Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace ina kika shige sai kice wani abu kike, baki san na ganoki ba tun tuni".

D'an mirmishi nai kawai na tashi zuwa d'aki don d'auko wayan tawa, tarar da tarin Miss call d'in shi sannan ba naga message d'in sa bud'ewa nai ina karanta abinda ya k'unsa,

_Hi_ _my_ _wife_ _ya_ _kk_ _ya_ _jikin_ _naki_ , _na_ _kira_ _biki_ _d'aga_ _ba_ _sweety_ _tace_ _kanki_ _na_ _ciwo_ , _sannu_ _Allah_ _ya_ _baki_ _lfy_ ,

Mirmishi nai bayan na gama karantawa sai na tsinci kaina da kiran wayar tashi, tana shiga ya d'aga " kin warke kenan, ya jikin naki "

"Hhhmmm na warke da sauk'i sosai,ka tashi lfy?"

"Na tashi ina lecture ne ma yanzu amma inna fito zamuyi waya"

"Ok bye".




Koda naje school inata tsammanin kiransa amma bai kira ba sai dare,nan mukasha k'aunar mu don yau abun yafi na kullum dagewa yai sai na turo pic d'ina na lokacin, nak'i sai da naga kamar zai fishi sannan nace tom bari na turo ina kashe wayan nai sauri na sakko da akwatin kayan baccina wanda yake shak'e da had'add'u kuma fitinan nun kayan bacci, wata riga da wando na Ciro wanda rigar iya kacinta k'asan breast d'ina kuma kan breast d'in ne kawai a rife shima d'in ana iya ganin sa kasancewar rigar roba ce ta d'ame sosai ta fitar da komai ana gani,saman albarkatun k'irjin nan duk suna waje, sumamman dake ina da fara period don haka suk sun k'ara cika sosai sunyi kyau,kuma daman Masha Allah don Allah yamin baiwar breast cikakku kuma tsayayyu wadatattu, wandon rigar shima iya kacinsa cinyata,kuma ya d'ameni sosai mazaunaina sun zauna d'am a cikinsa , da sauri sauri nai komai na d'auki wayan nai pic guda biyu na tura mai,ina turawa ya kira da sauri sauri naji yace" sunyi kad'an maza k'ara ko guda goma ne ki turomin yanzun"

Sake d'aukan wasu nai tayi tako ina na tura mai,

Kafin in kira ma ya kirani da d'ayan wayar sa, nace "ya naga ka kira da wannan layin"

"Um sabida d'ayan ina kallon ki ne ciki muna waya ina kallonki"

Cikin wata iskantacciyar murya ta narka maza nace "ahhhh nidai gaskiya kunya fa nakeji "

"Kunyar me?"

" kana kalleni kuma muna waya"

" hhhmmm to Mene ne don na kalleki ba mata ta bace"

"D'an mirmishi nai bance komai ba"

Lokaci guda muryanshi ta narke ta dashe tai can k'asa, gaba d'aya yaji hankalin sa ya tashi musamman inya kalli albarkatun kirj'in sai yaji kamar ana tsikaranshi, jiyai yana sha'awan shafawa a hankali yakai hannu kan screen d'in wayan ya shafi saman breaks d'in yana wani lumshe ido, tare da k'ank'ame jikinsa,

"Kayi shiru kuma"

"Dole inyi shiru tunda kin turomin abunda zai rufe min baki amma kinsan me?"

"Um um saika fad'a"

Muna gama wayan nan ki cire kayan nan ban san kowa ya ganki dashi"

Cikin taokana nace" ba wanda fa zai ganni sweety ce kawai a nan "

"Sweety mijin kice zaki ce ita kad'ai ce wannan shigar ni kad'ai zan ringa ganinta,muna gama waya ki cire su kinji ko"

"Um ba matsala amma don fa ka goge pic d'in Kar wani ya gani "
"Waye zai gani aini ba wanda ke karban wayana, kuma ko mutum ya ansa bai isa yaga folder d'in ba don kykkyawan ajiya nai musu sabida su dunga d'ebe min kewa"

"Hmmmmmm pic daman yana d'ebe kewa"

"Eh mana ni yana d'ebe min,wanda kika turomin rannan ma su naketa lalla ga na yau ma sun d'aga min hankali "

"Wayyo Allah me nai na d'aga ma hankali mijina"

"Gashi kin d'auki pic tsirara kin turomin yana neman hanani bacci"

Wata y'ar k'arar kissa na saki nace "wayyo don Allah ka bar fad'i tunda haka ne ma bari ni in goge ka daina kallona a haka"

"A'a wlh karki sake ki gogemin,nifa ma da wasa nake miki ina son Irin wannan shigan sosai kinyi kyau Allah".

Dad'i naji na narke murya " Tom zanyi bacci".

"Um um baza kiyi ba ban gaji da hiran ba fa"

Sake gyara kwanciya nai nace "Tom ka bani lbr me dad'i kaji "

"Ni labarin da zan baki ko kin d'aga min hankali yanzu ji nake kamar ma in taho gida"

"A'a wane irin ka dawo na kusa fa zuwa gunka"

"Tom ki shirya duk lokacin da kikazo ko hhhmmm"

Mirmishi kawai nai ina k'ara rungume pillow d'in don yanayin da yake magana duk motsani yakeyi, maganganu yake ta sakar min masu tsuma zuciya,wata Kalmar inya fad'a min saina runtse idona, kasa magana nake duk abinda yace sai dai ince um ko um um don ko idona na kasa bud'ewa sabida na shiga cikin shauk'i,bamu tab'a yin waya kamar ta yauba mun manta dare ne ma munyi soyayya mun cinye lokaci, saida naji yana magana har bana iya gane abunda yake fad'i,nan kuma fa tunanin ya fara zuwar min Kar muje muyita tayar wa da juna hankali kuma ya kasa control d'in kanshi ya fad'a wani hali, saurin yin ta'awizi nai na kauda tunanin araina, saida muka shafe sama da 2 hours sannan muka rabu, juyi naita yi a gadon ina jin yanayin na dad'uwa gareni, kusan awa guda na sake shafewa a saman gadon cikin shauk'i sannan na tashi na shige toilet na d'auro alwala, tsawon lokaci ina rok'on ubangiji ya tsaremin mutuncin mijina ya kauda idonshi daga ko wace mace.

Bani na bar kan prayer mat d'in ba sai k'arfe biyu na dare na koma can d'akin, sweety nata kwasar bacci nima idona cike yake taf da bacci na haye gadon tare da addu'ar kwanciya bacci kafin wani D'an lokaci baccin ya jani.





Gobe Talata insha Allah ilahirin musulmin duniya ke sa ran ganin wata jama'a nata shirye shirye haka muma a namu b'angaren duk gidan cike yake da kayan masarufi wanda Abba yai order d'in su zai rabawa talakawa, ga y'an aiki da aka k'aro sosai sabida girkin Abincin sadaka da akeyi ana kaiwa masallatai, ji nake kamar inyi me don murna sai kace yau ne zan fara azumtar azimin ramadan,duk da nasan k'ark'ari in an fara dani inyi d'aya ko biyu ya yanke min don ina gab da up.



Yauma haka muka raba dare muna waya sannan muka rabu, washe gari kuwa cikin ikon Allah watan azumi ya bayya don haka kowa ya k'uduri niyar d'aukan azumi a daran ranar.




Alhamdulillah mun shiga cikin ramadan don gashi yau Alhamis har ankai d'aya,muna baje part d'in su sweety kamar yanda Abba yace Anan zamu rink'a shan ruwa gaba d'aya a babban parlourn su,muna nan har aka kira sallar isha'i anan mukai alwala muka fita harabar gidan don bin jam'i mu sami Asham kasancewar masallacin na jikin gidan don haka matan unguwar da yawa suke shigowa bin salla a nan, sanda muka hau sahu za'a tada sallar nan wani Irin nishad'i nakeji kamar yanda yake ga duk cikakken musulmi in dai watan Ramadan ya kama to zaka zuciyar mutum tai wasai nishad'i na saukar mai, hakan yau nakejin zuciyata cike fal da nishad'inishad'i

Tsawon lokaci aka idar da sallar kai tsaye part d'ina na wuce na d'auki wayata yaya na haroon na kira muka gaisa na mai barka da shan ruwa sannan muka gaisa da Aunty Hafsah, gida sakkwato ma nika iyayenmu duk nai musu barka da shan ruwa na kira yayyaena sannan na kira Aunty Amrah itama mun dad'e muna hira bayan mun gama toilet na shige nai wanka nai shirin bacci sannan na kira wayan ogan muryanshi cikin yanayin bacci yake amsa sallamar da nake mai" precious ya kk"

"Lfy qlau ya ibada"

Jan numfashi yai sannan yace " mun kai azumi da k'yar shiyasa ina shan ruwa na kwanta yanzuma kiran kine ya tashe ni".

Cikin mamaki nace " wai ko sallar isha'i baka samu ba balle Asham ?".

Cikin rashin damuwa yace "wlh banyi ba sabida nasha wahla sosai ina shan ruwa bacci ya dauke ni".

" Ayya shed'an ne don karka samu ladan Sallar Asham na ranar farko na wata me alfarma shine ya sa maka bacci, amma daurewa zaka rink'ayi ka bari sai kayi sallar sannan ka kwanta kafin lokacin wayanmu yayi ko"

"Eh hakan zan runk'ayi precious amma fa ke sai naji kamar ma bikiyi azumin ba muryan ki fes da ita "

D'an mirmishi nai "hhhmmmm nayi mana ai yanzu ana goman farko azumi bai bada wahla kowa yana zumud'in sa, kuma ni azumi baya ban wahla sam "

D'an zaro ido yai yana fad'in " Ke kinsan wahalar azumi kuwa amma kice baya baki wahla lalle ma"

Mamakin d'abiun sa nake mutum ne shi bamai kula da al'amuran addini ba,iya salloli biyar d'inma da aka wajabta mai ba ko yaushe yake yinsu cikin jam'i ba matsayin sa na namiji, yafi k'aunar yinsu cikin gida kuma harga Allah na tabbata ba komai ya Sani na daga cikin k'aidojin sallar ba,amma in yana bin liman yau da gobe zai fahimci komai ya k'ara ganin yanda ma sallar take, batun nafilfili kuwa daman ba'a magana don innace ma yanayi nai k'arya, to gashi kuma anzo batun babbar ibada me tarin falala da girma kuma ya fara gazawa daga yin d'aya ya fara fad'in yasha wahla harya kasa yin sallar isha'i, lalle rayuwar mijina tana buk'atar tallafi da kulawa ta fannin addini".

Muryanshi ce ta katse min tunanin dana tafi " meya faru naji kinyi shiru?".

"Hhhmmm ba komai ,Kaga mu kuwa bamu dad'e dayin sallar ba munbi jam'i a masallaci wani irin nishad'i da farin ciki nakeyi yau d'in nan,kaima bari in barka kayi sallar inka idar mayi wayan ko, kamin addu'a don Allah kaji ".

" ok to ba damuwa bani y'an mintina kad'an ma"

"A'a na baka awa guda ma kayi sallolinka kai addu'a oinka ka rok'a mana rahma da dacewa wajan ubangiji".

" OK"

Bayan mun kashe wayan na kwanta lamo bisa gadon ina nazarin rayuwar mijina,lokacin da Allah ya fara karkato min da hankalin sa gareni nake da damar fahimtar dashi addini lokacin ne kuma yai nesa dani amma a hakan ma bazanyi k'asa a gwiwa ba zanyi iya yina cikin hikima Irin tawa in rink'a nusar dashi addini sannan zuwa ranar da Allah zai dawo dashi gida zan mik'e tsaye don bazan zauna ina kallon mijina cikin duhun jahilci ba alhalin inada ilimin da zan tallafeshi dashi, duk sai naji jikina ba fad'i zuciyata tamin rashin sukuni, tunowa danai da tsohon burina nason Allah ya bani miji ma'abocin addini matuk'a nasha hasasho rayuwata ta gidan aure tare da miji malami ina d'aukan darasi a wajan sa, amma sai gashi Allah yamin canji da burina kuma na tabbata wannan shine alkairi na tunda kullum zab'i nake bashi kan miji ba gari mafi alkairi sai gashi yamin zab'in kuma nasan akwai abunda Allah Ke nufi da hakan,don haka zanci gaba da rungumar k'addarata sosai kuma na k'ara godewa ubangiji na da bai barni da zab'in kaina ba, don ko yanda nakejin so da k'aunar sa na dad'a shiga raina na tabbatar akwai hikimar ubangiji a cikin haka, tunani kala kala naita yi har wajan 30 minutes naji kiran sa, da wani salon na k'ara zuwar mai wanda shima ya rink'a narke min tamkar wani D'an jinjiri,kamar ko yaushe mun dad'e cikin birnin masoya sannan muka rabu, alwala na d'auro nazo na tada salla don na k'ara d'aura d'amara kan yiwa mijina addu'a musamman cikin wannan watan,ina rok'on ubangiji ya k'ara tabbatar da alkairi cikin auranmu sannan ya sanya sona da k'aunata cikin zuciyar sa kamar yanda nasa ya d'arsu cikin nawa.

Yau kam kamar yanda na tabbatar banda rabon yin azumi hakan kuwa don muna tashi yin sahur na tadda bak'ona yazo don haka ma banyi ba na koma bacci na bakina d'auke da zikiri.



Bayan munsha ruwa gun Abba mun d"an tab'a hira na mik'e tunda nasan bazanyi salla ba part d'ina na wuce na kira wayan mijina kam da d'an k'arfinsa naji shi bayan mun gaisawa nai mai barka da shan ruwa nake tambayarsa su sunyi salla tuni ko dariya yai yace "Tun tuni ma mun manta munyi salla yau banyi bacci ba saida nai salla kuma yanzu fa nake shirin na d'anyi bacci ko na awa guda ne kafin muyi wayan"

"Um yau na kiraka da wuri ko"

"Kun idar da sallar ne kuma"

"A'a yanzu ma dai naji an fara raka'ar farko "

"OK to je kiyi Kar a wuceki"

D'an mirmishi nai cikin yin k'asa da murya nace "ni yau bazanyi ba"

"Meyasa baza kiyi ba".

Shiru nai ina d'an mirmishi k'asa k'asa ,
Ya sake cewa " ko kin gaji yau?"

"Hhhmmm ai gajiya bata hana salla ko"

D'an mirmishi yai don ya gano inda ta nufa kuma cikin tsokana yace
"Ohh Ashe yau Ke gandiya ce "

Mirginawa nai akan gadon ina dariya k'asa k'asa nace "waye yacema ni gandiya ce ,ai yara ne suke shan azumi ni kuwa babba ce ko"

Dariya yai sosai sannan yace "eh yara suna shan azumi sannan ma mata irinki suna sha kamar yanda kema yau daga yin d'aya kika b'ule".

Wayyo Allah kunya kamar yana kallona na runtse idona cikin tsananin kunya da shagwab'a na fara fad'in" Allah Allah nidai ka daina ban so "

Dariyar sa yake son ransa yace "meye bakya so gaskiya fa na fad'a Ke d'in yau ba magana zanwa Abba ma waya in fad'a mai karma ya k'ara damuwa kizo gunsa shan ruwa don kina shan abunki da rana"

"Wayyo Allah ka bari so kake ka kasheni da kunya ko nidai Allah ban so ".
Sheshshek'ar kukan wasa na farayi araina ina tunanin rayuwa irinta gidan zai fa iya sanarwa Abba wai wlh dana shiga uku,

Wutar duk da take aiki a jikinsa ce ta d'auke don kukan kissar da nakeyi ya tab'a ko ina na jikinsa, nan da nan yaji an fara mintsinin shi, muryarshi ya k'ara narkewa yace " yi shiru yi shiru my precious wasa fa nake miki, bazan fad'a mai ba ,ai nasan ko wace mace ma tanayi ko ".

" um kowa yanayi bani kad'ai bace".

K'ara kyalk'ylewa yai da dariya sosai yace "a'a wlh badai kowa da kowa yana yiba iya Ku iku mata ne kukeyi mu bamayi maza ".

Ya k'arashe maganar yana k'ara k'yalk'yala dariya.

Jin dariyan tashi tak'i k'arewa yasa na kashe wayan ina turo baki, kira ya k'arayi nak'i d'auka sau uku yana kira sai da ya turo tex yana rok'ona in d'aga ya daina dariyan,
D'an mirmishi nai sanda kiran ya sake shigowa na d'aga jinsa nai ya kashe murya sosai cikin salon shagwab'anshi yace " precious "

"Um" kawai nace

Jin yanda na amsa Kawai naji ya k'ara k'yalk'yalewa da dariya, maimakon inji haushi kawai nima sai na saki dariyan ina cewa " wai dariyan me kake min Allah ka daina" na k'arashe Nima ina dariyan, sai yai mai isarsa sannan ta tsagaita yana cewa "kin san meke bani dariya ?".

" um na sani mana ni kakewa dariya "

"A'a wlh bake nakewa ba wani labari zan baki "

"Tom bani ina ji"

"Kina ji lokacin da muna secondary school ne akwai wata yarinya a ajinmu sunan ta Deborah muna soyayya da ita a lokacin, bata san mata suna wannan abun ba ranar mun fito break muna zaune reception muna cin abinci da ita munata soyewar mu sai aka koma class tana tashi zamu tafi kawai sai naga jini a gun data tashi da sauri nace" Mene ne wannan a k'asanki"

Cikin kid'imewa take kallon jinin daya b'ata kujerar data zauna ai kuwa tasa hannu aka ta fara ihu nima na rikice don lokacin ban san meye ba, na rik'e ta tana kuka nima ina kuka don tunani na wani abune ya fashe a jikinta jinin Ke fita haka, muna wannan halin wata Auntyn mu tazo wucewa ganin halin da muke ciki yasa ta tsaya tana tambayar mu meya faru a tare muka shiga nuna mata inda jinin ya b'ata munayi muna kuka, fahimtar datai bamu san meye ba yasa,tamo hannunta tace ni in wuce class taje da ita staff room ni kuwa dana tafi aji na kasa komai haka na kwantar da kaina kan des inata d'an kuka na ina tunanin shikenan Deborah ta wani ciwon ya sameta maybe ma mutuwa zatai haka na k'arasa zamana a class har aka tashi bata dawo aji ba, kamar had'in baki ranar muna zuwa islamiyya lokacin bamu fara gudun islamiyya ba sai wata yarinya a ajinmu taiwa ya sayyadi tambaya kan wani karatu da yake mana a lokacin na manta dai tambayar datai mai amma nasan kan abun ne,to a ranar ne naji bayani kan abun don yanda yaketa mata bayani sosai na rik'e abun a raina, to a ranar nasan meye wannan jinin, shiyasa duk randa na tuna shirmen da mukai da Deborah sai naci dariya na k'oshi".

Ya k'arasa maganar yana wata dariyar ,nima dariya sosai nace "lalle ansha kunya kenan,kuma data zo school washe gari bataji kunyar ka ba?".

" Ke su arna meya damesu da wata kunya,da tazo ma ni na k'ara mata bayani akan abun, kin san me nifa duk a karatun da ake mana a islamiyya babu abunda ya tab'a zama akaina Irin wannan shima kuma don anyi karatun ne a lokacin nake buk'atar Neman Sani akan sa,sabida inaji da Deborah fargabata Kar inje wani ciwon ne ya sameta".
Wani haushi ne naji ya turnik'eni danaji yace yanaji da Deborah d'in sa don haka na had'e raina nace "um wato kanaji da ita ko, lalle kuwa".

" hhhmmm Ke nifa ban tab'a jin yarinyar data ratsa raina Irin Deborah ba don yarinyar akwai masifar brain ga aji komai nata me aji ne shiyasa nakeji da ita".

Jinai wani kishi ya taso min ya tsaya a k'irjina,don haka cikin dasashshiyar murya nace"Tom bari in kwanta ko"

"Ban gane ki kwanta ba tun yanzu,meya faru naji muryanki ta canja".

" ba komai "

Sai a sannan ya gano tabargazarda yayi don haka ya sassauta muryanshi yace "precious Kar kisa wani abu aranki fa, tsohon zance fa nake miki ni yanzu ma wlh ban san duniyar da Deborah take ba,don muna gama secondary suka koma garin su".

Sai a sannan naji d'an sanyi ya ratsani na saki raina mukaci gaba da hiranmu cikin nishad'i.









Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*Y'AN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣8⃣


Haka akaci gaba da gudanar da ibadar azumin Ramada cikin kwanciyar hankali , har yau ankai goma, Abba yayi matuk'ar k'ok'ari don kayan Abinci ya had'a bana wasa ba ya aika dasu can gidan mu sakkwato yace inji mijina, haka akaita rabawa y'an uwa na kusa da nesa tare da abokan arzik'i, sannan yasa turaman atamfaofi da yawa yace nasu umma da mama sauran na y'an uwa, Haka ma anan kano Ya aikawa yaya haroon kayan abinci bana wasa ba haka ma yaya Usman sannan yasa turaman atamfofi na Aunty Hafsa da Aunty Amrah suma su Yayan harda shaddodi, gaskiya Abba yayi k'ok'ari, waya tako ina aka rink'a kirana anamin godiya wai sunga kaya inji mijina sun gode, nikam sai dai inyi mirmishi kawai.


A daran ranar Abban ya kiramu nida sweety bayan munyi sallar Asham ya bamu kud'i wai na kayan sallar mu ne in zamu k'aro, ga Atamfofi da shaddodi yace mu d'auki iya yanda muke so, godiya nikam nai tayi yace "ba komai ai hakki nane"

Bayan kwana biyu ma saiga transfer kud'i daga Uk 100k wai inyi hidimar salla nace Abba ya mana komai, amma yace babu ruwan sa da kud'in Abba wannan kyautar shi ce tsakaninmu wannan kuma hakkin sane ya dole yayi min, nikam godiya nai tayi ina mai addu'a, a ranar nake tambayarsa zanje in yiwa su yaya na barka da shan ruwa, yace to ba matsala, washe gari da safe kuwa na tafi gida bayan na tsaya na saiwa su Ashraf wasu tsada tsadan kaya riga da wando wando masu masifar kyau da tsada kowanne kala biyu, sanda naje gidan kuwa murna kamar sayi me, bayan mun gaggaisa na sami nutsuwa nan na fito da kayan na basu sukaita murna, a gida nasha ruwa naje nawa su yaya usman ma barka da shan ruwa sai bayan sallar Asham sannan na koma gida a mota ta dake da ita na tafi.



Kwanaki nata gudu azumi nayin nisa yayinda muka k'ara k'aimi wajan bautar Allah da addu'oi,kullum in zanyi addu'a ta saina rok'i ubangiji shiriyar sa ga mijina da kuma k'ara neman alkairi cikin zamanmu, wanda kullum kuwa ina ganin canji na k'aruwa a zamantakewar mu.

A haka muka kammala azumi mukayi sallar idi cikin kwanciyar hankali da farin ciki, bisa umarnin da Abba ya bashi yace inje sakkwato inyi kwana hud'u don in gaida iyaye da y'an uwa,hakan yamin dad'i matuk'a ranar da na sanar da yaya nah Haroon yace ai suma sunyi shirin tafiya harda yaya usman da matarsa don haka muka rankaya ranar biyu ga salla mukai gida sakkwato, nayi tsaraba sosai kasancewar shine zuwa na farko tun bayan aurena,gashi Abba ya cikani da kud'i haka shima Uk ya turomin 50k yace inyi tsaraba, na zaga dangi sosai cikin kwana hud'un nan kuma Duk inda naje zan musu alkairi, badan naso ba na dawo son su yaya acan na barsu tunda mu muna tsakiyar semester don hutun sati d'aya kawai aka bamu, randa na dawo washe gari aka koma school amma banje ba sabida gajiya ga gyare gyare Dana d'anyi.




*************
Haka rayuwa taci gaba da gudana yai da dad'i gobe babu,amma nikam a fanni na sai dai nace masha

Please Login or Register in order to submit comment