Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsakani na da kai, kama rasa da wa zaka had'ani saida wannan Y'ar Arabic d'in me tarin duhun kai da k'auyanci, wadda ko Kalmar Love bata iya furtawa ba balle tayi shi, wlh da inyi love da Y'ar Arabic k'ara in mutu banyi aure ba, meta sani da zata min meta iya mutttsssss, AA kasan dai ni mijin wayayyiyar mace me aji ne wadda zan shiga da ita ko ina ta fiddani kunya."

Dariya sosai sauran abokan keyi na yanda ya daddage yake masifa har idonsa ya canja da b'acin rai.


Tsaki yaja ya bar gun sauran suka bishi.


"Khadeejah don Allah me kikaiwa wannan mutumin haka, Tun tuni nake ce miki mukai k'ararsa ga hukumar makaranta kika ce abarshi zai daina gashi nan yanzu ya bar skull d'inma bai fasa shigowa yimiki hauka ba."

D'agowa tai tana mirmishin yak'e Wanda yafi kuka ciwo ,
" Hafsah nifa ban jin haushinsa yanzu nasan jahilci da rashin sanin addini ke damunsa, yaje yayi duniya ce wata rana zai daina."

Ummy tace "ni kin san abinda yafi b'ata min rai dashi da yake cewa me macan Arabic ta sani a harkar love me zata iyayi, Allah ina rok'on ka daka had'a shi da y'ar Arabic a gidan auransa naga yanda za'ayi."

"Don Allah muyi abinda ke gabanmu mu bar wannan zancan haka."










Taku ce y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YAN* *ARABIC* 🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*




DEDICATED TO ALL
ARABIC/ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com




0⃣0⃣6⃣



Tsawon wata goma Nahnah bata k'ara ganin UK ba Wanda hakan ya tabbatar mata da ya kammala skul d'in gaba d'aya,kuma tasan a wannan lokaci yana hidimar k'asa tunda shi a b'angaran degree yake, hakan ya k'ara kwantar da hanlalinta harta manta shi cikin rayuwarta.

A lokacin suna N.c.e 2 ne shima sunyi nisa don har sun fara shirin zuwa Teaching practice (T.P) da sunyi exam d'in second semester d'in zasu tafi Wanda zasu cinye tsawon semester guda baza su dawo ba sai wata second semester N.C.E 3.


**************
Alhj Usman katsina shahararran D'an kasuwa me wasa da y'ay'an nera, mutum me karamci da girmama talaka bashi da girman kai ko kad'an yana da tsananin kyauta da son mutane, yana da gaskiya matuk'a a harkar kasuwancin sa, matsalansa d'aya ce masifar son ya'ya' baya son abinda zai sami d'ansa ko kad'an duk yanda kuke dashi to matuk'ar ka shiga harkar ya'ya'n sa to zaku raba gari abinda d'ansa ke so shi yake so ba tare daya kula da munin abun ba.

Wannan son ya samo asali ne daga rasuwar matar sa uwar ya'ya'nsa Wanda ta rasu tun yaran suna k'anana su uku a haihuwar autar ta rasu awa d'aya da haihuwar,
Tausayi da k'aunar ya'ya'n ta taka rawar gani wajen sangarta su.
Yakai tsawon shekara bakwai bayan rasuwar baiyi aure ba ya tara ma'aikata sama da goma agidan suke kula da yaran nashi cikin kulawa da aminci, yayin da shi kuma yake cika musu lalitarsu da kud'i don ya gamsu da kulawar da sukewa y'ay'an nashi.


Umar shine Babba Wanda yaci sunan kakansa suna kiransa da Daddy, sai ummu sulaim , sannan Ruk'ayya auta wadda taci sunan mamanta me rasuwa, suna ce mata sweety Wanda Abbanta yake kiranta har sunan ya bita.


Iya nacin da akewa Alhj. Usman akan yayi aure bai yi ba saida Sweety ta shekara bakwai sannan Allah ya had'ashi da Aunty Murjanatu wadda ta tab'a yin aure shekarta d'aya ta fito ya ganta ya aura kan sharad'in kulawa da y'ay'ansa cikin amana da aminci.

Zuwa yanzu tana da y'ay'a biyu a gidan duk maza zaid da haris.

Umar wato 'Daddy' a yanzu yana can kwara state yana N.Y.N.C.E d'insa Wanda ya rage mai wata d'aya ya gama, kuma anan gidansu Abban sa ya gama yimai shirinsa tsaf don tafiya k'asar India yin wani course na shekara biyu akan fannin karatunsa.

Ummu sulaim kuwa an Mata aure bada dad'ewa ba har yanzu tana kan karatunta a bayero.

Sai sweety itama yanzu tana shekararta ta biyu a northwest.


Yaya haroon abokin kasuwancin Alhj Usman ne yana karb'ar shinkafa a gunsu ya raba a wajan aikinsu da sauran store store, Jinin su ya had'u matuk'a Alhj yana son yaya Haroon sabida ya kula da amanarsa, wani sa'in har gida yake kiransa su tattauna a maimakon office d'insa.


Rashin lafiya ne ya kama Alhj Usman sakamakon yana da ciwon sugar har aka kwantar dashi a asibiti, kwanansa d'aya a asibitin yaya haroon yace Aunty Hafsah da Nahnah su shirya ya kaisu su dubashi.

Bayan sunyi sallar magriba ya d'aukesu suka tafi,
Kasancewarsa babban mutum yasa Asibitin cika da jama'a masu dubiya, a haka dai suka ratsa cikin d'akin,
Alh Usman yana hango Yaya Haroon ya fara mik'a hannunsa yana kirmishi irin na mara lafiya, a hankali yaya ya k'ara yasa Hannunshi cikin nasa suka gaisa yana tambayarshi ya k'arfin jikin, cikin jin ciwo ya amsa, nan su Aunty Hafsah da Nahna ma suka gaidashi suka mai ya me jiki sannan Duk suka gaida da mutanan d'akin.

Tun shigarsu d'akin Nahnah ta kula da Sweety dake gefan gadon tana share hawaye, tausayinta ya kamata tasan me take ji tasan k'aunar mahaifi, tasan tsoron Sweety kar mahaifinsu ya rasu, tana wannan tunanin wayanta tai k'ara alamar ana kiranta, fita tai daga d'akin don ta samin damar d'agawa,


Tana nan tsaye tana wayan taga fitowar sweety daga d'akin taje can nesa ta zauna tare da kifa kanta tana kuka sosai.

Bayan ta katse wayan ta zubawa sweety ido tana cike da tausayi, samun kanta tai da k'arasawa wajanta,a hankali takai hannunta ta dafa bayanta tare da mata sallama, da sauri ta d'ago kanta tana share idonta, tsugunnawa tai tana magana k'asa k'asa " kiyi hak'uri ki bar mai kuka, addu'anki yake buk'ata,asannu Allah zai bashi lafiya kinji."

Gyad'a kai sweety tai tana goge idonta tace"na gode"

"Ba komai naga ne tunda muka shiga d'akin kike kuka zaki karyar mai da zuciya, ki tamai addu'a,kinga ai jikin nashi ma da sauk'i tunda ance jiya baima San Wanda ke kansa ba."

Gyad'a kai kawai take don nuna gamsuwa da maganar Nahnah,

Ruk'o hannunta tai tare da cewa"shike nan insha Allah na bar kuka, taso mu koma d'akin."

Suna shiga yaya Haroon yace" Nahnah mu tafi daman ke muke jira"


Sallama sukai da mutanan d'akin suna k'ara addu'a ga Mara lafiyan.

Tunda Nahna ta dawo gida bata da sukuni duk tausayin Sweety ya kamata duk da bata Santa ba bata tab'a ganinta ba amma tasan y'ace ga Mara lafiyar, abinda kawai take tunowa sanda tana sakkoto kafin Baffa ya rasu in bashi da lafiya haka take zama taita kuka.



*BAYAN* *KWANA* *BIYU*

Ranar jumma'a ne Nahna bata je skul ba don basu da lecture, bayan an sakko masallaci suna zaune suna cin abinci dasu Ashraf suna shirmansu tana ta dariya, yaya ya shigo gidan da Sauri yaran sukaje suka tare shi, cikin fara'a tace "Yaya sannu da zuwa "

"Yauwa sannu Nahna, ina Auntyn tak . . . . ?

"Gani ma na fito, sannu da zuwa,Allah yasa lafiya naganka yanzu?"

Zama yayi yana shafa kansa yace "lafiya qlau wlh, ina sone mu koma dubo Alh Usman amma ina son ku d'an masa girki ne don naji yace min yana son fatan alkama da yakuwa da gyad'a, don haka ina son Ku shirya mai zuwa nan da k'arfe hud'u don Allah sai muje."

Nahna ce ta mik'e tana fad'in "Aunty bari inje in fara had'a kayan girkin"

"Yawwa Nahnah ki had'a harda na darenmu kawai basai mun k'ara yin wani abincinba kinga"

"Tom Aunty" ta fad'a tana shigewa kitchen d'in.

Yaya kuma ya mik'e yace " Hafsah kawomin abinci inci in d'an kwanta kafin la'asar d'in".


K'arfe hud'u da rabi suka fito Nahna ta bud'e motan tasa Abincin abaya itama ta shiga tare dasu Ashraf.


Yau asibitin da sauk'in jama'a y'an dubiya don d'akin daga Aunty murja sai Ummu sulaim da sweety da wata tsohuwa wadda da gani kasan Maman Alh ce,

Bayan sun gaggaisa da mutan d'akin sukai gaida Alh tare da mai sannu,duk da ma jikin nashi yau Alhamdulillah yayi sauk'i sosai yana zaune jingine da filow, sweety ce ta taso da fara'arta ta rik'e hannun Nahnah tana fad'in "k'awata sannu da zuwa"
Mirmishi Nahna tai tace "um munzo ya mai jikin"

"Me jiki Alhamdulillah, Dad itace fa wadda nake fad'a ma ranar da suka zo taga ina kuka taita rarrashina tana min nasiha".

Da mirmishi kan fuskarsa yace" Ayya sannu kinji y'ar nan, ai tun shekaran jiya sweety kemin zancenki."

Juyawa yai yana kallon Yaya Haroon yace"Haroon wannan fa ko k'anwar kace?"

Cikin mirmishi Yaya yace "eh autarmu ce Alh aguna take ai"

"Madallah yarinya me hankali,Allah yai miki albarka kinji, ya sunanki?"

Cikin jin kunya Nahna tace "Khadeejah"

" sannu khadeejah"

Nan suka ci gaba da d'an tab'a hira , yaya Haroon yace "Alh, ga faten alkama an maka ko zaka iya ci"

Cikin fara'a Alh usman yace" Tom na gode Haroon sannunku da k'ok'ari"

Aunty murjah ta mik'e ta d'uko plate da spoon ta zuba mai D'an kad'an don tasan ba wani ci zaiyi da yawa ba.

Abu kamar wasa ya cinye yace a k'ara mai da yawa ta k'ara mai nan ma ya cinye tsaf yai gyatsa da godiyar Allah.

Mamaki kowa yai na cin abincin da yai don tunda ya kwanta bai cin wani abin arzik'i.

Kallon yaya Haroon yai yace "Haroon wannan girkin yamin dad'i sosai na gode da kai da me girkin duk Allah yai muku albarka."

Cikin jin dad'i Yaya yace"ameen Alh, khadeejah kinji girkin ki yaiwa Alh dad'i"

Cike da kunya Nahnah ta sunkuyar da kai.

Hajiya Babbah (Babar Alhajin) kallon Sweety tai tace " kinga yarinya me hankali ta iya girki banda me sai uwar kwalliya da kinibe kika iya."

Turo baki sweety tai tana k'un k'uni na damunta da Hajiyan take.

Shikam Alh kallon Nahna yake da mamakin ta yanda ta iya girki haka kamar babbar mace gashi da gani nutsuwa ta ratsa yarinyar, lokaci d'aya yaji k'aunar yarinyar ta shiga ransa.






Y'ar mutan ja'oji ce πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YAN* *ARABIC*🌸

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / __ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com



_HAPPY_ _SALLAH_ _TO_ _ALLS_ _MUSULUM_ _UMMAH_
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰





0⃣7⃣



Zumunci ne sosai ya k'ullu tsakanin Nahnah da sweety, kullum sai Nahnah tayiwa Alh usman Faten alkama ta kai mai asibitin, anan sike zama suyita hira da sweety har aka sallameshi.


Koda yaushe sweety cikin kiran Nahna take suyi waya tai ta fad'amata"Nahna wlh kina birgeni kinada hankali. Abbanmu ma kullum sai ya yabeki nutsuwarki da iya girkinki,Daman a unguwarmu gidanku yake da kullum agidanku zan rink'a yini,"
Haka kullum take fad'i ita kam Nahna sai dai tayi dariya kawai.

Sweety irin emmatan nan ne masu iyayi da surutu, akwai jin kai da iya tsara kwalliya,bata son harka da tsamaye inka duba duk Wanda sweety ke harka dashi tofa gaye ne in mace ce sai babbar yarinya wadda ta amsa sunan had'ad'd'iya me aji,amma duk da haka in kikayi mata taji kin shiga ranta to zatai k'awance da Kai.


Yau ranar Saturday ne sweety taiwa Nahna waya kan zata to gidansu, don haka da wuri Nahna ta tashi ta shirya mata kayan motsa baki sannan tai wanka tai kwalliya cikin d'inkin doguwar riga na material fari da adon bak'i tasa d'an kwali bak'i akanta,kasancewar bata iya zama ba d'an kwali akanta koda cikin gida take, bayan ta kintsa gidan taiwa su Ashraf wanka suma ta shiryasu ciki kwalliya.


Tana zaune tana chart da wayarta kiran Sweety ya shigo, da murmishi kan fuskarta ta d'auka" Assalamu Alaikum"

"Hello my Nahna gani a akan layin naku kizo ki tafi dani."

"To gani nan d'an jirani kad'an."



D'akin Aunty ta shiga ta shaida mata zata je ta taho da sweety a k'ofar layin,
Sannan ta koma d'akin ta d'auko mayafinta ta kama hannun ashraf suka fito.

A hankali cike da nutsuwa take taka k'afanta tana tafiya.

Sweety kuwa tana zaune cikin motanta take hango tahowan Nahnah, d'an mirmishi tai aranta take fad'in"Gaskiya Khadeejah aji ce tanada nutsuwa komai nata cikin sanyi yake natural ce.

Nahnah tana tafiya a hankali tazo gota motan Sweety taji ance
" my Nahna"

Da sauri ta kalli gun, mirmishi tayi tana fad'in"daman kece cikin motan?"

"Tom zagayo mana mu k"arasa" sweety ta fad'a tana bud'e Mata murfin motan.

Tafiya kad'ance ta sadasu da gidan tunda daman duk cikin layin suke,fitowa Nahna tai ta bud'e d'an madaidaicin gate d'in nasu yayinda Sweety ta shigo da motan tai parking d'inta suka k'arasa cikin gidan.

Da sallama suka shiga parlourn Aunty ta amsa musu fuskanta d'auke da fara'a tanaiwa Sweety sannu da zuwa,itama cikin girmamawa ta gaida Auntyn sannan ta zauna suma su Ashraf suka gaidata.


cikin fara'a Nahnah tace sannu da zuwa,yau dai gaki gidanmu ko.

Hararan wasa ta wurga mata tace"eh ni nazo gidanku saura kuma kema kizo gidanmu wani week d'in."

Mirmishi kawai Nahnah tai ta shige kitchen don kawo mata abubuwan motsa baki.

Hira sosai suke don Aunty ta basu waje sannan yaran ma duk sun shiga d'akinsu, don sun saba indai anyi bak'i basa zama gun parlour.

Sweety kasancewarta wayayyiya yasa ta saki jikinta ta sha lemon da aka kawo mata tare da cincin.

Ganin lokacin d'ora girkin rana yayi yasa Aunty fitowa da niyar shiga kitchen tunda mai girkin tanada Bak'uwa, da sauri Nahna tace

" Aunty me zakiyi a kitchen? badai girki zaki d'ora ba."

"Eh yau na huttasheki kinada bak'uwa ki kula da ita kawai."

"A'a Aunty ki barshi zanyi sweety ba matsala bace zansa mata kujera a kitchen d'in inayi muna hira ko tawan"

Ta fad'a tana kallon sweety,

Ita d'inma dariya tayi tace"Eh Aunty ki barshi zan tayata sai
In koya nima."

" y'ar dariya Aunty tai tace" To kuyi ba damuwa,ke Nahna saiki tambayeta abinda take sonci Ku dafa."

"OK Aunty ba matsala."


Tare suka shiga kitchen d'in da sweety tana aikin suna hira yayinda take d'an taimaka mata da irin yankan su albasa da b'are magi, girkin ba mai Wahla sosai bane don sweety ca tai danbun cuos cuos take so, don haka nan da nan suka gama had'a komai, zuwa awa guda har ta zubashi a cikin food flask.

Har zasu fito a kitchen d'in Nahna tace"sweety ko kina shan lemon kwakwa muyi?"

"Yawwa tawan kamar kin san shine best d'ina cikin drink's, amma kina ganin bashi da wahla bazai gajiyar dake ba."

"Hhhhhmmm,kedai je parlour ki huta ko ki shiga d'akina don na lura kin gaji sosai."

"A'a ban gaji ba ni wallahi dad'in aikinma nakeji ,daman ina Girki a gidanmu don ina son inga na iya abubuwan girki da yawa.

"Hhhmmm karki damu zaki iya kinji k'awa ta, yanzu dai zo muyi lemon da sauri mu gama.

Nan da nan suka shirya leman suka jefa k'ank'ara,lokacin k'arfe biyu tayi,don haka suka shige d'aki don yin Sallah,suna shiga d'akin Sweety ta fad'a gadon ta kwanta tana fad'in " Wasshhhh,my besty na gaji sosai wlh, ashe haka masuyin aiki suke jin gajiya in sun gama".

D'an dariya Nahnah tai tace"kefa kika ce dad'in aikin kikeji,shiyasa tunda farko nace ki zauna".

"Hhhhhmmmm wlh da mukeyin aikin ban gaji ba sai yanzu".

Jinjina kai Nahnah tai tana mamakin D'an aikin da Sweety tayi amma har zatace ta gaji,gaskiya wasu y'ay'an masu kud'in sai a hankali.

A fili dariya tayi tace " To ko ruwan zafi zan had'a miki ki d'an gasa jikinki sai kiji dai dai".

" To d'an had'amin, don naji bayana har ya rik'e".

Ruwa me d'umi ta had'a mata sannan ta fito ta mik'a mata towel.

Bayan ta shiga wankan Nahna ta tada sallah,

Tsawon 10 minutes Sweety ta fito d'aure da towel tana tsamtsame jikinta, Cikin kirmishi Nahnah ta kalleta tace "Ki bud'e Woodrow ki zab'i kaya ko".

"A'a ki d'auko min da kanki, don ban san inyi wanka in maida kayan dana cire ne da bazanma canja ba".

Mik'ewa Nahna tai ta d'auko mata wata doguwar riga me matuk'ar kyau,

"Woww Nahnah wannan riganfa yayimin kyau sosai wlh,inada irinshi amma nawa ba kalan wannan bane, nawa copy color ne, wannan Orange colour d'in yafi kyau gaskiya".

"Hmmmm in kina so ki rik'e na baki duka".

D'an zaro ido tai tace" da gaske ki barmin"?

"Eh da gaske mana Sweety".

"Kai gaskiya Nahnah kinada kirki sosai wlh, na gode kinji, kuma kin San wani Abu wlh don ina k'aunanki ne fa har nace miki tayi kyau don ni bana kulawa da abinda mutum yake dashi balle in yaba mai kin San rainin hankalin mutane yanzu saisu rainaka, ke kuwa me hankali ce baki da matsala don haka kika shiga raina sosai, na gode kinji Nahnah".

Mirmishi ta k'arayi tace "sweety nice da godiya kinji".

A haka suka gama shiryawa suka fito don cin abinci, bajewa sweety tai kamar a gidansu take ta kwashi girkin nan ta kora da lemo.


Sai daf da magriba ta tafi tana k'ara fad'awa Nahnah tana jiranta itama ta kawo mata ziyara, ita dai mirmishi kawai take.


Tun daga lokacin Zumuncinsu ya k'ara k'arfi, duk da Nahnah bata tab'a zuwa gidansu sweety ba amma tabbas tasan y'ar hamshak'i ce daga yanda yaya yake bata labari zuwa yanayin d'abiunta ta shaida hakan,gashi tana ganin yanda take hawa motoci na kece raini, hakan yasa Nahnah baya baya don tsira da mutuncinta, dukda yawan zuwa gidansu da sweety take ita kam tak'i zuwa nasu gidan, kullum in ta dameta da mita sai tace tai hak'uri zata zo.

**********
Yau Nahnah ta kaiwa sweety ziyara inda taga abinda ya girmi tunaninta don gidane na alfarma agun, ko motoci sun kai 15 a gidan, abinda ya k'ara bata mamaki yawon maa'katan dake gidan haka suka rink'a zuwa suna gaidata kamar wata matar sarki, haka Auntyn su Sweety taketa ina taka saka da ita, da sauran k'annenta su haris, na yanda Nahnah taso awa biyu zuwa uku zatai a gidan ta tafi amma Sweety ta k'ek'ashe k'asa tace saita yini don itama in taje gidansu yini cur takeyi,
Haka badan taso ba ta zauna.

Kiran Abbansu sweety tai tayi a waya tana fad'a mishi Nahnah tazo ya dawo da wuri su gaisa.


Suna zaune a parlour sunata hira wata y'ar aiki ta shigo da kayan fruit yankakku tazo ta ajiye gaban Nahnah ta juya zata fita wata uwar tsawa sweety ta buga mata"keee jaka mahaukaciya, haka ake ajiye abu gaban mutane".

Jiki na rawa ta dawo ta k'ara gyarawa bowel d"in zama kan center table d'in.

Wani kallo Nahnah tabi Sweety dashi na rashin jin dad'in abinda tayi, ta kalli y'ar aikin tace "jeki abinki".

Bayan fitar ta sweety tace"Nahnah ya naga kin canja fuska haka?.

" gaskiya banji dad'in abinda kikai mata ba, ai d'an Adam ba abin wulak'antawa bane, dukda tana aiki k'ark'ashinku kinci zarafinta wlh".

Ta k'arashe maganar cikin yanayin b'acin rai,

"Hhhmmm Nahnah biki san way'annan y'an aikinba,basu da nutsuwa ko kad'an".

"Duk rashin nutsuwarsu basu can canci dizgi irin haka ba, tunda har Allah ya karrama d'an Adam ya dace muma mu karrama kanmu mu girmama junanmu, gaskiya sweety in har kina son mu shirya dake karki k'ara irin haka ba kyau irin hakan kinji".

Jin jina kai tai tare da fad'in "shikenan na daina Nahnah".

Cike da mirmishin farin ciki tace"yawwa my Sweety na gode da fahimtata da kikai".

Daga nan suka shiga wani zancen har Abbah ya dawo suka gaisa da Nahnah yaita sa mata albarka don shima zuciyansa na matuk'ar k'aunar Nahnah.

Da yamma Sweety ta dawo da ita gida a motanta, tare da tarin kayan kwalliya da turaruka Wanda ta had'a mata,sannan Auntynsu ta bata tirmin atamfa da wani less d'an ubansu da mayafi, sannan Abbah ya bata 20k Wanda tak'i amsa Sweety kuwa tasa mata cikin jakanta bata Sani ba, saida tazo gida ta gani. ta d'auka ta
kaiwa Yaya Haroon wai ya mayarwa Abban sweety ita bazata amsa ba, yaya yace " a'a ba haka za'aiba don Alh, baya son yayiwa mutum kyauta yak'i karb'a".

Don haka ya kirashi a waya yamai godiya, sannan ya bawa Aunty Hafsa kud'in yace ta ajiyewa Nahnah in tana buk'atan siyan wani saita bata.

Nahnah tai shiru can tace" yaya ba abinda zan buk'ata dasu,ka d'auki " 15k,ka bawa Aunty 5k".

Mirmishi yaya yai yana jin dad'in hankali da nutsuwa irinta Nahnah khadijah autar Baffah.πŸ˜€

K'irgo 5k Yayi ya mik'awa Aunty Hafsa,sannan ya k'ara k'irgo wata 5k d'in ya mik'awa Nahnah yace "to rik'e wannan a hannunki, karkice komai daga haka".

Badan zatai wani abu dasu ba amsa.








Taku ce
Y'ar mutan ja'oji.πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com



0⃣8⃣



Haka rayuwa taci gaba da garawa, lokaci yai nisa, Nahnah sun cinye semester sunyi exam har sunje tak'aitaccen hutu sun wuce T.P, nan wata secondary skul ta maza dake bayan gidansu taje, duk da taso zuwa ta bawa makarantarsu ta bada gudummawa, amma yaya ya bata shawaran taje wannan d'in,tunda itama Arabic skl ce, bata ja kan maganar yaya don haka kai tsaye ta zab'i wannan d'in, duk da tarin tsoron koyar da mazan da takeyi.

Ga

Please Login or Register in order to submit comment