Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fita yana tunanin aransa,wasa wasa fa yarinyar nan ta iya dressing ba tun yanzu ba tun had'uwarsu ta farko ya kula da iya adonta don dai kawai tana b'oyewa ne amma yanzu daya Ke zaune da ita yake ganinsa a zahiri,

Bayan na gama zuba mai d'an waken na zuba maihad'ad'd'an kunun ayan danayi wanda yasha madaran ruwa sosai da dabino da kwakwa,
Kurb'a d'aya yaiwa kunun ayan ya kad'a kai cikin gamsuwa da d'and'anon da yayi masa, bayan ya gama cinye na gabansa kawai naga yaja wanda Ke fagana yaci gaba daci ,d'agowa nai na kalleshi amma shi ko ajikinsa,ganin haka yasa na tsiyayi kunun ayan inasha tare da tunanin shi kullum in ina zuba mai abinci sai yace ya isa, kuma inya gama sai ya k'ara, daman ni d'an wake ba cimata bace don wanda ba zuba dinma ina fara ci ya gundureni sai gashi shi ya d'auke yana sank'amewa, banda ma shi da abinsa d'an wake ai bai dace da abincin dare ba,ina wannan tunanin naji maganansa" ki shirya in anyi sallar isha'i zamu je unguwa" daga haka ya mik'e,
Ni kuwa a raina nake tunanin To ina kuma zamuje,Hhhmmm lalle UK ya fara sauk'i.



Kwalliya na canja bayan nai sallar isha na shirya cikin doguwar riga y'ar k'asar dubai wanda k'irjinta zuwa cinya yake cike taf da adon stones masu d'aukan ido, ruwan powder ce nai rolling kaina da Vail fari kalan stones d'in rigar, nasa takalmi da fari da pors fara,ina fitowa parlourn shima yana fitowa daga d'akin sanye da t-shet blue a jikinsa da trouser baki k'afansa sanye da takalma sau ciki bak'ak'e, kallo d'aya nai mai na kauda kai, gaba yai tare damin nuni da hannu alamar muje , saida na kulle ko ina sannan na biyo bayansa a lokacin har yaiwa motan key, bud'e gaban nai na shige motan da sallama d'auke a bakina kamar nutse
d'abi'a ta take kullum zan shiga motan tasa sai nai mai sallama wata rana ya amsa wata rana ya fuske,

Mun hau titi sosai ya kunna music yana ji tare da kai ba tare daya tanka ba,ni kuwa idona naga titi ina d'an kalle kalle na, gani nai munyi parking motar bakin wani zazzafan Stor bayan ya gyara tsayuwan motan muka jera muna takawa a nutse

Cikin store d'in muka shiga kai tsaye yaja kwandon sa kaya ya turo gabana, muna tafe yana zab'ar abubuwa yana sawa ciki ,abunda ya d'auremin kai yanda yake zab'ar abubuwan mata kama daga turaruka,pard, powder sabulai da sauran abubuwan buk'atar mata, daga nan mukai b'angaren abubuwan ciye ciye da sannan kayan amfanin gida cika bayan mota mukai da kaya wanda duk kusan nawa ne shi abunda ya d'auka kad'an ne, duka shi ya zab'i komai don yace in d'auki abunda nakeso bace um um dan haka yaita jidar min da kansa, daga nan mukai wajan shan ice cream muna zaune kan kijeru ya bada akai mana oder d'in kayan shaye Shaye,muna zaune nan bame cewa da wani uffan hankalinsa naga wayansa wanda ni kuma nake wasa da d'an cokalin shan ice cream d'in,sai dai lokaci zuwa lokaci yakan d'ago mu had'a ido, mun D'an dad'e yace in tashi mu tafi.

Sannu a hankali muke takowa zamu fita a gun wani Alhaji ya shigo yana waya hankalinsa kuma naga wani b'angaren wanda hakan yasa bai kula ba ya bangajeni abunda ya haddasa min yin baya zan fad'i da sauri ya tallafoni zuwa jikinsa yana min sannu shima mutumin tsayawa yai yana min sannu tare da ban hak'uri,wata Irin gigitacciyar tsawa mukaji ya karad'e gun,ya gade rai matuk'a yana hararan mutumin "kai wane Irin bagidajen mutum ne Mara lissafi kawai kazo ka bangaje min mata ta kamar baka gani haba wannan ai sakarcine mutttssss"
Binsa mutumin yai da kallo yana jin wani b'acin rai shi za'a fad'awa wannan kalmomin ma don haka cikin fishi yake fad'in "Kai kasan ni waye kake fad'amin wannan Kalmar ni kake cewa sakarai lalle zaka gane kuranka,tunda kai jaki ne ban Sani ba na bige ta kuma na bata hak'uri shine zaka zageni ,har meye jikin matar taka zaka zageni kanta in ta shiga cikin mata ma baza' a ganeta ba.. . .

Kau kakeji ya d'auke mutumin da mari yana huci kafin me shima mutumin ya rama wani wawan naushi ya kaiwa mutumin a baki nan da nan jini ya b'ata mutumin wanda zuwa lokacin mutane sun cika gun suna bada hak'uri, ni kuwa jikina banda rawa ba abunda yake na rik'e hannayensa ina " don Allah ka barshi kazo mu tafi gida" ganin mutumin ya tunkaromu da k'arfinsa yana kwacewa daga ruk'on da mutune suke mai ruk'umk'umeshi nai ina kuka don shima k'ara tunkarar mutumin yake yana danna mai zagi.

Security d'in wajan ne suka k'araso suna tambayar ba'asi wani da akai komai a kan idonsa yake larabta musu nan dai sukaita bawa kowa hak'uri sukaja mutumin suka fita dashi muma muka fita zuwa gun motar mu.
Tunda muka d'au hanya yake sauke ajiyar zuciya me cike da tsantsar b'acin rai, ni kuwa sai matse D'an guntun hawayena nake yi, a haka muka isa gidan baiko bi takan kayan ba ya fice ya barni a motar, taimakon ma'aikatan gidan na naima sukaita kwaso min kayan zuwa parlour bayan sun gama nai musu godiya tare da rufe k'ofan nai cikin d'akina, zama nai bakin gado ina tunanin abunda ya faru lalle rashin hak'urin UK ya b'aci jibi yanda lokaci guda ya koma kamar wani horo jijiyoyin kansa Duk suka tashi, idonsa yai jajur kamar gauta,

To wai ma duk akaina ya shiga wannan yanayin, gaskiya ya kamata inje in bashi hak'uri don yanda yake furzar da iska bana tunanin zaima iya yin bacci yau d'in nan gaskiya gara inje in bashi kahuri tunda dai Duk akaina ne hakan ta daru, daga wannan tunanin na mik'e zuwa toilet don shirin bacci .


Shi kuwa a can d'akinsa yana kwance kan gado dafe da kansa ya sakko da k'afafunsa k'asan gadon don ko takalmansa bai cire ba,ya dad'e ba'a b'ata masa rai Irin haka ba an zageshi an wulak'antashi gaban mutane, yayi mari an rama,hannu yasa ya shafo began fuskarsa yana tab'o inda aka mareshi d'in, wai duk akan wannan yarinyar aka mai wannan wulak'ancin shi dama ya Sani bai fita da ita ba,kodake gaskiya dole ya kare hakkinta tunda dai sunanta matarsa. . . . .

A hankali na turo k'ofar cikin shigar riga da wando na Jean's kaiba ba d'an kwali na gyara gashina tsaf sai d'aukan ido yake ,d'an bud'e ido yai ya kalli ni ya maida ya rufe a ransa yana jin wani Abu na mintsininshi duk da shi bai fiye yawon sha'awa ba kuma fidda tairaicin mace bai sashi jin wani Abu amma bai san me yasa ba cikin kwana biyun nan yarinyar nan take fuzgarshi kodan ita d'in halalinsa ce . .
A hankali na k'araso bakin gadon na tsugunna ina zare mai takalman dake k'afarsa nakaisu ma'ajiyarsu na dawo tare da zama gefanshi, na k'ara sanyaya muryata na fara magana " Don Allah kayi hak'uri kaji naga ranka ya b'aci da yawa kuma duk nice sabadi kayi kahuri kaji"

Shiru yai bai magana ba kuma bai bud'e idon ba, na k'ara narkar da muryata kamar zanyi kuka" in ka tafi kana cikin fishi da b'acin rai hak'ik'a banci nasara ba, Kaga mutumin nan maybe shi yama manta amma Kai ya barka cikin b'acin rai,zaka bar gida gobe kamata yai ace yanzu kana cikin nishad'i da tunanin rabuwa da gida ba tunanin wancan banzan mutumin ba,don Allah ka fiddashi cikin ranka kaji"
Bud'e idon yai a hankali ya furta "karki damu "

"To yanzu me kake buk'ata in kawo ma"

"Ba wani Abu jeki kwanta"

Shiru nai kamar bazan tashi ba can dai na mik'e har nakai bakin kof'a naji yace "an shigo da kayan nan kuwa ?"

Kaina na gyad'a alamar eh
" OK ki ciromin duk abinda yake nawa ciki "

Fita nai na dudduba kayan ba wasu abubuwa bane masu yawa nashin , dana koma zaune na sameshi yana b'alle rigan jikinshi tsugunnawa nai ina mik'a mai ya amsa ya aje bakin gadon yana fad'in "ki d'an had'amin ruwan wanka pls"
"OK "

Bayan na had'a mai ya shiga ni kuma na koma kitchen na d'ebo abubuwan dana shirya mai, d'anbun nama ne da cake, dunout,meat pai ,coconut biscuit
Yana fitowa yabi kayan da kallo sannan ya wuce gaban mirror ya goge jikinsa tare da shafa mai da turare yazo ya zira rigan bacci,duka kaina na k'asa ina wasa da hannuwana, zuwa yai ya zauna gefan gadon baicemin komai ya fara duba wayansa, k'oka'rtawa nai nace "um daman snacks ne na maka ko zaka tafi dasu sabida shan tea ".

Sosai ya kalleni yana mamakin to me zaiyi da wad'an nan abubuwan acan kuma shida yake odar d'in abinci bashi da wata matsalan abinci ko abinsha, amma wani saahin na zuciyarshi yaji dad'i don koba komai ta nuna kulawarta gareshi kuma yana son a nuna an damu dashi, kawai sai ya tsinci kansa dayin murmushi yace " Tnx sannu da k'ok'ari"

Nima mirmishin nai nace " ba komai hak'k'inane "
Cikin ransa yace wai duk wannan ma cikin hidamar aure ne,lalle mata sunga ta Kansu,amma a zahiri sai yace "ki had'aminsu cikin wannan k'aramin truly back d'in tunda duk anyi raffing Nasu"

Tashi nai na d'auko jakan nasa ledan ko wanne na jera bayan na gama na d'ora kan jerin jakunkunan dayai parking a gefe, sannan na juyo ina cemai "To saida safe in Allah ya kaimu"
"Tnx good night"

Bayan fita na ya dad'e za'une yana nazarin da tunanin d'abiun na.

Haka Nima a can d'akina bayan nasa kayan bacci kawai juyi nai tayi a gadon ina jin farin cikin da ban san dalili ba kuma ina jin daman mu kasance tare har wayewar gari, gaskiya zuciyata ta fara zurfi cikin soyayyar mijina wanda Ke zaune dani a dole kuma don biyayyar mahaifinsa,har yanzu bai d'aukeni matarsa ba ma balle ya fara sona cikin ransa . . wani mirmishi ne ya sub'icemin dana tuno kalmarshi ta d'azu "kai wane Irin bagidajen mutum ne Mara lissafi kawai kazo ka bangajemin mata ta "

Tsintar kaina nai da sakin wata y'ar k'arar murna tare da rungume filo ina jin araina lalle mijina ya fara sona kamar yanda Allah ya fara jarrabata da k'aunarsa cikin y'an kwanaki, juyi kawai nake kan gadon ina hasashshen duk randa Allah ya tabbatar da soyayya tsakaninmu zanyi yak'i da wasu d'abiunsa masu yawa wanda basa cikin d'abiar cikakkan musulmi lalle zan dage da addu'a Allah ya sanya soyayyta cikin ziciyar mijina tunda dai yanzu shine majinginata don haka zanyi adduar samun farin ciki cikin rayuwarmu.








*Amin* *uzuri* *amin* *afuwa* *ina* *busy* *nayi* *bikin* *babbar* *k'awa* , *Aminya* *ina* *matse* *gajiya* *kwana* *biyu* , *muna* *Neman* *addu'arku* *na* *Neman* *alkairi* *da* *zaman* *lfy* *ckn* *auransu* *sa* *samun* *zuri'a* *d'ayyiba* .πŸ‘πŸ‘πŸ‘





Taku ce
Layuza kabir AdamπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣3⃣



Bayan sallar asuba nai azkar ina zaune kan sallaya ina addu'a na maida hankalina sosai ga rok'on ubangiji na ya tsaremin mijina daga fitinar dukkan wata mace Allah ya tsaremin mutuncinsa da addininsa Allah ya bashi sa'ar wannan tafiya,na d'au tsawon lokaci ina addu'oi na Shafa tare da tashi na fita kitchen don nema mana abun break fast, k'osai nai mai kwai tare da kunu sannan nai farfesun kayan kan sa, wanka nai d'an gaske cikin riga da siket English Wear masu jikin roba inda rigan take da bud'ad'd'e har k'irjina na iya fitowa sai skate d'in shima yayi tytn nawa sosai,wata hula na saka wanda gabanta yake kamar ribbon duk ansa stones kalan kayan itama red color na wadata jikina sosai da turaren humra ina fitowa parlourn na sameshi tsaye yana waya ya juya baya yana kallon k'ofa, takuna ne yasa ya juyo ya dubeni a sannan kuma ya kashe wayan tare damin wani kallo da bazance ga fassararsa ba,d'an duk'awa nai ina fad'in "barka da safiya "
Saida ya zauna kan kujeran sannan ya amsamin da cewa "kin tashi lfy"
"Lfy qlau Alhamdulillah"
Na amsa ina nufar table don had'amai abinci, biyo bayana yai ya zauna yana cemin 'ki zubamin sosai don yau da yunwa na tashi"
"Um hmmm " Nace ina k'ara zuba mai ,
Bayan na gama had'a mai komai na koma na zauna ina kallon shirin da akeyi a tashar m.b.c 3 daga inda nake ina iya kallon dai TV d'in tana saitin dining area d'in, bayan kamar 20 minutes naga ya mik'e yana cewa "bari naje na dawo ina zuwa "
"To a dawo lfy Allah ya kiyaye ganga"
"A'a ai bama nisa zanyi ba zanje gun Abba ne"

Mirmishi nai araina ina cewa wato inba nisa za'ai ba ba'a addu'a kenan hhmmmm , rakashi nai har bakin k'ofa bayan ya fita na rufe k'ofan tare da wucewa d'akinsa na gyara maishi tsaf ina tunani araina shike nan yau me d'akin bazai kwana ciki ba sai wata nahiyar kuma nan da nan naji wata irin kewansa ta kamani tun kafin ya tafi d'inma, had'a dukkan unders nashi nai na wanke su tas tare da turare d'akin da turaren wuta d'an mai duguri, ina shigowa d'akina naji ringing wayana kafin na d'auka ma ta katse dubawa nai naga 3 miss call a ciki a sannan wani kiran ya shigo na d'aga da sallama cikin k'ara sanyaya muryata "Ina kika shiga inata kira shiru"
"Ayya kayi hak'uri ina gyaran d'akinka ne wayan kuma tana bedroom dina "
"OK kizo Abba na kiranki"
"Tom ganinan "

Hijab na d'auka babba nasaka har k'asa me hannu na rufo part d'in,

Shi kuwa bayan shiganshi gun Abba bayan sun gaisa Abban Ke k'ara tambayarsa ya shirin tafiya y'ar dariya yai yace " Abba shiri kam an gama komai"
Yace "jiya da dare naso in ganka kuma Salis yacemin kun fita "
"Eh mun d'anje store ne nai mata d'an siyayya kuma bamu shigo da wuri ba"

Mirmishi yai cike dajin dad'in ganin sauyi cikin rayuwar tasu,kana ya nisa yace "Tom daman na kiraka ne don inji me kake buk'ata kuma in baka kud'i ka zubawa ita Khadijan a account nata wanda dai zata jima tana amfani dasu "

"Abba ai akwai kud'i sosai a guna kasan sun turomana fa da kud'i don muyi hidiman tafiyan dasu kuma account d'ina ma akwai nauyi sosai,na ware wasu kud'i sosai daman yanzu zan bata ta rik'e a hannunta kuma duk wata zan rik'a tura mata kud'i account"

Jinjina kai Abban yake cike da tsantsar jin dad'i yace "masha Allah hakan yayi Daddy nah Allah yai maka albarka ya saka maka bisa biyayyan da kai min Allah ya baka zuri'a ta gari".

" ameen ameen " kawai yaketa fad'i
"tom ka kiramin khadijan tazo yanzu ina son ganinta "
Shine kiran dayamin yanzu.

Da sallama na shiga parlourn na k'ara sa k'asan kujerar Abba na zauna kaina a k'asa nace "Abba barka da safiya an tashi lfy "

"Lfy qlau Nana Khadeejah ya gidan "
"Lfy lau Abba"

"Masha Allah hakan nakeso najinaji, to ya shirye shiryen tafiyan me gidan kuma " ya fad'a cikin mirmishi
Cikin jin kunya sosai nace "Alhamdulillah Abba"
"Madallah ,gobe iyanzu dai Daddy yayi nisa damu ko"
Wannan karon shiya amsa yana y'ar dariya yace "Abbah ai iyanzu baku fara missing d'ina ba sai zuwa kwana biyu ko"
"A'a komu bamuyi kewarka ba ai matar ka zatai yi "

Ba kunya wai ya lek'o fuskata yana cewa " Nahna wai zuwa 24 hours kin fara missing d'ina"?

Nidai kaina na k'asa duk kunya ta rufeni ina mamakin rayuwar Irin ta gidan cike da tsantsan boko ba ruwansu da wani jin kunyar d'a ko suruki, mirmishi kawai nake ina wasa da hannayena,

Nan Abba yai gyaran murya ya koma serious ya fara magana "Abunda yasa na kiraki Daman don na k'ara jan hankalinku kan hak'uri da juna da yanayin rayuwa musamman yanzu da zakuyi nesa da juna kuma wata rayuwar zaku k'ara shiga dole sai kun k'ara hak'uri musamman Ke da kike mace Khadeejah dole sai kin kai zuciya nesa kin k'ara ninka hak'urinki kinji, kusa aranku kunyi nesa da juna bukuyi nesa ba abun nufi Ku rink'a jin Kuna tare koda yaushe, ki rik'e amanar auranki kaima ka rik'e amanar matar ka,Ku mutunta junanku ko Kuna nesa ko Kuna kusa,Allah yai muku albarka biyayyar da kuke mana Allah ya baku masu yi muku "

Duka amsawa mukai da "ameen"

"Khadeejah in kinada wata matsala ki sanar mana yanzu kinji "

"A'a Abba ba komai wlh "
"To shikenan indai kinada wata damuwa dai kamar koda yaushe ina fad'a miki ki sanar dani kai tsaye karki damu ni gurbin Mahaifi nake a gareki kinji"

Gyad'a kai nake alamar gamsuwa da maganar, nan dai yaita mana nasiha daga nan suka shiga hira zuwa jimawa kad'an yace "Toku tashi kuje Ku k'arasa shiryawa ko"

Mik'ewa mukai a tare muna mai sallama.


Muna shiga part d'inmu na cire Hijab d'in na d'ora kan kujera zan wuce kitchen don yin wanke wanke, aikina nake a sannu Sannu naji alamar mutum a bayana d'an juyawa nai ai kuwa na ganshi tsaye ya hard'e hannuwanshi a k'irji ya tokara k'afanshi jikin k'ofa d'auraye hannuwana nai na k'araso kusa dashi a tausashe nace " Kana buk'atar wani Abu ne "?

D'an mirmishi yai kawai ya ruk'o hannuna zuwa d'akinsa,karo na farko daya tab'a rik'e hannuna a cikin gidan ,
Bakin gado ya zaunar dani ta bude bed site ya d'auko wasu bandir na kudi y'an dubu dubu Guda biyu wato 200k ya ajiyesu kan cinyata yana fad'in " ki rik'e wannan a hannunki sabida school da sauran buk'atu,komai na abinci akwai in nama da kayan miya ko kifi sun k'are bance ki siya da wannan kud'in ba ki fad'awa Abba in za'a kawo na gida za'a kawo miki kinji".

Gyad'a kai nai jikina duk yai sanyi idona harya fara kawo ruwa, ya kalli cikin idona yana girgiza kai "kuka kuma meye abun kuka kiyi shiru kinji "
D'aga kai nai ina had'iye kukan dakeson kufcemin,
"Jeki k'arasa aikin naki "
Mik'ewa nai na fita na shiga d'aki na ajiye kud'in sannan na k'arasa aikin duk jikina ba laka"

Sanda na dawo parlour na sameshi kwance kan kujera yana kallo zan wuce bedroom d'ina ya kirani "zoki zauna nan ki tayani kallon wannan film d'in "
K'arasowa nai inda ya nuna min kusa dashi na zauna ina jin wani banbarakwai kulawan dabai tab'a nunamin ba yau yake nunamin kodan zai tafi ne oho, tun ban fahimtar film d'in harna fara gane kansa donni ba masoyiyar kallon Indian film bane amma sai naji film d'in harya fara min dad'i tun ina zaune gefen kujerar tasa harna zame na d'an kwanta hakan yasa ya matsamin na kwanta sosai muna kallon ne tare da tattauna abunda Ke faruwa a film d'in in wajan dariyane muyi Har awa biyu cif ya k'are a sannan ne kuma aka kira sallar azahar na mik'e ina fad'in "bari in sallah in shiga kitchen me kakeso inma na lunch"
Shima mik'ewa yai yana mik'a yace "wasssshhh"
Y'ar dariya nai cikin dabara nace "kace wasshhh ni kuma bari in k'ara sa ma da La'ila ha illallah,Muhammadurrasulillah s.w.a, sai in samu ladan naka ko a raba mana tare".

Girgiza kai yai tare da fad'in " a'a baza kiyimin wayo ba bari in fad'i abuna da kaina,la'ilaha illallah Muhammadurrasillah"

D'an shagwab'e fuska nai nace "au ka k'wace Ladanka ko tom nima yanzu zan sami wani tunda zan dafa maka abinci "
D'akinsa ya shige yana y'ar dariya Nima na wuce nawa.

Bayan na shiga toilet na d'aura alwala harna shinfid'a prayer mat sai nai wani tunani don haka na fita zuwa bedroom d'in sa a hankali na tura k'ofan tasa a tsaye na sameshi ya shinfid'a prayer mat yana saka jallabiya alamar dai anan d'akin zaiyi sallar kamar yanda nai tunanin d'an mirmishi nai nace "em daman nazo ne nasan yanzu zaka tafi masallaci kuma ban Sani ba ko bazaka shigo da wuriba shine zan tambayeka me zan dafa maka "
Kunya yaji ta kamashi sai yaji bazai iya yin sallar a d'akinba don haka ya tsugunna ya nad'e mat d'in ya na fad'in "kimin sakwara da miyan agushi "
"OK ba damuwa"ina fad'a na juya na fita shima yabiyo bayana ya wuce masallacin, araina nake tunanin ko meyasa bai son yin salla cikin jam'i oho,
Ban tsaya doguwar addu'a ba nai kitchen d'in nan na fara had'a girkin cikin k'warewa da tsafta,awa biyu cif na shirya table d'in sannan na wuce d'aki na sakeyin wanka na shirya cikin doguwar riga na material d'in kin play k'irjin ya matseni sosai wanda hakan ya bawa k'irjina daman yin d'as cikin

Please Login or Register in order to submit comment