Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai ba kunya da kawaici kamun kai da nutsuwar mu mu Y'AN ARABIC ita kesa ake mana wani kallo na daban,abunda ba'a Sani ba mu fitsara ce ba fidda tsiya bamu iya ba amma a bed munfi duk wata da take jin kanta wayayyiya fanni soyayya mu d'in na daban ne domin mu soyayya mukeyi me y'anci Irin wanda musulunci ya koyar kuma take tafiya da kowane Irin Zamani, Khadeejah mufa d'alibai ne masu karantar Islamic tome za'a layance mana duk mutumin fa da yake karanta rayuwar gidan manzan Allah (s.w.a) babu wata rayuwa da zata bashi matsala kota dameshi, ya karanta yaji yanda ake zama da miji yanda ma ake zama dako wane irin mutum, duk duniya fa babu wani mutum daya kai manzan Allah iya soyayya da rayuwar aure shi yasan yanda ake kula mace a ririta ta tayima abunda bata san tana yinba, shi yasan yanda ake faranta ran juna kuma shi yake koyar da matansa yanda zasu kula dashi suyi Abunda ransa zai fari,agidan manzan Allah aka saukar da duk wata soyayya shauk'i da nishad'i to mu kuma d'aliban Arabic meye bamu karanta ciki ba meye bamu Sani ba,daman anfanin ka nemi Sani kan rayuwar manzan Allah ai don kayi koyi da ita ne to mukam mun koya mun san komai kuma mun gode Allah don haka Khadeejah kiyi amfani da 'sak'afa islamiyya' (wayewa ta musulunci" da 'sak'asa ilmiyya' (wayewa ta ilimi) ki daidai ta rayuwar ki da mijinki rayuwar zata fimiki dad'i, don wlh Allah duk rayuwar da babu namiji cikin ta rayuwa ce Mara dad'i mara armashi Khadeejah ki mori rayuwar ki kiji dad'i kuma ki sami aljannarki".

Sosai maganganun Aunty ummy suka shige ni kuma sukai tasiri a jikina da zuciyata lokaci guda naji wani Irin k'warin gwiwa ta saukar min, godiya nai mata sosai sannan muka shiga kitchen mukai miya a tare muka had'a kunun aya bayan munyi sallar azahar mukaci abincin nan mukaci gaba da hiran mu wanda nake k'aruwa da ita matuk'ar k'aruwa har bayan sallar la'asar sannan Abban boy yazo ya d'auketa nai mata rakiya gate da kayan shafa na mata cikin leda inata k'ara mata godiya.

Bayan na idar da sallar magriba ina zaune kan abun sallar tunanin duka maganganun mu na d'azu da Aunty Ummy nake tabbas saina cire duk wata kunya dake tare dani da kawaici na nemawa kaina y'an ci don haka daga yau insha Allah zan fara dukkan wani k'alubale na shirya karb'ar sa, ina nan zaune har akai isha'i na tashi anyi tare da shafa'i da wutiri nai addu'oina naje na watsa ruwa a lokacin ne sweety ta shigo a gajiye tik'is itama wankan tai ko abinci bata nema ba tanayin salla ta kwanta, parlour na dawo na kwanta kan kujera sannan na fara lalubar number d'in sa a hankali na danna kira harta katse ba'a d'aga ba ban karaya ba na sake kira shima tana gab da tsinkewa ya d'aga duummmm naji gabana ya fad'i amma saina kira sunan Allah wanda shi zai bani k'warin gwiwa, "Assalamu Alaika " na fad'a cikin wata murya
" wslm , ya kk ya Guda"
" lfy qlau muke kaifa"

"Nima lfy ta qlau"
"Masha Allah, ya karatu"

"Gashi munata yi"

"Tom Allah ya taimaka "

"Ameen"

Shiru ya ratsa na d'an sa'anni na rasa me zance,amma dana tuna meke gabana saina k'ara k'asa da muryata sosai kamar me rad'a nace" Saura ne wata nawa ka dawo "

Wani iri yaji tambayar wadda har taso bashi dariya amma sai ya basar yace "wata na nawa ne da tafiya yanzu "

Jim nai ina tunani can nace "um yanzu watan ka fa hud'u yanzu "
"OK Kinga basai na fad'a ba saiki k'irga ki gani saura wata nawa yanzu tunda dai wata goma sha biyar zamuyi"

Shagwab'e murya nai kamar zanyi kuka nace " nidai Allah watannin nan basa sauri nifa duk na matsu ma muyi hutu in kawo ma ziyara "

Tofa ya fad'a a ransa me yarinyar nan Ke nufi ne, d'an mirmishi yai yace " kina son zuwa inda nake ne?"

Kamar y'ar k'aramar yarinya nace "um ina son ganinka fa kullum sai naita tunaninka inji kamar ma inzo in ganka"
Wani bak'on yanayi yaji ya ziyarce shi, don salon yanda maganar Ke ratsashi har ya fara shiga cikin jikinsa, jin danai yai shiru yasa nace " mijinaaaaaaa"

Wawwwww ya furta cikin ransa yau kuma shi ake kira wannan sunan,
Ni kuwa rasa sunan da zan fad'a mai ne yasa na kirashi da wannan sunan don dai ba girma ba ladabi in kirashi da sunanshi na gaskiya Umar,kuma bazan iya cemai UK ba wannan sunan abokai ne, broth kuwa sunan da y'an uwansa Ke cemai ne,Sai Daddy shi kuma sunan da Abban sa da sauran dangi Ke fad'a mai ne ni kuwa nafi son in kirashi da sunan da wani bai tab'a fad'a mai ba,ai kuwa da gaske sunan ya bigeshi ,amma basarwa Irin tasa yasa ya basar d'in yana fad'in "um ina jinki "

"Baka kewanmu ne kai "
" hhhmmm inayi mana me kika gani "
"A'a naji baka cewa ma kana son zuwa ka ganmu ne"

"Inna fad'a ma baza tai amfani ba tunda nasan ba zuwan zanyi ba ko,nida gida sai nayi wata goma "

"Hhhmmm haka ne tom ni zan kawo ma ziyara nanda wata uku insha Allah, wannan karon semester d'in mu wata uku ce yanzu munci wata d'aya da komawa nanda wata biyu zamu fara exam muna gamawa insha Allah zanzo Abba ma yace har dashi zamuzo "

D'an mirmishi yai yace "To ina jiranku sai kunzo "

"Um hmmmm, daman nace um"

Jin nai shiru yasa yace "fad'i mana ina jinki ko akwai wata matsala "

"Um um daman ina son ince ne don Allah me yasa yanzu baka kirana "

Shiru yai don bashi da amsa tunda shima dai bayace ga shi ba,

"Naji kai shiru ko laifi nai maka "
"A'a ba wani lefi kawai aikine yake min yawa kin san course d'in namu akwai wuya"

"Oh to Allah ya taimaka ya bada sa'a,Allah yasa kafi kowa cinyewa "

Har ransa yaji dad'in wannan addu'ar don haka cikin sakin fuska yace "ameen na gode"

"Um tom zanyi bacci sai da safe "

"OK Allah ya tashemu lfy,ina sweety koke kad'ai ce "

"A'a tare muke kwana ai kullum tare muke yanzu dai tai bacci"
"OK sai da safe to"

Kashe wayan nai cikin fara'a nai wani juyi har cikin raina yau nakejin farin ciki wayan Sama da 10 minutes mukai yau wanda duka bama wuce 2 minutes a wayan namu, k'udurtawa nai araina gobe sai munyi 20 minutes insha Allah.

Tashi nai na koma d'aki na kwanta cikin nishad'i da farin ciki nai addu'a tare da lumshe idanuwa na.

Shi kuwa UK bayan kashe wayan binta yai da kallo yana wani mirmishi wanda bai san dalilin yinsa ba, d'ago ido yai suka had'a ido da fadlah dake zaune ta zabga uban tagumi tana kallon sa idonta duk ya tara hawaye,duk sai ya diririce don har ga Allah shi yama manta tana zaune kiran farko dai yasan tana gun suna searching wani abu cikin Laptop nashi don ko a lokacin ma yanata mata magana kan taje ta kwanta dare yayi sosai amma tak'i don haka kiran daya shigo yana kallon wayan yak'i d'agawa yace tashi kije gidanki, tak'i tashi tana lek'en wayan har kiran ya katse da kiran ma ya k'ara shigowa yai ta mata masifa tak'i ganin kiran yana neman katsewa yasa ya d'aga sai kuma yanzu daya gama ya waigo sannan ma ya tuna da ita, d'an tsare gira yai yace "Fadlah jeki gidan ki dare yayi sosai,ban son kina kai tsawon dare haka,kin san zargi zai iya shiga zuciyoyin mutanan dake tare damu in suna ganin kina dare a nan "

Had'iye b'acin ran dake taso mata tai tace "Don matar ka ta kiraka shine kake korata ko choice?"

"A'a wane Irin don mata ta ta kirani ai tun kafin a kirani nake cemiki kije ki kwanta,yanzu dubi ogogo fa k'arfe nawa yanzu?"

K'ara karkace kai tai cikin yanayin wai a tausaya mata tace "choice don Allah kayi wani Abu mana cikin rayuwar mu kasan fa yanda nake sonka ko . . . .

Dakatar da ita yai yace "naji koma dai meye kije zamuyi magana da safe "

Daga haka ya mik'e zuwa bedroom d'in wanda yake k'waya d'aya tal ya rufe k'ofa, gado ya haye yana shafa sumar kansa yana Neman mafita tsakanin shi da fadlah don a zahirin gaskiya shi bai san yanda zai da ita ba wlh,jin k'aran rufe k'ofa yasa ya gane ta fita don haka ya tashi ya fita ya rufe parlour sosai ya kashe duk kayan wuta yazo ta kwanta.









Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*Y'AN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣6⃣


Yau lahadi ina tashi da safe tuwona na jiya kawai na d'umama naci na fara k'ok'arin had'a kayan da zanyi dashishin alkama da miyar taushe, don yau na shirya yiwa Abba shi kwana biyu ban mai girki ba, kuma matsayin abincin rana nake son mai don yau nasan ba inda zashi yana gida, sweety tanata baccin gajiyan biki banyi k'ok'arin tashinta ba na shiga aikina sosai har wajan sha biyu na gama har had'amai zob'o wanda nasa sugar kad'an don yanayin jikin sa, bayan na zuzzuba Duk cikin warmers na zuba zab'on cikin wani k'aton juk, sanda na shiga zanyi sanka na sami sweety zaune bakin mirror tana Kwalliya, y'ar dariya nai nace "yau dai bazaki baccin dare da wuri ba sai yanzu zaki tashi "

Mirmishi tai tace "tun 11 fa na tashi waya nake da Hubby na kuma ina gamawa na fad'a wanka"

"Ok bari nima inyi wankan "
Na fad'i ina shigewa toilet,



Saida nai sallar azahar sannan na d'auki abincin na wuce wajan Abban sweety ta rik'omin juk d'in, sanda muka shiga Parlourn nashi yana zaune yana waya zama mukai muna jira ya gama ni ina d'an nesa dashi yayin da sweety ta zauna jikin sa kamar yanda ta saba kullum tana manne dashi, bayan ya gama wayar ya juyo da kalkonsa gareni cikin tsokana yace "Khadeejah wannan k'anwar taki bazata girma ba ya kamata ki fara shirin mata aure ko zata san ta girma ta daina wannan tab'atar"

Y'ar dariya nai nace "Abba ai tace in tana tare dakai jinta take y'ar yarinya "

Dariya yai yana shafo kanta yace "me aka kawo min ne a wannan kulan"

D'an mirmishi nai na gaisheshi ya amsa cikin kulawa sannan sweety ma ta gaisheshi ya amsa yana cewa a bud'e min inga me aka kawo "

Tasowa nai ba bud'e mai abincin ya gani shak'a yai yana dariya yace "Tom sweety jeki ce Murjah ta bar had'a abincin gashi Khadeejah ta kawo min"

Fita tai can ta dawo da Aunty murjah d'auke da flat da spoon, gaisheta nai itama ta amsa cikin fara'a tace " Khadeejah kice kin fansheni kenan "

Mirmishi kawai nakeyi kaina a k'asa ganin an zuba mai abincin zai fara ci yasa na mik'e ina cewa sweety "bari naje parlour"

Itama mik'ewa tai ta biyoni d'akinta mukaje muka zauna munata hira , ranar a part d'in su muka yini sai wajan k'arfe shida da rabi muka koma part d'ina muna zuwa mukai sallar magriba mukaci abincin da mukazo dashi da daga gun Aunty murjah.


Yanda na gama tsarawa daman ina yin sallar isha'i zan kirashi ,don haka kafin nai sallar nai wanka ina idar da sallar na koma d'aya d'akina nabar sweety itama tana kwance tana waya da saurayinta,
Bugu d'aya biyu uku ya d'auka yana d'agawa yace "Bari insa credit zan kiraki "

" um um inada credit sosai a ciki".

"OK Ashe hajiya ce Ke ko"

D'an k'ayataccen mirmishi nai nace "Barka da dare "

"Ya kk"

"Lfy qlau ya school"

"Um muna fama "

"Tom Allah ya taimaka"

"Ameen ya school d'in naki Ke"

"Alhamdulillah school tai zafi "

"Meyasa tai zafi "

"Sabida mun fara had'a kayanmu daga cikin ta"

"OK yaushe zaku gama ne"

"Da saura amma ba sosai ba yanzu dai da muncinye sauran wannan semester d'aya ce ta rage mana kuma itama bame tsayi bace"

"Allah ya kaimu "

"Ameen"

Shiru muka d'anyi can nace " um kasan me?"

"Um um sai kin fad'a"

"Don Allah in kayi salla in ka gama yiwa su Abba da kanka addu'a ka rink'a rok'amin Allah yasa na fito da first class"

Jim yai yana tunanin shi yaushe ma rabon sa daya tsaya yai wata addu'a inya idar da salla ai shi yana idarwa tashi yake don bai jin yanada wata buk'ata da zata d
Sashi damuwa ya tsaya yaita addu'a, (hhhhhhmmmm lalle kunji fa tunanin mutumin Ku uk)

Jin danai yai shiru yasa nace " kona d'ora ma nauyi"

"Um um kawai ina tunanin kema kina son ki fita da first class ne"

Y'ar dariya nai ta jan hankali nace "eh mana ina so, tunda kaima ka fita dashi Kaga sai muyi anko ko"

" hhhmmm haka ne zan rink'a miki addu'a insha Allah "

"Yawwwwa My na gode,kasan me?"

"Um um fad'i inji "

"Idan fa miji yanawa matar sa addu'a ko to da wuri Allah Ke karb'a, ko addu'a ta alkairi kota akasin haka, don Allah ina rok'on ka duk lefin danai maka ka yafemin Kar kayimin addu'ar da zata kaini wuta"

"Karki damu kinji "

"Yawwa na gode sosai "

"Hhhmmm"

"Ya naji kace hmmmm"

" ba komai kawai wani tunani nayi "

"A kaina kayi tunani"

"A'a ba akanki bane"
"Ummm hmmm"


Haka naita jansa da hira har kusan rabin awa sannan mukai sallama, nai juyi kan gadon ina mirmishi tare da rungume pillow na dad'e ina tunani sannan na taso na fito,ina shiga d'akin sweety tace "ina kika shige ne Aunty Nah"

"Hhhmmm ina wancan d'akin ne"

Daga haka na haye gadon ina addu'ar bacci.



Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakaninmu kullum zamuyi waya na kusan 30 minutes kuma kullum nike kira ko yace min in kashe sai ink'i ince mai inada kud'i, sai dai kawai yayi dariya yace hajiya wai wake samiki kati,nima dariyan nake nace mai kud'in da yake samin ne a account da wanda Abba Ke bani nake sa credit d'in dashi. A haka muka k'ara shak'uwa da juna har ya rage yau saura kwana uku a kama azumin Ramadan munata shirye shiryen shiga wata me alfarma.

Yauma kamar kullum da dare muna waya nai k'asa da muryana nace "Mijinaaa!"

"Um mata ta"
Ya amsa karon farko da nake kiransa da sunan ya tab'a amsawa ,
Wani bala'in dad'i naji ya lullub'eni nai mirmishi nace " ina son ka bani pic d'in ka inga yanda ka koma"

Dariya yace "me zakiyi da pic d'ina?"

"Um ina son in ganka ne mana"

"In kina son ki ganni ki duba pic's d'in weeding d'inmu mana kita kallo na"

Shagwab'e murya nai nace "um um nidai na yanzu nakeso ka turo min"

Wani yarrrrr yaji ajikinsa shima k'asa yai da murya cikin nashi salon da yake sace zuciyoyin mata yace" To bud'e Datan ki in turo miki ta WathApp ko"

"OK bari in bud'e"

Kashe wayan yai ni kuma na bud'e data na, bayan kusan 5 minutes naga pic's sun fara shigowa kusan guda goma ,bayan sun gama bud'ewa na zubawa wani guda d'aya ido ina kallon yanda yai kyau sosai a pic d'in d'an mirmishi nai araina nace " hhhmmm gaskiya ba k'arya mijina ya iya d'aukan wanka na Dad'e a duniya banga namiji daya iya dressing kamar mace Irin saba,duk da duk y'an uwansa sun fishi kyau nesa ba kusa ba amma kuma duk yafisu farar fata don shi fari ne sosai da sosai gashi yanada yawan gashi a fuskar shi wanda sajensa ya kewaye duk fuskar shi harda quarter million yake dashi, wanda hakan yasa shi yin kyau wanda a zahiri in magana ake ta kyawawan maza bazai zamo sahun farko ba sai dai a sahu na biyu kona uku amma farar fata da wadatar saje da iya tsantsar gayu yasa yake tafiya da hankalin mata da yawa,ciki kuwa harda ni tunda gashi nima yanzu ya janye hankali na gaba d'aya.

Bayan na gama kalla na darje kallon abuna sannan na sake kiran wayar yana d'agawa yace "nai zaton ma Kunyi bacci fa"

"Hhmmm ya za'i nai bacci kawai na tsaya kallon ka ne handsome guy, ka k'ara girma kayi kyau sosai "

"Allah ko?"
"Um da gaske"

"Ok to nima turomin naki ingani ko kin k'ara girma kema"

"Um um ni ina nan yanda nake"

"Ban yadda ba turomin in gani"

"Nayi missing duk pics d'ina fa yanzu"

"To ki d'auka yanzu ki turomin"

"Ummm yanzu fa night Wear ne a jikina ka bari gobe zan turo maka in na d'auka "

"Um um ban yarda da wannan wayon ba ni yanzu nake son ki turomin"

"Tom bari in d'auka ma"

"OK ina jira kuma in kika turomin wani ba na yanzu ba zan gane"

Mirmishi kawai nai na kashe wayan, tashi nai naje gaban mudubi na kalli kaina,naga komai normal sanye nake da riga wanda iya kacinta cinya kasan cewar ana tsananin zafi, bata da hannu sa D'an siriri kuma wuyanta bud'ad'd'e ne don haka saman k'irji na Duk a waje suke, zanin Dana d'aura kan rigar na ajiye a gefe, d'aukan wayan nai na fara buga selfie har biyar sannan na tura mai suna shiga naga ya bud'e bayan kamar 3 minutes na sake kiran sa nace "Sun shigo ko?"
"Um"
Kawai naji yace nima shiru nai jin yai shiru,jin shirun yai yawa yasa na sake magana "ya naji kayi shiru ko bacci kakeji ?"

Cikin wata dasashshiyar murya naji "da wannan rigar kike kwanciya kuma tare da sweety?"

"Um um nifa yanzu ina bedroom d'ina ita kuma tana d'ayan d'akin,kuma in zanje d'ayan d'akin ina d'aura zani".

" ok, kin cemin biki k'ara girma ba kuma ni naga kin k'ara girman".

Jin yanda muryanshi take a shak'e nasan yana cikin wani yanayi don haka na k'ara mak'ale muryata yanda zata k'ara Jan hankalin sa nace " kowa fa haka yake cewa na rame amma kai kace na k'ara girma"

"Um ai ba duka jikin naki ne yake k'ara girma ba wasu wajajan ne ya k'ara girma".

" hhhmmm tom ina ne ya k'ara girman"

A'a bazan fad'a ba amma nidai naga inda ya girma"

Bubbuga k'afata na fara yi kamar yana kallo na cikin shagwab'a nace "Allah Allah nidai ka fad'a min ko inma kuka".

Y'ar dariya yai yace " zan fad'a miki sai gobe,Kinga yanzu dare yayi sosai biki barni nai bacci ba".

"Tom gobe ko ina kira shi zaka fara fad'a min kaji ".

" OK karki damu,good night "

"Sweet dream"

Kashe wayan nai ina jin wani dad'i yana ratsani na lumshe idona ina godiya ga Allah lalle yanzu na fara tabbatar da soyayya ta cikin zuciyar mijina".





Manage


Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🍑🍑🍑
🌸🌸 🌸🌸🌸🌸
*Y'AN ARABIC*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🍑🍑🍑🍑🍑🍑

*NA*

*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*


DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣7⃣



Kasancewar yau Monday yasa ban sami sukuni ba a school muka yini ina dawowa da ciwon kai na dawo don haka ina wanka nai sallar magriba abinci ma Sama Sama naci nasha magani, anayin isha'i na kwanta ba jimawa bacci ya d'aukeni.


B'angaren uk kuwa yau duk da kewan ta ya yini lokaci lokaci hakan shiga cikin gallery d'in sa ya kalli pic's d'in sannan yayi mirmishi don haka yau yake Allah Allah lokacin kiran yayi ya k'ara cewa ta turo sabon pic kuma da kayan bacci yasha kallo ya more, amma abun mamaki dai dai lokacin da kiran ya sab'a shigowa yayi har ya wuce da kusan awa Guda don haka ya fara shiga damuwa meya faru yau bata kirashi ba har yanzu,zaman jira yake tayi har sama da awa biyu yaga kiran bai shigo ba,yanke shawarar kiran yai,amma abun mamaki kira kusan sau hud'u yai amma ba'a d'aga ba,shi kuma har ga Allah yau a matse yake da son yin muryar, sake kira yai shuru don haka ya kira wayan sweety bugu d'aya ta d'aga tana gaishe shima bai tsaya amsawa ba yace "Ina Khadeejah me take inata kiran wayar ta bata d'aga ba"
" tayi bacci wlh yau tunda wuri kanta ne yake ciwo ".

Ji yai zuciyar sa ba dad'i a dak'ile yace " shike nan ki mata sannu"



Ni kuwa ban san abunda ake ba don sosai nake jin dad'in baccin, wanda ban farka sai kusa da asuba shima fitsari ne ya farkar dani, ganin kuma an kusa asuba yasa na d'auro alwala nazo na fara nafilfili har aka kira sallar asuba,bayan nayi na zauna nai azkar har wajan k'arfe shida da rabi sannan na tashi na fara shirin had'a abunda zamuyi break dashi bayan na d'ora girkin na wuce toilet donyin wanka ina cewa sweety data tashi yanzu "ki kula mana da girkin zan shiga wanka".



Saida mukazo yin break sannan sweety Ke fad'amin Broth d'in ta jiya nata kira na ina bacci, D'an zaro ido nai nace" nifa nama manta da wayan wlh don jiyan nan na gaji, kuma araina nake cewa in lokacin yin wayan mu yayi zan tashi"

Dariya tai tace "um kullum sai a shige d'akin aita soyewa in

Please Login or Register in order to submit comment