Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abubuwa da suka shafi channel din da take sanya ran farawa aiki tare da dakon jiran shigowarsu. A qalla yanzun sun fara girma,shekara hudu cikin ta biyar ai sun san gabas sunsan yamma,ba zata barsu haka siddan su dinga zuwa waje me alfarma irin wannan ba tare da sunsan muhimmancinsa ba. Har ta gama jiran bacci ya saceta basu dawo ba,basu hadu ba sai data tashi sallar asuba,sai data kammala tata sallar sannan ta tashesu sukayi tasu,ta ritsasu tana tambayarsu me ya zaunar dasu jiya?.

Inda inda suka fara mata,daga qarshe batoul ta sanya kuka, benazeer ce me bada haquri,ta musu kashedi sosai,wanda tana tsaka da yin ama ta shigo.

Dariya ta dinga yi ciki ciki,ita tunda take bata taba ganin alaqar uwa da d'a irin ta sultana ba,gaba daya ta zame musu wata senior master bawai mummy ba. Da ama tabi ba'asi sultana ta gaya mata,sai ama taqi bin bayansu

"Eh da gaskiyar auntynmu,daga yau a dinga qoqarin zuwa masjid kunji ko?,amma kuma auty ayi mana afuwa,a dinga tafiya daga baya zamu taho tunda munsan wajen kuma bamu da nisa,munyi alqawarin ba zamu sake zama daki ba,idan kuma mukace mun gaji a barmu mu dawo daki mu huta" ama ta fada tana hada hannayenta waje guda. Murmushi ne ya subucewa sultana hadi da nauyin ama,saita kada kai kawai,ama dai ta samu ta kwashe 'yan jikokinta suka fice hawaye shabe shabe.

Tun daga ranar kuwa basu saba alqawari ba,kamar wasu manyan 'yammata,koda ta tafi zasu biyo bayanta,saidai kuma sai sun gama qailularsu,siye siyen chocolate da fadace fadacensu na tsakanin sako da sako.

Satinsu guda kacal bibi itama ta iso,sukayi jiranta ta gama nata ibadar suka wuce makka.


*_makka_*

*_Al_ajyad street_*

*_SWISSOTEL HOTEL MAKKA_*


Kai tsaye motar kamfanin dake da alhakin tarbarsa ta wuce dashi swissotel,wanda kusan duk sanda ya shigo garin makka din bashi da hotel din da ya wuce wannan,hotel ne da yake jin dadin zama cikinsa sosai,saboda daga nan yana iya hangen haram tarwai,har wasu lokuta idan yayi tsaye daga bakin window din dakinsa yakan yi addu'o'i sosai kafin ya sake labule ya wuce.

VIp suite suka bashi saboda cancantarsa da cab din,aka tabbatar da shigar da jakarsa ciki,da kuma tambayar abinda yake da buqata suka gabatar masa sannan suka danqa masa dakin a hannunsa.

A nutse yake cire lallausar rigar saman kayan jikinsa,daya daga cikin shigar 'yan qasar hindu,riga ce me wando da top dinta qarama me budadden gaba,wadda an saqata ne da yadin zaren vicuna mai matuqar daraja da tsada. Da baya ya zauna saman sofa din dake dakin yana lumshe idanunsa,kanshi yana kallon sama yana furzar da numfashi da kadan da kadan ta cikin bakinsa da wata iska me zafi.

Wata nutsuwa ke zagayashi,a duk sanda ya tsinci kansa cikin qasar sai ya dinga jin zuciya da qirjinsa wasai,saidai kuma hakan baya hanashi jin wani abu a jikinsa,irin jin da me nauyin laifi saman kansa yakanji a duk sanda ya gujewa laifinsa da ya aikata. Tsahon shekaru yana jin wannan abun a dukka wani motsi ko tattaki na rayuwarsa,ko sau daya koda na minti daya zuciya ruhi da kuma gangar jikinsa basu taba samun hutu ba game da hakan,a haka ya rayu.......darare da yawa bacci yana qauracewa idanunsa......lokutta da yawa yana sarayar da baccinsa ya zauna dangwargwar,sautukanta......furucinta da lafazzanta suna dawo masa sabbi fil cikin kansa..... zuciyarsa na tuhumarsa,tana sake maimaita tuhumrsa,me yasa?......don me ya gaza kai zuciyarsa nesa?,don me yasa ya kasa haquri ya dauke kai?,me yasa ta gaza cin albarkacin nafessa?,ya cika alqawari?,yayi abinda ya dace?,a yau inda nafessa zata dawo duniya zaya iya fuskantarta?. Bai sani ba shima.....baisan me yahau kansa ba,baisan me ya fusgeshi ba......kawai yaji har cikin ransa ya aikata,hakan kima shine dai dai.....shi zai sanyata nutsuwa,shi zai zama mafarin lanqwasuwarta da shigarta taitayinta. To ashe dukka yayi bahaguwar fahimta,ashe muqulli ya sanya zai kuma bude musu sabbin shafuka da qofofin qaddara masau tsauri da nisan zango irin wannan.

Sai daya samu nutsuwa gabbansa suka huta sannan ya bude idanun nasa yana duban agogon dake manne a bango, mintuna qalilan suka rage a tayar da sallar isha'i,kuma yana da matuqar muradin samun sallar cikin jam'i,kamar yadda duk tsanani ko wuya ko a ina yake baya barin jam'in kowacce sallah ya WUCESHI,musamman asuba da isha'i saboda falala dake cikinsu.

Kayan jikinsa ya fara ragewa,yana cirewar yana jin yadda wayarsa ke qugi. Baiyi koda attempting din tabata ba,saboda yaga wacece me kiran,yasan kuma ba Wanda ya shaida mata ya tabo nan din sai suhail,yanzun kuma ba lokacin wasa ko lokacin bata lokaci bane,duk da dama can ya bawa wajen muhimmanci me tarin yawa cikin rayuwarsa,da har baya iya daukan lokaci baizo ba,to amma yanzun buqatu gareshi masu nauyi,wani babban aiki ne a gabansa da yake da buqatar jajircewa yayi addu'a da kyau.

Cikin kayansa ya fidda bathrobe ya rataya sannan ya wuce toilet abinsa.

A gaggauce suka iso swissotel suka kuma gama komai suka karba maqullan dakuna guda biyu kamar yadda suka saba,daya na ama da aba,daya kuma nata da su benazeer da bibi,don haka classic room suka dauka me gadaje uku.

Suna shiga ta duba lokaci,sannan ta sake duba babban agogon nan dake garin makka. Lokacin isha'i ya kusa yi,don haka a gaggauce ta cire kayanta don watsa ruwa,tanason a qalla takai tsakiyar dare gaban ka'aba,akwai tarin buqatu da take dasu,ta kuma tabbatar tayi imani tare da yaqinin amsasu a wajen kamar yankan wuqa yake,ba wata addu'a da tayi bataga karbuwarta ba,a yanxun ma tazo da kukan yankewar igiyar aure da tayi saura tsakaninta da maina,don bata da qwarin gwiwar sake fuskantar su aba da zan can. Tun tana kasa kunnuwa taji aba din ya nemeta harta fidda rai,kullum zancan yana a ranta,saboda xuwa yanzun tasan girma da nauyin igiyar dake kanta tsahon shekarun........

"Ku gama abinda kukeyi da wuri,da minti goma yau zan rigaku fita" ta fada tana daga musu yatsunta gami da shigewa toilet din,sai bibi ta bita da kallo tana kama baki,abun mamaki wai yau sultana ce da tsantseni da tsananta tarbiyya

"Yar nema,kina kamarsu ma sanda kike zuwa daki kike kwance abinki har muje mu dawo kina bacci shine yanzun da wanan sirisirin hannuwan naki kike irga musu lokaci" qaramar dariya ta saki tana tsaka da brush,don fes taji abinda bibin ta fada. Itakam ta karanceta irin mutanen dake son jikoki da yayan jikoki ne fiye ma da yadda sukewa yaransu da suka haifa soyayya

"Allah yabar mana ke bibi" ta fada qasa qasa tana tuna wasu lokuta na quruciyarta can shekarun baya murmushi ya sake subuce mata

"Ba abinda bashi da iyaka sai ikon Allah" ta fadi a ranta

*_KACIBUS..........😂INJI HAUSAWA DON BANA QARASA BA,SAI NACE KUZO MUJE*_ 🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️



*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 45


Sun dudduba benazeer sun kuma tabbatar masa ba komai,don dama faduwar ba wata babbar faduwa bace. Dariya ta dinga yima maina

"Uncle......wai tsoro kaji?,banji ciwon komai bafa,faduwar ma kuma babu zafi" ta fadi tana dariya gami da tafa hannuwa. Idanunsa shidai carrr a kanta,sai ya saki qaramin murmushi sannan cikin tsokana yace

"Na ganki 'yar lukuta ne,kuma lukutaye basu da qarfi,sannan ma ance mutum idan ya cika fari shima bashi da qwari wai" ya qarashe fadi yana dan tabe baki kaman zai saki kuka yadda yara qanana sukeyi. Wannan karon har batoul sai data qyalqyale da dariya,sai shima ya biye musu yana tayasu,suka amsa receipt suka fito daga pharmacy din.

Shagunan ice cream ya nufa dasu,yaja kujera kawai yayi zamanshi abunsa kamar wanda bashi da sauran aikin yi yace su duba duk wanda sukeso. Aifa benazeer an samu abunyi,duk bayan daqiqa sai ya waiwayo ta dubeshi

"Uncle a sakamin banana flavor?"

"Eh a saka miki" sai ya amsata yana murmushi,bayan wata daqiqar saita waiwayo tace

"Uncle vanilla fa?" Sai ya sake murmushi yace

" A baki" at last ya fahimci sun saba da shansa ne,kuma suna sonsa sosai don haka yace da ma'aikacin wajen

"A musu takeaway na dukka flavours din da suke dasu". Murna ya kama benazeer harda qaramar rawa,shikam yana zaune tamkar wanda ya samu tv dake bashi nishadi.

Duk yadda suka sake dinnan dashi abinda ya bashi mamaki,qememe wani sukaqi bin wani balare da yace musu shagon gabansu zai siya musu gift na Pizza. Suka hau kallon kallo gami da maqale kafada suna kuma satan kallon maina din. Dariya suka bashi suka kuma burgeshi qwarai,dole sai nan ya siya ya kawo musu,a nan dinma maina ne yace su ansa,saboda yasan wajen wajene mai aminci,ba wani abu na cutarwa ko me cutarwa da zaiyi tasiri a wajen.

Shi ya riqo musu ledan suka qarasa haram sukayi sallah tare dasu bayan kowacce ta gyara mayafin abayarta,ya dinga dariya sanda suke gardama tsakanin benazeer da batoul,ita batoul tace lallai sai benazeer ta sauya alwala saboda ta fadi,kuma ma tayi surutu da yawa,itama kuma ta dage kai da fata alwalarta ba abinda tayi,da qyar ya raba gardamar.

Kiran wayarsa da akayi ya sanyashi miqewa don ya matsa gaba kadan ya amsa wayar saboda wajen da sukayi sallar yana ganin bai kyautu ya daga wajen ba. Yana Allah Allah yacemusu su tsaya ya maidasu masaukinsu amma number dake kiransa din tana da matuqar kima da martaba a wajensa,don haka ya taka a hankali yana qoqarin dagawa.

Kallon benazeer batoul tayi tana miqewa

"Mun dade B,nidai tafiya zanyi,kya taho"

"Bamu yiwa uncle sallama ba" ta fada cikin yanayin damuwa tana kallon hanyar da yabi

"Gobe sai muyi masa" ta bata amsa tana sanya takalmanta. Miqewa benazeer din tayi tana yarda da maganarta,suka gama sakawa suka dauki ledarsu sukayi hanyar da zata sadasu da swissotel hotel.

Sassanyan turarenta ta feshe jikinta dashi bayan ta kammala sanya rigar baccin me taushi da rashin nauyi,ta maida turaren ta ajjiye tana satar kallon bibi dake kwance tana kallon tv. Daga kai tayi sai suka hada ido da sultana

"Wai ina yarannan ne suka tsaya haka?" Bibi ta fadi tambayar kuma data yiwa sultana din dadi kenan. Abinda taketa lissafawa kenan cikin zuciyarta,sun dade fin yadda suka saba,duk da dama shiriritarsu yawa ne da ita amma basa kaiwa haka basu dawo ba.

"Ban sani ba bibi,hala shiriritarsu suka tsaya" ta amsa mata cikin basarwa tana ninke abayar data cire

"Ke kinga banson kidifirin banza....sanya jilbab dinki ki bisu,don kunga waje amintacce ne kunsan ba abinda zai faru dasu amma ai yana da kyau a dinga bibiyarsu ko?" Bata musa ba ta miqe ta saka hijab din nata,don dama abinda takeso tason yi kenan,kunya da kawaici ya hanata. Bata taba tsammanin akwai yaran cikun zuciyarta da rayuwarta gaba daya ba sai yanzu.

"B fuskar uncle fa kamar ba santa Allah" benazeer ta fadi tana yamutse fuska irin na yara masu surutu da shegen wayo. Harara batoul ta balla mata tana tura baki gaba

"A'ina kika sanshi,yau muka fara ganinsa fa,kuma Allah duk sai na gayawa auty da ama abinda kika dinga yi" ido ta zaro tana kallon batoul din

"Me kuma nayi?"

"Ba an hanaki surutu da kula wanda baki sani ba,shine kiketa bashi labarin school enmu ko da fada masa sunayenmu"

"Kuma daga wannan shine zakice zaki gayawa aunty?,don Allah B kinji kada ki fada,kinga uncle ai yana da mutunci,kuma ai don ya bugeni ne na kulashi,bazamu sake ma ganinsa ba inajin tunda bamusan ina yake ba"

"Sai an fada din" ta fada tana murguda baki tare da fitowa daga elevator din bayan ya tsaya a floor dinsu benazeer ta biyo bayanta tana magiya.

"Meye ake cewa kada a fada?" Suka tsinci muryar sultana dake qoqarin shiga elevator ta fasa saboda ganinsu.

Tsuru tsuru dukkansu sukayi,sai kuma suka hau kallon kallo. Idanunta ta zuba musu sosai yadda ta saba musu duk sanda takeson gano laifi ko gaskiyarsu,a hankali kuma ta maida dubanta ga ledar hannunsu

"Daga ina kuke?,waye ya baku wannan kuma?" Tayi furucin tana nuna ledar

"Uncle haidar ne" benazeer ta furta da shagwababbiyar muryar nan tasu data cakuda da sauti na tsoro.

"Uncle haidar?,waye haidar kuma.?" Ta tambayesu gabanta na wani irin faduwa,sunaye ukun nan a duniya,duk lokacin da zata jisu sai sun barwa zuciyarta razani ALIYYU HAIDAR MAINA.

"Mun taho masallaci na siya ice cream dina ya bugeni ya zube,shine ya kaini pharmacy aka dubani ya kuma siyo mana wannan" yadda suka tsorata ya sanya ta sassauto

"Da nace kada a siyoshi sai anyi sallah shine bakuji ba?,ku wuce ku bani waje" ta fadi a dan fadace. Da sauri sauri har suna rige rigen wuceta a tsakaninsu suka bar wajen,tana nan tsaye sai data tabbatar sun shiga dakin sannan murmushi ya qwace mata. Tabbas idan bakayi da gaske ba yaran saisu maidaka wani abun wasansu.

Kudin hannunta ta duba,akwai abinda takeson sauka qasa ta siya itama,don haka ta matsa gaban elevator din tana yunqurin kiranshi, saidai ta nuna mata akwai mutum ciki dake haurowa saman,wannan ya sanya ta tsaya daga gefe tana danna wayarta tana jiran isowarshi.

Kansa yana qasa,shima kuma wayar yake dannawa,a haka ya fito itama idanun nata nakan waya ta sanya kai ciki. Lokacin da suke gifta juna......iskar data debo kowa ta bugi dan uwansa har cikin jini da jijiyoyinsu sai da sukaji wani irin yanayi. Turarensa shi ya fara bugar da ita ya kuma haifar mata da qaqqarfar faduwar gaban data fusgi hankalinta,ta kuma kawar da hankalin nata daga kan waya,ta daga kanta tana duban bayansa......yana takawa ne a hankali kamar bayasin taka qasar,tsayyayen namiji me cikakkiyar siffa da zati,kwantacciyar sumarsa dinnan na kwance luf daga qeyarsa da take iya hangowa, dogayen hannayensa dake dauke da wasu veins kawai take iya hangowa,ta zubama bayan nashi idanu tana jin mahaukacin bugun da zuciyarta keyi irin wanda bata taba ji tayi irinsa ba,tilas ta yiwa kanta da kanta tambayar a fili yadda iya labbanta ne kawai suka motsa

"Waye wannan?" Ta furta idanunta bisa bayan nasa. Tayi imani ba'a banza zuciyarta ke wannan bugun ba,tayi yaqinin koma waye akwai wani abu me qarfi tsakaninsu,tabbas!!!!..... zuciyarta ba zatayi wannan bugun da ya sabawa qa'ida ba muddin ba wani abu mummuna ke shirin faruwa da ita ba,wanda wannan tunanin ya sake haukata bugun zuciyarta.

Shi kansa yasan ya danyi nisan tazarar taku tsakaninsa da elevator din yana replying saqon da ya zame masa kaman dole ne ya amsa din bawai don yana so ba.......amma cikin kowanne jini dake harbawa jikinsa wani abu yaji yana bibiye da harbawar tasa zuwa qwaqwalwa da zuciyarsa. Cikin jikinsa yaji kamar akwai wasu idanuwa masu kaifin gaske dake kallonsa,akwai wani dake bibiye dashi daga bayansa,wannan ya sanya ya juyo a hankali zuwa saitin elevator din,daidai sanda ta gaji da barin kanta da kanta a hangame ta soma rufe kanta.

Cikin idanuwanta idanunsa suka fada,haduwar idanuwa hudun da suka bada wani gigitaccen yanayi cikin zukata da qwaqwalensu. Dukkaninsu jinsu sukayi kamar daga wata duniya suka fado kwatsam ba tare da kowannensu ya shirya ba,babu wani dake iya cikakken motsi bare yunqurin janye idanunsa tsakanin shi da ita,har sai da qofar ta fara motsawa zata rufe din. Kamar wani magnet ya jashi haka yaji,ya fara takawa da wani irin sassarfa da hanzari yana nufar elevator din.

Ruf ta rufe kanta kafin yakai ga isa,yana miqa hannu kuma ta fara sauka qasa dauke da sultana wadda ta kama qarfen jikin elevator din kam ta riqe gudun kada takai ga faduwa,saidai kuma duk da hakan zuciyarta da ruhinta dukka sun gaza samar mata da qarfin da zaya iya riqeta a tsayen,dole ta sulale a hankali cikin elevator din ta zauna dirshan tana jin kamar tana shirin fita a hayyacinta ne.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 46


Da sauri ya lalubi wani elevator din,ya kuwa samu a kurkusa dashi,ya iso ya shige,saidai ya kasa tsaiwa waje daya,yana jin kamar dakin ba tafiya yakeyi dasu ba,kamar a tsaye yake cak waje daya,cikin qwaqwalarsa wani abu ke masa yawo kaman ana yamutsata.

Cancan nesa da hotel din nasu ta kai kanta,wani mayalwacin guri da babu kowa sai haske da tsirrai da aka qawata wajen dashi. Sulalewa tayi agun,ba ruwanta da wai a qasa take,ta zuba dukka hannuwanta saman fuskarta tana qoqarin maido da numfashinta daidai.

Kokawa tsakaninta da zuciyarta ruhi da kuma numfashinta,tsahon wasu mintuna masu yawa kafin ta samu numfashin ya dai daita a qirjinta

"Maina na gani?,haidar?,Aliyyu?,da gaske yana rayen kenan kamar yadda goumar yasha gaya mata?.......kenan hakan yana nufin watan watarana zai dawo zuwa cikin rayuwarsu?,ama tasan yana raye?,yana kuma kusa dasu?,aba fa?" Tambayoyin da sukayi mata tsaiwar mashi aka kenan,saidai daga bisani zuciyar ta bata tabbacin

"Basu sani ba!,duka tambayarki amsarsu basu sani ba" kanta ta sanya tsakanin cinyoyinta,sai taji kawai babu abinda take sha'awar yi irin kuka,kuka data jima da ajeshi cikin rayuwarta,ta tattara duk wani koke koke tun daga sanda ta soma hankali cikin hassan Ibrahim gwarzo ta ajjiye ayau shi ya dawo mata sabo fil,ta sakeshi a hankali ya soma fita da wani zazzafan tsohon miki.

Daga cikin swissotel tun daga first floor zuwa floor na qarshe baisan adadin sau nawa ya duba ba,daga nan ya sake maida qafafunsa zuwa cikin haram bayan zuciyarsa ta gaya masa ta tafi tayi addu'a,ya zagaye haram har qafafunsa suka soma gaya masa tafiyar ta soma yawa akan wadda ya saba yi.

Duk wani tunaninsa ya kulle,abinda kawai yake iya tunawa sultana ya gani,kuma ita yakeson ya lalubo,baiji gajiyar zaryar da yakeyi ba har sai da zuciyarsa ta ladabtar da dukka gabansa,ya sulale ya samu waje cikin reception din gaba ya zauna bayan ya shafe awanni yana abu daya.

Wayarsa kawai ya sake zarowa,ya lalubi number yayi kira. Cikin nauyin bacci suhail ya daga kiran ya saka a kunnensa

"I thought kayi bacci tun tuni,ko murnar ganin dream twins dinka ya hanaka?" Idonsa ya lumshe yana jin bugawar da zuciyarsa takeyi,shi kam ya manta ma da batun yaga yaran,abinda ya gani yanzun duka ya shafe wannan

"Inason kayima mutanen nan magana,nijer da Nigeria duka nakeson shiga,banzan ainihin inda zan sameta ba,a rage lokacin da aka dibamin,bazan iya kaiwa har sannan ba.......next week zan bar nan".

Duka zantukan sai suhail ya kasa ganesu,don baisan komai akan abinda maina ke magana ba

"Wacece zaka samo?,me zakayi a nijer kuma?"

"Kayi yadda nace please,ayi arranging komai saboda idan na shiga bansan ranar fitowa ta ba sai Allah" yayi furucin duk wani qarfin gwiwa da yake tunanin zai samu yana narkewa daga zuciyarsa

"Are u okay maina?"

"Yes iam" ya bashi amsar dashi kansa yasan ba ita bace haqiqanin gaskiyar yana zare wayar daga kunnensa,sai kawai ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing,idanunsa naci gaba da bibiyar kai kawon mutane cikin wajen,yana jin kamar ya tabbata a wajen har sai ya gano ainihin location nata.

Maida dubansa yayi ga ma'aikatan dake wajen,yayi imanin da zai bincika akwai komai nasu cikin hotel din muddin a nan din ta sauka,to amma bashi da yaqinin daga ina take?,ina ta tafi?,wajen wasu tazo?,duka bai samu wannan information din ba. Number goumar da ya rasa shine mafi girman rashi da yayi a wancan shekarar,ya daina jin komai,komai ya yanke,baisan kuma ta yaya zai sake samo wani abu da zai sadashi da goumar din ba. Abune me wahala su bada information na wani room,ba zasu bada ba,hasalima zai sanya sunyi zarginsa da wani abu. Wannan tunanin ya sakashi qarasa debe duk wani tsammani nasa,ya maida idanunsa ya lumshe,sai ya dinga jin sunayen Allah na zuwa kanshi. Fara maimaitasu yayi daya bayan daya,yana yi a hankali yana samun nutsuwar zuciya da kuma ta ruhi.

Sosai taji yadda idanunta sukayi nauyi suke mata kuma mahaukacin radadi,ko da bata duba ba tasan sunyi kumburin da duk wanda ya kalleta zai fahimci kuka tayi ba na wasa ba.

"Ya hayyu......ya qayyumu..... birahmtika astageesu....hasbiyallahu lailah illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ta dinga furtawa a fili,saidai can qasa ta yadda idan ba mugun kusanci bane a tsakaninka da ita kunnuwanka ba zasu iya jin abinda bakinta ke furtawa ba.

Sanda ta duba agogon wayarta sai tayi mamakin yadda lokaci yaja dare kuma ya fara nisa,tasan zasuyi tsammanin ta koma haram ne saboda sun santa da nacin addu'a idan akazo wajen. Ta saba raba dare a wajen,baccinta kuma qalilanne,wannan dalilin tasan shine kadai ya sanya basu nemeta ba.

Dukka wani kuzari da za'a samu jikin dan adam babu shi a jikinta,a haka ta dinga takawa har ta maida kanta swissotel.

Ta samesu dukkansu sunyi bacci,yaran na jikin bibi duk su biyun,da alama tatsuniya ko labaran data saba basu take basu bacci ya daukesun. Taji dadin hakan qwarai,saita lallaba ta daura alwala,daga zaune tayi sallah raka'a biyu amma ta kasa roqar komai,ta maida kanta ta kwantar saman qafafunta wasu hawayen na zirarar mata.

Wani irin wahalallen dare yayi cikin wani yanayi dashi kansa baisan taqaimemen inda ya

Please Login or Register in order to submit comment