Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'ina kika kwanta bacci har k'arfe tara".


Da sauri na kalli agogo saina fara k'ok'arin sakkowa a gadon ina daddafawa tare da rik'e mara irin dai na masu tsohon ciki. Wani wawan tsaki naji yaja tare da sakin k'ofan d'akin ya juya,jiki a sanyaye na k'arasa sauka zuwa toilet nai fitsari ko wanka ban tsaya yiba na wanke fuskata na fito,sauka nai zuwa kitchen d'in k'asa na fara k'ok'arin had'a me saukakken abun karin kumallon, doya da k'wai na soya tare da daga ruwan tea daya sha kayan k'anshi, sai sauran parfesun jiya na d'umamashi, zuwa nai na kwashe duka kayan dining table d'in anan naga uban abincin daya d'iba,girgiza kai kawai nai na kwashe kayan tas nakai kitchen sannan na gyarashi na jera mai girkin.
K'ararrawar d'akin masu aiki na danna,bayan Lami ta shigo nace tayi wanke wanke ta gyara kitchen d'in, sannan na koma d'akina.


Wanka nai na tsara kwalliya bame tsauri ba sannan na shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi don yanzu babu kayan da nake jin dadin su kamar dogayan riguna, turare na feshi jikina dashi sannan na fito zuwa d'akin nasa inata knocking ba'a amsa ba nai tunanin kulawa ne bazai ba dana lek'a k'asa ta tsakiyan k'arfinan da akaiwa corridor d'in ado dashi saina hangoshi yanata uban kwasar girki.
d'akin na shiga na fara gyara mai dukda dai komai k'arfin hali nakeyi,sabida yanayin jikin nawa,na wanke mai toilet tas tunda daman ba wani datti bane ,sannan nasa mai freshener na d'akin ya d'au k'amshi, ina k'ok'arin fita ya turo k'ofar ya shigo,matsawa gefe nai na bashi hanya,baiko kalleni ba ya wuce risinawa nai kamar yanda na saba na gaisheshi ciki ciki ya amsa min ya wuce bakin gadon ya zauna yana saka safa da takalma, jinai zuciyata ta karye hawaye ya kunshe min,a sannu na k'arasa gabanshi na tsugunna tare da rik'o k'afafunsa cikin shashshekan kuka nake fad'in "Ka yafe min mijina ka yafewa laifina,insha Allah bazan sakema laifi makamancin wannan ba,wannan d'in ma bansani ba rabo ne ya ratsa bansan na samu wannan cikin ba".

D'aga min hannu yai cikin razanarwa " karki raina min hankali mana ,don kin maidani gara zakice tsautsayi ne, in rabo ne me yasa da kikaga cikin ta bayyana biki sanar min ba tunda wuri insa a zubdashi,ai na fad'a miki ban son haihuwa yanzu ban shirya zama baba ba yanzu,d'an yaro dani anmin aure cikin shekarun k'uriciya na hak'ura na amsa kuma ma sai ciki sai haihuwa, shi kenan mutum ya zama tsoho, wlh impossible, badai dani ba".

Yana kaiwa nan ya janye k'afar sa yabar d'akin.

Niko nace( ohπŸ€” me hali baya fasa halinsa,anata murna UK ya shiryu ya gyara d'abi'unsa ashe da sauran rina a kaba)

Bin bayan sa nai da kallo ina share hawaye na,cikin zuciya ta nake rok'on Allah ya dafamin ya kawo min agajin sa cikin lamarin nan.


Yana fita kai tsaye gidan su ya shiga don jiya yana cikin damuwa Sam bai samu damar komawa sun k'ara gaisawa dasu ba.

Yanda Abba yai tunanin ganin sa cikin tsananin farin ciki ba haka ya ganshi ba,don fuskar nan tashi d'aure tamau yai sallama cikin parlourn Abban ya shiga, binsa yai da ido yana mirmishi yace "Babana ka samu fitowa ".

Zama yai sosai gaban Abban yana d'an kalato fara'a ya risna ya gaida shi,cikin farin ciki yake amsa mai tare da tambayar sa ya hanya ya gajiya kuma.

Cikin d'an yak'e yace " Abba gajiya ta gudu sai abunda ba'a rasa ba".

"To masha Allah, ina fatan dai komai lfy ko".

" eh Abba,ina Aunty murjah ?".

" Taje kawo min abinci ,amma kuma Daddy ya naga fuskar ka kamar da matsala".

D'an shafo gashin sa yai yana d'an tsakin gefan baki yace "A'a Abba ba komai kawai kaina kemin ciwo tunda na tashi a bacci amma na sami magani ma a gidan nasha".

"To Allah ya sauwak'e gajiya ce kawai kuma daka sani ka kwanta ka huta sosai zuwa azahar sai ka fito".


Zaiyi magana Aunty murjah ta shigo d'auke da kayan Abinci fuskar ta kuwa cike da fara'a tace" A'a mutanan k'asar Hindu har ka fito ".

Cikin mirmishin yak'e yake gaisheta bayan ta sauke kayan abincin, zama tai tana amsa mai da tambayar sa ya gajiyan hanya,sannan ta had'awa Abba abincin suna d'an hira kad'an kad'an .

" Daddy matso muci Abincin mana".


Girgiza kai yai yana fad'in "Wlh Abba a k'oshe nake sosai yanzu na gama break fast".

Dariya Aunty murjah tai " Haba Abba kaima dai tsokana kakeyi yaushe zaici abincin mu ,bayan kasan y'ata ta cika mai ciki da kayan dad'i ".

Dariya sukai ita da Abba amma shi kam d'an mirmishi yai yana shafa kansa.


Jimawa kad'an Aunty murjah ta tashi ta basu waje don su D'an tattauna, Abba nacin Abinci suna hira yana mai tambayoyi kan karatun nasu da company nin da suka bud'e.


Yaso cinye maganar cikin nan Amma abun bazai cinyu ba,don haka ya k'ara gyara zama yace " Abba kasan sama Khadeejah nada ciki".


Fara'ar Abba ce ta yalwata yace "Eh na sani mana Daddy nah, amma nima bai wuce Wata biyu dana sami labarin ba,nai farin ciki kuma na godewa Allah me kyauta da k'ari don shine Abun godiya".


"Amma Abba meyasa kaima da kake tare dasu gida d'aya baka sani da wuri ba sai wata biyu da suka wuce".


Cikin dariya yace " An fad'a min uzirin dayasa ba'a sanarwa kowa da wuri ba ".


" To Abba Amma meyasa baka sanar dani ba tun ina can".

"A'a ba ruwa na ance min karna sanar dakai don sai dama na d'au alk'awarin bazan sanar dakai ba sannan aka fad'a min ciki,don ance ana son yin surprise d'inka ne,shine gift d'inka ".


D'an cizan gefan bakin sa yai cikin taikaci yana tunanin rainin hankalin da yasa ta b'oye mai ma .


Dafo kafad'ar sa Abba yai yana d'an bugawa a hankali " Karka damu my boi ai babban abun farin cikin samun cikin fatan mu Allah ya rabasu lfy,komai abun buk'ata na riga da na gamai musu, yanzu haihuwa kad'ai muke jira Allah ya baku masu albarka,kar kasawa kanka damuwa kan rashin sanin da cikin kaga yanzu daka sani ai farin ciki ninki ninki kenan abunda baka Sani dashi ba unexpected ka ganshi sai godiyar Allah ko ".


Cikin ransa yake mamaki wato Abba zahirin farin ciki yake da wannan cikin harya gama mai hidima ko.


Jin Abban ya dafoshi yasa yai saurin k'irk'irar mirmishi,yace " zo muje ka rakani unguwa in kan ya daina ciwon".

"Ok ba damuwa Abba".

Mik'ewa sukai suka fita zuciyar UK cike taf da tunani da b'acin rai.


Bayan na idar da sallar azahar ina zaune kam prayer mat ina addu'a, naji knocking d'in sweety a bakin k'ofa "Aunty nah in shigo ko in koma ".

Shafawa nai ina fad'in" Me zai hanaki shigowa sis ".

Turo k'ofan tai ta shigo taja stool ta zauna idonta cikin nawa ,zama nai nima bakin gado ina fad'in " sai yanzu kika shigo tun safe".


Y'ar dariya tai tace "wlh Aunty na bacci nai sosai sai around 12 na tashi Aunty tace min broth d'in ma ya shiga yana tambaya ta ".

" hmmm y'ar hutu sannun ki".

"Hhhhhhhh ba wani y'ar Hutu kawai dare na raba ina aiki a system wlh. Amma sai naga idonki kamar kinyi kuka ".

K'ok'arin danne damuwa ta nai nace " ah haba wane kuka zanyi kuma,kawai ban sami ishashshan bacci ba,kin San wannan babyn naki tunda ya girma bai barina baccin kirki".

Zuba min ido tai tana son fahimtar gaskiyar zance na, "Amma Aunty nah . .".

Shiru tai kuma kawai
Nace " ya kikai shiru ?".

Mirmishi tai tana girgiza kai "A'a kawai dai ina son kiyi hak'uri da duk abunda zaki gani daga broth, kar kisa wani Abu a ranki kinga hawan jini baida dad'i game ciki kuma damuwa ke kawo shi.


" karki damu sis ba komai kinji".

Jinjina kai tai daga nan muka shiga hira.



*********
Yau kwanan sa biyar da dawowa babu abunda ya canja tsakanin mu, zan mai girki yaci in gyara mai d'aki, iya kaci inna gaisheshi ya amsa a ciki ciki daga nan kuma ba wata kalma da zata k'ara had'a mu.

Duk yanda nakeson dannewa abun ya faskara kullum bana bacci amma ban gajiya da kaiwa Allah kukana, abun yana ban mamaki da d'aure min kai ace d'an Adam Allah yai mai kyautar d'a guda amma ya rink'a nuna k'iyayyar abun a zahiri, abunda yake k'ara sani cikin damuwa shin haka zan haifi d'an ya taso babu soyayyar uba,wannan ke k'ara samin damuwa matuk'a.




********
Cikin dare yana kwance kan katafaran gadon sa me cike da ni'ima amma babu wani walwala a tare dashi, buk'atar daya tara ta tsawon lokaci ce ke taso mai, juyi kawai yake yana damk'e marar sa data d'aure mai tamau,tun saukar shi garin yake jin wutar sha'awar shi na ruruwa gashi Khadeejah tasa waigi tsakanin shi da ita,ta b'ata mai ta ha'ince shi, yanzu badan wannan cikin ba da yanzu ya kauda k'ishin dake damun sa,da tuni yanzu suna kwance jikin juna suna shan soyayyar su tabbas da yasan da labarin cikin nan tun yana karami babu abunda zai hana yasa a nik'eshi.

Tabbas yana son Khadeejah so mai tsanani yana jinta can cikin k'asan ransa,amma wannan b'acin ran ya danne komai yanzu in banda haushin ta babu abunda yakeji. Ko son kallon ta bai yi,don in ya ganta ma b'acin rai ke taso mai, ya zama dole ya nemawa kansa mafita,bai k'aunar auran mace sama da d'aya a rayuwar sa,amma yanzu tunda Khadeejah ta zab'awa kanta haihuwa to zai barta da haihuwar zaije ya nemo matar wuce sa'a wadda bazata tara mai yara a gida ba,kawai don soyayya zai aureta,don shi baiyi aure don ya haihu ba.







*Taku* *ce*
*Y'ar* *mutan* *ja'oji* βœπŸ™‹
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*'YAN* *ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
πŸ“
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_



*ALLAH* *KAI* *KAD'AI* *KASAN* *DAMUWAR* *DAKE* *K'ASAN* *ZUCIYA* , *ALLAH* *KA* *KAWAR* *MANA* *DA* *DUKKAN* *DAMUWAR* *MU* πŸ™πŸ™πŸ™




0⃣5⃣0⃣



Damuwar da nake ciki ta wuce zuciya har ta fara bayyana a zahirina,duk yanda nake k'ok'arin b'oyewa abun ya wuce haka,yau tsawon sati biyu da dawowar sa amma kullum cikin bak'in ciki nake yini ina kwana babu sassauci tsakanin mu, duk iya hakkin sa dake kaina ina iya k'ok'arin saukewa amma shi ya gagara sauke nawa ko guda d'aya.

Yau kam na tashi jikina ba dad'i gashi wancan satin ban samu naje awo ba,don haka yau nace mai ina son zuwa ganin likita in kujerar da yake zaune ta ban amsa to shima ya bani,haka nq gama magana ta na tashi na fita. Banda inaiwa Allah na biyayya da babu abunda zai hanani fita a wannan ranar don ni kad'ai nasan ciwon da nakeji a tare dani, a daddafe nake har yamma sweety ta shigo kallo d'aya tai min ta gane halin da nake ciki, bayan ta zauna ta rik'o hannu na" Aunty na ya dai na ganki a haka ko baki da lfy "

D'an cije bakina nai cikin son basarwa nace " kawai kin san yanayin jikin namu sai a hankali".

Cikin nuna tausawa tace "Ayya sannu Allah dai ya rabaku lfy,ai an kusa insha Allah".

Mirmishi nai ina cije ciwon da nakeji, a hankali take jana da hira da son kawar min da damuwar data gani kwance kan fuskata, ni d'in ma cikin k'arfin hali nake b'iye mata har aka kira magriba ta wuce gida nima na tashi don yin salla.

Bayan sallar isha'i na samu da kyar naci abinci ba kwanta don wani zazzab'i ne me zafi ya rufeni, sosai nake kakkarwa har hak'ora na na had'ewa cikin ikon Allah a haka wahalallan bacci ya d'auke ni ,duka duka na awa guda nai na farka da wani sabon ciwon mara tun ina juyi kan gado harna sakko k'asan rug inata murk'ususu da ambaton Allah, tsawon awa biyu na d'auka ciwon ba sassauci a sannu na d'aga kai ina kallon agogo duka duka lokacin k'arfe d'aya na dare, koda ban tab'a haihuwa ba amma inaji a raina wannan yai kama da ciwon nak'uda nake yi, amma ya zanyi ko in kira sweety a waya ne ko dai Aunty Hafsa zan kira ,na rasa me yakamata inyi nasan a wannan halin ko na kira UK bai zama lalle ya kula dani ba, don haka kawai na mik'a kamarina ga Allah nasan ya isar mini, Hukunci na ubangiji wajan k'arfe biyu wani wahallan baccin ya sake d'aukata ina jingine jikin gado shikam ban San iya lokacin dana d'auka yin saba,nadai san bawai dad'in sa nakeji ba, cikin mafarki naji ciwo na k'ara sand'ata inayi sannu sannu harna farka tofa tun daga lokacin ganga ganga ya taso min ba sauk'i yi nake inaji kamar raina ne zai fita kiran sunan Allah nake ina neman d'aukin sa.
A kunnena aka fara kiran sallar Asuba har aka shiga masallaci a lokacin k'arfi na ya gama k'arewa numfashi ma da k'yar nake fiddawa, ina kwance kamar kaya.

UK ya dawo sallar asuba har zai wuce d'akin sa sai ya tuna yau k'arfe shida zai fita don katsina yake son zuwa ya gaida su kuma a yau yake son zuwa ya dawo don haka bari ya sanar dani in had'a mishi break da wuri.
Yana turo k'ofan ya ganni kwance yai zaton ma bacci nakeyi a k'asan amma me sai yaga jini na bina da sauri ya k'araso cikin d'akin yana fad'in "Ke Khadeejah Khadeejah ".

Idona na rufe ruf alamar ma ban cikin hayyacina a firgice ya k'araso ya d'aga ni yana jijjigani da kiran sunana, amma ba amsa tsoro ne ya kamashi yace " innalillahi kar dai rasuwa tai" ki yai gaban sa ya fad'i kwantar da ita yai ya fice a guje zuwa d'akin sa ya d'auko wayar sa bayan ya dawo d'akin ya k'ara d'agoni jikin sa yana kakkarwa ya fara lalubo number d'in mutan gidan su duk Wanda ya kira tak'i shiga sai da yai tayi sannan ta Abba ta shiga yana d'awaya yace "Abba Khadeejah Khadeejah Abba kuzo don Allah".
Cikin d'imuwa Abba yace " ba lafiya ne UK to gamu nan zuwa".

Aje wayar yai yana hura min iska a hanci na,wani numfashi naja ina ambaton Allah dishi dishi nake kallon sa murya can k'asa nace " Reality Kaine?".

"Nine Khadeejah nine sannu kinji ".

" ka yafemin laifin da nai maka mutuwa zanyi ka yafe min".

". Kiyi shiru ki daina cewa komai Khadeejah kinji".

A haka su Aunty murja da sweety suka fara knocking " Aunty Ku shigo k'ofar a bud'e take ".

Da sauri duk suka turo k'ofar ganin jinin dake bina yasa Aunty sakin wani salati tana fad'in" garin yaya ka barta haka da ciwo Daddy".

Girgiza kai yake yana fad'in "Aunty nima yanzu na risketa a wannan halin,muje asibiti ".

Ciccib'ota yai da gudu gudu suka fito inda Abba yake cikin mota harya kunnnata su kawai yake jira don ko takan driver bai biba, baya yasata shida sweety Aunty ta zauna gaba, tafiya suke kowa cikin tashin hankali bamai magana,tafiya bamai yawa ba ta sadasu da family hospital d'in su, cikin gaggawa aka karb'eta zuwa maternity.


Zaman awa uku cif sukai ba wani k'ok'k'waran bayani duk likitan daya fito sai dai yace musu su k'ara Mata addu'a ta kusa. su yaya haroon da suka zo tun d'azu suma suna zaune sunyi jigum jigum kowa bakinsa d'auke da addu'a.

Tunda nake ban tab'a tunanin ciwon nakuda yakai haka ba,duk da inajin yanda ake fad'ar sa,kuma ansha yin nakuda a gabana amma yau danaji ciwon a jikina na tabbatar iyayen mu sunyi jihadi wajan haihuwar mu,ciwo ne wanda bashida misali,rok'on ubangiji nake ya karb'i raina in huta,don k'arfina ya k'are, ko hannuna ban iya d'agawa duk iya rarrashin da nurse's d'in nan da suke min kan inyi nishi abun ya faskara na kasa, UK kuwa da yake kaina rik'e da hannayena zuwa lokacin yai kuka ya k'oshi likitocin sunyi sunyi ya fita yak'i, don har mari ya kusa tsinkawa wata nurse data Dame shi kan ya fita,ca yake ai mata ta tace kad'ai a d'akin babu inda zanje Ku kashe min mata ta".

A hankali nake mai alamar ya sunkuyo inmai magana,cikin muryata dabata fita nace "Kayi hak'uri zan mutu kana fishi dani,don Allah ka yafemin ko ban haihuba na mutu ka yafemin ka rink'a bina da addu'a. . . . in kuma na haihu don Allah kayi hak'uri ka nunawa abunda na haifa gata ka kaunaceshi,bana so d'ana ya tashi da rashin soyayya mahaifi da maraicin uwa kuma,ka yafemin kaji mi . . .

Ban k'arasa ba idanuwa na suka rufe,
Wata gigitacciyar k'ara ya saki yana fad'in" Karki tafi don Allah Khadeejah karki mutu ki barni wlh ina sonki ban gaji da zama dake ba,ki taimaka min Khadeejah ki tashi wayyo Allah mata ta".


Kukan sa ya k'ara jawo hankalin jama'ar dake waje har y'an gidan mu suka k'araso wajan d'akin a rude ta window suke lek'awa suna tambayar mene ne amma gunjin kuka kawai hakan yasa suma sakin kuka don tunanin su kawai na rasu , likitocin da suka shigo d'akin suka k'ara dubani nan suka tabbatar musu da raina suma nayi,kuma ya kamata a gaggauta yin aiki a cire min cikin.


Da k'yar Abba ya lalkab'ashi ya sami nutsuwar yin signing kan takardar cs d'in da za'a min.hankalin y'an uwa ya k'ara tashi wasu na kuka wasu na salati,shi kuwa gogan cikin firgici yake fad'in " don Allah kuyi kuyi mata aikin nan Ku cire mata wannan cikin mata ta nake buk'ata don Allah karku bari ta mutu, kin gama Khadeejah bazaki k'ara haihuawar nan ba kin gama ta batada amfani".

Ganin yana neman zaucewa yasa Abba kamoshi zuwa kafad'ar sa yana bubbuga bayan sa"cool down my man kayi shiru haka kaita mata addu'a zata tashi insha Allah, zata tashi bazata tafi ta barka ba kaji ".

Cikin shashshek'ar kuka yake fad'in" Abba ka sani fa ka sani a irin haka mamy ta rasu muka rasa ta a gun haihuwa mamy ta rasu ga Khadeejah ma zata mutu wajan haihuwa ".

K'wallar data taru a gefen idon sa ya share da hannun yana jijjiga kai don shima Abba cikin rud'ani yake,haka mamy tai haihuwar sweet taita zubda jini harta rasu,don haka yake jin mutuwar ta ta dawo mai sabuwa A yau duk ya rud'e shima.



Duk abunda ya kamata anyi aiki kawai za'a shiga da ita yanzu.yanda aka turo ta kwance akan keken zuwa d'akin operation d'in ya k'ara saka y'an uwa cikin rud'ani sunata d'aga mata hannu da fatan dacewa.


UK dai kuka yak'i k'arewa kamar k'aramin yaro rik'o hannunsa Abba yai suka shiga masallaci dasu yaya haroon don yin sallar azahar, ko bayan da suka idar ca yai mai ya zauna nan suyita nafilfili do rok'on Allah yasa ayi mata a sa'a.


Likitocin kuwa nata k'ok'arin su wajan ganin komai ya tafi dai dai, sunyi nasarar ciro mata 'ya mace masha Allah nan nurses suka fito da ita don a gyara ta su kuma likitocin na k'orarin mata d'inki.

Su Abba yaya haroon yaya usman da uban gayyar na masallaci tun sallar azahar basu fito ba,don haka koda aka fito da Babyn basa gun su Aunty murjah ne sukai ribibin karb'arta suna godiya ga Allah duk da duk hankalinsu naga son ganin halin da za'a fito da uwar hakan bai hanasu farin ciki da nuna godiyar su ga Allah ba.

Bayan sallar la'asar su Abba suka fito a masallaci suna k'arasowa ana fito da ita daga d'akin zuwa d'akin hutu itada matacciya ba maraba,don haka jiki a sanyaye sukabi bayan su, bayan an d'ora ta bisa gadon likitan dake tsaye ya tsawatar kan banda magana ko motsi me k'arfi a d'akin insha Allah zuwa magriba zata iya farfad'owa.


Nan akai ta kiran y'an uwa da abokan arziki ana sanar dasu haihuwar, kowa dai ya sami sukuni zuwa yanzu amma banda UK fatan shi dai yaga matar sa ta farka.

Sweety na gefe rungume da baby da take nannad'e cikin farin over role da towel sai baccin ta take,zubawa Babyn ido tai tana d'an mirmishi tace "Aunty hafsa kinga Babyn nan kamar su d'aya sak fa da broth komai nata ".


Mirmishi Aunty Hafsah tai tace "gaskiya kam kunwa yarinya ta wayo babu abunda ta d'auko nata duk gidan ku tayo".

Murna fal kan fuskar sweety ta k'ara rungume Babyn a jikin ta tana jin k'aunar ta na ratsata.



******
Duk yanda ake zaton zan farka da wuri ban farfad'o ba sai cikin dare cikin ikon Allah kuma sai na farka cikin hankali na bakina d'auke da salati, Aunty murjah da Aunty Hafsah da suke tare dani suka yo kaina suna fad'in " Khadeejah kin tashi sannu sannu kinji ".

Lumshe idona da yai min nauyi nai ina son tunano abunda ya faru dani amma na kasa tuno komai,don haka nabar idon a lumshe ina son samun nutsuwa, UK dake zaune a parlourn yaji kamar suna ambatan sunana hakan ya tabbatar mai na farka, da sauri ya turo k'ofan ya shigo tare da k'arasowa gaban gadon yana kamo hannun wana yace " Khadeejah, kin farka ko Khadeejah ta".

Ina jinsa amma naki bud'e idona yaita magana nai shiru a haka bacci ya k'ara d'auka na, jin sauke numfashi na ya tabbatar mai na koma baccin.

"Auntyn data farka meta fara cewa?".

Aunty murjah tace " Wlh da salati ta farka kuma ta bud'e idon kuma ta rufe".

Girgiza kai yai yana kallon fuskata data fad'a fayau ta rame tsakankanin lokacin,wani tausayi ne ya kamashi ya dafe kansa dake mai ciwo, Aunty Hafsah tace "Umar kaje ka

Please Login or Register in order to submit comment