Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaushe daga safiya zuwa yamma duk wajan su Aunty Murja yake yini sai Abbansa ya dawo ya ke shiga ya karb'o shi.





________________
Watan cikina tara da y'an kwanaki Allah ya sauke ni lafiya,Wannan karon ma namiji Allah ya bani,an kuma don shi d'in ma kamannina sak ya d'auko har bak'ar fatata.

Murna wajan UK kamar wannan karon aka tab'a mai haihuwar, hidima sosai ya shiga yi damu,haka ma Abba yai rawar gani daga gidan mu ma kamar ko yaushe y'an uwana sun yi min iya k'arfin su,yaro yaci Sunan Abba wato Usman ana kiran sa da Nurain, an yi taron suna an watse cikin murna da farin ciki.

Haka naci gaba da rainan yarana cikin kulawa da k'aunar su,sun taso gwanin sha'awa musamman dake Nurain me jikin girma ne irin na Abbansa sai nan da nan watan sa uku ya fara zama wanda a lokacin kuma Raees ya ke gudun sa ko ina, masha Allah.


**********
Haka rayuwa taci gaba da gudana mana cikin Wadata da annushuwa,ban nemi komai na rasa ba na rayuwa,mijina ya na matuk'ar sona da yayana kullum burin sa ya faranta ranmu,in ya dawo duka lokacin sa yake bawa yaransa har sai ya shiryasu sunyi bacci sannan ya dawo gareni kuma.




**********
Watan Nurain Goma cif na yaye shi sabida tafiyar aikin hajji da ta yaso mana,ni da UK da Abba da Aunty Murjah, nima na tattara kud'ad'ena na biyawa yayana abin alfaharu na,don banda wani abu da zan sakawa yaya Haroon dashi a duniya yayi min komai na rayuwa,lokacin dana sanar dashi har dashi tafiyar nan farin ciki yasa har k'walla yayi,nan ya kira y'an uwa ya shiga sanar dasu,kowa addu'a yai tamin da sa albarka,ni kam a raina nake fad'in "To in ban yiwa yaya ba wa zanwa? Kud'in da suke account d'ina sunyi yawa matuk'a, ga Wanda UK ke samin ga kud'in albashina,ban siyan ko abun k'wandala a ciki kullum mijina cikin yimin hidima yake."





Zulk'ida na kamawa mune jirgi na uku zuwa k'asar Saudi,kuka rurus nake lokacin da na ganni cikin masallacin manzan Allah, nai godiya gare shi da ni'imar da yayi min.


Munyi aikin hajjinmu cikin kula da shauki,sosai na dage da yiwa iyayena addu'ar samun rahmar Allah a wannan waje me girman daraja da nake.


Bayan salla babba da kwana goma muka dawo gida Nigeria cike da kewar k'asa me tsarki.




*************
Dawowar mu da ga saudiya da wata biyu wani cikin ya bayyana gareni, godiya nai ga Allah daya bani wannan n'iima,lokacin Nurain yana da shekara da wata biyu,tafiyar sa ko ina,UK ma murna ya sha ya gode Allah.





~Bayan shekara biyar~👇🏼
___________________
Lokacin muna da Yaya Biyar Raees,Nurain,Yusuf (Baffa) Umar(junior) sai k'aramar su Little(Ruk'ayya)

Lokacin Raees na da shekara bakwai,Nurain shida,Baffa,Hud'u junior biyu sai Auta me wata takwas.


Yarana Masha Allah Gwanin sha'awa kowa ya kallesu sai ya k'ara kuma ya tanka,don haka kullum cikin tofesu da addu'a na ke,ba dare ba rana,sun taso cikin Tarbiya da girmama junan su,haka jama'ar gari kowa Aunty kowa uncle, ko basu San mutum ba in sunsan ya girmesu basa fad'ar sunan shi, haka tsakanin su suke b'oyewa junan su suna.

Yare uku dam su ke ji,larabci English Hausa, duk Wanda suke yi baza kace suna jin wani yaran bayan sa ba,don makarantar ma da suke boko da Arabic ce, ban yarda sun karkata da iya boko ba,don haka Qur'an ma hadda sukeyi duk da karancin shekarun su,don haka suka zamo taurari ko cikin yaran family.kuma kula da yarana Sam bai shafi aikin koyarwa ta ba,komai ina bashi lokacin sa da yin komai cikin tsari.



_______________
Duk ran jumma'a Abban su sha biyu yake tashi aiki,suma kuma sha biyun suke dawowa daga makaranta don haka suna dawowa kowa yake shiryawa su tafi masallaci, kafin su dawo na shirya abunci don tare muke cin abinci da yaranmu in har suna gida.


Yau ma na shirya tsaf cikin riga da zani na atamfa wanda sukai min das a jiki suka amsheni, Little ma na shiryata cikin kwalliyar ta gwanin sha'awa na saka ta cikin keken ta don ta barni nai komai a nutse.

Ina tsugunne ina jera cups dintda zamuyi amfani dasu na fara jiyo hayaniya,mirmishi nai na san sun dawo,sallamar Baffa ce ta katseni ya shigo cikin nutsuwa "Assalamu Alaiki ya ummy"

Kafin na amsa sauran ma suka shigo duk da sallama kamar yanda yayi,amsa musu nake fuskata d'auke da mirmishi ina binsu da kallon sha'awa don dukkansu sanye suke da shadda fara tas babbar riga da y'ar ciki,ga hulunan su zanna akawunan su,duk k'ok'arin cire rigunan suke nace "Wai ina Abban na ganku ku kad'ai?."

Junior ne yace"Yana tsaye da Baba me gadi."

Kafin nace wani abu ya shigo shima cikin irin shigar yaran tsaf da babbar riga, "Ga Abba ya shigo madam ni ake jira ko?".

Fakar idon yaran nai na kashe mai ido guda tare da k'yasa mai alamar yayi kyau,dariya yayi kawai yana amsawa a sirrance.


Bajewa mukai muna kwasar garar girki baka jin komai sa k'arar k'ashi😜, bayan mun gama kowa yai hamdala sannan Raees ya taimaka min na gyara wajan,shi kuwa oga ya d'auki little sai wasa suke mata shi da junior, Baffa da Nurain kuma suna harhada kayan su da suka cire suna ninkewa.


Bayan duk mun dawo mun zauna hira muke da yaran mu wanda a haka ne muke gane damuwar moka da kuma burin da kowa ke dashi,Baffa ne yai gyaran murya da fad'in" Abba ni inna girma fa lauya nake son zama."

Da sauri Nurain yace"A'a wallahi na riga ka ko yaya."

Ya k'arasa da kallon Raees,shi kam dariya yayi da d'aga musu kai,nima dariyar nai nace"Kullum dai sai anyi wannan muhawarar fatana kullum Allah ya baku ilimi me amfani wanda Alumma zasu amfana dashi musulunci yayi alfahari da Ku."

Amsawa sukai da amin, UK ya juya ga Junior yana fad'in "Namesake fa mema kace kana son zama inka girma?."

Cikin murna da zak'uwa yace"Abba ni Sarki zan zama."

Dariya mukasa gaba d'ayan mu don daman mun San k'arshen zancan nashi.






_*Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatummassalihin*_


_*Anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa me suna 'YAN ARABIC abunda nai dai dai a ciki Allah ya bani ladan sa,abunda na kuskure ina rok'on ubangiji ya yafe min*_




_*Dukkan abunda kuka ga nai dai dai wannan daga Allah ne,Abunda kuka ga kuskure wannan daga gareni ne,kumin afuwa Ajizanci ne irin na d'an Adam*_🙏🙏



_*Na gode da jimirin bina da kukayi tsawon lokaci cikin wannan rubutu na gode muku ba adadi kuma masoyana ina musu fatan Alkairi a duk inda suke a duniya,nima ina sonku sama da yanda kuke sona,ana tare har abada*_🤝🤝🤝



~Ku kasance dani cikin littattafaina masu fitowa~

*MAKOMAR KOWA*
*'YA'YANA MATA SUNE SANYIN IDANIYATA*


~Domin k'orafi,gyara ko shawara ga number ta~👇🏼
*07067270055*



*25/9/2019*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment