Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juna irinta D'an uwa da y'ar uwarsa.


Ana kiran sallar azahar yaya haroon ya dawo,nan suka rungume juna da yaya usman suka gaisa da cike da k'aunar juna sannan suka d'aura alwala suka wuce masallaci ,kafin su dawo Nahna ta shirya musu abinci tare da had'ad'd'an zobo.

D'aki itama ta shiga tai sallah tana zaune tana addu'a taji shigowarsu shafawa tai ta mik'e don ta had'a musu abincin.

A tare a flate d'aya ta had'a musu abincin duka sukeci suna hirar zumunci cike da nishad'i,nan yaya usman yake bawa yaya labarin ya samu mata zaiyi aure sannan zai samu transfer zuwa Kano don haka yace ya fara nema mai gida nan kusa zai siya, shima yaya murna yai ya godewa Allah sannan yace zai shaidawa wani abikinsa me saida filaye da gidaje ya samo mai.

Anan ma yaya usman yake cewa yaya ya bar Nahna su wuce tare yaji tana cewa zataje wani week d'in, yai Jim sannan yace to ta had'a kayanta su wuce amma sati biyu zatai ta dawo.


Bayan la'asar yara suka dawo daga skl nan sukaita murna dunga Auncle d'insu, basu jimaba Aunty Hafsa ta dawo itama da fara'arta suka gaisa da Yaya usman sunata barkwanci.


Da dare da wuri na kwanta bayan na gama parking kayana cikin trolley back,
Aunty ta lek'o taga ina bacci ta koma take shaidawa yaya nayi bacci, jawomin k'ofa datai yasa na farka jin tana cewa yaya nai bacci yasa na gane nemana yake, dammm naji gabana ya fad'i don nasan kan dai wannan maganar ne. . .

K'asa k'asa nakejin muryan yaya Haroon yana magana tsam nai da raina ina sauraran me yake fad'awa yaya usman.

" wato usman uban gidana Alh Usman ne yazomin da wata buk'ata kan Nahna wai yana son in bashi auranta ga D'ansa, to tun a ranar na fad'amai bazan tab'a yiwa Nahna doleba, amma zan shawarceta kan batun inji ra'ayinta, to nai mata maganar tsawon kwana biyar na bata lokaci tai tunani ta yanke shawara , amma sai bayan nai mata maganar kuma nake dana Sani don na lura tun lokacin kamar batada kuzari,ina tsoron kar in takurata, bisa ga alk'awarin dana d'aukarwa kaina da kuma mahaifinmu kan rik'e amanarta da kuma kaucewa duk abinda zaisata cikin had'ari."

Cikin mirmishi yaya usman yace " To yanzu Yaya Haroon shike nan Nahna bazatai aure ba don gudun damuwarta, ina tunanin zuwa yanzu ya dace ace ko Nahna ba'a mata aure ba ace dai tanada wani tsayayye amma fa ga yanda Aunty Hafsa ta shaidamin Nahna ko saurayi batayi duk nacin mutum akanta hak'ura yake ya barta, kaga ai dama wannan da zaka tsaida mata shi a mijin aure tunda ba tab'a yin saurayi taiba shi d'in bazai sha wahala wajan jawo hankalinta ba , sannan Abu na gama kaga dai irin tarin Alherin mutuminnan a gareka bai kyautuba karon farko daya zoma da buk'ata ka watsa mishi k'asa a ido, kuma me sonka aishi zaiyi sha'awar had'a zuri'a da kai."

"Wato usman duk alherin da Alh Usman yaimin bazan manta dashi ba domin kuwa d'an halak bai manta alheri,ammafa hakan bazai sa inyiwa Nahna dole akan auran d'ansa ba koda kuwa hakan zai Kawo k'arshen mua'malarmu dashi,sannan wani abu Nahna fa bata tab'a ganin yaronba inba a hoto ba, koni bai wuce in K'irga ganina dashiba,kuma a ganina na farko dashi na gane irin sangartattun y'ay'an masu kud'in nan ne, duka shine abinda ya fara kashemin jiki dashi."

"A'a yaya karka karaya ka kira Nahna dai kaji meta Yanke shawara kafin mu wuce gobe , sannan maganar sangartacce ne wannan D'abi'ace ta mafi yawon y'ay'an masu kud'i matuk'ar dai yaron baya shan giya baya Neman mata to ba matsala bace auransa."

Jin jina kai yaya yai sannan ya d'ora
" a gaskiya Umar baya daya cikin lefukan nan Don na tab'a tambayar sectare d'in Alh yace baya d'aya ciki sai dai kawai ji da kai da nuna Isa tare da sangarta, sannan zan k'ara bawa Nahna dama harta dawo Daga Sakkoto sannan inji ra'ayinta,don bansan takurata ko kad'an sannan kafin nan zanta k'ara nufar Allah da lamarin yai mata zab'in miji mafi alkairi".



Wani gumi naji yana tsatstsafomin tun daga kaina har k'afata don a hirarsu na gane Yaya yana son had'in nan sai dai yafi k'aunar farin cikina fiye da komai, don haka nasa araina daga yau nai d'amarar sadaukar da burina zan amincewa auran uk kodan mu sakawa Abbansa Alherin da yake mana duk da nasan babu komai cikin auran Uk sai hak'uri da karb'ar k'addara amma zan jurewa hakan,kuma zanci gaba da kaiwa Allah kukana nasan bazai bari in wulak'antaba.

Sai kuma naji wasu hawaye masu zafi suna bin gefan kuncina ,Tunowa danai burina ya karye nason auran miji ma'abocin addini,don nasan Uk bai San komaiba cikin addini zanyi jahadi zan sadaukar da soyayyta ga Wanda ya tsaneni yake musgunamin Wanda bai San darajar d'an Adam ko kad'an . . . a haka bacci ya d'aukeni bayan nasha kuka na gode Allah.




**************
Da safe kafin in tashi har Aunty ta gama had'a break fast ta shirya Yara sun tafi skl Wanda duk aikina ne, ganin ina bacci yasa duk tayi hakan.

Bayan na fito a wanka a gaggauce nasa Kaya don ina toilet inata kiran yaya Usman inyi sauri in shirya da wuri yake so mu wuce , don haka ko kwalliya ban tsaya yiba na fita parlour.

A zaune na samesu suna jirana mu karya bayan na gaishesu na zauna muka karya, bayan mun gama yaya Usman ya dubeni yana fad'in "To maza d'auko jakarki mu wuce banso muyi rana "

Mik'ewa nai zuwa d'aki na yafo mayafina na d'auki jakata ta hannu na jawo trolley d'ita na fito,
Aunty ce cikin wasa take fad'in " To su Nahna yau sai Sakkoto birnin Shehu in anje a gaida Mama da umma a gaida duka mutan gidan".

Cike da fara'a nace " Tom Aunty duk zasuji insha Allah ,in su Ashraf sun dawo kice musu mun tafi bamuyi sallama ba."

"Tom zan fad'i musu Allah ya kaiku lafiya".

Yaya Haroon ne ya kaimu tasha muka d'auki shatar mota k'arama don Yaya usman bai son matsuwa .

Tunda muka d'au hanya muke hira daga bisani yaya usman ya jefomin maganar da sukai da yaya jiya yana nusar dani kan In tsaida hankakina gu d'aya koda zan d'ora degree d'ina hakan bazaisa in k'iyin aureba, sannan yaci gaba da nusar dani kan iniwa yaya biyayya don duk cikin y'an uwana ba Wanda yai hidima dani tun daga k'uruciya har zuwa yanzu, koshi da muka fito ciki d'aya baimin ko rabin abinda yaya yakeminba,tun kuwa mahaifinmu na raye har izuwa yanzu.

Shiru nai ina sauraran sa duk jikina ya mutu murus.

Haka yaita min nasiha da jan hankali kar in watsawa yaya k'asa a ido , a haka bacci ya d'aukeni nidai don jikina ya mutu da nasihar har mukaje Sakkoto ban tashiba saida naji motar ta tsaya a k'ofar gidanmu.





Taku ce
y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation.@gmail.com





*Ina* *taya* *d'an* *uwa* *Abokin* **aiki* *d'aya* *daga* *cikin* *jagorori* *na gidan *marubuta* *murnar* *auransa* ( _Jameel_ _Nafseen_ ) *Allah* *ya* *bada** *zaman* *lfy*, *ya* kawo *zuri'a* *ta* *gari* .
❀❀❀❀❀❀❀




0⃣1⃣4⃣



Kwana na biyu a sakkwato Dangin Baffanmu sukayo Kano don zuwa nemawa yaya Usman auran Amrah agidansu dake badawa bisa jagorancin Yaya Haroon, anyi komai an gama sun bada kud'in aure dasa rana an tsaida lokacin bikin wata biyar, za'a had'a da bikin safwan d'an gidan Babban yayanmu zata auri yar gidan Auntynmu juwaira.

Naji dad'in hutuna a garinmu nai ziyarar dangi sosai duka gidan yayyena mata naje nai musu kwana d'ai-d'ai.


Saura kwana biyu in dawo da dare ina kwance d'akin ummana ina chart naji muryan ummana ta zauna kusa dani tana fad'in " Khadeejah tashi zaune muyi magana "

Dammmm naji gabana ya fad'i, a nutse na mik'e zaune ina kallonta nace "umma inaji"

Gyaran murya tai sannan ta fara magana " Khadeejah wata magana naji daga gun usman, jiya kawunku na k'ofar fada yazo da maganar yaronsa Hisham yace yana sonki da aure in ba'aimiki miji a Kano ba, to amma yana fad'a usman yai tsalan yace wai yayanki yaimiki miji d'an uban gidansa ne yakesonki har kun gama shirya kanku, shin wannan zancen haka yake?"

Jinai kamar an tsoma ni cikin tafashashshen ruwan zafi yanda zufa ta wankeni, da k'yar na fizgo numfashina tare da Kalmar "ehh"

Shiru umma tai tana naxarina na d'an lokaci, sannan cikin hikima irin tasu ta manya ta shigamin tambayoyi Wanda naita fad'i mata yanda abin yake Daga k'arshe nace " Umma nidai na amincewa yaya inna koma zan sanar dashi na amine da auran Umar".

"Sunan yaron umar ne ?"

"Eh Umar sunansa amma Daddy suke kiransa"

Tsakanin d'a da mahaifi sai Allah duk sai naga jikin ummana yai sanyi, tai shiru tana naxarin maganata don a zancena ta fuskanci abubuwa da yawa, jin muryanta nai tana fad'in
" Khadeejah kina son sa"

Dammmm na k'arajin gabana ya fad'i don ba komai cikin raina sai tsantsar tsanar Uk da k'in d'abiunsa, amma taya zan sanar da mahaifiyata bana son sa kuma inje in cewa yaya na amincewa,shin banbar zuciyar mahaifiyata cikin damuwa ba kuwa. . . .

"Khadeejah tunanin me kikeyi ne inata miki magana ?"

A dibirbirce nace " um um umma dadai ban sonshi amma yanzu na fara. . . "

Gani nai ta saki wani hikimtaccen murmishi irin nasu na manya tace "Nahna Khadeejah ina horonki daki zama yarinya ta gari,me Neman zab'in Allah a dukkan lamuranki,kici gaba da biyayya ga yayanki, kana ina haneki dayin soyayya domin wanin Allah,duk Wanda zakiso ki shoshi domin Allah,kada wani abin duniya ya rud'eki a soyayya, kud'i ko kyau mulki ko nasaba kada susaki a k'aunar wani bawa duka son da aka ginashi badon Allah k'arshensa tozarci ne da rashin alfanu kinji ko Autar Baffah".

Jinjina kai nai jikina amace nace " insha Allah umma zaki sameni me biyayya ga dukkan nasiharki".

"Allah yai miki albarka Khadeejah ya tsare rayuwarki daga dukkan abin k'i, Allah ya d'oraki Akan mak'iyanki yabaki galaba a duk lamuranki".

" Ameen ameen ummana "
Kawai nake fad'i don tsantsan dad'in addu'ar ummana da naji,wayyo Allah uwa uwa uwa dabance Allah ya sakawa iyayenmu da alkairi.


Bayan fitar ummana a d'akin na kwanta tare da lumshe ido zuciyata cike da tunani Kala kala harma na rasa Wanda zanyi ciki, kawai dai nasan naji dad'in hiran da mukai da ummana da adduo'in da taitamin Wanda najisu har cikin zuciyata.



Kamar yanda yaya ya umarceni sati biyu cif nayi na d'auko hanyar Kano cike da kewan dangina.


Sai yamma na isa gida a gajiye tik'is ina shiga su Ashraf sukayo kaina da murna, Aunty Hafsah ma ta tareni da "sannu da zuwa mutanan sakkwato ya hanya"

Cikin gajiya na amsa da "yawwa sannu da gida Aunty na sameku lafiya?"

"Lafiya qlau Nahna k'arasa d'aki ki huta, kafin mu gaisa".

" Tom Aunty"

Ina Shiga d'aki na cire kaya na tare da fad'awa toilet na watsa ruwa me d'umi na d'auro alwala don in maida sallar la'asar data kufcemin.

Saida nai sallar magriba sannan na fito parlour a lokacin yaya ya dawo nan na zauna muka gaisa cike da d'okin ganin juna,sunata tambayata yana barosu ya gajiyan hanya.

Bayan munci abinci munyu sallar isha'i nan na fito da tsarabar kowa na bashi mukaita hira har bacci ya fara d'aukana,na mik'e tare da musu sallama na shige d'aki.


Washe gari da safe ya kama asabar ban fito da wuri ba don kowa na gidan bacci yake, tunda yara ba skl yaya ba office, har k'arfe goma banji motsin Aunty ba don haka na fito na shiga kitchen don had'amana break fast, banyi wani abu me wahla ba kunu kawai na dama na soya doya.

Har nagama na wanke kwanukan dana b'ata,na share parlour tare da mofin ko ina, anan naji motsin Aunty a d'akinta alamar sun tashi,don haka na koma d'aki na tashi su Ashraf nai musu wanka Nima nayi muka fito don karyawa anan na tadda su yaya suma sun fito,muka gaisa naje kitchen duk na fito mana da kayan abincin ni INA had'awa Yara Aunty tana had'awa Yaya,bayan mun gama karyawa yaya ya kirani d'akinsa nasan dalilin kiran, don haka ba tare da dogon tunani ba naje na zauna ina fad'in "yaya gani"

"Tom zauna sosai mana Nahna,kan wannan maganar dai da mukayi dakene kafin tafiyarki,na baki lokaci sosai don kiyi tunani da kuma shawara me kyau, don haka Nahna ina sauraranki me kika yanke?"

Saida nai jim sannan na numfasa nace "Yaya na amince"

Kallona sosai yayi don ya gano gaskiyar abinda na fad'a ko akasin haka amma be fahimci komaiba taredani.

" Nahna kin tabbatar da abinda kika fad'i har cikin ranki haka yake ,bana son ki cutar da kanki don wani dalili, farin cikinki nakeso ba nawa ba,Nahna shin har ranki kin amince da auran Umar duk kuwa da biki tab'a ganinsaba ?"

Karo na biyu na k'ara fad'in "eh Yaya na amince kuma insha Allah bazaku sameni me baku kunyaba."

"To Nahna na gode Allah yaimiki albarka ya faranta miki."

A hankali na amsa da "ameen"

"Tashi kije to autar Baffah"

Mik'ewa nai ina mirmishin yak'e. Idona har dishi dishi yakemin.

Kitchen na wuce na shiga aiki Mara dalili don in sami kwanciyar hankali,inda Allah ya taimakeni Aunty ta wuce d'aki gun yaya don indai yana gida daman bata komai shigewa suke d'aki abinsu, saisu Ashraf ne keta damuna da surutu,nikam banko bi takansu abubuwa kawai nake cikin rashin kuzari.

Haka naita aikin badan inajin dad'insa, tuwon shinkafa miyar agushi nayi tare da lemon kwakwa na zuzzuba a coolers na ajiye don nasan sai wajan ma la'asar za'aci, lokacin Dana Shiva d'aki sallar azahar kawai nai nasawa su Ashraf uniform d'in islamiyya, nace suje akwai Abinci na zuba musu a plate a parlour, suna fita na fad'a gado na hau aikin nawa wato tunani, kusan awa guda ina sak'awa da kunewa da tunanin irin rayuwar danasa kaina aciki, nasan babu abinda zan tsinta cikin auran UK sai tsiya da zunzurutun wulak'anci Wanda nafi tsana a rayuwata, To waima wane yasa na furta Kalmar amincewa ne ,me yasa idona ya rufe naiwa kaina ganganci? Ya Allah Allah ka fitar dani cikin k'anginnan kasadar dani ga dukkan allkairanka. . . da wannan tunanin bacci yai gaba dani Wanda ban farka ba said a naji ana kiran sallar la'asar na mik'e zuwa toilet na dauro alwala nai sallah,sannan na fito parlour mukaci abinci.



Takanas yaya yaje gida ya sanar da Abban sweety amincewa danai, farin ciki kamar zai kar sa yaita godiya ga Allah yana k'ara godewa yaya,nan yake sanar da yaya zuwa yan watanni Uk zai dawo k'asar Bayan ya dawo sai akawo kud'in aure dasa rana, yaya ya amince shima ya sanar dashi Nahna zata d'ora degree d'inta ,ba damuwa yace yana k'ara godiya.

Da dare Abban sweety ya kira Auntynsu da sweety yake sanar dasu yanda sukai da yayana ,wata irin k'ara sweety tasa cike da tsananin farin ciki tace " Wayyo Allah yau ranar farin cikin a kenan, mafarkina ya zama gaskiya, wlh Abbah na dad'e ina wannan fatan har maganar na tab'a yiwa Nahna tace bata so Ashe dai Nahna Rabon gidanmu ce Alhamdulillah."

Murmushi kawai Abban yake yace " murjah ke bikice komai ba"

Dariya tai tana fad'in " nayi far in ciki Alh Allah ya Santa Alkairi yasa abokiyar arzik'ice, yanzu ya d'an gidan nawa an sanar dashi ne ?"

Jim Abbah yai kana yace " a'a ban sanar dashi ba tukum, ina wani shiri ne , don jiyama munyi Waya yake cemin 5-6 months insha Allah zasu gama".

"To Allah ya tabbatar da alkairi yasa damu za'ayi"

"Ameen ameen murjah, sai muyita addu'a Allah ya dai daita tsakaninsu yasawa kowa soyayyar d'an uwansa don wannan shine damuwata".

" karka damu Alh, insha Allah a sannu zasu so junansu".

Nan dai sukaita hira har sweety ta fara batun yanda zasusha shagalin bikin, su Abbah sai dariya suke mata na d'okin da takeyi.


A b'angarena kuwa kullum sai tunani da damuwa na rasa ya zanyi da raina, Allah yana gani ban k'aunar Uk na tsaneshi kamar yanda ya tsaneni, shin ahaka za'ayi zaman auran? Kuma babbar damuwata ma shine shin Uk ne yasa Abbansa ya nema mai aurena don yaaci gaba da wulak'antani da yagani, ko kuwa ma bai San da maganar ba shima kawai jinta yai Daga sama, in kuwa haka ne ya zasu kwashe dashi,nasan wulak'ancinsa zai iya cewa ma ni nasa had'amu, ire iren tunanin da suke hanani sukuni kenan, ganin banda mafita yasa na maida dukkan lamarin ga Allah tare da Neman zab'insa in wannan had'in alkairine Allah yasa min nutsuwa a raina in babu alkairi Allah ka Kawo silar rugujewarsa cikin sauk'i.




Kamar yanda yake a k'aida bayan yin graduation a school d'inmu zamuje entrepreneurship 'koyon Sana'a ' domin dogaro da kai to haka muma muka sai form muka cike tare da mayarwa.


Ranar Monday muka fara zuwa entrepreneur acikin school d'in, ni na cike catering wato koyon girki da snacks drinks da sauran duk abinda ya danganci girki,domin ina k'ara Neman k'warewa sosai kan harkar snacks da cake.
Hafsa k'awata kuwa b'angaran makeup and saloon ta zab'a, Wanda zamuyi tsawon sati takwas.






Taku ce
Y'ar mutan ja'oji πŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation.@gmail.com






0⃣1⃣5⃣






Hak'ik'a na samu k'arin wayewa a fannin girke girke a entrepreneur d'in da muke , sannan fannin mu'amala na k'ara had'uwa da mutane iri-iri Kasancewar department ne mabanbanta aka had'a agun, nayi sabbin k'awaye dukda ba d'abi'a tace ba kwashe kwashen k'awaye,amma wani dole ka kulashi don yanda zaita tura kansa gareka, hakama malaman da suke koya mana girkin sun sanni sosai a gun har yasa suka ban jagorancin captain a gun sabida hazak'ata don sau d'aya in aka koya abu na d'auke shi don dama ba yabon kaiba ni gwanace wajan girki Aunty Hafsah ta horar dani da girki sosai.


Tsawon satittikan da mukai na samu ci gaba sosai abin sai godiyar Allah,haka b'angaran make up wani sa'in in mun tashi a gunmu da wuri su Hafsa busu tashi ba nakan shiga gunsu in zauna anan ma na d'an koyi kwalliya irin wadda ake yayi, tare da gyaran gashi.


Cikin nasara muka gama entrepreneurship d'inmu , aka bamu shaidar kammalawa "certificate".


Duk wani abu daya dace muyi a school d'inmu munyi mun had'a duk Slip's d'inmu dasu semester form zuwa duk wasu takardu da ake buk'ata munyi bucking result.


Sati shida dayin bucking d'inmu result d'ina ya fito tare da tarin nasarori ,ranar Dana amshin result d'ina na shaidar N.C.E ina zuwa gida na zube nai sujudishshikur ga ubangijina na gode mai tare da naiman agajinsa a karatuna na gaba da zan d'ora.

Aunty cike da farin ciki ta d'auki Waya ta kira Yaya, ai kuwa ba'afi 30 minutes ba sai gashi a gidan fuskarshi d'auke da fara'a yazo yakarb'i result d'in yana dubawa ,ai kuwa hak'oransa tar a waje ya dube ni yana fad'in " Alhamdulillah, Allah kaine abin godiya Autar Baffah ta fito da kyakyawan sakamako ,Allah ya sanya alkairi, yayi miki jagoranci a karatun da zaki d'ora"

"Ameen ameen yaya" abinda kawai naketa maimaitawa kenan zuciyata da fuskata cike da tsantsan farin ciki.



Da dare ina kwance d'aki ina charts saiga kiran sweety ya shigomin, saida nai d'an mirmishi sannan na d'auka, bako sallama ta faramin k'orafi,

"Lalle Nahna kin kyauta kin nuna min ni d'in ba komai bace a gunki biki d'aukeni yanda na d'aukekiba ,wai Nahna har ki karb'i result d'inki amma ki Kasa fad'amin sai a status d'inki naga kinsa, ba komai na gode".


K'it naji ta kashe wayan, mirmishi na kuma sannan na bita ,harta kusa katsewa sannan ta d'auka,

" haba tawan kinsan ke d'in ta dabance a guna, Abubuwa ne kawai sukai min yawa shiyasa ban samu kiranki ba kiyi hak'uri kinji my sweety ".


Sai sannan naji ta d'anyi dariya sannan ta faramin murna tana min fatan alkairi, nan muka d'an tab'a hira sannan mukai sallama.


Tun a washe gari Yaya yaje ya siyamin form d'in degree, yana kawomin naje cafe na cike tare da tura musu, ba'a d'au lokaciba muka gama komai na fara lecture inda suka bani level 2.


Yanzu banda wani ishashshen lokacin zama a gida kullum in na fita tun safe sai yamma lis, don haka na manta da duk wani Abu sai karatuna kawai nasa agaba.



Fannin addu'a kuwa ban gaza ba kullum nai sallah saina rok'i ubangiji ya tabbatarmin da alkairi cikin wannan had'in.


Addu'ar da nake yasa naji hankalina yana k'ara kwanciya, yanzu banjin tashin hankalinnan da nakeji inna tuna batun auran.



Kwanaki sukaita wucewa bikin Yaya usman ya matso don yanzu saura wata guda cif, munata shirin biki harda sweety don tunda na fad'a mata zancen bikin tace ai tafiyar da ita za'ayita itama zata garinmu,don haka duk ankon bikin da aka turo mana sakkwato tare yaya ya siya mana, ashe itama acan tasa Abbansu yai mana sabbin d'inkuna har kala hud'u hud'u Kaya masu tsada, tare da takalma da jaka harda mayafai.



Naso ace tun saura Sati d'aya bikinnan zan tafi amma school bazai bari ba, gashin kwana biyar za'ai Ana programs na bikin inata tunanin ya zan b'ullowa tafiyar, haka dai ina gani zan tauye wasu lectures d'in nawa don ba k'aramin shiri dangi sukaiwa bikin nan ba , bikin mutum uku ba wasa ba , don haka ma yanda aka tsara duka gidanmu za 'ayi komai , suma su Aunty juwaira gida zasu taho da gidansu yaya Babbah don hankali ya tsaya waje guda.



Kwatsam labarin tafiya yajin aiki ya taso daga makarantun gaba Da secondary a k'asa baki d'aya, Wanda babu ranar komawa har sai Baba ta gani, duk son karatuna naji dad'in wannan yajin aikin don ko ba komai zanyi shagalin biki hankali kwance.


Nan na fara tunanin tafiya a washegarin ranar,don lokacin ya kama bikin saura kwana biyar a fara, amma matsalata guda Sweety inna tafi nace sa taho dasu Aunty Hafsa baza taji dad'iba, kuma in nace mu tafi tare inaga kamar Abbanta bazai bartaba taje tai kusan sati biyu,

Please Login or Register in order to submit comment