Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ja yace duk abinda zaka yi kayi,Ibrahim zai sake magana Sahil ya nufi inda yake,ai da gudu ya zaga tare da fadawa motarsa ya ja ya bar wajen a guje,yasan karfin aljanu ne da su yanzu sai su illata mutum a banza.


Islaha ya kalla ta kalle shi tsoro taji sosai yanda ya bata rai kamar zaiyi gunduwa gunduwa da ita haka ya koma ya nufi inda take idonsa sai zallar bacin rai a ciki,Juyawa tayi da gudu tana tibi tibi wai gudu take yi abinda taku daya zai kamata,Juyowa tayi taga ya biyota, wayyooo tace tana gudu,dariya ma ta bashi yanda take gudun.
Tsayawa yayi ta tsaya nesa da shi tana hakki tace karya nake ba kulashi nake ba,to dawo yace, Wayarta ta dakko ta kira Maheera,Maheera mamaki tayi tana kwance a palo taga kiran Islaha,dagawa tayi tare da furta Islaha kece? Ina kofar gida ki bude min dan Allah Sahil zai duke ni,Maheera ta bude kofar taga Islaha can nesa Sahil a nesa shima,Islaha ta shige ciki da gudu,Sahil yayi tafiyarsa inda zaije,farin ciki yake.


Yace yau duk garin nan ba wanda ya isa ya kaini nishadi,harda canja taku,yau kowa sai ya shiga uku da mutunci na.
Sohail kuwa ya tsaya siyowa Maheera kayan ciye ciye bai dawo gida da wuri ba sai da Sahil yaje ya karbo tsarabarsa ta lagos sannan Sohail shima yayi parking da motarsa ya fito sai ga Sahil a taxi da kaya a buhu har biyu manya,yace wai sai da ka siyo wani abu amma a mota ka dora mene haka? Sahil yace ina ruwanka na Maheera ne ba itace me girki ba,Me taxi din ya bawa kudi yace shigar min da shi ciki please,Sohail yace tab ya barsu a nan haka kawai ya shiga ya kallar min mata,Me taxi yayi murmushi,Sahil yace jeka to na bar maka kudin,yayi godiya ya tafi,da kansu suka dauki kayan suka shigar da su da kyar, su biyu amma daukan kaya ya zama aiki sai wahala suke sha a haka suka shigar da shi da kyar.


Maheera da Islaha sun shige bedroom sai labari suke bawa juna bayan rabuwa,Islaha tace ashe dai Allah ya buda gashi har kin auri Sohail saura muga ciki,Maheera murmushi tayi tace bayan ke ake jira ba abinda aka yi,Islaha ta bude baki Maheera tace wlh bama ko romance wai sai kin dawo Sahil ya aure ki,Islaha ta dinga dariya tace kinga ta kanki Maheera Allah ya kara hakuri,yanzu ni tunanina idan aka aureni nima aka ki yin komai fa muka dora a haka,Maheera tace a hankali zasu gane karki damu,kawai dai ki dinga hakuri da su tunda kin san halinsu.


Sohail ne ya kwalawa maheera kira me shago tashi tayi ta fito, murmushi suka sakarwa juna tace yau kuma me shago nake? ta tambaya tare da rungume shi gashin kansa ya sosa tare da mika mata ledar,tace me yasa kake sosa gashi ne? Kwarkwata ce dani maybe,Sahil ya kawo miki tsaraba yace kiyi ta girki,dariya tayi tace ya dai kawo maka kaine me gida ai naku ne ba na Maheera ba,Kitchen suka shiga ya nuna mata buhu biyu ko budewa ba ayi ba,ta furta ashe abin na yi ne ,daurin da aka yiwa buhun ta kwance da wuka taga doya tace dama tamu bata fi daya ba gaskiya yayi kokari tab ga tsada,ta duba dayan taga dankalin turawa d,a ciki kuma ga ledar bacco biyu,ta fito da su daya taga garin kwakwi yellow dariya suka yi har Sohail yace ke wannan daraja ce da shi yanzu ajiye mana abinmu idan yunwar yamma ko ta rana ta taso ai ko da marmari shanye abinmu zamu yi, Maheera tace har Eba zan na yi ma,aka fito da Egusi da yawa,ga kwakwar manja ga kwakwar ruwa,ga kuma Guava,ga manja,Maheera tayi dariya tace ni wannan Lagos indai haka ne a dinga zuwa wlh,Islaha tana zaune a bedroom Sahil ya shigo tsoro taji ganin ya danna key a kofa.
Islaha sai zare ido take,ina kika tafi? Ya tambaya yana daga tsaye tace wai ranar da na tafi bayan an gama party? Wanne party? Waye yayi party? Islaha tace party fa wanda Sohail ya samu aiki har kuka ce ayi musanyan budurwa ka tuna? Wanne mahaukaci ne ke musayar budurwa kin taba ji anyi? Party yaushe muka hada wani party kuma? Islaha tace to ranar kuka ce na tafi da kanka kace na tafi wallahi zata yi kuka,ae wannan nasan ni nace sai nace ki tafi da dare? Zuciya nayi Allah ya gani ni yanzu ma ba dan kai nazo ba Wajen Maheera nazo,uhm naga alama ai cewa kika yi baza ki iya zama ba a wajen Hajiya kulu dole sai kinzo kin ganni mu fa ba a mana karya,Kasan Hajiya Kulu ne? Harararta yayi yace ban sani ba,kauyenku kika tafi ai,gidan Lalai,duk abinda suka yi da Lalai sai da ya bata labari ,tun da ba a fada masa ba sai yanzu da ta riga ta dawo,Islaha tace naci wahala a hannun Lalai har kanta hannuna yayi sabo da daka,Sahil yace tab Lalai sai ta kwana a tsaye tana daga yau,Islaha tace Kyaleta na yafe mata,ni ban yafe ba ya furta.


Yar uwata ce fa dattijuwa nace na yafe mata,ni ban yafe ba babu ruwana da wata Lalai, Kofar Islaha ta mike zata bude ya rike hannunta yace Lagos din me ya kaiki siyar da abinci? Tunda ka sani mene na tambaya kai fa ka koreni,ni ba wajenka nazo ba yanzu,wajen Maheera nazo jibi kuma zan tafiya ta naci gaba da tuwo tuwo na a bakin tasha kowa ya ganni, kuma shigar banza nake yi,dariya Sahil yayi yace to dan kinyi shigar banza ai ba sabon abu bane da dan bente ma na taba ganinki ,naji to ka bude kofar,Sohail ma da yake kwana da mace ba abinda ya mata har yanzu bare ni,kullum baccin asara suke yi,Islaha tayi dariya tace dan Allah ka kyale su suyi sunnar su mene sai an jira mu? Sahil yace me? ai ko ni Allah ya tsare ni da kallon Taskirar mace bare Sohail,dariya Islaha tayi tace to shike nan ai, muje ni yunwa nake ji,kofar ya bude suka fito,Maheera tana kitchen tana girki Sohail yana zaune ya ja kujera ya zauna bazai tayata aikin ba ko daya,Islaha ce ta shigo tace me zan gani haka kai da zaka mike ka tayata,Sohail yace so kike na zama mijin tace Allah ya kiyaye tuwo fa take yi kawai sai na fara tuka tuwo,Maheera tana tuka tuwon shinkafart tana jinsu.


Sahil yace maza sai dai su tuka nasu a Taskira,Sohail kunnensa ya toshe da sauri,Maheera tace Sahil babu kunyar sirika,Sahil yace gamu muma Daddy fa har England yaje ya tuka ya dawo,Sohail ya tashi yace karka koya mana iskanci,Ai Daddy shi ba Bismillah bare a'uzu shi yasa muka zo a haka,sai da Sahil ya bari Islaha ta dawo yace ni ai da nine nayi aure baka yi ba wlh bazan jiraka ba,ba dan iska bane ni da zauna ina jiranka,Maheera ta kalli Sahil haka kace Sahil? haka nace me yasa kuka jira ni,Islaha tayi dariya tace ai kunga sai ku dauki darasi.


Sohail yace an fada ma jiranka nake dama nima fakewa nake baza a ganni ba kaya ba,Maheera tace Allah ya kyauta kawai ta kasa gane ina suka dosa suyi gaba su dawo baya.


Yau Lalai da yamma ta kawo surfen masara ta zuba a turmi ta fara surfe abinta tunda ta fara bata tsaya ba daka kawai take ba hutu ko digo har dare yayi masarar tayi dugu dugu a turmi,ga uban zufa ta hada amma wani kaimi take karawa a dakan duf duf duf duf daka ba tsayawa, Abdulrazaqu ya shigo tun daga kofar gida yake jin daka na tashi ga dare yayi,maganar duniya Lalai ta kasa cewa kala kawai sai daka take, Abdulrazaqu ya riketa amma taki dainawa sai zazzaginsa da tayi tace wlh ka sake rikeni sai na tsine maka ka fita ka bar gidan nan zan tsine maka, Abdulrazaqu ya fice da sauri yana tambaya me yake faruwa ne da Lalai,Lalai taci gaba da Daka abinta makwafta na ji an rasa daga ina ake jin luguden daka,gashi kauye basa daka da dare sannan karamin gari ne kusan kowa sai yaji.


Abdulrazaqu gidan yan uwa da makwafta ya shiga tare da kiransu su kawo dauki Aljanu sun shigi Lalai,mutane suka taru a gidan Lalai amma kowa ya kasa kwace tabarya,duk wanda yaje jikinta sai ta zubar da shi a kasa yaji rauni,malam Ishu suka kira shi kuma ba malamin kirki bane kawai tsubbu ya iya,shima ya shigo da babbar riga da rawaninsa yaje da Niyyar dakatar da Lalai,hannu tasa ta bugar da shi nan take ta bazar da shi a kasa ya fadi baki duk ya fashe sai jini,mutane suna ganin haka suka ce yo Malami ma bai sha ba bare mu suka firgita suka fara tserewa aka rasa wanda zai dakatar da Lalai.


Allah sarki Abdulrazaqu shine ya zauna a gefe yana kallon Lalai tana ta faman daka kafin safiya Masara ta koma gari tilis hade da dusar, hannunta duk ya ruruce,tana daka ana tuna mata dakan da ta saka Islaha a kanta,kawai maganganu ake mata a kunne akan wahalar da ta bawa Islaha,sai da gari ya waye anyi kiran sallah sannan Lalai ta zube a wajen sumammiya, Abdulrazaqu yayi kanta da gudu yana bata agaji.


Sahil ya takurawa Islaha kamar jela ta shiga kitchen ya bita,Maheera kawo na tayaki cewar Islaha,Sahil yace a'a ki barta tayi abinta itace matar aure itace nauyi ya hau kanta,idan ma bata yi ba mijinta ne zai sha wahala,Islaha tace harda mu fa za aci,wa yace tace tuwo zata yi ai kinibibi ne sabo da taga kinzo shine ta tsiro da tuwo,Sohail ka tayata mana duk bautar da ka yiwa su Adnan sai matarka zaka kasa tayawa kuma kullum tare kuke bacci,gashi nan hannunka da jikinka duk sun kara laushi sabo da yanda Maheera take takura maka da rungume rungume,Maheera tace yaushe rabon da naji kana hira haka tunda Islaha ta tafi sai yau Sahil.


Sohail yana jinsu yace kanku ake ji,Islaha tukunyar miya ta bude tace me ya rage? yanzu fa zanyi ki nika min Egusi,Sahil hannun Islaha ya bige yace da nasan haka za ayi bazan kawo tsarabar nan ba ko hutawa bata yi ba,kina ganin yarinya ta taho zubar da mutuncinta ki takura mata,Islaha dariya tayi ta rufe baki,Sohail tashi yayi yace duk kuje baza a zauna ana wulakanta min mata ba.
Mikewa yayi ya taya Maheera girkin suka gama su Islaha suna palo taki magana sosai wai yanga take nan ramawa take a haka wulakanci take yiwa Sahil a ganinta,bayan kulashi take yi.


Sahil ne ya sata a gaba yana kallonta ya zuba tagumi yana kallonta kamar ya samu tv,Sohail ne ya fito ya tsaya a gaban Islaha,Sahil ya ture shi gefe ba tare da yayi magana ba yaci gaba da kallonsa,Islaha har gajiya tayi da kallon jarabar da yake mata,Sohail yace kai wannan kallon ya wuce na musulunci sabo da kaga araharta kawai a tura a kai kudi danginta a huta wannan wanne irin abu ne sai ka sa budurcinta ya lalace ai.


Dariya suke mugun bawa Islaha,Maheera tana gamawa ta wuce tace bari nayi wanka Sohail yace muje kiyi wankan ki bani na saka miki brazia burina kenan ni kullum na dinga sakawa mata ita,Maheera tace au ba ni kadai ba mata ma? yace to yanzu ina zanje na sawa wata idan ba ke ba,jeki ina kallo ai yanda kike sawa nayi degree,ka daina jin kunyar tawa? Jin kunyar marar kunya asara ne muje kawai amma ni zan fara wanka tace naji jeka,Toilet ya shiga sai data bari yana wanka ta bude toilet din,da sauri ya tsuguna yana zuba mata ruwan masifa kamar zai cinye ta,masifar da yayi bata taba ganin Sohail yayi fada ba sai yau,ba shiri ta fito ta zauna a gefen bed ta zuba tagumi tace wai mijinka guda wannan wacce masifa ce.


Sai da ya gama ya fito idonsa har ya canja yayi ja sabo da masifarsa ta kalle shi ba kaya,Maheera ta kalle shi ya dalla mata harara sai huci yake shi kadai,tace Sohail ni fa matarka ce, baka san me akeyi ba idan anyi aure? A haka zamu rayu kenan? tsaki ya ja tare da nuna ta da yatsa yace dan kawai kece amma duk ranar da kika min haka ko da wasa wlh sai kin gane duniyar nan juyawa take,Maheera ta zaro ido tace duk akan na kalleka kana wanka? An kalleka to wlh zan cire wannan towel din naga yanda zaka yi,Sohail yace da kuwa kin kwana a bayan Uwarki yau,Uwata fa kace ke kika jawo koma mene ai, ya sake jan tsaki ya juya yana shiryawa,Maheera ta dade a tsaye sannan ta bawa zuciyarta hakuri da ta tuna yanda suke,Wanka ta shiga ta fito yana ta shafa turare ya sanya 3qtr da riga armless yana ta fushi fuska ba rahma.


Maheera tana satar kallonsa tsokanarsa tayi tace Sweet goyani,wani mugun kallon ya mata,dariya tayi tace to na hakura shafa min mai yau daya dai,bai kula ta ba uzurinsa yake,bayansa ta tako ta tsaya tace haba Sweet ka manta aurena fa kayi,zamanka nake yi sabo da kai nazo nan nake zaune,na rabu da iyayena da kowa nawa na yarda na dawo wajenka,ka manta ni me shago ce fa,baki ya turo da shagwaba yace ai kece bakya ji na fada miki bana so,to na daina I'm sorry Sweet,rungume shi tayi daga ita sai towel, murmushi yayi ka fasa saka min bra din? yace ke wasa nake miki ina ni ina kallon wannan chamber taki,dariya tayi tace to jira na shirya sai ka dauke ni ka goyani,daga na miki sau biyu ke baki san kadan ba,dan Allah ta marairai ce masa,Okay to shirya,wayarsa ce tayi kara ya duba da sauri yaga a wajen aiki ne aka sake kara masa matsayi,ihu yayi yace kinga an kara min girma yanzu, Maheera murna tayi ta rungume shi suna ta murna,ya sake duba wayar yace tayani karanta turancin nan ance naje gobe zamu tafi Meeting rivers state ko?,Maheera tace Alhmdllh I'm so Happy,zamu kara zama masu kudi,Dama Oga yace yanzu indai aka canja min matsayi to babu zama kuma kullum tafiye tafiye zan dinga yi,Maheera ta dan ji damm sabo da ita ta saba da mijinta kullum suna tare suna kula da juna sannan so take a hankali ta dan ganar da shi yanda ake soyayyar aure ko Allah zai sa ya gane.


Islaha sai da su Maheera suka fito sannan suka samu labarin,Murna suka tayasu sosai,Sahil yafi kowa murna gashi shima zai fara nasa.
Maheera tace ke Islaha kece kika sha hanya kizo ga abinci fatan kuma kin kira Hajiya kulu,Na kira ta na fada mata muna tare.


Dining suka zauna Sahil yace shi bazai ci tuwo ba,Maheera tace amma sai ka fada min tun dazu na maka wani abin,Sohail yace yanzu ma ai tashi zaki yi ki masa ko da yunwa zaki bar min shi? Sahil yace Jullof din taliya zaki min da kifi,Maheera ba musu ta mike Islaha tace zauna naje nayi masa,Sahil yace ke kina da aure ne? Bana son ki dinga shiga hurumin da ba naki ba,aikin matar aure sai matar aure,mu yanzu muna da mata girki sai na me aure idan baki da aure kawai ke kazama ce.


Maheera haka ta shiga kitchen ta masa nasa ta kawo masa yace yawwa Sohail sa mata Albarka,Sohail yace Allah miki Albarka Allah yasa ki haifo min yan biyu,Maheera harda cewa ameen da sauri,yace taki ma samun cikin har yanzu shuru,Islaha dariya tayi a ranta tana jinjinawa Maheera da zaman auren nan yaki mata ciki yace itace taki samu.


A boye Maheera tace dan Allah Islaha kiyi sauri a daura muku aure ko na samu sauki da twins ki daure ki janye min dayan ki rage min,Islaha tace bai ce ba zance yazo aure ni ne.


Washe gari Sohail da sassafe suka yi Sallama yabi flight suka wuce,Sahil ne ya kaishi airport din tare da Alhaji Saminu suka tafi sabo Sohail sai ana sasu a hanya.
Kwanan Islaha daya tal a gidan Hajiya kulu ta kira tace ya kamata fa ki dawo gobe tunda kin ganshi idan sonki yake yaje ya kai kudin aure danginki,bata yi musu ba tace to zan dawo Inshaallah,Sahil yana ji ya fito yace naji kamar kina cewa gobe zaki koma lagos,ae haka Hajiya Kulu tace,kamar abin kirki yace kira min ita muyi magana,Kiran Hajiya kulu tayi a waya tace ga Sahil zaku gaisa,ya karba bayan sun gaisa yace wai yarki ce Islaha? tace a'a Allah ne ya hadamu to na raba ku,dan Allah ki kyaleta ta sarara,Hajiya kulu tace kaji yaro dan ubanka sanda ka koreta waye ya riketa,ai ni sirikarka ce,Sahil yace sirikita tana kushewa ta rasu bani da wata sirika,dama ni haka nake so ba ruwana da kunya ki zare min ido nima zare miki zanyi,Hajiya Kulu tun a nan tace Islaha zata yi babban ganganci da rayuwarta yanzu wannan zata aura shi yasa tace ba normal yake ba,ai kuwa zata yi kuka da idonta watarana.


Sahil tuni ya kashe wayar yace sai dai ki jira Sohail ya dawo mu tafi kauyenku da yan uwan Daddy a kai kudi,Islaha tace wlh baza su daura ba Ibrahim zasu bani,Sahil yace zasu daura ki kyale su dai dai muke da su,Islaha tace to shike nan,Amma baka kyauta ba da ka yiwa Hajiya Kulu haka ka bata hakuri,Tunani ya lula yace sai kuma naga ban kyauta ba,sake kiranta to,Islaha ta sake kira tace dan Allah Hajiya kiyi hakuri,Hajiya kulu tace na fahimta ai karki damu Islaha,Wayar ya karba yace kiyi hakuri naga ban kyauta ba zanyi hakuri na kalle ki a sirikata watarana idan ta kama
Hajiya Kulu ta jinjina kai tace ba komai na gode ta kashe wayar tace tab a haka yarinyar nan zata kai kanta.


Maheera ita bakuwa tayi tana can tare da kawarta ce tazo Sadiya,suna zaune a bedroom,Sadiya tace Maheera wani zance naji ance wai mijinki mahaukaci ne? ance basu da hankali gaba dayansu,ana ta gulmar a gari, Maheera fuska ta bata tace nifa bana son munafunci kizo har gidana kice da mijina mahaukaci,munafukar banza indai wannan ne ya kawo ki tashi ki bar min gida,Sadiya tace daga fadar gaskiya,Islaha tana palo tare da Sahil taga ya jawo belt a jikin wandonsa ya boye a bayansa ya mike ya tare kofar palo ta fita.

Sadiya ce ta fito zata tafi sum sum Sahil ya tare hanya yace munafuka to naji duk abinda kika ce,wato mu mahaukata ne,ke ubanki mene bayayi naga chacha yake yi tun yana matashi yake chacha har yanzu bai daina ba,shine kika taho munafunci gidan masu aure zaki rusa musu aure dama haka kuke yi kuna ziga mutane,Sadiya Tsoro taji tace kayi hakuri,bazan hakura ba cewar Sahil,mijinta yana can ya tafi nema kinzo kina munafunci zaki ziga masa mata,Belt dinsa ya fito da ita nan take ya zugawa Sadiya daya,ta saki ihu kafin ta shanye ya kara mata,yace gobe kya kuma zuwa gulma gidan wasu yaci gaba da zuba mata belt ta ko ina tana ihu tana rokonsa, gashi ya tare hanyar fita,da kyar Islaha ta bude mata kofa ta fice da gudu ya taka zai bita Islaha ta rike shi tana dariya,Maheera ma data fito dariya take tace wlh ka birgeni,yace ai laifin ki ne da jaye jaye.


Tunda Sohail ya tafi sam ko time din waya baya samu,Maheera duk ta damu kanta ita ya daina sonta,gashi har an kwashe 5days bai dawo ba,sai a kwana na shida ya dawo yana dawowa yace zasu tafi Dubai next week,Maheera ta fashe da kuka wiwi a bedroom,Sohail ya fito daga wanka yace menene Sweet? Me ya faru?


Ni wallahi wannan kudin ya ishe mu rayuwa me ake bukata ga gidan zama kana aikinka daidai misali,muna ci muna koshi Alhmdllh yanzu ace wannan bai isa ba,shike nan an dauke min mijina waya ma ta gagara,kana can zaka dinga yawo a gari mata shike nan daga nan wata ta ganka ni na shiga uku na lalace.


Sohail yace kwantar da hankalinki Sweet kince zamu haihu wannan kudin fa mu nake nemawa neman da nake yi dan wa nake yi? Shekara da shekaru tunda muka taso a bauta muke da wahala ana neman aiki sanadinki na samu aiki gashi munyi aure to mene dan an kara nema wasu kudin sabo da rayuwar gaba mu samu muji dadi da yaran da zamu haifa gaba,Maheera tana kuka ta sakko kasa ta zauna zaman dirshan ta cire dankwali ta jefar,gashinta da ya sha gyara yana sheki ya bayyana,tana ni dan Allah ka hakura wannan ya ishe mu muna zaman mu kullum ni bana so kayi nisa,okay...okay...to nace kayi min ciki na samu na cika gidan nan da yara idan ina ganin yarana ko zaka yi tafiya bazan damu sosai ba,kace ba yanzu ba na rasa inda kasa gaba tsakani da Allah ko tabani baka yi kuma shine dan kulawar ma yanzu ka samu canji sai dai kasashen waje wallahi Allah ni bana so dan Allah ka tausaya min ,Kafafunsa ta rike tana kuka,Sohail ya tsaya yana kallon ikon Allah ta haukace gaba daya.


Yace na dade ina ji ana cewa muna da aljanu ashe ba mu kadai bane,yanzu daga tafiya sau daya? Wasu matan mazajen fa wasu sai su kwashe 6months basu zo gida ba kuma suka hakura,mikewa tayi tsaye ta rirrike shi ni bazan iya ba,ba irinsu bace ni na saba da mijina kullum muna tare sai dai a barni ni kadai dan Allah ni wannan aikin kwai jaraba zai rabani da mijina Allah ya isa tsakanina da Alhaji Saminu.


Sohail girgizata yayi yace mene haka kwaya kika sha ne? Tana uban kuka ya zaunar da ita yace dan Allah mene haka ne? Kinki fahimtata,bawan Allah ya bani aiki ya min abin arziki sai ki zage shi kamar bakya so na,ki kwantar da hankalinki babu wacce zan so ba wacce zan kula in kika ga na kula wata sai kaddara idan Allah yayi zan kara aure,Maheera kasa ta zamo wayyo na shiga uku a hanya zaka hadu da wata garin jarabar yawon aiki shike nan kishiya zaka min,ashe har kana tunanin kara aure ban sani ba.
Sohail tagumi ya zuba wajen lallashi ya bata komai,gani tayi duk ransa ya baci ya shiga damuwa,sakkowa tayi kuma tace to kaje na hakura dan Allah karka kula wata ka dinga bani kulawa ko a waya waccen lokacin bana samun jin muryarka,Murmushi yayi yana kallonta yace to kiyi hakuri zan gyara Inshaallah ki daina wannan borin haka duk kin birkice kalli yanda kika hada gumi,duk a kaina kike wannan? To ba sonka bane ya jawo nifa zan iya mutuwa a kanka,Sohail yayi dariya yace baza ki mutu bama inshaallah sai nayi kudi munji dadi mun haifo yara kin aurar da yara suma yaran sun haihu wanda aka haifa ma sun haihu,Maheera taji dadi ta rungume shi tace wayyooo duniya ta....dariya yayi yace Baby...hannu ta yarfe tana jin kunya tace kana fada sai naji kamar na sume ,kana fasa min kai,yace to abincina, fita tayi taje ta kawo masa,Yace gobe zamuje kauyen su Islaha kafin na tafi Dubai,Yana ambatar tafiya Maheera ta zuba tagumi,kin san ina sonki ba wata wacce zan kula,tace to ai ni caring din please ni a kulani,yace to yana murmushi,abincin ma a baki take bashi,yana mamaki a duniya shi kuwa da me zai biya Maheera,bashi da kudi ga halin da yake ciki amma take masa mahaukacin so haka.


A ranar Sahil waya kawai yayiwa su Kawu Nafiu yace suzo za a kai kudin aurensa,Ba ko musu suka ce muna tafe gobe,Sahil Address ya tura musu

Please Login or Register in order to submit comment