Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi dai dai,yanzu dai Auntynka da y'ar uwarka,sun nema ma alfarma, kan wannan maganar,don haka yanzu za'ayi bikin da komai da komai sai ta tare anan gidan in yaso saika tafi in Allah ya kaimu lokacin dawowar taka yayi sai Ku tare a gidanku"

Cikin in ina ya fara fad'in "Abbah nifa auran ne bana so gaba d''aya ni duka banson maganar auran,don Allah kayi hak'uri ka k'yaleni da batun auran nan wlh ko an d'aura auran nan bazan tab'a son matar ba don tasa an illata ni an lankwashemin rayuwa haka kawai ni . . .

Tassss Tasss kakeji ya d'aukeshi da mari, " don ubanka ko zaka mutu sai an d'aura wannan auran,kuma ma tafiyar na fasa barinka,bazaka ba kuma in dai ina raye da izinin Allah sai anyi auran nan".

Kuka wiy wiy UK yake da idonsa, yana rok'on Abban nasu amma yasa k'afa ya mangareshi, ya wuce cikin d'akinsa.

Aunty murjah da Ummu sulaim Wanda duk suka mik'e tsaye cikin tashin hankali, Sweety ta shigo tana share hawaye ganin yanda d'an uwan nata yake kuka kamar k'aramin yaro, ta rik'oshi tana fad'in "Kayi hak'uri broth ka daina yiwa Abbah gaddama don Allah, taso ka koma d'akinka".

Itada ummu sulaim suka kamashi zuwa d'akinsa,ita kuma Aunty murjah tabi Abbah d'aki donta k'ara rarrashinsa amma tana shiga ya nuna mata k'ofa don bai son ganin kowa tare dashi.

A d'akin UK kuwa kuka yake rizga kamar anmai mutuwa,y'an uwan duk sunyi tsilli tsilli suma sai sharar k'walla suke an rasa me bakin magana, a haka mijin ummu sulaim yazo d'aukanta yai mata waya, ta fito su tafi, badan taso ba ta mik'e tana fad'in " Broth ka kwantar da hankalinka kaji zan k'ara dawowa mu tattauna da Abbah inya huce,sweety ki kawo mai copy yasha yasha paracetamol kada kansa yai ciwo, Daddyn Aslam yazo zamu tafi".

Haka sweety taci gaba da rarrashinsa tana fad'a mai kalaman kwantar da hankali ahaka bacci ya d'aukeshi sannan ta tashi ta for tafi d'akin ta jiki ba k'wari.


*****
Bayan kwana biyu Alhj usman ya sami yaya da zancan sa ranar aure da kai kud'in auran,nan yaya yace zaiyi waya da y'an gidan can sakkwato abinda sukace zai sanar dashi.


****
B'angaran UK kuwa ba sassauci ya k'ara sawa kansa tsangwama, duk yana tunanin Abbah zai gaji ya sauko,ya hak'ura shi duk mamaki ma ya kamashi akan y'ar wani Abbah zai takura d'ansa,wannan wace irin yarinya ce meye had'in iyayenta da Abbansa har ya k'wallafa rai akan aura mai ita,kai duk yanda akai mahaifinta Babban k'usa ne maybe abokin kasuwancin sane kuma yasan tabbas yafi Abbah kud'i da ido a k'asa, don haka kawai yasa a ransa Abbah wani jarin yake son d'aurawa a kansa don haka wlh bazai yarda ba Sam".

******
Yaya haroon yaiwa Babban yayansu waya ya shaida mai za'a zo kawo kud'in auran Nahna dasa rana don haka su shirya ,nan ya amsa da ba komai duk sanda sukazo a shirye suke, da tararsu.

Da dare ya kira Alhj Usman ya shaida mai yanda sukai da yayansa,ba b'ata lokaci yace to zai sanar da Abokinsa da Y'an uwansa guda biyu saisu had'u su uku suje.


Ranar lahadi da safe wakilan Alhj Usman suka d'au hanyar sakkwato bisa jagorancin yaya Usman Wanda direban Alhj Usman usman yajasu.


Tarb'a ta musamman suka samu a gun mutanan sakkwato ina kasa ina ka aje sukai ta musu , bayan sunci Abincin da aka kawo musu sunsha sunyi k'at daga nan suka fara tattaunawa kan mak'asudun zuwansu,cikin girma da mutunta juna akai komai nan suka tsaida Ranar aure wata uku suka bada kud'in aure dana sa rana 100k, haka suka taho cikin farin ciki da nisad'i na tarar da suka samu.




Taku ce
Y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€9⃣
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​
(Me laya kiyayi me zamani)


0⃣2⃣0⃣


Gab da sallar magriba suka shigo gidan don haka Allah alwala kawai sukai suka wuce masallaci tare da Alhj Usman d'in donshi yaya sauka yai tun a hanya ya wuce gidansa.

Bayan sun fito a masallaci suka yada zango a turakar Abban nan da nan aka cikasu da abinci da lemuka,bayan duk sun gama cin abincin yayan Alhj Usman ya fara sanar dashi duk yanda sukai da irin yarar da suka samu a gun surukan nasu,nan abokinsa ya d'ora da fad'in " Ai Alhj Usman kayi dace da surukai masu mutunci da addini, domin kuwa sun mana tarb'a ta k'warai,mun dai daita auran nan da wata uku cif insha Allah ".

Cikin jin dad'in duk maganganunsu ya fara magana " hak'ik'a naji dad'in albishir d'inku, daman nasan tabbas duk inda Nahna Khadijah ta fito babban gida ne,dukda bansan dangintaba bayan yayanta,amma sweety ta sanar dani lokacin da sukaje biki ta shaida min karamcin zuri'arsu Khadijah to gashi yau na k'ara tabbatar da hakan daga bakinku, tabbas na sani komin dad'ewa wata rana Daddy zaiyi alfahari da auran Khadijah ".

Nan sukaita tattaunawa Baffah yace " Usman ina Daddyn yake inmai albishir da samun gidan surukai manyan mutane".

Jinjina kai Abbah yai kana yace "Baffah ai Daddy baya son wannan auran dole nake mai. . ."
Nan ya zayyane musu komai daga farko har k'arshe,

Duk kuma sai jikin su yai sanyi Baffah yace " ka sasauta mai dai Usman kabi a sannu kaita mai nasiha,da kansa zai fahimci alkairin abin,sannan maganar komawa da zaiyi kayi tuni kan maganar dai karkace zaka hanashi kaji ko".

"To Baffah za'ayi yanda kace insha Allah".

" yawwa sannan ka turomin shi gobe ko jibi zan k'aramai nasiha da Jan hankali".

"To ba damuwa zan turo shi Baffah Allah yaja da rai ya k'ara girma".

Nan yaita yi musu godiya sannan ya kira driver yasa ya maida kowanne gidansa.


******
A can gidansu Nahna kuwa bayan yaya ya koma gida yai sallar magriba ya kira Nahna da Aunty Hafsah bayan duk sun zauna ya fara magana " Nahna yau munje sakkwato da wakilan Alhj Usman don nemawa D'ansu auran ki,to duk abinda ya dace anyi , su yaya Babbah da wakilansa sun tsaida ranar aure nan da wata uku in Allah ya rayamu, don haka ke Hafsah sai Ku fara shirya duk abinda ya kamata ki samu Amrah ku yi list tun daga furniture har kayan kitchen duk dai abinda ya dace na gida kuyi list".


Cikin sanyin jiki tace
"To Allah ya sanya alkairi,yasa muna raye za'ayi".

Ni kuwa a lokacin ban San takamaimai halin da nake ciki ba,kawai dai nasan ban gane sauran zantuttukan da yaya kemin Wanda duk akan hak'uri ne da juriyar zama da miji, amma kalma d'aya bazan ita maimaitawa ba cikin nasiharsa, tsawon lokaci yana min maganganu masu dad'i Wanda daga bisani yace " Nahna tashi kije ki k'ara hak'uri kinji,Allah yai miki albarka".

Hakan ma banji ba saida ya sake maimaitawa na gane me yace,don haka na tashi na shige d'aki kaina na bala'in sarawa.

Tunda na shiga na kwanta kan gado ban San tsawon lokacin da na d'auka kwance ba sai da naji Aunty Hafsah na tab'a ni na firgigi ina kallonta, " Nahna bacci kike ne haka anyi sallar isha'i tun d'azu bikiyi ba,ga Amrah tana ta kiran kwayarki taji har Tara tayi biki jeba, tashi maza ki tafi kar hanya ta k'ara duhu".

Tashi nai jikina ba k'arfi na d'auki hijab d'ina nasa tare da d'aukan duk abinda zanyi amfani dashi da safe na zuwa school na d'au wayata na fito parlour, nan na samesu zaune nai musu saida safe na wuce".


A hanya ma ina tafe tanata kirana ban d'auba tunda naga na kusa da gidan, sanda na k'arasa nai knocking cikin tsoro tazo tana fad'in "waye nace " nice Aunty Amrah".
da sauri ta bud'e k'ofan tana k'aremin kallo tace "lafiyanki Nahna? Inata kira shiru gashi biki shigo da wuri ba yau".

Wucewa nai cikin gidan na aje kayana a saman kujera sannan na gaisheta,ta amsa tanata bina da kallo, sallar isha'i nai tare da shafa'i da wutiri,na dad'e kan sallaya ina kai kukana ga ubangiji akan ya daidaita tsakanina da UK don yanzu kam na tabbatar da shine abokin rayuwata, araina ina tabbatar da tasirin addu'ar da nakeyi don yanzu Sam banjin tsanar sa kamar da a zuciyata sai dai kuma tsananin tsoron abinda zan riska a zamana dashi, ban gajiya ba naci gaba da kai kukana ga rabbil izzati,nakai k'arfe goma sha biyu kan abin sallar sannan na tashi,

Aunty Amrah na kwance kan gado tanata zuba soyayyarta da mijinta a waya, ko kayan jikina ban k'ok'arin cirewa ba na haye gadon,addu'a nayi na tofa, ina rufe idona naji maganarta " Nahna "

Ban amsaba sai bud'e ido danai ina kallonta,ta d'ora ". Nahna Aunty Hafsah ta kirani kina sallah ta sanar dani an tsaida ranar auranki wata uku nan gaba, na tabbatar wannan maganar ce ta sauyaki yau duka na ganki wata iri,a kullum Nahna ina k'ara fad'a miki k'iyayyar UK gareki bamai zuwa ko ina bace,tabbas akwai abinda Allah yake nufi da lamarinku tun daga had'uwarku har yanzu da Allah zai k'ara had'aku a matsayin ma'aurata,ki kwantar da hankalinki,in kina nuna damuwarki ga lamarin nan zaki tayar da hankalin y'an uwanki,kuma kin shaidamin kina son farin cikin yayyanki sama da farin cikinki koba haka ba?".

Gyad'a mata kai nai ina k'ak'alo mirmishin yak'e nace " karki damu Aunty Amrah insha Allah zaku sameni yanda kuke so,matsala dai daga gareni akan wannan auran baza'a tab'a samu ba".

"Yawwa Sistanmu haka nake son ji daga bakinki,muyi bacci dare yayi".



******
A gidan Alhj usman kuwa UK ya sami labarin Neman da Baffah yake mai,dukda bai San ankai kud'in auransa har ansa masa ranaba tabbas amma yasan bazai wuce dalilin auran nan bane ake nemansa, washe gari da yamma ya shirya ya tafi gidan Baffah,yanda yakejin jikinsa ba k'arfi yasa ya nemi driver yakaishi.

Tunda suka gaisa da Baffah yake binsa da kallo da irin ramar da yayi,nan yai gyaran murya ya fara magana" Daddy mun tattauna da mahaifinka ya shaida min gaddamar da kake yi mishi bisa umarnin daya baka,shin Daddy kana son ka haifi y'ay'a suyima biyayya?shin kana tunin zaka shiga aljanna in har ka mutu a wannan hanyar ta sab'awa mahaifinka? Daddy ka Sani koni Hajiya bani na ganta nace ina soba,mahaifina ne ya zab'armin ita a matsayin matar da zan aura,kuma na aureta a gaba naga alkairin hakan don haka ba umarni ba ina baka shawara da kayiwa mahaifinka biyayya zakaga alkairi a gaba kaji ko Daddy?.

Duk jikinsa a mace murus ya d'aga kai alamar gamsuwa da maganar,
Nan Baffah ya d'ora da fad'in " kaga munje Sakkwato mun kai kud'in aure dasa rana,an tsaida lokaci wata uku masu zuwa,
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​


*ALLAH* *KA* *SHIGA* *LAMARINMU* , *ALLAH* *KARKA* *BAR* *WANI* *BAWANKA* *YA* *CUTAR* *DA* *RAYUWARMU* πŸ‘


0⃣2⃣1⃣

Kamar saukar ruwan zafi haka yaji batun Baffah,wato ma har ansa mai rana wata uku wayyo Allah ina mq ya mutu ya huta da ganin bak'ar ranar nan,

Baffah baiyi k'asa a gwiwa ba yaci gaba damai nasiha cikin salon kwantar da hankali " Daddy Kaga sabida gaddamar da kaiwa mahaifinka har yace ya fasa ma barinka ka koma,don haka yanzu inka koma gida kaje ka sameshi ka bashi hak'uri kace ka amince da auran,yayi hak'uri ya barka ka koma ka samo ci gaba, ka kaskantar da kanka ka nemi gafarar mahaifinka kaji domin ka b'ata masa rai matuk'a da gaske, kuma albishir d'in da zanma kayi dace da mace y'ar babban gida,idan nace y'ar babban gida ina nufin gidan Addini da Tarbiya, na tabbatar inka auri yarinyar nan zakai alfahari a gaba har ka godewa mahaifinka da yaima wannan gatan, ka tashi kaje gida ka baiwa mahaifinka hak'uri kaji ko".

Jiki ba sanyi yawa Baffah sallama ya fito driver yaja suka wuce gida.

Kai tsaye d'akinsa ya wuce ya kwanta bisa gadonsa yana fidda wata k'walla me zafi a gefen iidonsa.

Sai da dare ya fito zuwa d'akin Abbansa ya sameshi zaune yana kallon labarai,waje ya samu ya zauna jiki a sanyaye ya gaida shi,cikin rashin kulawa ya amsa mai ba tare da ya ko kalleshiba, jim yai a zaune duk jiki ba laka, can dai ya numfasa ya fara " Abbah don Allah kayi hak'uri ka yafemin,nayi nadamar gaddamar da nai maka,yanzu na fahimci abinda kake nufi na yarda da auran nan bisa umarninka".

Kallonsa sosai Alhj Usman yai yana nazarinsa tsawon y'an mintina yace " Daddy kayi abinda banyi tsammanin zakayi minba ka bijiremin a lokacin da nake Neman had'in kanka, Daddy na soka matsayin d'a mafi soyuwa gareni na nuna ma dukka nin gata da ake nunawa ko wane d'a,naso farin cikin ka dukkan muradinka shine nawa, babu abinda na rageka dashi Daddy amma Nazo da buk'ata ta karo na farko gareka amma ka watsamin k'asa a ido,kasa k'afa kai facali da buk'ata ta ko ".

Cikin nadama da k'asa dakai yake fad'in " ka gafarceni Daddy yanzu na amince zanma biyayya, fata na d'aya in an d'aura auran nan ka barni in koma in samu ci gaba Abbah ".

" daman nasani Daddy nasan don buk'atar Kane yasa kace ka amince badan farin cikina ba,amma dukda haka ina jan kunnanka daka zama d'a abin alfaharin iyayensa, kuma in amma d'aura auran saika kwana biyu yarinyar ta saba dakai naga rik'on ludayinka sannan zaka Taci, badanma yarinyar karatu take anan makarantar daga gama Sa'adatu rimi ai da tare zaku tafi ma can k'asar,amma dukda haka inta sami Hutu ta rink'a zuwa maka hutu, tashi kaje Allah yai maka albarka ".
Jiki a sabule ya tashi ya fad'a d'akinsa,yana zama gefen gado dafe da kansa tai sallama ta shigo d'akin,d'agowa yai yaw kalleta ba tare daya amsa sallamarba,itama bata damu daya amsa ba ta sami waje ta zauna, daf dashi ta rik'o hannunsa tana fad'in " broth yada Irin wannan tagumin haka,don Allah ka sararawa kanka, kar wani ciwon ya kamaka, Broth matar da Abbah ya zab'a maka abin alfaharin kowane namiji ce, tanada rik'o da addini matuk'a".

Cikin zafin rai yace "sisy na samu Abbah na fad'a mai na amincewa auran nan amma wlh inna bar k'asar nan banda ranar dawowa,don k'iyayyar auran nan a can k'asan raina take, sweety bani labarin wace yarinya Abbah zai auramin har kuke zuzuta ta haka y'ar wace ce meye matsayin mahaifinta a k'asar nan meye matsayin karatunta,yaya wayewarta take ?".

Dimm sweety taji gabanta ya fad'i don Duk abinda UK ya lissafo tasan babu abinda Nahna take dashi banda ilimi, amma cikin k'arfin gwiwa ya dakewa tace ina zuwa Broth bari in d'auko wayata in nuna maka pic d'inta, daga haka tasa kai ta fice zuwa d'akinta cikin minti biyu ta dawo da wayarta,wajan data tashi ta koma ta zauna ta fara mai magana cikin kwanciyar hankali " broth sunanta Nahna khadijah y'ar asalin garin Sakkwato ce, mahaifinta ba Kowa bane face tsohon alk'alin musulunci a garinsu Allah yamai rasuwa tunda dad'ewa, tana zaune hannun yayanta wanda aiki ya kawoshi kano, yanzu haka suna huld'ar kasuwanci da Abbanmu, danginta duka ma'abota addini ne kuma duk suna karatun boko masu rufin asiri ne matuk'a domin kuwa sunfi k'arfin komai na buk'atar rayuwa, amma baza ace musu masu kud'i ba, zuria'ace abin shawa'a da birgewa, don haka ma Nahna ta kasance mai kyakkyawar d'abi'a, matsayin karatunta N.C.E ne y'ar Arabic ce Nahna inda yanzu take degree d'inta a Sa'adatu Rimi college of education, tana karanta Shari'a low, tun farkon karatunta Islamic Arabic take karanta har izuwa yanzu atakaice dai Nahna *y'ar* *Arabic* ce, itace wadda nacema naje sakkwato bikin Yayanta, a halin yanzu banda wata babbar k'awa data wuce ta".

Cikin takaici ya dakatar da ita da hannunsa yana girgiza kai tare da fad'in "yanzu Duk cikin labarin yarinyar nan sweety meye abun birgewa,meye abun Jan hankali, wane Abu zan fad'awa friend d'ina guda d'aya in sun tambayene labarin matar daza'a aura min, maza da sauri fitomin da pic d'inta in gani in k'arasa d'iban takaici".

Cikin sarewar gwiwa sweety ta shiga lalibo pic d'in Nahna cikin wayarta tana nuna mai,

A firgice yake kallon pic d'in yana nunashi da yatsa " wannan itace yarinyar da ake k'ok'arin lik'amin,gidahuma da ita me halin y'an k'auye, *Y'ar* *Arabic* ??? Yarinyar da inuwarmu bata had'uwa na tsaneta tun tuni,sabida rashin wayewarta,a farkon kallona da ita taimin kama da wayayyiya amma ina latsata na gane ba komai tare da ita sai hauka da k'auyanci, wlh an cuceni an gama dani,na shiga uku ni yanzu wannan yarinyar zan gani matsayin matata? To wlh Allah inma ita ta bibiyi rayuwata tabi Duk hanyar databi tasa wanta ya lik'awa Abbah ita don na aureta to wlh ta tafka kuskure ta halaka kanta, me zanyi da auran *Y'ar* *Arabic*? Hhhmmm lalle yarinyar nan tasa kanta a bala'i wlh saina azabtar da ita matuk'a, wato game d"in da muka buga a college ne bai isheta ba shine ta bibiyi rayuwata tsawon wannan lokacin ".

Rik'o hannunsa sweety tai cikin kuka tana fad'in " haba broth me kake fad'a haka,don Allah karka cutar da y'ar mutane ,wlh ita batama sanka ba in banda a photo. . .

"Waye yace miki haka waye yace bata sanni ba k'arya take miki wlh pretend ne tasanni tsaf ita tasan abunda ta k'ullo amma ki barni da ita,zan maganinta".

" broth wlh Nahna mutuniyar kirki ce, kuma wlh itama Sam bata son auran nan kamar yanda baka so,kawai biyayya takeyi,broth don Allah ka rik'eta amana wlh ina sonta sosai mutuniyar kirkice Nahna ".


Dariyar mugunta yai yana fad'in " tashi kije ki kwanta dare yayi kibar kukan nan".
Kamar bazata tashi ba amma ganin ya had'e girar Sama yasa ta mik'e ta fice ranta d'auke da nauyi.





Taku ce
Y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​



0⃣2⃣2⃣


Tunani ne ya cika zuciyar Sweety, shin wai dama akwai sanayya tsakanin Nahna da broth d'inta, amma kuma ai Nahna bata tab'a nuna mata tasan shi ba,koda ta ganshi a photo ai bata nuna sanayya tsakaninsu ba,amma dai Gobe Duk yanda ake ciki zata nemi Nahna taji komai, tana wannan tunanin har bacci ya d'auketa.


A gidansu Nahna kuwa koda yaushe mik'a lamarinta ga Allah take, bata dogon bacci kullum tashi take cikin dare tana kai kukanta gun me share mata hawaye, don haka koda yaushe take jin zuciyarta na mata sanyi,kamar ba wani abu gabanta, Sam take jin tsanar UK da tsanar auransa na fita cikin ranta,Duk da baza tace ta fara son abin aranta ba amma baza tace tana k'insa kamar farko ba.



Da yamma lik'is Sweety tazo gidansu Nahna bayan sun gaisa da Aunty suka shige d'aki,cikin fara'a sa tsokana ta dubi Nahna " Aunty nah zance ko amarya zance?".

Mirmishi Nahna tayi tace "ko d'aya karki fad'a,in bazaki kice Nahna ba kice Khadijah".

" a'a ni yanzu wannan sunan yamin nauyi a baki ai sai mutane suga rashin kyautawa ta ina fad'ar sunan matar yayana".

Dukanta tai a baya tana fad'in "ai kuwa Duk abinda zakice in dai ba Nahna ba ko Khadijah bazan amsa ba ".

Dariya sweety tai kana ta gyara zama kan gadon tana fad'in " kai gaskiya Nahna kina da zurfin ciki na bala'i wlh,yanzu Duk tsawon zamanmu dake ace biki tab'a nuna min kin san Broth ba koda wasa,ashe akwai sanayya tsakaninku,to shi ya fad'amin kun Dan juna a college ba kad'anba don zumunc kukai sosai ".

Zaro ido Nahna tayi ba tare data tuna ba ta fara fad'in " kai sweety UK d'in ne yace miki munyi zumunci?to wlh tsawon sani na dashi a college ba wani Abu na arzik'i daya tab'a had'a mu in banda tsantsar tsanar juna da tsangwama da yakemin,Duk inda nake UK sai ya bibiyeni yaje ya tozar tani ya wulak'anta ni gaban tarin jama'a,har randa na daina ganinsa a skul d'in".

Ruk'o hannunta sweety tai ganin yanda yanayinta ya sauya lokaci guda tace "kiyi hak'uri Nahna amma don Allah ina son ki fad'amin tsakani da Allah komai dake tsakaninki da Broth tin farkon saninki dashi".

Nahna bata b'oyewa Sweety komai ba ta sanar da ita tun farkon had'uwarsu,idonta yana tara k'walla ta k'arasa zancen , hannu sweety tasa tana sharewa Nahna ido " kiyi hak'uri Nahna don Allah karki k'ullaci Broth a zuciyarki,karki k'ulla ceshi hakan zai hanaku jin dad'in zaman aure,matuk'ar kina tuna Irin haka bazaki tab'a ganin farinsa ba zaki rink'a jin tsanarsa a ranki, nasani Nahna Ke me ilimi ce sanin addininki yana miki amfani,don haka nasan auranku zaiyi albarka Duk abunda yaya zaiyi gareki don Allah ki daure Nahna komai lokaci ne wata rana ba zaiyi ba kinji Nahna, hak'ika Duk wanda yaji wannan labarin yasan akwai wani abu da Allah ya b'oye gareku shiyasa harya had'aku a baya cikin rashin fahimta yanzu kuma ya had'a Ku matsayin ma'aurata,tabbas akwai wani Abu da Allah ya b'oye tsakaninku kiyi hak'uri kinji don Allah ".

Mirmishi Nahna ta k'ak'alo tana Gobe k'wallan idonta tace " karki damu sweety Duk wannan na san yana cikin k'addarata, auren UK babbar k'addara ce gareni wanda sanin tsakanina dashi yasa hankalina ya tashi amma dana kai kukana game sharemin hawaye sai naji Duk hankali na ya kwanta, ni yanzu banda wata matsala da wannan auren domin na rok'i ubangiji zab'i kuma da alkairi don haka karki damu,insha Allah ni dai daga gareni babu wata matsala kan auren nan matsalar

Please Login or Register in order to submit comment