Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ranar da zuciyarta ta karye sosai ranar da wani hafizzou ya shaida mata soyayyarsu ba zata iya ci gaba ba. Shigowar maina gidan kenan daga makarantar manya ta dare,yaga fitar hafizzou ya kuma ga shigewar nafessa ciki da sassarfa sassan bibi,sai kawai ya take mata baya yana addu'ar Allah yasa bame afkuwa bace ta auku.

Yana shiga ya sameta saman cinyar bibi din tana sharba kuka. Aba na falon haka haka ama,suna list na abubuwan da bibin keso ama zata taho mata dasu daga Nigeria,don saura kwana uku ta wuce can din,kasancewar bata rabo da zuwa don suna da tamfatsetsen gida a can da idan sunso suna iya share wata uku ciki kafin su dawo niger,ita da aba ko ita daya dinma.

"To sai meye?,a kansu kike zubda hawayenki nafessa?,suyita tafiya din,ni zan aureki,na yarda ni aliyyu zan aureki" ya fada cikin tsanani fushi da zafin zuciya. Ba ama kadai maganar ta yiwa luguden duka ba,har bibi da ita kanta nafessa din. Dif falon yayi abinda maina bai tsaya wani la'akari dashi ba yaci gaba da zazzaga masifa.

Sakale ama kawai tayi tana kallon ikon Allah kuma zatonta yana sake qarfafa lallai aliyyun wasu ta haifawa. Zuciyarta ta gaza daurewa ta daka masa tsawa me qarfi

"Yima mutane shuru dalla,shashasha!,fita ka bawa mutane guri" ta fadi a harzuqe. Har ya fitan suka gama abinda sukeyi ta fice itama babu wanda yace komai akan maganar.

Cikin kwanakin ukun tanata shirin tafiya Nigeria amma ranta a matse yake,gaba daya ta rasa walwalarta,hatta aba da maina sunga canzawarta,tanata juya furucin maina a ranta,tana kuma hankalce da yadda suketa dan shige da fice a sassan bibin lokaci zuwa lokaci. Bataji koda d'ar ba,saboda ta riga ta sama ranta ko sama da qasa zasu hade ba zata yarda maina ya auri nafessa ba,abumma sam bai kama hankali ba,ko ita da mahaifinsa da sukayi aure duniya nada ragowar kwanciya ai dukkansu sai da suka mallaki hankalin kansu sannan sukayi,uwa uba ma kuma bataga dalilin da zai sanya ta bari maina din data dora buri a kansa ya auri sicklier ba,duk da nafessa bata da matsala ko makusa tako ta ina,amma abun ita sam bai kama zuciyarta bama bare hankalinta.

Haka ta tattara harda maina din suka wuce Nigeria,abinda yasa ta gane da wani abun a qasa,tun sanda zasu taho basuyi sallama da aba ba yadda suka saba,sannan a qa'ida tare suka tsara zasu tafin amma shi ya janye tashi tafiyar,bataji dadi ba amma ko a jikinta suka wuce din.

Sanda ta kammala kwanakin data diba zatayin sai taji kwata kwata bata sha'awar komawa nijer,tayi zamanta a nan din duk da lura da tayi maina ya takura su koma din. Suna hutu ne a sannan,kuma hutunsu yakan dauki dogon zango wani lokaci wata uku har hudu ma,ba guntun hutu irin namu ba,wannan ya sanya ta sake miqe qafa,tayi biris kamar bata karanci damuwarsa ba.

Sati guda ta qara akan ainihin kwanakinta aba yayi mata dirar mikiya. Hakanan kadaran kadaham babu wannan karsashin kamar yadda suka saba. Kwana daya kwana biyu shuru,a kwana na ukun suna breakfast da safe ya dubeta yana gaya mata labarin da ta jishi kamar saukar aradu

"Mun yanke shawarar daura auren maina da nafessa" a wani hargitse ta dago tana dubansa

"Wanne maina din?,kana nufin aliyyu haidar?,wanda ko qaramar secondry bai gama ba?dududu shekarar haidar din nawa?,,baya ga haka ka manta nafessa sa'arsa ce?,watanni sha biyu kacal ya bata?,ka manta matakin lafiyarta?"*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 08



"Dukka wadannan lissafinki ne,ba ruwana dasu" ya furta cikin halin ko in kula.

Wannan magana ita tayi silar kawo rikicewar familyn MAYAK'I a karon farko,ta nesanta zazzafar soyayyar dake tsakanin aba da ama me matuqar danqo,soyayyar da bibi bata taba sasanci ba a tsakaninsu,saboda ba qarya hamdiyya ta iya riqon miji qwarai da gaske.

Batayi qasa a gwiwa ba ta yanki tikitin komawa nijer saboda ta tabbatar ba shi daya yayi wannan shawarar ba. Ta dire gaban bibi takuma lissafa mata dukka hujjojinta na rashin amincewa da batun auren maina da nafessa. Bibi din jinjina kai kawai tayi, bata fidda matsayarta ba,don a duniya ba wanda zai kaita son ganin maina da nafessa qarqashin inuwa guda.

Ganin yadda abubuwa keta rikicewa cikin gidan ya sanya oncle mohmoud wanda tunda aka fara lamarin har sanda su bibi suka yanke hada auren bai taba magana ba sai yanzu ya gurfana gaban bibi yace yana roqon alfarmar abar wannan batun,ko don hamidou ya samu zaman lafiya da iyalansa,maina kuma ya samu albarkar mahaifiyarsa. Kai da fata aba yace shifa baisan zance ba,ya riga ya bawa maina nafessa,babu kuma fashi, saidai hamdiyya tabar aurensa.

Sosai maganar ta taba bibi,salin alin ta kwabeshi itama,tace kuma an janye maganar. Kamar jira hamani yakeyi yace shi zaya auri nafessa. Ba wanda ya qyamaci abun a cikinsu,saboda hamani din managarcin mutum ne,kuma dama can shi bame kule kule bane,hasalima babu wata yarinya da yake nema. Dai dai sanda ya kammala Phd dinsa daidai sanda nafessa ta kammala secondry school,babu jinkiri aka gabatar da komai,aba ya daure qarqashi akayi gagarumin biki, Wanda kamar ama tasan za'a yi hakan ta saka maina a gaba suka wuce Nigeria.

Tunda suka tafi din bai dawo nijer ba,hasalima sai ya fara neman gurbin karatu a can,don baijin zai dawo nijer kuma rayuwa taci gaba da gudanar masa kamar yadda yakeso. duk da yayi murna qwarai da nafessa ta samu mutum kamar hamani,yayi imani ba ita babu kuka saboda nagarta da kyan zuciyarsa.

Duka duka auren nafessa watanni shida,tana da ciki wata hudu bintou mahaifiyarta ta rasu. Mutuwar ta girgiza ta ta kuma jijjiga mohmoud,saboda shi kadai yasan irin macen da Allah ya bashi. Albarkacin samun nagartaccen miji dukan mutuwar yazo mata da sassauci,ya tsaya kai da fata ganin matarsa bata fuskanci raurawa ba.

Watanni uku da kwana goma nafessa ta haifi SULTANA, yarinyar da ta samu soyayyar da har ta dara wadda mahaifinta da kuma maina din ya samu,yarinyar data debo kamannin NADEEYA abinda ya qara adadin soyayyarta a zuciyar kowa da kowa. A sannan tuni dukiya ta fara yiwa aba ambaliya,ya fara shiga jerin sahun attajiran 'yan kasuwa masu cin gashin kansu,don bai jima da dukiyar ama a hannunsa ba ya damqa mata komai ya dorata akan turba ya kuma bata cikakken damar kula da dukiyarta kamar yadda kowanne namiji zaiyi shi kuma ya waiwayi tasa.

Iya bikin suna kawai kudade aba ya zuba masu ciwo yace ayi,duk da hamanin ma ba baya bane gurin samu,don tun yana lavel one a jami'a ya fara kasuwanci,kawo yanzu kuwa shima ya zama babban qwaro. Gata iya gata ta kowanne fanni. Ga hamma MAHMOUD jin sultana yake kamar wani yanki na jikinsa, soyayyarta bata taba boyuwa muddin zaka zauna dashi koda na minti talatinne. Ya zubawa sultana so wani irin so me tsayawa a zuciya tun tana zanin goyonta. A haka aka fara rainonta kafin me afkuwa ta afku,mutuwa ta rabata da mahaifiyarta nafessa.

Mutuwar ta daki maina matuqa ta kuma galabaitar dashi,sai kuma a lokacin mutuwar ne ya fara dora idanunsa akan sultana da a sannan take koyon zama watanni uku da kwanaki a duniya.

Wani irin masifaffen so ya azawa sultana,bama shi kadai ba kusan kowa na cikin gidan,yana ji a ransa kamar yanzun sultana responsibility nasa ce,kamar shike da alhakin komai nata. Rasuwar nafessa da samuwar sultana ya sanyashi ajjiye karatunsa ya dawo gida nijer. A hannunsa sultana ta taso,ya zama shine uwa kuma shine uba a gareta,tsarkin kashi wanka raino rashin lafiyarta dama walwalarta dukka na hannun maina. Maina ta budi idanu ta gani a matsayin uwarta kuma ubanta tun gabanin ma hamani da hamma mohmoud din suma subi bayan nafessa sanadiyyar hatsarin motar da suka samu shi da shi a hanyarsu ta dawowa daga ziyarar kabarin nafessa din. Wannan maraicin da sultana ta sake tsunduma ya sake ninka soyayyarta,ya kuma sanyashi sake ninka kulawarsa ninkim baninkin a kan sultana,ya ajjiye karatunsa gaba daya saboda ita,wasu abubuwan tun bai iya ba har ya qware sosai,hatta jakar goyon sultana yana da ita,yadda yarinyar ta taso tana qulafucinsa sai ya masa kamanceceniya da mahaifiyarta. Ta dabance sultana cikin gidan kamar yadda komai nata ya zama na daban,tana da farinjinin da kowa ya shigo sai ya dauketa ko ya tankata,tana da yawan surutu tun shekarunta suna qananu ainun,tana da kazar kazar irin ta masu cikakken lafiya.

Halasci da sadaukarwar mohmoud ba abune qanqani ba da zaiyi saurin bacewa zukatansu ba,ba qaramin abu bane da zaiyi saurin shafewa a rayuwarsu ba,a wajen aba hamma mohmoud din uba ne wanda yayi masa komai a rayuwa,bashi da abinda zai saka masa dashi face ya bawa jininsa qwaya daya tal da ya bari a duniya dukkan soyayya qauna da kulawa,wannan ta sanya ya fifita sultana akan kowa cikin gidan,buqatarta ta zama gaba akan buqatar kowa.

Ya koma makaranta a nan maradi amma saboda hankalinsa nakan rainon sultana sai karatun nasa ya zamana asha ruwan tsuntsaye ne,yaqi ya maida hankalinsa duk da karatunsa karatu ne me tsada da wahalar samu,yake kuma da buqatar maida hankali akai. Aba da kansa da ya fahimci muddin yana tare dasu ba karatun zaiyi ba,sai ya maidashi niamy,ya tafi kuma da sharadin sai yayi shekara cur aba yaga kamun ludayin karatunsa sannan zai barshi ya fara zuwa gida weekend. Itadai ama bata tanka ba,don zuwa sannan ta zama 'yar don't care game da komai na cikin gidan,ba komai take sanya baki ba duk da dama ba halinta bane shishshigi,sa'annan har kawo yau aba zafinta yakeji akan hana auren maina da nafessa. Dukka tulin soyayya da suke nunawa sultana bataga aibu ba,don sultana din jinin mohmoud ce, MAHMOUD kuma abun asoshi ne,ko ita yana daya daga cikin mutane masu muhimmanci cikin rayuwarta,abu daya ne ta dinga jiye musu wanda a yanzun ya riskesu,sangarcewa da lalacewar tarbiyyar da maina keta fadi tashin ganin tafi kowanne yaro cikin gidan,abinda ta dinga gane musu kenan,amma taja bakinta tayi shuru don tasan ba muhallin da zatayi magana bane,don ba lallai su fahimceta ba. Kaf yaran gidan ita kanta sultana din tafi shiga ranta,tana tausayinta saboda maraicin da take ciki ta kowacce fuska,amma hakanan ta barma ranta hakan saboda a qalla dai a samu wanda koda da kallo zaya nuna mata kuskure idan ta aiwatar cikin gidan,sannan ba lallai su gamsu da ita ba wai don ta nuna tana qaunarta,duk da cewa tasan kusan komai ya riga ya wuce,family ne da basa da riqo sam sam sam,daya daga cikin halayensu dake burgeta.

Sanda ya cika shekara ya fara zuwa gidan bai fahimta wani sauyi sosai daga gareta ba. Saidai bahaushe yace sannu sannu hata hana zuwa saidai a dade ba'a je ba, shekara guda da fara zuwan nasa ya karanci komai,hankalinsa ya dagu sosai,yayi iya bakin dukka qoqarinsa wajen saita komai amma inaaaa......wannan shine ya zama SILA kuma SANADIN KADDARAR data samesu a yanzu.........KADDARAR da zata budewa SULTANA da MAINA qofofi masu tarin yawa.....

_Barkanmu da sauka😄,muje zuwa guwa ga tsakiyar labarin_🤩

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 09


Numfashi me nauyi ama ta aje tana sake murza tafin hannun sulatana dake tsakiyar hannunta wanda ya sake yayi laushi sosai

"Ya hayyu ya qayyumu birahmtika astageesu" ta furta qasa qasa tana lumshe idanuwanta. Batasan me qaddara ta tanadarwa gobensu ba gaba daya,saidai ko meye tana fatan yazo ya wuce sa gaggawa,ko meye kuma tana fatan yazo ya wuce musu cikin sauqi.

Hannunta ta saje miqawa ta jawo wayarta tana sake lalubar number wayar maina,har yanzu akwai dacinsa da ciwonsa qasan zuciyarta,tana sake jaddadawa kanta da gayawa kanta ba zata masa ta sauqi ba,ba zata kuma sassauta masa ba dole tayi masa mafi munin hukunci,saboda ba haka takeso ya rayu da nashi iyalin ba,ba haka takeso ya soma gina rayuwarsa data zuri'arsa ba,tana da buqatar tsatso me kyau wankakke daga wajensa tamkar yadda ahali da salsalar mahaifinsa suka kasance.

Babu wani abu da ya canza,har yanzu dai gaya mata akeyi wayar na a kashe ne. Furzar da iska tayi daga bakinta tana sake gayawa kanta duk nisan kiwon da yayi zaije ya dawo ya sameta.

Sai data duba lokaci taga yadda dare yaketa sake nisa sannan ta fidda hannunta daga na sultana,ta miqe ta zare yalwataccen mayafinta da kowanne motsi yake fidda qasaitaccen qamshi. Toilet ta shiga ta dauro alwala don batajin zata iya samun bacci,ta shimfida darduma ta tada salla.

Raka'a shida tayi ta sallame,ta bude ipad dinta tana buda app na qur'ani cikin nutsuwa ta soma karantawa ko zuciyarta zatayi sanyi daga abinda takeji.

Duk bayan kowannw minti sai ta aza idanunta akan sultana da har yanzu jiya iyau. Tayi nisa takai gwargwadon izifi biyu ta sake dora idanunta akan sultana,sai taga hannunta da qafafunta suna wani irin motsi kamar ana jijjigasu.

Da hanzari ta aje qur'anin ta kuma miqe tana nufarta da sassarfa,dab da zata isa inda take sultana din ta soma fusge fusge kamar wadda aljanu suka yiwa mummunan kamu,kafin daga bisani ihu ya biyo baya da dakusashiyar muryarta data fara budewa. Gaba daya gigicewa ama tayi da irin abinda taga sultana din tanayi,sosai take jijjiga tana kuma ihu tare da kiran sunan maina kaika dauka wasu gaggan mayu ne suka kamata. Rungumeta tayi sosai a jikinta gudun kada ta farke dinkin jikinta ko ta jiwa kanta rauni,tana rungume da ita din tana kiran sunanta,saidai bisa dukkan alamu bata fahimtar ma abinda takeyi bare wanda ke kusa da ita,abinda ya sanya hawayen tsananin tausayinta ya sauka a idanun ama. Tanason ta matsa gaban abun kira ta kirayi nurses amma tana tsoron sakin sultana din,cikin taimakon Allah kamar Dr chafa'atou tasan halin da ake ciki sai gata ta turo qofar dakin ita da Dr cha'aibou.

Hannuwanta dake cikin aljihun labcoat dinta ta zare tana nufosu da gaggawa

"Ta farka ne?" Ta tambayi ama tana tayata riqe sultana

"Ta farka Dr amma a mafi munin yanayi" ta bata amsa tana qoqarin dauke qwallar data sauka saman idanunta. Dr cha'aibou ta yiwa magana ya qaraso ta sanyashi ya duba allura cikin drawer din da suka ajjiye dukka tarkacen allura ruwa da magungunan da sukasan ciwonta yana da buqata.

Shi ya hada allurar ya kuma yi mata. A hankali sai yanayinta ya fara daidaita,saidai kuma dukka jikinta ya fara sakewa,kafin daga bisani ta sake komawa wani baccin.

Shuru dakin ya dauka idanunsu dukka a kanta,kafin daga bisani Dr chafa'atou ta furzar da iska tana maida dubanta ga ama

"Dole zata hadu da attack dama irin wanda aka yiwa rape suke haduwa dashi,saboda wannan abun da akayi matan kusan daidai yake da rape a tunani da kuma qwaqwalwarta,tunda anyi shine bisa qarfi da tilastawa,kwanyarta sam batasan meye sahihin ma'anar aure ba bare ta banbance,amma in sha Allah ina saka ran idan ta sake farkawa zata farka babu dukka wadannan abubuwan,ki kula da kyau don ba dogon bacci zatayi kamar irin wannan data fark daga shi ba,ko na turo miki nurse hajja ta tayaki zama?" Kai ama ta girgiza a sanyaye,bata buqatar kowa ya tayata tunkarar wannan,bata da buqatar wani ya aboceta cikin wannan lamarin,tanason ta tunkari komai ita daya da zuciya da gangar jiki irin ta UWA.

Tunda Dr chafa'atou ta fadi haka ta tattara ta dawo gaban gadon ta tare,qarfe biyu qarfe uku qarfe hudu dukka saman idanunta suka wuce,bacci ko gezau baibi ta kusa da ita ba bare ya gwada daukarta,har zuwa sanda sanyin dake bayyana gabatowar asuba ya soma busawa,a sannan sultana din ta fara bude idanunta a karo na biyu,wannan lokacin cikin nutsuwa,saidai kuma tana jin dukka jikinta wani iri babu dadi,sannan daya idon nata kuma yaqi bude mata da kyau yadda takeso. Jin hakan ya sanyata daga hannu da niyyar shafa fuskar taji me ya hanawa idon nata budewa da ganin abu da kyau. Riqe hannun nata ama tayi da sauri tana fadin

"Bari karki goce qarin ruwan" a nutse ta waiwayo gefanta,idanunta suka sauka kan fuskar ama din,a hankali kwanyarta ta fara tuna mata abinda ya faru da ita na qarshe. Tunanin da ya sake hargitsata karon farko cikin hayyacinta,sai wani irin nannauyan kuka me sauti ya kufce mata.

Tana iya tuna sanda maina ya tsiraitata ya yage kowanne tufafi dake jikinta,tana iya tuna sanda hannuwansa ke kaiwa guraren da ita kanta tana kyautata zaton ma qilan bata taba tabawa ba,tana iya tuna sanda lokacin da ya sadar da kansa da wajen da ko kallonsa bata yi duk da a jikinta yake......wani kukan ya sake qwace mata me matuqar sauti fiye dana baya,sai dukka wani qarfin hali da qwarin gwiwar ama ya kwaranye,ta rungume sultana din sosai a jikinta tana lallashinta.

Sun jima a haka kafin kukan nata ya ragu,sai ta koma sauke ajiyar zuciya kafin ta bude bakinta cikin hardewar harshe tace

"Ruwa" sakinta ama tayi ta bude carton din ruwan dake aje gefe ta ciro guda daya ta hado da glass cup din da aka shirya a wata qaramar cabinet a dakin. Ajjiuesu tayi a gefe sannan ta fara qoqarin tadata zaune don taji dadin shan ruwa. Siririyar qara sultana ta saki tana runtse ido saboda azabar da taji na ratsata,kowacce gaba ta jikinta ciwo takeyi mata

"Sannu,daure kisha ruwan sai na saka ruwan dumi na gasa miki jikinki ko?" Ama ta fadi a tausashe tana kallon qwayar idanun sultana cikin matuqar tausayin ta shigo stage din da bai kamata ce ta shigo shi ba.

Tana qananun qwalla tana komai ama ta tada ta,ta zuba mata ruwan ta shanye ta kuma sake buqatar wani,haka ta dinga zuba mata tana shanyewa har sai da tasha rabin gorar sannan tace ta qoshi.

Da kanta ama ta tara ruwa me dumi qwarai ta dawo cikin dakin

"Muje ki wanke jikinki ko zakiji dadi" a hankali sultana ta kauda kanta gefe kadan tana jin zuciyarta kamar zata fashe,ganin ama kawai tuna mata yake da maina da abinda ya aikata mata,wai shin ta yaya zata iya ci gaba da kallon ama?,ta yaya zata iya tubewa ama jikinta tayi mata wanka?. Mutum biyu rak a rayuwarta suke mata hakan,daga bibi sai tanja,batajin akwai sakewa tsakaninta da ama da har hakan zata kasance

"Ina bibi ta?" Ta tambaya cikin rauni ba tare data Kali ama ba

"Suna gida,dare yayi yanzunma asuba ce,amma goben nasan da sassafe zaki ganta"

"Zata yimin idan tazo" tace da ama tana jin kamar harshenta take yanka a duk sanda ta buda baki tayi magana,saboda sam sam a yanzun furta kowacce kalma ta daina bata sha'awa,tafi sha'awar kurumtaka da bebantaka akan komai,batason jin duk wani sauti ko kuma kalma bare ta tuna mata da ALIYYU MAINA.

Tsaiwa ama tayi kawai tana nazarinta,har yanzu taqi waiwayowa bare ta dubeta,sai ta taka a hankali ta isa sashen data maida kanta ta zauna,ta jawo hannunta ta saka cikin nata

"Sultana?" Ta kirata kiran da ya ratsa mata jiki,ta kuma daga kumburarrun idanunta da dayan bai iya gani da kyau ta kalli ama sannan ta maida dubanta qasa

"Inason ki daukeni daga yau a matsayin bintou mahaifiyarki da baki santa ba,inaso daga yau ki sanya a ranki ni ba babar maina bace,ban haifi d'a aliyyu ba,ke kadai na haifa,zaki iya daukata a matsayin mamarki da zaki iya gayawa dukka damuwarki?" Kiran sunan maina din ya saukar mata da wani zafi daga zuciyarta,amma kuma data dubi ama saita tuna cewar.......matar bata taba takura mata ba,bata taba shiga huruminta ba bare ta dameta ko ta hantareta cikin gidan yadda sauran matan kawunnanta suke mata,bata taba mata wata mummunar magana ba,hasalima ko meye zatayi ba ita cikin masu yi mata caaa. Abinda kuma ta gani idanun ama din a sannan yayi kama da abinda d'a yake gani cikin idanun mahaifiya,haka kawai taji wata nutsuwa ta saukar mata tattare da ama din,bata daice mata komai ba,amma kuma bata sake musawa ba,ta kamata ta kaita bandakin ta kuma fara yi mata dukkan wani abu da tasan zai sanya taji dadi cikin jikinta,cikin hikima kuma tana shaida mata ciwukan dake jikinta don kada tayi wani abu me qarfi da zai kawo matsala a wajen.

Abun yayi mugun yi mata banbarakwai tare da daure mata kai,dinki a wajen hanyar fitsarinta?, tabbas kasheta kawai maina yaso yi,bata taba gani ko jin an dinke wajen ba,sai qwalla ta cika mata idanu ta kuma ga gangaro tabi ta saman kuncinta ta hade da ruwan wankan dake a jikinta,dama koda ama bata gaya mata ba tasan wajen ba lafiya yake ba,don ita kadai tasan yadda taji gurin yayi mata,tanajin kamar ba'a jikinta yake ba,zallar radadi da zugin da yake mata ne kadai yake tabbatar mata a jikinta har yanzu yake.

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba

Please Login or Register in order to submit comment