Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma kenan da lafiyar su.


Daddy yace aiki yayi min yawa Adnan na kusa zuwa garin akwai wani meeting da zamu yi da me gidana zanga me suke yi,Adnan yace shike nan,Na bawa Ibrahim kyautar gida shima ya kamata yayi aure,Adnan yaji dadi,cikin Daddy ya buga yace twins fa?
Daddy yace su nake tunani gaskiya babu wata mace da zata so twins a haka bare ma suyi aure,ai baza su iya rike aure ba sabo da rashin lafiyar su,Adnan yaji dadi yace gaskiya dai,sai da suka gama hirar kamfani suka kashe wayar.


Sohail yau an bashi sabuwar Motarsa da takardun gidansa sannan ga Alert na kudi masu nauyi,Murna tasa yau da wuri ya shiga motar ya dawo gida,Adnan yana shirin fita yaga mota baka kirar Marcedes baka me kyau sabuwa ta shugo gidan anyi parking.
Sohail ne ya fito daga ciki da takardunsa a hannu,Adnan ya saki baki yana kallonsa ina ya samo mota ne,yanda bai kulashi ba shima Sohail bai masa magana ba ya wuce ta gabansa ya shige ciki.


Sahil ya samu yana kallo a palo,yace wai Sahil baza kayi hakuri ba akan yarinya ta tafi fa, please kaci gaba da rayuwarka,kaga Allah ban zanci zan iya komai a duniya ba duba da yanda a makaranta gaba daya bani da kokari ba abinda na sani sai dai a jarabawa,amma yanzu kuma komai sai naga kamar ba yi nake yi ba da kaina kamar yi min akeyi,ta ya zan san wannan uban turancin Sohail,amma sai naga na karanta sai naga na iya computer,amma a school bamu iya komai ba muyi ta jin kunya,ni dai mamaki nake yi da nake iya aikin nan sai mu kasa abu watarana kuma mu iya shi,turanci fa ka duba watarana sai muji munyi watarana sai mu kasa ko sentence daya.


Sahil yace rayuwa ce kawai ni ta Islaha nake yi,na gaji kada Allah yasa ta dawo tayi ta tafiya na gaji da halin yarinyar nan,bata da kunya dama badan haka ba daga yar magana sai ta tafi cikin dare ita ga me zuciya,tana dagula min lisaafi.


Sohail ya nuna masa key din mota da takardun gida ya nuna masa Alert yace to wahala ta kare gobe zan fara aiki.
Sahil wannan murnar tasa ya share zancen Islaha sunyi kudi yanzu.


Sohai ya furta Yanzu Oga yace Business na kayan da suke shigowa da shi za a koya min sosai nafi dacewa da wajen sabo da ko wanda bai boko ba zai iya wannan bangaren na shige da ficen kaya ta kamfanin yace shine daidai ni,tunda na fada masa watarana zata iya kwabewa na kasa karanta komai ko computer din ma ta gagareni,shine yace to wannan bangaren shine daidai ni ko ba boko zan iya.


Bari a nunawa Maheera Sahil yace kai baka da hankali ka nuna mata gida da mota amma kudi ba a nunawa mace samu baka ji maza suna fada ba,Sohail yace ahhh gaskiya a nuna mata na farko shike nan ai,ita ta iya bata yi kyashi ba ta samo aikin sai mune zamu ce baza mu nuna mata ba"
kai nuna mata karka ishe ni,ko ni yanzu baka so na irin Maheera,komai ita komai ita cewar Sahil.
Dariya Sohail yayi yace nima na rasa dalili ba a son raina ba ban san ina yi ba,abin yana damuna ka tayani da addua,Sahil ya furta Allah ya yaye maka to.


Sohail Maheera ya samu a kitchen lokacin ta dawo daga gida tana girki a hankali ya tsaya a bayanta,kamshinsa ta ji ta juyo da sauri,dariya yayi yace kin fiye tsoro,matsawa tayi daga yanda suke tsaye gaf da juna,Maheera ta kalle shi tace any Good news naga kana wani murna kai kadai,wayarsa Samsung ya mika mata yace gashi ki kalla,Maheera ta duba ta gani ta rufe baki da tafin hannu tana murna,Key din mota ya karkada mata a saitin fuska,ta karba ta gani tace wow,sai takardun gida, Alhmdllh gaskiya na muku murna sosai Allah sanya Alkhairi.


Yace to aikinki ya kare kuma ki shirya ki koma gida,Maheera tace a'a ni ka kyale min aikina gwara na dogara da kaina,au ke bada Allah kika dogara bama da kanki kika dogara? Karki shirka dai.
dariya tayi tace wai kudin nake nufi, badai albashi ne ba ni zan dinga biyanki abinda suke baki,maganin Mama da sauran matsala ta kannenki duk zan dinga yi.


Maheera tace idan ka daina yi fa? ku maza wani dorar da alkawari kuke yi wannan ba yuwuwa zaiyi ba, haushi Sohail yaji yace kice kawai karya nake yafi miki,wanne irin abu ne haka ana fada miki bakya ji,kinfi so ki zauna kiyi ta girki,Maheera tace gida kake so na koma? Na barku kuci gaba da wani abin ba daidai ba nasan me zaku aikata gaba.


Da ke kika raine mu ba haka kika tsince mu ba Allah ne yake tafiyar da komai,Kice dole sai kin samu a hanya,ke zaki shiryar damu? badan muna ganin mutuncinki ba 'yar tatsitsiya dake har ke zaki ce kato kamata nayi abu nayi,Kalle ki fa kalle ni baki wuce na goyaki na zagaye Abuja da ke ba gaba daya ko hutawa bazanyi ba.


Maheera dariya take tace Sohail ni kwana biyu naga kamar hankali kuke yi sai kuyi ta magana ta normal mutane,kallonta yayi kawai tare da shafa gemunsa yace girma ne yazo kalli fa gemuna ya furta yana shafa gemunsa.
Sahil ne ya shigo ya kalli farfesun da Maheera tayi yace mota ta dawo min da hankali na yanzu yunwa nake ji,nama daya ya dauka ya cinye ya karbi key din motar yaje ya shiga ya tafi dani shima wanda da akwai karambani Sun iya mama Asmau ke hanasu hawa sabo da matsalar kwakwalwarsu.


Maheera suna ta hira da Sohail basu saba rike kudi ba sabo da ba a basu kudi sam,yace yanzu ya za ayi da kudin nan ne? Sun isheni a accnt dina ni na rasa abin siya,Maheera tace ance maka kashewa zaka yi lokaci guda? Matsalar data dame ku zakuyi,Sohail ya lula tunani yace matsala mu bamu da wata matsala muna ci muna koshi muna da sutura to mene za muyi?


Kuje kuyi tunani mana matsalar taku,Sohail yace yawwa kika ce muna bukatar aiki mu samu kudi muyi aure mu haifi yara ko? Maheera tace ae mana to ai a fara ta kansa,dariya tayi tace kuma daga samun kudin sai auren kana da budurwar ne?


Sohail yace ba gaki ba,ka taba ce min you love me ne da zaka kace nice....to I love you Sohail ya furta da sauri kafin ta rufe baki,Sahil dinfa ko kaine zaka yi auren ka rigashi sabo da kai kayi kudi? to ba Allah ne yace ayi ba tunda bashi da budurwa a kasa ba shike nan ba,a'a a daura dai auren tare ku aure ni ku biyu kawai ai kunce na ishe ku ko?
Kaga sai a raba muku kwana yau kai kazo mu kwana tare gobe Sahil yazo,Sohail yace ai kuwa da an rataye Sahil anyi hanging dinsa kawai an huta, yarinya na sani to namiji daya shi yake auren mata hudu mace namiji daya tal take aura.


To yanzu mata hudun zaka yi kenan? Sohail yace to a Office tv dina naji wa'azin Allah ne yace malam yace a taimaki mata sunyi yawa a gari idan da hali mutum yayi ta karawa har su kai hudu,kinga kece uwargida zan miki wannan alfarmar na aureki a farko daga baya sai a karo miki ta biyu a haka har na cike hudu na,Yan mata hudu rigis ni kadai gaskiya mun muku wayo mu.


Maheera tace wanne malami ne yayi wannan wa'azin? ban sanshi ba channel din a tv din Office dina take,Maheera a ranta tace dole na kira Alhaji Saminu a tsinke wannan Channel,ina so ya dinga jin wa'azi amma banda na kishiya,inda baida kai ai sai yace sai yayi, sai ya aure su.


Maheera tace Sohail ba haka malamin yake nufi ba,nufinsa idan mutum zai iya adalci kuma yana da kudi sosai,Sai zai iya adalci aka ce idan bazai iya ba yayi zamansa da guda dayarsa,Sohail yace aya da hadisi ya kawo to Hajiya.


Maheera tace uhmm ai shike nan yace ae ga kuma Hurul ayni yace na lahira suna can a lahira suna jirana gaskiya mun gama da ku mata kuyi hakuri 10-0 kawai.
Dariya ya bawa Maheera tace ashe kai mayen mata ne ban sani ba,daga kaga ka fara kudi shine ka fara zancen mata,Adnan shi da matarsa daya ta ishe shi abinsa gwanin sha'awa kai da mamanku take baturiya baka gaji halin turawa ba mace daya danginku suke yi,Sohail yace ni nasan wata mama ne ina ruwana da su.


Yaushe zaki tafi gidanku? Maheera tace ina nan bazan tafi ba,aikina zanyi,Sohail yace shike nan ki ta zama tunda ke bakya son ci gaba,tace ae naji mutumin da zaiyi mata hudu waye zai dogara da shi jeka can da matanka bada Maheera ba.


Maman su Maheera aka kwantar a asibiti ciwonta ya tashi,kannen Maheera ne suka kaita asibiti sai da suka kwana kudinsu ya kare sannan suka kira Maheera,tare da sanar mata.
Sohail kuma ya rigata sanin ma an kai Mama asibiti yau aljanun sun waiwayo,Zuwa yayi har asibitin ya dubata su Juwairiyya basu sanshi ba sai kallonsa suke yi,ya tambayi kudin nawa zasu biya? Suka ce dubu dari biyu da hamsim mun biya dubu hamsim,dubu hamsim dinsu ya basu yaje ya biya kudin komai da komai da duk wani magunguna da ake bukata masu tsada ya siya mata da yawa aka siya wanda zai dade bai kare ba.


Abincin masu ciwon sugar daban haka yasa aka masa list duk ya siyowa Mama,komai naci sai da ya siyo har na kannen Maheera abinda zasu ci lemuka da fruits da kayan shayi etc sai kudi ya basu yace ga wannan ku rike idan zaku siyi abinci,Suka ce mun gode.
Ammar yace dan Allah waye kai? Sohail yace sunana Sohail idan Maheera tazo ku fada mata ta sanni,suka ce to an gode.


Yana tafiya Maheera taje asibitin ko zama bata yi ba tace ya jikin maman? Bacci take tun rana,me suka ce za a biya?
Wani yazo ya biya komai kalli abinda ya siyo yace sunansa Sohail,kawai ganinsa muka yi yazo, Juwairiyya tace Aunty wani kyakyawa ne wlh,Sahil ne ya shigo kamar ana fada musu,Ammar yace yawwa gashi ma ya dawo,basu gane ba Sohail bane,ita kanta Maheera sai da yayi magana taga wushiyarsa yar karama ta gane Sahil ne.
Tace dan uwansa ne fa ba shi bane wannan Sahil ne waccen Sohail,Su Ammar suka ce ikon Allah basu da banbanci,Sahil zuwa yayi ya ja kujera ya zauna ya tambaya ya jikin Maman? tace da sauki,Su Ammar suka gaida shi yayi musu ya me jiki.
Sahil harda cewa kaiii Mama tana jin jiki wannan kibar tata bata Allah bace ciwon ne ya hura ta karku dauka jin dadi ne yasa tayi kiba haka, suka ce ae haka likita yace,Allah ya bata lafiya ya furta,20k ya basu yace sa suyi wani abun,suka ce kaima sai ka bamu?


Yace ya zanyi Sohail yace na baku ba yin kaina bane Sohail ne ya min dole yace lallai na baku,ba wani kudi ne da mu ba rufin asirin Allah ne,Maheera ta boye dariyarta tace to mun gode ka gaida gida,yace a'a sai kace mahaukaci zance gida ance ana gaisheka gida ba mutum ba ba komai ba kice na gaishe shi bazan yi ba ya fice yana cewa Mama Allah ya baki lafiya kiba haka kamar ta jin dadi kai ciwo da wuya yake,sai kace kibar sihiri kafafu tutum tutum haka.


England
Wata dattijuwa ce zaune a garden din gidanta tare da wani tsohon bature Halley Maman su Sohail,Mijinta ta kalla Ivan,cikin harshen turanci tace ina so zanje Nigeria zuwa nan da wata uku,tun daga yarana dana bada su na zaci idan nayi aure zan sake haihuwa ban sake haihuwa ba tunda na aure ka wanda a baya ina da kuruciya bani da aiki sai club da holewa na sa a gaba,yaro na daya bashi da lafiya suka dameni na bawa ubansu shi ya sake ni,yanzu ni nasan nayi kuskure suna can sun zama musulmai,bana so kuma su kasance musulmai gaskiya,bana son musulunci,bayan haka yanzu basu sanni ba ina bukatar yarana su sanni na jasu a jiki.


Na nemi ubansu rannan da kyar na samu number dinsa wajen abokinsa Harry na kira yana ji nice ya kashe wayarsa,yanzu Nigeria zan tafi na ja yarana a jikina su san wace ni tunda ban haifi wasu ba.
Mijinta Ivan yace kinyi ganganci kuma baki yi daidai ba,yanzu baza su saurare ki ba,baza ki iya canja musu addini ba,indai hakane Halley har yanzu to baki hankali ba,na zaci ma zaki ce bari kije ki basu hakuri su karbe ki a matsayin uwa amma ke ta addini kike yi,sannan kuma tunda baki haifi wasu ba shine zaki neme su,yaran naki kisan da marar lafiya baki tausaya musu ba,baki da hankali Ivan ya mike ya wuce ciki ya barta iskar lambu na fifita mata sisirin dogon wuyanta ,Halley tace zan je dai naga yarana ya suka koma yanzu,murmushi tayi tana tunano su.


Online ta hau ta shiga searching sunansu ko zata gansu,har cikin friends din mahaifin su Sohail ta shiga ko zata gansu bata san uban ma bata su yake ba,shi dai kawai ya basu ci da sutura shine kawai,text ta turawa Alhaji Ali ya turo mata pics din yaranta yana ganin haka yayi blocking number dinta gaba daya ya shiga harkarsa.


Islaha kuwa kwananta daya da asuba Lalai ta tasheta tace maza kiyi sallah kije ki cika gidan nan da ruwa,Islaha tace Abdulrazaqu fa ai shi naga yana ebo miki tunda shine namiji a gidan nan kuma danki ne na cikinki sai yau zaki ce ni, Lalai tace to ke naga dama zan dafa na baki kici a kwance ne,Islaha brush tayi tayi alwala da sallah ta zauna azkhar dinma Lalai damunta tayi ta tashi haka,da kuturin iyayi mu zaki nunawa addini zaki zauna kina mismis da baki.


Tashi Islaha tayi ta dauki botiki duk garin babu budurwa me girmanta da shekarunta sai kallonta akeyi,gashi kasan ba yar garin bace kana ganinta yar birni ce,rijiyar da suke iban ruwan ta karasa,kowa da gugansa yake zuwa.


Ruwan ta jawo ta cika botiki duk maza ne a wajen sun fito iban ruwa kafin su tafi gona wasu su tafi kiwo,Islaha tana gama Iba ta dauka ta kai gida haka ta dinga jidon ruwa sai da ta cika ko ina na gidan sannan Lalai ta bata dumamen tuwo da wani dan koko a kofi kamar na yaron yaye tace gashi nan.


Islaha tace kaddara kenan in ba kaddara ba me zai sa naci wannan tuwon,Lalai ce ma zata yi wani girki ta bani naci,Lalai tana ji tace uban wa ya kawo ki gidan,ji nake ke kika kawo kanki kinibabbiyya.
Islaha haka tana kushewa ta cinye tuwo ta shanye koko tace dan dai kawai na rayu ne wlh da bazan ci ba,Lalai ta fito tana masifa sai kije kiyi wanke wanke ko a banza zan zauna ina dafawa ina baki kina ci.


Islaha taje tayi wanke wankenta tayi shara ta gyara gidan,Lalai tace saura daka, mu kin san a nan sai munyi sissika,surfe ma da hannu muke yi a turmi sai ki fito ai,Islaha ta dauki tabarya ta tsaya a jikin katon turmi,Lalai ta zuba dawa tace bismillah mu fara wannan dai zan tayaki,kyazo kici a kwance ne,sabo da Allah sai dai a baki kici ki koshi, sa jiki yi da jiki maza saka tabarya,Islaha ta saka tabarya daya chakwal chakwal sam bata iya ba,Lalai ta sa tata tace yar bibiyu zamu yi muje zuwa a hankali zaki goge.


Islaha ta dinga yi suna yi a haka da Lalai kaikayi yana tashi zuwa jikinsu, Abdulrazaqu ne ya shigo sai faman zagasu yake yana karewa Islaha kallo yana sannunku da aiki,Islaha ashe kin dawo nan da zama yana wage baki,da wata hularsa bokoko.


Lalai tace tayi aure taki ka ganta nan kalar bazawara, Abdulrazaqu yace ai watakil rabon na gida ne shi yasa Allah ya dawo da ita,yin Allah ne,Islaha..Islaha...kaga Islaha sarkin aiki cewar Abdulrazaqu,Islaha haushin Abdulraqu ya gama kamata da irin kallon da yake mata.


A cikin gidan ya nemi jikin bishiya ya zauna sai faman kallonta yake yana murmushi baki a bude,Islaha ta gaji amma sai da aka gama daka da ita,sannan Lalai ta kwaso danyen rogon da Abdulrazaqu ya kawo ta mikawa Islaha wuka tace maza mu fere shi za a dafa yau aci da kuli.


Islaha ta karba bata ce komai ba haka suka fere rogon nan tas Lalai ta wanke ta dora a murhu ta fara dafawa,tace share wajen,Islaha ta sake share ko ina taje tayi wanka,tana yin wanka Lalai tace kinyi asarar sabulu ai zamuyi surfen dawa,Tazo ta zuba dawa a turmi da dan ruwa tace sa tabarya muje,Islaha tana daka tana kuka tace wlh ni ban iya irin wannan aikin ba,ban saba da yi ba,kashe ni zakiyi haka, Abdulrazaqu ya fita amma bai dade ba sabo da Islaha ya sake dawowa.

Ya ganta tana kuka yace ji banza raguwa mu anan yarinya karama ba sai ta daka dawa kwano biyar ba amma ke dan wannan aikin kike wa kuka karki bada ni mana,Islaha tayi banza da shi tana hawaye, sai da suka gama tas sannan Lalai tace ai bamu bushe an wanke dawar ba,dakko faranti da faifai,Islaha taje ta dakko haka suka bushe tass tace dauki ki wanke,Islaha taje ta wanke ta shanya a wani karamin tempol.


Tashi na aikeki ki siyo kuli,Islaha ta mike da kyar take tafiya,haka ta karbi kudin tace gidan su Baffa Gali zaki je matarsa tana siyarwa,Hijab ta saka ta fice.
Tana shiga gidan Baffa Gali kowa ya fara murna tunaninsu Aunty ce ta sake aiko Islaha da kudi ko wani abu,Sai lale ake yiwa Islaha,Baffa Gali yace ashe kinzo garin gidan Lalai kika sauka ne? Islaha tace ae,yace Ja'ira gari duk danginki amma mu baza ki dinga sauka a wajen mu ba,mufa yan uwanki ne na kusa ba na nesa ba,Islaha tace ai na dawo nan da zama gaba daya ba Aunty ce ta aiko ni ba.


Gali yace toooo....fada kuka yi? Islaha tace itace tace ta gaji dani,Gali yace kece kika mata rashin kunya Islaha,laifinki ne,ba ruwan Auntynku mutuniyar arziki ce,ku yaran yanzu baku iya samun waje ba,yar banza kina zare ido kamar na uwarki, Gwara ma da kika sauka gidan Lalai din ni nan baza mu shirya ba,kuma ki fidda miji kinji na fada miki.


Islaha tace a bani kuli inji Lalai,Matar Gali ta karbi kudin a wulakance ta kawo kulin ta bata tace ki gaida Lalai,Islaha ta juya tayi tafiyarta,a ranta tace nina jawowa kaina da ban lallaba Aunty ba da tuni ina Lagos abina,ashe Aunty dai duk da haka tayi kokari ta iya rike ni,inci insha duk da itama irin lalai ce sai naci aiki ake bani ga zagi ga gori amma da dama aikin nasu ba irin na kauye ba,idan nayi sati ina wannan aikin sunan na tashi a aiki na zama tsohuwar karfi da yaji bazan iya ba idan na gaji guduwa zanyi wlh.


A haka ta dawo gidan Itace ta daka kulin Lalai ta kwashe rogo shi suka ci suka koshi sannan ma ta samu tayi sallah.


Maheera tana can suna jinyar Mama kullum su Sohail sai sunje asibitin dubiya har Mama ta samu sauki aka sallame su,amma Zayna da su Adnan an fada musu ko ya me jiki basu ce ba,Ibrahim kuwa ya tafi kano gida wurin Daddy har yanzu bai dawo ba tunda suka tafi tare da Amal bai ma san Islaha bata gidan ba sai yau da ya dawo da yamma,ya gaji ya tambayi Maheera tace ai ta tafi garinsu,yace ina ne? Tace Taraba kauye,wanne kauyen? Tace ban sani ba,yace baki da hankali duk zaman da kuke yi baki tambayi address dinsu ba ya ja tsaki ya fara gwada kiran Islaha number bata shiga.


Bai gaji ba yace amma indai ta taba kunna layin a garin da take ai masu tracking number zasu gano zanje na bincika har kauyen da take zanje.


Sohail dai yana ta zuwa aikinsa gwanin sha'awa Alhaji Saminu ana ta samun ci gaba a kamfani mugun kaunar Sohail yake yi sun saba sosai,bangaren da Sohail yake basai me karatun boko me zurfi ba,sannan akwai wani a kusa ko da haukar zata motsa.


Gidan an zuba furniture da komai na bukata flat house ne me kyau,dauke yake da 3 bedrooms sai parlo,ga katon kitchen da Dining area daban,gaba daya estate din irin ginin kala daya ne komai kai daya kowa da wajen parking da komai, ko ina yaji fulawoyi kamar a turai,basu bar gidan su Adnan ba amma kullum sai sunje sabon gidan kuma watarana su kwana acan watarana su yini su dawo gidan su Adnan su kwana haka suke sintiri.


Motar ma kusan Sahil yafi Sohail hawa,Kayan abinci da duk wani nauyi Sohail ya daukewa Maheera na gidansu bata musu komai yanzu,gashi bai taba zuwa gidan ba,sai daga baya tunda yasan gidan ya dame su da zuwa, Mama ce ta kira Maheera a waya,bayan sun gaisa tace Maheera nifa yaron nan da yake ta mana hidima ya kamata ace idan soyayya kuke kin fitar da shi tunda yana da aikin yi,kuma yana da hankali ni na yaba da shi gaskiya,indai kin san soyayya kuke yi banga amfanin zaman haka ba,Maheera tace to ni dai mutunci muke yi da shi Mama,ban tabbatar da so na yake ba.


Mama tace shike nan tunda haka kika ce amma ni bazan so ace yana kashe mana kudi a haka ba gaskiya kawai kisan yanda zaki ko ki dakatar da shi ko ki tsaida shi a mijin aure kawai,Maheera tace to,Mama tana kashe waya sai ga Sohail yayi parking motarsa sanye yake cikin sky shadda ya zuba kyau,gidan ya shiga kai tsaye,Mama ta amsa sallamarsa tace Sohail kaine kazo? Sohail ya sosa gashinsa daga bakin kofa yaki shiga kuma yana daga tsaye ya leko da kansa yace Mama Ina yini? Baza ka shigo ba kuma yau? Ai ka zama dan gida,Sohail yace kunyarki nake ji kunyar surukai nake yi,Ammar yayi dariya kamar me,Yace dan Allah ka shigo? Sohail yace wallahi Allah bazan shugo ba yau kullum sai nazo na shigo, nazo ina raina sirikata,Mama dariya ta kamata,tace yau naji shashan yaro kai kuwa kalau kake?


Sohail yace ki fadawa Maheera Mama ta dawo gida nayi nayi taki ta dawo ai ba mutunci bane ta zauna cikinmu,gwara zayna ita tana da miji,Amma mu maza mu hudu ne a gidan ita budurwa ta hakura da aikin nan zan mata komai ni kadai kudina ya isa,amma taki sai Iyayi take min wani ita ai kaza kaza ya gwada yanda Maheera take magana,Mama tana daga palo yana daga bakin gate a haka suke zancen,Mama tace to ka turo iyayenka indai sonta kake suje dangin ubanta a nema maka aurenta na gaji da wannan soyayyar in ka tabbatar sonta kake kayi magana,Sohail yace zan dai tabbatar, zan tafi,yau Mama bazan baki kudi ba Ammar zan bawa,Mama tace to ai abin naka yayi yawa ni kyautar ma taka ta ishe ni,Sohail yaji dadi ya kira Ammar ya bashi kudi ya juya ya tafi yana murna yace yawwa dama nace Mama sai ta shiga uku da kudi gashi tace kyautar har ta isheta,sai nan gaba ma, ya shiga motarsa ya tafi.


Please Login or Register in order to submit comment