gaisa a nan mu baza mu shiga ba,Ya mike yaga kudi harda sauri ya shiga ya kira su Abu suka fito tare da Zulai,Zulai tace au wai dama kune shine baza ku shiga ba?
Sahil yace wa zai shiga kuna ta kazanta a gida sai kace bola,ko ruwanku baza mu sha ba kuji gaskiya, babu ga amarya ba ga uwar gida ba me tashin wani kuna zaluntar Kawu wlh ku gyara halinku Ina yininku Sahil ya furta ko yawu bai hadiya ba kamar uban su.


Zulai tasan hali suka rufawa kansu asiri suka yi shuru suka amsa gaisuwa,Sahil ya basu 5k ko wacce yace gashi nan a samu a dinga gyara daki,suka amsa suna godiya,Sohail hannu a cikin aljihu yace in mun dawo kawo muku amarya Allah yasa muzo baku canja ba sai dai kuga wannan jeren samirar na dakin ku suna ruftowa kasa sai anyi daga daga da su,Zulai ta zaro ido dan tun suna yara ta taba dukan Sohail kwana tayi bata yi bacci ba ana tsikara mata allurai a jiki.


Mu zamu je wajen Kawu Tukur,suka musu sallama suka tafi.
Kawu yana tsakar gidansa yana cin abinci a saman tabarma suka shiga kai tsaye gidan,gidane shima kamar na Kawu Nafiu shima na bulon siminti komai a sumulmule, zama suka yi a gefensa shi gidansa da tsafta me tsafta ne.


Suka ce Kawu ina yini yace lafiya lau yan biyu kune? Ae mune cewar Sohail,meke tafe...aure mun yiwa Kawu Nafiu bayani kawai zakuyi maganar da shi,sannan kaima ga kudin mota suka bashi shima,yaga kudi ya rude,yace zanje naji me ake ciki yanzu Inshaallah,Sahil yace ba maganar kin aiwatarwa idan ba haka ba zai fada maka wlh an tanadi bulalai kawai kuje,suka zauna shima suka kora masa warning,ko ba da sanin Daddy ba kuje kawai da uwar kudinmu,Kawu yace InshaAllah za ayi ma ai haka ake so.
Ina matar taka? Yace wanka take yanzu zata fito,Sahil yace to bari mu jira ta, gashi 5k zamu bata baza mu baka ba sai ka rage mata ko ka hanata.
Matar ce ta fito tace Sohail wai kune? Sohail yace mune ke kam kin huta bakya kazanta gashi ya mika mata ta karba tace an gode to bamu gaisa ba,mun gaji tunda muka zo muke gaishe gaishe kai tashi mu tafi cewar Sohail suka barta babu gaisuwa suka yi tafiyarsu,sai lallonsu ake yi a garin ana cewa turawa ne suka zo.
Me taxi yana jiransu suka shiga suka koma airport suka bi jirgi abinsu.


Suna komawa ya kira Maheera ya fada mata yace ta fada za azo gobe wajen manyanta,Maheera tayi mamaki sai murna take yi bata taba zaton da gaske zai iya hakan ba,sabo da abin nasu sai sunyi gaba suyi baya basu da tabbas sam.


Su kawu Nafiu yau suna kano gidan dan uwansu Alhaji Ali,tunda suka zo suke faman ganar da shi akan ya amince yaki yarda,da kyar dai yace na yarda amma wlh bazan yi bincike ba duk abinda ya biyo baya ba ruwana kar iyayen yarinya su kawo min kara tunda sun san yaran basu da kan gado,Kawu Nafiu yace ka daina haka duk fa kaika haife su,kuma aure Rahma ne ka sani ko shine silar warkewar su,Daddy yace ba ruwana koma wace suje nidai ba abinda ya dameni Allah sanya Alkhairi abinda kuka yi ku fada min,badai daurin aure bane zanje inshaallah sauran kuma ba ruwana.


Kawu Nafiu yayi hamdala yace a ransa mun tsallake bulalai,dama su kansu tsoron bulalar da suka ji yasa suka jajir ce din,kuma ba wata bulala da za a musu wayo su Sahil suka musu tunda sunga ana jin tsoron su,Kawu Nafiu Sohail ya kira a waya ya fada masa yanda suka yi da Daddy,Sohail yace ko daurin auren ma ba sai yazo ba amma da na su Adnan ne ai da tuni shi zai raba IV, idan cikin shegenmu yayi ya fada mana ai ba sai ya zauna yana haka ba,mene dan ya fadi gaskiya mun san sharrin shedan ne.


To mudai gobe zamuje dangin matar a turo mana addreshi,Maheera wajen walliyyan nata ma suna Suleja nan zasu zo an tura musu Address.


Washe gari kuwa da rana suka isa,gidan Waliyin Maheera me kyau katon gida me gate babu batun wahala a gidan,su Kawu Nafiu palo aka kaisu me kyau aka cika musu gabansu da kayan ci sha komai cikin girma aka yi musu Sahil a nan yazo ya same su harda shan babbar riga da hula kamar wani ango ka rantse yaune bikin ya sha farar shadda,komai cif cif shi,Kawu suka boye dariyarsu yanda suka ga Sahil ya nutsu abu kalau kamar wani cikakke.


Kawu da waliyan Maheera suma su uku suka zauna wanda waliyan Maheera sun san komai akan su Sohail mahaifiyar Maheera bata boye musu ba,sabo da a magana ta aure ba wasa da boye boye, amma tunda yarinya tana so kuma ba wani aibu bane da su dangi sun bincika kuma dai yanzu in kana da kudi an gama kawai,su ma dai sun yiwa su kawu cikakken bayanin asalinsu da komai basu boye ba.


Su Kawu Nafiu sunyi naam mutanen kirki ne,nan dai suka gama maganganunsu aka yanke kudin aure da komai komai nan take Sahil ya biya ta accnt,sadaki kadai dubu dari biyu ga sauran kudade shima daban duk na wani bidia ya biya.
Rana kuma ance wata uku amma Sahil yace mu mun shirya amarya ma ba abinda za a kawota da shi sai kayan sawa kawai sati biyu,Kawu yace Lefen fa? Sahil yace to ai matar Ogan Sohail an bata kudin komai kila ma ta hada,Kawu Nafiu yayi mamaki a ransa yace lallai yaran nan da gaske suke yi ashe suna da tunani haka ganewa ne ba ayi,har sun san su hada lefe a boye.
Kawu Tukur ma mamaki ya gama kama shi.


Sahil sai da aka gama komai lafiya zasu tafi yace ina da magana,suka ce bismillah, angon Sohail ko an kai amaryar munce ko dakinta bazai shiga ba sai an daura nawa tukun yanzu abotar su zasu ci gaba da yi a gidan kawai, jirana zasu yi.
Waliyan Allah yasa sun san zancen Su Kawu Nafiu kunya ta kamasu suka ce kai muje da Allah,Sahil yace ai gaskiya ce kar a ganta bata da ciki a zarge ta ace juya ce, bazai yi komai ba sai nima nayi,Waliyan Maheera suka yi dariya dai suka raka su suka shiga motar su,
Sahil ya kaisu tasha suka shiga mota ya sake biyan kudin mota ya musu godiya,yace kun tsallake rijiya da baya amma da kun sha bulalai,dariya suka yi sosai ya juya ya shiga mota ya ja ya tafi.


Direct gidan su Adnan ya wuce sun kulle gidan Sohail ance na Amarya ne baza a kara shiga ba,Komai har kujeru an rufe su da ledoji,Aisha matar Alhaji Saminu taje ta sake ganin gidan duk abinda babu na mace da ake bukata ta saka Sohail ya zuba ta sake canja musu tsarin gidan gaba daya,komai da ita ake shawara,itama tana kokari tana dorasu

Please Login or Register in order to submit comment