Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mik'awa yaron kud'i yana karb'ar ledan da yake mik'omin kan cinyata yaja motan don lokacin har an bada hannu.

Motan na tsayawa k'ofar gidanmu naji farin ciki ya lullub'eni na bud'e mirfin cikin zumid'i na zan fice yace " Ke in kin shiga kice zan shigo mu gaisa".

Ina bud'e gate d'in naci karo da yaya na yana goge motarsa kasancewar weak end baya fita,da sauri na k'arasa gabansa cikin farin ciki ina cewa "yaya"
Shima cikin farin cikin yace "Nahna Oyo yoooo" duka dariya mukasa na zube k'asa ina gaisheshi ya amsa cikin fara'a yana tambaya ta ya gida yame gidan "Ai yaya tare ma muke dashi yana waje ".
" OK to shiga gamu nan shigo wa dashi ".

Da sauri na k'arasa ciki da sallama ina kwalawa su Ashra kira ai kuwa da gudu suka fito suna rungumeni nan Aunty ma ta fito da murnarta tana min sannu da zuwa, bayan mun gaisa naji sallamar yaya sun shigo,Sai sannan nake ce mata "Aunty tare fa muke dashi gasu nan shigowa da yaya". Da sauri ta tai d'aki don d'auko hijabin ta,
K'arasowa sukai parlourn ni kuwa inata faman wasa dasu Ashraf d'ina suna ban labari,anan Aunty ta fito tana mai sannu da zuwa bayan ta zauna suka gaisa cikin girmama juna ta mik'e tana fad'in " Bari a kawo ma ruwa ".

Mik'ewa shima yai yana " a'a wlh ki barshi tafiya ma zanyi".

Yaya yace "A haba Daddy ka zauna mana kasha ko D'an ruwan ne daga zuwa sai tafiya".
Mirmishi yai yana mik'ewa Ashraf kud'i yace" ba komai yaya wani lokacin inna dawo na sha".
Yaya yacewa Aunty " Tafiyar tashi ce fa ta taso wannan satin zai wuce ".

" Au Daddy tafiyar ce tazo,To Allah ya kiyaye hanya ya bada sa'a ".
Amsawa yake da "amin amin " ya fita yaya yabi bayan sa.
Bayan sun fita muka d'an fara hira da Aunty sai ga yayan ya shigo yana cewa "jeki zai wuce "
Mik'ewa nai cikin jin kunya na fita, a bakin mota na sameshi yace " In anyi sallar magriba a zanzo in d'auke ki "
"To Allah ya kiyaye saika dawo".
Juyawa yai ya shiga motan na shiga cikin gida.

Yinin ranar muna tare da Aunty tanata k'ara koyar dani dabarun zaman aure da yanda ake kula da miji .

Bayan sallar la'asar na tafi gidan yaya Haroon muka rungume juna da Aunty Amrah wadda naga cikinta harya d'an fito, itama dai k'ara min darasi take kan dai rayuwar sai gab da magriba na koma gida na koma gida, ina salla naci abinci banfi minti biyar da gamawa ba ya kirani a waya in fito yazo,anan ma saida yaya ya fita suka k'ara yin sallama yana mai fatan alkairi muka wuce.








Taku ce
Y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣1⃣



A hanya muka tsaya yai take away, sannan muka wuce gida, muna shiga ana sallar isha'i don haka kai tsaye toilet na wuce nai wanka sannan na d'auro alwala nai salla,ina kan sallayan ya lek'o d'akin karo na farko kenan daya tab'a zuwa " In kin idar ki Samar min abinda zanci don wannan abincin dana siya yai yaji da yawa"

Kafin ya k'arasa ma na mike ina nade abin sallar na saka riga y'ar k'arama iya gwiwata na fice " a zaune na hangoshi a k'aramin parlourn yana kallon ball,don haka da azama na shige kitchen d'in na fara k'ok'arin dafa mai ko jelof Na taliya ne.

Cikin 30 minutes na dafa mishi taliyan tasha kifi sai k'amshi take,lokacin danake zuba mai kuwa har yawunsa ya tsinke don shi akwai son dad'i, ina zaune gefenshi harya gama na tashi na had'a kayan ina cemai "saida safe " d'agowa yai ya kalleni tsaf sannan yace "OK"

Ni kuwa ina shiga d'aki handouts na d'auko nai karatuna Sama Sama don ina jin bacci, nan da nan kuwa bacci ya d'auke ni.

Yauma kamar kullum da asuba na tashi nai duk abinda zanyi na had'a break fast sannan nai wanka,ina shiga d'akinsa naga ya shiga wanka kafin ya fito na gama gyaran d'akin bayan ya fito na gaisheshi ya amsa na wuce toilet d'in na wanke.

A dining na sameshi muka karya,amma yau sai naga baici abincin da yawa ba, haka ma muna tafiya a mota naga sai d'an yatsina yake kamar bai jin dad'i, munje zai saukeni naga ya d'an matse cikin sa yana rufe ido ,tsayawa nai ina kallon sa yana bud'e ido muka had'a ido a sanyaye nace " baka da lafiya ne"
Girgiza min Kai yai alamar a'a nai Jim sannan na fice ina cemai "na gode "


Tunda muka fito a lecture nake kiransa ganin ban ganshi inda ya saba jirana ba in yazo, kusan kira biyar sannan ya d'aga wani iri naji muryansa " ki d'an jira na turo driver yazo ya daukeki".
Bayan ya kashe wayan saiga driver ya duk jikina a mace na shiga motan ina tunanin baida lfy daman naga alama tun safe amma yace ba komai .

Koda mukaje gida da azama na shiga parlourn a kwance na sameshi kan rugs yanata juyi dafe da k'irjinsa ban san sanda na ruk'o shi ba ina fad'in " meya sameka don Allah sannu ".
Damk'e hannuna yai yana cemin " Bani ruwa insha pls"
Da sauri na tashi na cire hijab d'ina na d'auko mai ruwan ina zuba mai a cup na d'aga kansa ina bashi a baki, saida ya shanye na dire cup d'in ina cewa " bari in kira sweety muje asibiti ko " girgiza kai yai yace cikin muryar Wahala "karki kira min kowa nasha magani zuwa anjima zai daina "
Haka mukaita zama ciwo baya baya sai gaba don rik'e k'irjinsa yai yana juyi cikin wahla yake fad'in " my god my god help me "
Ni kuwa sai salati nake ina mai sannu can naji ya fara kakarin amai da sauri na tafi d'aki na d'auko varf nasa mai nan yaita aman bayan ya gama na d'auko mai ruwa ya kuskure baki sannan naje na zubar,sanda na dawo naga ya fara samun relief don haka na zauna gefansa inata tunanin kodai in kira sweety amma ina tsoran Kar yace na tara mai jama'a, bacci ne ya fara daukansa Sama Sama na shiga d'aki don in watsa ruwa sabida zafin da akeyi sosai, da sauri sauri nai wankan na fito Nasa riga da skirt na Atamfa ina k'ok'arin fitowa naji kakarinsa da gudu na k'arasa na sameshi ya damk'e ciki yana wani kakkafewa salati nasa na fice da gudu zuwa part dinsu sweety, ina shiga na sami Aunty murja a kitchen tana ganina haka ta fara tambaya ta lfy, cikin tashin hankali nace mata "shine baida lafiya Aunty "
Salati ta fara tana biyo bayana,sanda muka shiga harya fice hankalinsa kamar ya suma juyawa tai da gudu ta kira ma'aikatan gidan maza da driver tace d'auko hijab d'inki mu tafi asibiti cikin kidima na d'auko suka d'aga shi zuwa mota a lokacin ma Aunty ta d'auko mayafinta ta fito"

Asibitin da suke ganin likita mukaje da gaggawa doctor sukai kansa don sun san Case d'insa, anan Aunty Murjah ta kira Abbah ta fad'a mai ta kira sweety don itama tana gidan ummu sulaim.
Zuwa lokacin idona yak'i tsaida hawaye wani Irin tausayinshi nakeyi ganin yanda yake jijjiga gadon da yake kwance sabida bala'in ciwon ciki, allura akai mai amma kamar ba'ayi ba,
Hannayena na cikin nasa inata mai addu'a ina tofa mai, a lokacin Abbah ya shigo ya shigo da sauri yana fad'in "Daddy sannu sannu kaji a garin yaya me kaci ciwonka ya tashi haka"
A lokacin nema su sweety suka shigo tare da ummu sulaim suna kar'asowa bakin gadon duk hankalinsu a tashe, ganin Irin hawayen dake gudu a idona yasa sweety dafani tana cewa "ki daina kuka Nahna zuwa anjima zai dawo normal, ulcer d'in sace ta tashi daman ciwonsa ne duk sanda yaci yaji ko yayane yana tashi ".

Cikin shashshek'a nace " Take away yai jiya da zamu dawo gida,kuma yacemin da yaji daman ".
Abbah shima cayai" kiyi shuru haka ki daina kukan kinji"

A lokacin ya k'ara wani juyi tare da k'ara damk'o hannuna yana Wani Irin kakari, kowa addu'a yake mai cikin tausayawa, doctor d'in ne ya shigo da alluran bacci yace kowa ya fita amma ganin irin rik'on da yai min yasa yace ni in tsaya, alluran akai mai wanda baifi minti biyar ba bacci me nauyi ya d'auke shi,dukda haka hannuna na cikin nasa,sai a sannan na sami nutsuwa naja kujera bakin gadon na zauna,lokacin har anyi sallar magriba,kasancewar period d'ina yayi ban tashi nai sallar ba ni, su Abbah suka k'ara shigo wa yace "yayi bacci ko " nace "eh Abbah"
Duk sannan su sweety suka shigo tace "Doctor yace sai zuwa safiya za'a sallamemu insha Allah yana farkawa zai dawo normal".

Muna nan zaune aka kawo Abinci daga gida akai akai naci nace " a'a sai dai zuwa anjima"

Sai k'arfe goma sukai shirin tafiya ummu sulaim ma Mijin ta yazo d'aukanta,Abbah yace Sai in zauna gun mijina,ga d'aya nan daga ma'aikatan gidan namiji za'a barshi ya kwana a receptions kozan buk'aci wani abu sannan za'a je a kawo mana duk abinda zamu buk'ata,
Sweety naiwa alaman tazo nai mata rad'a in zata had'o mana kaya ta d'auko min pants d'ina da pard tace to ba damuwa.

Bayan fitansu doctor d'in ya k'ara shigowa yace " in rage mai rigan dake jikinsa yaga yanata gumi sannan yace inya farka in bashi malt da d'an abinci kad'an" sanna ya d'aura mai drip ya fice .

Driver ne Ya dawo ya kawo min jaka da duk abinda zamu buk'ata,toilet naje na gyara jikina.

Bayan na gama duk abinda zanyi na dawo bakin gadon na zauna ina k'arewa fuskanshi kallo, kana kallonshi zaka gano tsantsan wahalar da yake ciki,wajan nakai k'arfe d'aya na dare zaune sannan bacci ya d'aukeni.

Juyi yai cikin wahala yana yatsina fuska yaji hannunsa d'aure da robar k'arin ruwa, bin robar yai da kallo na y'an sakanni sannan yai k'asa da idonsa,kallo ya bita dashi ganin yanda take bacci a takure kan kujera bakin gadon, ga hawaye bushashshe duk a gefen idonta,lumshe ido yai yana tunanin yanda ta rud'e taketa kuka dataga yanda jikinsa ya tsananta, yana a haka yanata tunani har bacci ya k'ara d'aukanshi.

Wajan k'arfe uku na farka sannan naga ruwan saura kad'an don haka na zauna ina jira ya k'are,baifi 10 minutes ba ya k'are na zare mai robar ,bud'e idonsa yai cikin yanayin bacci yana kallona nace mai "sannu ya jikin naka"
Lumshe ido yai yana amsawa cikin wahalalliyar murya,nace " in had'a na abinci"
Girgiza kai yai alamar a'a nace "ka daure ko maltina kasha doctor yace a baka wani Abu kaci "
Rufe idonsa yai muryanshi can k'asa yace" bari sai anjima"
Daga haka bai k'ara cewa komai ba,ina tsaye kansa kusan minti goma naji yana sauke numfashi alamar ya koma bacci,don haka na koma Nima na zauna anjima kad'an bacci ya k'ara d'aukana.

Ban k'ara farkawa ba sai asuba ina tashi toilet d'in na shige nai wanka na gyara jikina bayan na fito nasa kayana da Hijab d'ina tunda bana salla sai azkar nai, inata zaune ina kallonsa naga bai ko motsawa ba sai wajan k'arfe bakwai saura sannan ya farka matsawa kusa dashi nai ina mai sannu sannan nace "bari in had'a ma ruwan wanka ko"
D'aga kai yayi, na shige toilet d'in kasancewar da heater a ciki na sirka mai ruwa me zafi,na fito ina fad'a mai na had'a, mik'ewa yai yana rik'e da k'arfen gadon ya daddafa ya shige toilet d'in.
Bayan ya fito na ciro mai jallabiyar da aka kawo mai,yasa na k'ara mai sannu,maltina na juye mai a cup na mik'a mai, ya amsa cikin sanyin jiki ya kafa kai yana sha kad'an kad'an,a sannan sweety ta k'wank'wansa k'ofar naje na bud'e mata muka sakarwa juna murmushi na matsa ta shigo gaisawa mukai tana tambayar ne jiki nace "da sauk'i " zama tai kan gadon kusa dashi tana tambayanshi ya jiki " ya amsa cikin d'an sakin fuska ,kallona tai tace "Aunty na muna ta kiran wayoyinku duk ba'a d'aga ba"
D'an bud'e ido nai nace "Ai Duk suna gida wayoyin "
"OK to ga abinci nan Abbah yace kuci sosai kafin yazo ,wanka kawai zayyi yanzu zaizo".

Tashi nai na d'auki flat na zuba mai chiefs nasa spoon,na kawo mai ,karb'a yai ya fara ci naga ya d'ago kai yana kallona can naji yace " Ke bazakici ba"
"Um sai anjima banson karyawa da safe haka "
Bai k'ara magana ba sai sweety ce tace "amma ai Kinga kin kwana bakici abinci ba na tabbata yanda muka barki jiya bikici komai ba"
Kauda zancen nai ta hanyar cewa ta bani aron phone d'inta ,mik'omin tai nan nasa number d'in yaya na bugu d'aya ya d'auka nake fad'a mai asibiti muka kwana Daddy baida lfy'
Jajantawa yai sannan yace inya fito office anjima zai shigo ya dubashi .
Bayan na kashe naga ya zuba min ido kamar zaice wani Abu kuma naji yai shiru,
Muna zaune a haka sweety na d'an janmu da hira kad'an kad'an, a sannan Abbah ya shigo tare da Aunty murjah da sauri na tashi kan kujerar da nake zaune ina mai sannu da zuwa, amsawa yake tare da fad'in "a'a Daddy na jiki yai sauk'i Alhamdulillah,sannu kaji " shima cikin y'ar fara'a ya amsa suka gaisa da Aunty murjah ma,tsugunnawa nai na gaishesu cikin ladabi suka amsa suna tambayata me jiki na amsa da sauk'i, A sannan doctor ya k'ara shigowa ya dubashi yace za'a k'ara mai allura wajan k'arfe goma sai a bamu sallama tunda ya dawo normal.

Bayan fitan doctor Daddy ya gyara kwanciya yana cewa "Abbah yarinyar nan fa bataci abinci ba na mata magana wai ba yanzu ba"
Juyowa Abbah yai yana fad'in " Haba Khadeejah ya zaki zauna da yunwa haka Kinga jiyama fa k'inci kikai kema Kar ulcer d'in ta kamaki fa,Sweety zuba mata taci kinji"
"OK Abbah bari ma in zuba mana muci tare don Nima banyi break d'inb"

Nidai cakula kawai nake don duk kunyar Abbah ta hanani sakewa duk yanda yake k'ok'arin Jana a jiki amma na kasa sakewa in daina jin kunyarsa,kula da hakan da yai yasa shi fita waje nan na samu na d'anci da yawa na mik'e.

Anjima kad'an suka shigo tare da yaya na,
Bayan sun gaisa da me jikin yamai sannu sannan Nima na matsa kusa dashi ina gaisheshi rik'o hannuna yai yana tambayata me jikin na amsa da sauk'i, ya d'an jima a tsaye yai sallama damu ya wuce office,
K'arfe goma doctor yazo ya k'ara mai allura tare da bashi magunguna kuma ya k'ara gargad'insa da cin yaji komai k'ank'antarsa,don ulcer d'insa bata son yaji ko kad'an,sannan ya sallamemu, sweety taja mu da Aunty murjah zuwa gida Abbah kuma ya wuce kasuwa.

Kwanaki biyun da yai jinya duka cikin kulawata yake sosai nake bashi kulawa,shi kuma ma yanda na lura har wani k'ara shagwab'emin yake kodan yaga hankalina ya tashi da ciwon nashi ne oho, abin yana baka'in d'auremin kai yanda nake ganin sauyi tare dashi in yaimin wani abun har tunanin nake araina kodai UK ya fara sona ne kamar yanda na yarda tabbas zuciyata ta fara kamuwa da son sa sabida lokaci lokaci ina zama inyi tunaninsa har inyi mirmishi,hak'ik'a addu'ar da nakeyi koda yaushe cikin zamana dashi ta fad'a akaina tunda gashi zuciyata ta fara kamuwa da k'aunarsa,duk da shima kamar canji ya fara samuwa cikin kwana uku kacal,
Yau Alhamis in Allah ya kaimu gobe juma'a k'arfe tara na dare jirginsu zai tashi,yau d'in da wuri yai shirin fita don yaji k'arfin jikinsa sosai yana son yaje yaiwa y'an uwa sallama,ina tsaye a dining ina serving d'insa na zuba mai kunun gyad'a na d'an juyo na kalleshi naga yana kallona,k'asa nai da murya nace "in k'ara maka koya isa"
Kallona yai ido cikin ido yace "me kika maidani ne,wannan uban kunun kuma kina maganar ki k'ara min"
D'an mirmishi nai kawai na bud'e gwangwanin madara na zuba ina juyamai duk abunda nake idonsa na kaina, harna juya na bud'e flask na zuba mai lafiyayyan k'osai dayasha albasa,bayan yaja ya fara ci naga ya lumshe ido alaman yamai dad'i d'an mirmishi nai na d'aga wayana na kira Hafsa a waya ina tambayarta ya lecture, dariya tai tace "ai Ke ango ya b'oyeki,ya jikin nasa"
"Hhhmmm da sauk'i me jiki, kinsan gobe in Allah ya kaimu zai tafi to ina d'an . . . ."
Rufe bakina nai sanda na tuna a inda nake maganar Kar nai sub'utul kalam, Aunty ummy wata y'ar department d'inmu matar aure ce da y'ay'anta biyu muna shiri da ita sosai,ita ta amshi wayar tana cewa "Sis yi zamanki ki kula da mijinki kinji duk abinda akai in kin dawo zamu nuna miki ki zauna ki nemi lada"
y'ar dariya nai nace "To Maman boy zan kula sosai "
"Yawwa sis ki dage fa kinji "
Dariya kawai nai na kashe wayan, sweety na k'ara kira tana d'agawa nace "nayi mutuminki kunun gyad'a gashi kina school"
"Don Allah da gaske Aunty na,don Allah ki samin a flask in na dawo zan sha"
"OK zan ajiyemiki har ki dawo yana jiranki "
Bayan na kashe wayan naga yana turomin cup d'in gabana "kina neman kai da kununa to ban yarda ba ki k'aramin one cup kuma ki barmin sauran cikin flask d'in in na dawo zansha "
Dariya nake gintsewa na yanda yake cewa da cup d'aya ya isheshi amma gashi yanzu yana neman k'ari "
Saida ya kuma shan cup guda sannan ya mik'e yana fad'in "zanje inyi sallama da y'an uwa kafin in dawo ki k'ara yimin Irin d'an waken jiya "
Mik'ewa Nima nai ina cewa "To a dawo lfy,insha Allah kafin ka dawo an maka"
Juyawa yai ya fice,ni kuwa daman aiki ne dani sosai,
Don haka na shige kitchen na fara had'a snacks kala kala don nai mai tsaraban tafiya. . . . .. . ..




https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?



Taku ce
Layuza kabir Adam πŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣2⃣



Sosai na zage naita aikina,kasancewar akwai isassun na'urori don haka cikin sauk'i nai komai na gama,d'an waken ne ban mishi ba sai bayan la'asar sosai don nasan zai iya kai magriba bai dawo ba don karya huce, hai wanka na tsaf na shirya cikin riga da wando sak'ar Pakistan na gyara kaina na jera mai ribbons k'anana masu kyau ban d'aura d'an kwali ba,nasa d'an kunne da sark'a suma na k'asar Pakistan d'in,sannan na bad'e jikina da sanyayyan turare,nan da nan na fito d'as dani kamar y'ar k'asar, k'ara gyara gidan nai sosai na turarashi da turare,ina zaune a k'aramin parlour ina jiran akira sallar magriba Aunty Hafsa ta kirani tace min da k'aninta nan Isma'il ta bashi sak'ona ya kawo min yace yazo yana k'ofar gate in aiko biyeni 'amin,nai mata godiya tare da kashe wayan, Hijab d'ina nasa na fita na sami d'aya cikin ma'aikatan gidan na fad'a mishi akwai bak'o a baking gate don Allah su amso min sak'o a gunsa, ina nan tsaye naga an bud'e gate d'in gidan mota ta shigo, ta cikin glass na ganshi muka had'a ido, bayan yai parking na tsinci kaina da k'arasawa gefen mirfin motar ina bud'ewa tare damai sannu da zuwa, D'an sakin fuskarsa yai yana amsawa a sannan ne wanda na aika ya kawomin watan k'atuwar leda na karb'a ina mai godiya, bin ledar yai da kallo bayan ya fito daga cikin motar,gaba nai shi Kuma yana biyeni har zuwa part d'in namu,ina Shiga na ajiye ledar ina cire hijab d'in dake jikina, nai baking standard fridge dake palourn na d'auko mishi robar ruwa me sanyi tare da glass cup,tsugunnawa nai gaban kujerar da yake na zuba mai ruwan ina mik'a mai,yana karb'a yace "tnx"
Bayan ya shanye ya mik'omin cup d'in tare da mik'ewa ya shige d'akinsa, binsa nai d'akin, ya juyo yana kallona ganin na biyoshi ban damu ba na shige toilet na had'a mai ruwan wanka da turaruka masu k'amshi na wanka, na fito ina cemai "ga ruwan wanka na had'a ma"

"OK tnx" ya fad'i yana k'ok'arin cire kayansa.

Bayan fitowansa daga wanka ya zauna bakin gado yana tunani a ransa shin wai yarinyar nan me take nufi da wannan hidimar wai duk mata daman aikinsu kenan a gidan miji, kai haba gaskiya bazai zama haka ba,kawai dai maybe itace me hidimar,ya dad'e zaune yana tunanin abubuwa masu yawa game da ita,ya gano wasu qualities tare da ita tanada kirki da girmama babba,tanada tausayi da k'ok'rin faranta ran wanda take tare dashi koda hakan zai bak'anta mata,ya dad'e zaune yana tunanin ganin hakan bazai masa ba yasa ya tashi ya wuce toilet d'in.

Ni kuwa na gama shirya table tsaf ina jiran fitowansa,inata zaune ina jiransa har aka kira salla na wuce d'aki don gabatar da sallah.

Ina tsaye bakin mirror ina fesa turare ya turo kofan yana fad'in "Azo a bani abinci ina jin yunwa sosai"

K'asa k'asa nai da idona ina dubansa nace "OK ina zuwa kad'an "

Ya juya

Please Login or Register in order to submit comment